An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KA AURE
N
HAUSABООK.COM
2
KA AURE
BILKISU H. MUHD
Harafi Publlshers KaAure Ni
BILKISUHAMUHD
KA AURE NI=2
KA AURE NI-2
BILKISU N.MUKD
a cе, "Kada ka sake Ytambayata, don babu abin da
za ka ji daga gare ni, in har ka
amince ni ne mahaifinka ka sa a ranka
tamkar ba ka taba saninta ba, amma kafin
nan ina so ka sani babu wani gado da ya fi
kwaun hali amfani, kuma babu wata taska
da ta fi ladabi duk abin da ya yi yawa ya kan
yi arha, amma ban da kyawun hali. Shi yana
kara yawa ne yana kara tsada, al'umma ta
kan tabbata ne matukar kyawun halinsu ya
tabbata, in kuwa dabi;arsu ta tafi su ma sun
tafi da yawa mutane sukan mutu yayin da
dabi'unsu suka mutu, sai ka ga mutane a
raye amma matattu ne.
Jikin Mu'allim ya yi sanyi sosai. Ya
mike ya shiga gida.
Wuni ya yi sur yana nazarin
maganganun Abbansa, yana matukar son
Humaida, ya zai ya tursasa wa zuciyarsa a
kan ya rabu da ita? Bai taba tunanin sonta ya
4
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
yi zafi haka ba, yana jinta tamkar
numfashinsa. Yana zaune a kan tsohuwar
kujerar da ke dakinsa, lokaci daya ya mike
ya shiga zarya har lokacin laluben mafita ya
ke, damuwa ce karara lullube a fuskarsa.
Wayarsa ta yi kara, ya dauka ya duba,
Humaida ce, ya dubi agogon da ke daure a
tsintsiyar hannunsa, karfe daya da kwata na
dare, ya ja tsaki ya maida wayar ya ajiye, ya
koma ya zauna defe da kai har ta gaji da ruri
ta katse, kiran ya sake shigowa, hannayensa
biyu ya saka ya toshe kunnuwansa, sai da ta
sake katsewa ya sauke hannayen nasa ya
kwanta.
Ba a jima ba kiranta ya sake shigowa,
a zafafe ya mike ya dauki wayar gabadaya
ya kashe ta.
*** *** ***
Ta fito daga daki rike da mukullin
mota, ko kallon inda su Dad suke ba ta yi
ba, kokarin gota su ta ke yi, sun sa mata ido
5
KA AURE NI=2 BILKISU M.MUND
kurum. Da Dad ya tabbatar fita za ta yi sai
ya yi saurin dakatar da ita.
"Humaida, ya kin an.
Tana tsaye ba ta kallo inda suke ba, ta
ba su baya.
Ya yi murmushi cikin kada kai.
"Zo ki gaya min waye ya bata miki
rai?"
Gabadaya ta juyo tana fuskantarsu,
cikin muryar kuka ta ke magana.
"Dad, ka daina ganin murmushi a
fuskata!"
Ya mike tsaye ya yi tattaki zuwa inda
ta ke, ya се.
"Murmushi ba zai taba gushewa a
wannan kyakkyawar fuskar taki ba muddin
ina raye, rashin murmushi alama ce na bakin
ciki, ni kam burina a kullum in ganki cikin
farin ciki, muddin kina da ni babu ke babu
matsala".
Wasu sababbin hawaye suka dinga
sintiri a kan fuskarta, ta runtse ido ta bude.
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Ina son ka tabbatar mini da haka, don
na gaji da gafara sa kullum zancenka guda
daya ne, ban ga ka cika shi ba, ka dauke ni
tamkar 'yar baby, Dad in har abin da ka ke
fada na murmushi ba zai gushe a fuskata ba,
ka amince min in aure shi".
Ya kai hannu ya dafa mata kafada.
"Zan yi yadda ki ke so, akwai nazarin
99 da na ke yi ne...
"No Dad!" Ta ce da karfi, "Kana so
ka rusa mini tsari na.
"Wannan karon zan kara rokonki ki
יי ba ni kwana uku kin ji?"
Ba taice komai ba, ta janye jikinta ta
fice tana sharar kwalla.
"Please, ki fita daga rayuwata na huta,
tunda ki ka shigo rayuwata farin cikina ya
gushe, ke shu'uma ce mahaukaciya, ki je ki
koyi hankali sannan na saurare ki".
"Mu'allim!" Ta kira sunansa cikin
muryar kuka.
7
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Saboda ina nemanka da alkhairi shi
ne za ka samu damar ci mini mutunci, ashe
ra'ayi yana zamowa laifi don na ce ina
ra'ayinka shi ne duk ka janyo ka ke kirana
da dabba, mahaukaciya?"
Cikin rashin damuwa ya ce.
"In kin je ki tambaya ki ji babu mutumin da zai sa ki a sahun masu hankali,
don duk abin da ki ke yi na mahaukata ne, ki
je ki tambayi bambancin hankali da rashinsa".
Wata kara ta kwalla da sauri ta shige
mota ta bar gurin.
Adnan ya karaso inda ya ke.
"Tabbas ba ka dara ba, na yarda abin
a jininka ya ke".
Ya dube shi a fusace.
"Don Allah ka kyale zuciyata ta huta,
ka rabu da ni".
Ya yi tsaki ya bar gurin.
*** *** ***
8
=
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Saboda ba ni da shi sai a turo mini
kananan yara suna yi mini fitsara har suna
jifana, sannan ki ce na yi hakuri? An dade
ana yi min wadannan abubuwan ban taba
daga kai ba, amma abin ya ishe nim wannan
karon zan dauki mataki".
Saudatu ta kada kai.
"Ba za ki iya da su ba saboda ba ki da
komai in ki ka doshe su mahaukaciya za su
dauke ki".
Ta dafa goshinta inda ya kumbure
saboda jifan da yaron ya yi mata.
"Shi ke nan Saude, na bar su da Allah,
domin na san shi ne kadai zai bi mini
hakkina".
Ta fada tana sharar kwalla.
"Ki yi hakuri, ga wannan babu yawa
kin sayi magani".
Ta mika mata naira dari biyu.
"Ni zan tafi".
9
KA AURE NI=2
Da sauri Mu'allim
BILKISU M.MUND
ya ja da baya,
Saude ta fito ya yi saurin rufa mata baya, ya
koma ya sha gabanta.
"Mu'allim kai ne?"
Ya kada kai yana kallonta da idonsa
jajir.
"Ina son ki gaya mini waye ya aikata
wa Ummata?"
"Ka yi hakuri ba na son haddasa
fitina".
"Ba fitina ba ce, ina son kwatar mata
'yanci".
Saude ta yi murmushi, "Mu'allim ke
nan, akwai babban 'yancin d ya wuce ka
mike ka nemi kudi ba za ka taba daina ganin
kaskanci ba da kai da iyayenka har sai ka
zama wani, me ya sa ba za ka zamo da na
gari mai kishin iyayensa ba? Wallahi
muddin ba ka yi haka ba kana tare da la'ana,
bakin jama'a zai fada maka, ka ganka namiji
har namiji amma sai dai ka kwanta a nemo
ka ci, to in ba ka sani ba idanun jama'a а
10
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
kanka ya ke, kullum zagi da tsinuwa a kanka
ya ke karewa.
Ka ji tsoron Allah ka tashi ka nemi na
kai a ko ina ne, muddin halali ne ka taimaki
Hajara, ka ga yadda ta dawo".
Ga Ummakinsa kwalla ya ga Saude na
yi.
"Wallahi Mu'allim da na haifi dan da
ba ya tausayina gwara na zauna a haka, kа
tabe ka gama tabewa".
Da sauri ta bar gurin, jiri ne ya dinga
- daukarsa, idanunshi suka rufe ya daina gani
ya koma ya bi jikin bango ya zauna jabar
dafe da kai.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
Ya ke ta maimaitawa, da kyar ya
samu ya dawo daidai, ya mike ya nufi gida.
Da kumburarren goshinta ya fara arba,
gabansa ya buga, da kyar ta ke iya bude
idanunta.
"Umma, waye ya aikata miki haka?"
Ta yi kokarin kirkiro murmushi.
11
KA AURE NI=2
"Bugewa na yi..."
BILKISU H.MUHD
"A'a umma, kada ki gaya mini haka,
kada ki 6oye mini don Allah".
"Kai ka ji min yaro, wa ka ke tunanin
zai yi mini haka?"
Ya sani ba za ta fada ba, don haka bai
tilasta ba.
"Allah ya sauwake"
Ya ce, ya koma dakinsa ya dinga
zarya zuciyarsa na yi masa ciwo, abubuwa
iri-iri ya dinga sakawa, Humaida ita ce
damuwarsa, babu abin da ya tsana irin ya
zamo mijin Hajiya, yana Ummakin mazajen
da ke auren jaro, ya tsani irin wadannan
mazajen, yau ga shi burinsa zai janyo ya bi
sahun wadannan mazaje, dole ya amince da
Kudirinta.
Tun daga aruber gida ta soma kiran.
"Dad! Dad!! Dad!!!?
12
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Har ta isa babban sitroom. Yana zaune
shi da Hajiya Zainab, ya yi saurin mikewa
yana duban ko'ina na jikinta, sai da ya
tabbatar ba ta tare da wata matsala sannan
ya sauke ajiyar zuciya.
"Uhum baby ke na ke sauraroro".
"Dad, ina son ka sanar da ni yau me
ye hankali, me ye kuma yarinta? Mene ne
bambancin hankali da rashinsa?"
"Kafin na ce miki komai ki koma ki
zauna, ki kuma daina kukan nan".
Ta yi kamar yadda ya bukata.
"Dad, ba ka ba ni amsar dukkan
tambayoyina ba".
"Humaida zan ba ki amsar
tambayoyinki".
Ta kafe shi da ido alamar shi ta ke
sauraro, ya сe.
"Hankali shi ne nutsuwa, wanda kuma
tunaninsa bai jirkita ba bambancin hankali
kuma da yarinta, kin ga kamar ke da
Mustapha hankalinku ba daya ba, yanzu na
13
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
hana ki fita da yamma za ki iya ki yi
ficewarki, ta yuwu fitar da za ki yi za a yi ta
kawo mini kararki, wani fannin za a ce kin
kade wane ko wance, ko kin ci kwalar
wancan da dai sauransu. Amma shi
Mustapha a wannan lokaci yana ina?"
Ya karasa maganar yana kallonta. Та
yamutsa fuska.
"Na san ba zai wuce a ce yana can
yana fama da carbi ba, ni ko tun farko kai ne
ka hana ni ka ce in na yi ba zan dinga samun
hutu ba".
"Okey, kin gamsu da amsoshina, sai
wacce tambayar za ki yi?"
Ta kada kai, ta ce.
"Ban gamsu ba Dad, asalima soki
burutsu kurum na ji kana yi"
Hajiya Zainab ta mike a fusace tana
nunata da yatsa.
"Ki minin shiru na ce ko na karya ki
sakarya, shashasha kawai, wallahi...
14
と
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"A'a Zainab, kyale ta, in ba
tambaye ni ba wa ki ke so ta tambava?"
Ya juya ya kalli Humaida.
ta
"A karo na biyu kin ga hankali shi ne,
kin ga yanzu an gan ki fes da ke kamar mai
hankali, amma za ki ringa abu na kuruciya
...tsantsa وو
Ta sake dubansa cikin rashin
gamsuwa, ba ta kuma bari ya sarara ba, ta
dora da cewa.
"Dad kawai ka fito fili ka gaya mini
ina abu na marasa hankali, domin Mu'allim
ma kullum maganarsa daya ce a kaina".
Cikin kuka ta juya dakinta.
Hajiya Zainab ta dube shi ta ce.
"Ka ga irin ta ko?"
"I say shut up! Saboda haka sai na
kamata na daka ki ke so ko? Ina gaya miki
baby yarinta ce ke damunta..."
"Haba alhaji, yarinya ta kai shekaru
ashirin ka dinga kiranta da yarinya? Wane
15
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
mataki ne ba ta taka ba na imili, ashe ke nan
ba za ta taba yin hankali ba?"
Ta kada kai ta shige faki, shi ma ya
tashi ya nufi dakin Humaida.
Tana zaune a kan gado ta rafka
tagumi, idanunta na ambaliyar da hawaye.
Ya tausasa murya cikin tsananin tausayinta.
"Kuka ki ke yi har yanzu? Tashi goge
hawayenki mu yi magana, mai ya yi zafi? In
kina son in dauki mataki a kan wanda ke
kiranki da mara hankali sai na dauka..."
"Dad, me ya sa ka gurbata min
rayuwa ba ka sa ni a sahun masu hankali ba
ka sa ni a sahun mahaukata?"
Ya rude sosai, ya ce.
"A'a, ba haka ba ne. babu wanda zai
kira ki da mahaukaciya, duk wanda zai
ganki sai dai ya yi da ma shi ne ke".
"Dad, mutane da yawa na yi mini
kallon haka".
"Ke ki ke ganin haka, wadancan masu
fadin haka ba su san zafin 'ya'ya ba, suna da
16
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
su da yawa, ke ko kin ga ni ke kadai ce gare
ni, ke kadai ce a gidanku, ba ki ga bature ya
bai wa kowa 'yanci ba, misali ba mun je
Rasha da ke ba, kin gani ba mun je America
da sauran kasashe kin gani ba? To me ki ke
son ai miki?"
Ta mike tsaye tare da juya masa baya.
"Dad, ka yi hakuri da abin da zan
gaya maka, ku kuka jawo mu mu zama
rakumi ku akala mu ja ku mu tafi
jahannama..."
Da sauri ya katse ta da daka mata
tsawa.
"Ni za ki kawo wa rashin tarbiyya da
rashin mutunci? Kina bin wadancan 'ya'yan
talakawan suna gurbata miki tunani?"
Hajiya Zainab ta shigo a sukwane, ta
fidda hannu ta tsinka wa Humaida wani
gigitaccen mari tana huci.
"Ga irinta nan, yarinya ta kai tsaiko
abin da kullum na ke jiye maka ke nan”.
17
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ita kam 'yar lele juyawa ta yi ta fita a
guje cikin ihun kuka.
*** *** ***
"Ka yi hakuri tunda Abbanka ya ke
bai san me ye dadi ba, don haka babu abin
da zai dorar a rayuwar ya kare a talauci,
zuciyarsa ta riga ta mutu ba zai taba ganewa
ba, yakin naka ne duk lokacin da ka cire
musu wannan tsatsar a nan ne za su gane
ashe da su mutane ne su. Ka aure ta in sun yi
fushi a hankali watarana za su gane gaskiya,
talauci ya yi musu mugun kamu, ya zame
musu illa kada ka bari yarinyar nan ta
subuce maka. Ba zan gaji da ce maka ba in
har hakan ta kasance za ka yi nadama, su fa
yanzu su Abba rayuwarsu ta zo gangara
yanzu kai ne ka ke tasowa in ba ka yi da
gaske ba za ka yi rayuwa irin tasu, a wannan
karnin in ba ka da shi ba mai tausaya makа.
Jama'a gudunka za su dinga yi, 'ya;yanka su
rainaka, ka zamo abin zolaya da tsokana
18
1
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
su da yawa, ke ko kin ga ni ke kadai ce gare
ni, ke kadai ce a gidanku, ba ki ga bature ya
bai wa kowa 'yanci ba, misali ba mun je
Rasha da ke ba, kin gani ba mun je Americа
da sauran kasashe kin gani ba? To me ki ke
son ai miki?"
Ta mike tsaye tare da juya masa baya.
"Dad, ka yi hakuri da abin da zan
gaya maka, ku kuka jawo mu mu zama
rakumi ku akala mu ja ku mu tafi
99 jahannama...
Da sauri ya katse ta da daka mata
tsawa.
"Ni za ki kawo wa rashin tarbiyya da
rashin mutunci? Kina bin wadancan 'ya'yan
talakawan suna gurbata miki tunani?"
Hajiya Zainab ta shigo a sukwane, ta
fidda hannu ta tsinka wa Humaida wani
gigitaccen mari tana huci.
"Ga irinta nan, yarinya ta kai tsaiko
دو
abin da kullum na ke jiye maka ke nan".
17
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ita kam 'yar lele juyawa ta yi ta fita a
guje cikin ihun kuka.
*** *** ***
"Ka yi hakuri tunda Abbanka ya ke
bai san me ye dadi ba, don haka babu abin
da zai dorar a rayuwar ya kare a talauci,
zuciyarsa ta riga ta mutu ba zai taba ganewa
ba, yakin naka ne duk lokacin da ka cire
musu wannan tsatsar a nan ne za su gane
ashe da su mutane ne su. Ka aure ta in sun yi fushi a hankali watarana za su gane gaskiya,
talauci ya yi musu mugun kamu, ya zame
musu illa kada ka bari yarinyar nan ta
subuce maka. Ba zan gaji da ce maka ba in
har hakan ta kasance za ka yi nadama, su fa
yanzu su Abba rayuwarsu ta zo gangara
yanzu kai ne ka ke tasowa in ba ka yi da
gaske ba za ka yi rayuwa irin tasu, a wannan
karnin in ba ka da shi ba mai tausaya maka.
Jama'a gudunka za su dinga yi, 'ya;yanka su
rainaka, ka zamo abin zolaya da tsokana
18
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
cikin dangi, duk abin da ka yi ba ka iya ba
babu wanda zai damu da kai,
wannan sai ya fi ka daraja, wasu ma sa sur
mai da kai karamin mahaukaci.
Mu'allim, talauci na da zas na ban
Ummaki in ba ka da shi kullum za ka
kasance cikin kunci, shi kansa Abba talauci
ne ya sanya ake kiransa da sunaye iri-iri, in
yana da shi wannan makantar ba za a gani
ba. Ka je ka yi tunani, kuma ma ai yarinyar
ba ta da makusa. Daga karshe ina son
tunasar da kai shi kansa shugabanmu ya се,
mu nemi tsari da talauci don haka ka kyale
su Abba, tunaninsu irin na mutanen da ne".
"Adnan ina matukar sonta, ba don su
wasu ba ne. yadda na ke jinta a raina zan iya
zama da ita ko da ba kowa ba ce, sai dai
matsalar yarinyar duk dabi'unta ba su yi
ba".
"Wannan ba wata matsala ba ce,
muddin tana sonka za ka bi da ita ta yadda
ka ke so sannu a hankali, kada ka yi saurin
19
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
mika kai ka kara jan aji. Sai fa ka jajirce a
kan matsalar su Abba".
Bayan ya koma gida ya shiga
shawarwarin ya kira ta, sai dai yana jinjina
abin yadda kya yi mata da kyar ne in za ta
sake bibiyarsa. Ya ja tsaki ya janyo wayar
tare da kura mata ido, ga Ummakinsa ya ji
wayar ta soma ruri, kamar a mafarki
lambarta ce ya gani. Ya ji wani sanyi a ransa
da ita ce ta kira shi da kanta. Ya yi
murmushi yana sani ya barta ta ci gaba da
ruri har ta katse. Can wayar ta sake daukar
ruri ya danna kore ya kara a kunne. Cikin
kaurara murya ya ce.
"Please and please, ki fita a rayuwata,
kin takura min".
Daga can 6angarenta, ta ce.
"Na ji, zan yi yadda ka ce. Amma
kafin nan ina son mu hadu, zan yi maka
wata muhimmiyar magana".
Ya ce, "Ba zan iya ba".
Ta raunana murya cikin bayar da kai.
20
KA AURE NI=2
"Ka taimake ni".
BILKISU H.MUHD
Cikin daga muryar karfin hali ya се.
"Wai ke wace irin mara zuciya ce?
Kina son ne na yi miki karya?"
Та се, "Ка yi hakuti, na riga na zo ina
kofar gidanku".
Ras! Gabansa ya buga, ya mike da
sauri ya leka tsakar gida, Ummansa ba ta
nan. Ya sauke ajiyar zuciya tare da yin kasa
da murya.
"Humaida, ki gaggauta barin kofar
gidan nan, wai ke wace irin mace ce, me ya
sa ki ke son ki dinga bata mini suna? Iye?
Me ya sa?"
"Da ma ka daina daga hankalinka.
Duk wannan abin da ka ke yi ban san kana
yi ba. Na dade ina shaida maka ban san
bakar magana ba da ma ka bi komai a
sannu, kuma na rantse in ba ka fito ba ni zan
shigo".
Da sauri ya katse wayar a guje yana
fadin.
21
KA AURE NI=2
"Na sani za ta iya".
BILKISU H.MUHD
Hajara wadda ta ji tsiraru daga cikin
maganganunsa ta shiga tararrabi, shin me ke
faruwa? Hankalinta ya yi matukar tashi,
musamman da ta ga yadda ya fito a hargitse.
Daki ta koma ta janyo hijab a jikin kyaure ta
nufa masa baya.
Zaune a cikin mota kofar motar a
bude ta zuro sam6ala-sambalan fararen
kafafunta waje, cikin daure fuska ya ke
kallonta. Bai yi magana ba ya zagaya daya
bangaren ya bude murfin motar ya shiga.
"Shigo na ce". Ya ce da ita.
"Ina za ka kai ni?" Ta tambaya.
Bai ce komai ba, ta zuro kafafun cikin
motar, ya dan rankwafo ya janyo murfin
motar ta inda ta ke da karfi har sai da ta
firgita. Suka soma tafiya, sai da suka bar
unguwar a can nesa ya yi fakin a gefen titi
ya fito daga cikin motar yana faman huci. Ita
ma ta rufa masa baya, ta ddube shi kawai
tana murmushi.
22
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Zan tambaye ki, gaya mini me ki ke
so? Me ya sa ki ke son jefa rayuwata cikin
bala'i? Me ya sa?"
Ta yi murmushi da nuna ko'inkula.
"So na ke KA AURE NI!"
Duk lokacin da ta furta wannan
kalmar Ummaki ya kan kama shi,
musamman in ya yi duba daga tsantsar
kyawun da Ubangiji ya ba ta. Ya gaza furta
komai.
Ta kalle shi sosai, ta ga wani guri can
ya ke kallo, ta maida kallonta gurin, wata
budurwa ce ta zo giftawa sanye da hijabi har
kasa. Ta koma ta dube shi.
"Ni za ka kalla, ni ya kamata ka kalla
ba ita ba, babu abin da ta fi ni da shi".
Ya yi tsaki tare da kawar da kai gefe.
"Akwai abubuwan da ta fi ki da su da
yawa".
Ta yi murmushin karfin hali, duk da
kalaman nasa sun mata ciwo, amma ta
sakaye abinta.
23
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Ni na sani, ka fadi son ranka. Ni na
sani a cikin mata dubu da wahala a sami
wacce ta dara ni, in akwai ka gaya mini".
"Shi ya sa na ke kallon waccan mai
hijabin, saboda ta fi ki komai".
Meganarsa ya sanya ta sake kallon
mai hijabin, baka ce mai jiki, tana da
yankakken hanci, ba za a taba saka ta a
tsarin kyawawa ba. Ta maida dubanta gare
shi tana girgiza kai.
"Da me waccan abar ta fi ni?"
Cikin murmushi ya ke kallonta da
alama ya soma ba ta haushi, ya cе.
"Kin ga na daya, ta fi ki kunya,
Saboda lunda ta tsaya kanta a kasa ya ke
alamar mace ce mai kunya ke nan. Na biyu
ta fi ki ilimi, saboda wani haske a fuskarta,
ga shi ta sako hijabi alamar ta fito daga
gidan kwarai, gidan mutunci. Da alamun
kamun kai a tattare da ita.
Na uku, ba za ta tari namiji a hanya ta
ce ya aure ta ba, idan namiji ya ganta shi zai
24
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Zan tambaye ki, gaya mini me ki ke
so? Me ya sa ki ke son jefa rayuwata cikin
bala'i? Me ya sa?"
Ta yi murmushi da nuna ko'inkula.
'"So na ke KA AURE NI!"
Duk lokacin da ta furta wannan
kalmar Ummaki ya kan kama shi,
musamman in ya yi duba daga tsantsar
kyawun da Ubangiji ya ba ta. Ya gaza furta
komai.
Ta kalle shi sosai, ta ga wani guri can
ya ke kallo, ta maida kallonta gurin, wata
budurwa ce ta zo giftawa sanye da hijabi har
Kasa. Ta koma ta dube shi.
"Ni za ka kalla, ni ya kamata ka kalla
ba ita ba, babu abin da ta fi ni da shi”.
Ya yi tsaki tare da kawar da kai gefe.
"Akwai abubuwan da ta fi ki da su da
yawa".
Ta yi murmushin karfin hali, duk da
kalaman nasa sun mata ciwo, amma ta
sakaye abinta.
23
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Ni na sani, ka fadi son ranka. Ni na
sani a cikin mata dubu da wahala a sami
wacce ta dara ni, in akwai ka gaya mini".
"Shi ya sa na ke kallon waccan mai
hijabin, saboda ta fi ki komai".
Maganarsa ya sanya ta sake kallon
mai hijadin, baka ce mai jiki, tana da
yankakcen hanci, ba za a taba saka ta a
tsarin kyawawa ba. Ta maida dubanta gare
shi tana girgiza kai.
"Da me waccan abar ta fi ni?"
Cikin murmushi ya ke kallonta da
alama ya soma ba ta haushi, ya ce.
"Kin ga na daya, ta fi ki kunya.
Saboda tunda ta tsaya kanta a kasa ya ke
alamar mace ce mai kunya ke nan. Na biyu
ta fi ki ilimi, saboda wani haske a fuskarta,
ga shi ta sako hijabi alamar ta fito daga
gidan kwarai, gidan mutunci. Da alamun
kamun kai a tattare da ita.
Na uku, ba za ta tari namiji a hanya ta
ce ya aure ta ba, idan namiji ya ganta shi zai
24
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUKD
je gidansu zance ba ita ta je ba, in ya aika ya
ce ta zo sai ta dan jima kafin ta fito ba tana
rawar jiki za ta fita ba. In ta fito din ma za ta
tsuguna ta ce maka, ina yini ba tana tsaye
kerere a kanka ba, ba kuma ita ce za ta ce ka
zo a yi zancen aure ba, sai dai kai ka ce ki
gaya wa iyayenki zan turo neman aurenki.
Iyayen suna yanga ba kawai a hau zuba ba".
Gabadaya yanayinta ya sauya,
maganganunsa sun shige ta, cin fuska ne
muraran ya ke gwada mata, yau ne ta ke jin
wani abu a jikinta, wanda ga dukkan alamu
ita ce wannan kunyar da ya gama goranta
mata, me ya sa ba za ta hakura da wannan
mutumin ba? Me ya sa ta bari ya samu
damar da ya ke tozartata ya ke gasa mata
magana yadda ya ga dama?
Yanayin da ya gani a tare da ita ya
tabbatar maganganun sun yi mata zafi, duk
da ya ji ba dadi a zuciyarsa bai sa ya nuna
alamar nadama a fuska ba. Ya dan yi
murmushi, ya ci gaba da cewa.
25
Γ
1
1
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Ya isa haka, ko