Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
gudu horn nawa nayi miki amma aban za. dakyar ta iya tashi tace '' wallahi Allah, Allah ya isana ban yafe ba ai wannan rashin mutunci ne baka bani hakuri ba sai ka tsaya kana faɗa min bak'ar magana.'' komawa cikin motar sa yayi yana cewa Allah ya isanki babu abin da za tayi min. Nimrah da sauri ta ga ƙusa saka mai tayi aikuwa nan take tayar motar ta fashe fara dingisa kafar ta , tayi tana share hawaye. dakyar ta ƙara so gida a zaure ta tarar da malam yana ƙwance da mafici a hannun sa Halifa yana kusa dashi yana cin gyada. lafiya naga kafarki da rauni..?." Malam ya faɗa yana tashi zaune. zama nimrah tayi, ta fashe da kuka tace '' malam naje gidan uwani shi ne mota, ta buge ni.'' ba nace miki, ki barta da Allah ba tun da taji ta gani zata iya cinye kudin nan amma shi ne da yake kunne kashi gare ki , kika ƙi ji.'' share hawaye tayi tace '' malam yaushe zani gurin gwaggo?.'' Ranar duk randa kika ga dama ya faɗa yana komawa yana kwanciya. tashi tayi, tana shiga cikin gidan wanke kafar'ta , tayi ta shiga dakin su fatima ce sai umaimah suna zaune suna hira kwanciya tayi akan matacciyar tabarmar ta duk tabi ta yage pillow ta jawo ta tada kan'ta dashi tace '' dan girman Allah umaimah dauko abin fifita kiyi min ko na samu sauki.'' Fatima tace '' a ina kika ji wannan ciwon?.'' NIMRAH tace '' mota ce ta bige ni.,, Allah ya sawwake. Cewar fatima. Umaimah tace '' amin ya Allah gaskiya kin ga girkin dare nake yi na gaji wallahi bazan iya yi miki ba.'' NIMRAH tace '' dan Allah kina gamawa ki kwasa min nawa mamanku muguwa ce ba , bani za tayi ba sai tace ita , tayi sana'a ta samu kudin ta ni ba zanci ba kuma kinga ni idan na samo haduwa ake yi a rufawa juna asiri.'' Umaimah tace '' to.,, nimrah a hankali bacci ya fara daukar ta , Wannan kenan. N.D.C quarters. ma'aruf wannan duk zancen banza ne kai kasan yayan ku ba zai taɓa aure ba , ba tare da na sani ba. Cewar Hajiya zakiya. ma'aruf yace '' hakene daman kawai faɗa miki nayi ina su miemie?'' tayi bacci shi kuma faruq yana gurin baba jummai. tashi yayi yana cewa ga wannan chocolate din ki basa ya ajiye mata wata ledar shopping a kasan capert. to tace , tana mayar da hankalin'ta gurin labaran da ake yi, gaban tane ya faɗi lokacin da aka hasko picture ma'aruf ya rike wata mace wacce bata san ko wacece ba tsayawa tayi tana jin me ake fadi kamar haka. ayau ne larabawa ake zargin sharararen dan kasuwan nan Alhaji Saheer dallahat ya daura aure amma na sirri hankalin mutane ya rabu kashi biyu wasu suna cewa wacce me sa'ar ce ta samu nasarar auren sharararen dan kasuwan nan me faɗa aji number daya a jakar nan tamu a ɗaya bangaren kuma inda yan yarfe suka ce wa ba aure yayi ba budurwar sa ce to zantuka dai kala kala mun yi kokarin jin ta bakin sa amma abin ya faskara domin na tuntubi me magana da yahun bakin sa yace mu dai jira komai ake ciki zan mu gani.'' tufa ta dauka ta gutsura tana mamaki to kodai gaskiya ne amma ai tasan wane saheer ba zai taɓa yi mata haka ba duk yadda aka yi akwai wata a kasa. daukan wayar ta , tayi tana ƙoƙarin kiran sa , sai gashi nan ma ya shigo hannun sa rike da faruq ajiye wayar tayi tace '' kaga daddy ku ba zama ko.'' saboda taga bakin yaron yaƙi rufuwa. saheer ɗurkusawa yayi yace '' Hajiya ina wuni?.'' Hajiya tace '' lafiya qalau alhamdulillah.'' zama yayi a ƙasa faruq ya hau kan cinyar sa yana dariya tare da riƙe hannun abban nasa , tausayin su ne dukka ya kama ta , tace '' saheer a kawo maka abinci?.'' Saheer yace '' eh amma ba wannan yarinyar bace tayi ba ko?'' yana nufin ihsan. Murmushi tayi tace '' ni ce nayi saboda yau bana sha'awar cin wa'yannan girke girken nasu su ke nan kullum ace basu da abincin ci sai kayan maiƙo ni yanzu shekaruna sun ja ga rashin lafiya daman ina fama da ita dakai na nayi tuwon shinkafa miyar kubewa idan zaka ci na saka a zubo maka.'' Saheer yace '' zanci.'' Baba jummai baba jummai. da sauri matar ta fito ba wata babba nace can kenan kawai suna taci dan Hajiya ta girme ta , tace '' Hajiya gani.'' zubowa saheer wannan ragowar tuwan. Yallaɓai ina wuni sannu da zuwa ta faɗa tana durkusawa amsawa yayi yana tambayar ta ya aiki alhamdulillah tace , ta juya ta bar gurin faruq ban da murmushi babu abin da yake can yace '' daddy dani zaka tafi ko? mu dinga yin breakfast tare.'' tausayin yaran ne ya kama shi baya jin zai iya kai wa Hidaya ya'yan sa , haka kurum sam be yarda da ɗabi'ar ta ba , ajiyar zuciya ya sauke yace '' a'a kai zaman ka a gurin hajiya.'' ba dan ya so ba yace '' to.'' tashi yayi Hajiya ta bashi chocolate din da ma'aruf ya bashi tsalle ya dinga yi yana murna. Hajiya tace '' saboda me kaki yarda su faruq su koma hannun ka ? bana jin Hidaya ko bera zata iya cutarwa balle mutum musamman ma wanda ya fito daga zuri'ar mu ko baka ga yadda muke ba ni da mahaifiyar ta? gaba ki Dayan su Mutanen kirki ne.'' ƙasa yayi da kan'sa yana da zurfin ciki, yana so ya fadawa Hajiya shi be aminta da ita ba amma besan yadda zai mata wannan bayanin ba matar da kudi ne a gaban ta , za'a yi bata su domin a cutar mai da ya'yan sa yace '' insha Allahu zan gyara .'' yayi haka ne baya so maganar tayi tsayi. baba jummai ce ta kawo mai abinci da ruwan wanke hannu, wanke hannun sa yayi ya dauke robber. bismillah yayi ya fara ci Hajiya ci gaba tayi da kallon ta . baba jummai ce ta fito hannun ta dauke da afrah yarinyar ta tana ganin sa ta fara dariya tana cewa daddy jummai ajiye ta , tayi ta tafi gurin sa da gudu ta faɗa kan cinyar sa tana cewa Allah daddy yau sai na bika zuciyar sace tayi rauni, da ace A'isha na raye duk da basu shiga wannan halin ba tun tana yarinya ƙarama ta mutu bata sam mahaifiyar ta shafa kan'ta yayi da aka raba shi gida biyu yace '' afrah wayayi miki kitson kanki...?.'' uhmm aunty ihsan ce amma ba kitso bane kalba ce ta faɗa tana wasa da hannun lis ɗin sa da ya cire. saheer yace '' yayi kyau.'' Daddy zaka tafi da ni da faruq ko?.'' Hajiya tace '' kai kuwa ko dan nacin da yaran nan suke yi ka tafi dasu da ni nayi zatan sai ta dan kwana biyu yau zaka mayar da su amma na lura sam zaman su anan yafi maka kwanciyar hankali, yaran ka suna da kulafici bana gudun su wallahi tausayin su nake ji idan ka tafi kuka suke yi kafin su dawo dai-dai Wallahi ana daukan lokaci me tsayi.'' zare hannun sa yayi daga cikin plate ɗin yace '' Hajiya ba ko wacce macece za'a kai mata ya'yan da bata haifa ba ta riƙe kin ga Hidaya bata taɓa haihuwa ba , bana tunanin tasan yadda za ta kula da su.'' saheer kenan kawai kafi son zaman su anan amma Allah na tuba ita daman mace ai yar raino ce yarinya karama idan aka siya mata yar tsana kai zaka kayi mamakin yadda take kula da wannan yar tsanar nan tata.'' shiru yayi bece komai ba , Hajiya tace '' da gaske ne aure za kayi?.'' dam dam haka kirjin sa ya bada wani irin sauti dakyar ya iya saita kan'sa yace '' daman maganar da ta kawo ni kenan aure nake so na ƙara.'' Hidaya tana wani abu ne wanda baka so? Hajiya ta jefo mai wannan tambayar yace '' a'a.,, HAJIYA tace '' bazan hana ka ba Allah ya sanya alkairi amma saheer ban ji dad'i ba auren ku shekara ɗaya da yan wasu watanni kace zaka ƙara aure yarinyar nan tausayi take bani duk mazajen da take aura basu da kirki ita haka kenan haka ƙaddarar ta , take wallahi ranar da na ganta a waya naji dad'i ganin yadda ta yi kiba alamar tana jin dad'i duk da kai sai dai kazo badai ka kawo min ita ba , ka kyau ta kenan? bansan me kake tunani ba baka so ta rabi yaran ka wallahi karka bari ta gane haka idan ta gane ba zata ju dad'i ba.'' Saheer yace '' Hajiya ba haka nake nufi ba , amma ni kin ga ba zauni bane ba na bata dama taje in dai gidan su ne da gidan mu to bansan bata zuwa ba.'' hmmm Saheer ban sanka da karya ba karka fara yi min ita yau yarinyar da take son zuwa gidan nan kullum kafar'ta na nan gidan kullum da abin da zata kawowa yaran nan shi ne zaka bata damar zuwa taki zuwa. be taɓa zaton haka Hidaya tayi wa Hajiya illa ba irin haka sai yau kai gaskiya mutum me two face be yi a rayuwa ba , kallon arfa yayi yace '' afrah daddy tashi zan wanke hannu na.'' to daddy afrah ta faɗa tana tashi dauke plate ɗin yayi, ya tafi kitchen shi rayuwar sa me sauki yake yi ba ruwan sa , da girman kai, ajiye wa yayi ya wanke hannun sa ya fito faruq ne ya matso kusa da shi yace '' daddy zan bika.'' shafa sumar kan'sa yayi yace '' ba tafiya zan yi ba muje parlour ko.,'' to yace suka tafi parlour wasa suka dinga yi yana biye musu idan ka gan'sa a cikin ya'yan sa ba zaka yi zaton wannan mutumin bane me daure fuska, sallah magariba aka tayar tashi yayi ya riƙe hannun faruq aikuwa ihu afrah ta saka ihsan ce ta fito ta gaishe dashi ta riƙe ta , suka fita alwala suka yi sannan suka tafi masallaci. Wannan kenan. abbas ba zaka fahimta ba wallahi ni yanzu bani da wani right jiya saheer ya dawo ƙasar nan kai hakuri zuwa na samu kaina ni kaina nayi kewar ka , Cewar hidaya Abbas yace '' ke dai kawai kice baki da lokaci ne ke yanzu namiji baya burge ki sai mace.'' a zuciyar ta , tace kamar kuwa ka sani a fili kuwa sai tace '' no ba haka bane abbas ni nace bana son namiji yanzu mace nake aure ko namiji..?.'' kin ga sai an jima ya faɗa yana kashe wayar sa , tsaki taja ta kunna datar ta ƙara yiwa bestie magana tayi cikin Sa'a tana online tace '' wallahi Allah na manta amma bara yanzu nayi mata magana ina fa garin ku ko na zo ne ?.'' dan jin tayi kafin ta bata amsa Sannan tace '' to dan Allah kiyi mata kece baki iya gamsar dani ba wallahi shi ya saka ma ni ban neme ki ba.'' emoji's din dariya bestie ta sako mata tace 😂 aini tun ranar farko na fahimci ke wace'ce amma karki damu zan gyara wallahi ina bala'in son ki, Hidaya tabe baki tayi ita bata son mace me kananun breast tafi son masu auki wa'yanda zata dinga kama su , su cika mata hannu kuma g**ndinta bashi da zurfi daga antaɓa ta , ta kawo tace '' to ki zo amma gaskiya idan baki shirya kwana muna yi ba to karfa kizo, nifa bana gajiya wallahi, bestie sai ta ce 💃 gani nan zuwa yau sai kin yi kuka. reacting din dariya Hidaya ta sako mata , ta kashe datar ta. number amrah ta nemo buga daya tayi mata ta dauka gyara muryarta tayi kamar tana magana da namiji tace '' baby na ina cike da kewar ki, kin je gida lafiya.'' a shagwaɓa tace '' uhmm uhmmm bayan tun safe baki neme ni ba sai yanzu ni nayi fushi.'' Sorry my princess daughter bani da kamar ki wallahi ko wacce mace idan na kalle ta gani nake bata cika mace ba kece dai nake wa kallon cikakkiyar mace. Cewar hidaya. Amrah tace '' i love you.'' wani farin ciki ne ya kama Hidaya tace '' i love you too,, amrah tace '' yau za'a kawo min kudi fa..'' gaban Hidaya ne ya buga tashi tayi daga kwanciyar da take wutar kishi tuni ta fara ruruwa a cikin zuciyar ta , tace '' wanne kudin?.'' Kai aunty wanne kudi ake kawowa mace ban da na aure. Cewar amrah. Hidaya tace '' sam ba zai yiwu ba wallahi ban yarda ba , kin ga idan auren kike so ni ki aure ni zan yarda.,, da sauri amrah, ta tashi zaune bata , yi zatan shedancin hajiya Hidaya yakai haka ba tace '' auzubillahi ina neman tsari haba mommy kamar ba musulmai ba a'a wallahi sai ki saka duniya ta zage ni, mahaifana su tsine min ina kaunar naga ya'ya na idan na aure ki mene riba ta ke ba'a gidan mijin ki , kike ba ? gaskiya idan kika ƙara yi min wannan maganar za mu rabu.'' Hidaya rasa ina zata saka ran'ta tayi kawai sai ta kashe wayar neman mafita, ta shiga yi bata kaunar taga amrah tayi nisa da ita dole ta wargaza auren nan idan har tana so taci gaba da kwanciyar hankali kafin hawan jini da ciwon zuciya su kama ta tashi tsaye tayi ta shiga kai kawo a cikin parlour zuciyar ta , tana yi mata wani irin bugu kamar zata faso kirjin ta , ta fito... Wannan kenan... N.N.D.C QUARTER. ana idar da salla ya dawo afrah bata dena kuka ba tana ganin sa sai ta tawo gurin sa rungume ta yayi yana cewa hi shiru gani nan na dawo. shiru tayi ta kwanta a jikin sa , tana sauke ajiyar zuciya. HAJIYA tace '' ka samu wacce kake so ne ? .'' ɗago kan'sa yayi yace '' eh so nake na fadawa abba ya je ya tambayo min gidan su.'' ikon Allah a ina take daman iyayen ta basu san ka bane ko yaya naji kana maganar tambaya...?.'' Ajiyar zuciya ya sauke yace '' yar nan tudun bala ce so nake na fara neman izinin mahaifan ta.'' Hajiya jin jina kai tayi tace '' wane mahaifin ta ?.'' abinci ken da nayi ance min direba ne suna zaune a wani gida , gidan ma na haya ne amma ni duk ba shi ne damuwata ba yabon da ake mata shi ne abin da yafi min dad'i. HAJIYA tace '' kai kuwa saheer be ka gani a jikin yarinyar nan bafa naso ka auro dangin yunwa duk su ɗora maka nauyin da ba naka bane ci da shan iyayen ta ya zamo yana kan ka , kasan talakawa ne ke son mallake miji da yan uwan sa Gaskiya da zan faɗa maka ka dauka sam ba tayi min ba ni nayi zaton auren nan za ka yi na ƙwarya tabi ƙwarya sai kaje ka samo mana yar gidan malam shehu.'' jikin sa ne yayi sanyi, da zai iya faɗa mata da yayi mata bayani auren nan shine rufin asirin sa, zai toshe bakin alhaji nuhu ne musamman ma sharrin da yake kokarin yi mai sharri mafi munu duk da ya fitar da wannan labarin amma wannan maganar ta auren sa ta danne wannan yace '' Hajiya kamar dai yadda kika ce a farko kin amince dan Allah ki amince bana son abin da zan yi ya zamo ba da yardar ki ba.'' Buɗe baki tayi za tayi magana sai ga Alhaji Tahir yayi sallama hamdala tayi me taya ta yaƙi ya zo ta amsa mai sallamar sa tana gaishe da shi amsawa yayi yana zama. tace '' yauwa gwara da Allah ya kawo ka dan ka yau ya dauko mana abin da yafi karfin mu nan ta faɗa mai komai.'' Alhaji Tahir yace '' a'a ai ba wani abu bane Hajiya ki taya shi da addu'a kiyi mai fatan alkairi saheer yana da kudin da zai iya auren mace hudu har da kwarkwa'ra .'' shiru tayi ya ci gaba da cewa ni wallahi sam matar nan tasa ba tayi min ba , gwara ya auri yarinya kina ga tun da akai bikin nan ya dauke wa kowa ko ni da ina ganin ta a cikin gida na amma yanzu bata zuwa ita nunawa take a yanzu tafi karfin kowa kawai kiyi mai fatan alkairi sau da yawa abin da muke gani duhu ne ba haka bane haske ni talaka da me kuɗi duk ɗaya ne Hajiya. Ba yadda ta iya haka ta amince yace '' ni yanzu haryar ma zan yi sai na biya bani address din.'' HAJIYA tace '' da sauri haka?.'' to Hajiya shi da ba yaro ba , me kuma za a jira, HAJIYA tace '' haka ne.'' Saheer sosai yaji daɗin zuwan kahun nasa , bashi address yayi, baba jummai ta kawo mai abin motsa baki faruq zama yayi akan cinyar sa da yake mutum ne me son yara be damu ba. WANNAN KENAN. kwanon abincin ta hafsatu, ta dauka tana cewa ke umaimah uban wa yace ki zuba mata kamar haka yafi na kowa...?.'' nimrah ɗaga kan'ta tayi, ta kalle ta buɗe baki tayi, zata yi magana sai ta kalli malam da yake zaune jira take taga wanne mataki zai dauka sai taji yayi shiru. hmmm idan baku san wata ba to yanzu zaku gane Allah da girma yake ta faɗi haka a cikin zuciyar ta . tashi tayi, ta fara tafiya sai da taje dai-dai tabarmar da hafsatu take zaune ta zube ta sako wani irin ihu dukkan su tashi tsaye suka yi suna kallon ta. mimmiƙewa tayi tana cewa shi ne kuke takura mata kuna kuntatawa rayuwar ta akan kun ga bata da gata to mune gatan ta yau za mu toshewa kowa taka shi, shi kuwa malam mun dade muna tara shi yana gani ana hanata abinci amma baya magana saboda yana ganin ba shi bane ya nemo to yau za mu dauke shi mu kai shi duniyar mu, muhukunta shi dole mu hana yin bacci na tsawon shekara arba'in. salati malam ya saki lokacin da yaji tsassauran hukuncin da aljanun nimrah sukai mai. Hafsatu tace '' dan girman Allah kuyi hakuri ku sassauta min banyi zaton abin zai bata muku rai ba , yarinyar ce bata da kunya.'' Kan uba lallai yau zamu nuna miki ainihin mu suwa ye , kin ƙara laifi cikin laifi dole mu katsai miki jijiyar idon ki na tsawon shekara dari uku dole mu sakar miki gudawa.'' habawa hafsatu tana jin haka , cikin ta yayi wata iriyar murdawa dafa cikin ta , tayi ta fara matsar kwalla hawaye shar shar yana bin fuskar'ta tace '' dan girman Allah kiyi hakuri.'' Khuce nayi meri zandagi bayya mun gama dake au kai wuyan ka ya isa yanka baka iya bada hakuri ba ko? yau zaka fuskanci hukuba wallahi. Malam yace '' a'a kai na bisa wuya na kuyi hakuri jira nake ta gama sai ni nayi kar kuce nayi muku kutsai cikin lamarin ku ko kuce na nuna rashin girmama wa kuyi min afuwa.'' Umaimah tace '' malam Ayatul khursihu za kuyi mata sai su tafi.'' Yeeee huuuuuuu Yeee huuu dan bantan uban ki damu jiya aka sauke Kur'ani dole mu tsayar miki da bakiin ki a buɗe mu zubar miki da haƙora sai muga da abin da za kice ayi mana addu'a. fatima tace '' ni wallahi ba ruwana kuyi hakuri.'' wata uwar atishawa tayi sai kuma jikin ta ya saki , malam yace '' Alhamdulillah ku dauke ta , ku shigar da ita daki idan gobe tayi zan je gurin malam Liman, yayi mata rubutu ni daman gani nake nimrah kamar tana da aljanu .'' mama hawaye ta share tace '' na shiga uku malam gudawa fa Allah ka yaye min.'' Ke ba abin da suka isa suyi miki bara zana ce. nimrah da take kwace ta saki wata ƙara tace '' yanzu zamu aiwatar da shirin mu tun da kace baraza ce dole mu dauke ka.,, almajiri ne ya shigo yana sallama cikin tashin hankali fatima ta amsa mai tana ja baya almajirin nan yace '' wai ana sallama da malam.'' da sauri umaimah tace '' karka je malam wata kila sune , sukai basaja.'' malam bece komai ba ya fara tofawa nimrah duk addu'ar da tazo bakin sa , tashi tsaye yayi yace '' muje.'' fara tafiya yayi suka fita kofar gida sai da gaban sa ya fadi Saboda wata ƙatuwar mota da ya gani kasa ƙarasawa yayi ya tsaya yana addu'a domin ko tantama baya yi aljanun nan sune suka zo daukar sa to ayar Ubangiji tafi su..... yana tsaye yaga an buɗe murfin motar nan shi dai tsayuwa ya ci gaba da yi domin gani yake shikkenan ƙarshen sa ya zo.,, Assalamu alaikum. yaji sallama, amsawa yayi mutumin miƙa mai hannu yayi suka gaisa. Sannan yace '' idan ba damuwa ina so muyi magana da kai.'' kallon kayan jikin mutumin yake turkashi to shi da ba wani attajiri ba , balle yace yana da hadi da wannan attajirin da alama ma tukashi ake yi ,malam yace '' to ba damuwa Allah dai ya saka lafiya wallahi ni nan talaka ni kuma ba ruwana da , shiga sabgar wasu balle nace hadakar kudi ta haɗo ni da wani, murmushi Alhaji tahir yayi yace '' alkairi ne ke tafe dani ka kwantar da hankalin ka .'' malam yace '' to ina jin ka .'' domin shi har ga Allah, Allah Allah yake ya bar mai kofar gidan sa barin yanzu da duniyar nan bata da gaskiya sai a cutar dashi kuma ba yadda ya iya ba shi da ke rama mishi idan ba Ubangiji ba , kaf dangin su babu wani me sharararen kudin da zai daukar nauyin sa kowa takan sa yake. murmushi Alhaji tahir yayi yace '' okay ba damuwa na lura tsoro kake ji har yanzu hankalin ka be kwanta dani ba da farko dai sunana Alhaji tahir bashir nazo nemawa ɗana Alhaji saheer dalhat dauren yar ka , nimrah idan ba ayi mata miji ba .'' Ƙwaƙwalwar Malam Umaru ce ta tafi tunani da sauri ya ɗago yace '' saheer dalhat me Company manfetur ko wani ba wannan ba ?.'' Alhaji Tahir yace '' shi.,, Malam jinjina maganar sa yayi a gaskiya ba zai iya aurawa nimrah kamar saheer ba Saboda a komai ya fisu baya so tayi auren da ba kwanciyar hankali a cikin sa , irin su ma basa so talaka ya rabe su, to shi bashi da wannan son zuciyar a ina ma yaga nimrah anya kuwa daman ance masu kudi suna tsafi ko dai dodon tsafi su ne ya nuna musu NIMRAH duk da kowa yana yi mai kyakkyawan zato musamman ma temakon al'umma, malam Umaru yace '' kayi hakuri NIMRAH ba sa'ar auren sa bace kaga dai a yadda muke ba sai nayi maka bayani ba kai hakuri Allah ya basa dai-dai da shi itama Allah ya bata dai-dai da ita.'' turus Alhaji Tahir yayi mamaki ne ya kama shi daman akwai irin mutane nan har yanzu yace '' kayi dai tunani na baka nan da sati biyu kayi shawara.'' Hmmm Alhaji ke nan gaskiyar nan ɗaya da na faɗa maka ita ce sai dai ban san me Ubangiji zai yi a gaba amma ni in a ra'ayina ne babu chaji. Alhaji Tahir yace '' Allah ya zaba mana abin da yafi Zama alkairi. amin ya Allah yace. sallama yayi mai ya shiga motar sa shi kuma ya shiga gida jikin sa a sanyaye abin da yake fatan samu gashi ya samu amma yafi karfin sa. ganin NIMRAH yayi a zaune kamar ba ita bace ta gama aljanu yanzu.,, zama yayi hafsatu tace '' kaga an samu ta farfaɗo.'' dan Allah mama me nayi naga duk kuna kallo na Malam yace '' hmmmm nimrah kedai ki dinga addu'a Allah ya baki lafiya yau cewa kika yi za'a dauke ni duk irin soyayyar da take tsakanin mu.'' dariya ce ta kusan kubbuce mata ganin yadda malam ya koma abin tausayi tace ''dan Allah malam?.'' hmmm kedai idan ana cin ɓaure ba'a tone tone. kwanciya tayi tana cewa mama akwai abinci kuwa ...? mama da sauri tace '' eh sauran nawa umaimai dauko mata , taci.,, NIMRAH tace '' a'a mama ci naki bazan ci ba .'' NIMRAH ba komai ki ci ai ba wai koshi kikai ba. Ke dan uban'ki, ba zaki je ki dauko mata ba.'' to ta faɗa tana tashi zuwa tayi ta dauko mata amsa tayi

Chapter 3 of 6