Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels LAIFIN ZUCIYATA ALAMонD MAKOSA BALA MOH MAKOSA HAUSABOOK.COM Harafi Publlshers KaAure Ni BILKISUHAMUHD GABATARWA Da suna Allah, wannan daya halicci halitta, ya fifita bil-Adama birbishin dukkan halitta, tsira da aminci su tabba ha annabi Muhammad (S. A. W) da Iyalan gidansa, da Sahabbansa nagargaru. Bayan haka, wannan littafi mai suna (Laifin Zuciya ta) na rubuta shine musamman, domin wadansu al'amura da suke faruwa a rayuwar yau, ta fuskanci lalacewar al'umma da tabarbarewar ta. Da kuma abubuwan da suka yi kama da haka. Hakika littafin ya bankado, kuma ya tona asirin wadansu mutane da suke amfani da dukiyar da Allah ya basu, wajen cimma wadansu munanan dabi'u na su. Maimakon yin amfani da dukiyar wajen neman kaykkyawan makoma a lahira. Haka littafin ya ta'allaka ne kusan kacokaf akan halayyar wata yarinya Jamila da yadda ta rungumi mummunan rayuwa, а maimakon bin sahihiyar hanya. Da sakamakon abinda ya same ta, saboda laifin zuciyar ta da yadda ta yi na dama. A takaice, wannan littafin hannunka mai sanda ne ga irin wadannan jincin jama'ar da na lissafa a sama, domin ta zama ma'auni ga masu aikata irin haka, ta yadda za su fuskanci kyakkyawan rayuwa mai tasiri a duniya da lahira. Su kuma kaucewa shiga bin son rayuknasu, domin gudun kaskancin duniya da lahira. Wannan littafin ba wai zai kasance don nishadi ba ne kadai ga masu karatu. Za kuma a iya amfani da shi a makarantu da dakunan karatu da cibiyoyin bayar da ilimi. Ina fatan Allah ya tabbatar mana da mafificin alherins, Amin. Bala Mohammad Makosa Zaria 20/2/2005 BABI NA FARKO LAIFIN ZUCIYA TA Yau lahadi ce, babu aiki ga ma'aikatan gwamnati, sai dai 'yan kasuwa. Dalibai ma, ba ranar ba ce a garesu ta karatu, don haka rana ce ta shakatawa ga masu aikin sarki da masu bin sawun su. Rana ce ta farin ciki ga Jamila da sauran kawayenta su biyu, domin kuwa su na ziyartar samarinsu domin a sheke aya. Misalin karfe tara da rabi na wannan safiya, kamar yadda agogon bango na dakin ta ya nuna, Jamila ta fito daga wanka, tana daure da zane iyakan kirji kanta babu dan kwali, sai dai daure-dauren kitso, kafufuwanta salifa ne dan Madina. Da shigowa dakin ta aje kwandon soson a gefe daya, ta wuce ta zauna akan wata kujera tana fuskantar wani katon madubi ta soma shafe-shafe. Tana cikin haka, mahaifiyar ta, ta faga labule ta leko, ba tare da tayi sallama ba ta shigo. Jamila ta waiwaya da sauri, fuskarta tana nuna alamun bacin rai, suka yi ido hudu, daga nan ta saki fuska. Mama ina kwana? Ta gaishe da mahaitiyar a yayin da take kokarin shafa hoda a fuskarta. Mahaifiyar bata amsa gaisuwar ba, ta dube ta soma yi maa magana. Jamila ina ake shirin zuwa ne tunda sanyin safiya aka yi wanka? Jamila ta yi 'yar murmushı, a yayin da take goga gazal a girarta, ta ba wa mahaifiyar amsa. Wallahi Mama, unguwa zamu ni da wasu kawayena, shine nake shiryawa kafin su zo!! Ta kammala maganar tana sauraren abinda mahaifiyar za tace. To ba ki gaya min ko ina za ku, kuma dasu wanene, ko kuwa wacece ban sani ba cikin kawayen naki? Mahaifiyar ta sake 1 tambaya, tana nuna damuwarta a fili. Jamila ta daina abinda take yi, ita ma ta nuna ranta ya baci, ta dubi mahaifiyar. "Haba Mama, ai bazan miki karya ba, wata kawarmu ce za tayi wani liyafa, shine ta gayyacemu, ni da Asabe naira, da Balkisu kwandala zamu tafi, shine nake jiransu. Mahaifiyar ta bude baki za tayi magana kenan, sai akayi sallama daga kofa, ta waiwaya, sai ta ga su Asabe naira, da Balkisu kwandala, wadanda ake magana, kowannensu ta kure gayu. Da ganinta, gaba daya suka tsuguna cikin ladabi, suka gaisheta cikin natsuwa, da da'a kamar wasu mutanen kirki. Da ganinsu ta yanke maganar da take yi da 'yarta Jamila, ta juya ta koma dakinta, tana mai juyayi da tunanin halin yayan yau. Jamila ta tashi da sauri, har zanenta yana nema ya kwance, ta rungume Asabe da Bilkisu, tana dariya, suma suna yi, daga nan ta dube su lokaci daya ta soma yi musu magana. Ta daga kai dubi agogon bango dake kusurwar gabas a dakin, sa'annan ta sake duban su; "Kai 'yan iska, sai yanzu kuke zuwa, ai kun so ku yi latti, ku duba agogo lokaci ya soma tafiya. Balkisu da Asabe suka dubi juna, suka fashe da dariya, suka tafa hannuwa. Asabe ta soma magana. "Ahayye ka ji 'yar-iska, wai ita da muka samu tana shiryawa, shine zata ga laifin mu, da muka bar gidajen iayayenmu, muka zo, amma lallai kin ci sunanki Jamila Tsari. Balkisu ta amasa, gaskiyar ki wallahi Asabe, ai rainin wayo ne irin na Jamila, ko kin manta mutuniyar taki ce? Gaba daya suka fashe da dariya, a yayin da ita kuma Jamila take ci gaba da shiryawa. 2 Asabe ta mike daga gefen gado d take zaune, ta nufi wajen wata kanta, inda wata damafareriyar rikoda da talabijin mai launi suke, tasa hannu ta danna rikodar, kaset din dake ciki ya soma juyawa, sai sauti ya soma tashi. Tun daga inda take, ta soma taka rawa, ta juyawa da rausaya. Ita ma Balkisu ta mike ta soma jujjuyawa, suna fuskantar juna, suna matsowa, Jamila na gefe tana sitati tana kallonsu tana dariya. Su kuwa suna rawar, har suka rungume juna. A dai-dai wannan lokaci ne, Jamila ta gama dukar haske, ta caba ado, da wata damfareriyar atamfa, ga awarwaro da 'yan kunnaye masu tsada, ga wani daurin dankwali, mai suna zamani mu tafi tare tayi, ga takalma yarinyar taka samaru ta kwama, ta rataya wata jaka a Landan. Kai idan aka ce za'a bayyana irin shigar da 'yan matan nan gaba dayansu suka yi, da yawa da basu san zamani ba, sai su ce suki ta mallace kawai, ko kuma almara. Kai da ganin shigarsu lallai kaga yau 'yan matan zamani. Jamua ta fuskanci saurain, a yayin da ta kashe rikodar da sauti ke tashi, ta soma gaya musu hirar da tayi da mahaifiyarta kafin su zo, kuwa ta gaya musu domin bakin su ya zama, daya. Su ma Asabe da Bilkisu suka gaya mata irin tsarin da suka yi wa iyayensu har aka kyale su suka fito. Gaba daya suka fashe da dariya, sukayi shewa. Daga nan suka yi waje gaba daya da niyyar zasu tafi. Da zuwansu kofar dakin mahaifiyar Jamila, gaba daya suka yi sallama suka shiga, suka samu tana zaune, tayi tagumi, da gani kasan da akwai abinda ke damunta. Jamila ta karasa inda take, ta zauna kusa da ita, Asabe da Bilkisu suka rage tsawo sukayi kamar ruwa ya ci su, kamar wasu salihai. Jamila ta dubi mahaifiyar; Mama zamu tafi, sai mun dawo. 3 Mahaifiyar ta soma magana, ba tare da dubi inda take ba: To me zance miki, Allah ya kiyaye, sai kun dawo, na gaya miki dai babanki yayi waya zai dawo yau, ki rufamin asiri ki dawo da wuri, idan kuwa ya dawo baki nan, to babu ruwana. Mama idan Allah yaso za ki ganni da la'asar; Jamila ta mike suka yi waje tare da kawayenta. Ya zama lallai rayuwar Hajiya Asama'u mahaifiyar Jamila ya tashi, domin irin halin da 'yarta take ciki. Koda yake bata taba gani da idonta ba, amma tana da labarin halin da Jamila take ciki. Rayuwa irin ta bin maza da shaidanci, rayuwar ta holewa. Tun lokacin da ta shiga makarantar sakandare, ta gamu da su Asabe da Bilkisu, rayuwarta ta canza, ta zama iskar duniyar na dibarta. Mahaifiyar na bakin ciki da wannan hali datake ciki, amna saboda dauna da take wa Jamila, ba ta iya ce mata komai, sai dai addu'a take mata, Allah ya shiryeta. A duk lokacin da Jamila tace za ta je unguwa, to kuwa har ta dawo mahaifiyar bata da kwanciyar hankali domin ta san kwanan zancen, musamman idan aka ce tare suka fita da Asabe naira, da Bilkisu kwandala. Koda yake wadannan 'yan mata suna wannan harkar, babu wanda zai ce ga inda suke yinta, sai Allah, su kadai suka san makwanensu. Sai dai kuma a duk fadin makarantar horas da mata malamai ta garin ziyara, idan ana maganar Jamila tsari, da Asabe naira, da Bilkisu kwandala, sai dai a shafa fatiha. Babu wanda bai san su ba, dalibai na shakkarsu, malamai kuwa, har sun rasa yadda zasu yi dasu. Sau da yawa suna ta da hargitsi a makarantar, ana basu hutun dole, daga baya su dawo. Kai idan aka ce za'a tsaya bayyana halayen wadannan 'yan mata sai a cika wani karamin littafi. А takaice, basu da halaye masu tasiri. Mahaifin Jamila, mutum ne mai dukiya, kuma tsohon ma'akacin gwamnati Bayan da yayi ritaya, Alhaji Hamisu, sai ya zama yana zuwa kasashen waje yana safara, zuwa cikin kasan nan. Ba mutum bane mai zama, shiyasa bai san halin da 'yarsa take ciki ba, gashi kuma ba mutum mai jama'a bane, ballantana wani ya tsegunta masa halin da take ciki. Mutum ne wanda kansa kawai ya sani da iyalinsa. Duk halin da Jamila take ciki, Alhaji Hamisu bashi da labari. Shima yana kaunarta matuka, don haka baya bukatar wani abinda zai dagula mata rai, musamman da yake ita kenan tilo, da Allah ya bashi, tare da matarsa daya. Asabe naira, da Bilkisu kwandala, su labarin su ya banbanta da na kawarsu Jamila, domin su iyayensu talakawa ne gaba da baya, basu mallaki komai ba, sai rufin asiri. Amma duk da haka, sai ka rantse suma iyayensu sun rufa sun tayar da kai, domin babu abinda basu samu a wurin Jamila, suturu, takalma, abin wuya, kai da komai da komai. Kai haseli ma, sune suka hure wa Jamila kunne, suke kara tura ta a halaka. Duk abinda suka ce, bata tsallakewa. Haka dai rayuwar wadannan 'yan mata yake tafiya a kullum. Karfe hudu da rabi dai-dai na yamma, Faruku barazana, da Dan-Male, da Kabiru naci, suka iso kofar gidan da ake wannan sheke ayar. Tun daga nesa, motoci ne birjik masu tsada, da 'yan kabu-kabu, ka ke hange. Dan-Male ya rungumo Asabe, shi kuwa Kabiru naci na tare da Bilkisu daga baya. Kowanne na tafiyar tare da tasa masoyiyar. Gaba daya suka yi cikin katon falon da ake wannan bidirin. Da shigarsu, masu taren baki, suka nuna musu wurin da zasu zauna. Kowanne ya zauna, yana tattaunawa da tasa. Bayan wani dan lokaci, sai wani saurayi dogo, sanye da wando da shat, yayi zanzaro, ya sa bakin nikitaya, ga bakaken takalma ya kwama, hannunsa da wani agogo yana daukar idanuwa. Da zuwa ya tsaya a 5 dandamali, ya umurci kowa yayi tsit. Da aka natsa, wannan saurayi ya fuskanci samari 'yan uwansa da 'yan mata ya soma magana; "Abokanmu maza, da kawayenmu 'yan mata, barkanmu da yammaci. Yana nufin haka, sai gaba daya wurin aka dau tafi raf,raf,raf, wasu kuma na fito. Ya cigaba, "yau rana ce muhimmiya, da Kawarmu, Jummai taba gemu masoyiya, kuma abokiyar abokinmu Aminu falle-falle, take cika shekaru ashirin da biyar, da shigowa wannan duniya tamu. Dan haka ne ma'abota soyayya, duk muka taru, mu taya su murna. Amma kafin nan, ina fata, mai kula da kide-kide ya zabi wani arnen kida yasa mana gaba daya, domin mu yi sharen fage. Don haka gareka, Danladi Dujal! Koda jin haka, sai nan take Danladi Dujal, ya saka wani kaset a katuwar rikoda, sai ji kake dif,dif, kwash, falon duk ya rude kamar ginin zai rushe. Nan take duk wurin aka mike aka hau dandali. Faruku barazana, ya dubi Jamila da suke zaune kamar kashin awaki, ya kyafta mata ido ya matsa kusa da ita, yayi mata rada a kunne. "dalin tashi mu taka rawa mana! Ta kalleshi da manyan fararen idanuwanta, tayi murmushi, tace, tashi mana mu je. Ya mike tsaye, ya kama hannayenta, ya fago ta, ta mike, daga nan suka soma taka rawa. Suma Asabe da Bilkisu da nasu samarin, suna cikin jama'a suna takawa. Wuri duk ya rude, baka jin abinda na kusa da kai yake cewa. Karfe bakwai da rabi na dare dai-dai, Faruku barazana ya taka burkin motarsa a kofar gidan su Jamila, bayan ya kai kawayenta gidajensu, ya kuma kai abokansa. 6 Da zuwa ta bude kofa ta fito, daga nan t sunkuya su ka soma magana. "Dalin sai yaushe, zan sake ganinki? Faruku ya tambaye ta, yana nuna alamun yana so ya ji. Ta girgiza kai, tayi masa kallon kauna, tace, Dalin kaga babana yau zai dawo, kaga babu daman zuwa yawo, amma kada ka damu, zaka ganni ko yaushe! Ya dube ta, ya soma magana; amma ki daure ki zo, da akwai maganganu, kin dai gane. Ta dube shi, kada ka damu, za ka ganni bada dadewa ba! Da suka gama 'yar hirarsu, sai suka yi sallama ya ja motarsa yayi gaba, ita ma tayi cikin gida. Da shigarta, tayi sallama, amma ta ji shiru. Sai ta Karasa kofar dakin mahaifiyar, ta daga labule ta shiga. Suka yi ido hudu da mahaifiyar tata, amma Jamila ta sha jinin jikinta saboda yadda ta samu mahaifiyar. Ta aje jakarta gefe daya ta karasa ta zauna kusa da ita ta dube ta cikin ladabi; Mama lafiya naga ranki a bace, don Allah ki gaya min. Ta kammala maganar tana nuna damuwar ta a fili. Mahaifiyar tata, tayi gyaran murya, ta gyara zama, ta soma magana ba tare da ta dubi Jamila ba; "Haba Jamila, me yasa ke kullum sai kin bata min rai, kin ce za ki dawo da la'asar, amma yanzu karfe nawa? Sai ta duba dan karamin agogon dake daure a hannunta na dama. Sannan ta daga kai ta dubi Jamila a karo na farko tunda ta shigo. Ita ma Jamila tayi sauri ta dubi agogonta, kuma ta oma magana kanta na sunkuye; "Mama kiyi hakuri, nima ba haka na so ba, yanayin al'amuran ne". Da ta kawo nan, sai tayi shiru. Mahaifiyar ta dube ta ranta a bace. 7 Wai ke jamila, don Allah wace irin 'yar iska gagararriyar yarinya ki ke so ki zama? Ko kina ce bani da labarin irin barbafan da ku ke yi ne a cikin gari? Jamila ba ta bukatar mahaifiyarta tayi mata fada ko kadan, don haka sai ta yamutsa fuska, annurin fuskan ya kau. Ita kuwa mahaifiyar, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, tayi wa Jamila kaca-kaca kamar za ta buge ta. Tana cikin maganar Jamila ta zuciya, ta tashi fuuuuu, ta fice daga dakin, ta tafi dakinta; Da zuwa ta haye kan gado, tana kananan maganganu. Tana kwance ta rika tunanin cewa; Kai jama'a, nifa Mama na ta soma kure ni, domin tana takura min rayuwa. Ya ma za'ayi haka, zamani na Annabi, kowa yana yagar rabonsa, yana sheke ayarsa, ace ba za'a kyale ni in hole rayuwa ta ba? A gaskiya ni a kyaleni in sakata in wala, in more rayuwata anini-anini, kada a takura min. To ita Mama da take cewa tana da labarin abinda nake yi, to ita wa ya san abinda suka yi a lokacin ba'a haife mu ba. Kaiina, ni yanzu na soma wasan soyayya, a kyaleni inyi soyayya da wanda nake kauna Faruku barazana, mu hole rayuwarmu, daga baya mu yi aure, idan ma ba mu yi ba, ai lallai mun karu da juna. Kai auren me, ai tukuna, sai mun buga duniya, domin yau ake, gobe sai labari. Tabdi. jan, ina ni ina aure yanzu ai ko baba da mama sun ce inyi zane a'a, ai aure sai wadanda kansu bai waye ba amma mu sai buga duniya. Ni idan ma aka matsa min sai in soma barin musu gidan ina kwana a wurin Faruku barazana, ai dole su kyale ni inyi abinda nake so. 8 6 eho ehw eo ehs ehr Irin wadannan tunani shaidan yayi ta kawata wa Jamila a c ikin zuciya, yana kawata mata rayuwar duniya, yana nuna mata cewa ya kamata ta ci gaba da hole rayuwarta, wata rana sai labari. Nan take ta ji kanta ya fashe, ba ta jin tsoron Allah ballantana iyayenta da suka haife ta. Don haka komai za ta iya yi, babu mai takura ta. Bayan da Jamila ta gama wannan tunani nata, sai ta jawo mayafi ta lulluße kanta, ta ci gaba da tunani, har barci ya kwashe ta zuwa safiya. BABI NA BIYU sai bengo ya tsage kadangare ke samun wurin shiga, kuma sanda tun tana karuwa ake tankarama ake tankwaea ta, idan ta girma aka ce za'a tankwarata, sai ta karye. Irin tunanin da Hajiya Asama'u, mahaifiyar Jamila takeyi kenan, tun da sanyin safiya, bayan a tayi wa Jamila fada a daren jiya, amma ta nuna ita a rabu da ita. Та cigaba da tunani, a yayin datake kan wata kujera mai laushi a zaune, tana cewa; lallai wannan sakaci ne daga gareta, har da ta bawa Jamila dama ta shaki gardin rayuwar banza tare da kawayenta 'ya'yan banza. Ta gane cewa lallai babban kuskure ne ga yaye idan suka ba wa 'ya'yansu musamman mata 'yancin yawo da ko wadansu irin kawaye, domin ta haka ne ake gamuwa da mugayen kawaye, kamar yadda 'yarta Jamila ta gamu da su Asabe naira, da Bilkisu kwandala. Yanzu wace hanya za ta bi, ta hana 'yarta Jamila bin wadane an muguwar dabi'ar, cikin ruwan sanyi, ko kuwa da karfi da yaji? Ke Jamila barcin kike har yanzu baki tashi ba, ai gara ki tashi kiyi sallah! Hajiya Asama'u tayi wannan maganar, a yayin da ta daga labulen dakin Jamila, ta leka. Jamila tayi motsi kadan kamar za ta tashi, amma ta dake, ta sake jan bargonta, ta rufe jikinta, sai kanta kawai ke waje. Mahaifiyar ta sake matsawa kadan cikin dakin tana so ta sake magana; Jamila da ke fa nake yi, ko kuwa baki ji na ne? Da gama fadin haka, Jamila ta tashi, ta saka kafafuwanta а kasa, tana zaune a gefen gado, tayi tagumi, ba ta ce wa mahaifiyar uffan ba. Ita kuwa mahaifiyar ta sake magana; Ki daure ki tashi haka, ga karin kumallo can, kada ya huce; Ta amsa ciki-ciki, to Mama ai gashi nan na tashi. Koda fadin haka, mahaifiyar bata sake cewa komai ba, ta juya ta daga labule ta fice. ******* ******* Faruku barazana, saurayi ne kyakkyawa, wanda Allah ya bawa iyayensa arziki mai tarin yawa. Kusan a duk garin idan ana lissafin masu 'ya'yan banki lallai idan ba'a sa mahaifinsa na farko ba, ba zai wuce na biyu ba. Alhaji Karma-karma, shine mahaifinsa. Ba banza ba ake kiran mahaifin da wannan sunan, domin mutum ne wanda ya tara dukiyarsa, ta hanyar yaki halas yaki haram, murdiya cin dukiyar jama'a, da danne filaye, sune hanyar da ya tara dukiyarsa. Mutum ne mai girman kai, da son ya wulakanta jama'a, ga rashin taimako. Ba ma maganar taimako ba, hatta idan akayi masa babu mai jin dadinsa, masu morewa dukiyarsa, sai matarsa daya, da dansa Faruku sai kuma karuwansa,. Mutum ne wanda yayi Kaurin suna wajen lalata 'yan-mata masu kwadayin abin duniya, Da yawa yana da 'ya'yan banza da aka haifa 10 masa, amma bai taba amincewa da ko daya ba, dole kuma a rabu dashi, domin yana da abokan tafiya, kudi wadanda sun saye talakawa, sun saye sarakuna da masu mulki, sun saye yara da manya, maza da mata, sun saye alkalai da lauyoyi, da joji-joji, sai wadanda Allah ya kare. Kai saboda irin halayensa, mutanen gari suke masa kirari, suna cewa; Alhaji Karma-karma abokin shaidan, maso zama da kai ya rungumi duniya, lahira kuwa ko oho, baban Faruku anci dubu sai ceto, mai fankama na Hajiya Laure, lahiranka da kallo. Irin kirarin da ake masa kenan. Kamar kumbo kamar katanta, Faruku bai yar a Kasa ba, domin halayensa iri daya ne dana mahaifinsa. Yaro ne da Alhaji Karma-karma mahaifinsa, da hajiya Laure mahaifiyarsa suka shagwaba. Ba ya jin shakkar kowa a garin sai dai yayi yawo a cikin motarsa, ya dau 'yan mata. Tun lokacin da suka gamu da Jamila yake nuna mata kauna a fili, amma cikin zuciyarsa ba haka bane. Shi burinsa, ya tsallaka ta kawai, daga nan ya san nayi. Ita kuwa ta sakar masa jiki, ta hakikance komi nisan jifa kasa zata komo, wato duk lalacewar suka yi, kawai yake shiya mata ba. Ko banza dai Farukų ya san ba zai dauru a wannan garin ba, don haka yake abinda ya ga dama, har jama'ar gari suke ce masa Faruku barazana. Jamila na kaunar Faruku iyakar so, kuma ta hakikance zai aure ta komi runtsi. Kaunar da take masa, kusan saboda abinda iyayensa suka mallaka ne, domin yarinya ce mai hangehange, da tsabagen kwadayin abin duniya. Ba ta lura da abinda Allah ya bawa iyayenta, sai dai ta hangi abinda wadansu suke da su shiyasa ta zama kaska ga Faruku, don tana karuwa da shi yadda ba zai misaltu ba. Hidima kowace iri shi yake mata, kamar jijinta. Shi yasa yadda take gudun zuciyarsa ba ta gudun na iyayenta, musamman mahaifiyarta wacce sun fi kasancewa tare, da yake mahaifinta ba mai zama bane. Yarinya ce wacce ta yi 11 imani da rayuwa irin ta karya, wanda yasa bata godewa Allah ga duk abinda Faruku ya bata, sai ta hada da bin Alhazan zamani, ta basu mutucinta, vadansu ma sun girmi mahaifinta. Sai dai kuma bata yarda Faruku yasan tana bin Alhazan zamani ba, wadanda kawai suka sani sai kawayenta, masu ci a karkashinta, Asabe naira da Bilkisu Kwandala. ****** ******* *****市市 Karfe biyar da rabi dai-dai, Faruku barazana ya taka burkin motarsa a kofar gidansu Jamila, ya kashe injin ya dora hannunsa akan sitiyari, ya soma matsa ham, kamar yadda ya saba yana yi idan ya zoita idan ta ji ta san kwanan zancen. Yau ce daman ranar da suka yi alkawarin zasu je kantin karya arzikinka, domin tun karfe biyu na rana Jamila ke saurarensa su je su dawo da wuri, don lallai mahaifinta zai dawo a wannan rana da yake bai samu dawowa ba a ranar lahadi da ta wuce. A saboda haka ne ma, ya rika tunanin watakila ba zata samu damar zuwa ba. Idan haka ne kuwa, zai yi bakin ciki, saboda ya riga ya dana bakarsa ta sheke ayar da zasu yi a dakinsa na otal. Yana wannan tunanin, sai ga Jamila ta fito rike da jakarta, ta caßa ado. Da zuwa ta soma bashi hakuri a kan dadewar da tayi bata fito ba. Nan da nan ta shige motar ya tada injin suka yi gaba. Jamila ta dubi Faruku, da manyan fararen idanuwanta, a yayinda suka hau kan babban titi, suna bin sahun sauran motoci. Tayi masa kallo, mai firgita mai Kwalama. Dalin kasan dalilin dadewa ta ban fito ba? Ya girgiza ba tare da ya kalleta ba; ban sani ba, mene va faru ne, kinsan kuwa har na soma jin haushi. Tayi 'yar muimushi, har hakoranta suka fito, iska ta kada gyalenta, tasa hannu ta gyara, ta kalle shi; "In 12 gaya maka, Mama ta ce tace ita sam babu inda zanje, ita wai yamma tayi, shi yasa ma nake so mu yi sauri mu dawo. Ya waiwaya da sauri ya dube ta, da alamun damuwa; Me kike nufi, kuma me yasa tace babu inda za ki? Ya mayar da hankalinsa ga kallon gabansa, bayan da yayi mata wannan tambayar. Tayi dariya, ta karfin hali; Dalin babu wani abu, kasan yau babana zai dawo, kaga ya kamata ace ina gida, domin ya hana ni zuwa ko ina idan baya nan. Ya sake waiwayo da alamun 6acin rai a fuskarsa; Yanzu kina nufin kenan, ba za muje duk inda muka yi alkawari ba? kafada. Ta kalle shi, ta dan matsa kusa ta dafa masa Haba Faruku, ba haka nake nufi ba, amma kayi hakuri, naga ranka ya 6aci ne. Bai ce mata komai ba, ya karya kwana ya shiga harabar kantin karya arzikinka, ya taka burki ya kashe inji, suka fito, suka rurrufe kofofin suka shige cikin kantin. Da suka gama sayayyan da zai yi mata suka fito suka sake bin hanya, sai otal din sabuwar duniya, nan ma suka rho sha to shiga sfn to domin******* su tafka ta'asa. Takwas da rabi dai-dai na dare Faruku ya taka burkin motarsa a kofar gidansu Jamila. Ya

Chapter 1 of 5