bari ai ni ma tamkar
mahaifinka na ke, ni ne shugabanku, zan iya
jagorantar komai a kan jama'ata. Wannan
hargagin nasa na dan lokaci ne, da zarar an
kwana biyu da kanshi zai sauka".
Ya ji dadin bayanin mai unguwa
sosai, bai taba yin tunani a kan maganganun
mai unguwa ya ji yana yi don shi ma har
kyauta ya yi masa. Bayan kwana biyar
Alhaji Auwal ya sake dawowa a gidan mai
unguwa sun dade suna tattaunawa da kwana
biyu da rabuwarsa ya sake komawa gurin
Malam Musa.
"Malam Musa kada ka tauye wa yaro
rayuwarsa don kawai kana mahaifinsa in ka
yi haka ba ka yi masa adalci ba, yadda yaron
nan ke maka biyayya bai kamata a ce ka yi
biris da abin da ya zo da shi ba. Na kira yaro
mun yi magana, ya nunan yana kaunar
yarinyar".
"Hakan ya ce maka?"
"Kwarai kuwa".
89
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"To shi ke nan tunda haka ya ce ka yi
masa ja gaba, amma ni kam in dai ni ne har
abada".
Mai unguwa ya yi dariya.
"Tunda kai ka ba ni amanna zan yi
י5 hakan, ai da na kowa ne.
Hannu ya sa cikin aljihu ya dauko kati
ya mika masa. Cikin rashin fahinta ya
tambaya.
"Me ye wannan?"
Mai unguwa ya ce, "Katin daurin
auren dan namu ne
"Na yafe, ka rike kayanka
Ya mike ya shiga ciki
"Yau ni na zamto abin wolintarwa da
wulakantawa a gurinka? Ni za ka tozarta
ashe da ma ban isa da kai ba? To shi ke nan
ka je ka yi, amma Allah ba zai bar ka ba.
Bakin cikin da ka dandana mini da yardar
Allah kai ma sai ka dandana"
Mu'allim zuciyarsa ta soma karaya,
amma son da Ubangiji ya jarrabe shi na
90
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Humaida yana jin in ya rabu da ita ba zai
sake moruwa ba.
"Abba ka yi hakuri, na ce ka gaya
mini abin da suka yi maka ka ki ba ni hujjar
da in na rabu da shi zan bayar inda ka gaya
mini da.lili sai na sami madogara".
Malam Musa ya harzuka sosai
idanunshi sun kada sun yi jajir.
"Ba zan gaya maka dalili ba, ka je ka
aure to amma albarkar da ke cikin aure ba
za kme shi ba".
ra mike yana sharar kwalla ya fita.
Shin mai ya yi zafi Abbansa na kuka abin da
bai taba gani ba a rayuwarsa, duk jikinsa ya
gama yin sanyi, sai dai har lokacin yana kan
bakansa ko Hajara bai nema ba ya fita.
*** *** ***
"Adnan kaina ya kulle, ina tsoron
Abba ya ambata mini abubuwa da yawa,
yana gaya min magana mai kama da
tsinuwa. Na rasa ya ya zan yi, yau Abba
91
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
kuka ya yi ban san mai mutanen nan suka yi
masa ba, da zan iya da na rabu da Humaida,
sai dai ina matukar sonta, ruhin soyayyata
yana hannunta ka gaya mini ya ya zan yi?"
"Yadda za ka yi kawai ka rabu da ita".
Wani abokinsu ya fada, Adnan ya
kalle shi.
"Wai kai Ahmad me ye haka?
Wannan ai nuna bakin ciki ne kuru-kuru, in
da za ka sami irin wadannan su ce suna
sonka kai ma so za ka yi".
Ahmad ya ja tsaki ya се.
"Irin wadannan idan za su kwanta in
dinga taka su ina wucewa ba zan aure su ba,
domin na san kwadayi da buri ne, kuma
akwai nadama a cikinsa. Yarinyar da ba ta
da cikakkiyar tarbiyya, su kansu iyayenta ba
ta girUmma su..."
"Wa ya gaya maka, ko da ma zama ku
ka yi kuna gulmarsa a cikin unguwa?"
Shi dai Mu'allim ya sa musu ido
kawai yana jinsu, Adnan ya dube shi.
92
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Wallahi Ahmad yana daya daga
cikin mahassadanmu, duk mutumin da bai yi
maka murna ba makiyinka ne yana bakin
cikin ka yi masa nisa za ka hau mota mai
tsada, za ka shiga gida mai kyau, za ka yi
harka da manyan mutane ai ba damuwa
tunda tana sonka za ka iya sarrafa ta ta daina
abin da ta ke yi".
Mu'allim ya gamsu da maganganun
Adnan ya kalli Ahmad yana son gamsar da
shi, ya ce.
"Wannan abubuwan da ta ke yi duk
zan san hanyoyin da zan bi na sarrafa ta ta
daina".
"D Allah abokina kyale shi duk abin
da ya ke yi kyashi ne da hassada".
Ahmad ya mike, "Na ga zancen nawa
ba za ku fahince shi ba, kun dau zafi da
yawa, sai an jima".
Ya dubi Mu'allim, "Ranar da nadama
ta zo maka ina nan ina jiranka".
93
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Mu'allim na ga ka yi shiru tunanin
me ka ke yi, kar fa ka dauki zancen wannan
dan bakin cikin. Ka nutsu mu tsara yadda
bikin zai tafi".
*** ***
Har ta iso gare shi ba tare da ya lura
ba, gabadaya ya nutsa cikin tunani ta kai
hannu tana shafa masa fuska. A hankali ya dago kai wani kamshi ya shaka, ya dora
hannunsa a kan nata. Sun dade a haka, ya
lumshe ido.
"Humaida ina sonki, na ba ki duniyata".
Ta yi murmushi kawai, ya zare
hannunta daga fuskarsa.
ki ba".
"Yau ki ce mini kina sona ba in aure
"Sau nawa ina ce maka aure shi ne
gaba da so?"
94
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ya ce, "Na sani, amma furta ina sonka
a gare ni zai haifar mini da wani yanayi mai dadi".
"Uhm, amma ka san me?"
Ya kada kai yana kallonta.
"Mun dace da juna, ina alfahari da
samun kyakkyawan mutum kamarka, ka
gaya mini za mu dauwama da kai har
Karshen rayuwa?"
"Haka na ke bukata”.
"Kuma ka san me? Zuciyata in ta
dokanta da mutum na sati daya ne zan so
abu kamar hauka, amma ba za mu yi
cikakken wata ba abin zai fice min, sai dai
kai na daban ban taba gajiya da ganinka ba,
yau ga shi ka aure ni na gode da cika
alkawari da ka yi min. mom ta shirya dinner
har kashi uku ta ce duk za ka halarta, da
fatan ba za ka ba da matsala ba? Ga kuma
wannan kudi ne masu yawa duk sun ishe ka
ka yi abin da ka ke so daga bangarenka, ka
yi shiru kana kallona".
95
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Humaida ina tunani ne, ina tunanin
ranar da zan dauke miki dawainiyata, ina
son a ce yau ga shi ke ma kina alfahari da ni
zan so a ce ke ce za ki sami duk wadannan
abubuwa daga gare ni. Ina jin kunya duk
lokacin da ki ka yi mini wata kyauta..."
Ta katse shi, "Anya kuwa za ka ga
wannan ranar don ina ganin ba za ka taba yi
mini wata kyauta da ba a yi min ba, ba za ka
taba yi mini abin da za ka burge ni ba. Duk
abin da ka ke sa ran za ka yi min ina da shi,
an taba yi mini. Dukiyar Dad yana nema ne
saboda ni, a ka ke nan a karkashinsa don
haka ka daina wannan tunanin, har abada
kana a kasanmu".
Ta dube shi tana murmushi, sakonta
ya cika can cikin kwakwalwarsa har yana
son tuna inda ta dosa... ta katse shi.
"Babban abin da za ka faranta mini da
shi, ka yi hakuri da ni, ka faranta mini ka da
ka tada kosawa da ni, shi ne kawai".
Ta riko hannunsa.
96
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Taho mu tafi gurin Momy za ku yi
magana
Tunda ya gaida ta ya ji ta amsa a ciki
ya san sako ya isa gare ta, ba ta bukatar
karin bayani. Ya sa hannu cikin aljihu ya
dauko bandir din naira dari bibbiyu ya ajiye
a gabanta.
su".
"Na me ye?" Ta tambaya.
"Kudin da za ki yi na ki hidimar da
Ai gabadaya ta suri kudin ta cilla
masa cikin muryar kuka ta ce.
"Mu'allim me ke damunka ne, ko me
za ka samu a duniyar nan a bayan albarkar
iyaye ya ke, anya ma kana son ganin da
kyau kuwa? Kada ka bari fushin zuciyar
mahaifinka ya kama ka, ka kwadaitu da
neman albarkar addu'ar iyayenka, ka ji
tsoron muguwar addu'arsu a kanka, domin
kuwa kibiya ce da ba ta kuskurea. Ya
kamata ka nutsu ka yi nazari".
97
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"To Umma na ce masa ya sanar da ni
abin da suka yi ya tsane su haka ya ki, ya ku
ke so na yi? Ina sonta in na rasa ta mutuwa
zan yi". Ya fada a kufule.
"Shin ke ma kina goyon bayan Abba
ne? ke ce ya kamata ki fahince ni, amma ke
ma kin kI".
Duban Ummaki ta ke masa.
"Tir da yaran zamani, tir da yaro
irinka".
Ta kada kai, ta kuma sanyaya murya,
ta ce.
"Dukkan zunubai Allah yana jinkirtar
da su zuwa ranar alkiyama amma ban da
cutar da iyaye, Yana gaggauta sakamako ga
mai yin shi tun a nan duniya kafin
mutuwarsa, ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron
faduwar masiba a akanka, ka lura da abin da
ya faru ga masu cutar da iyayensu, wadanda
suka gabace ka, kada ka maida kanka abin
izina ga sauran jama'a, ka dubi irin annobar
da ta lalata karshen rayuwarsu, ka dubi
98
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
yadda suka shuka tsiya suka cutar da
iyayensu amma daga baya suka girbi kavar
hasara da da na sani a hannasu
'ya'yan..."
"Wai Umma me na yi ne?
A karo na biyu ta sake duoansa cikin
Ummaki, ashe wannan nasihar bai risinar
zuciyarshi ba, lallai Mu'allim ya yi nesa.
"Ba ka yi komai ba, babu abin da ka
yi, wannan kudin ka diba ka kai ma mai
unguwa tunda shi ya tsaya maka ku yi taron
naku a can".
"Umma!" Ya kira sunanta.
"Haka za ki yi mini, in Abba ya ki ai
ke mahaifiyata ce, a tunanina ba za ki
wofintar da ni ba, kada ki yi mini haka, in
kina tsoron Abba ne, ni zan dauke ki in
nema miki wani gidan, kuma..."
Ta daga hannu a zafafe ta tsinka masa
mari. Cikin daga murya ta ce.
"Mahaukaci, shashasha wanda bai gaji
mutunci ba, Mu'allim ina tantama a kanka,
99
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ina tantama ma kai ba jininmu ba ne, kа
tashi ka fita yau na tsane ka! Na tsane ka!
Ka dauki kudinka ka fita".
Ta dauki muciya ta yi kansa, da sauri
ya dauki kudin ya yi waje. Bai zame ko ina
ba sai gidan mai unguwa wanda ya riga ya
zamo dan gidan don ko ba shi da shamaki da
gidan duk lokacin da ya zo kai tsaye ya ke
shiga.
Mai unguwa ba ya nan sai matarsa
yanayin da ta ganshi a ciki ne ya sa ta soma
tambayarsa, bai 6oye mata komai ba.
"Yanzu kai wannan shi ne ya sa duk
ka fice a hayyacinka. Yanzu fa lokaci ne na
farin ciki, ka kyale Umma, duk abin da kа
ga tana yi ba yin kanta ba ne, Malam shi ya
assassa komai, domin bai barta haka ba, ni
na san komai, kafe ta ya yi a gidan babu
wanda bai san wannan ba, don haka ka yi
mata uzuri, yanzu ni zan tsaya maka ba ka
da matsala duk abin da za a yi na hidima ni
100
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUND
zan yi, zan kuma yi wa mai unguwa
bayani
Ya mika mata kudin hannunsa. Ta
daddage ta rangada guda, tana ci gaba da
zuga shi.
"Ai muna nan da kai, Malam Musa da
kansa zai neme ka, ita ma Hajara za ta dawo
rakiyarsa, ka rubuta ka ajiye".
Kullum abu na matsowa kusa, yau ga
shi an wayi gari gobe za a daura aure duk
gidan rediyon da ka kunna sanarwar daurin
aure a ke, unguwa gabadaya ta dauka.
Ango kai ya dau zafi in ya fita tun
safe sai kwanciyar bacci, yana yawon raba
aibi, sai yau ya sami damar ziyartar gidan da
za su rayu a ciki shi da Humaida, ganin
gidan ya gigitata tunaninsa, ya mantar da shi
duk wani bakin ciki da ke karkashin
zuciyarshi. Yanzu ne ya ke jin shi mutum
ne.
Yana zaga ko ina na gidan cikin
Kasaita kansa ya gama kumbura, yana
101
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
rayawa a ransa duk mutumin da ya ke daure
mishi gindi a kan wannan lamari ya zamo
babban makiyinsa, to in haka ne iyayensa fa
ya matsayinsu ya ke? Ya tambayi zuciyarsa,
ya yi saurin kawar da wannan tunanin.
Kayan da a ka zuba musu odarsu aka
yi daga waje, ga masu gadi da masu yi musu
wanki da guga duk sun gabatar da kansu
gare shi, haka ya baro gidan cike da
matsanancin farin ciki.
*** *** ***
gefc.
"Hajara ina ki ka shiga?"
Hajara ta fito daga bayi ta aje buta a
"Malam ya na ganka da jaka?"
A raunane ya ce, "Tafiya zan yi, ki
kula da Kawu Yusuf ki dinga ba shi abinci a
kan lokaci".
Ta fara kuka, "La'ilaha illallahu, yau
na ga ta keina, Malam in ka zauna akwai
102
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
wanda zai tursasaka ya ce sai ka halarci
daurin auren nan?"
"ki yi hakuri Hajara, kin ga gobe za a
daura auren, jibi sai na dawo, muddin, na
zauna akwai wadanda za su tursasa ni a kan
halartar daurin auren, ni kuma zan ji kunyar
gardama a gare su".
"To yanzu ina ka nufa?"
Ya ce, "Rano na nufa, na ji rade-radin
za a yi taron bikin a gidan mai unguwa ban
yarda ma waņi nawa ko naki ya taka gidan
ba, ina kara gargadinki kada na ji labarin kin
je in ko kin je kada ma ki dawo mini gida, ki
yi SABI ZARCE kawai".
Har Malam Musa ya jima da fita tana
zaune tana faman kuka. Sallamar mutane ya
sanya ta,saka wa zuciyarta lisilama, kowa ya
shiga sai ya tambaya wai bikin Mu'allim ake
yi amma ba a gayyace su ba? Ita kam sai ta
rasa abin cewa, sai kawai ku yi hakuri ta ke
cewa.
103
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Haka mata suka dinga sintiri ta san
tsegumi ne ke kawo su, karshe gajiya ta yi ta
kulle gida duk wanda ya zo sai ya yi zaton
ba ta nan.
Shi kam Mu'allim gabadaya ya ki
zuwa gidan duk wasu shirye-shiryensa a
gidan su Adnan ya ke yi.
Washegari abokanansa suka hadu a
gidan Mai unguwa daga nan motoci suka
dinga dibarsu zuwa gidan Injiniya, mai
unguwa ya yi amsa wakilci aka daura aure a
kan sadaki naira dubu dari hudu wanda
Alhaji Suwal ne ya ce ya dauki nauyi.
Bayan an daura aure abokan ango
suka wuce country mall walima, an ci an
sha, kudin da aka kashe ya tsone wa kowa
ido, haka aka fashe ana yi masa sam barka.
Washegari unguwa ta dinke mutane
cike a gidan mai unguwa, makada kala-kala,
kowa ya yi Ummakin wannan al'amari,
sanin halin mai unguwa ne ya hana kowa
furta nasa batun.
104
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Bayan sallar magriba aka sake
haduwa a wani katafaren gida inda Hajiya
Zainab ta shirya nata dinnar, wai ba na kowa
da kowa ba ne, sai masu ido da kwalli, sai
kuma abokanan ango.
Hajiya Zainab ba ta ji kunya ba ta ja
hannun ango suka shiga filin rawa guri ya
dinke da shewa, shi kam Alhaji Sunusi dolas
ya dinga kika musu, shi ma babban amini ya
shiga lika 'yan dubu-dubu, daga nan sai
abokan ango suka shiga suna yi wa ango
kara da dari biybbiyu, masu karfin halin ciki
suka dinga likawa.
Sai karfe goma sha biyu na dare taro
ya watse. Washegari ma wani bikin akа
tashi da shi a gidan Alhaji Sunusi, daga gefe
Mustapha ne ya hangi Mu'allim da sauri ya
nufo shi, ya mika masa hannu.
"Ina taya ka farin ciki da auren
kwadayi, wanda karshensa nadama ce za ta
biyo baya".
105
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Da sauri ya zare hannunshi daga cikin
nasa, "Kai ma?" Ya tambayi kansa wanda a
tunaninsa a zuci ya yi maganar, yayin da a
fili kuma ya ambata.
"Ban fahince ka ba, kuma waye kai?"
"A hankali wataran za ka gane waye
ni, amma a zahirance kana da kirki, ina yi
maka kyakkyawan zato, akwai kamala a
tattare da kai, ga ka ingarman namiji, duk
wanda ya dube ka zai yi maka kallon
jarumta, in ko haka ne lallai abin ba a jiki ya
ke ba".
Kansa ya kara daurewa, zai sake
magana Mustapha ya bar gurin, duk sai
jikinsa ya yi sanyi.
"Ina son Humaida, zan bai wa kowa
Ummaki, zan jure duk abin da zai biyo
baya".
Yanayin da ya tsinci kansa a ciki bai
barshi ya shiga gidan ba, komawa ya yi gida
ya dade tsaye a kofar gidansu yana tunanin
106
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
yadda zai fuskanci iyayen nasa. Karshe ya
juya ya sani yanzu suna cikin fushin zuciya.
A can shagon gidan su Adnan sun dukufa shi da abokanshi suna faman
kwantar masa da hankali, saboda yadda
zuciyarsa ke yi masa kwan gaba kwan baya,
gabadaya ya birkice musu da fadin, yana jin
fasa auren zai yi saboda har yanzu babu
wani sauki daga bangaren iyayenshi.
Hajiya Zainab ce ta kira shi a waya,
tana cewa za ta wuce da amarya ita da
Alhaji Sunusi, ruwansa ne abokansa su yi
masa rakiya...
Ya katse wayar cikin 6acin rai yana yi
wa Adnan bayani.
"Ka tashi ka je abokina, kai ma ba ka
bukatar rakiyar kowa, ka saki ranka wannan
rana na da matukar muhimmanci a gare ka,
wannan rana na daya daga cikin ranakuln
farin cikinka. Da zarar ka ayi tozali da ita za
ka mance duk wani bakin cciki. Ina yi maka
fatan alheri".
107
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Wannan karon ma bayan ya bar gurin
kofar gidansu ya koma ba tare da motarsa
ba. Ya dade a tsaye kuka ya ke yi sosai yana
kallon lokacin da Abbansa ya fito daga gida
ya zauna cikin rafka tagumi cikin 'yar kuka
tamkar yana a gaban Abban nashi.
"K yafe mini, wannan aure
mukaddeti ne kada ka zarge ni. Babu yadda
ban yi don na tirsasa zuciyata akan bin
umarninka ba amma na kasa, ji na ke yi
tamkar rayuwata na hannunta ne".
Da sauri ya juya yana sharar hawaye.
GIDAN AMARYA
Lokacin da suka isa gidan da ita
lallashinta suka dukufa yi, saboda tsananin
kukan da ta ke yi har ta sanya Hajiya Zainab
kuka. Ta rike ta tamau wai ita ba za su tafi
ba, a al'adance duk yarinyar da aka kai
gidan miji sai iyaye sun yi mata nasiha
yadda za ta bi mijinta, da yadda za ta ja
108
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
dangin mijinta a jiki, ita kam maimakon
haka ita nata fadan shi ne.
"Humaida son da muke yi miki ne ya
sanya muka bari ki ka hada jini da talaka
mara galihu, don mun aura miki shi ne ba
mu amince ki bari ya raina ki ba, muna son
ki dinga nuna masa ke ce sama, ba mu
laminta ki saki jiki da 'yan uwansa ba a yi
miki zugar dangi a cika miki gida da 'yan ba
ni ba ni. In muka ji labarin wata mu'amala
da hada ku da su za ki hadu da fushinmu.
Daga karshe gobe za mu turo kuku,
aikinsa girki da gyara miki daki, Allah ya
sanya alkhairi".
Suka mike za su tafi ta sake rungume
ta da kyar suka lallaßata Injiniya Sunusi ya
се.
"Zamanki cikin gidan yau da gobe ne
kawai zuwa jibi, hijabinki a yaye ya ke, kina
iya fita ki je duk inda ki ke so, ki yi hakuri
babyna, ban so kunshe ki a gida ba, sai don
hakan ya zama dole".
109
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Yana maganar yana sharar hawaye, ta
kada kai suka fita.
Bathroom ta shiga ta yi wanka, ta
zauna a bakin madubi tana shafe jikinta da
turaren shu'umin humra, ta mike ta bude
akwatin da aka zubo mata kayan bacci a
ciki, riga ta dauko da wando ta saka, rabin
cinyarta ba su rufe ba kayan masu sharashara kana ganin duk wani abu da ke
jikilnta, ta koma ta kwanta a gado, bacci mai
nauyi ya dauke ta.
Karfe goma ya iso gidan maigadi ya
risina yana yi masa sannu da zuwa, sai da
kya yi tafiya mai dan nisa ya isa harabar
gidan da ledoji rike a hannunsa.
Ya dinga sallama yana kara yaba
yadda gidan ya tsaru a zuciyarsa, ga wani
kamshi mai dadi da gidan ke yi.
Sai da ya kara zagaya gidan sannan ya
nufi sashin da bedroom ya ke, ya san
amaryar na can. A hankali ya ke tafiya, 'a
wani kayataccen falo ya ganshi, wanda
110
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
bedroom din ke manne a jikinsa, kai tsaye
ya nufi bedroom ya kutsa kai.
Arba ya yi da ita ta yi shame-shame
tana faman bacci abinta, shigar da ta yi ne
ya tilasta masa saurin dauke kai, wannan
wayewa ce ke nan? Abin da ya sani ko kuma
na ce a al'adance lokacin da ango ya shigo
dakin amarya zai tarar da ita a suturce cikin
lullubi ko da idonta ba ta bari a gani. Ya
kada kai kawai a hankali ya dinga kiran
sunanta.
Ta yi wani mika tare da wani irin juyi
tamkar tarwada, da sauri ya kawar da kai
tare da lashe lebe, wani irin yanayi ya ji shi
a ciki.
Ta mike zaune tana mutsika ido, ko
kadan babu alamar kunya a idonta, ya kawar
da kai.
Ta sake wata mikar tare da hamma.
"Yana daga cilkin al'adata, in na yi
bacci ba a tashina, mancewa na yi ban sanar
da kai ba".
111
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Yadda ta ke magana cikin murmushi
ne ya zaci ko zolayarsa ta ke yi. Ya koma ya
zauna a kusa da ita yana satar kallon kirjinta
wanda ya fi komai daukar hankali.
Ya shiga bude ledojin da ya shigo da
su.
"Na sani kacaniyar biki bai bari kin ci
komai ba”.
"Wa ya gaya maka? Ai ni ko a ina ba
na sake da cikina".
Ya jinjina kai.
"Kin kyau mana, amma kin san wani
abu?"
Ta kada kai kawai.
"Jina na ke yi na fi kowa sa'a a
duniya. Humaida ina matukar sonki, ba zan
iya rayuwa ba in babu ke".
"Mu'allim kana burge ni don haka na
zabi na yi rayuwa da kai, za mu zauna lafiya
in har za ka bi ni babu mai jin kanmu".
112
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ya yi murmushi kawai har yanzu
akwai kuruciya a tattare da ita. Ya maida kai
jikin agogon da ke manne jikin garu.
Karfe goma sha daya, ya mike.
"Ya kamata mu raya wannan dare
wanda na lakaba wa FARIN DARe, wannan
dare yana da matukar muhimmanci a gare
mu, bismillah taso ko".
Ya karasa zancen cikin tattausan
murya.
"Abin da na sani angon da ke son
kusantar matarsa shi ke umartarta da ta yi
alwala don nuna godiya ga Ubangiji, da
kuma fatan samun zama na gari".
"Ni kam a sanina ban yi wannan aure
don ka mallaki jikina ba".
"Me ya sa?" Ya tambaya cike da
zulumi.
Ta ce, "Saboda cewa na yi kawai KA
AURE NI, kuma ka aure ni saboda kana
burge ni in sanya ka a gaba ina kallo wannan
ne burina”
113
KA AURE NI=2
Mamaki ya kasa barinsa.
BILKISU H.MUHD
"Humaida!" Ya kira sunanta can
kasan makoshisa. Da sauri ta dakatar da shi.
"Please kada ka kawo mini kitabul
ra'asi, babin glo da MTN ko ka taba jin na
ce ina sonka?"
Bai gama mamaki ba ta dora da fadin.
"In ka fita ka turo min kofa, akwai
dakin da aka ware musamman don kai"
Ta juya ta kwanta.
Humaida ce kuwa? Anya wannan
Humaidarsa ce? Ya shiga zargi ko iskokai
ne suka shige ta, ko kuma tana dan taба
shaye-shaye ne? Zai yi mata uzuri zai kyale
ta zuwa lokacin da za ta dawo daidai.
Ya juya ya fita cike da tsananin tashin
hankali.
Cikin damuwa ya ke faman kai komo,
ya koma ya zauna yana jin kansa na wani
irin sarawa tamkar zai tarwatse. Ya sake
mikewa kai tsaye ya nufi dakin da Humaida
ta ke ya tura. Gam ya ji shi a kulle ko
114
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
motsawa ba ya yi. Ya koma ya mike a kan
doguwar kujera ya daga kai yana kallon
agogon da ke manne a jikin bango. Karfe
uku, zuciyarsa ta shiga bugawa tunda ya ke
bai taba ganin inda aka yi haka ba, kalaman
Abbansa ya shiga dawo masa.
"Ka je ka yi auren, albarkar da ke
cikinsa ba za ka samu ba!"
Zumbur ya mike cikin faduwar gaba
tamkar wanda aka yi wa allura.
"Azzaluma ce!".
Ya sake tunowa a karo na biyu. Ya
shiga zarya lokaci guda ya ji kamar an
doddoke masa hakarkarinsa, kafafunsa sun
gaza daukarsa, gabadaya ya zube, a kan
doguwar kujera yana maida numfashi da ido
jajir.
Bai san iya tsawon lokacin da ya
dauka a gurin ba, ji ya yi ana kwankwasa
get, da sauri ya daga kai ya dubi agogo,
karfe bakwai saura minti goma. Ya mike
cikin rashin walwala.
115
KA AURE NI=2
"Waye?" Ya tambaya.
"Ni ce".
BILKISU H.MUHDYa dan yi jum, muryar namiji ne
babu isasshiyar Hausa, ya ce.
"Kai wa?"
Ya ce, "John".
Ya kai hannu ya bude get, ya yi arba
da wan Raton mutum, murdadde yana
sanye da riga da gajeren wando, hannunsa
rike da faranti dauke da kwanuka a ciki.
.Kan Mu'allim ya daure, fuska ya
faffake, cikin kaurara murya ya сe.
2
"Lafiya?"
"Ke ne majin ogana? Alaja ne ta turo
ni, ni ce zan dinga yi ma Hajiya aiki".
Ya fada cikin gurbatacciyar
Hausarsa mara dadin sauraro.
A zafafe Mu'allim ya karbi farantin
hannunsa.
"Ka koma ba ma bukata".
116
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Humaida wadda ke tsaye a bayansa
ta gama jin duk abin da ke wakana, ta ce.
"Me ya sa za ka ce haka?”
Ya ji muryarta, da sauri ya juyo tana
sanye cikin wasu makalallun kaya riga
body fitted da wando iya gwiwa ya kama
sosai, ta ci gaba da fadin.
"An taba rayuwa babu tsaftace gida
in ka ce ba ka bukata kai ne za ka yi? Don
ka san ni babu abin da zan daga a gidan
nan, ina gida ma ban yi ba balle yanzu da
na sami gashin kaina".
Ta maida kallonta ga John ta ce.
"Welcome, come in.
Ya ko wuce yana fadin.
"Thank Madam, amma this your ago
is not good".
"Don't mind". Ta ce tana murmushi.
Mu'allim ya yi mutuwar tsaye, ba ta
bi ta kansa ba ta rufa wa John baya.
117
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Humaida kin sauya mini, kin
shammace ni, ganin komai na ke tamkar a
mafarki". Ya fada a zuci.
Kwana biyu bai shiga shirginta ba,
tunda ya lura da take-takenta ko kadan bai
ma cika zama a gidan ba. Hutun sati daya
da man ya samu a gurin aiki shi ke nan bin
gidajen abokai ko ya je ya zauna a bakin
get daga waje.
Daga gidan su Yusuf ya dawo a
gajiye ya riske ta kwance a kan doguwar
kujera tana bacci, jarida kife a ruwan
cikinta. Ya dube ta kurum ya kawar da kai,
ga wani irin sonta a can karkashin
zuciyarsa.
Sashinsa ya ke kokarin shiga ya'ji
motsi a can cikin uwar dakinta, kai tsaye
ya nufi gurin. Ya daga labule, John ya gani
yana gyaran gadon madam din tasa. Cikin
wani mugun tashin hankali bai san sanda
118
KA AURE NI=2 BILKISU M.MUHD
ya ci kwalarsa ba, ya fidda hannu ya tsinke
shi da mari, cikin daga murya ya ke fadin.
"Ashe kai dabba ne, mara hankali,
waye ya ba ka izinin shiga dakin nan? Iyee
waye?"
John ya yi wuki-wuki da ido cikin
rawar murya ya cе.
"Madam ne ya ce na cala mata
daki".
Ya kara shako shi ya janyo shi