ciki a cikin
aljihu, yayi waje jiki na rawa, ya shiga motarsa ya taka a
guje ya nufi gidan likita, dakta Dattijo. Duk inda ya gibta
sai an kalleshi,domin irin gudun da yake yi akan titi.
Allah cikin ikonsa saboda rudewa, Alhaji na na cikin gudu
bai san lokacin da ambulan din da wasikar da Jamila ta
rubuto masa, ta fita daga aljihun gaba na rigarsa ba, ta yi
waje, zuwa gabas, bai kula ba, burinsa ya cimma gidan
dafta Dattijo.
BABI NA HUDU
Sha Biyu da rabi dai-dai na rana, Alhaji KarmaKarma ya taka burkin motarsa a kofar gidan likita Dattijo.
Ya bude kofar ya fito, ya mayar ya rufe garam, ya sabe
hannun babban rigarsa, ya soma takawa zuwa kofar gidan
da take kulle. Idan ka debe manyan itatuwa,da iska dake
kada ganyayyakinsu, da kuma kukan tsuntsaye, unguwar
44
babu kowa a wajc. Da zuwa bakin kofar, ya sa hannu ya
soma kwankwasawa, ya dan yi shiru, yana sauraren takun
sawu da ake zuwa domin watakila a bude masa. Aka
murda"kofar ta ciki aka bude, sai ga likita Dattijo, wani
dogon mutum fari mai farin gemu, fuskarsa 'yar karama,
ga wushirya ta cikin jerin hakoransa. Suka hada ido da
Alhaji, likita Dattijo yayi murmushi ta rashin sani, yana
nuna bai gane Alhaji ba, shima Alhaji ya yi dariya irin ta
karfin hali. Likita ya bukaci Alhaji ya shiga falon, yayi
yadda aka ce, aka nuna masa wuri ya zauna. Likita ma ya
zauna yana fuskantar Alhaji yana nuna damuwa ya ji ko
me ke tafe da Alhaji'? shi kuwa ya gyara zama ya dubi
likita.
Ina ganin alamun ba ka waye dani ba ko? Likita
ya gyara zama ya dan yi zurfin tunani, daga nan ya dubi
Alhaji, lallai kam ban waye da kai ba, sai ka bani sani.
Likita yayi shiru yana sauraren Alhaji.
Yayi wata 'yar manafukar dariya ta karfin hali, ya
soma yi wa likita bayani.
Ba abin mamaki bane idan ka ce ba ka waye dani
ba, a takaice nine Alhaji Karma-Karma, wannan da kake
jin labarinsa a garí Ya kammala maganarsa cike da
alfahari.
Likita ya gyara zama ya tsurawa Alhaji idanuwa
sosai yana nuna alamun razana da mamaki, Alhaji KarmaKarma? Ya tambayi kansa a cikin zuciya. Alhaji ya dube shi cikin alamun kasaita, kada kayi mamakin haka likita, ina fata za ka bani cikakken hadin kai akan abin da nake bukata. Ya kammala maganar yana kallon akwatin da ya zo dashi, wanda ya aje a gefe daya.
Kafin likita ya ce wani abu, Alhaji ya sake duban
sa yana cika baki, Likita wannan alfarma da zan tambaye ka, wata dama ce a gareka, da za kayi ban - kwana da talauci, ka fada tsundum cikin kogin arziki da wadata,
45
amma idan wannan alfarma tawa kayi watsi da ita,lallai
kam ka zama maras rabo a duniya, abin da ya dace sai ka
bar duniyan kawai>
Likita yayi sauri ya gyara zama, ya dubi Alhaji,
fuskarsa tana nuna farin ciki da kuma alamun tsoro, Alhaji
ai ku namu ne, fadi duk bukatar ka, yanzu nan ayi duk
abin da kace.
Alhaji ya sa kafa ya shuri wannan akwati dake
gabansa zuwa inda likita yake zaune, sannan ya daga kai
ya dube shi suka hada ido, Likita bude wannnan akwati ka
gani, idan ka bi umarni na, abninda ke ciki na ka ne, idan
kuwa ka bijire......... Bai kammala ba yayi shiru ya
girgiza kai.
Likita yana rawar jiki ya bude, sai ga wazobiyoyi
sabbi fil a dankare, Allah kadai yasan yawan su. Tun da
yake aikinsa na likita bai taba ganin kudi masu yawa irin
wadannan ba, musamman idan ya tuna albashin sa da ake
bashi, wadanda duk yawansu a cikin aljihun wando yake
zuba su. Nan take ya rude, ya dubi Alhaji.
"fadi duk bukatar ka,wallahi zan yi ko menene,
yana maganar idanuwan sa na kan wadannan kudin".
Alhaji ya gyara zama yana mazurai, ya soma maganar sa
tare da barazana da yaudara:
Wata-kila ka san wata shara'a da ake yi a kotun
ku,wadda ake tuhumar wani yaro Salim da yi wa wata
yarinya Jamila ciki?
Yayi sauri ya amsa,kwarai da gaske na sani
Alhaji, hasalima ni aka ba wa bincike in gane idan da
gaske Salim shine yayi wannan ciki ko kuma ana masa
sharri ne.
Alhaji ya girgiza kai, to me ka gano a binciken ka,
shine yayi mata cikin ko kuwa sharri aka yi masa? Likita
ya amsa cikin karfin hali, a gaskiya na yi bincike, wannan
48
yaro Salim ba shine yayi mata ciki ba, na riga na kammala
rahoto na gobe kuma zan gabatar dashi ga alkali a kotu.
Alhaji yayi murmushi, ya dan yamutsa fuska, abin
da na ke so kayi min shine, wannan rahoto na ka na farko
ka canza shi, ka bada rahoton cewa wannan yaro Salim
shine yayi wannan ciki, ka nuna kada a zargi kowa sai shi.
Idan kayi haka to wadannan kudi da kake gani sun zama
naka har abada, idan kuwa ka bijire ko kuma daga baya
kuma ka tona asiri, kaga makomarka. Sai Alhaji ya ciro
wata yar karamar bindiga ya nuna masa.
Likita yana rawar jiki, Alhaji wallahi an gama, na
gane manufarka, zan yi duk yadda ka ce.
Bayan kotu ta cika,kowa ya zauna a mazauninsa,
magatakarda ya mike domin ya soma bayani. Yau kotun
babu masaka tsinke, daga kowane lungu na garin mutane
sun kwararo domin su ji sakamakon rahoton likita Dattijo.
Idan shine za su ji yadda za'a yanke masa hukunci, idan
kuwa rahoto ya nuna ba shi bane,za su ji yadda za'a fitar
masa da hakkinsa. Shi dai Salim da abokinsa Abdul da
mahaifiyarsa sun zo kotun da karfin gwiwa, da kuma
alfaharin cewa gaskiya za ta bayyana, Jamila kuwa, duk
da cewa ta san abin da ta kulla tare da Alhaji KarmaKarma, cikin ta ya duri ruwa tana tunani wata kila dabarar
ta ta ba za ta ci ba. Alhaji Karma-Karma kuma ya turo
domin ya ji yadda za'a kwashe ya kai masa rahoto.
Lauyoyin wanda ake kara da kuma mai kara duk suna
zaune suna saurare.
Yayin da magatarkada ya mike, sai duk idanuwa
suka koma wurinsa, ya bude wata 'yar gajeruwar takarda
mai ruwan kwai ya soma karantawa,
Yau ce ranar da aka umarci likita Dattijo ya bada
rahoton da ya samo akan biniken da aka bashi, ya
47
tabbatarwa da kotu, idan da gaske Salim ne yayi wa
Jamila ciki,ko kuma sharri tayi masa. Don haka kotu tana
bukatar likita ya fito nan ya ba da rahoton sa. Likita garcki.
Yana gama bayaninsa ya zauna, shi kuma likita
Dattijo ya mike daga inda yake zaunc, ya soma tafiya
zuwa inda aka ce. Shima aka bi shi da kallo, ya fito ya
tsaya, idanuwa na kansa. Salim duk ya kagara ya tabbata
shike da gaskiya. Likita ya bude wata 'yar takarda ya
soma karantawa:
Kotu ta bani umarni inyi bincike akan wannan
al'amari. To kamar yadda na rantse cewa zan yi bincike
na tsakani da Allah, to na yi, na auna jinin Salim da
Jamila,kuma na tabbatar na gano cewa: salim shine yayi
wa Jamila ciki, babu wata tantama akan wannan magana ta
wa.
Yana gama karantawa,sai Salim ya dube shi ya
fada da karfi: Likita wallahi karya ka ke, Ka ci
amana,wallahi ba ka yi gaskiya ba.
Jamila tayi murmushi, gadar zaren da ta shirya ta
ci nasara. Lauya filla - filla mai kare Salim ya girgiza kai
ya bata fuska. Shi kuma lauya Sabulu mai kare Jamila
yayi mumushi,aikinsa yayi kyau.
Mahaifiyar Salim ta dubi, Abdul ranta a bace
hawaye suka soma kwarara mata. Hajiya Asma'u kuwa
mahaifiyar Jamila, da Alhaji Hamisu suka soma
murmushi.
Jama'a kuma 'yan kallo wannan ya dubi wannan,
kowa na fadin albarkacin bakinsa. Likita Dattijo na tsaye
ya sun kuyar da kai yana kallon kasa, ya san abin da ya
kulla. Alkali ya gama rubuce-rubucen sa,daga nan ya
dago kai ya tsawata sannan aka yi shiru. Ya soma
bayanin sa:
48
Kotu ta ji bayanin Likita Dattijo, wanda muka
tabbatar baya goyon bayan kowane bangare. Rahoton sa
ya bawa bangaren mai kara galaba, don haka idan
bangaren wanda ake kara sun amince da wannan rahoto,
shike nan,idan suna da wata magana, sai mu ji. Daga nan
yayi shiru.
Lauya Filla-Filla yayi Zumbur ya mike, fuskarsa
babu annuri, ya dubi alkali, ranka ya dade ina neman kotu
ta bani izini in binciki likita, domin ban amince da
wannan rahoto nasa ba.
Da gama bayanin sa, alkali ya amince da bukatar
sa,aka bashi izini. Daga nan ya fito farfajiyar shara'a ya
dubi likita. Likita Dattijo kai ne ka yi bincike ka gano
wannan bayani da aka bayar yanzu ko?
To wacce hujja za ka bamu mai karfi wacce za ta
tabbatar mana da gaskiyar maganar ka.
Likita ya kalli lauya, Hujjar kenan,na bincika na
gano gaskiyar lamarin. Lauya ya gyara rigarsa, ya sake
tambayar sa, Likita a misali ka amince da mutum, ka
tabbata ba zai ha'ince ka ba, sai ka gwada shi akan wani
abu wanda kai ka riga ka san yadda yake, saikuma kaga
wannan wanda ka amince masa ya ba ka rahoton da kake
kokwanto a kansa,me za kayi? Likita ya yi gyaran murya,
tana rawa, sai in ki binciken sa?
Lauya Filla-Filla ya dube shi, to ni ma ban
amince da kai ba, akan wannan rahoto naka, don haka ni
ma zan bincike ka.
Lauya Filla Filla ya dubi alkali ya soma
magana, ranka ya dade, an nuna mana cewa ka bar abin da
kake kokwanto, ka koma wanda ba ka kokwanto, don
haka ni a matsayina na lauya filla-filla,ina so ayi ta fillafilla, kuma ina karar likita Dattijo akan cin amana da
canza rahoto, don haka ina nema kotu tayi wani abu akai,
yana gamawa ya koma ya zauna.
49
Sai lauya Sabulu yayi zumbur ya mike, ya dubi
alkali yace, ranka ya dade, bayanin da lauya yayi
yanzu,babu komai a ciki sai soki burutsu,domin kuwa,
Likita wanda kotu ta amince masa shi yayi wannan
bincike, kuma ya bada rahotonsa,don haka ina fata kotu
tayi watsi da wannan shara'a,kuma ta dau matakin
ladabtar da wanda ake kara,domin ya tabba shine yayi wa
wannan baiwar Allah ciki. Yana gama bayaninsa shima
ya zauna.
Alkali yayi 'yan rubuce - rubucensa, daga nan ya
dago kai ya soma magana, Kotu ta ji bayanai daga duk
bangarorin nan biyu, abinda ya kawo mu nan shine mu
tabbatar da adalci a tsakanin al'umma. Bayan rahoton da
Likita ya kawo mana, wanda ake kara ya nuna rashin
amincewar sa da haka. Kotu ta yi nazari, ta amincewa
lauyan wanda ake kara ya binciki Likita. Amma idan
bincikensa ya nuna Likita ya fi shi gaskiya, likita zai iya
nema a bi masa hakkinsa. Don haka kotu ta dage wannan
shari'a har sai sati mai zuwa. Ta amince likita ya tafi ba
tare da beli ba, shi kuwa wanda ake kara kotu ta bada izini
a kai shi ruman har zuwa mako mai zuwa. Wannan adalci
ne na musamman na kotu. Yana gama bayaninsa, sai ya
mike,jama'a ma suka mike, kotu ta dage zamanta.
Abdul ya dubi mahaifiyar Salim wadda take
faman kukan, bayan sun dawo daga kotu, yana ba ta
hakuri akan abinda ke faruwa, "baba kada ki ki damu kan
ki da komai,ni na yi Imani Salim ba shine ya aikata
wannan al'amari ba, kokari dai ake a makala masa dole"
Ta dube shi tana kokarin share hawaye, "Abdul
kai dai kana goyon bayan abokin ka ne, amma ai ge likita
ya bada rahoto cewa, lallai Salim ne yayi wa wannan
yarinya ciki". Ta kammala maganar tana cewa, oh, ni na
50
shiga uku, yau ni a duniyan nan,ina zan saka kai na,dan
kuka mai ja wa uwa jifa. Ta sake fashewa da kuka..
Ba haka bane baba, wallahi ni ina shakkar rahoton
wannan likita, kin san halin duniya, za'ayi yin komai,
domin a batawa Salim suna. Shi yasa ki ka ga lauya ya
nuna bai amince ba, da akwai abinda ya lura dashi, kuma
Allah ya kai mu sati mai zuwa, da yardan Allah gaskiya
za ta bayyana.
Bayan Abdul ya gama tausar zuciyar ta, sai ya
sallame ta kafin ya dawo da yamma su tafi wurin Salim da
ke zaman ruma. Ya fito waje, ya tura kekensa, ya haye,
ya soma tafiya zuwa gida. Yana tafiya,ransa a bace, yana
tunani, irin sharrin da ake so a kullawa abokinsa. Shi ya
tabbata ba Salim yayi wa Jamila ciki ba, ba aikinsa bane.
Da aikinsa ne, da kuwa ya sa ni, domin shekaru da yawa
suna tare.
Wata katuwar mota ta zo ta wuce shi fuuuu, iska
ta buga, har takardu da sauran tarkace suka warwarse, ya
ga wata doguwar ambulan mai kyan gaske, iska ya kada ta
gaba kadan. Har ya wuce, sai wata zuciyar ta gaya masa
ya kamata ya duba wannan ambulan din nan, wata kila
yayi gamo da katar, wato kudi ke ciki, ko kuma wani abu
mai muhimmanci. Nan da nan ya sauka akan keken, ya
tokare ta gefe daya, ya soma takawa zuwa inda ambulamn
din take. Da zuwa ya duka ya dauka ya soma dubawa,
yayi mamaki da ya ga an rubuta a jikin ambulan din da
manyan bakake kamar haka:
ZUWA GA ALHAJI KARMA-KARMA. Ya
fada a cikin zuciyarsa, Alhaji Karma-Karma, wannan
matsayacin mai kudin da na sa ni? Ni kuwa sai na karanta
na ga abinda ke ciki. Ya bude jiki na rawa, ya soma
51
karantawa cike da mamaki. Har ya kawo inda aka rubuta
kamar haka:
To na san watakila kana sane cewa na lakafawa
Salim mai aikin gidan mu wannan ciki da kayi min, har
sbin ya kai kotu, yanzu ma alkaliya bada umarnin likita
ya auna mu, ya gane idan cikin da gaske Salim ya yi min,
ka san kuwa dole zai gane ba cikin Salim ba ne. Idan
haka ta faru kaga na ji kunya,kuma ya zama dole in fallasa
ka cewa kai ne kayi min wannan aikin. Shawara anan
itace ka hanzarıa ka sami ganin dakta Dattijo sanannen
likitan nan mai yi wa kotu aiki, domin ku daddale dashi,
ya canza bayani kuma ya lakafawa salim wannar ciki
dole. Ka hanzarta Alhaji, kada dare yayi wa mai wankin
hula. Nice Jamila.
Abdul ya girgiza kai, wannan wasika ta daure
masa kai kamar a mafarki,ya ma rasa abin yi. Sai kawai
ya saka wasikar a aljihu ya haye kekensa, sai gidan fillafilla.
BABI NA BIYAR
Jiki na rawa, Abdul ya isa gidan lauya Filla-Filla
yana tafiya yana tunani, watakila kaya ne ya tsinke a
gindin kaba. Idan haka ne kuwa,lallai Ubangiji ba
azzalumin kowa bane. Da zuwa kofar gidan, ya sauka
daga kan kekensa,ya tokare ta ya je bakin kofar gidan ya
kwankwasa, ya tsaya yana saurare. Lauya Filia-Filla ba
shi da mata, shi kadai ne a cikin gidan. Yayin da ya ji aa
kwankwasa kofa ya taso da sauri ya bude, suka vi ido
hudu da Abdul cikin mamaki da annuri a fuska, ya dube
shi, Abdul na ganka da rawar jiki ne, lafiya dai ko?
Abdul ya rike masa hannu suka yi ciki, ba tare sun rure
kofar ba, lafiya kalau, takarda ce na tsinía, nace bari na
kawo maka wata-kila alheri ne.
52
Yana gama fada suka zauna su na kallon juna.
Abdul ya mikawa lauya wannan ambulan yana murmushi,
Lauya ina tafiya a hanya na tsinci wannan ambulan din, na
bude na karanta, sai na ga kamar a mafarki yayi kama da
hujjojin da muke nema akan maganar Salim da Jamila.
Lauya yayi hanzari ya fisge, ya bude da sauri ya
soma karantawa yana girgiza kai cike da mamaki ya gama
karantawa, ya kai ya dubi Abdul cike da mamaki, Abdul
ya aka yi ka samu wannan takardan, ko kuwa Allah yayi
niyyar ya yanke mana wahala ne?
Abdul ya gyara zama, lallai ina fatan haka, Lauya
yayi ajiyar zuciya, lallai kuma zamu yi bincike akan haka,
Allah yana tare da mai gaskiya.
*********** **
Alhaji Karma-Karma,ya dubi na hannun
damansa, Namuzu kawali,ransa a bace, yana ganin asiri zai
tonu idan ba an tashi tsaye ba, abubuwa biyu ne suka
daga masa hankali. Ga shi duk dabarunsa zasu tafi a
banza,kuma ya jefar da wasikar da Jamila ta aiko masa.
Yana bakin cikin idan ta fada hannun wadanda suke
abokan gaba, shike nan asiri zai tonu.
Namuzu wai wace hanya ce mafita, ka duba duk
da yadda na kashe kudi na bawa likita Dattijo ya canza
rahotonsa,tsinannan lauyan nan Filla-Filla,sai da ya
dagula al'amuran, ka ga ya zama babban makiyi shima.
Namuzu ya shafa gashin bakinsa, ya dubi Alhaji,
Alhaji ai kowa ya ci tuwo da kai miya ya sha, ina ganin
sai ka hada da daukar rai, wannan al'amari zai tafi dai-dai.
Amma idan ka tsaya lakwa-lakwa ko tausayi, lallai asiri
zai tonu, ya gama maganarsa yana nuna rashin tausayi.
Alhaji ya gyara zama, yayi dan murmushi kwarai
Namuzu, kayi tunani, ni ma ina ganin idan ba na raba
53
lauya filla-filla da duniya ba,zai kwance min zane a
kasuwa.
Kai! Kai! Kai! Namuzu ya amsa, ya ci gaba da
cewa Alhaji ai ba lauya za ka kashe ba Alhaji,wanda lauya
ke tuhuma za'a raba da duniya, wato likita Dattijo, domin
yanzu idan ya sha wahala zai tona maka asiri, idan kuwa
ya bar duniya,shi ma lauya babu wanda zai bincika,ka ga
dole ayi amfani da rahoton likita da ya bayar da farko.
Alhaji yayi farat ya amsa,kwarai Namuzu, tun
kafin in yabawa aya zaki,kamata yayi ka shugabanta,aje
har gida a raba likita Dattijo da duniya, mu ga wanda
lauya zai tuhuma. Haka za'ayi a daren yau.
Karfe biyu na dare, gari yayi tsit, baka jin komai
sai haushin karnuka,da kukan tsanya, gari duk babu farin
wata,idan ka debe Namuzu da sauran mutane uku da suke
tare da shi suna sanda a kofar gidan likita Dattijo,babu
kowa a unguwar ta turawa. Shi kuwa yana ciki yana
sharar barci. Namuzu tare da sauran suka lababa ta baya,
suka kama katangar suka haura, suka dira a ciki. Duk
kofofin da zasu kai mutum inda likita ke sharar barcinsa a
rufe suke. Namuzu ya tsaya yana tunanin yadda zasu yi.
Wata dabara ta zo masa. Ya tsaya a bakin wata kofa, yana
kwankwasa ta a hankali, sauran kuma suna labe. Likita
yana barci ya ji kamar daga sama ana kwankwasa masa
kofa yayi firgigi ya tashi ya zauna ya kunna lantarki,
haske ya bi duk dakin ya tashi ya dau wata 'yar karamar
bindiga tasa, yana sanye da doguwar riga ta barci, ya nuti
zuwa kofa.
Namuzu da sauran na kallon sa. Da ya je bakin
kofar ya ci birki,wanene yake kwankwasa kofar nan?
Shiru babu amsa. Namuzu dai yana labe, da wukarsa mai
daukar idanuwa.
Likita yayi karfin hali,ya kai hannu ya murda
mukulli, kofar ta bude, ya soma turawa a
54
hankali,bindigarsa na rike a hannun damansa. Ya tura
kofar ta bude a hankali. Bai sa ni ba, da fitowarsa,
Namuzu ya shaki wuyansa suka soma kokawa, har ya
harba bindigar sama, har masu gadi suka ji karar harbi,
suka ji kuma ana cewa La'ILAHA ILLA LLAHU ku
taimaka zasu kashe ni. Da jin haka, masu gadin suka tashi
da gudu, suka nufi kofar gidan, su na haska tocilan.
A dai-dai lokacin kuma, Namuzu da sauran
wadanda suke tare, sun ci karfin likita Dattijo. Sauran
suka danne shi da karfin tsiya. Namuzu yasa sharbebiyar
wukarsa, yayi masa yankan rago. (Allahu Akbar). Allah
ya raba mu da rashin imani, amin. Dai-dai masu gadin nan
sun shigo. Nan fa aka soma dauki ba dadi. Namuzu da
suaran su na neman su gudu, masu gadi na neman su
cafke su, saboda ganin abinda suka aikata. Namuzu ya
samu ya tsallake ya gudu, haka sauran mutum biyu.
Mutum daya da ya rage, kafin ya samu ya gudu, aka samu
cikin masu gadin, wani gwanin saiti ya auna kafarsa da
bindiga, ji kake daram. Yayi kara, wayyo Allah, ya fadi
yana shure-shure-. Likita Dattijo kuwa yana gefe cikin
jini, ya riga mu gidan gaskiya.
********* ************ ***
Duk gari, labari ya ba zu akan irin kisan gillar da
aka yi wa likita Dattijo. Ba a san ko su wanene ba, amma
an cafke mutum daya, wanda ake tabbatar da cewa za'a
samu bayani daga gareshi. Za'aji wane yasa su, kuwa
saboda wani dalili?
s4 af4 ofe sfa sle Dja eja aha aft ahe ohe sje aje eje eje sfa
Idanuwan Alhaji. Karma-Karma sun fito,
musamman labarin da ya samu cewa an cafke daya daga
cikin yaransa da suka je wajen kisan likita Dattijo. Shi
55
yana ganin laifin Namuzu ne, wanda bai ba su cikakken
vadda za su yi ba.
Alhaji ya tashi daga inda yake zaune jiki na rawa,
ya nufi inda Namuzu yake tsaye, yayi tsuru-tsuru. Ya rike
masa wuyan riga, ya daga hannu, ya sharara masa mari
tas! Ya dube shi. "Mutumin banza da wofi, kai ne kayi
sakaci, aikin ka bai yi kyau ba". Namuzu ya dubi Alhaji
cikin fushi, ga ka nan matsiyaci, mutumin banza maci
amana maras imani.
Sai ya nufi waje, ya tsaya a dai-dai kofar fita, ya
waiwayo ya dubi Alhaji, Na tafi, bani ba kai har abada,
kuma asiri zai zai tonu. Ya juya ya wuce ya tafi.
**********
A Ofishin 'yan sanda, jami'an leken asiri, suna ta
binciken dalilin kisan da aka yi wa likita Dattijo. Tuni dai
labari ya bazu ko ina da ina. Mutane sai zuwa suke su na
ba wa idanuwansu abinci. Aka tura 'yan sanda suka dauko
gawarsa aka kai mutuware. Shi kuwa wanda aka kama,
bayan an kai shi asibiti anyi masa maganin harbin, ya
samu sauki, hankalinsa ya zo masa. Daga nan aka soma
bincikensa, ta hanyar amfani da wutan lantarki, da sauran
hanyoyin horaswa. Bukata ita ce, ya bada bayanin wanda
ya basu umurnin kashe likita Dattijo. Bayan ya sha bakar
azaba, sai ya bayyana cewa Alhaji Karma-karma ne ya
tura su. Koda jin haka, mamaki ya kama jami'an tsaro.
Nan da nan, aka bada umurni ga wata bataliyan 'yan
sanda su je su kamo shi. Shi kuwa yana gida hankalin sa
ya tashi.
'Yan sanda ne ta ko'ina sun firfito daga cikin
motoci guda biyar, duk sunyi wa gidan Alhaji Karma56
karma kawanya. Kowanne rike da doguwar bindiga, yayi
balas yana jiran ko ta kwana. Da saukan su, wanda ke
shugabantarsu, ya attakura yayi harbi sama. Ji kake
daram! wanda ya gifta ko tsuntsu ne, idan bada izini ba a
kakkabo shỉ.
Alhaji Karma-karma yana zaune a falonsa, tare da
matarsa, tunani ya dame shi, sai ya ji harbi Kofar gidansa.
Zuciyarsa ta buga ras! Jiki na rawa, ya tashi ya bude
wundo ya leka. 'Yan sanda ne iyakan ganinsa. Hankalinsa
ya tashi, lallai yasan asiri ya tonu kenan, ya tabbata shi
aka zo a kama. Ya waiwayo ya gayawa matarsa, ita ma
hankalinta ya tashi. Yana wannan ya ji ana kwankwasa
masa kofa, ya tafi da rawar jiki ya bude, suka yi ido hudu
da shugaban 'yan sanda. Ba da bata lokaci ba, aka gaya
masa an zo a kamashi ne, saboda tuhumarsa da akeyi.
Koda yake yasan asirinsa ne ya tonu, amma sai ya tsaya
barazana wai a dole shi mai gaskiya. Da 'yan sanda suka
ga zai tsaya soki burutsu, sai shugabansu ya bada umarnin
a dauke shi. Nan take aka yi cuku-cuku dashi, aka daga
shi cak, matar tana kallo tana kuka da salati, aka yi waje
dashi, aka jefa a mota. Dai dai za'a jefa shi a mota, sai ga
dansa Faruku barazana ya zo a motar sa, ya fito da sauri,
yana tambayar 'yan sanda dalilin kama mahaifinsa, amma
babu wanda ya kula shi. Nan take aka tafi dashi, sai
ofishin 'yan sanda.
Da zuwa babu kakkautawa aka soma binciken
Alhaji ya fadi dalilin da yasa ya bada umarni a kashe
likita Dattijo. Da farko ya karyata, amma da aka kawo
wannan da aka kama ya shaida cewa lallai shine ya basu
umarnin su yi haka, sai Alhaji yayi tsuru-tsuru. Ana haka,
Kwamishinan 'yan sanda tare da alkali mai gaskiya suka
zo domin labarin da suka sınu. Da zuwa, duk 'yan sanda
suka kame, suka sara domin girmamawa, Alhaji na zaune
57
ankwa kafa da hannu. Kwamishina ya dube shi cikin
bacin rai.
"Alhaji daman muna da labarin irin ta'asar da
kake yi a garin nan, domin kana da kudi, kuma da yake
kana ganin kamar kafi karfin doka al'amarin ya wuce
lalata 'yan matan mutane, har ya kai ga zama dan
ta'adda,mai bada umarnin ayi kisan kai.
Kwamishina ya matsa kusa dashi, ransa ya bace,
ya cakumi wuyan rigarsa, ya dago kansa, ya daga hannu
ya sharara masa mari tas! Ya fada da karfi, ko kai ne kayi
masa rai da ka sa aka kashe shi? Alhaji yayi shiru.
Ina tambayar ka, ko kuma yanzu nasa bindiga in
harbe ka, kai ma ka ji idan da dadi kisan. Kwamishina
yasa hannu a aljihu ya ciro bindiga yar karama yayi saitin
Alhaji.
Za ka gaya min dalilin kisar ko sai na kashe ka
yanzu nan? Daga bayan sa, sai ya ji ance, ranka ya
dade kada ka kashe babban mai laifi, kamin a fitarwa da
jama'a hakkinsu, ni ma ina karar sa!
Kwamishina da sauran dake wurin suka waiwaya
da sauri su ga mai maganar. Sai suka yi tozali da Lauya
Filla-Filla tare da Abdul. Lauya na rike da wata doguwar
ambulan. Nan da nan ya karaso, Abdul na bin bayansa, ya
tsaya gaban Kwamishina, yayi masa ladabin da ya dace
dashi. Daga nan ya ciro takarda daga cikin ambulan din
ya soma cewa, ranka ya dade,wannan takarda da ka gani,
wasika ce da wata yarinya ta aikawa wannan azzalumin da
dalilin wannan wasika idan ka karanta, za ka ga ya dace
da halin da ake ciki, domin kuwa wacce ta aika masa da
wannan wasikar kara ta kawo cewa wani saurayi yayi
mata ciki, amma sai ga shi an tsinci wannan wasikar, har
ga inda ta aikawa Alhaji cewa ta lakafawa wannan saurayi
ciki, don haka......
58
Bai kammala ba, Kwamishina ya fizge takardar ya
kammala karantawa. Ransa a bace, ya daga kai, ya dubi
'yan sanda, ya ba da umarnin a tafi a kawo masa Jamila,
nan take aka bi umarninsa. Bayan kamar minti sha biyar
sai ga ta tare da iyayenta an ingizo keyar su. Da ganinta
cikin ta yayi girma, dole ko makaho zai gane. Da zuwa
Jamila ta hada ido da Alhaji sai ta sunkuyar da kai kasa,
shima ya sunkuyar da nasa.
Kwamishina ya dube ta cikin alamu irin na
tsoratarwa, ya bata wasikar nan, ta karba jikinta na rawa.
Ko kin san wannan wasikar? Ta soma dubawa,ta daga kai
ta kalleshi, ya daka mata tsawa, ba kallona nace kiyi
ba,kin san wannan takardan nace?
Tayi shiru bata ce komai ba. Mahaifiyar ta dube
ta da nuna tausayi, Jamila ki gaya musu gaskiya, kin ga
al'amarin sun dagule.
Hawaye süka soma kwarara mata, bakin ta na
rawa, ta dubi Kwamishina, Eh! na san