ta tashi tsaye ita ma ta dauke ta da mari ko da
Hajiya ta ji saukar mari sai ta rike kunci, abin ya bawa
Jamila mamaki sosai, lokacin Fiddausi ta kwacewa Hajiya
zani da mayafin daek jikinta, Allah ya sa dai Hajiya akwai
siket a jikinta. Fiddau si ba ta tsaya a nan ba, sai ta hankade
Jamila ta je ta bugu da kujera ta fasa goshi, a lokacin Jamila
ta soma kuka. Amma Hajiya ta kasa y in k omai ga shi yau
ma Abba baya nan, kuma ga shi yanzu ta fi karfinta, a
lokacin Fiddausi ta dakawa Jamila tsawa ta ce m aza ki hada
min hita a bokiti zan yi wanka Jamila ta mike jini na diga ta
sa ruwa ta wanke sannan ta hadawa Fiddausi ruwan, bayar
nan Fiddausi ta waiga ta ce da Hajiya ke kuma maza ki je ki
32
kawo min abinci nan ta tashi ba ko musu ta tafi ta kawo wa Fidduai abinci Kuma dama abincin shi ya rage kawai. Nan Fiddausi ta ce ke Jamila dauki ruwan ki kai min bandaki, nan ko musu babu ta kai mata, to Fiddausi ita dama ba don babu ruwan zafin ba ne kawai dai don ta rama irin mu guntar da ake yi mata ne, kuma ta ce kada wanda ya ssoma cin sauran abincin nan. Sai a shiga wanka, bayan shigarta ba ta juma ba, sai ga Jamilu ya yi sallama yana shigowa koda ya hau sama
sai Hajiya ta soma fada masa abin da Fiddausi ta yi musu
Jamilu ya ce Fiddausin? Hajiya ta ce E" ran Jamilu ya baci
ya ce yau ma sake dawowa ta yi a lokacin Jamilu ya ce yanzu
tana ina Gaji ta ce tana bandaki tana wanka. Ya ce ina bulala,
Hajiya ta bashi, ya tafi yana jiran fitowarta. Fiddausi sai ta
fito su Hajiya suka bita da kallo Fiddausi ta shiga dakin
mahifiyarta tana shiga sai su kai arba da Jamilu a falo sai ta
huce shi ko kallonsa ba ta yi ba sai kawai ya dau bulala wai
zai doki Fiddausi, koda ta ga haka sai ta rike daga hannu
Jamilu sannan ta fisge abin ka da ragowar AIDS' sai nan da
nan bulala ta dawo hannun Fi ddausi, koda ta zo hannunta sai
ta dunga tsalalawa jamilu, tana cewa da kenan, amma yanzu
na huce nan. Domin wu tsiyar rakumi ta yi nesa da kasa
Yayin da ta ci gaba da dukansa, lokacin Hajiya da Jamila sai
mu rma suke ba su san reshe ne ya juye da mu jiya ba don su
a zatonsu Fiddusi ake `KILA" lokacin su ka shigo dakin
baki daya koda su ka shigo sai su ka shiga dakin baki daya
koda suka shigo sai suka tarar duk bayan Jamilu ya farfashe,
kuma gashi nan a kwance. hajiya ta rike baki tana mamaki,
nan dai ta dunga bawa Fiddausi hakuri amma ina Fiddausi ta
ci gaba da tsalala mar, bayan Jamilu ya sami dama sai ya fice
a guje. Suma su Hajiya suka arta a guje sukai waje bayan da
suka fita Hajiya ta ce yau mun shiga uku, yau ya ya za mu yi
da wannan shegiyar yarinyar, ni ban san wanda ya koya
mata wannan rashin kunyarba. lalle bahaushe ya yi gaskiya
33
da ya ce komai ya yi farko ya yi karshe, to mu dai karshen
mu ya zo kenan don na san ko Alhaji ba zai iyawa Fiddausi
ba. Ni dai idan ya dawo sai in ce mu tashi, do min idan muka
zauna to kashe mu za ta yi. Don haka idan dai ya sami kudin
da ya je karbowa shike nan, don na ga ta fitsare sosai. Haka
Gaji tai ta y in surutu ba ji ba gani, haka su ka kasance cikin
wahala da bakin cikin Fiddausi lokacin da su ke azabtar da
ita ai babu wanda yake jin tau sayinta, amma yanzu sa
tausayawa kansu gashi ma suna neman mafita. Koda gari ya
waye sai Fiddausi ta sa su aikin gida a wannan lokaci duk
cikinsu babu wanda ya yi mu su domin yanzu tsoron ta suke
sosai, haka su ka wanka gidan ta sa suka share shi tas! Suka
goge leda, sannan inda kafet yake su ka kadae shi fes, haka
Diddausi ta yi ta sa su aiki iri-iri. Gaji da 'yarta jamila abin
du niya ya yi musu zafi, su kawai so su ke Alhaji Abba ya
dawo ko ya yi musu maganin Fiddausi. Shi kuwa Jamilu tu n
lokacin da Fiddausi ta zane shi ya kwanta rashin lafiya
zaza!6i, ciwon kai, kumallo tare da gu dawa. Hajiya tana son
ta kai Jamilu Asibiti, amma-saboda Fiddausi ta kasa domin
Fiddau si ba-za ta bari ba. Du niya kenan wai yazu Hajiya се
ke tsoron Fiddausi, dama masu iya magana su n ce abin da
ya baka tsoro wata rana shi zai baka tausayi, dama can Jamila
na shakkar yarinyar da su ka rainawa wayo, kuma suka wu
lakanta. Kuma ba su taba zaton haka za ta faru a gare su ba.
Bayan da aka sami mako daya da tafiyar Alhaji Abba,
kwanakin Fiddausi kenan a gidan, har Hajiya Gaji ta soma
rama saboda rashin kwanciyar hankai da tsabar aiki, а
wannan lokaci Jamila ta fahimci cewar Fiddausi ba ta da
niyyar barin gidan, sai ta ce Hajiya ni fa zan hada kayana na
bar gi dan, koda Gaji ta ji haka sai ta ce to yanzu Jamila ni ba
kya tausayina haka za ki tafi ki bar ni, wato ko mutuwa zan
yi haka za ki min. Gaji t asoma hawaye, suna cikin haka sai
kwatsam ga Abba ya dawo, ya yi sallama koda Gaji ta je sai
34
ta share hawayenta ta ce Allah na gde ma da ka dawo min da
Abba, kun ji fa sai yau Hajiya ta tuna da Allah Hajiya ta
leko, sai ta ga Abba rai bace ta ce wai mun shiga uku nan ma
ai wani bakin cikin ka taras 'Abba ya hau sama, Hajiya da
Jamila su ka bi shi su ka yi masa barka da zuwa ya amsa da
kyar, Gaji ta ce yà ya me yake damunka, abba ya ce ai
wahalar banza na sha domin asarar kudın tikiti na yi, don ban
sam komai ba, amma ban sami ba ko alhaji Hamisu ne ya yi
waya ya ce kada a bani. Ko kuma watakila Fiddausi ce ba ta
sa hannu dai-dai ba domin yanzu ta zama tatacciyar 'ya kuma
za ta hadu da ni bayan ya huta, sai Hajiya ta kawo masa
ruwa kawai, koda ya ga haka ya ce to ina abincin, Hajiya ta
ce ai Fiddausi ta hana a yi, kuma wallahi ta matsa mana
sosai, dama ni so nake ka dawo mu bar gidan don har.
dukana ta yi yanzu ga Jamilu can a kwance ta hana akaishi
asibiti,don shi ma duka ne ya kwantar da shi ni dai kam ka
san matakin da za ka dauka akan Fiddausi don kuwa tą
takura mana. Sosai, Abba ya ce to yanzu ta tafi, Gaji ta ce
tananan ba ta da ranar tafiya balle ma mu huta. Nan dai
Gaji ta kwashe labari ta sanar da Abba. Ya yi mutukar
bakin ciki ya zamar masa biyu. Yaje AMURKA kudi babu,
ga kuma abinda Fiddausi ta shuka a gidan. nan ya fusata ya
mike ya ce ian bullar nan har yaushe ta isa, ni ba ta isa ta yi
min iskancin ba. Ina bulalar nan Hajiya ta ce ga ta, kuma
baka ga jikin Jamilu ba, nan ya karba ya hau sama. Ya huce
dakin da Jamilu yake kwance, Abba ya ce sannu Jamilu, a
lokacin Jamilu duk ya rame ya soma kanjamewa. Dama ai
Kanjamau ce ta kama shi don haka sai na ce Jamilu sai mun
taho. Lokacin da Abba ya gama duba dansa, sai ya huce
inda Fiddausi take, koda ya shiga ta ganshi amma ko
magana ba ta yi masa ba. Abba wani ta kaici ya sake kama
shi yayin da ya kai mata duka sai Fiddausi ta rike bulalar
kamar yadda ta yi wa Jamilu, ta, fisge daga hannun Abba
35
sai da ya yi laryin faduwa, ta ce da kenan! Ka dake ni ka
aki banza. Amma yanzu na huce haka a gurinku baki
ya, Fiddausi ta dunga tsalalawa Abba bulala ba ji ba
gani, da ya ga ba dama sai ya fito da gudu ba shıri. Ya yi
kasa, dama Jamila da Gaji ba su bi shi ba don şun san da
kyar zai yi nasara a kan Fiddausi, ko da suka ga Abba da
gudu riga duk a yayyage sai suka ce gaba daya yau mun
shiga uku, Abba ma ta gagare shi to waye zai yi maganinta
kemaGaji ta ce wayyo! Ga shi Alhaji duk ya sayar da
kadarorinsa ga shi gidansa ya bawa su GIZAGO da sai mu
koma can muhuta da wannan bala'i. Haka dai Alhaji ya
sauko ba shiri.
Bayan kwana biyu' da yin haka Fiddausi ta sa su aiki
sai Jamila ta yanke a hannunta jini yana zuba, a lokacin ta
rasa yadda zata yi, da Fiddausi ta ga ba ta aiki sai ta daka
matsa tsawa. Jamila ta nunamata sai tace ci gaba ai zai
tsanene, Jamila sai hawaye ne ke zubo mata har suka gama.
Bayan da suka gama sai ta ce su share yana ta ce kuną
ganin duk gidan yayi yana, to ku share. Da zama za ku yi ai
zama bai same ku ba, bayan sun gama sai Fiddausi ta ce ga
kwakinan ku jika ku ce. don dama kai Abba sunanka
(АВВА ЛКО) don daga yanzu sai ka fi kowa iyama'amala
da kwaki. Haka nan suka dau kwaki suka jika ba ko sukari
suka ci. Bayan gari yawaye jamila ta debe kayanta ta yi
gaba. Dama ta kware a wajen iya iskanci, amma ita
Fiddausi bat san ta gudu ba. Koda Abbada Gaji suka ga
haka sai suka yanke shawarar abin da za su yi kan Fiddausi.
Gaji ta ce ko gidan Hayane mu koma amma yaya zamu
yadda yarinya take ci mana mutunci ni ba abin na ce ka je
gidan su Hajiya ba, sun san gidan ta ne, kai ka ji fa ashe
wuya ba dadi
Lamarin. GIZAGO da yake hannun 'yan sanda to
yanzu dai wuya ta yı wuya don yanzu ya fadi yanda aka yi
36
kuma ya fadi sauran da suka nadu suka yi wa HANYA
ZAINAB kisan gilla ya kuma fadi wanda ya sasu. Alhaji
Abbab abin ya zame masa goma da ishirin ya ya zai yi da
ransa ga wannan ga wancan. Kun ga dai ramuwar da
Fiddausı take yi, ga takaicin rashin kudi ga Jamilu ba shi da
lafiya, ga Jamilata zama karuw ta yi nisa a karuwanci ga
kuma hukunci zai hau kansa, to dama haka duniyatake wata
rana a sha zuma, wata rana asha madaci, a lokacin da
GIZAGO ya fadi komai sai 'yan sanda suka sa shi a gaba a
inda suka bi shi ya nuna musu inda su NAMUZU suke, aka
yi sa'a aka kamo su sannan yakai su har gidan Alhaji Abba
baban mahadın. Koda suka isa suka yi sallama a lokacin
Abba duk jikinsa kumfa domin wanki ya ke wa Fiddausi
bayan an yi sallama da shi, ssi Fiddausi ta bi bayansa don
ba ta amince ba ko guduwa yake son yi shima. Koda ta leko
sai ta ga 'yan sanda sun sawa Abba ankwa a hannunsa. Sai
ta ce da su ko lafiya ‘yan sanda suka ce tuhumarsa ake a
kan laifin kisan gilla. Koda fiddausi ta ji sai ta gane cewar
da hannun Abba a kisan da aka yi wa mahaifiyarta, a
lokacin sai hawaye ne yake zubowa Fiddausi nan dai 'yan
sanda suka hankada keyarsa aka yi gaba da shi zuwa
ofishinsu ita kuwa Fiddausi sai ta yi sauri ta nufi gidan
Kakanninsu don ta sheda musu komai. Amma Hajiya Gaji
ko da ta ga Abba da Fiddausi sun daďe ba su šhigo ba, sai ta
fita waje tatambaya sai aka ce ai an kama shi ‘yan sanda ne
suka tafi da shi. Ta ce har da yarinyar suka de a'a, sai ta ce
to ina kuka ga ta yi sai suka nunamata. Nan dai Hajiya ta
koma ciki tana mai bakin cikin kama Abbaita ba abin ta þi
shi ba ga Jamilu a kwance haka dai ta kasance kan takaicin
wannan lamari da dana sani, don dma masu magana sunac
cewa dana sani keya ce a baya take zuwa.
Laokacin da Fiddausi ta isa gidan kakanninta.
Abdullahi da mahaifinsa suka ga ba'a hayyacinta take ba,
.37
sai suka ce yaya me yafaru, sa’a ba su labarin abin da
yafaru ta ce ashe Abbane yayi sanadiyyar rasuwar hajiya,
don gashi can an tafi da shi POLICE STATION. Lawan ya
ce lalle biri ya yi kama da mutum, don bana mantawa
Jokacin da aka gama zaman makokin Hajiya cewa na yi da
dai ba shi da rai ne to ashe macuci ne don ya zalince ki ne
to ni dai ban yaje masa ba, duniya da lahira, ai dama
Allahba azzalumin Sarki bane don ga shi ya tona masa
asiri, haka ma Hajiya Binta ta ce ita ma ba ta yafe ba.
Lamarin Abbakuwabayan yasami mako daya a hannun
'yan sanda suna yi masa tambayoyi, haka.su Namuzu ma
suka tabbaatar wa da 'yan sanda cewar shi ne ya sa su har
yaba su kudi da gida wnda yake ciki a da bayan komai
yadaidaita. Bayan an gama bincike Abba da su Gizago suka
hallara a kotu, domin yanke hukunci a cikin jma'ar da suka
hallara don ganew idonsu akwai Alhaji Abdullahi,
Mustapha, Alhaji Lawan, Alhaji Hamisu da Fiddausi, don
su jiyewa kansu hukuncin da za a yankewa su Abba, haka
ma Hajiya Gaji ta jewai tana ta addu'a don mijinta yayi
nasara ba ta son Allah ba ya zalintar bayins,kuma ba ya
karbar du'ain azzalumi sai dai wanda aka zalinta. Bayan
kotu ta cika makil da jama'a, sai mai shari'a ya iso. Koda
ya iso sai duk aka mike don girmamawa agare shi, bayan ya
zauna sai kowa ya zauna a lokacin mai gabatar da kara ya
mike yafara karanto tuhumar da ake yi wa su Abba, lokacin
mai shari'a ya nemı wadanda ake tuhuma sai suka mike
gaba dayansu, mai shari'a ya ce to kun ji laifin da ake
tuhumarku da shi, kafin kowa yayi magana sai Aba ya ce
mun ji to amma ni sharri a kai min domin babu hannunaa
ciki, kun ji Abba ba kunya bare tsoron allah ya ce shi
bahannuns a ciki Lokacin mai shari'a ya ce ko kana da
shaida wanda zai kare ka daga zargin da ake ma. Abba ya
ce Allah yagafarta malam ni ba ni da shida sai mai dakina!
38
Mai shari'a ya ce ai matarka ba za ta yi shedarka ba. Abba
ya ce tuba rake Allah ya gafarta malam don ni ba ni da
masanıya akan wannan zargin. Mai shari'a yace ko za
rakarantse da Alkur'ani akan cewar baka da masaniya akan
zargin da ake maka, na kisan Hajiya Zainab. Abba yace
tuba nake amma bazan rantse ba rantse ba. Mai shari'a ya
nemi Gizago da ya yi bayan i akan abin da ya sani kan
wannan tuhuma. A lokacin Gizago ya fara bayni kamar
haka, wata rana ina zaune da safe sai ga Abba ya zo wajena
sai ya nemi da mu kashe H ajiya Zainab akan kudi Naira
dubu goma, tare da bamu gidansa wanda yake ciki, shi
kuma ya koma gidan Alhaji Bello marigayi. Alokacin
Gizago ya ba wa mai shari'a t akardun da Abba ya ba shi,
alkali ya karba ya ga sa hannun Abba da wasu shedu. nan
alkali ya tabbatar Abba shi ne makasudin kisan
HajiyaZainab, Gizago ya ce shi ne abin da na sani akan
tuhumar da ake yi mana. Alkali ya juyo gurin Abba ya ce
ka ji abin da shaida na farko ya fada. Sannan alkali ya juyo
kan Dansanabe, nan shi ma yaba da shaida kamar yadda
Gizago ya bayar haka ma Namuzu, sannan alkali ya juyo
kan Abba ya ce ka ji abin da suka ce ko kana da abin da za
ka ce,. Nan Abba ya ce tuba nake, alkali ya ce to yanzu dai
ka amsa laifinka na hada baki da kai a yi kisan kai don
neman dukiya, ga kuma cin amanar 'yan'uwanka, don haka
na yanke muku hukuncin daurin rai-da-rai gaba dayanku. A
lokaçin aka iza keyar su Abbą zuwa gidan wakafi. Koda
aka fita da su Abba da su Gızago, sai Alhaji Lawan da
Alhaji Hamisu suka yi murna sosai, amma koda Hajiya
Gaji ta ga an tafi da su Abba, sai ta dora hannu a ka tana
kuka, sai ta koma gida, ko da ta koma gida, tana shiga sai ta
tarar Jamilu rai ya yi halinsa. Koda Hajiyata ga haka sai ta
yi waje tana kuka shikenan makasudin haukacewarta. Ga
shi kuma Jamila an shiga. karuwanci, bata san halin da
39
ryayenta ke ciki ba bare mutuwar dan uwanta, wannan shi
ne sakamakon da ya faru ga Alhaji Abba da iyalinsa to
jama'a sai a lura a gane. Cutar maraya ba abu ne mai kyau
ba, kuma hatta mugwayen makota masu yin tsafi ko wani
surkulle ga makocinsu sai su gane, domin zaka ran da Allah
ya nufa da cara.... Mu dai mun san tsintacciyar mage ba ta
mage, don haka kowa da yarensa tur Allah ya rabamu da
hali irin na su Abba. Sannan ga masu hali irin wannan su
sani cewar ba za a bar mutum jiran duniya ba, domin ko
wanne rai sai ya dandana mutuwa don haka a yi hattara
wajan gujewa son zuciya da zalinci on h aka wnnan sai ya
zama darasi ga masu irinw annan halaya hakı kuma ga cin
amanar 'yn'uwa. to yanzu Abba ya ga sakamako akan
wacce ya so ta mutu, ammaba ta mutu ba sai ga'shi shine ya
zama matacce a tsaye, tun da an yi ma sa faurin rai-da-rai.
To mu dai sai mu ce Allah ya kare mu da irinw annan
zucıya irin ta su Alhaji Abba amin. Dama an ce son zuciya
bacin zuciya don da bai so ransa ba, babu shakka haka ba
za ta same shi ba.
Lamarin Fiddausi kuwa babu abin da ya dame ta sai
murna take da irin hukuncin da aka yanke wa Abba sosai. A
lokacin Alhaji Lawan da iyalinsasukayi wa Allah godiya
mai yawa bisa wannan sakayyada ya yi musu tun daga
duniya. Ana cikin wannan murna, sai ga sako daga Katsina
kan cewar Hajiya Na'ima tahaihu kuma an sami da namiji,
murna, sai ta kasance biyu. Ga ta nasara da aka yi wajan su
Abba ga kuma ta karuwa. haka dai al'amu ra sukai ta
gudana a gidan Alhaji Lawn, bayan an sami nutsuwa sai ga
Alhaji Hamisu da dattijo mai rikon amana ya yi sallama a
gidan Allah ya bamu hali irin na su Alhaji Abdullahi ya
fito, suka gaisa da juna. Sai ya ce da Abdullahi ko Alhaji
Lawan yana nan. Sai Abdullahi ya ce ko Alhaji Lawan
yana nan. Sai Abdullahi ya ce yananan a lokacin Alhaji
40
Abdulllahi ya yo magana da shi, bayan da ya fito, suka
gaisa da Hamisu, ga kuma Abdullahi a gurin, sai ya се
dama Alhaji Lawan zuwa na yi na baka dukiyar Fiddausi,
domin ni ma akwai yara da yawa a gabana, kada na bar
baya da kura domin saboda halin mutuwa. Domin gudun
kada a zo ana rigima akan wadannan kamfanoni da kuma
kudaden da suke banki na wannan marainiya. Don haka ga
takardun kowane dukiya, kuma ga cek din banki a lokacin
ya mikawa Alhaji Lawan, sai ya ce a'a shi ba zai karba ba,
kuma Allah ya yi maka albarka, bisa rike amanr da ka yi
kuma Alllah ya raya zuriyarka amin. nan dai Alhaji Hamisu
ya dunga hada shi da-Allahakan ya karba, amma ina. Sai da
Alhaji Abdullahi ya sa baki, ya ce shi ma ai Hamisun ya yi
gaskiyaka san halin yau yadda yake. Sanan ya karba domin
Alhaji ka san yanzu takarda ita ce sheda domin ka ga nan
gaba idan babu taakardun to ba ka da hujja a kan komai
nata, a lokacin Alhaji Hamisu yayi godiya mai yawa ya
kuma ce zan kai ku duk inda kamfanoninta yake in nuna
muku. Ya yi bankwana da su suna masu godiya yatafi.
Washegari Alhaji Abdullahi ya ce shi zai koma domin
a yi suna yana nan. Lokacin fiddausi ta ce ita ma za ta don a
yi sunan tanan nan. Haka suka tafi, to bayan tafiyarsu da
kwana daya sai iyayen Mustapha suka hada kaya suka aiko
gidan Alhaji Lawan nan dai aka karba cikin aminci da
karimci. Amma a can Katsinakuwa da ranar suna ta zo sai
aka sawa yaro suna Muhammad Lawan, wato yamayar da
sunan mahaifinsa. Don dama tuni ya riga ya sa sunan
mahifiyarsa. Bayan da aka kammala harkar suna da wani
lokaci sai ak fara shirye-shiryen biki. Aka sa Fiddausi a
lalle, a lokaicn akai shagalin biki mai kayatarwa ga duk
mutumin da ya halacci wurin, Alhaji Hamisu yayi wa
Fiddausi kayan daki na gani na fada; don shi ne madadin
Alhaji Bello marigayi. akai ta yi masa godiya d sa masa
41
albarka, ita kuwa Fiddausi suka yi zamansu lafiya da
masoyinta. Dama wnnan shi ne burinsu gashi allah ya cika
musu sai mu ce Allah ba da zuriya ta gari amin summa
amin. Wannan shi ne karshen wannan littafi mai suna MAI
RABON GANIN BADI, inda Hausawa suka ce wai ko ana
dakawa a turmi sai ya gahi. Ai wuyaba ta kisa sai kwana ya
kare to a nan zan takaita ni ce-'yar uwarku HAUWA
ALHAJI BASHIR AYAGI, mawallafiyar SO SARTSE
Allah ya ba shi kabuli amin. Bissalam, Allah ya ba mu
alheim sa amin na barku lafiya.
Lokacin da mutun ya fahimci cewar ya bi watą hanya
wadda ba za ta kai shi ga alheri ba, to shi ne yake neman
aimako ga Allah da ya nisanta shi da ita kuma ya kare shi
daga sharrin shaidan da sharrin mutane da za'a yi musu
azaba ranar kiyama. Kamar yadda wannan littafi ya kunsa,
wannan dai a takaice muna neman shari'a ta gari daga gun
Allah kuma muna so ya nisanta mu ga dukkan mai kawo
fitina a duniya 'yan uwan shedan da shi kansa muna neman
tsari da shi mutun kada ya yi tsmmani rayuwarsa ta kare
bayan mutuwa, ita dai mutuwa tana raba shi da duniya ne
kawai zai sake sabuwar rayuwa fil ba irin wadda ya yi a
duniya ba wnnan rayuwakuwa zai sake yinta ne ranar lahira
wwanda Iamni da shi da abin da yatattara na hisabi da
sakamako yana shika-shikan Musulunci. Kuma babu wni
maimulkia wnnan rana sai Allah, dubi Suratul Infidari aya
ta 17/8/9
BAKIN CIKIN RAYUWATA NA BIYU
A gaskiya Kairiya babu yadda za'a yi na daina sonki
da kaunarki don duk lokacin da na kwanta da sunan bacci
dare ko rana to wallahi tunaninki ba ya barin na yi bacci,
42
inda na ga wuni haka zan ga kwana, don haka Kairiya ki
tausaya min. Ga irin sonki da ya mamaye min zuciyata don
hka kada ciwon sonki ya hallaka ni, domin idan kika ce ba
kya Kaunata lalle ciwon zuciya zai kama ni, domin idan
bana kusa da ke to rayuwata bata da amfani. yake
masoyiyata, Kariya ta kalli Sa'ad sai dai na ce ka yi hakuri
kuma Allah ya ba ka mai kaunarka kamar yadda kake
Kaunata. amma Kariya sai Jabir. Kadan kenan daga littafi
na biyu, NA BAKIN CIKIN RAYUWATA. 'Yar uwarku
HAUWA A. BASHIR AYAGI, Allahya bamu alherins
amin summa amir. Na barku lafiya, na gode.
BAKIN CIKIN RAYUWATA NA DAYA
Wata rana Sarki Abdulhamid suna zaune shi da
matarsa Hamida suna hira sai ta ga yana hawaye a lokacin
hankalinta ya tashi ta ce lafiya Sarki ya ce yanzu nine a
cikin gidan baban makiyina wanda ya raba ni da iyayena da
dan uwana da matarsa saboda abin duniyaya sa ni bakin
cikin rayuwata. nan Hamida ta rarrashe shi, ta ce abinda ya
fi duk lokacin da muka yi sallah to muyi musu addu'a ga
Allah ya yi musu rahama ya ce amin. nan suka ci gaba da
hirarsu ta masoyan juna na zamantakewa ta aure, Sarki
Abdulhamid ya kalli Hamida suka yi murmushi ya ce
yanzuna farka da bakin cikin rayuwata. Kuma yanzu zan yi
godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba ni ikon samun
masayi. Don jin yadda hirar za ta kasance nemi littafin don
jin yadda za ta kasance. HAUWA A. BASHIR AYAGI
MASOYINA NA DAYA
Nafisa a gaskiya kin san cewar babu wanda ya fi wannan
mu'amala da nisa ko in ce ganin nisa ga wanda ya hau
giginya ya fado bai zarce ko ina ba sai cikin rijiya ina ganin
wanda zai fi shi ba da labari game da nisa ko in ce da kai
43
ganinsa, don haka kar ki ji tsorn nisa game da mallakar
junanmu a halal ce. (Aure) Fatana kuma shi ne ki rike alkawari, amana, ta numfasa ta ce kai nemi wannan labari
`na UMAR akwai gwa-gwarmaya a ciki kafin a yi aure.
Neme shi a kantin sai da littattafai na kusa. NA HAUWA
A. BASHIR AYAGI.
MASOYINA NA BIYU
Lokacin da nafisa ta fito ta ga Aliyu ya ce ina son
ganinki ta ce kai dakata ya rike baki ya ce baki sanni bane.
Ta ce ban sanka ba don Allah ka tafi ka bani guri mara
zuciya, mara tunani, jibeka wani "YABGI" da kai kamar
mara hankali shashasha. Ni banasonka bana son mai sonka.
Aliyu ya yi kasake yana kallonta, yace sai na aure ki in dai
kudi ne suke aiki akwai su. nafisa ta kama hannu Umar
suka koma cikin gida, suka bar Aliyu a tsaye yana
cizonyatsa nemi wannan littafi ka ji karshen batun
HAUWA A. BASHIR AYAGI.
SO AJIYAR ZUCIYA
Muhammad ban yi tsammani za ka yi min haka ba.
Amma Muhammad ka ci amanata, kuma ka yaudare ni ka
sani a cikin wani hali ka tuna alkawarin da ka yi min.
Muhammad ka shiga zuciyata ka mamayeta domin ba wani
mahaluki da yake cikin zuciyata in ba kaiba. Na kori
jama'a da dama amma za ka yi min haka, haba Muhammad
kaceto