don haka na yanke wa kaina
hukuncin komowa nan. Fiddausi ta ce hatta Jamila sa'a ta cе
amma saita zage ni ta do ke ni. ba ni da ikon ramawa domin
Hajiya da Abba sun daure mata gindi, dubi gadon bayana
duk katakore ne "bell' na injin nika da shi ake ba ni kashi.
Haka Fiddausi ta yi ta ba su labari suka tausaya mata. Alhaji
Abdullahi ya ce ai sam ba zan yarda da haka ba. Kuma ya
Kara da cewa, kuma duk wulakancin da su kai miki sai kin
rama kuma idan wulakancin ne kowa ya iya kuma namu ya
fi nasu kuma da hannunki za ki rama babu wanda zai rama
miki. Alhaji Abdullahi ya yi t a fada tare da cin alwashin
cewar sai ya ga dalilin da ya sa ake ta bautar da wannan
marainiyar yarinya haka domin abin ya huce misali
Wata rana bayan an sami lokaci mai tsaho da maganar
Fiddausi kan irin matslar da take ciki, kwatsam sai ga
Mustapha ya yi sallama a gidan Alhaji Abdullahi, ko da
Fiddausi ta dau muryar masoyinta sai ta leko,......Sai suka
hada ido hudu da masoyinta, ta yi masa sannu da zuwa ta
ce bari na fada cewar ka zo, Mustapha ya ce ba ji Fiddausi
ta koma ta shaidawa Anti Na'ima cewar ta yi bako daga
Kano. Anti ta ce maza a dau mukulli a bude masa sttitum,
bayan ta bude suka shiga tare da Mustapha, ya zauna
Fiddausi ta koma ta kawo masa lemo ta dire a tebirin da
yake gabansa, wanda a wannan lokacin Fiddausi ta sake yı
masa barka da zuwa ya yi da shi kuma yana zaune ne a kan
kujera, ta kuma gaida shi gaisuwa kuwa irin ta ma'abota
21
soyayya, koda Mustpha ya amsa sai ya ce kai amma na sha
hanya, Fiddausi ta ce kwarai kuwa domin ni ma lokacin da
na zo haka na gani, don naza ta tafiyar ba ta da nisa,
Mustpha ya ce ni ma banaiya irin wannan tafiyar a mota,
amma da yake garin masoyi ba shi da nisa, ga shi na zo
saboda ke, a lokacin Fiddausi ta ce ai ni ban zaci kwanan
nan za ka zo ba. Mustpha ya ce ai kin san idan ba ganinki
nake kusa da ni bato ba na jin dadi Duk da yake dai Abba
ya hana ni zuwa to amma ai muna haduwa. Fiddausi ta yi
murmushi mai tada hankalin-mai bege, Fiddausi ta ce ka ci
abinci kada ya huce ka ga yanzu aka gama. Mustpha yace
ko ganinki ya isa ya sani na koshi, Fiddausi ta ce bari na
fita ko ka daina ganina ka ci da yawa. Mustapha ya yi
murmushi ya soma ci har ya koshi ya yi hamdala sannan ya
sharuwa ya sha lemo, Fiddausi ta ce bari na koma ciki ko
ka huta, nan ta mike ya bita da kallo dimin ya ga
kamanninta sun canza kamar ba ita ba, idan ba wanda ya
gani da idonsa ba, ba wanda zai ce ta taßa wahala, don shi a
lokacin gani yayi har ta fi da kyau sosai, a lokacin Mustpha
ya yi tasbihi ga Mahalicci da- cewar sarki ya tabbata ga
Allah Madakakin Sarki, Allah Subhanahu wa Ta'ala da ya
shirya gabban wannan yarinya alokacin ya mike a doguwar
kujera yana mai tunani da addu'ar Allah va tabbatar da
aureps da Fiddausi. Lokacin da Fiddausi ta koma cikin gida
sai Anti Na'ima ta ce waye bakon namu Fiddausi ta ce
Mustpha ne, Anti ta ce ni kuwa ban san shi ba, amma ba
dan uwanku ba ne. Fiddausi ta ce ai dan abokin Babana ne.
Anti ta ce ko dai saurayinki ne, Fiddausi ta yi shiru, nan dai
Anti ta gane cewar Mustpha biyo Fiddausi ya yi. Tana rufe
bakinta sai ga Alhaji Abdulllahi ya dawo, nan Na'ima da
Fiddausi suka yi wa Alhaji sannu da zuwa ya amsa
Fiddausi ta kawo wa Alhaji abinci, don yanzu it take yin
abinci kasancewar Hajiya Na'ima na da tsohon ciki, Alhaji
22
ya soma cin abinci, bayan ya gama, sai Hajiya Na'ima take
gaya masa cewar mun yi bako yake cewa daga ina ta ce
sirikinmu ne daga Kano. Alhaji yayi jum yana tunani, sai
Hajiya ta ce to saurayin Fidddausi ne ya zo gaishe mu ka
san garin masoyi ba ya nisa in ji Hausawa Alhaji ya се
wanna gaskiya ne, Alhaji ya ce ko yana ina! Ta ce ashe
baka kula ba ai yana sitirum, Alhaji ya ce amma na ji dadi
da kika karrama shi, a lokacin ya yi kiran Fiddausi, ko da
tazo ta durkusa ta ce gani ya ce maza kirawo min bakon da
muka yi Fidausi ta nifi inda bakon yake wato Mustapha, ta
ce ka zo Baffa yana kira koda Mustapha ya ji haka sai ya
tashi da sauri suka yi cikin gida, da isarsu saí Mustapha ya
durkusa ya gai da Alhaji da mai dakinsa, Na'ıma, bayan
sun amsa Alhaji yace saukar yaushe Mustpha yace dazun
nan naiso, Alhaji ya ce na ji dadin zuwanka, Alhajiyа се
yaya mutanen gida Mustpha ya ce suna na lafiya lau. Alhaji
ya ce lafiyanaganka ko Alhaji ne ya aiko ka Mustaphaya ce
a'a, ni dai abin da yake tafe da ni shi ne na zo neman auren
Fiddausi ne domin tun muna Kano ni ne nake sonta. To
bayan da muka dade ina nemanta da aure, har ya kasance
mun fahimci juna to sai wata rana na je Abbaya ce da ní ko
da na sake zuwa ya ci mutuncina ya ce wai ya raba mu.
Kumaya kara da cewa muddin ya sake ganina a kofar
gidansa sai ya sabar min. Wata rana Fiddausi ta bar gida sai
Abbaya zo har gida yayo sallama da ni, kp da na fito sai
naga Abba a tsaye sai na durkusa na gaishe shi ya amsa da
kyarya ce wai nafito masa da 'yarsa Fiddausi. Na yi masa
rantsuw da Allah akan bata wajena amma ina Abba
baiyarda ba, ya ce wai da a ce ni wani bare ne da sai ya ci
mutuncina ya sa an taran gajiya. Nan dai na bi shi a
hankali muka rabu lafiya. Domin kowa ya san halinsa shi
yasa ban yarda hakan ya jawo wata illa a soyayyata da
fidddausi ba. Na lallaba shi muka rabu lafiya. Shi ne muka
23
ci gaba da soyayya boye har ta taho nan. Domin lokacin da
za ta taho nan sai da ta shedamin cwear za ta taho nan. Shi
pe na yi mata alakawarin lale tana jika domin ba nisa ga
garin masoyi, bakin zaren maganar shi ne zan ziyarce ta, to
wannan shi ne dalilin zuwana kuma na ji dadi da na sami
kyakkyawar maraba. Alhaji ya ce kai amma na ji dadi
kuma ka kwantar da hankalinka in Allah ya yarda komai zai
yi daidai. Alhaji Abdullahi ya ce ni ma daman ‘yan shiryeshirye nake domin za mu Kano. In ji dalili da ya sa Abba da
mai dakinsa da ‘ya'yansa suke gallazawa Fiddausi sukai
musayar kallo, suka yi murmushi. A lokacin Mustapha yace
Allah ya kai mu lokacin don ni koda yaushe a shirye nake
Alhaji yace amin. Alhaji yace da Mustapha ya koma
masaukinsa, nan Mustpha ya mike tsaye tare da
girmamawa a gare su, lamarinsu kenan.
Amma a can Kano abin ba’a cewa komai domin Alhaji
Abba ya kai Alhaji Lawan kara don yana gani shi ne ya
foye Fiddausi, koda suka je kotu sai mai shari'a ya tashi
mai kara don yayi jawabin karar da yake kan Alhaji Lawan.
Alkali ya ce ka ji abin da mai kara ya ce Alhaji Lawan ya
ce na ji Allah ya kyauta yin mallam, ko yana da sheda
wanda ya ga 'ya a gidana, lokacin Alkali yajuyo gurin
Abbaya ce ko kana da shaida Abba yace ni ba ni da shaida,
sai dai akwai wani lokaci da ta je gidansa ya hana ta
dawowa, don da na je sai da muka kai ruwa rana, shi ne ya
sa nake zarginsa don sai da makotansa suka sa baki
sannan ya bani ita. To shi ne yanzu na nemeta na rasa. To
shi ne nake zaton tana gidansa, mai shari'a ya ce ko ka san
zato zunubi ne, koda ya kasance gaskiya, don haka na
yanke wannan shari'a taku, domin babu shaida Alhaji
Lawan yi tafiyarka. Na sallame ka. Ya yi godiya ya share.
abbaya koma gida ba gwiwa. hajiya Gaji ta ganshi ransa
abace, ta ce yaya ko ba sa'a ne haushi ya sake kama shi ya
24
ce lalle wannan maı shari'ar ko alhaji Lawan ne ya gans
shi don na ga ni shari'ar ba tai min ba. Gaji ta ce E" Lalle
haka ne abin da ya fi to kawai ka sake kotu. Ko ka shigar da
sabuwar kara ko ka sami rinjaye don na san babuinda
Fiddausi in ba gidansa ba amma da yake munafiki ne ka ji
ya dage kan cewa ba ta gidansa. Amma ai matarsa ba ta
sanni ba. zan shirya naje gidan da daddare domin ka san ko
aike ne ba za su aiketa ba a wannan lokaci, ka ga ko ni na
ganta na isa shaida. Tunda idona ya nuna min. Shi kuma
Abba sai ya amince ka ji, SAHON JAHILI. Ko da dare ya
yi sai munafukar matarsa Gaji ta yi shiri ta nifi gıdan Alhaji
Lawan, koda isarta ta yi sallama ta ce da Allah tambaya
nake ko nan ne gidan Alhaji Abba, sai Hajiya Binta ta ce ai
ko ba nan bane, bama a nan unguwar yake ba. Kuma da
'yar tazara zuwa inda yake, sai Gaji ta ce kai amma na
wahala tun safe nake neman gidan, sai Gaji ta ce da man
mai unguwa ne ya iko ni, Binta ta ce daman a nesa kike,
Gaji ta ce a nesa nake can Koki, dama wata yarinya aka
tsinta ta ce sunan babanta Abba, Hajiya Binta ta ce ita kuwa
yaya sunanta, Gaji ta ce sunanta Fiddausi, kuma ta gayan
wani suna idan ban sami gidan ba sai na tambaya sai na
manta sunan. Ko da ta ji cewar Fiddausi take neman
iyayenta sai ta ce ko dai Alhaji Lawan. Sai Gaji ta ce
yawwa can, ko nan ne sai Binta ta ce nan ne ba ki ga neman
da mukai ba amma ba'a same ta ba. Kuma shi Abban har
karar mai nan gidan ya yi domin, sun zato tana nan, mu
kuma ko gidan nan ba ta zo ba, amma watannin baya da ta
zo, ya zo ya dauke tato shi ne yake zaton tana nan. Hajiya
ta ce gashi kuma Alhajin ba ya nan da sai ku tafi a dawo da
ita, kuma da za ki kwana da saiki yi kwanciyarki da safe kи
je a dawo da ita. Gaji ta ce ai ni ba zan kwana ba domin
za'a neme ni a gida, na san ba zai kasa sanin Koki ba idan
Ailah ya kai mu sai ya zo ya tafi da ita. Gaji ta ce to ni
25
4
Hajiya zan koma sai an kwana biyu, Binta ta ce to madalla
an gode Binta ta kuma kawo kudi ta ba ta ta ce ga shi kin
shiga mota. Gaji ta ansa ta yi godiya, ta fita ranta a 6aсе
ganin ba ai nasara ba,don da a ce Fiddausi na nan to zaman
da ta yi ya isa a ce ta ganta. Nan dai ta koma gida ba
gwiwa, ita kuwa Hajiya Binta sai Allah-Allah take Alhaji
Lawan ya dawo ta ba shi labarin ganin Fiddausi, bayan
wani lokaci da tafiyar Hajiya Gaji sai ga Alhaji ya dawo
bayan ta yi masa sannu da zuwa sai ta soma ba shi labarin
abin da ya faru cewar yanzun nan wata mata ta zo daga
gidan mai unguwar Koki fitarta kenan. Alhaji ya ce lafiya,
wai Fiddausi aka gani a can baka ga dadewar da ta yi baa
nan, tana jiranka, amma ba ka dawo ba. Amma ta-ce gobe
da safe ka je ka taho da ita, Alhaji ya yimurna sosai ya ce
Allah ya kai mu, wannan shi ne abin da yafaru a gidan.
Lamarin Gaji munafukakuwa tana isa gida ta tarar
Abbayana jiranta, ta yi sallama Abba ya amsa yana ta
murna tana zama, Abba ya ce yaya tana can Gaji ta ce ba ta
nan, Abba ya yi takaicin rashin samun Fiddausi. Sannan
kowa daga cikinsu ya zauna yana zulumi tare da bak
cikin rashin ganinta, domin hanyar kudi t toshe rashin
zamanta da su kenan. Bayan gari yawaye sai Alhaji Lawan
yashirya ya nifi Koki don dauko fiddausi ba su san makirci
ne Gaji ta kada musu ba. Koda ya ısa ya nemigidan mai
unguwa suka gaisa sai Lawan ya ce don Allah tambaya
nake, mai unguwa ya ce Allah ya sa na sani, Lawan ya ce
wata yarinya Budurwa na zo karba, don jiya wata ta zo
gidana daga gidanka ta ce tanan nan an ganta, wai ana
peman iyayenta, don lokacin da ta je bananan, to shine na
zo yanzu, amma da tun jiyan za mu taho. Mai unguwa ya yi
shiru sannan ya ce wata mata? Lawan ya ce E" Mai
unguwa ya ce shi tun da ya hau kujerar nan bai taba aika
wani yaje nemo iyayen yara ba. Toballe mace, mai unguwa
26
ya ce shi sam ba daga gidansa ba, a lokacin yasa aka fito
masa da duk yaran da suke gidansa ya duba, ko Allah ya sa
ya same ta. Lokacin da Alhaji Lawan ya ji wannan batu, sai
ya ce to lalle duk yadda aka yi wani makirci aka
shiryamasa, a lokacin ya cewa mai unguwa na gode
madalla, snnan aka fitoda batattun yaran ya duba yaga sam
ba Fiddausi. Don haka ya yi ban kwana da mai unguwa ya
koma gida,, ya shedawa mai dakinsa cewar lalle wannan
mata karya take akwai dai abin da take nufi da mu domin
idant an biya ma Abbane ya turo a gani ko tana nan. Ni kona
same ta ma ba wanda ya isa ya sa na sake ba shi ita domin
wata rana idan ana haka ganinta ma ba za a yi ba muddin
aka sake mai da ita, haka suka kasance.
Bayan wasu kwanaki, Alhaji Abdullahi ya shirya suka
taho Kano da shi da Fiddausi da Mustapha, koda suka iso
Kano lafiya sai Alhaji ya nifi gidan mahifansa, suka yi
sallama Hajiya Binta ta amsa, tana lekowa sai ta ga Alhaji
Abdullahi da Fiddausi ta yi musu barka da zuwa, inda ta yi
musu shimfida bayan sun zauna Alhaji y gaida
mahaifiyarsa, sannan Fiddausi da Mustapha suma suka
gaishe ta, Hajiya tana fara'a da ganin dawowar Fiddausi, ta
ce Fiddausi daga ina, Fiddausi ta ce Katsina na je, kuma
yanzu daga can muke domin Baffa ne ya ce mu taho na yi
ramuwar abin da Abba da mai dakinsa Gaji da 'ya'yansa
suka yi min. Amma da ba zan dawo ba. Koda Fiddausi'ta yi
shiru, sai Abdullahi yafara shaidawa hajiya abin da
Fiddausi ta gaya masa, kuma yace don Allah me ya sa
lokacin da na zo ba ku gayan ba ai da komai ake ciki da
tuni an gama. Don ni ba zan yarda ba, don haka yanzu
daukar fansa muka zo yi, a lokacin Hajiya ta ce yanzu ya
za'a yi ta iyarama abin da sukai mata, ni daia ganina kawai
a barwa Allah shi ya fi. Domin shi zai saka mata, Alhaji ya
ce dama Hajiya ba du za ta rama ba, ai wani abin
27
ma ta
manta, amma kin san ramuwar gayya, taf ta gayya safi
Don haka ko kadan sai la rama A lokncn yn gии
Mustapha, Hajiya la ce ai na san shi ha tun унн bн. Миужн
sunsaii wani lokaci mat tsaho suna hira s Alhaji wn
ya dawo Abdullahi, Mustapha da Fiddaust sukиi
barka da zuwa ya asн Ya ce lafiya na g ku suke dawowи
ya ce I, sannan ya Kara da cewa a nи ун gаno Fiddaue?
Abdullahıya ba shi labarin duk yadda ta kиsance yu gaунми
uban Shi ma uban ya ba shi labarin yadda suka kwashs An
Abba, yace yanzu Fiddausi can ta je Abdullahi yu ee at
tama dade a can Sannan ya ce kawo ta na yi, Albaji Lawan
sam ba za ta k oma gidan Abbaba abdulllahiya ce ai ba can
zan kai ta ba dama zuwa na yi tayi ramuwa, Lawan ya ee
lalle wannan shi ne abin bida, gaskıyane an yi dai-dai allah
ya yi maka albarka! Amin in ji HajiyaBinta, a lokacin
Mustapha ya ce ni zan tafi sai an kwana biyu Abdullahi
yace to madalla, ka gaida Alhaji ka ce ni ma na zo ni da
Fiddausi, kuma zan zo har gida na gaishe shi. Mustapha
yace to zan gaya masa. A lokacin ne Alhaji Lawn da Binta
suka ce ka gaida gida. Sanan Fiddausi ta yi wa Mustapha
rakiya har kofar gida, ta ce sai yaushe yace zan zo byan
kwana biyu, ta ce to na gode. nan dai suka yi ban kwana, ta
ce don Allah ka gaida Baban da Hajiya, Mustapha ya ce sa
ji da haka suką rabu, ta dawo gida. A inda Alhaji Abdullahi
yake cewa anama ban ji dadi ba da na zo watannin baya ba
ku gayan ba. Ai da tuni na dau matakin da zan dauka,
Alhaji yace ai ba komaika san tashin hankalibabu dadi
yanzu ba gashi ka ji ba. Haka dai suka yi ta yin hira. Amma
shi kuwa Mustapha bayan ya isa gida, yayi sallama Hajiya
ta amsa Mustapha ya shiga ya gaishe ta, ta ce har ka dawo
ya ce E" Ta ce yaya ka baro su ya ce lafiya kalau, kuma ai
tare muka taho haddda Alhaji kuma da Fiddausi domin
28
ramuwa ta zo yi, Hajiya ta yi murna kuma duk sun ce
gaisheku, Hajiya ta ce muna amsawa.
a
Bayan an kawan biyu da zuwan Abdullahi sai ya ce to
Bab, yau fa mu za mu je gidan Abbaa lokacin Alhaji da
Binta sukai musu a dawo lafiya suka ce amin, suka fita
suka shiga mota suka nifi gidan su Fiddausı sai suka tsaı da
motar, Abdullahi ya ce maza ki shiga ki yi min sallama da
Abba, a lokacin da ta yi sallama suna sama dukkaninsu, sai
da ta hau sannan suka ji tana shiga inda suke, sai
dukkaninsu suka juya sai suka ga Fiddausi, sai mamaki ya
kama su, ganin Fiddausi ta sake kama ta sake kyau sosai,
nan dai su kai cak suna ta tunani wai ko fiddusi ce koba ita
ba ce, Fiddausi d ta ga haka, sai ta ce wai ana sallama, nan
dai Abba ya tashi yana mamaki bai cew kowa komai ba ya
fita. Domin yasha jinin jikinsa cewar ba banza ba Fiddausi
ta shigo kai tsye ba, kodaAbba ya daga kan kujerar da yake
kai, sai Fiddausi ta dare. Yayin da ta ga kwanukan abinci a
jere sai kawai ta soma ci. Ba tare da ta yi wa kowa magana
ba, koda Hajiya Gaji ta ga haka sai wani sabon mamaki ya
kama ta, ta kasa cewa komai, su Jamila 'yan duniya yau ana
gida. Ta ce hajiya kina ganin abin da Fidausi take yi kuwa,
Hajiya za ta yi magana sai Fiddausi ta mike ta cewa Jamila
daman wajankina zo, munafika. Sai Fiddausi- ta ciro
almakashi daga cikin jakarta ta datse gashin kan Jamila
koda Jamila ta ga ta zama Gwai-gwai sai ta dunka kuka
tana cewa Hajiya kina ganinta ko, Hajiya Gaji ranta ya 6асі
sosai a lokacin ta daga hannu zata mari Fiddausi, sai ta ce
"Ahir kika kuskurakika taba ni, yanzu nayi kasa-kasa dake
munafuka, koda Gaji ta ji haka sai jikinta ya yi sanyi. Ga
shi Abba ya fita yayi zamansa kuma dama Fidausi ta fi
Karfin Jamila daman don da ana mulkkin kama karyane shi
yasa Jamila ke rawa da bazar su Abba, to dama an ce
ramuwar gayyata fi ta gaya zafi. Lokacin dasuke mata
29
azaba, sun manta cewar wata rana za ta rama ne tn da dai
Allah bai dauki ranta ba. Koda Fidddausi ta rama yanke ga
shi da aka yi mata sai ta sauka ta bar banzaye biyu 'ya da
uwa azzalumai. Gaji munafuka sai ta bita da kallo. Bayan
Fiddausi ta fito sai ta tarar da Alhaji da Abba suna magana.
Domin shi Abba a zatonsa Abdullahi dawowa ya yi da
Fiddausi, don shi har ya shiryaabin da zai mata idan ya
koma, sai kawai ya ga Fiddausi ta fito. A lokacin shi Abba
ko godiya bai masaba. Don Abdullahi bai nuna masa komai
ba. Sai Fiddausi ta ce baffa na fiito mu tafi ta shiga mota
Abdullahi ya tashi.ya bar Abba a zaune ya yi sallama da
shi, Abba ya kasa cewa komai saboda mamaki shi kuwa
Abdullahi ya shiga mota sukai tafiyarsu, lokacin Abba ya
koma ciki yana bakin cikin abin da Abdullahi ya yi masa,
koda ya hausama, sai ya taras da Jamila tana kuka yaya
lafiya Abba ya tambayi Gaji, a lokacin nan Gaji ta hau
masifa tana wallahi ni ba zan yadda da haka ba, domin ba
zanyadda 'yar ciina ta dunga yi ***min rashin kunyaba,
kawai ka je ka yi zamanka a wajc ai da kana nan da ba tai
mana hka ba, kaiAbba da abin ya zame masa biyu, ga
takaicin abin da Abdulahi ya yi masa ga kuma shi Gaji tana
yi masa fada, shin wai me aka yi ne ni na tambaye kini ba
ki bani amsa ba kuma gashi sai fada kike ta yi min, ta ce ai
dole nena yi ma fada mana wai yarinyar nan Fiddausi har
ita za ta iya zuwa har nan gidan ta yankewa Jamila gashi,
wai har ni take cewa za ta yi kasa-kasa da ni, idan na
kuskura na taba ta, Abba wani sabon bakin ciki ya zo masa,
ya ce ai wan Hajiya Zainab ne ya sa ta ta yi komai, Hajiya
ta ce ba dai wanda ya zò kwanakin baya ba, ya ce shi mana!
Gaji ta ce ashe ba shi da mutunci, Abba ya ce ai ni ma sai
yanzu na sani ashe da ta bar gidan nan ta je gidan Alhaji
Lawan can ya tura ta, ya ce amma ba komai i wata rana za
ta ske dawowa za ta san lahira babu dadi kai Abba kenan!
30
To ai lahira ita ce mai dadi ga wadanda sukai aiki na gari,
domin sun fi son ma lahirar a kan duniya, a lokacin Abba
ya ce da Gaji ki yi hakuri ya kuma rarrashi Jamila, ya ce to
yanzu kin ga wan Hajiya Zainabya soma zuwa kuma yasan
komai, to mai yiwa a karbe dukiyar Fiddausi daga gun
Alhaji Hamisu shi ya ce zai a jiye a hannunsa, to ammaidan
yasan wata ai bai san wata ba, kin san kafin fiddausi ta bar
gidan ta samin hannu a takardun banki, to amma na je sun
hana ni, amma zan je bankin Amurka na karbo na can, idan
na dawo nan sai na sake gwada wa ko za su ba ni, ko yaya
kika gani, to a lokacin Hajiya dai ranta a 6ace yake amma
koda ta ji maganar kudi sai ta murmure yake to amma fa ki
yi dabara tun da dai mu ne ba'a son mu ci arzikinta, to
mune masu ci ko an Ki ko an so.
Al'amarin su Abdullahi kuwa bayan sun koma ida
yake tambayar Fiddausi in ce ko kin fara ramawa kuma ina
mai yi miki gargadin cewa kada ki ji tsoron kowa, kuma
duk abin da kika san an yi miki ki rama kin ji ko. A lokacin
Fiddausi ta ce ai na soma ramawa Baffa, kuma babu wanda
zan ji tsoro a gidan daman rashin wayewa ne ya kawo haka
da kuma halin yarinta, amma yanzu za su dandani kudarsua
wajena sosai, nan dai sukai ta yin hira. Lamarin gidan
Alhaji Abba lokacin da gari ya waye sai Alhaji abba ya yi
shirin tafiya AMURKA, Hajiya ta yi wa Abbafatan samun
nasara. Kai ina ruwan wahalalle haka kurum ba ka ajiye ba
ba ka bawa wani ajiya ba, ka shirya ka ce wai kai kudi za
ka karbo. Alhaji Abba ya niif filin jirgin MALAM AMINU
INTERNATIONAL AIRPORT. A inda ya tashi zuwa
Amurka, byan rana ta daga kamar fiddausi ta sani sai Alhaji
Abdullahi ya kawo ta, ta ce baffa yau kwana zan yi. Ya ce
to a lokacin ya sake gargadinta cewar kada ta ji tsoron
kowa, kuma idan ta ga ba sarari ta dawo gida, fiddausi ta
ce, to, alhaji ya tafi, Fiddausi ta shiga ta yi sallama Jamila
31
a amsa ba ta san Fiddausi ba ce, a wannan lokacin Hajiya
Gaji tana daki tana sharar barci, a lokacin Fiddausi ta hawo
sama koda Jamila ta ganta sai gabanta ya fadi ji kake ras,
Fiddausi ta wuce ba tare da ta yiwa Jamila magana ba sai ta
aifi baranda koda ta isa, sai ta sami kujcrar da Abba ne
kawai, ke hawanta lokacin da yake nishadi sai kawai ta yi
ramanta a kai, ita kuwa Jamila sai ta biyo Fidddausi ta ga
abin da za ta yi, koda ta ga Fiddausi a kan kujerar Abba ga
shi kuma Gaji tana sharar barci. Sai Jamila ta ce wannan ai
iskanci ne yaya kujerar da Abba yake hawa za ki hau don
wani sabon rainin hankali da kika sake, koda Fiddausi ta ji
haka sai ta mike ta ce ba za a tashi ba, a lokacin Fiddausi ta
Kwace zanin Jamila da mayafin da dan kwali gaba daya, ko
da Jamila ta ga haka sai ta shiga daki da sauri tana kuka har
sai da Hajiya ta tashi ta ce yaya me ya faru? Ta ce kin ga
abin da Fiddausi ta yi min kuma ga ta can a kan kujerar
Abba wai don na ce ta tashi shi ne ta yi mn haka koda
Hajiya ta ji haka sai ta ce yau ma dawowa ta yi Jamila ta ce
E" Hajiya Gaji ta tashi a fu sace ta n if inda Fiddausi take,
koda ta iso inda Fiddausi take sai k awai ta ganta Gaji ba ta
yi wata-wata ba sai kawai ta dauke Fiddausi da mari, nan
Fiddausi