Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
take yi ba ta ita ba. Saheer mamaki ne ya kama shi i gaskiya dole ya te'maki yarinyar nan baya so yaga rayuwar kananan yara ta gurɓata yanzu ace wani ta haɗu dashi ba shi ba yake nan ajiyar zuciya ya sauke yace '' ina ne gidan ku?.'' da sauri nimrah ta goge hawaye tace '' aikin rainon yaran ma sai na nuna maka gidan mu?.'' Saheer haɗe rai yayi yace '' tambayar ki nake kina tambaya ta.'' Nutsuwa tayi domin a kalla tasan babban mutum ne zai iya yin malam mahaifinta tace '' dan Allah karka kai karata gurin malam.'' wayar sace , tayi ringing kallon screen din wayar yayi sunan hidaya ne ya fara yawo a screen din wayar dauka yayi ya ƙara a kunne bece komai ba. daga can ɓangaren hidaya tace '' har yanzu fa baka turo ba naji shiru ? kasan karshen wata yayi to na zuba ido ban ga alert ba.'' rintsai ido yayi besan wacce irin mace ya aura ba kudi shi ne gaba da komai a rayuwar ta , duk kwanan da take a cikin gidan nan kwanan kudi take kamar ba matar saba ba ƙaramin mamaki yayi ba da har ta iya bugo mai duk da Irin abin da tayi mai , ya samu wani magani ne to yana ganin kamar an dace ya fara samun lafiya da yaje gare ta kin yarda tayi dashi ta nuna mai sam ita bata yarda ita bata shirya yi ba. Allah sarki A'isha Ubangiji Allah ya jikan ki haka ya raya wannan a cikin zuciyar sa afili kuwa sai yace '' okay.'' kashe wayar sa yayi a lokacin ya tura mata kudin ta ya ajiye wayar yana cewa ina jin ki. Nimrah da ta , tafi tunani da sauri tace '' Ni?.'' wani kallo yayi mata da sauri tayi ƙasa da kan'ta tace '' a unguwar tudun bala nake nan kusa da taransifoma biyar kana zuwa idan kace a kai ka gidan su nimrah yar boko za'a kawo ka gidan mu.'' ajiyar zuciya ya sauke yace '' okay zaki iya tafiya.'' tashi tayi tace '' to ka dauke ni aikin ne gobe nazo? amma bani da kudin mota.'' ciro kudi yayi ya ajiye mata dubu biyar yace '' karki zo.'' dauka tayi ta dauki dubu biyu ta ajiye tace '' sun yi min yawa wannan ma me napep zan bawa idan be yi fushi ba ya tafi wannan sai na koma gida.'' Saheer haɗe rai yayi yace '' dauke .'' a'a ta faɗa tana girgiza kan'ta bata kula ba ta buge da kujera da sauri Saheer ya taso ya riƙe ta ganin tana shirin kifawa kasa dai-dai lokacin kuma aka turo kofar dukkan su kallon kofar suka yi wanda ya shigo babban mutum ne sai ya fara tafi yana cewa Saheer daman abin da kake kenan? .'' da sauri nimrah ta ja baya ta kalli mutumin kwata kwata tunanin ta da ƙwaƙwalwar ta be kawo mata komai ba. Saheer yace '' Alhaji Nuhu kar ka yi kokarin danganta ni da kalmar da hat abada kasan bazan taɓa aika abin da kake zargi ba.'' Alhaji Nuhu bece komai ba ya saki wani malalacin murmushi ya fita. Saheer kallon nimrah yayi yace '' daman aiko ki aka yi ko domin ki bata min suna?.'' a'a wallahi ban san sa ba ta faɗa tana ja baya ganin yadda ya koma mata. Saheer cikin ɓacin rai ya wullo mata , takardun ta suka tarwatsai anan yace '' ki fitar min daga office tun kafin na balla ki.'' ko tsayawa daukan takardun ta ba , tayi ba ta fita da sauri tana share hawaye , sosai jikin ta yake rawa. ganin kamar security din wajen suna kallon ta da gudu ta fita tana ganin me napep ɗin nan ta shiga jikin ta yana rawa tace '' dan girman Allah mu barnan kar su kama ni.' Za kici kuttumar uban ki fito min da kudina fitar min daga mashin ai ke basan yar akuya bace wallahi ko wani na gani zai temake ki sai na hana shi. dan girman Allah kai hakuri ga wannan nan mu tafi. ta faɗa tana bashi kuɗin hannun ta. karɓa yayi ya duba ya tura a aljihu yace '' a bakin titi zan ajiye ki.'' to, ta faɗa tana share hawayen ta. A bangaren Saheer kuwa rasa ina zai saka kan'sa yayi ɓacin rai ya hana shi sakat, sadam ne ya shigo da yake ya aika a kirawo shi yace '' kasan yarinyar nan...?.'' zama yayi yana cewa wallahi ban santa ba ni da farko na zata mahaukaciya ce lokacin da zamu shigo Company nan da Mahmud muka gan'ta da zan mata magana sai Mahmud ya hanani saboda mun gansu ita sa wani namiji ya biyo ta , yana zage zage. wani irin sarawa kan Saheer yayi yace '' aiko ta aka yi.'' da sauri sadam yace '' oga wa'zai aiko ta?'' yanzu baka ga alhaji nuhu ya zo ba ? waya faɗa mai na dawo kasar nan ? ko yan jarida basu sani ba cikin dare na dawo ko hidaya bata san da dawowa ta ba sai yau da safe ta ganni motar da na fita da ita, taka ce abin da ya ban mamaki beyi sallama ba ya shigo min office kuma ya akai yasan ina wannan office ɗin? cije lips ɗin'sa yayi ya ci gaba da bashi labarin yadda abin ya faru. kan sadam ne ya kulle yace '' gaskiya biri yayi kama da mutum, me ya saka tun farko ba mu dauki wani action ba, oga ga wata shawara.'' kai ya gyara mai alamar yana jin sa. Sadam ne damu ba saboda ya saba da haka yace '' me zai hana kafin ya ɓata maka suna saboda banzan dalilin sa na son ku haɗa hannu ku gallazawa al'umma dole sai price din ku ya zo daya ka dinga kawo kaya mara inganci da yayi maka sharrin kana shigo da hodar ibilis a wannan karon sai ka toshe bakin sa , ka auri yarinyar nan ta haka za ka gano dukkan wata makarkashi da suke kullawa kasan zargin da muke yi motar ta sa kahau kai da Allah ya jikan rai bula maka tankin motar aka yi mai yake zuba a hankali har kai wannan hatsarin Allah ne yayi da kwanan ka a gaba da tuni ka mutu.'' sadam aure fa kace me zanyi da sa'ar autar mu wannan na tabbata ko ihsan ta girme ta baka ganin hakan abin kunya ne kamata na auri wannan yarinyar baka ganin za'a dinga maganganu...?'' gyara zama sadam yayi yace '' da ace kana neman yar cikin ka da ace ka auri yar cikin ka , wanne yafi wani muni ? aure ne , na dan wani lokaci kafin komai ya dai-dai ta , ka sake ta yanzu tun kafin ya , yaɗa wannan labarin nasan tun da ya fita to akwai abin da hakan yake nufi kayi maza ka dauki blogger's su fara rubutu suna cewa ana rade radin zaka ƙara aure, hakan zai dauki hankalin al'umma wasu ma suce ai kayi kaga bashi da hanyar fito da wannan maganar ita kuma yarinyar gurin iyayen ta zamu ayi komai a gama nasan Hajiya za ta iya nuna rashin amincewar'ta tun da tana kaunar Hajiya hidaya ka kwantar da hankalin ka a hankali ka fahimtar da ita.'' ajiyar zuciya ya sauke yace '' sadam na barma ka komai a hannun ka .'' inshallahu zan yi komai yadda muka tsara inshallahu haka komai zai tafi. Saheer yace '' Allah ya yarda.'' amin ya Allah yace yana fita. Wannan kenan. tun da suka fara tafiya sai hankalin ta ya dawo jikin ta, tunowa tayi da takardun ta ɗora hannu aka tayi ta zunduma ihu. da sauri me mashin ya juyo yana cewa lafiya..?.'' nimrah tace "' takarduna wallahi na baro su acan gashi ban san yadda za a yi na ƙara samun su ba shikkenan ba zan zama ma'aikaciya ba burina ba zai cika gaba.,, a fusace matashin nan yace '' kuttumar uban ki haka kurum ki zunduma min ihu to sauka..?.'' nimrah tace '' bamu zo ba fa.'' wallahi sai kin sauka. parking yayi, ta fita jikin ta yana rawa, baki daya bata cikin nutsuwar'ta haka take tafiya har ta ƙarasa kofar gidan su, shiga tayi tana cire mayafin ta , ta rataye a kafaɗa cikin Sa'a ta , tarar hafsatu, ta ajiye abincin ta fara da mai yaji salak da tumatur har da kokomba da sauri ta dauki buta ta wanke hannun ta , ta zauna ta fara ci cikin kwanciyar hankali. Kan uba kin ajiye ne kike cimin abinci na . Fatima kanwar, ta faɗa tana kallon ta . Nimrah tace '' idan kin isa zo ki kwata wallahi ki ga yadda ake soya fuskar mutum sai na dilmiya fuskar ki a cikin wutar nan.,, To yar ta'adda kin dawo na sha faɗa miki ba ruwan ki da ya'ya na amma kin ki ji duk ranar da kika sake na kama ki wallahi Allah na lahira sai yafi jin dad'i shegiya zaki ci uban ki ne indai ina raye bake ba ganin ci gaba a rayuwar ki.'' wallahi Allah ke baki isa ki yi min abin da Ubangiji be min ba. wata dariya hafsatu tayi. Nimrah ci gaba da cin abincin ta , tayi cikin kwanciyar hankali aikuwa hafsatu kamar ta ari baki haka ta dinga faɗa ta inda take shiga ba tanan take fita ba. nimrah gama ci tayi ta , tashi ta wanke hannun ta, ta saki gatsa tace '' to yanzu tun da cikina ya dauka sai na tafi nayi sallah na kwanta kafin yamma tayi naga ina kuma zan nufa .'' Malam ne ya shigo yana cewa sai da kika fita kenan?.'' juyowa tayi tace '' wallahi Allah neman aiki na fita malam na gaji da suyar awaran nan , kullum ina gaban kasƙon suya kuma har yau kudin jarabawar tawa yaki haduwa , to har yanzu ban samu ba yau ma da naje wani Company wallahi dakyar na fito saita ni sukai da bindiga , dariya fatima da hafsatu, suka saka. nimrah bin su tayi da kallo ta share kwalla tana kaunar tayi karatu me zurfi amma abin yaci tura kullum idan ta nemo ci suke yi malam direba ne to a yanzu yafi shekara uku bashi da mota sai dai ya karɓi haya yaje ya dan nemi na abinci kwana biyu ma abin yaci tura baya samun motar hayar shi ya saka lamarin gidan ya ƙara tabarbarewa. Malam yace '' nimrah yawon nan da kike yi duk bashi bane mafita, ke yanzu kin gwammace adin ga nuna ki da baki? Sa'anin ki wasu na dakin mijin su wasu wata me kamawa bikin su wasu sun haihuwa, amma ke babu lissafin aure a gaban ki.,, Nimrah tace '' malam kenan abin da ba sauri nake na ni wallahi rayuwar talauci ce bana so bawai samarin ne ba ni da su ba ka naga yar kazar nan ma cinta gagarar yake yi a cikin gidan nan idan na auri talaka haka rayuwar zata dinga tafiya kai dai kai addu'a Allah ya kawo na gari.'' girgiza kai yayi duk sanda yayi mata wannan maganar, wannan lissafin take mai bata san wani kudin ba hatsari ne a wani gidan me kudin ga kudin nan amma ba kwanciyar hankali.'' nimrah daukan buta, tayi, ta shiga bayan gida. Fatima tace '' wallahi Allah mama nimrah tana abin da ta ga dama gashi malam baya son yi mata fada.'' Uban'ki zai min bayan wanda ya yi min okay wallahi i well slap you now now stupid daman ba tun yau ba nasan ke cream (criminal) ce wallahi.'' Fatima tace '' aikin kawai daga anyi magana sai ki dinga yiwa mutane turanci Allah ya saka ma dai-dai kike yi yanzu da wasu malaman Turanci za su ji cewa za su yi kina yiwa Turanci fyade wallahi sai sun hukunta ki.'' hhhhh in fitsari banza ne kaza tayi mu gani yau da naje gurin neman aikin nan suna yi min na fara yi musu tsuru tsuru suka yi da wani ya kawo min maganar banza nace shut up gerewe (get way) tuni kowa ya kama kan'sa Ni nan wallahi ko queen Elizabeth karya take ya nuna min turanc balle ke kina tundun dan bala tantagaryar talaka. Yauwa mama dan Allah an buɗe wata makaranta nan bayan mu ta yaki da jahilci ki daure ki shiga kema ki dinga turo dauri gaban goshi kina riƙe book a hannun ki. Nimrah idan kina haukan ki karki ƙara saka ni a ciki cewar hafsatu. Nimrah tace '' hmmm mama kenan to nidai ina tunanin film zan shiga saboda abin mamaki lokaci ɗaya mutum yake shiga yake arziki sai ki ganni da ƙatuwar mota ana yimin jiniya.'' kaf cikin su ba wanda ya kula ta har ta idar da alwalar ta , ta shiga daki shinfida da'duma tayi, ta tada sallah. wannan kenan. Baby badai tafiya za kiyi ba cewar Hidaya. amrah zama tayi, tana shafa maman Hidaya da yake shimi ce a jikin ta. wata malalaciyar kara ta saki tana gantsarewa tace '' gaskiya ke ta dabam ce.'' murmushi tayi tace '' hajiya ta.'' riƙe hannun ta , tayi tace '' tun da nake wannan harkar ban taɓa haduwa da wacce tasan sirrin gigita mace sama dake ba .'' haɗe baƙin su amrah tayi tana aika mata da wani mugun wasa. a hankali ta saki bakin hidaya, Hidaya girgiza kai tayi tace '' Please kar ki tafi.'' Amrah tace '' gaskiya Hajiya tafiya zanyi ai na faɗa miki dakyar aka bar ni, na kwana karya nayi a gidan mu.'' limshe ido Hidaya tayi tace '' okay amma zanyi missing din ki wallahi.'' Nima haka mommy na komai naki me kyau ne , amma kin haɗu da miji dutsai baya more wa dad'i. Dariya Hidaya tayi tace '' dazu ya fita yana wani kumbure kumbure kallon inda yake ban yi ba wallahi ni fa ATM na mayar da saheer lokacin da nake tsananin bukata na nemo shi ya biya min baka ta, ta wai yana ganin ya samu lafiya yana ai.....tun kafin ya karasa na gane ina zancen sa ya dosa nuna mai nayi sam ni ban san zancen ba komai sa an shirya ake yin sa , amma ni yanzu bani da time din da zan bude mai ya shiga.'' Amrah tace '' Allah sarki Allah Hajiya ki dena yi mai haka kar wata ran reshe ya juye ga mujiya nima wannan abin da kike gani wallahi dole ta saka ni yi da kuma ƙaddara.'' ZAMAN KAN'TA TAKE EPISODE 3 Hidaya tace '' hmmmm ba zaki fahimta ba ke yarinya ce .'' murmushi tayi, ta , tashi rataya jaka tayi rungume Hidaya ta ƙara yi ta yi mata kiss a gefen kumatun ta , tace '' bye.'' ta kara she maganar tana sakin ta tare da , daga mata hannu. Hidaya hannu ta daga mata tace '' bye , fita tayi tana murmushi Hidaya zama ta gyara wayar ta, ta dauka ta kunna datar ta messages ɗin Whatsapp ne suka ɗinga shigowa musamman ma na group din su na matan manya shiga tayi ganin message din yayi yawa da alama an saki sabon update ne. a hankali ta fara bin hirar su murmushi tayi ta buɗe DP din wacce taji tayi wani voice to voice din ya dauki hankalin ta musamman ma muryar ta , sai ta haifar mata da wata kalasa babu picture din'ta sai picture din kyakkyawar kafa anyi mata kunshin nan na yan sudan ga sarkar kafa sosai ta shagala da kallon kafar to ina ga ta'ga me kafar . shiga ciki tayi kamar za tayi mata magana sai ta fasa, domin bata son disgi da girman ta , tana matar babban mutum kamar Saheer ta tsaya wata mace na hulakan'ta ta.. contact din admin din group din ta shiga ta fara yi mata voice tana cewa hy bestie yakike ya harkoki am naga wata so ban san ko new comer bace Please connect me with her urgently Amrah has left, and I really need this as soon as possible ... tura mata , tayi ta she datar ta ganin bata online. tashi tayi ta fara tafiya , handle din kofar dakin ta , ta murɗa ta shiga wayar tace tayi ringing ganin sunan kanwar ta da sauri ta dauka tana cewa sai yau kika tuna dani. ta faɗa tana murmushi. daga can bangaren samha tace '' aunty kin san me yake faruwa kuwa? mommy ce tace sai na buga miki waya baki sanar da ita ba , wai mijin ki yayi aure labari ya karade social media ga wani picture dai babu fuskar matar sai dai bayan ta amma shi dai wallahi Allah ba Al bane shi ne zance dai kala kala wasu sunce karuwar sa ce ko fa minti talatin ba ayi ba da ɗora labarin amma ke kin ga uban liking da comments.'' Hidaya , tace '' aure fa kika ce ? hhhh wallahi karya ne, ni kai na be iya dani ba ɓalle yake ya dauko wata kin ga , ku kwantar da hankalin ku, saheer ba zai taɓa yin aure ba.'' Samha tace '' aunty bafa a shedar na miji.'' zama Hidaya tayi ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya daukan lemo tayi ta sha ta ajiye ta saki wata uwar gyatsa tace '' nasan saheer sarai tun kafin na shigo cikin wannan gidan na gama karantar halin sa , bashi da burin aure aure mace ɗaya ta ishe shi tun kafin A'isha ta haihu be karo mata kishiya ba haka yayi hakuri har Allah ya basu da ta mutu ya dade be yi aure ba sannan ya aure ni abu biyu zuwa uku saheer ya saka a gaba ci gaban kasuwancin sa mahaifiyar sa ya'yan sa da yan uwan sa , Saheer wallahi ba irin mazan da kika sani bane yana da hakuri da kawaici amma baya daukar raini, ko ni da kika ga ina abin da nake so to akwai wani sirri a tsakanin mu.''' dan Allah aunty faɗa min na dinga yiwa abban eman shi kinsan fa wallahi ba tun yau na san yana bin mata ba kawai hakuri nake , nake zaune dashi Allah aunty samin irin mijin ki sai an tona. Hidaya tace '' hmmm ke Allah dai ya kyauta amma kusan haka maza suke ko ni nasha kama abbas da mace .'' ai gashi nan duk da ya sake ki, kin yi wani auren baki rabu da shi ba. Cewar samha. Hidaya tace '' ke sai da haka wannan rayuwar badai da aure na ba kuma ni yanzu wallahi na fi karfin namiji ya raina ni shima ai yasan wacce ni shiya saka har yanzu yaƙi rabuwa dani shekaran jiya, matar da kira na ,tayi tana kuka tana zagina wai idan na cika cikakkiyar mace na bari miji na ya sani ita bata ga amfanin auren da nayi ba nace sai naci abu takazar uban'ta , idan ta sake na fito to wallahi Allah zaman ta da abbas ya ƙare.'' Aunty kenan , me ya saka kike haka ni wallahi Allah ban ga amfanin wannan abin ba. Hidaya tace '' ke yarinya ce , wallahi baki san me duniya take ciki ba , zuwa gidan ki kayi ne ?.'' Samha tace '' a'a yaji nayi.'' Ikon Allah yaji kuma me ya faru...?.'' cewar hidaya. Samha tace '' aunty ki wacce mace ya gani yace yana so ni wallahi gwara ko aure ne yayi nasan aure yayi jiya kama shi nayi shi da budurwar sa akan gado na me yafi wannan muni shine na dake ta na yi fashe fashe a cikin gidan na fito.'' Ikon Allah to me mommy tace ...?.'' Samha tace '' wai muje gurin malami ni kuma nace a'a idan dai ba sakawa za tayi ayi min saukar Alqur'ani ba , bazan je gurin mashiriki ba , cewa fa suke yi kayi kaza kayi kaza abu mafi muni suce ka dauki period din ka , ka yiwa mutum abinci gaskiya ni bazan iya ba na kwanaki da muka je cewa yayi sai ya kwanta dani nace sam ban yarda ba da aure na haka kurum.'' Kuttumar uban ki da hallacan kashe min waya kaga shegiyar yarinya dan uban ki mu abanza muke juya mazajen namu da kika ga ba yadda suka iya damu ina cewa saki na da abbas yayi sai da ya kusan hauka..'' tana gama fadar haka ta kashe wayar ta , tana jan tsaki kiran bestie ne ya shigo wayar ta , da sauri ta daga tana cewa hajiyan yan air kwana biyu..?.'' Bestie women leader tace '' uwar gida kuma amarya yau jarabar ce ta motsa...?.'' dariya hidaya tayi tace '' tun da naga kiran ki nasan sakona ya je miki to ya an samu ne ?.'' bestie tace '' no ni ban ma gane wa kike nufi ba mene user name din'ta..?.''' Hidaya tace '' pretty.'' oh tab wallahi wannan da kike gani yarinyar hajjo ce kuma bata ma kasar nan tana america. dafa kan'ta Hidaya tayi tace '' innalillahi wallahi kin ga prevent din'na har tsiyaya yake yi gaba ki ɗaya na kasa samun nutsuwa tun ɗazu ki haɗa ni da ita ko Muryar ta naji muyi hira.'' dariya women leader tayi tace '' okay yanzu dai bata online idan na ta hau sai muyi magana amma mene lada na..?.'' Baki da dama zan tura miki wani abu ta account din ki. Bestie tace '' godiya nake ranki ya dade .'' dariya tayi tana yi mata sallama, kashe wayar tayi ta ajiye kome ta tuna da sauri ta dauki wayar ta , ta kunna data shiga Instagram tabe baki tayi ganin maganar kara auren saheer ake yi wasu har cewa suke sun san amaryar sai canki canka suke yi dariya abin ya bata kashe datar ta , tayi tana cewa aikin banza ba ku san dutsai bane da baku tsaya kuna ɓatawa kanku lokaci ba. shiga toilet tayi ta cire rigar ta kunna shower tayi tuni ruwan ya fara ratsa tsakiyar kan'ta. limshe idon'ta, tayi tana sakin dariya abinda ya saka ta dariya shi ne , wai saheer da aure tab Lallai akwai kallo to a ina zai saka ta yana dutsai bashi da amfani fa marabar sa da shi da babu duk ɗaya. Wannan kenan. kan uba lafiya kika tsaya min akai na ?.'' Kinga gaskiya ni nagaji uwani fito min da kudina ni na fasa adashin nan bani kudi na tun da bana ubale bane. UWANI tace '' nimrah ni kike fadawa haka? to kudin ki na cinye bazan biya ba.'' wata uwar dariya ta saki tace '' kan uban can amma dai gaskiya baki da hankali yau zan nuna miki wace ce ni haka kurum kin cin yemin kudina to wallahi Allah yanzu nan zan dauki kayan kudina mu haɗu a police station.'' ta faɗa tana surar akuyar ta , salati uwani ta saki tana cewa nimrah ashe baki da hankali akan dubu goma zaki daukar min akuyar dubu talatin sauke min ita sauke min wallahi ko naci uban ki. Nimrah tace '' idan kin isa ki biyo ni wallahi Allah sai na tara miki mutane ashe ba dad'i ki bani kudina na sauke akuya idan baki bani ba wallahi Allah daga nan sai gurin me dabba ina zuwa bakin kasuwa magana ta ƙare cas zai cake min kudina ya bani.'' salati ta saki tace '' ke anya kuwa ina da hankali..?.'' NIMRAH tace '' asibitin mahaukata ne akai na.'' Wallahi Allah baki gado halin uwarki ba nazifa mutuniyar kirki Owo dai ta faɗa tana fita da sauri uwani ta dauki mayafin'ta da yake kan igiya ta bita a guje nimrah gudu ta saka akuya sao ihu take . haba baiwar Allah kamar ba matar aure ba kina bin wannan yarinyar me yayi zafi cewar wata mata da tazo shigewa. tuff tuff aniyar kowa ta bishi ina ruwan ki dani da nake cewa ki riƙe min ita ai baki, riƙe min ita ba. Cewar uwani. Matar bata kula ta ba , tayi gaba , abin'ta. NIMRAH a sosai take gudu da akuya ganin tayi wa uwani nisa sai ta saita tafiyar ta , da sauri uwani ta ƙara so inda take tana ganin haka sai ta kuma kwasa wani irin ihu akuya ta saki itama cin birki tayi amma ina sai da motar nan tayi gaba da ita akuya kuma tayi tsalle ta fita a guje tana zabga uban ihuuuuuuu. UWANI tana ganin haka tabi akuyar ta , gana cewa ai gashi nan da yake banj da hakki a akan ki Ubangiji ya kama ki. NIMRAH kuwa kuka ta dinga yi wani Irin rauni taji a kafar ta ji take kamar bata taɓa jin dad'i ba , a duniyar nan. me motar fitowa yayi yana cewa ai wannan hauka ne ki biyo kan titi kina

Chapter 2 of 6