kashe inji suka
fito su na fuskantar juna, domin su yi sallama. Sun soma
magana babu dadewa, sai ga wata mota ta tsaya kusa da
inda suke.
Jamila ta dubi Faruku da sauri.
Dalin ga babana nan ya dawo, don Allah idan ya
fito daga cikin mota ka gaishe shi.
13
Da gama maganar, ta ruga a guji na ya tsaya,
dai-dai shi kuma ya fito; sannu da zuwa baba.
Alhaji Hamisu dogo ne kakkaura, fuskarsa da
akwai fara'a amma bata son hurda da mutane ba. Yana
sanye da kananan kaya, da wata jaka a hannunsa. Da
ganinsa, kaga wanda ya goge da zama da turawa, Allah ne
ma ya san abinda yake yi in yaje turai.
Ya dafa kan Jamila, ya dube ta yana murmushi;
Yawwa Jamilata, kina lafiya? Ya mika mata jakarsa ta
amsa.
Faruku yayi hanzari, ya tari gabansa ya dan rage
tsawo, kamar mutumin kirki.
"Sannu da zuwa baba".
Alhaji Hamisu ya dube shi cike da mamaki;
"yawwa sannu dana".
Daga ina ne ka zo?
Kafin ya amsa Jamila ta dubi mahaifinta tana
murmushi, baba wurina ya zo. Alhaji Hamisu yayi 'yar
murmushi. To madalla, sannu ka ji.
Daga nan yayi cikin gida ya barsu tare. Suma
basu dade ba, suka yi sallama, suka shirya ranar da zasu
sake gamuwa.
****** ******* ********
Alhaji Hamisu ya dubi Hajiya Asama'u yana
niyyar yayi mata magana.
"Tun jiya da daddare dana shigo nake so in
tambaye ki game da wannan yarinyar, wai wani hali take
ciki ne, wanene na gansu tare domin har ya gaisheni cikin
ladabi.
Hajiya ta gyara zama da alamun dan razana a
fuskarta, tana tsoron watakila an tsegunta masa halin da
Jamila take ciki ne, ta dube shi, za ta bashi amsa.
14
Wani saurayi ne wai take so, sun kuwa dade tare
yaro kuma mai ladabi. Tana kawowa nan, sai tayi shiru,
tana sauraren abinda shi kuma zai ce.
Ya gyara zama ya sake duban ta; a ina yake ne,
wanene babansa a kan garin?
Bata bashi amsa ba, suka ji sallama daga waje
wanda yayi sanadin yankewar hirar.
Alhaji Hamisu ya amsa sallamar yayi waje. Da
fitarsa Hajiya Asama'u tayi sauri ta samu Jamila a
dakinta, ta gaya mata cewa koda babanta yace ta gaya
masa sunan mahaifin Faruku, to kada ta fada masa ainihin
sunansa. Dalilin wannan dabar ita ce, Hajiya bata bukatar
Alhaji Hamisu ya san Faruku ko dan gidan wanene tun
yanzu, sai nan gaba ya dace, domin wai kada a kawo wa
'yarta cikas ga wanda take so, saboda halin Alhaji Karmakarma, ba kowane zai so ya hada zuri'a dashi ba. Da ta
gayawa Jamila wannan magana, sai ta dawo falo ta sake
zama.
Zaman Hajiya ke da wuya, ga Alhaji ya dawo,
wani saurayi na biye dashi a baya. Da zuwa ya zauna, ya
kuma bukaci saurayin ya zauna shima. Alhaji ya dubi
Hajiya yana niyyar magana, ya nuna wannan saurayi.
Na manta in gaya muku tun jiya dana dawo,
wannan saurayi da kike gani, sunansa Salim, da ne ga
wani ma'aikacina daya rasu a kwanakin baya.
Alhaji ya gyara zama ya cigaba; mahaifinsa ya
rike min amana iyakar kokarinsa, gashi babu mahaifin
nasa yanzu, shi kuma jiya dana dawo na bi ta gidansu na
gaishe da mahaifiyarsashine take gaya min ya gama
sakandare, tace tana bukatar ya rika min wasu ayyuka
kafin takardunsa su fito, in taimaka masa ya samu
makaranta. Shi ne na tambaye shi yace zai iya aikaceaikace a nan gida, musamman da yake ya iya tukin mota,
zan bar masa mukullin mota ta kirar Fijo dake gareji
15
domin idan za ku aike shi ko kuma za ku unguwa ya kai
ku" Yana zuwa nan, yayi shiru.
lajiya ta dubi Alhaji, ta dubi Salim, tace; sannu
saurayi kaji, Allah ya jikan mahaifinka!
Salim kansa a sunkuye, muryarsa tana rawa ya
amsa; yawwa sannu na gode.
Nan take Alhaji ya kwalawa Jamila kira, ta amsa
tazo. Ita ma ya gabatar da Salim kuma yayi mata bayani
kamar yadda yayi wa mahaifiyarta. Ta dubi Salim suka
hada ido, sai tayi ajiyar zuciya tace, sannu da zuwa. Shi
ma ya amsa mata. Washegari, Alhaji Hamisu ya kimtsa ya
bar kasar sai an ganshi.
Salim saurayi ne, dan kimanin shekaru ashirin da
biyar, kyakkyawa ne, ga iya sa sutura, ga cika ido, ga
kunya da sanin ya kamata. Allah ya bashi basira, da
kwazo a lokacin yana sakandare. Mahaifinsa Mallam
Kallamu talaka ne, domin masinjan Alhaji Hamisu ne a
lokacin da yake da rai. Mutum mai hakuri da rikon
amana, sun gama da Alhaji lafiya shi yasa yaji tausayinsa
ya kawo shi gidansa domin ya rika samun abinda zai
taimaki mahaifiyarsa. Tun ranar d Alhaji ya kawo Salim,
ya soma aikace-aikace, da zuwa unguwa a mota, da
sauransu. Sai dai abinda ya kawo shi kawai yake yi, ba
ruwansa da wata harka da ba tasa ba, musamman Jamila
da take shisshige masa, amma babu abinda ya dame shi da
ita. Tun yana burgeta, har ya soma bata haushi, domin ya
nuna babu ruwansa da ita, bayan kuma yana ci a
Karkashin su. Irin tunanin da take yi kenan kullum. ********
********
Jamila na takawa dai-dai a gefen hanya, tana
barazana, duk ta kagara ta kai inda tayi niyya. A lokacin
la'asar tayi, motoci, manya da kanana sai kaiwa da
16
komawa suke. Ga babura da kekuna, wasu kuma na taka
sayyada. Burinta shine ta je gidansu Asabe-naira, domin
sun dade basu gamu ba, tunda aka samu hutu. Tayi jira
Salim ya dawo ya kaita, amma shiru ya shiga gari bai
dawo ba, shine ta zuciya ta tafi, da niyyar idan ta koma
gida ta same shi, sai tayi masa tsiya.
Na.muzu kawali, yana cikin bin jerin gwanon
motoci, a cikin motarsa kirar makauniya sabuwar yayi,
yayi tozali da Jamila, tana tafiya komi na jikinta yana
juyawa, sanye yake da bakin gilashi, Nan da nan ya cire
ya c i gaba da kallonta. Tunani ya zo masa a cikin zuciya,
kai jama'a kaga wata tsalelliyar budurwa haka, tashin
hankali, lallai ta hadu, lallai wannan ta dace da Alhaji,
bari in latsa, idan ta amince, ni tsaf, domin zan yanki
Alhaji da kyau, idan ya ganni da wannan yarinyar.
Da gama wannan tunani, Namuzu ya sauka daga
kan titin ya taka burki a gefe, yana kallon Jamila tana
zuwa ta cikin madubi. Da zuwa dai-dai inda yake, yayi
gyaran murya, ya sako kai yana mata magana.
Uhum, ji mana yan-mata, nine nake magana.
Ta waiwayo ta dube shi; lafiya kake kirana? Tayi
maganar, amma ba ta tsaya ba. Ya taka motar kadan ya bi
ta, tsaya mana 'yan mata, magana zanyi dake minti biyu.
Da yake daman ta sa ba, bayan tayi 'yar barazanar
ta, sai ta tsaya. Shi kuma ya sako kansa waje, suka yi ta
magana, babu mai jin abinda suke cewa. Jim kadan Jamila
ta bude gidan baya Namuzu ya ja suka yi gaba.
BABI NA UKU
Alhaji ya gyara zama, yayi gyaran murya, ya rike
hannun Jamila ya soma yi nata magana; ""yan mata nine
Alhaji Karma-karma, watakila Namuzu yayi miki bayani,
ko kuma bai yi ba, nayi murna d zuwanki".
17
Jamila ta gyara zama ta soma mutsu-mutsu.jikinta
na rawa,ta soma tunani a cikin zuciya.
Alhaji Karma-Karma, ai shine mahaifin saurayina
Faruku, kai jama'a wane tsautsayi ni kuwa ya kawo ni?
Ga da, ga uba. Kai kai kai, sai gumi ya karyo mata.
Alhaji ya dube ta yana murmushi, me ya sameki
ne kike gumi haka, bari a kunna miki iyakwandishan, Ya
mike ya kunna ya dawo ya zauna kusa da ita. Ya sa hannu
ya taba ta, ta noke, ta matsa daga gareshi. Tunani ya sake
zuwa mata.
"Ke Jamila, yi sauri ki tashi ki bar nan, ya za'a yi
ace mahaifin saurayinki ya kwanta da ke?"
*******
Tun ranar da Jamila ta gamu da Alhaji Karmakarma,mahaifin saurayinta Faruku, ta sakar masa jiki,
saboda tsabagen ruwan naira da yake mata. Alhaji bai san
Jamila budurwa ce ga dansa ba, bai kuma san ita ko 'yar
gidan wanene ba. Shima Faruku bai san wainar da ake
toyawa ba. Ita kuwa tasan komai, amma naira sun rude ta,
don haka take takatsantsan, kada Faruku ya gane ita
budurwar mahaifinsa ne. Shima bata bukatar mahaifin ya
gane ita budurwar dansa ne.
Tunda haka ta soma faruwa, Jamila ta juyawa
kawayenta baya, shima Faruku ya ga canji, gaba daya
suka rasa gane kanta, ta zama mazari babu wanda ya san
inda ta fuskanta. kawayen suka gaji suka rabu da ita, shi
kuwa Faruku suna tare, sai dai ba kamar da ba. A wannan
lokaci ne kuma, Allah ya jarabci Faruku da mutuwar
kaunar Jamila, ba kamar da farko ba, da yake yaudararta,
ya zama yana jawo hankalinta ta amince ya aure ta. Ita
18
kuwa duk kallon raini take masa, domin tana ganin da
ubansa mahaifi take taku, ballantana shi kwaro a ganinta.
Idan ka ganta ta canza tayi kyau, cikin lokaci kankani, ga
karin suturu, da sauran kyalkyali na mata.
Shima Alhaji Karma-karma, Allah ya jarabce shi
da mutuwar son Jamila, domin irin kirar dirarriyar 'ya
mace da Allah yayi mata. Sai abinda tace yake yi mata.
Gemai-gemai da shi, ya mayar da ita tamkar matarsa ta
aure, ba kunya babu tsoran Allah. Yayi kokarin aika
Namuzu ya dauko ta, amma bata gaya masa ba. Ita tana
gudun kada wata rana tana tare da Faruku, ya ga an zo a
motar mahaifinsa za'a tafi da ita, kaga kenan zai gano
bakin zaren. Don haka duk wani kokari na Alhaji ya gane
inda take, ya ci tura. Haka aka ci gaba da zama har na
tsawon wani lokaci. Ita kadai ta san yadda abn yake.
Faruku ya dubi Jamila, a yayin da suke zaune tare
a dakinsa, yana mata magana, ya rike hannunta ya dube
ta; dalin ni naga duk kin anza ne, baki da wani kuzari,
tun 'yan kwanaki, lafiya dai ko?
Da fadin haka,zuciyar Jamila ta buga ras,
kamaninta ya canza, amma tayi karfin hali ta dake. Dole
ne hankalinta ya tashi, domin kuwa yau watanni biyu
kenan ba ta ga al'adarta ba. Ta san cewa ta samu juna biyu
tare da Alhaji Karma-karma, baban Faruku, amma ba ta
gaya masa ba, shi kuwa bai gane ba. Ita kanta Hajiya
Asama'u ba ta san halin da Jamila take ciki ba, duk kuwa
da cewa ta canza. Dalilin shine Jamila yarinya ce mai
karfin bali wacce za ta iya kowace irin badda kama,
domin kada a gane abinda ke damunta.Taki yarda tayi
wani abu irin na masu juna biyu a gaban mahaifiyar duk
abinda ya taso mata, sai ta daure. A 'yan kwanakin nan,
19
hankalinta yana kara tashi domin yawan tunanin makomar
wannan ciki da Alhaji Karma-karma yayi mata. Hakika ta
tabbata Alhaji ne yayi mata wannan ciki, ba dansa ba
Faruku, domin shi Faruku ma, tunda ya yanke shawarar
zata gayawa Alhaji domin yasan dabara. Shiyasa
hankalinta ya tashi a yayin da Faruku yayi mata wannan
tambaya, amma da yake yarinya ce mai karfin hali da iya
tsara magana, sai ta kawo wani zance ta kau da waccan
maganar, har suka yi hira suka gama, ya sallameta, ba tare
da ya fahimci komai ba. Da rabuwarsu, Jamila ba ta zaune
ko ina ba, sai gidan sirri, inda suke sheke ayarsu da Alhaji
Karma-Karma da niyyar tayi masa bayanin halin da take
ciki saboda a san dabara, tun kafin dare yayi wa mai
wankin hula.
******* ********
Jamila ta dubi Alhaji Karma-karma tayi
murmushi na karfin hali ta soma yi masa magana; dama
ina so inyi maka wata magana tun kwanaki, amma na
kasa, yanzu kuma naga ya da ce in gaya maka. Ta
kammala maganar tana rawar murya da tsoro-tsoro.Ya
dube ta, shima yayi 'yar dariya, ya dafa mata kafada, ya
soma ba ta amsa; kada ki ji komai yi maganarki Jamila
tawa, me kike so, me kike gani wajen wata kawarki ko
kuma wata 'ya mace da baki dashi? Gaya min yanzun nan
in saya miki ko menene.
Tayi shiru na wasu 'yan dakikoki, ta numfasa, ta
soma magana tana murmushin karfin hali.
Wallahi ,ba wani abu da na gani bane ya tsokane
min ido, domin kayi min komai, sai dai wani abu ne da ka
sakamin nake so ka taimaka ka ciremin, wato juna biyu,
wanda kayi min. Tana gama fadin haka, sai hawaye sharshar-shar-shar.
20
Alhaji ya mike tsaye iskar fanka tana kada
doguwar rigar da yasa jallabiya ki sai gwani, ya fashe da
dariya, da karfi, har Jamila ta daga kai tana kallonsa, yayi
shiru bai ce komai ba ya taka gaba kadan,ya sake juyowa
ya dawo kusa da ita ya zauna. Yasa hannu ya share ma ta
hawayen dake kwarara sau daya, ya dubeta yana
murmushi; haba Jamila, kada ki karaya mana, ina wata
damuwa anan, na amince ni na saka miki juna biyu, kuma
zan cire miki shi bada dadewa ba.Ya gyara zama ya
cigaba da magana, haba Jamila ki bar damun kanki za ki
rabu dashik, irinki babu iyaka, haka ta faru dasu tare dani,
anyi maganin abin kwantar da hankalinki, yanzu zamu je
gidan wani likita na, na musamman a unguwar turawa. Ya
kammala maganarsa, amma hawaye wani na bin wani a
idanuwan Jamila,shi kuwa jiki na rawa ya soma shiri.
Karfe biyar da rabi dai-dai,Alhaji Karma-karma
ya taka burkin motarsa da ya ke badda kama da ita, a
kofar gidan likita Baffa,dake unguwar turawa. Gaba daya
suka fito, Jamila tana biye dashi duk ta kagara. Suka isa
kofar shiga ta gilashi, wadda kake ganin inuwarka a jiki.
Alhaji ya sa hannu ya kwankwasa sau biyu, daga nan ya
daina. Jim kadan aka bude kofar. Wani mutum ne mai
matsakaicin tsawo wankan tarwada, sanye da doguwar
riga ta likitoci fara, da farin gilashi,ya fito. Da fitowarsa
ya soma kallon Jamila ya kuma dubi Alhaji, suka yi
dariya.Gaba daya suka yi cikin falon ba tare da sun soma
magana ba, har sai da suka shiga,ya nunawa Jamila wuri
ta zauna, shima Alhaji ya zauna.Daga nan ya ce musu
yana zuwa ya daga labule ya shige wani dan daki. Kafin
ya dawo, Jamila ta mayar da hankalinta ga kallon yadda
aka kawata dakin da kayayyakin zamani. Tana cikin kallekallen sai gashi ya fito rike da kwalaben lemo da 'yan
kana nan kofuna, ya soma ajiyewa a kusa da Jamila, ya
dan matsa ya ajewa Alhaji a gabansa.Daga nan ya samu
21
wuri ya zauna. Alhaji ya kalli abinda aka aje masa kuma
ya dago kai, ya dubi likita yayi 'yar murmushi. Shima
likita yayi 'yar dariya, a yayin da ya ke satar kallon Jamila
da gefen ido.
Dakta Baffa, 'ya kwana biyu ya aka ji damu, ina
fata dai komai lafiya? Ya cire gilashin dake idonsa, ya
rike a hannu; lafiya lau Alhaji, ya na ka ayyukan? Alhaji
bai bashi amsa ba, sai ya rika shafar gemunsa yana kallon
Jamila yana murmushi.
Dakta Baffa, ba sai na gaya maka ba, idan dai ka
ganni irin haka, ka san kwanan zancen.
Likita yayi hanzari ya kalli Jamila wacce take
sauraransu kuma ya kalli Alhaji ya soma magana yana
murmushi.
Alhaji ba'a ganinka,sai idan ka saka kwai. Da
fadin haka, gaba daya suka fashe da dariya da karfi Jamita
tna kallonsu.
Alhaji ya dubi likita, a yayin da suka daina
dariyar, kai dakta Baffa bana son shegantaka, kai dai yi
min abinda ya kawoni in tafi.
Ba tare da yayi wata magana ba, ya tashi daga
inda yake, ya nufi inda Jamila take, tana kallonsa yana
zuwa, fuskarta na nuna alamun razana. Ya karasa inda ta
ke ya kama hannunta ya rike tafin hannunta yana latsawa, daga nan ya girgiza kai,ya rike ta suka shige wani daki.
Da shigarsu, Alhaji yayi wata 'yar murmushi, ya koma ya kishingide, yana jiran su fito.
Kamar minti goma, suka fito, dakta Baffa na
gaba, Jamila na biye. Alhaji ya soma murmushi, ya mike
ya zauna, yana kallonsu. Amma irin yadda dakta Baffa ya
fito fuskarsa a murtuke, yasa Alhaji ya sha jinin jikinsa,duk ya kagara ya ji kwanan zancen. Jamila ta
zauna, shima likita ya zauna, yayi tagumi ya fuskanci
Alhaji. 22
Alhaji ina bakin cikin abinda zan gaya maka,
domin idan aka ce za'a zubar da cikin wannan yarinya
lallai za ta mutu dole sai dai ayi hakuri har ta haihu, kuma
duk likitan da yayi karambani ya ce zai yi wata dabara,
lallai kam zai kashe ta.
Da gama fadin haka, annurin fuskar Alhaji ta
canza, Jamila kuwa da ta ji sai ta fashe da kuka.
******* ******** ***********
Alhaji Karma-karma ya dubi Jamila wacce take ta
faman rusa kuka, yana ba ta hakuri, yayi imanin cewa
abinda dakta Baffa ya gaya masa gaskiya ne. Tun da kuwa
ya gaya masa cewa wannan ciki babu yadda za'a zubar
dashi ya yarda, domin kwararren likita ne, wanda yayi
karutunsa a turai, yayi suna a gida da waje. Babban abinda
ya sa Alhaji yake ba wa Jamila hakuri shine, labarin da ta
gaya masa cewa ita 'ya ce ga Alhaji Hamisu. Hankalinsa
ya tashi, domin duk da irin girman kansa,yana ganin
mutuncin Alhaji Hamisu, tun wani lokaci da suka gamu a
wani taro, kuma suna ganin mutuncin juna. Kai da ya san
Jamila 'yar Alhaji Hamisu ce da bai yarda wata hurda ta
shiga tsakaninsu ba. Sai dai kuma bakin alkalami ya
bushe, aikin gama ya gama, sai dai tunanin wace hanya се
mafita? Idan kuwa aka yi lalaci za'a ji kunya. Idan yana
takama ne ma da dukiya, Alhaji Hamisu kuma na takama
da gwamnati. Wannan a tunanin da ya ke yi yasa
hankalinsa ya tashi, ya kulla wannan idan ya hango
wancan, sai ya kwance. A karshe ya gano wata hanya,
wacce ya ke tunani ita ce mafita. Don haka ya dubi Jamila
ya soma ma ta magana, yana neman hadin kanta.
Jamila ki daina kuka, idan Allah ya yarda babu
komai da akwai yadda za'ayi.
Ta dube shi tana shekin kuka; to Alhaji menene
za'ayi, ni ka gama dani, ka gama da rayuwata, yanzu me
23
zance wa iyayena.Ta sake fashewa da kuka, ta surkuyar da
kanta tana kallon kasa;
"Ki daina kuka Jamila, ina da dabara." Ba ta
saurareshi ba, ta ci gaba da shekin kuka; "yanzu abinda na
ke so in ji ki gaya min gaskiya, kina da wani saurayi
matashi, wanda kuke hurda dashi?
Jamila na jin haka sai hankalinta ya sake tashi,
domin tunanin Faruku .Tana ganin ta ci amanar Faruku,
har da ta amince tana harka da babansa mahaifi, bayan
kuma tana sane. Ta tabbata sakayya ce ta Allah, shi yasa
ya tona mata asiri. Ya za ta da ta tuna da wannan, sai ta
sake fashewa da kuka, ba tare da ta ba wa Alhaji amsar da
yake bukata ba.
Ya sake kallonta, hankalinsa a tashe, haba Jamila,
kuka ba shine ba a irin wannan lokaci, ni saurayinki nace
ki gaya min, ki ji dabarar dana shira.
Ta dago kai, ta kalleshi, idanuwanta sunyi jawur,
domin kuka; Me za ka yiwa saurayina idan na gaya maka?
Ke dai fada mana ki ji, ya amsa ma ta da damun
ya kagara;
Jamila tayi zurfin tunani. Da farko har za ta gaya
masa Faruku ne dansa saurayinta, amma wata zuciya ta се
a'a, kada ta yi haka, ita dai ta amsa masa cewa tana da
saurayin, domin ta gane gudun ruwansa.
Ta sake dubansa.
Eh, to ina da saurayi!
Ya gyara zama ya ka00lleta, a yayin da ita kuma
ta sake sunkuyar da kai tana kallon kasa;
Madallah, kuma dalilin da na ce haka, kinga da
shirya mata maganganu, yadda za ta amince da abinda zai
gaya mata. Ya ci gaba d cewea, "kinga Jamila ni tsoho ne,
kuma da kunya ace kamarki yarinya mai ii da kanki kin
auri kamana. Don haka na ke so, mu shirya wata amana ni
dake, ko nawa kike so zan baki, sai kice wannan saurayi
24
na ki shine yayi miki ciki, kuma koda talaka ne shi,zan
baki ko nawa ne, ki bashi yayi hidimar aurenki. Ke dai
abinda na ke so, duk wata hanya da za ki bi, to ki bi, ki
makala masa wannan ciki, shine na ke so. Yana zuwa nan,
ya mike ya dauko wani akwati dankare da kudi ya mika
mata; ki soma rike wannan, amma me kika ce?
Jamila ta ga kudi, ta ga cewa ai Faruku ne
saurayinta, kuma shine da ga Alhaji, don haka daman da
maganar aure a tsakaninsu. Faďuwa ta zo dai-dai da zama
kenan.
Nan take Jamila ta amince da maganar Alhaji, shi
kuma yayi murna, bai san cewa dansa Faruku bane,
Jamila za ta makalawa wannan ciki. Ita kuwa ta amince,
kuma ta san dabara.
BABI NA HUDU
"Jamila tunda kika shigo na ga baki da kuzari, ko
kuwa ba ki da lafiya ne?
Faruku ya soma tambayar ta, yana kokari yasan
halin da take ciki, a matsayinsa na mai kaunarta.
Ta san shirinta, da kuma kisisinar da take so ta yi,
domin ta makala masa cikin da mahaifinsa yayi mata. Ta
riga ta gama shirya abinda za ta yi, gabatar kawai ya rage.
Ta tabbata koda Faruku zai karyata abinda za ta gaya
masa, dole kuma ya yarda, idan ya tuna shine aka sani
saurayinta.
"ki yi magana mana Jamila, ki gaya min kinsan
damuwar ki, ita ce damuwata.
Ta matso hawayen karfin hali suka soma diga
tana nema ta fashe da kuka.
"Kada ki yi kuka Jamila, ina kaunarki, bani
bukatar bacin ranki, fadi ko menene, babu damuwa".
25
Ta soma magana ciki-ciki, tana rawar murya,
Faruku ina da juna biyu, kuma na ka ne; Ta kammala
maganar ta fashe da kukan karya.
Ya mike da sauri ya je ya kunna fankar sama, ta
soma juyawa tana bada iska, amma gumi na keto masa.
Ya dawo ya zauna kusa da ita, ya dafa kafadarta;
"Me kike nufi Jamila, kina kuwa da gaskiya?
Ta dago kai suka hada ido; to Faruku, wa na ke
dashi, sai kai kasan ba zan maka karya ba".
Ya mike ya hada hannuwansa da karfi, ya koma
ya zauna, ya dube ta;
Kai Jamila ina da shakka, gaskiya. Za ta yi
magana, amma ya hana ta, ya rike hannunta, suka yi waje,
suka shiga mota, ba ta san inda zasu ba.
******** *****
Faruku ya taka burki a kofar wani karamin dakin
shan magani, domin ya samu ganin wani likita abokinsa,
ya auna jininsa dana Jamila, saboda ya gane idan shine
yayi mata ciki. Ya riga ya yanke shawara a zuciyarsa cewa
idan har wannan ciki nasa ne, zai amince dashi, kuma zai
sa a zubar dashi, kuma zai ci gaba da kasancewa tare da
Jamila. Idan kuwa ba shine ba, kamar yadda yake shakka,
lallai Jamila ta ci amanarsa kenan, don bai yi tsammanin
tana da wani ba, sai shi. Irin wadannan tunani ya ke yi har
suka shiga cikin dakin shan maganin, ya samu likitan da
ya je nema, yayi masa bayanin abinda ya ke so. Nan take
likíta ya soma auna Jamila. Bayan misalin minti goma sha
biyar ya kammala bincikinsa, kuma ya dubi Faruku ya
soma yi masa bayani.
"Ranka ya dade ina bakin cikin shaida maka
cewa, ba kai ne kayi wannan ciki ba, hasalina koda ace kai
26
ne kayi babu yadda za'ayi a zubar dashi, dole sai ta
haihu".
Faruku ya mike tsaye, daga inda ya ke, jiki na
rawa, ya dubi likita, ya kuma dubi Jamila, sai ta yi hanzari
ta sunkuyar da kanta kansa, domin ta san daman wannan
ciki ba Faruku ne yayi mata ba. Dabarar ta ba ta ci ba, ya
kenan za'ayi. Ta fito ta bayyana gaskiyar al'amarin ne, ko
kuwa?
Tana wannan tunani, Faruku ya matsa kusa da ita,
ransa a bace yasa hannu ya dago kanta, suka hada ido, ya
harareta; Jamila kin ci amana ta, kin munafunce ni, sai ya
dago hannu ya tsinke ta da mari tas. Ta fashe da kuka, ya
sake dagawa zai sauke mata biyar, likita yayi hanzari ya
rike masa hannu.
********* ********
Jamila ta shigo cikin gidansu sumu-sumu, tana
rike da 'yar jakarta a hannu. Hajiya Asama'u
mahaifiyarta, tana tsakar gida tana 'yan aikace-aikace.
Jamila ta yi sallama, mahaifiyar ba ta ta amsa mata. Sannu
da aiki Mama
Ta gaishe da mahaifiyar tayi gaba za ta wuce
dakinta.
Mahaifiyar ta dube ta sama da kasa, ta ga duk ta
yamutse, ta fita kamanninta, da gani da akwai abinda ke
damunta; har ta wuce za ta shiga daki, mahaifiyar ta kasa
hakuri.
a fili.
"Jamila, Jamila".
Ta tsaya ta waiwayo fuskarta na nuna Bacin ranta
"Wai Jamila me ke damunki ne a 'yan kwanankin
nan, na ga duk kin canza kin lalace, ki gaya min gaskiya
'ya ta". Jamila ta yamutsa fuska; ni babu abinda ke
damuna, zazzabi ne kawai da na ke yi.
27
Mahaifiyar ta girgiza kai, ta yi ajiyar zuciya; to
shike nan, Allah ya kyauta.
Da shigarta daki, ta tura kofa ta rufe ta ciki, ta
kunna fankar sama, ta jefar da karamar jakarta akan kafet,
ta wuce ta zauna a gefen gadonta, ta cire takalmanta, daga
nan ta haye kan gado, ta kwanta a rigingine tana kallon
rufin dakin.Hawaye shar-shar, suka soma zubo ma ta, ba
kakkautawa. Dole al'amura su dagule mata, gaba kura
baya za ki, ta jefa kanta a cikin masifa, wacce ta
gwammace 'ace ta mutu. Ta tabbata dole iyayenta su san
wannan al'amari, kai har ma da mutanen gari.
To wanene za ta ce yayı mata cikin? Alhaji
Karma-karma kai ai abin kunya ne ace yadda take cikin
'yan matan zamani, ace aji labarin wannan tsoho shine
yayi mata ciki. Ko kuwa ta rufe ido ko za'a kada a raya
tace Faruku ne?
Kai jama'a ita gaba daya ma yanzu b a ta kaunar
Faruku, domin irin wulakancin da yayi ma ta, shima ya
gaya mata wai ta ci amanarsa, don haka maganarsa ba ta
taso ba.
To wane zata makalawa? Kamata yayi ta samu
wani ta ce shine, koda kasa da sama zasu hadu.
Wanene wannan kuwa, wanda take ganin za ta ma
iya aurensa, idan ta makala masa, wanda dole ma iyayenta
su tilasta masa ya amince.
Ta yi ta wannan tunani mai tsawo, har a karshe
tunani ya zo mata.Koda yake al'amari ne mai wuya,
amma za ta kwatanta. Dabarar da ta yanke ita ce, idan aka
tambaye ta wanda yayi ma ta ciki, za ta tsaya kai da fata
cewa Salim direban gidansu ne, ko babu komai idan ya
yarda zai aure ta.Da sauki a gareta, hasalima da yake
saurayi ne kyakkyawa, mai ilimi da sanin ya kamata.
Ta ci gaba da tunani;
28
Shin wace hujja za ta bayar cewa Salim shine yayi
mata ciki? Wannan ita ce matsalar. Koda yake tana da
hujjoji, amma basu da tasiri. Mahaifiyarta dai takan tafi
unguwa ta barsu tare a gida, haka kuma takan aike su,
unguwa tare, kai da dai sauransu.
Jamila ta sake tunani;
Lallai kam za ta dauki alhakin bawan Allah haka
kawai. Amma ita tana ganin cewa ita ce kawai mafita a
gareta, da a ce a gane Alhaji Karma-karma ne yayi mata
ciki, ba