mu ci gaba?"
Ga Ummakinsa kwalla ya gani a
fuskarta, ba ta ce masa komai ba, a sanyaye
ta soma tafiya har ta isa ga motarta ta shige,
ta tayar. Yana kallonta ta tafi, duk sai ya ji
ba dadi, so bai ce haka ba, ya yi mata abin
da bai dace ba ko a musulunce. Ta yi juriyar
kula shi, ya kyautu shi ma ya kulata, ya bi
da ita ta sigogi masu kwantarwa ya nuna
mata illolin da ke tattare da ita ba ta wannan
hanyar ba.
A can gida kuma abin da bai sani ba, a
gaban idon Hajara ya shiga motar Humaida,
tunda ta ga haka zuciyarta ke mata zafi, ta
kasa zaune ta kasa tsaye, abubuwa kala-kala
ta ke ayyanawa.
Ta gama cika wa Malam baki, ta gama
alfahari da cewar Mu'allim ba zai ba su
kunya ba, ga shi tun kafin a je ko'ina ya
nuna musu halayen zamani, shin ina
Mu'allim ya kai tarbiyyar da ta dade tana ba
shi? Ina ya kai ladabin da kowa ke yabonshi
26
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
a kai? Ina ya kai kunyarsa da halin da ya
tsiro da shi? Ba ya cikin halin kamammun
yara...
"Assalamu alaikum". Mu'allim ya
shigo cikin sallama.
Kallo daya ya yi mata, yanayinta
gabadaya ya nuna tana cikin matsanancin
damuwa. Gabansa ya fadi, jikinsa ya ba shi
lallai ta ga zuwan Humaida, musamman da
ya ga ba ta amsa masa sallamar tasa ba.
Sum-sum ya nufi kofar dakinsa.
"Na gode wa Allah, a duk yanayin da
na gan ni a ciki yadda na ke ganin ina
sha'awarsu ni ima haka wasu ke ganina su yi
sha'awar irin tawa ni'imar, burina a kullum
shi ne Ubangiji ya kara mini wadatar
zuciya".
Ya san da shi ta ke, don haka ya
dakata ya tsaya kurum.
Ta dube shi cikin daure fuska, ya
dago kai suka hada idanu, ya yi saurin dukar
da kai. Ta ci gaba da fadin.
27
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Duk lokacin da na tsaya a gaban
Ubangijina dukiya ita ce koma bayan abin
da na ke roka a gurin Ubangiji saboda na
gaskata cewa, rashinta ya fi samunta
kwanciyar hankali. Ku san duk wanda ya ke
kokarin ya same ta har abada ba za ka raba
shi da bin kazaman hanyoyi da aka haramta
ba, karya, ansar haram da zamba gami da
hanci da dogon buri, wanda har abada ya ke
hana shi godiya a kana bin da ya samu".
Ta yi tattaki ta karasa gabansa ta се.
"Mu'allim, da kai na ke, ka sauya
daga akidar da muka dora ka, kwadayi da buri karshensu nadama, ka dai bi rayuwa a
hankaii".
Nan ta barshi tsaye motsi ya kasa yi,
wata matsananciyar kunya ce ta kama shi,
daga bisani ya sauke ajiyar zuciya ya juya kofar gida.
28
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Kin tabbatar kwatancen da ki ka yi
mini daidai ne, kada ki sa ni wahala fa?"
"Dad, haka ne mana, amma jikina
yana ba ni kamar wani abu zai faru, amma
ina son ka sani in har ka sake shawara a
kana bin da ka tafi da niyya zan mutu, za ka
rasa ni".
Ya yi murmushi, ya се.
"Baby, shirye na ke na so duk abin da
ki ke so".
Ta saki wata karar farin ciki.
"Thanks Dad".
Ya mike yana murmushi.
"Zan wuce".
"Dad a dawo lafiya".
Da sauri ya sake kallonta cikin
Ummaki, babu ranar da Humaida ta taba се
masa a dawo lafiya sai yau.
A harabar gida ya sami Hajiya Zainab
ta tare shi cikin rashin walwala.
"Shin da gaske ka ke yi, za ka je ka
wulakantar da kanka ka nemi a auri 'yarka?"
29
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ya ce, "Ke ce wadda ta kamata ki fi
kowa sanin halina, kin fi kowa sanin har
abada ba na fatan wata mu'amala ta shiga
tsakanina da talaka, ballantana in dauki
jinina na ba shi, amma dai ki bari in je in
dawo za ki ji yadda muka yi".
"Haba ko kai fa, na ji ja'irar yau har a
dawo lafiya ta ke maka, maimakon Dad a
taho mini da katin waya, a taho mini da
biskit".
Ya kyalkyale da dariya.
"Haka ne, shi ya sa na ke tsoron
95
yaron, lamarinsa azimun ne".
A kofar gidan su Mu'allim Malam
Musa ne ke ta faman kokawa da Yusuf
mahaukaci (Kawu) kokari ya ke ya shigar
da shi gida abin ya gagara, duk ya bi ya
gama gajiyar da shi, ban da cizo da yakushi
da ya sha, Yusuf ya ga in bai yi da gaske ba
za a je a sake daure shi, dutse ya dauka ya
buga masa a kafa, wata gigitacciyar kara ya
saki, bai san sa'adda ya cika Yusuf ba ya
30
KA AURE NI=2 BILKISU N.MUND
rike kafar wanda ya ke jinta kamar za ta
karuye. Abinka da mahaukaci cikin gidan ya
juya.
Injiniya Sunusi ya fito daga cikin
mota yana hange-hange yana neman wanda
zai tambaya, idonsa ya kai ga Malam Musa,
ya yi tattaki zuwa inda Malam Musa ke
zaune rike da kafa.
"Barka da rana bawan Allah".
Malam Musa ya amsa ba tare da ya
dube shi ba.
"Gidan su Mu'allim na ke nema".
Sunan Mu'allim da ya fada ya sa shi
dago kai. Ya dube shi ya kawar da kai yana
kokarin tuno inda ya san Alhajin. Injiniya
Sunusi ya kara maimaita tambayar.
Malam Musa ya nuna masa gidansa.
"What? Kana so ka ce wancan
mataccen gidan nan ne Humaida ke gaya
mini? Amma Humaida na son tozarta ni!!!"
31
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Furucinsa ya sanya Malam Musa yi
masa kallon tsaf, gabadaya yanayinsa suka
sauya.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
Ya dinga maimaitawa, ya yi kokarin
danne 22ciyarsa amma a cikin zuciyarsa
yana jin amkar ya makure shi.
Injiniya Sunusi ya katse masa tunani.
"Ba na jin zan iya karasawa gidan"
Ya sa hannu aljihu, dubu daya ya
dauko ya mika masa.
"Ga wannan, ina son ka je ka yi mini
sallama da mai gidan".
kai.
Bai amshi kudin ba, ya ce.
"Ni ne mai gidan!"
Ya sake dubansa sosai, yana gyada
"Tabbas biri ya yi kama da mutum,
yanayinka gabadaya ya nukna hakan. Kai
yau na yi mugun gamo, ban da makanta har
da talauci? Kai tunda na ke ban taba ganin
mutum mara sa'a irinka ba. Da saurinka ka
32
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ke fadin kai ne maigidan ka dauka banza ce
ta fadi ko? To ba haka ba ne, tsaya ka ji,
zuwa na yi kawai na yi maka akshe di, ka ja
wa yaronka kunne in bai rabu da diyata ba
za ku karasa rayuwarku a kurkuku, ba zan
taba raga muku ba, wallahi ban taba ganin
mutumin da na tsana lokaci guda ba sai yau.
Ba zan taba raga muku ba".
Ya ja tsaki ya juya zai tafi.
Malam Musa yana tsaye kawai kamar
wanda aka dasa, yana son ya fadi inda ya
tsani mutum ya kuma yi masa tunin abin da
ya ke tunanin ya manta. Yana son ya tunasar
da shi.
Addu'o'insa kaf a kansa ya ke
karewa, yana son ya gaya masa cewar bai
san abin da a ke nufi da kiyayya ba sai a
kansa, yana son ya gaya masa bai taba yi wa
wani mahaluki mugun fata ba sai shi, yana
son gaya masa abubuwa da yawa, yana son
sanar da shi da yana da ikon kashewa da ya
kashe shi.
33
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Sai dai ta ya ya zai iya sanar da shi
duk wadannan abubuwan? Idanunsa suka
ciko da kwalla saboda tasowar mikin da ke
zuciyarsa ba zai barsa haka ba sai ya gaya
masa ko da kalma daya ce don kada ya mutu
da bakin ciki.
"Ji mana!" Ya ce lokacin da ya ke
kokarin shiga mota.
Ya dakata da shiga motar yana
Kankance idanu jin irin sigar da Malam
Musa ya tsayar da shi a matsayinsa na talaka
fitik.
Malam Musa ya karasa kusa da shi, ya
се.
"Kafin ka tafi ina son ka sani,
Annabawan Allah sun rayu a cikin irin
wannan rayuwar talaucin, inda Ubangiji ya
so da ya azurta su fiye da kowa ka da ka
manta, arziki ya sa Fir'auna, Hamana da
Lamarudu suka yi wa Ubangiji dagawa, ka
manta ina Karuna wanda shi ma kudi ya
saka shi ya yi wa Annabi kazafi ya nutse a
34
KA AURE NI=2 BILKISU N.MUND
kasa ko rayuwar wadannan mutanen ka
duba hakan ya ishe ka aya, don haka ka ji
tsoron Allah..."
Injiniya Sunusi ya katse shi ta hanyar
daka masa tsawa.
"Kai talaka me ka ke gaya mini haka,
wa'azi ko maula? To bari ja hu kurwar
diyata ta fi karfin taku".
Malam Musa ya yi murmushin takaici.
"Lallai iska na wahalar da mai kayan
kara, kowane mutum burinsa ya hada zuri'a
da gidan mutunci ba gidan masu halin
dabbobi irinku ba, a kan na hada zuri'a da
ku gwara in roki Ubangiji ya kashe dana
kafin ganin hakan, yarona mai tarbiyya ne
ba irin 'yarka ba, shashasha".
Ummakin karfin hali irin na Malam
Musa talaka ya hana shi motsi, kallonsa ya
ke tun daga sama har kasa yana son ya
shake shi, sai dai ya sa a ransa lallai akwai
abin da Malam Musa ya taka. Bai iya yin
35
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
kwakkwaran motsi ba har Malam Musa ya
shige cikin gidansa.
*** *** ***
"In har kana son samun albarkata kada
na kara jin ka kalli yarinyar nan in har ka sake wata mu'amala da ita ko da ta magana
ce ban yafe ba".
Yadda ya ga Abban nasa ya birkice ya
yi matukar Ummaki ya ci gaba da fadin.
"Shekaru da yawa ina zaman lafiya na
iya talaucina, don haka babu wanda ya tabа
yunkurin wulakanta ni sai yau mahaifinya
ya zo ya kare mini cin mutunci wanda babu
wani da ya taba yi mini. Tashi ka tafi".
Ya koma daki jiki a sanyaye, ya shiga
rudu sosai.
Adnan da Yasir sun dade tsaye a
kansa suna magana, sai daga karshe sulka
taba shi tare da neman gurin zama.
Adnan ya dube shi.
"Abokina gaya mini?"
36
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUND
Mu'allim ya kada kai ya ce.
"Abba ya tsananta a kanta, wai ya ce
babanta ya zo ya ci masa mutunci, wai da
ma Abba ya san shi ne, al'amarin nan na ba
ni Ummaki".
"Da ka ce ya goya maka baya, ya
kuma saka zai sauya, anya babu masu
kewayowa su zuga shi?"
"Haka na ke zargi".
Yasir ya ce, "Ni a tunanina tsoro ya ke
ji saboda su masu kudi ne, ni dai shawarar
da zan ba ka kada ka bari damar nan ta wuce
ka. Ko don ka ceto Kawu daga halin da ya
ke ciki, kana da tabbacin cewar kawu zai
warke, ina ganin hakarka ta kusa cimma
ruwa da zarar ka auri Humaida ka gama
talauci".
"Haka ne, sai dai matsalar Abba ba żai
taba fahintata ba, kawu ya yi dawainiya da
ni burina a duniya bai wuce in sama masa
lafiya ba, ina son Ubangiji ya ba ni wannan
'damar ko da shi ne kadai abin da zan yi a
37
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
duniyar nan ina Kaunar Kawu fiye da kaina,
zan jure duk wani kalubale daga Abba, na yi
amfani da wannan damar da ta zo mini.
Na yarda zai yi fushi da ni
matsananci, zai yi Ummakin yadda yaro mai
biyayya ya sauya masa, sai dai nan gaba zai
gane abin da na ke nufi, musamman in
Kawu ya sami lafiya"
"Yaron nan ya fara ballo mini ruwan
da cinye ni da yaki. Alhaji Auwal ka gaya
mini ya zan 6illo wa al'amarin nan?"
Alhaji Auwal ya fuskance shi, ya сe.
"Humaida kadau ka mallaka, hakan ya
sa tun farko ba kwa nuna mata abu mai kyau
da mara kyau ku ka barta ta yi duk abin da ta
so, ka ga yanzu kuwa ka ce za ka tilastata a
kan barin wani abu zai yi wuya. Shawarata
kawai ku amince mata tunda duk binciken
da na yi a kan yaron ba shi da wani aibu,
talauci da rashin aikin yi shi ne matsalarsa".
38
KA AURE NI=2 BILKISU N.MUND
Injiniya Sunusi ya ce, "Wannan shi ne
babbar matsala, zan iya juriya a kan komai
amma ban da talauci na tsani talaka don
haka kullum na ke neman tssari da talauci,
duk inda ya ke ba na rabar gurin gudun kada
ma ya waske ni".
Alhaji Auwal ya ce, "Ina ganin haka
ne ya sanya ayar Allah ta sauka a kanka
gurin nuna maka ishara. Ina ba ka shawara
kada ka soma ja da ikon Allah..."
huci.
"Ban fahince ka ba?"
"Ina nufin ka bari ya aure ta".
Zumbur Hajiya Zainab ta mike tana
"Wallahi ba za ta sabu ba, wannan ba
shawarar kirki ba ce ka ke ba shi. In talaka
ba abin gudu ba ne mai ya sa da za ka aurar
da Amina ba ka bai wa talaka ba? Ji na ke yi
wanda ta ke so talaka ne amma fir ka ki
amincewa ka dauke ta ka ba wa dan gidan
"
mataimakin gwamna aurenta...'
39
a
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Ji nan Hajiya Zainab, diyata tun
farko ina tsaye a kanta na kan kwabe ta
kuma in tirsasata ta yi yadda na ce ki da
kuwa ba ta so, hakan ya sa ta amince da
zabina, ku kuwa taku na sani ko da za ku
yankata ba za ta bi ra'ayinku ba, turbar da
ku ka dora ta a kai ke nan tun asali".
Ai ko gabadaya ta hau jifansa da
bakar magana.
"Karya ka ke, da ma an ce
munafikinka tabarmarka, gwara da ka yi a
gabanmu..."
Injiniya ya katse ta da fadin.
"Ke Zainab! Ki san da wanda ki ke
99 magana
Ya juya ga Alhaji Auwal.
"Ka yi hakuri mu koma ofis mun
karasa maganar a can".
Suka mike za su fita, ta bude murya bakidaya.
40
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Ya dai tawa ce ba wani ne ya haifa
mini ba, in kai ya shanye ka don ya dinga
juya ka ni na fi karfinsa".
Alhaji Auwal ya girgiza kai kawai
yana murmushin takaici.
gurin.
"Injiniya Sunusi ya се.
"I say stop it mana!"
Ta ga ransa a bace ne ya sa ta barin
Ya ga dai Humaida da gaske ta ke, ya
dauki waya a kan tebur yana son kiranta, ya
yi karfin halin lalubo layinta.
Tana kwance a doguwar kujera ta ji
wayarta ta dau ruri ta mika hannu kan tebur
ta dauka, lambar Mu'allim ta gani, ta mike
da sauti ta amsa kiran tare da karawa a
kunne.
"Talaka na ganinku?"
Ta yi murmushi, "Wace ni, barinka na
yi ka sha iska".
Ya ce, "Iska kamar ya ya?"
41
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Та се, "Macen arziki namiji ke zuwa gidansu ba ita ta je ba, na damu da kai don
haka na bi yadda ka ke so. Nasiharka ta
sanya ni jure rashin ganinka".
ya ce.
Ya yi murmushin da ta jiyo sautinsa,
"Allah sarki, Humaidata".
Ta zabura a dokance, ta ce.
"Me ka cе?"
Ya ce, "Cewa na yi Humaidata
Ta ce, "Sake fada na ji".
Ya yi murmushi, "Humaidata!
Humaidata!! Humaidata!!! Ya isa haka ko
na ci gaba?" YBW
"Ya isa haka Mu'allim, yau ka ba ni
farin ciki ina tsoron zan roki wata alfarma a
gare ka..."
"fadi duk abin da ki ke so, na
sadaukar da wannan ranar a gare ki".
Ta yi shiru zuwa wani lokaci.
"Ke na ke sauraro
Ta ce, "Ina fargaba...
42
KA AURE NI=2
"Kada ki damu"
"Ka ce mini za ka zo".
BILKISU H.MUHD
"Abin da ki ke bukata ke nan? In na
ce zan zo ya za ki yi da Dad?"
"Kada ka damu, ya yi nadamar abin
da ya aikata maka".
"Gaya mini, yaushe ki ke so na zo?"
"In na ce yanzu ya yi?"
"Ki yi mini uzuru zuwa gobe".
*** *** ***
"Kana da kudi in ka so za ka iya
maida shi yadda ka ke so zai hau motoci zai
rayu a babban gida kerarre, ta ya ya hakan
دو zai yiwu, duk kai ne za ka mallaka masa".
"Alhaji Auwal mai ke damunka, kana
da lafiyar kwanya kuwa? Tun ina karami na
ke bin hanyoyi iri-iri don na tsira daga
talaucin da na yi karatuna babu wanda ya
taba taimakona kai ma ka san wahalar da
sha ta ya ya za ka ce na mallaka wa wai duk
43
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
wadannan abubuwa na sauya masa rayuwa
dare daya? Ba zai yiwu ba!"
Ya fada ciin kakkausar murya.
Alhaji Auwal ya mike tsaye ya karasa
gurin da Injiniya Sunusi ke zaune ya zube
hannayensa a kafadunsa.
"Kwantar da hankalinka mana, haba
sai ka ce ba dan garin nan ba, bari in yi
maka gwari-gwari yadda game din zai
kasance"
Tsawon mintina biyar yana gaya
masa, Injiniya ya ce.
"kana ganin hakan zai yuwu?"
"Sosai kuwa".
Suka yi dariya. دو" Kai mutumina ba ka da dama".
A karo na biyu yau ma duk ta birkice
sif da akwatina tana neman kayan da za ta
saka saboda zuwan Mu'allim. Ta sake janyo
wata akwati ta bude ta dauko doguwar riga
English wears, ta bude shi tana kallo ta kada
kai ta yi ciki da shi, ta sake dauko riga da
44
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
wando fakistan ta daga shi shi ma bai yi
mata ba. Ta cije lebe ta mike ta hau ta kawo.
Hajiya Zainab ta turo kofar dakin ta shigo.
Ko'ina a birkice ta dube ta.
"Humaida, me ye haka?"
Cikin yanayin damuwa ta ce.
"Mom please, ki taimaka ki gaya mini
inda zan sami kayan hausa".
Ta ja tsaki, "ban fahince ki ba".
Humaida ta ce, "Ina nufin riga da zani
da hijabi".
"Me za ki yi da su?"
"Mu'allim zai zo na kuma lura shigar
da ya fi so ke nan ya ga ina yi".
Ta tabe baki ta kuma kwaikwayi
muryar Humaida cikin abin da ta се:
"Mutuniyar wofi, har ki dinga kokarin
faranta wa wani can kina muzanta mana in
an yi magana Dad dinki ya ce kuruciya, ai
ga irinta nan shaidaniyar banza".
Ta yi tsaki ta fice a dakiln.
45
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Humaida ta rushe da kuka, "Mom bа
kya sona tunda ba kyá son faranta mini".
Ta yi waje, Mustapha ta tarar yana
karatun alkur'ani ta yi masa sannu, ya bi ta
da ido yana Ummaki, ya rufe alkaur'anin.
Та се, "Mustapha ka taimake ni
please
Ya sanyaya murya, "Me ki ke
bukata?"
"Ina so ka samo mini riga da zani da
hijabi".
Ta mika masa dubu ashirin.
"Ina sonsu a dinke nan da awa uku,
please akwai tukwaici mai gwabi".
Bai wani sami matsala gurin shiga
gidan ba, tuni maigadi ya san da zuwansa,
yana tsaye a harabar gidan yana laluben
layinta.
Tsaye a gindin madubi cikin shigar
zani da riga tare da hijabi ta ke tana kallon
kanta. Ta yi murmushi.
46
KA AURE NI=2
"Malama Humaida!".
Ta kyalkyale da dariya.
BILKISU H.MUHD
"Babu laifi, na yi kyau sri dai zafi".
Karar waya ya katse ta ta dauka ta
manna a kunne.
"Ka iso ke nan?"
Ya amsa da, "Eh".
Ta yi saurin katse wayar ta dauko
turare ta feshe jikinta da shi, cikin sauri ta yi
waje.
Hajiya Zainab da jarida rike a
hannunta tana dubawa.
"Mom, ya ki ka gan ni?"
Ta dago kai tana dubanta.
"Ina za ki je?"
Ta tambaya cikin daure fuska.
"Haba Mom, sau nawa zan gaya miki?
Ji na ke dazu na sanar da ke cewa 'zan yi
bako?"
Ta mike ta ajiye jaridar a gefe.
"To ba za ki je ba".
"Uhm Mom na sani wasa ki ke yi"
47
KA AURE NI=2
Cikin daga murya ta ce.
"Ki koma daki na ce.
BILKISU H.MUHD
Ko dar ba ta ji ba ta dube ta.
"Mom, ko Dad ba na tsammanin zai yi
abin da ki ke kokarin yi".
Ta kausasa murya tana fadin.
"Ashe ba ki da mutunci
Ta kama hanya za ta fita cikin
kunkuni.
Cikin zafin nama ta finciko ta.
"Mom kina son wasa da rayuwata, ki
cika ni ina fargaba kada na ba ki Ummaki.
Idanuna sun rufe zan iya yin komai".
Ta kwace daga hannunta ta fice daga
sitroom din, Hajiya zainab ta koma ta yi
yaraf a kan kujera, Humaida ta yi nisa ba ta
jin kira, ya ya za su yi?
"Kina da kyau, kin fita daban cikin
mata Humaida, yau zan sanar da ke ina
sonki, ina matukar sonki".
Ta yi murmushi mai yalwa.
"Sannu da zuwa".
48
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Lambu ta ja shi, ya dube ta yana
murmushi.
"Kin jima ba ki fito ba, Allah ya sa
lafiya?"
"Macen arziki in aka aika kiranta sai
ta dan jima kafin ta fito, ba ta fito nan da
nan tana rawar jiki ba".
Ya shafa kai cikin jin kunya. Ya yi
saurin basarwa.
"Humaida ke nan, na same ki lafiya?"
"Lafiya kalau, sai dai kewarka".
"Da gaske ki ke?"
Ta ce, "Sosai ma kuwa".
"Amma kin ba ni Ummaki".
"Kamar ya ya?"
Ya ce, "Sai ana sonka a ke kewarka,
ko kin mance kin ce ba sona ki ke ba, kina
so ne na aure ki?"
"Na rasa me zan kira abin da na ke ji a
zuciyata game da kai, yadda na ke ji ya fi
karfin so, shi so wataran ya kan rikide ya
49
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
zamo kiyayya, in ko na ce KA AURE NI,
hakan na nufin ba zan taba kinka ba".
"Babu namijin da zai dube ki ba tare
da ya yi fatan ki zamo mallakinsa ba, ina
donki tuntuni, to matsalar in na amince da
me zan aure ki? Ba ni da komai".
Hon da suka ji ne ya katse shi, a
tsorace ya dubi Humaida.
"Dad ne ya dawo".
Bai san sa'adda ya mike tsaye ba.
"Kada ka damu".
Yana kallo ya fito daga mota, ga
Ummakinsa gurinsu ya ke tahowa. Tuni ya
yi mutuwar tsaye.
"Please ka zama namiji, dad ba ya son
6acin raina babu abin da zai faru”.
Lokacin da Injiniya Sunusi ya Karaso
daf da su tsoro ya bayyana karara a kan
fuskar da sauri ya durkusa cikin rawar
murya.
"Sannu da dawowa".
Ya dube shi da fuska a sake.
50
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Kana lafiya, baby in kun gama sa: ya
zo ya same ni ko?"
Ya wuce ya tafi, ajiyar zuciy ar da ya
saki ya sanya Humaida kyalkyala dariya
"Haba irin wannan kidimewar haka
taho mu je in. nuna maka inda za ka same.
shi".
"Ka dauke ni a matsayin uba, na kan
so duk abin da babyna ta zo mini da shi tun
farko da ka ga na ki na yi tunanin irin yaran
nan ne mayaudara, masu gurbata tarbiyya da
lalata sai dai da na gama bincike na sai na ga
ba ka daya daga cikinsu don haka na ke son
mu yi magana ta fahinta. Kana sonta ne ko
samartaka kawai ka zzo ku yi?"
Ya sunkuyar da kai cikin jin kunya.
"Ina sonta, sai dai zan so a jinkirta
mini har zuwa lokacin da zan sami aikin yi".
"In dai wannan wannan ce ba wata
matsala ba ce gobe ka same ni a kamfanina".
Ya dauko card ya ba shi.
51
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Wannan Katina ne ka taho da
takardunka don na san inda zan yi".
Ya risinar da kai yana godiya.
"No babu godiya a tsakaninmu, ai yi
wa kai ne".
Suka yi sallama ya fito. A kofar gurin
ya sami Humaida.
"Ya ku ka yi da Dad?"
"Cewa ya yi kada na sake zuwa gurinki".
Ta juya cikin sauri za ta shiga gurinsa,
cikin kiran, "Dad! Dad!!".
"Humaida! Kin san abin da ki ke yi
kuwa? Wannan ai ba tarbiyya ba ce, in ba ki
girUmma shi ba zai iya yiwuwa ni ma ba za
ki girUmmani ba bayan na aure ki”.
"Idanuna sun rufe, ka gaya mini me ya
ce da kai".
Ya mika mata katin hannunsa, gurin
karba ya yi ido biyu da wasu irin farata
masu kyau sun sha kunshi, sai dai sun yi
tsayi da yawa. Ya gaza dauke idanunsa.
52
シ
KA AURE NI=2
"Me ka ke kallo?"
BILKISU H.MUHD
Ya ce, "Rumfar shaidan na ke kallo".
"Ban fahince ka ba".
Ya ce, "Faratanki su ne rumfar
shaidan".
"Faratan nawa? Ka san kuwa nawa na
ke kashe musu a duk sati? Haba Mu'allim
kar fa ka zaci don na ce KA AURE NI
hakan na nufin ba ni da sauran 'yanci ke nan
ba"
"Yanci? Mene ne 'yanci? Al'adun
yahudu su ne suka zamo 'yanci? Humaida
dole ne ki sauya duk wannan dabi'un, dole
ki rage su. Ki je ki yi nazari ba zan dauka
ba".
Ya juya zai tafi, ta yi saurin shan
gabansa.
"Ga katinka".
Ya ce, "Ba shi da amfani a gurina".
Ta raunana murya, "Ka gaya mini me
ka ke so?"
53
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Humaida ina son ki sauya duk wani
'yanci da ki ke tunanin kina da shi, ina son
ki sauke shi ki koma saiti kamar yadda
musulunci ya tanada, in kin amince da haka
Humaida zan aure ki".
Ya ci gaba da tafiya, ta sake shan
gabansa.
"Kada ka tafi ka bar ni".
"Humaida zan tafi".
Ta ce, "Ina ji a jikina Dad zai amince
da batunmu me ya sa ba za ka amsa
gayyatarsa ba?"
"Zan amsa lokacin da za ki zamo
macen bahaushiya sai anjima"
"Mu'allim! Mu'allim!! Please kada ka
tafi, ka saurare ni kada ka tafi”.
Ko waiwayenta bai yi ba ya fice daga
gidan.
Gabadaya hankalinsu Malam Musa
kya kwanta suna tunanin sun kashe matsalar
Mu'allim, shi ma kuma ya iya takunsa, ba
54
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ya taba nuna musu da akwai sauran alaka
tsakaninsa da Humaida.
Yau ya kawo musu labatin samun
aikinsa, Hajara da Malam Musa sun kudiri
aniyar daukar azumi don nuna godiyarsu ga
Ubankgiji.
Wata daya kacal da fara aiki
rayuwarsu ta soma sauyawa, albashin farko
kayan abinci ya jibgo musu da dai abin da
ba a ra a.
ara da Malam Musa a tsakar gida
Suna ra cikin nishadi, malam Musa ya
dubi Hajara.
"Kin ga danki da rigima ko?"
Ta kalle shi, "Wacce irin rigima?"
"Ya dage wai lallai sai na daina likin
takalmi".
"Malam ai abin da kullum mu ke roko
ke nan, U ngiji a kawo ranar da za ka
.huta دو
nan?"
"Au ke ma kin na da goyon baya ke
55
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Gani ya yi ta yi shiru ya kira sunanta.
Ta kalle shi.
"Tunanin me ki ke yi haka?"
"ina tuno Kawu Yusuf, lokacin da
yana da lafiyarsa kullum addu'a ya ke yi wa
Mu'allim, yau ga shi ba ya a hayyacinsa
addu'arsa ta karbu".
Malam Musa ya ce, "Amma kin san
wani abu Hajara? Kawai na ji hankalina ya
kasa kwanciya da Mu'allim".
Та се, "Кamar ya ya ke nan? Haba
Malam me ya sa ka ke haka? Takardun
yaron nan fa a gurinka suke, ya zo ya amsa
in ba aiki ba ne zai karba ne? Ko kana son
ka ce sata ya ke yi?"
"Ba na taba zargin yarona, sai dai
zuciyata tana raya abubuwa da yawa, amma
ina nan ina bincike, ko ma me ye zan ci gaba
da gaya wa Ubangiji, koma me zai bayyanar
da gaskiya".
Ran Hajara ya gama bасі.
56
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Haba Malam in ba za ka fadi alheri
ba ka yi shiru, kada ka yi masa baki ya fada
kansa..."
Sallamar Mu'allim ya sanya su yin
shiru, ya durkusa yana gaida su, ya mika wa
Hajara leda.
"Me muka samu?" Ta tambaya.
Ya ce, "Kaya ne na siya wa Kawuna".
Malam Musa ya ce, "Allah ya yi
albarka, Ubangiji ya sa ka fi haka, ba ka
gajiya da hidima".
Hajara ta ce, "Da izinin Allah sai
kawunka ya samu lafiya ya tabbatar da
fadawar addu'arsa a kanka".
"Umma da izinin Allah ya kusa samun
lafiya nan da wani kankanin lokaci komai
zai zamo labari".
"Ubangiji Allah ya tabbatar, amma
kafin nan sai ka ayi aure ko?"
Ya dan shafa kai.
"Umma lafiyar kawu ne a gabana".
57
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Malam Musa ya bude ledar shaddoji
ya