Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
ma a maganar dansa Faruku, wanda ya ci mata mutunci ita dai a karshe ta gano dabara. ***** ************** Sati daya kenan Salim yake cike da mamaki, ta yadda Jamila ke jan sa a jiki. Ta sakar masa jiki, iyakar saki. Hatta idan za ta ci abinci sai ta kirashi, ko kuma su raba dare suna hira. Idan ya tambaye ta dalilin da yasa take masa haka, sai tayi dariya ta dubeshi da manyan fararen idanuwanta, ta ce, uhum Salim, menene kuwa, sai Kauna? Shi kuwa ya saki jiki tana ta yaudararsa, domin ta samu hujja a kansa. Ta san cewa ba da dadewa ba, bakin alkalami zai bushe za'a gane tana da juna biyu, kuma za'a ce ma ta ta fadi wanada yayi ma ta, sai ta lakafa masa.Haka suka ci gaba har zuwa wani dan lokaci kafin Salim ya samu sabon sauyi a rayuwarsa. Da daddare wata juma'a Salim yayi doguwar hirn da Jamila har misalin sha biyu, daga nan ya sellameta ya tafi. Bayan tafiyarsa da kamar minti goma tana kwance akan gado, al'amuran duniya na ci gaba da damunta, musamman gashi cikinta ya kai watanni biyar, amma babu wanda ya gane. Tana cikin wannan tunani, sai ta soma ganin jiri, dakin ya soma juya mata, nan da nan sai tari, sai amai, ta kasa tashi, duk amai ya bata zanen gado. Hajiya Asamu'u, tana daki ta ji kakarin amai, tare da kuka, nan da nan ta fito da sauri, zuwa dakin Jamila. Da zuwa ta tura kofar da karfi ta shiga, ta samu Jamila babu inda take. Ta fashe da kuka, hawaye na zubo mata; Lal'ilaha Illallahu.... Jamila me ya sameki, na shiga uku, ga shi dare yayi babu wanda zai kai ki asibiti. Jamila ba ta iya magana; ta mikawa mahaifiyar hannu, tana fada a hankali; Mama a kai ni asibiti. Zan mutu! Hajiya ta sake rudewa, tayi waje gidan makota, ta shaida musu abinda ake ciki. Nan da nan aka taimaka, aka dauki Jamila a cikin mota, sai asibiti. Da zuwa babu bata lokaci, wani likita ya soma duba ta, domin ya gano abinda ke damunta. Hajiya Asama'u tana gefe duk hankalinta a tashe, ta kagara ta ji abinda ke damun Jamila. Bayan kamar awa guda, likitan ya waiwayo ya fuskanci hajiya wacce take zaune, tayi tagumi. "Hajiya a gaskiya 'yarki ciki gareta wata biyar, kuma babu dama a zubar dashi, idan kuwa aka ce za'a zubar lallai za ta mutu, dole sai dai ta haihu". Hajiya ta mike da sauri ta yi salati, jiri ya debeta, ta yi kamar zata fadi, sai da likita ya rike ta. Ta soma magana; La'ilaha Illallahu; Ni kuwa wanene ya bata min rayuwar yata? Amma ko wanene ya gama damu, yanzu me zance wa mahaifinki Jamila? Sai ta fashe da kuka da karfi har dakin yana amsawa. ********* *soje * en ejn ***** ** **** ****** * Hajiya Asama'u ta dubi Jamila tana niyyar ta yi mata magana. Koda ganin Hajiya kasan ta fita daga. hayyacinta. Tsakanin daren jiya, zuwa safiya da suka dawo gida, ta zama kamar wacce ta shekara babu lafiya, annurinta ya canza, tayi baki, duniyar ma ta yi mata baki. 30 'Yarsu ta jawo musu abin kunya abin fadi, abin gori, abin tir da Allah wadai. Menene abin yi yanzu? Sai ta tambayi Jamila wanda yayi ma ta wannan aika-aika, domin daukar mataki a kansa. Hajiya ta dubi Jamila, wacce take zaune ta sunkuyar da kai tana kuka; "Ba kuka za kiyi ba, ba lokacin kuka bane yanzu, da kinsan za kiyi kuka da baki saka kanki a cikin wannan rayuwa ba, yanzi ki gaya min wanda ya aikata miki wannan danyen aikin kafin babanki ya dawo musan nayi, kaddara ce ta faru babu yadda za'ayi". "Jamila bata kulata ba, sai kuka take yi. Koda yake kuka ne na munafunci, domin tasan shirin data yi, sai gabatarwa ya rage" Jamila da ke nake, ko kuwa. Za ki ci gaba da bata min rai ne, bayan bakin cikin da kika jawomin, ki gaya min nace miki! Ta kammala maganar, tana nuna damuwarta a fili, idanuwanta na kawo kwalla. Jamila tayi karfin hali, domin ta gabatar da abinda tayi niyya! Tana gamawa ta sake fashewa da kukan munafunci. Hajiya ta mike da sauri jikinta na rawa tayi salati, ta sanar da Ubangiji. Ta kalli Jamila cike da mamaki da alamun razana. Kina nufin Salim direban mu? Eh Mama, shine; Jamila ta amsa cike da karfin hali. Hajiya ta fashe da kuka; tayi salati; wayyo Aliah,amma Salim ya ci amana, gaskiya daman yake shisshige miki. Tana gama fadin haka, Salim yayiі sallama ya daga labule ya shigo ya tsuguna ya gaishe da Hajiya. Bata amsa ba, sai dai ya ga ta fashe da kuka, ta kalleshi. 31 "Salim ka ci amanar mu, Allah ya isa ya saka mana, ashe duk yadda muka rike ka da amana, shine za ka yiwa Jamila ciki, Allah ya isa. Salim ya mike tsaye da sauri, makullin mota da ke hannunsa ya fadi kasa, ya kalli Jamila, kanta na sunkuye, ya kalli Hajiya suka hada ido, ya soma magana bakinsa na rawa. Hajiya da gaske kike ko wasa? Cikin lafiya sai đai ayi min sheri wallahi. Ya kammala bakinsa na rawa, idanuwansa suka kawo kwalla. Da rufe bakinsa, sai ga Alhaji Hamisu ya daga labule ya shigo. Gaba daya dake cikin dakin, akayi tsurutsuru. Jamila kanta na sunkuye. Alhaji ya dube su bi da bi; Lafiya na ga anyi tsuru-tsuru, ku gaya min mana, kada ku boye min komai. Hajiya ta fashe da kuka ta soma gayawa Alhaji halin da ake ciki. Da ta gama gaya masa, sai akwatin dake hannunsa ya fadi kasa, ya dubi Salim, wanda ya sunkuyar da kai. Salim me yasa ka ci amanar mu, ka gaya min gaskiya in san abinda zan yi asiri a rufe. Salim ya tuma ya rantse da Allah bai san wannan labari ba. Aka tambayi Jamila, tace ita shi ta sani. Da Alhaji ya ga ya bi ta lalama amma Salim bai amince da nauyin da ake so a dora masa ba, sai ya fusata, zuciyarsa ta rika tafarfasa. Bai san lokacin da ya daga hannu ya tsinke Salim da mari ba tas! BABI NA BIYAR Bacin rai da tsananin tunani sune suka sa Salim duk ya lalace, domin tunanin halin da yake ciki. Ya gayawa Alhaji Hamisu gaskiya cewa ba shine yayi wa Jamila ciki ba,amma ya ce sam bai yarda ba, musamman da Jamila ta shafawa idanuwanta toka tace ita shine yayi mata. Alhaji yayi fushi da Salim sosai, domin a ganinsa 32 shine ya aikata wa Jamila wannan abu, har yana ce masa ya ci amana. Ba tare da dogon bincike ba, Alhaji ya kai Salim ofishin 'yan sanda domin a tuhume shi, ya amsa laifin da aka ce yayi. Tun jiya yake tsare, a dakin kulle masu laifi na ofishin 'yan sanda, babu abinda yake yi sai kuka yana tunanin yadda aka kala masa laifin da bai yi ba, ba tare da wani bincike ba. Mahaifiyarsa da ta samu labari, ta je musamman ta roki Alhaji Hamisu arziki ya sa a fito dashi, domin a sasanta, amma ya ce fatau ba za'ayi haka ba, domin Salim ya ci amanarsa, don haka ba zai kyaleshi ba. Aka ci gaba da tuhumar Salim, shi kuwa yace sam bashi bane. Salim na zaune akan siminti a cikin dakin da aka kulleshi a ofishin 'yan sanda, zarnin fitsari da wari duk sun dame shi. Domin wuri ne mai kazantar gaske, ga kudin cizo ga masifaffun sauro, ga shi babu sakewa, baka da wani 'yanci, sai yadda akayi dakai. Kai Allah ya raba musulmi da shiga wannan wuri, albarkacin Annabi Muhammadu (S.A.W) amin. Salim na daga kai, sai ga mahaifiyarsa, tare da wani abokinsa na kusa mai suna Abdul sun zo, wani dan sanda dogo, mai faffadan fuska, wacce ba ta da annuri, shine yayi musu rakiya. Abdul na rike kwanon abinci, mahaifiyar Salim na binsa a baya. Salim na zaune, ya hada kansa da gwiwoyi, sai ya ji ance; Salim. Ya daga kansa da sauri, sai yayi tozali dasu. Ya dafa bango ya mike, ya tashi yayi 'yar tafiya, ya zo ya tsaya. Dogayen karafuna da akayi katanga dasu sune ke tsakaninsu. Ya hada ido da mahaifiyarsa, sai kwalla suka cika mata idanuwa, ta dube shi. "Salim kaga abin nan yayi karfi, don naji ance gobe kotu za'a kai ka, idan kasan kai ne ka aikata wannan abu ka gaya min gaskiya in je in ba wa Alhaji hakuri, domin kada aci mana mutunci, kaga bamu da wani a 33 mataimaki sai Allah. Ta fashe da kuka, Abdul ya rika bata hakuri. "Haba Mama,ai ya kamata yayi kiyi shaida ta. Salim ya soma mayar mata da amsa, hawaye na kwarato masa; ya ci gaba; "Mama ba wai ina alfahari bane, amma da ace ina wannan harkar, dakin sani, ko kuwa da kin ji labari. Ya kammala maganarsa yana cewa; waliahi Mama gaskiya dokin karfi ne, Jamila ta yi min sheri. Iyayenta sun amince da haka babu bincike don haka mu sa musu idanuwa, Allah baya barci, zai fallasa maras gaskiya. Yana gamawa yasa rigarsa ya share hawayen dake kwararo masa. Mama kada ki damu, na yarda da Salim na amince masa, Abdul ya amsa, ya ci gaba da maganarsa yana jaddadawa. Mama Salim ba shi yayi wannan abu ba, kuma Allah zai bayyana mai gaskiya, Allah ya kaimu goben, aje kotun wa ya ke tsoro? ******** Tunda sanyin safiya, mutane daga cikin gari suka soma kwarorawa zuwa babban kotun daukaka kara dakе kan titin 'yanci, domin su saurari yadda wannan shari'a za ta kwashe. Labari ya watsu ko ina cewá Jamila, 'yar gidan sanannen tsohon ma'aikacin gwamnatin nan Alhaji Hamisu. Da yawa mutane da suke fadin albarkacin bakinsu sukan ce: ai babu mamaki. Da yawa da suka san Salim, idan suka ji ance shine yayi wa Jamila ciki, sai su cika da manaki, domin sanin halayensa masu nagarta. Za ka ji suna cewa; "Allah Sarki ta lakafawa Salim, irin su sun fi talka ta'asa" ta Ko wasu jinsi da nasu ra'ayin, shi yasa ake tururuwa a zo kotu a ji yadda za ta kare. A nan ne zaka gane mutanen duniya, idan abun alheri ya samu saboda sins is a 34 bakin ciki da hassada, ba za ka ji ana labarin ba, amma idan sheri ya samu mutum, sai ka ji duk labari ya bazu a gari wasu na dariya, wasu na shewa. Ashe haka duniya take, duniya mai wuyar gane hali, abokinta da shi za'a kulla a cuce ka. Lallai mu yi takatsantsan. Alhaji Karma-karma yana gida ya samu labarin halin da ake ciki. Hankalinsa ya tashi domin kada magana ta yi zafi Jamila ta tona masa asiri. Amma kuwa daga baya ya kanne, domin idan haka ta samu, sai ya karyata idan yaso ayi ta tafka shari'a. Shima Faruku barazana wannan labari ya zo masa. Koda yake yasan ba shine ba, amma hankalinsa ya tashi, kada Jamila tace shine, gashi kuma an kawo wani alkali sabo, wanda baya amsar cin hanci sai dai tabbatar da gaskiya. Asabe naira ma, da Bilkisu kwandala sun yi bakin ciki, musamman saboda shakuwar da suka yi, jikinsu kuma yayi sanyi. Kai labari duk ya bi ko ina da ina a cikin gari. ********* ************ **** Aka shigo da Salim cikin kotu, wani ramammen dan-sanda na binsa a baya. Jama'a suka bi shi da kallo. Aka shigo dashi wani wuri da aka zagaye da katako, ba'a ganin komai nasa, sai daga kirjinsa zuwa kansa. Aka kira Jamila, ta ttaso daga inda take zaune tare da iyayenta. Ta taso tinkis-tinkis. Mutane suka bi ta da kallo. Sai nan da nan mutanen suka soma kallon junan su, suna 'yan kananan maganganu. Ita ma aka shiga da ita irin wannan wuri da aka shiga da Salim. A can daga sama, alkali mai gaskiya shine yake zaune, yasa wani farin gilashi, gabansa da wasu manyan littafai, ga suturun alkalai ya sanya. Daga kasa kuma a gabansa, magatakarda ne, da mai gabatar da kara, suke zaune akan kujeru a gaban wani bankamemen teburi. Daga hannun hagu kuma, lauyoyi ne su biyu. Daya shine wanda Alhaji Hamisu ya dauko haya domin ya kare Jamila, daya kuma wani abokin Abdul ne, 35 shima kwararren lauya ne, domin ya tsayawa Salim. Shi kansa Abdul da mahaifiyar Salim suna cikin jama'a sun zauna, su ji yadda za'a kwashe. Sajen gishiri, wani kakkauran dan-sanda, mai bakar fuska, ga gashin baki da jajayen idanuwa, kayan sarkinsa duk sun kode, shine mai gabatar da kara. Ya mike ya soma karanta karar yana cewa: Ranar lahadi, ashirin da biyu ga watan Octoba na shekarar alif dari tara da casa'in da biyar, Jamila 'yar gidan Alhaji Hamisu, ta kawo rahoton cewa Salim Kallamu, wanda yake musu aiki a gida yayi mata ciki, amma ya ce ba shine yayi ba. 'yan sanda sun kawo shi ofis, anyi bincike shi kuma ya karyata, shine mai kara ta ce a kawo maganar kotu domin a fitar mata da hakkinta; yana gama karanatawa sai ya koma ya zauna. Alkali ya sunkuyar da kai yayi wasu 'yan rubuce-rubuce, sa'annan ya dago kai, ya dubi wajen lauyoyi; Lauyoyin mai kara da wanda ake kara kun ji bayanin mai gabatar da kara, ko da akwai me wata magana? "Lauya Sabulu, lauyan mai kare Jamila yayi zunbur ya mike, mutane duk aka bi shi da kallo, shi kuma ya dubi alkali; ranka ya dade ina so kotu ta bani izini in gabatar da wani bincike akan wanda ake tuhuma. Yana gama maganar ya zauna. Lauya filla-filla, wanda ke kare Salim da ake kara, shima ya mike; ya dubi alkali; "Ranka ya dade, a dokar shari'a ta kasa, lauyan da ke kare wanda ake kara shine ya kamata ya soma bincikensa ga mai kara, don haka ina fata kotu tayi watsi da bukatar da lauya yayi yanzu, ta bani dama inyi bincike na musamman a kan mai kara. Yana gamawa, sai ya zauna. Alkali yayi 'yan rubuce-rubucensa, ya dago kai yace, "kotu ta bada dama 36 ga lauya mai kare wanda ake kara yayi bincikensa ga mai Kara. Koda fadin haka lauya falle-falle, ya mike jama'a suka bishi da kallo, ya soma tafiya zuwa farfajiyar bincike, rigarsa ta lauyoyi tana jan kasa, da yake gajere ne. Da fitowarsa, sai magatakarda ya mike, rike da wata 'yar doguwar takarda, ya nufi wajen da Jamila take, ya kalleta, ya ce ta daga hannunta na hagu, kuma ta ce duk abinda ya ce. Ta yi yadda ya ce. Shi kuma ya ce; ni Jamila Alhaji Hamisu, na yi rantsuwa zan fadi gaskiya, a gaban wannan kotun, babu abinda ba gaskiya ba, Allah ya taimakemu amin. Da ya gama rantsar da ita, sai ya koma ya zauna abinsa. Lauya falle-falle ya soma takawa a hankali, ya nufi inda take, ya dafa murfin dan dakin katakon da take ya daga kai ya kalleta, suka hada ido, ta yi sauri ta sukuyar da kai. Jamila ke musulma ce, kuma wacce tayi imani da Allah ko? Ki bani amsa. Jamila ta amsa ba tare da ta daga kai ta kalleshi ba. Eh ni musulma ce mana. Aauya ya sake dubanta, domin ya ci gaba da bincikensa. Shin kin san ko wanene Salim, kuma ya kuke da shi? Ta dan dago kai ta kalli jama'a ta ga, duk ita ake kalloni ta sunkuya da sauri, ta soma ba wa lauya amsa. Na san Salim, yaron gidan mu ne, shi muke aike, kuma yana mana 'yan aikace-aikace. Shikenan sanin da ki kayi masa, babu wani abu? Ta dan dago kai ta kalleshi, a yayin da take wasa da 'yan 'yatsunta. "Shike nan sanin da na yi masa mana". 37 Lauya falle-falle, yayi kamar yayi dariya, sai kuma ya sha kunu, ya waiwayo ya kalli alkali, wanda ya dukufa yana ta rubutu, ya kuma kalli jama'a ya ga duk su ake kallo da saurare. Daga nan ya sake fuskantar Jamila. Wato dai kina tabbatar ma da wadanda basu sani ba cewa ashe ma salim yaron gidanku ne kawai, ba wata tsiya ba. Jamila ta amsa da sauri, cikin karfin hali. kwarai da gaske! Lauya ya girgiza kai. To ya akayi kuma yaron gidanku wanda babu wani abu a tsakaninku har yayi miki ciki? Ta amsa da sauri; ai kuma saurayina ne! Tana fadin haka, sai jama'a da ke kotun kowa ya soma fadin albarkacin bakinsa, duk wuri ya rude sai da aka tsawata. Da aka yi shiru, lauya Falle-falle ya sake duban Jamila. Ko kina da wata hujja, wacce ni da alkali, da sauran jama'ar dake nan zasu amince babu tantama cewa lallai Salim saurayinki ne? Jamila tayi shiru tana tunani na wani dan lokaci, kowa ita ya zurawa ido, ta dau misalin minti daya ba ta cе komai ba. Lauya ya dubeta, ko baki da hujjar da muka tambaya? Ta sake yin shiru. Ko Salim ya taba baki hoto, ko kuma wata wasika tun da kuka soma soyayya? Bai taba bani ba, ta amsa tana rawar murya. To ke wacce hujja za ki bamu komi kankantar ta cewa shine yayi miki ciki? Ta amsa ma lauya, kanta na sunkuye. "cikin da yayi min shine hujja ta". Koda Jamila ta fadi haka, duk kotun aka fashe da dariya, har na kamar rabin minti, sannan aka sake yin tsit. Lauya Falle-falle, da ya gama bincikensa, sai ya waiwayo, ya dubi alkali, ya soma cewa; Ranka ya dafe, ka ji ma kunnuwanka irin wannan al'amari. Jamila ta gaya 38 mana cewa Salim shine yayi mata ciki. Mun san kuwa idan mutum ya ce anyi masa wani abu dole ya kafa hujjoji masu karfi, domin masu saurare su amince. Lauya ya sake matsawa kusa d gaban teburin alkali, ya kalleshi, Ranka ya dade babu wata hujja wacce mai kara ta kawo da zai tabbatar mana da cewa shine yayi mata ciki. Abinda muka sani shine yaron gidansu ne kawai. Ya waiwayo ya dubi jama'a kamar zai yi musu lacca. Kuma jama'a kun shaida, kuma na san za ku tabbatar Salim salihi ne, babu laifi a kansa. Ya sake waiwayo, ya dubi alkali. Ranka ya dade, ina bukatar kotu tayi watsi da wannan karar, kuma ta bi wa Salim hakkinsa, domin bata masa suna da lokaci da aka yi. Da ya zo nan ya dan sunkuya, a gaban alkali ya mike ya nufi inda yake da farko ya zauna. Jam'a duk anyi tsit ana sauraren yadda za'a kwashe. Lauya Sabulu mai kare Jamila yayi zumbur ya mike, ya dubi alkali. Ranka ya dade lauyan da yayi bayani yanzu babatu kawai yayi, ya manta da wasu ka'idoji na aikinsa, don haka ina fata alkali ya bani izini in binciki wanda ake kara, kada a tauyewa yarinya hakkinta. Yana zuwa nan yayi shiru, yana, jiran umarni. Alkali ya nuna masa alamun ya fito. Nan da nan jiki na rawa ya fito ya tsaya. Magatakarda ya tashi ya je ya rantsar da Salim ya dawo ya zauna. Lauya Sabulu, ya matsa kusa da inda Salim yake, ya daga kai ya dube shi. Ko kasan Jamila? Na santa mana! Lauya ya sake tambayarsa; Wane irin sani kayi mata, na fili ko kuma na boye? Salim ya dan yi shiru na wasu dakikoki yana. nazarin wannan tambaya, da 39 mamakinta. Daga nan ya bada amsa. Ni sanin fili nayi mata, bana 6oye ba. Menene matsayinka a wurinta? Ni mai aikin gidansu ne. Bayan lauya Sabulu yayi wa Salim tambayoyi na ya akayi aka haifeka, sai ya waiwaya ya dubi alkali, yayi surutu, yayi babatu, ya nuna bai amince ba, ayi bincike mai zurfi. Da ya gama ya koma ya zauna. Da alkali ya gama rubuce-rubucensa, ya dago kai, ya soma magana, yana cewa "kotu ta ji bincike da bayanin lauyoyi, don haka a karshe ta yanke shawarar cewa, likitan da ke wa kotu aiki zai bincike Salim da Jamila ya auna su, domin ya tabbatar mana da gaskiyar lamari, ta haka ne kawai wannan matsala za ta warware muna fate likita zai yi bincikensa saboda Allah ya gabatar mana da rahotonsa ranar ashirin da takwas ga wannan watan, da misalin karfe tara na safe. Masu kara da wadanda ake kara sai su halartoa wannan rana, dai-dai wannan lokaci. Kotu za ta bada belin wanda ake kara ga kowane tsayayyen mutun mazaunin wannan gari idan ana bukata. Da gama bayaninsa, sai ya mike, kowa kuma yа mike, kotu ta tashi. BABI NA SHIDA Jamila na zaune a daki, duk abin duniya ya dame ta. Tun jiya da alkali ya bada umurnin a binciki jininta dana Salim, hankalinta ya tashi. Ta yi imani gaskiya zata bayyana, kuma zata ji kunya, domin likita zai tabbatar a gaban alkali da sauran jama'a cewa ba Salim ne yayi mata wannan ciki ba. Idan aka gane haka, lallai alkali zai yi mata mummunan hukunci, domin kazafi da 6ata suna da ta yi bawan Allah. Hankalints ya tashi duk ta fita. hayyacinta. Ita dai ba za ta yarda da tona ma kanta asiri ta ce Alhaji Karma-Karma ne yayi mata ciki ba. Ai abin da 40 kunya. Dabara dai ta rage ga mai shiga rijiya. Iyayenta Alhaji Hamisu da Hajiya Asama'u bakin ciki da kunyar duniya duk ta rufe su. Bilkisu Kwandala tayi sallama ta daga labule ta shigo, bayan da ta gaishe da Hajiya Asma'u a tsakar gida. Jamila na zaune a gefen gado tayi tagumi, da ganinta ka ga mai juna biyu, duk tayi haske tana kyalli, kafafuwanta da hannayenta sun zama manya, fuskarta ta kumbura. Da ganin Bilkisu Kwandala ta yi murmushi irin na karfin hali, suka gaishe da juna. Bilkisu ta samu wuri ta zauna, suna fuskantar juna. kenan? Bilkisu ana ganin ku a duniya kuwa idanuwan Jamila tayi maganarta cikin karfin hali, tana kokarin gyara zama. Bilkisu ta sake yin murmushi, mai nuna alamun ta ji kunya. Uhum, ni dai Jamila sai dai kiyi hakuri abinda zan iya cewa kenan. Jamila ta kalleta, suka hada ido,kada ki damu Bilkisu haka al'amura suke tafiya. Nan hira ta tsinke,mai tsawo. Bilkisu ta nuna matukar rashin jin dadinta ga wannan kaddara da ta samu Jamila. Ita kuwa Jamila tana ta kuka. Bilkisu ta dubi Jamila cikin alamun tausayi, ba kuka za kiyi ba Jamila,kada ki damu da komai, tun da kin tabbata Salim shine yayi miki wannan ciki, ai koda ya karyata dole a gane, tun da alkali ya umarci likita ya binciki jininku ai babu damuwa, ta gama maganar, tana ci gaba da kallon Jamila. Jamila tayi gwauron numfashi, tayi wani dogon tunani ba ta ce komai ba, har Bilkisu ta sha jinin jikinta ta yi niyyar ta tambaye ta. Jamila ko da akwai wata magana ce da ki ke so kiyi na ga alamun haka? 41 Jamila ta sake yin ajiyar zuciya, ta kalli Bilkisu, wallahi Bilkisu ke kawata ce, na amince miki da akwai amana a tsakanin mu, na tabbata miki ko kisan kai na yi ba zaki tona min asiri ba. Bilkisu ta girgiza kai, amma ba ta yi magana ba. Jamila ta ci gaba da cewa, a gaskiya zan gaya miki wata magana, ni dake ce, amana idan ki ka tona min asiri Allah ya saka min. Wallahi Bilkisu in gaya miki ba Salim ne yayi min wannan ciki ba, Alhaji Karma-Karma ne baban Faruku. Bilkisu tayi zumbur ta mike, har daurin zanenta yana kwancewa, ta dubi Jamila, wai da gaske kike Jamila ko wasa, kina nufin Alhaji Karma-Karma baban Saurayinki Faruku? Shi fa, Jamila ta amsa cike da karfin hali. Bilkisu ta rike baki, ta koma ta zauna a dai-dai lokacin da take salati. Amma Jamila kin yi kuskure, shine kuma kika lakafawa Salim bai ci ba bai sha ba? To menene dalilin ki na yin haka? Jamila ba ta boye mata komai ba, ta kwance mata bakin jaka, ta gaya mata yadda aka yi ta gamu da Alhaji Karma-Karma da yadda ya yaudare ta,da abubuwan da suka biyo baya da kuma dalilin da yasa ta lakafawa Salim. A karshe ta nemi shawarar Bilkisu, musamman ta yadda za ta kaucewa binciken likita. Ta tabbata likita zai kwance mata zane a kasuwa,kuma kashin ta ya bushe, menene mafita yanzu? Bilkisu jikinta yayi sanyi tausayin Jamila ya kamata, ta yi niyyar za ta taimake ta komi wuya, sai dai su mutu tare. Ta dube ta hawaye na zuba, Jamila kada ki damu zan taimake ki muddin rai, kuma na gano hanyar da zamu bi har a karya kudirin likita, ta yadda zai ba da rahoton karya ga alkali,ai idan sun san wata basu san wata ba. 42 Jamila ta yi 'yar dariya ta dubi Bilkisu, wace hanya ce wannan kawata,don Allah gaya min. Bilkisu ta ce, "kin gane ko Jamila, kamata yayi ki rubuta wa Alhaji Karma-Karma wasika, ki gaya masa halin da ake ciki,da sunan likitan da aka bawa aikin wannan bincike, na san idan Alhaji ya ke zasu sasanta komai. Ni ki rubuta koda yake bai san ni ba, sai in kai masa in yi masa bayani". Da gama fadin haka, Jamila ta taso cikin murna, ta rungume Bilkisu, ta dube ta suka hada ido, da kyau Bilkisu kawata,na gode kin taimake ni, wallahi na gode. ******** ********* Alhaji koda yake baka waye dani ba, amma nine Bilkisu kuma Jamila ce ta aiko ni da wasika na kawo maka. Tana gama yi wa Alhaji Karma-Karma bayani, ta mika masa wasikar da Jamila ta rubuta,wacce take cikin wata amdulan. Jiki na rawa ya amsa, ya san kwanan zancen, ya soma karantawa, yana girgiza kai kamar haka: Zuwa ga Alhaji, Da fatan kana lafiya, Allah yasa, Alhaji ka lalata min rayuwa, amam babu abinda ya dame ka a cikin zuciya. To na san watakila kana sane cewa na lakafawa Salim mai aikin gidan mu wannan ciki da kayi min, har abin ya kai kotu, yanzu ma alkali ya bada umarnin likita ya auna mu, ya gane idan cikin da gaske Salim ya yi min, ka san kuwa dole zai gane ba cikin Salimba ne. Idan haka ta faru kaga naji kunya,kuma ya zama dole in fallasa ka cewa kai ne kayi min wannan aikin. Shawara anan itace ka hanzarta ka sami ganin dakta Dattijo sanannen likitan nan mai yi wa koti aiki, domin ku daddale dashi, ya canza 43 bayani. kuma ya lakafawa salim wannan ciki dole. Ка hanzarta Alhaji, kada dare yayi wa mai wankin hula. Nice Jamila. Alhaji Karma-Karma ya mike, fuskarsa duk ta canza ya soma tunani a zuciya, lallai karya za ta kare, za'aji babbar kunya idan ban yi aiki da abinda yarinyar nan tace ba, kamata yayi na hanzarta zuwa in samu ganin wannan likita kamar yadda tace. Zan bashi ko nawa ne domin ya canza rahotonsa. Idan kuma bai amince ba fa? To lallai ya shia uku, domin ba zai samu daman kai rahoton sa ba, don zan sa 'yan iska su je har gidan sa su murde wuyansa. ya mutu murus, idan ya so komai ta tafasa ta kone. Da gama wannan tunani, Alhaji ya sallami Bilkisu, ya bata wasu kudi ta kaiwa Jamila, ita ma ya bata, a matsayin toshiyar baki. Shi kuma nan da nan ya saka ambulan din nan wacce wasikar Jamila ke

Chapter 3 of 5