gani kala biyu dinkakku. Ya dubi
Mu'allim.
sai
"Ubangiji ya aba ka masu yi maka".
"Amin Abba, bara na ci abinci in huta
na yi masa wanka na sanya masa.
Sun sake sosai'cikin soyayyarsu, yau
shi ne ta ja shi wancan guri, gobe ta ja shi
wani guri, gidajen abinci kam kala-kala
Mu'allim ya sani, dawainiyarta gare shi ya
wuce misali, gabadaya ya sauya tamkar ba
shi ba, duk irin suturar da ta ke ra'ayin ta
ganshi a jikin da namiji ta siya masa, da
zarar ya dawo daga kamfani gidansu ya ke
wucewa, Hajiya Zainab tun tana tsanarsa har
ta watsar, kyawawan dabi'unsa ya sauya
mata kiyayyarsa musamman da yanzu ya
soma sauya rayuwar 'yarsu za ta iya cewa
Allah ya dora shi a kanta, duk wani tsiwa da
dagawa ta kan ajiye shi muddin suna tare da
shi.
58
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Yau tunda ya iso kimanin mintina
talatin yana zaman jiranta har ya soma
sha'awar tafiya daga can nesa ya hango ta,
ta taho sanye cikin kananan kaya, ta yane
kanta da dan siririn gyale kan nan nata ya
sha karin attach. Tana tafe da Kyar tamkar
tana tausayin kasa, a sace ya ke kalionta
yana jin kansa cikin wani irin nishadi,
Ubangiji ya yi masa baiwa da ya mallaka
masa Humaida. Yana sonta tamkar ransa,
haka kya sa wani fanin ya ke kasa tsawatar
masa a kan duk wani tabararta, ya lura wasu
halayyar tata sun riga sun zame mata jiki,
musamman tara farce, karin gasji, shagwaba
da rashin iya magana.
"Hello". Ta ce da shi a daidai, saitin
kunnensa.
Ya ji tsigar jikinsa na tashi
musamman da ya shaki wani shu'umin
turare ya lumshe ido ya bude ta zauna a
kujerar kusa da shi tana murmushi.
"Kina da kyau".
59
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ta shiga yi masa kallo mai lumshe
idanu kallon da a duk lokacin da ta ke masa
shi ya kan ji tamkar ya rungume ta. Ta daga
masa gira.
"ba ka gajiya da yaba mini?"
"Ta ya ya zan gaji da yabonki?"
Ta ce, "Amma ka san wani abu?"
"Sai kin fada".
"Wallahi Mu'allim ka fi ni kyau, don
haka na ke kishinka, ina yi maka kallon fure,
ba zan taba hin kunya ba yayin da na nuna
wa duniya mijina, don haka na сe KА
AURE NI”.
Ya so ya yi mata wata tambaya ya dai
basar, ya се.
"Ina rokon alfarlma mai ya sa ba za ki
adana kwalliyar nan ba har sai kin je
gidana? Wannan kwalliyar ni ne kadai ya
dace na gani".
"Haba ai a gidanka kuma ba zan yi
wannan shiga ba, akwai irin shigar da na
tanadar maka".
60
KA AURE NI=2
Farcenta ta ga yana kallo.
BILKISU H.MUHD
"Ba ka son wayewa, ni a ckikinta na
taso, domin ba haramun ba ne. To ma me ye
wayewar?"
Ta daga hannu tana kallon faratanta.
"In yi wanka, in ci abincin da na ke
so, in hau motoci masu tsada, mai kuma
matsalata? Ji na ke yi wannan ita ce
wayewar ko ba su ba ne?"
Tunda ta soma maganar ya kasa janye
idanu daga kanta har sai da ta bushe masa
ido, ta kai hannunta za ta riko nasa, ya yi
saurin janyewa.
"Please, sorry Mu'allim". Ta ce.
Ya sake dubanta.
"Kada ka dauki rike hannu a matsayin
wani abu daban, na kan rike hannun
abokaina, wannan ra'ayina ne, so kada ka
damu".
Ya yi murmushi kawai.
Mustapha ya zo wucewa ya yi masa
sannu da zuwa.
61
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Amma kuna yanayi da shi".
"Uhm haka a ke cewa, kanin Dad ne".
"Kaninsa ne?"
"Eh, kana Ummaki ne?"
"A'a ba na yi, ni zan wuce".
Ya mike ta rufa masa baya. A harabar
gidan suka hadu da Injiniya Sunusi.
"Mu'allim da ma kai na ake zaman
jira, ga wannan makullin”.
Ya mika masa, ya durkusa ya karba.
"Motarka ta iso".
Gabadaya kansa ya kulle. Injiniya ya
fahinci hakan, ya ce.
"Ina nufin mota ce na siya maka,
yanzu haka da ita za ka wuce gida".
"Wow! Dad thanks".
Ta rike hannunsa tana murna. Ya
nuna musu motar, a gaban Dad din ta janyo
hannunsa.
"Taho mu je".
62
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Godiya ya dinga rangadawa ta ja shi,
Injinkiya na yi mata dariya ko a jikinsa
kama hannun kato da 'yarsa ta yi.
Hakika talauci bai yi ba, ji yadda
Mu'allim ya sauya, tabbas 'yarsa ba ta yi
zaben tumun dare ba, ta samu namiji tamkar
da dubu. Ya gama yi ta ko'ina.
Ta bude masa motar tana nuna farin
cikinta, hannunsa nade a kirji.
"Dad ya siya maka mota mai kyau
kamar kai Dad ya san duk abin da ya dace
da kyakkyawan mutum. Okey, shiga ka
tafi".
Har lokacin Ummaki ya kasa sakinsa,
yana jin komai tamkar a mafarki, da kanta ta
karaso gabanshi neman riko shi ta ke yi,
haka ya san ya yi saurin shigewa motar,
haba wani sanyi da kamshi ya ji ya dinga
rige-rigen ratsa shi. Ya ji wsani nishadi ya
rufe shi, ta rufe masa kofar tana daga masa
hannu.
63
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
A can gida Malam Musa da Hajara
sun dunguma kofar gida kallon mota tare da
sanya albarka.
"Abba ai shiga za ku yi mu zaga gari
da ku".
"Ba shakka Malam kanaji fa?"
"A'a Hajara ina ni ina shiga wannan
babbar mota? Ai sai yara".
"Malam gaskiya fa yaro ya fada
shigarmu shi ne sanya albarka".
"Sai dai ke ki je in ba dole ba ba son
shiga mota na ke ba, kin fi kowa sani ina ba
so ku ke ku dawo da ni magashiyan ba".
"To ni kam zan saka albarka".
Tuni ta shige motar, Malam na faman
yi musu tsiya, ta kame a gaban mota tana jin
wani matsanancin farin ciki na ratsa ta. Ba ta
san sa'adda ta fashe da kuka ba.
A hankali ya gangaro gefen kwalta.
"Umma me ke faruwa?"
"Mu'allim kukan dadi na ke yi, ashe
za mu sami irin wannan 'yancin? Ubangiji
64
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
na gode maKa. Wallahi ko yanzu na koma
gare ka zan mutu ina mai farin ciki da
godiya yau burina ya cika, Ubangiji ya yi
maka albarka"
Ta dinga jero masa addu'a bai maida
ta gida ba sai da ya yi mata soyayya sama da
dubu hamsin tukunna suka dawo.
Da kanshi ya taya ta suka share mata
daki, ya shimfida mata leda tare da alwashin
zai sauya musu gida.
Su kansu su Adnan sun san abokinsu
ya samu, domin sam abinshi ba ya rufe masa
ido, musamman zai siyo kaji ya sa
Ummansa ta dafa musu a zuba su kwashi
gara, alheri tsakaninshi da su ba ya yankewa
haka ya sa a kullum suke kara kwarara masa
gwiya.
Yau ma kamar kullum suna zaune a
shagon shi Adnan ya kalli yadda ya sauya
komi na shagon, ya с
65
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Lallai komai na son gyara, ka ga
shagon nan tamkar ba shi ba, wallahi
abokina ka gama shan kwana".
Mu'allim ya kada kai, "Ka san wani
abu yanzu ji na ke yi ina son na juya fiye da
wannan dukiyar, yanzu ko da za a janye
dukiyar zan iya ci gaba da sonta
"A'a abokina kada ka zafafa saboda
gudun matsala, dole fa ka dinga dannewa,
haka ne zai sa ka zamo jajirtacce muddin ba
haka ba kai ne za ka zamo macen bayan an
yi aure, duk runtsi ina son ka dinga nuna
mata kai ne shugaba, in ka bari ta samo
lagonka za ka gama yawo, don na ganta 'yar
rainin hankali ce".
Gabadaya suka yi dariya.
"Adnan abin kuma har da sharri?"
Ya ce, "Sharri ko gaskiya?"
"Zan fa gaya mata?"
"A'a rufa min asiri".
*** *** ***
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Sister, kina ganin yadda gabadaya Alhajinku ya maida hankali kan wannan kan
ta wayen kina kallo har da saya masa waya,
kina kallo har da saya masa mota? Ni ka
mina cikin gidan nan bai taba siya min ko da keke ba".
"Amma da bai saya maka ba wacce
irin mota ce ba ka hawa? Babu motar da aka
yi maka shamaki da hawanta, ka gode wa Allah mana".
"Sister, ko yau Alhaji ya fadi ya mutu
na yi imani daina hawa zan yi, ko kuwa bai
hana ba wannan fitananniyar Humaida za ta
hana..."
"Dakata Aminu me ka ke fadi ne?
Humaida diyata ce ba ta kishiya ba, ka budi
baki ka kira ta fitinanniya a gabana? A
gaskiya ka sake da yawa
"In ita 'yarki ce ni kuma kaninki ne,
ina kuma da ikon da zan gaya mata ko me
ye".
67
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Ba ka da shi, domin ba kai ne ka
haifa mini ita ba".
"Okey, daure mata gindi shi ya sa in
rashin mutuncinta ya tashi a kanki ya ke
karewa, kuma za ta ga ni sai na kunno mora
wutar da za ta kasa kwacewa, ba dai ita
soyayya ba? A tafin hanuna ta ke, na san
yadda mahaifin yaron ya ke kinta za a yi
auren in gani".
Ya fice yana faman surutai marasa
kan gado.
Hajiya Zainab ta hada kai.
"Tabbas ba ka hayyacinka, zan daga
maka kafa sai ka dawo daidai in karta maka
rashin mutunci, wanda za ka ji a jikinka,
yanzu ko da na yi ba za ka fahinta ba, dan
iskan karya".
Shi kam Adam tunda Mu'allim ya
shiga rayuwar gidan ya soma tausaya masa,
ko da labarin siyen motar ya riske shi ya yi
mamaki, kodayake ya sani akwai abin da
Injiniya ya taka, ya kan yawaita yi wa
68
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Mu'allim addu'ar tsira daga sharrin 'ya'yan
nasa sau tari in Mu'allim ya zo ya kan ji
tamkar ya tsare shi ya ba shi labarin mugun
hali na Alhaji, sai dai in ya dube shi ya akan
gano tsantsar son Humaida kwance a
idanunshi ya yi imanin ya riga ya yi nisa,
don haka kurum ya zamo dan kallo shi dai
yana gefe zai ga zuwan lamarin da
dawpwarsa, sai dai kullum fatan alheri ya ke
bin Mu'allim da shi.
Kamar yadda malam Musa ya saba
kafin ya tafi masallaci sai ya daura alwala a
kofar gida, yau ma hakan ce ta kasance a
can nesa da shi.
Mudansir da abokinsa, cikin daga
murya suke hira, abokinsa ya ceе.
"Gaskiya yaron gidan can ya sami
kudi, tabbas dare daya Allah kan yi bature,
kai ka ga motar da ya ke hawa?"
Mudansir ya ce, "Haka ne, amma ai
baban budurwarsa ne ya mallaka masa duk
69
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
wadannan abubuwan, ciki har da sama masa
aiki a kamfaninsa..
Abokin ya ce, "Haka ne, caf in ko
haka ne bai kyautawa kansa ba, ka ce shi
auren kwadayi zai yi?"
Mudansir ya ce, "Kai di bari, ba giringirin ba tai mai, in dai wannan mutumin ne
sharri ne zai biyo baya, muna nan za ka
gani".
Abokin ya ce, "Auren kwadayi babu
abin da ke biyo baya sai tsantsar nadama".
Malam musa ya ji wani jiri na dibarsa,
ya mike da kyar, masallacin da bai iya zuwa
ba ke nan, sai a gida ya yi sallah. Yana
zaune a kan darduma, magana ya kasa yi.
Hajara ta dire masa abinci shinkafa da miyar
naman kaza sai kamshi ya ke, na gama
girkin.
Ya dube ta.
"Ki dauke abincin nan ba zan ci ba, ba
zan sake ci ba har abada kin ji ko".
70
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ya fada cikin daga murya, ta dube
shi.
"Allah ya ba ka hakuri mai kuma ke
faruwa, ji na ke yi yanzun nan ka ce mini
kana jin yunwa in wannan abincin ne zai
dauke mini yunwa ta na muu, malam na shiga hudu, ka gaya min abin da ke faruwa".
"Yaron nan yana tare da wannan yarinyar".
Ta ce, "Yanzu har yanzu ba ka daina zarginshi ba?"
"Babu zargi, shi ne ya ke ba shi duk
wani abu da ju ja ga ya mallaka, yana kuma
aiki ne a karkashinsa".
Ta shiga tafa hannu.
"La'ilaha illallahu, yanzzu bain da
yaron nan zai yi mana ke nan?"
Ya tashi ya koma kofar gidan yana
jiran dawowar Mu'allim, har bayan sallar
magriba bai dawo ba, zuciyar Malam Musa
tamkar za ta fashe, a can nesa ya hango shi
yana tafe rike da manyan ledoji guda biyu.
71
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Da sauri ya mike, ya tsaya a dokin kofar
gida yana faman huci. Sannu a hankali ya
karaso.
"Sannu da gida Abba".
Bai ji ya amsa ba hakan ne ya sa ya
dube shi, ras gabansa ya buga.
"Abba lafiya, ina Kawu?"
Yunaninsa Kawun ne wani abu ya
same shi, kokarin ratsawa ya ke ta gefenshi.
Ya daka mishi tsawo.
ya ce.
"Ina za kaа?"
Cike da Ummaki ya се.
"Ciki zan shiga'.
Cikin kakkausar murya Malam Musa
"Da wannan kayan?"
"Abba ai kayanku ne na siya muku
don ku yi amfani da shi".
"To ka juya ka maida su".
Ya yi turus, "Amma Abba ban fahince
ka ba? Na ce ka juya ko ba ka ji ne?"
72
S
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ya durkusa, "Abba na tuba ban san
me na yi ba".
Cikin zafin nama ya kai hannu ya
cizge ledojin ya watsar da su, suka tarwatse
kayan shayi ne sai gasassun kaji da sabulun
wanka da na wanki. Yana huci ya ce.
"Daga yau ban lamunci ka shigo min
ko da kwallin shinkafa ne in ko ka kawo ko
da ba da sanina ba, ba zan yafe ba".
"Abba ban san me na yi ba, hukuncin
ya yi mini tsauri, ka yi hakuri na tuba".
Ya ce cikin rawar murya.
"Ka nuna mini ban isa ba, ka ci
amanata ka kuma tozarta ni, amma ba komai
akwai Allah".
Ya juya ya shiga gida; Mu'allim ya
mike cikin tsananin damuwa ya rufa masa
baya.
Hajara tsaye a tsakar gida fuskar nan a
daure tamau.
"Ina shakku a ce wannan Mu'allim
dina ne, Mu'allim mai jin tausayinmu yau
73
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
shi ne ya rikide zai zamo silar tarwatsewar
farin cikinmu. Ka yi hakuri ka sani Malam
ne kadai gatanmu, ba ni da kowa idan ka
haifar masa da wani ciwon ya ya zan yi? Ina
Kara umartarka ka gaggauta rabuwa da
wannan yarinyar, ka rabu da ita".
"Ummi ku yi hakuri ni ban ga aibun
yarinyar nan ba zargi kawai ku ke yi a kai ba
kamammiya ba ce, rayuwarsu ce a haka da
zarar na aure ta zan maida ta yadda ku ke
39
so...
Zuruf Malam Musa ya fito daga daki,
ta inda ya shiga ba ta nan ya ke fita ba.
"Wallahi Hajara da ya auri wannan
yarinyar gwara ya auri tantiriyar karuwa, da
ya aure ta gwara ya auri gawurtacciyar 'yar
fashi saboda na san wata rana Allah zai
shirye ta, in kuma karuwa ce mutane nawa
ne ke aurensu kuma karshe dalilin haka su
sami shiraya".
Ya dabi Mu'ailim da ido jajir.
74
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Wallahi da ka auri wannan yarinyar
gwara ka mutu, da na ga aurenku da ita
gwara na roki Ubangiji ya dauki raina, in
kuma ban mutu ba zan haukace, dzan dawo
kamat yadda kanina ya ke".
Kuka Mu'allim ya saka wanda bai san
lokacin da ya kwace masa ba.
"Abba ka sanar da ni, me suka yi
maka ka sanar da ni zan rabu da ita".
"Ni ne na haife ka ba kai ka haife ni
ba, zan iya tilasta ka a kan komai ba tare da
na gaya maka dalili ba, in har ni ne
mahaifinka dole ka bi abin da na ke so ko da
kuwa abin zai zamo ajalinka"/
Ya juya ya fice daga gidan.
Ya durkusa a gaban Hajara.
"Don Allah Umma ki gaya mini kada
ki boye mini, kada ki 6oye mini me
mutanen nan suka yi wa Abba ya tsane su
haka? A da na yi zaton irin abin da na hanga
na rashin kamun kanta ne ya sa ya ke nuna
kyamarsa gare ta, sai dai na lura ba haka ba
75
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ne. Umma ki nusar da Abba ba zan iya
rabuwa da ita ba, ban san yadda aka yi sonta
ya yi nisa a zuciyata ba, ki tausaya mini
wallahi ba ta da wani mugun hali".
Hajara ta dube shi kawai tana kada
kai, yau Mu'allim ne ke ambato mata yana
son wata, yaro mai kunya da kawaici,
wannan al'amari abin duba ne.
Ta sanyaya murya tana girgiza kai.
"Malam na da kafiya fiye da
tunaninka, tunda ya kafe ka yi hakuri, ina
tsammanin akwai abin da ya hanga..."
"Umma na fahinta, Abba ya fi son ya
gan ni cikin wahala da tozarci. Umma
zuciyar Abba ta mutu, wahala ta raunana
tunaninsa, shin kina son dawowar rayuwarki
na da shin me ya sa Abba zai nuna bakin
99 cikinsa da abin da Ubangiji ya bai wa...
Ji ka ke tas! Tas!! Tas!!! Hajara ta hau
marinas ta ko'ina.
"Mu'allim ka haukace? Wallahi ka
gama yawo, mahaifinka ka ke gaya wa
76
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
wadannan maganganun saboda dan abin da
ka soma samu? To in har kudi zai sauya ka,
na roki Allah ya barka a haka".
Ta juya ta shiga ciki tana sharar
kwalla, shi ma ya juya ya koma dakinsa.
Yana zaune a gado jin zuciyarsa ya ke
tamkar ta lfashe, ba ya taba tunanin zai iya
rabuwa da Humaida, yana sonta sa'annan
yadda ya dandani wannan daular ba zai yi
saken dawowa gidan jiya ba, don me ya sa
za su dinga ja masa jafa'i? shin da ma akwai
iyayen da ba su son ci gaban 'ya'yansu?
Wallahi yanzu na fara son Humaida". Ya
fada a fili.
Daga nesa suka hanfo Mu'allim ya
fito daga mota rungume da wasu takardu,
Alhaji Auwal ya dubi Injiniya.
"Ya kamata. ka yi wa yaron nan
magana ya turo manyansa, ina tsoro kada
wani abu ya gilma, saboda mahaifin nan
nashi ba shi da dama".
77
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Ni ma tunanin da na ke yi ke nan,
amma ina ga yaro ba wani cikakken dangi
ne da shi ba, iyayensa duk suna kauye".
Alhaji Auwal ya ce, "Duk da haka a
bai wa uban hakkinsa a matsayinsa na
mahaifi".
Shigowar Mu'allim ya katse su, ya
durkusa yana gaida su, ya mike zai tafi
injiniya ya dakatar da shi.
"Lokaci ya yi da ya kamata ka turo
magabatanka ko?"
"An zo gurin". Ya fada a ransa.
"Ka yi shiru, ko akwai wata matsalar
ne? Okey, shi ke nan zan je gurin mahaifin
naka da kaina na fahince ka, tashi ka je".
*** *** ***
Sun dade tsaye a kofar gidan kafin su
sami yaron da za su tura. Wata yarinya za ta
wuce suka kira ta.
"Maza shiga nan gidan ki ce ana
sallama ada maigidan".
78
31
KA AURE NI=2
ya ce.
BILKISU H.MUHD
Bayan shigar yarinyar Alhaji Auwal
a
"Yaro-yaro ne, in ban da Humaida
mai za a yi da mutumin da ya ke rayuwa irin
ta wannan, don Allah ji wani gida ko
Kauye ba karamin matalauta ne ke jure
rayuwa a cikin irin wannan gidan ba, gida
rube, a lalace, Allah sarki Mu'allim".
a
"Wai yana zuwa". Yarinyar da suka
aika ta idar musu da sakon.
Injiniya ya mika mata dari biyu, ta
karba tana tsallen murna, eh
waye.
Ya nufo su cikin rashin gane ko su
"Ku ne masu salláma?
"Mu ne Malam. Injiniya ya fada.
Da sauri ya daga kai ya dube su.
"Oho kai ne ka dawo Alhaji Haruna?"
dan odlnjiniyasyas yiamurmushi mai ciwo,
enwannandtsohon yana tofo shi da jafa'I, ya
kanne tare da kokarin danne zuciyarsa, don
yadda ya ke jinsa kamar zai shako 'shi.ss
08 79
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Mun zo ba ka hakuri ne da neman
iri".
"Wannan karon kuma da abin da ka
zo ke nan? Aniyarka sai ta bi ka, kuma
wannan irin ya fi karfinku saboda dana ba
irin 'yarku ba ce".
Mu'allim zai shiga gida ya hango su,
Ummaki da tsoho suka bayyana a fuskarsa,
PYLya so ya yi baya sai dai Malam Musa ya riga
ya gano shi cikin kakkausar murya ya kwala
masa kira. Ya taho cikin rashin kuzari
musamman da ya gano irin kayan da ke
jikinsa. Ya siya masa kaya bila'adadin bai
san me ya sa ba ya sakawa ba, duk kunya ta
kama shi, ya durkusa ya gaida su Injiniya.
Cikin daga murya ya ce.
"Mu'allim, kafin na dauko wuka ka
yanka ni muddin ba ka fita daga shirgin
wadannan mutanen ba sai na tsine maka,
wallahi ko da za ka tattaro duka mutanen
Kano a kan na amince da wannan auren ba
zan amince ba".
80
KA AURE NI=2
Ya dubi Injiniya ya cе.
BILKISU H.MUHD
"Da nawa ne, ni na haife shi, na fi
klowa iko da shi, ba zai auri 'yarku ba, in
kuma kuna ganin za ku ja mu zuba ku
gani... kai shige mu je".
Ya finciko Mu'allim cikin zafin rai
suka shiga gida.
A cikin gida suka maida wa Hajiya
Zainab abin da ya biyo baya bayan zuwan su
gidan su Mu'allim, hankalin Humaida ya yi
matukar tashi, Injiniya ya dube ta.
"Kada ki daga hankalinki baby, zan yi
amfani da karfin dukiyata don na ga wannan
auren ya yiwu. Yanzu na fi ki bukatarsa".
Hajiya Zainab ta ce.
"Yana ikirarin ya fi kowa iko da shi
har yana cewa ku zuba, Alhaji ya kamata ka
nuna masa kudi na maganin komai”.
Ya yi murmushi, ya cе.
"Ban taba ganin kazamin matsiyacin
talaka irin wannan dattijon ba, sai dai har
-81
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUND
gobe ina tunanin me ya taka, domin ko
kadan ba shi da tsoro".
Alhaji Auwal ya ce, "Da me ya ke
takama kuwa in ban da tijara? Jira ya ke
kawai ka taba shi ya bingire salon ua jaza
mana bala'I".
Gabadaya suka tuntsire da dariya.
"Burinsa mu rabu da yaronsa".
Injiniya ya ce, "Ai ba zai yin wannan
saken ba, Zainab yaron nan bai yo jinin
ubansa ba, yana da kashin arziki, tunda ya
soma aiki a kamfani na ke ganin ci gaba".
fadin.
Alhaji Auwal ya amshi maganar da
"Haka ne, shi ya sa na ke so mu bi ko
ta wace hanya don mu mallake shi, ka ga
zamowarsa sirikinmu shi zai ba mu damar
yin hakan, inya so mu ga mai iko da shi
tsakaninmu".
"Amma Auwal kana ganin aure zai
yiwu ba tare da sa hannun iyaye ba?"
"Ka bar komai a hannuna"
82
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Duk wanda ya kwana ya tashi a
unguwr su Mu'allim ya san halin mai
unguwa yana da matukar son bin duniya, in
ma bai fahinci kana da shi ba sam ba ya
hada hanya da kai. Yana da son karya ga
hadama da zakin bakiduk lokacin da aka ce
ana sallamada shai sai ya tura yararea 3
gano mai kiranda alama yana da mauko ko
ya ku bayi ne, yau da gobe ta fi karfin wasa,
da zarar ya yi baki yaran har sun sanin ba su
ga alamar danshi ba da kansu suke cewa,
Abbansu ba ya nan kafin ma su sanar masa
saboda su sani ba fitowa zai yi ba.
Yana zaune yana cin naman kaza
gasasshiya, daya daga cikin yaransa ya
shigo gida da gudu ya zube a gabansa yana
faman haki, ya ma kasa magana.
"Jabiru mai ke faruwwa haka? Wa ya
biyo ka?"
Mai unguwa ya tambaya.
Yana haki ya ce, "Bako kayi Abba a
cikin wata katuwar mota".
83
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ai tuni ya tura naman gefe ya mike
bai jira karin bayani ba, takalmi ma da ya
saka wari da wari ne, sai matarsa Binta ce ta
lura tana kiransaya zo ya sake, ina bai bi ta
kanta ba.
Akofar gida ya riski Alhaji Auwal, ya
mika masa hannu suka yi musabiha, sai fada
ya durkusa masa jikinsa har rawa ya ke.
"Shigo ciki mana, ai muna da gurin
saukar baki".
Binshi kawai Alhaji Auwal ya ke da
kallo suka shiga wani shago wanda aka
shimfida shi da kafet.
"Bara a kawo maka ruwa ko?"
"A'a mai unguwa na gode, a kan
hanya na kee".
Cikin nutsuwa ya warware masa abin
da ke tafe da shi, mai unguwa ya jinjin kai.
"Hakika Musa makaho zai aikata
amma ku bar mini komai a hannuna zan
same shi ban da tsiya irin tasa kana wannan
hali arziki na binka kana gudu? Ji yadda
84
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
yaron nan ke yi musu hidima, billahil azim
ba za ka sha Ummaki ba sai in ka san uwar a
da ka kuma ganta yanzu ba za ka yarda ita
دو ba ce...
"Wannan kuma wani abu ne daban, ni
dai ka yi mini kokari".
Ya sa hannu cikin aljihuya dauko kudi
ya kirgo dubu hamsin.
"Ga wanan somin tabi ne kafin mu ga
yiyuwar abin".
Ya dade yana samun tukwici da
kyautuka amma bai taba samun kamar
wannan ba, godiya ya dinga zumbuda masa.
Sun rabu da sharadin zai dawo bayan kwana
biyar, ya raka shi bakin motarshi yana wani
takun takama da jin kanshi shi wani ne, ko
ba komai ganin wannan hamshakin zai
sanya jama'a su fara kiyayarsa.
Yana son hulda da irin wadannan ko
da ba za su ba shi rakan na kore yawa ba. Ai
kuwa Alhaji Auwal na jan motarsa ya yi
85
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
kwana zuwa kofar gidan Malam Musa, daga
kofar gida ya dinga kwada sallama.
Ya gane waye da sauri ya fito.
"Yallabai da kanka ai da sai ka turo ni
na zo".
Mai unguwa ya cee, "Komau kamawa
ya ke yi".
"To ina zuwa.
Komawa ya yi ciki ya dauko tabarma
ya dawo, ya shimfida masa suka zauna suna
kara gaisawa. Mai unguwa ya ce.
"Kai Malam Musaya ya abin da a ke
nema ya tarar da kai har gida ka yi wa
Ubangiji butulci?"
"Ban fahince ka ba". Ya ce da shi.
"Wannan attajirin Injiniya Sunusi
suka zo mini da maganar yaronka na
soyayya da 'yarsu...
Da sauri ya katse shi.
"Oho ta nan kuma suka billo? To bari
ka ji mai unguwa, ina ganin kimarka don
86
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Allah don Annabi kada ka sa kanka cikin
wannan maganar".
"Malam Musa me ya yi zafi? Ban san
ka da kafiya ba, a sanina kai mutum ne adali
mai saurin fahinta tunda yaron na son
yarinyar mai ya sa za ka ja da yin Allah? In
fa ka ce za ka ci gaba da kafewa sai rabo ya
kashe ka".
"Bari ka ji mai unguwa, wallahi
mutuwar za ta fi yi mini kwanciyar hankali a
kan yin wannan aure".
"Ya ilahi, shin Malam me ya yi zafi
haka?"
"Ka ga mai unguwa, yaro dai dana ne
na ce ba zai aure ta ba, ka gaya musu
wannan naci har ina?"
Lallashi da ban bakinsa bai sa ya
rusuna ba, karshe suka rabu baram-baram.
Ya zauna a kofar gidansa yana huci, ba zai
bari wannan arzikin ya wuce shi ba.
Ya mike zumbur ya nutsa cikin
unguwa yana neman Mu'allim har bayan
87
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
magriba babu shi, karshe ya je ya nemi guri
a kofar gidan Malam Musa inda ya cі
alwashin sai ya gana da Mu'allim yau komai
dare.
Bai shigo unguwar ba sai karfe tara da
rabi, ji ya yi ana kwala masa kira, ya karasa
inda ya ke jin muryar, da sauri ya risina
yana gaida mai unguwa.
"A kan maganarka da 'yar gidan
Injiniya Sunusi ne, shin me ke faruwa, mai
ya sa mahaifinka ba ya son ci gabanka? Shin
ba ka sonata ne? Ka yi mini magana ta
yadda zan fahince ka, na san yadda 6illo wa
mahaifinka".
"A kwanakin nana bin da na sa a gaba
ke nan don na fahintar da shi, amma ya ki
ganewa ban san mai ya sa ya hana lamarin
nan ba, da ban sonta da na hakura da ita".
"Lala kada ma ka soma, Malam Musa
tunaninsa ya tafi, ba ka ganin girma ya kama
shi, duk mutumin da ya kai wannan
munzalin sai hakuri don tamkar mahaukaci
88
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ya ke zamowa, ka