wannan takardan,
ya girgiza kai, ya nuna Alhaji,kin san wannan mutumin?
Ta amsa, Eh! Shine na aikawa wasikar.
Da jin haka, gaba daya wurin kowa ya soma fadin
albarkacin bakinsa. Shi kuwa Alhaji yayi tsuru-tsuru.
Kwamishin ya dubi Alhaji, kai azzalumi maci amana,
laifunka biyu manya a kanka, na haddasa kisan kai, ga
nayi wa karamar yarinya cikin shege, don haka mu hadu a
kotu.
****
Faruku barazana da mahaifiyarsa, hankalinsu ya
tashi, suna zaune a gida, suna tunanin dalilin kama Alhaji
sai suka ji a rediyo ana labarai, ana cewa! 'yan sanda cun
cafke Alhaji Karma-Karma, sanannen mai kudin nan dake
nan garin, yayin da yake bada dalilin kamun,
Kwamishinan 'yan sanda yace an cafke Karma-Karma ne
59
a dalilin haddasa kisan wani mutum, wanda yake likita ne
a Kofun wannan gari. Koda fadin haka,sai Faruku ya
gyara zama ya dubi mahaifiyar, ita kuma tayi tagumi.
Daga nan aka ci gaba da labarai kamar haka,
"haka kuma an sake kama Alhaji Karma-Karma da laifin
ya yayi wa wata budurwa mai suna Jamila Alhaji Hamisu
cikin shege,wacce ake kyautata zaton budurwar dansa ne,
mai suna Faruku barazana,wanda ya shahara a fagen raina jama'a da rashin kunya a cikin garin nan".
Koda jin haka,idanuwan Faruku suka firfito ya
sake duban mahaifiyar,aka ci gaba da labarai ana cewa,
yanzu haka gobe ne za'a shiga kotu, domin yanke
hukuncin wadannan laifuka guda biyu,saboda haka ana
gayyatar jama'a da su je su ba wa idanuwan su abinci.
Da gama labaran, Faruku ya mike a fusace ya
dubi mahaifiyar, Mama kin ji ta'asar da Baba ya dafka
ko? Sai ya bugi wani teburi dake kusa dashi da hannusa.
Ji kake gam!.
Kotu ta cika Makil, babu masaka tsinke, jama'a
sai tururuwa suke su ba wa idanuwansu abinci, kuma su ji
yadda za'a kwashe. Asirin Alhaji Karma-Karma dai ya
tonu,dubu ta cika, dukiyar ba ta hana ya fuskanci tuhuma
ba. Daman kuma haka ake so ga masu mulki,kada su
bambanta tsakanin mai kudi da talaka wajen tabbatar da
doka da oda. Ga laifin haddasa kisan kai, ga shi kuma
Jamila ta tabbatar da cewa lallai Alnaji shine yayi mata
ciki, ba Salim kamar yadda ta lakafa masa da farko ba.
Bayan da aka kawo Alhaji a motar nan bakar ashana, tare
da yaronsa, daya da aka kama a wurin da aka kashe likita
Dattijo, ga Jamila da iyayenta,Salim a gefe ga Faraku
barazana da mahaifiyar sa, Ga alkali da sauran ma'aikatan
kotu kowa yayi balas Jama'a kuwa iyakan ganinka,basu
60 ,
lissafuwa. Ga Lauya Sabulu mai kare Jamila yayi tsurutsuru, saboda sanin halin da ake ciki. Ga Lauya Linzami
wanda Alhaji ya dauka domin ya kareshi wuri dai babu
masaka tsinke. Da aka natsu, mai gabatar da kara ya mike
ya soma bayaninsa kamar haka,
Yau shari'i'on namu sune: Hukuma tana karar
Alhaji Karma- Karma da haddasa kisan kai, wanda akayi
wa likita Dattijo ranar sha hudu ga wannan watan, da
misalin karfe biyu da rabi na dare. Haka kuma tana
tuhumar sa da yi wa budurwa mai suna Jamila cikin
shege,ya kuma sa ta lakafawa wani saurayi Salim wanda
bai ci ba bai sha ba.
Da gama bayaninsa, ya zauna,alkali ya gama 'yan
rubuce-rubucensa, ya daga kai ya ce, yau ce daman muka
sa za'a yanke hukuncin shara'ar Jamila da Salim, akan
maganar ciki, to amma yanzu ta sake zane, domin kuwa
inda aka za ta, ba'a nan take ba, an gane cewa Alhaji
Karma-Karma shine ya aika wannan ta'asa, don haka
magana ta juye,me lauyan wanda ake kara zai ce, wato
lauyan Salim?
Lauya Filla-Filla yayi zumbur ya mike, ya fito
farfajiyar shara'a ya fuskanci alkali, ya dan sunkuya a
matsayin ladabi, ranka ya dade, daman mu mun tabbatar
ba Salim bane ya aikata wannan mugun aiki mai kama da
kisan kai, amma wani lauya sukurkutacce, wanda bai san
aikinsa ba, yayi karanbani, ya kare marasa gaskiya.
Ranka ya dade tun da gaskiya ta bayyana mu ba
mu da ja, sai abinda kotu ta zartas, mu dai mun san mune
masu gaskiya.
Yana gamawa, ya dan sunkuya, ya juya ya koma
wurinsa yana barazanar samun nasara. Alkali yace, ko
lauyan dake kare Jamila vana da ta cewa, sai lauya Sabulu
ya mike, gwiwarsa a sacce, ya fito bagazan-bagazan, ya
sunkuya a gaban alkali ya nuna ladabinsa, ranka ya dade
61
mun ji yadda ta kaya, kuma tun da an samu hujjoji cewa
Alhaji shine yayi wannan ciki,to shi muke kara yanzu,
kuma mun janye kara daga kan Salim. Kuma ina rokon
ranka ya dade ka jawa lauyan wanda ake kara kunne, ya
daina kirana da sukurkutacce, yayi aikinsa kawai in yi
nawa.
Yana fadin haka,sai duk jama'an dake nan suka
kwashe da dariya, sai da aka tsawata sannan aka yi shiru.
Alkali ya dube shi,ko me lauya zai yi ya wanke
kansa ta yadda suka lakafawa yaro laifi, suka wahalar
dashi, suka bata masa suna da lokacinsa, suka cuci
lafiyarsa?
Lauya ya girgiza kai, ranka ya dade ai rashin sani
ya fi dare duhu, don haka muna neman ya yafe mana
laifin mu.
Alkali ya dubi lauya Filla-Filla,lauyan Salim ka ji
abinda suka ce, kun yafe musu,ko kuwa kuna da ja dasu
abi muku hakkin ku?
Lauya Filla-Filla ya mike,ranka ya dade muna
bukatar a fitar mana da hakkin mu yanzun nan kuwa, yana
gama fadin haka, mahaifiyar Salim ta mike da sauri ta ce
ranka ya dade, sai duk aka waiwaya inda take. Ta ci gaba
da cewa, idan Salim da na ne, ni na haife shi,to ya yafe.
Ai Allah ya fitar mana da hakkin mu, tun da ya nuna
gaskiyar al'amarin.
Tana gama bayanin ta sai ta zauna. Alkali ya
bada umarni Salim ya mike. Bayan da ya mike aka
tambaye shi idan ya yafe, shi kuma ya fada cewa tun da
mahaifiyar sa ta ce ya yafe, bashi da wata magana.
Alkali ya sake duban lauya Sabulu. "Lauya tun
da wadanda aka yi kara sun ce sun yafe, ko kana da wani
bincike da za kayi ga Alhaji Karma-Karma,wanda yanzu
aka tabbatar shine yayi wannan ciki?
62
Lauya ya gyara rigarsa, ya amsa, kwarai da gaske
ina da bincike da zanyi a kansa, don haka ina fata kotu ta
bani dama.
Nan aka ba shi dama yayi binciken sa,kuma aka
rantsar da Alhaji akan zai fadi gaskiya.
Lauya ya dubi Alhaji, a yayin da duk idanuwa sun
koma gareshi, sannan ya soma magana, ban tambayar ka
ba, sai dai kayi min yadda zan fahimta.
Lauya ya sake kallonsa, abinda nake nufi anan
shine, tun da dai Jamila ta ce kai ne kayi mata ciki, kuma
daman can mun san halinka ne,me za ka iya cewa?
Alhaji yayi shiru na wasu 'yan dakikoki, zai yi
musu, amma sai ya dake ya dubi lauya, yace: Ai wannan
al'amari abinda zan ce shine aikin kaddara ne. Lauya ya
girgiza kai, ya zamu tabbatar da cewa wannan aikin
kaddara ne?
Alhaji ya sunkuyar da kai, "domin ya ri ga ya
faru". Da kyau in ji lauya, bayan ya girgiza kai. Daga
nan ya dubi Jamila, ko za ki iya tunawa da tsawon lokacin
da kuke tare?
Eh mun dai dade da shi. Lauya ya ce, yanzu da
yake mun tabbatar shine yayi miki ciki, ga shi haihuwa
yau ko gobe, ta wace hanya ki ke bukata a kwatar miki
hakkinki?
Jamila ta soma bada amsa, jiki na rawa, ni dai
kawai idan na haihu ya amshi dansa, kuma a bi min
sauran hakkina daga gareshi.
Lauya ya girgiza kai, ko kina bukatar ki aure shi?
Ta amsa da sauri,Allah shi kiyaye in auri wannan
mayaudarin tsohon azzalumin.
Daga nan lauya Sabulu ya waiwaya ya dubi alkali
ya soma cewa, "ranka ya dade ya tabbata Alhaji KarmaKarma shine ya aikata wannan mugun aiki ga wannan
yarinya. 63
Ranka ya dade wannan mutum a fili yake, ya
lalatawa wannan yarinya rayuwa, domin 'yar wani ce,
Kanwar wani, matar wani, uwar wani, kakan wani ko
kuma wata,ko wasu.
Ranka ya dade ina fata kotu za ta tsaya da
cikakken adalcinta ta yi nazari ta fitarwa da wannan
yarinya hakkinta, kuma ta ladabtar da wannan mutum
domin ya zama ishara ga sauran masu hali irin nasa.
Da gama bayaninsa ya koma wurinsa ya zauna.
Alkali ya duka yayi rubutu na kamar rabin minti, sa'annan
ya daga kai ya dubi lauya linzami mai kare Alhaji KarmaKarma, ko lauyan Alhaji yana da wata magana ko kuwa
kariya?
Lauya ya mike duk jikinsa yayi sanyi, ranka уа
dade akan yi kariya ne idan babu wata hujja, amma a nan
da akwai hujja. Hasali ma Alhaji ya amsa laifinsa, don
haka ina rokon kotu wajen hukuncin ta, ta yi adalci da
tausayi da sanin ya kamata, domin kaddara za ta iya hawa
kan kowane daya daga cikin mu anan. Yana gamawa ya
zauna. Shima alkali ya gama rubutunsa, daga nan ya daga
kai yace:
"Kotu ta ji bayanai daga duk bangarorin biyu, ta
gama nata nazarin sai dai idan da akwai karin bayani sai
ayi, domin yanzu yanke hukunci ya rage". Yayi magana,
ya sake yi, amma babu wanda yace kanzil. Daga nan ya
bada umarnin aje hutun rabin lokaci, daga nan a dawo ayi
shara'a ta gaba, kuma a yanke hukunci. Ya mike, kuma
kowa ya mike, jama'a suka soma fadin albarkacin bakinsu
kafin a dawo.
Da aka dawo, gabatar da kara ya mike, ya soma
karanto bayanin shari'a ta biyu,yace, shari'a ta gaba,akan
kisan da aka yi wa likita Dattijo ne. Daga nan sai ya
zauna, alkali ya daga kai ya soma magana ya ce, shima
wannan kisa ya tabbata cewa Alhaji ne ya sa aka yi shi.
64
Shi kansa bayan tsanadin bincike ya gayawa 'yan sanda
cewa shine yasa aka yi kisan,kuma wai domin kada likita
Dattijo ya tona masa asiri,a domin haka kotu ba ta bukatar
wani lauya ya ba ta mata lokaci, domin gaskiya ta riga ta
bayyana.
Abu daya ne kotu za ta yi wa Alhaji, kafin ta
yanke masa hukunci shine ta ba shi kamar minti daya ya
roki afuwar da yake so ayi masa, don haka gareka Alhaji.
Alhaji ya fashe da kuka, duk idanuwa suka koma
kansa, ya ce ni dai bukatata ita ce ayi min rangwami kuma
ba zan sake wannan aiki na kaddara ba. Daga nan yayi
shiru, Alkali yayi kamar minti uku yana rubutu, duk kotu
tayi tsit, shi ake saurare aji hukuncin da zai yanke ga
shari'un nan biyu. Jim kadan ya daga kai ya soma cewa:
Kotu ta tabbatar da laifin Alhaji na farko akan yi
wa budurwa ciki. Mun tabbatar yayi mummnan laifi,don
haka ba tare da bata lokaci ba, idan wannan yarinya ta
haihu Alhaji zai bata kudi naira dubu hamsin,ta soma
daukan nauyin abinci da magunguna,da suturu na jariri ko
jaririya. Sannan zai bata wasu dubu hamsin,domin neman
lafiyar ta,kuma zai ba ta dubu dari domin lalata mata
rayuwa da yayi, bayan ya fita wayo da hankali. Sannan
kuma kotu ta daure shi shekara uku, domin laifin cin
amana da lalata rayuwar 'ya mace.
Ita kuwa Jamila kotu ta ci tarar naira dubu goma,
ko kuma daurin wata biyu, domin bata lokacin kotu da ta
da bata wa Salim suna. Wadannan kudi idan su za ta
bayar sai tayi alkawarin ba wa Salim da zarar sun bar nan.
yi
Wannan ita ce adalci ta kotu, yana gama fadin
haka, ya buga kan sarki, wanda ya nuna cewa, ya yanke
hukunci babu ja a kai.
Ya ci gaba da cewa, kotu kuma ta daure Alhaji rai
da rai. domin kisan da yasa aka yi wa bawan Allah likita
Dattijo, babu wata afuwa akan haka, shi kuma daya daga
65
cikin wadanda aka kama a wurin kisan, kotu ta yanke masa
hukuncin kisa ta hanyar bindigewa. Kotu tayi adalci bata
bukatar wata magana kuma.
Da gama fadin haka, Alhaji da yaronsa suka fashe
da kuka suna rokon afuwa amma ko sauraren su ba'ayi ba.
Nan take aka sa musu ankwa sai gidan maza. Ite kuma
Jamila ta yi alkawari a rubuce za ta bawa Salim dubu
goma,tarar da alkali yayi mata. Faruku barazana yayi ta
kuka shi da mahaifiyar sa. Nan dai kotu ta watse jama'a
na ta fadin albarkacin bakinsu.
Iyayen Jamila sun ji kunya akan abinda suka yi
wa Salim. Suka je har gida suka kaskantar da kansu, suka
ba shi hakuri ya manta da komai, amma ya ci je sai da
mahaifiyar sa ta sa baki, ta ce ya manta da komai, kaddara
ce ta faru, kada Allah ya maimaita. Daga baya ya amince.
Alhaji Hamisu ya ba shi jari ya sake amince masa. Ba'a
dade ba, Jamila ta haifi da namiji. Sai dai babu wata
murna. Da rana ta zagayo aka sawa yaron Dan Asali. Da
ka ganshi kaga Alhaji Karma-Karm. Bayan 'yan
kwanaki, sai jaririn ya ce ga garinku. Bayan ya rasu,
sabon bakin ciki ya rufe Jamila da iyayenta, domin ta
zama babu wani mai zuwa wurint ta, saboda bakin fenti da
ta samu. Abin ya dame ta,ta rasa yadda za ta yi ita da
iyayen suka kasa yi wa Salim magana ko zai aure ta.
Rannan Salim ya zo gidan su, ya gaishe da
iyayenta zai tafi. Sai da Jamila ta bari yayi waje, sai ta
faki idon mahaifiyar ta ta bi bayansa, bai sa ni ba. Ta kira
sunansa, ya waiwayo ya tsaya cik.
Ya dube ta, lafiya? Ta yi murmushi ta dube shi,
Salim wata magana ce zan gaya maka amma ina jin
nauyi.... Yayi 'yar dariya, fadi maganar ki, babu
komai.
Ta soma magana, hawaye na zuba, Ni dai Salim
kai nake so, ka m,anta da komai,ka ceci rayuwata daga
66
nakasa ka aure ni saboda Allah. Wallahi abin da na aikata
a baya, ba komai bane sai laifin zuciya ta.
Idanuwansa suka canza suna nuna alamun tausayi,
ya dube ta, kada ki damu Jamila, na yarda zan aure ki
muddin rai, ki kwantar da hankalin ki na amince.
Tana jin haka, ta ruga da gudu ta rungume shi,
suka sumbaci juna, hawaye na kwarara musu.
GARGADI
Ba'a yarda wani ko wata ko kuma wasu kungiyar mutane
su sarrafa wannan littafin ba, ta hanyar yin fim, ko sake
buga shi, ko wasan dandali, ko wasu abubuwan da suka yi
kama da haka ba,sai da izinin masu hakkin mallaka.
Copyrigh
JAKARA 2005
67
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels