Ahaji Lawan ya yi sallama. Aka
amsa, Abdullahi ya taso ya karbi kayan da suke hanunsa, ya
yi masa sannu da zuwa. Alhaji Lawan ya ce Abdullahi saukar
yaushe, ya ce ai ban dade da zuwa ba, koda suka shiga falo
Abdullahi ya zauna inda ya gai da mahaifinsa cikin ladabi da
girmamawa a gare shi. Haka shi ma yake yi masa ta'aziyyar
'yar'uwarsa Hajiya Zainab. Nan ma hira ta 6arke tsakanin
Ahaji Lawan da dansa Abdullahi, su na ta bawa ju na labarin
al'amuran yau da kullum.
Wata rana Alhaji Abba da mai dakinsa suna hira, sai
yake cewa ni, kuwa zan matsantawa wannan shegiyar
yarinyar Fiddausi, lamba duk lokaci da munafikin nan Alhaji
Hamisu ya zo ta samin hannu a duk ta kardunta na banki ko
don gaba. Don kwanakin baya da Alhaji Hamisu ya zo ya
hana mu kudin nan baki ga yadda raina ya baci ba. Gaji ta ce
ranka ya 6aci ko dai nawa don ka ga a lokacin mu n yi da
Hajiya mai Danyen kaya za ta kawo min wata set din sarka
na Daham, na siya, daman da ya bayar jamila zan saya wa
don za ta.dace da ita domin baka ga kyan ta ba su masu
kawaye Abba ya ce, ai don h aka zan saka ta dole ta saka
hannu. Gaji ta ce ai kuwa da mun warke so sai. Haka dai su
kai ta yin hira suka tsare Fiddausi kan sai ta sa hannu cewar
du k lokacin da Alhaji Hamisu ya zo sai ya ba su abin da
suke bukata. Koda ba ta nan haka kuwa aka yi Fiddausi ba
tantama haka ta sa hannu koda yake ta san ba zai ba su ba,
10
amma saboda tsoro ta sa hannu Abbaa da Gaji su kai murna
kwarai da gaske h aka suka kasance. Amma lamarin Alhaji L
awan kuwa, bayan Alhaji Abdullahi ya ce zai je ya gano
Fiddausi, dop ya dade bai ganta ba. Lokacin Alhaji Lawan ya
yi kiran wani yaro mai suna Rabi'u do n ya raka shi gidan
Alhaji Bello marigayi ko da Rabi'u ya zo ya durkusa ya ce
gani, sai Alhaji Lawan ya ce Alhaji Abdullahi za ka raka
gidan Alhaji Bello marigayi, Rabi'u ya ce gidan su Fiddausi
ya ce E" Abdullahi ya mike su ka fita da Rabi'u suka shiga
motar da ya zo da ita. Bayan wani lokaci karami su ka isa
kofar gidan Alhaji Bello marigayi, sai suka y i fakin su ka
fito, Abdullahi ya ce da Rabi'u ya shiga ya yi sallama da mai
gidan, Rabi'u ya shiga ya yi sallama da Alh. Abba ya ce yana
fitowqa, lokaci kankani Abba ya fito ya duba sai ya ga Alhaji
sai ya mika masa hannu, suka gaisa bayan sun gaisa sai Abba
ya ce shigo mana don ya ganshi a mota don ya zata ci ne.
Abba ya shiga gaba Abdullahi yana binsa a baya, bayan sun
shiga Abba ya bude "Sitirum" ya ce Abdullahi, ya zauna,
bayan zamansa suka sake gaisawa lokacin Hajiya Gaji ta
kawo wa bako lemo da ruwan sanyi da kofuna masu kyau ta
dora a kan tebirin dake girke a gabansu, bayan ta ajiye sai ta
gaishe shi ya amsa, sai Hajiya ta haye kujera ta yi zamanta.
Alhaji Abba ya ce Bisimillah ga lemo, a lokacin ya zuba
masa a kofi, Alhaji ya dan sha kadan ya ajiye sannan ya cе
baku shaida ni ba ko. A lokacin ya ce kwarai kuwa. Ya ce ni
ne wan Hajiya Zainab marigayiya, ko da Alhaji da Gaji suka
ji haka sai suka yi musayar kallo gabansu'ya fadi sai dukan
uku-uku gabansu yake domin sun zata ya san irin wahalar da
Fiddausi ta ke sha haka Abba ya kanne ya ce kai sannau da
zuwa, amma na ji dadin zuwanka yaya iyali, suna nan lafiya.
Gaji maza ta kirawo Fiddausi ki ce ga Kawunta ya zo ta zo ta
gaishe shi, a lokacin Gaji ta mike jikinta duk ya yi la'asar ta
shiga ta ce maza Fiddausi ta kimtsa don kada ya gane ta zo ta
11
2
gai da Kawunta. Ka ji saboda iya makirci da kisisina, Hajiya
ta ba ta kaya masu kyau, wanda ita Fiddausi ta manta da
wadanna kayan tun da aka karbe aka bai wa Jamila, ko da ta
gama kintsawa ta dawo kamar ba ita ba.
Fiddausi ita da Hajiya Gaji suka isa tare koda suka isa
suka yi sallama aka amsa suka shiga Abba ya ce wa Fiddausi
zauna sai ta zauna ta gai da Kawunta. Ya yi murmushi ya
amsa ya ce kin manta ni ko ta ce E" a lokacin ya ce to ni
babanki ne da ni da mahaifiyarki cikinmu daya don haka sai
ki gane. Da Fiddausi ta ji haka sai ta yi murna ta yi wa Allah
godiya da ya kawo mata hanyar hutawa bayan wani lokaci
Abba da Gaji su ka bar Abdullahi da Fiddausi suna hira
Fiddau si ta ce, "Baba ni kuwa a wacce jiha kake aiki don ni
ban sani ba kuma su Hajiya ba su taba gaya min ba. Kuma ga
shi wata rana ina son na kawo maka ziyara ta ce don Alah
Baba ka ba ni "Address" dinka nan Abdullahi ya ba ta
Address" dinsa na gida, gurin aiki, kai har lambar wayarsa
sai da ya bata, Fiddausi ta yi masa godiya mai yawa, koda
suka sami lokaci mai tsaho su na hira sai ya ce to sai an
kwana biyu ni zan koma. Fiddausi ta ce to Baba sai an kwana
biyu madalla. Ko da su ka fito sai ya ce to kirawo baban naki
mana mu yi sallama. Nan ta yi kiran Abba ya ce za ka tafi ne
ya kawo kudi ya bawa Fiddausi, yayin da ta sa hannu biyu ta
karba ta yi godiya mai yawa a gare shi, haka Abdullahi ya yi
wa Abba godiya bisa karrama shi da ya yi, Gaji ta ce a sauka
lafiya ya ce amin. Nan suka fito da Abba da kuma yaron nan
da ya rako shi wato Rabi'u, sukai yo waje tare. Bayan sun
fito sai Fiddausi ta ce to Baba Allah ya kiyaye ya ce amin.
Lokacin sukai sallama da Alhaji Abba, ya shiga mota shi da
yaron da ya rako shi suka tafi gida. Haka Abba da Fiddausi
suka koma cikin gida bayan shigarsu Abba ya zauna,
Fiddausi ta mika masa kudin da Abdullahi ya ya ba ta nan ya
karbe ko tausayi babu suka raba shi da matarsą Gaji, ita
12
kuwa ko oho. Haka ma ta cire kayan jikinta ta mayar inda
suke kafin ma a ce ta cire, ba dan komai ba sai don gudun
kada a ce ta cire kuma gudun lafiyar jikinta. Ta ci gaba da
aikace-aikace kamar yadda ta saba. Shi kuwa Rabi'u da suka
isa gida, sai Alhaji Abdullahi ya ba shi Naira dari, domin ya
ji dadin rakiyar da ya yi masa. Yaro Rabi'u ya nifi gida yana
murna daman ya san zakin takardun yabo wai!!! shi kuwa
Alhaji Abdullahi ya shiga cikin gida ya yi sallama aka amsa
ya zauna, Hajiya ta ce har ka dawo ya ce, E" ya kama cewa,
amma kuwa Alhaji Abba yana da kirki sosai. H ajiya ba ta ce
komai ba haka dai suka yi ta yin hira, ya ce Fiddausi ta ce
wata rana za ta Katsina. lokacin da Hajiya Binta ta ce to
Allah ya kai mu. ashe kana da manyan baki Abdullahi ya yi
murmushi
Bayan gari ya waye Abdullahi, ya ce da mahaifansa shi
zai koma su ka ce to madalla, Allah ya yi maka albarka, ya
ce amin. Nan ya yi musu alheri mai yawa, suka yi godiya
Sannan suka yi mas addu'a cewar Allah ya kai shi gida
lafiya ya ce amin, Lamarinsu kenan. Amma a can gidan
Alhaji Abba kuwa watą, rana Alhaji Hamisu ya szo wajan
Fiddausi don ya ga lafiyarta bayan sun gaisa da Abba, ya ce,
Fiddausi tanan nan Abba ya ce tana ciki, sai nan da nan ita
Gaji ta yi kıranta, Fiddausi ta zo sai ta durkusa ta gai da
Alhaji Hamisu, ya amsa sai ya ce daman Fiddausi zuwa na yi
na gaya miki cewa yanzu banki babu kudi don kada ki ga y
anzu bana tambayarki. Fiddausi ta ce ai babu komai Baba,,
ya ce to ni zan tafi sai an kwana biyu. Ta ce Allah ya kai mu
ya yi sallama da su Abba ya yi tafiyarsa. To a gaskiya abin
da ya sa Alhaji Hamisu ya ce babu kudi a banki, to ya dai
fada ne, don ya san ko yaushe ya ba ta karbewa suke yi don
haka ya ce babu kudi, amma a lokacin Abba da mai dakinsa
ba karami bakin ciki suka yi ba. Domin ba karamin buri suka
ci ba a wannan karon ba. To haka da suka dangana. Bayan 13
1
e
wani lokaci wata rana sai aka wayi gari Jamilu bashi da
lafiya. Don kuwa ciwon gudawa ne yake damunsa, don dama
tuni na sanar da ku cewar tuni ya kamu da muguwar cutar
nan wato "AIDS" hankalin Abba da Gaji ya yi matukar tashi
nan da nan suka kai sh i HOSPITAL" don bashi magani ba
su san "AIDS" ba ta da magani ba, maganinta shi ne k abari.
Bayan an yi bmcike, likitoci suka ba da bayanin cewar
AIDS" ce a jikiusa don haka sai dai ya ji sauki amma babu
batun warkewa, nan ma hankalin Abba da Gaji ya sake tashi
sosai, nan dai aka ba shi kwanciya, Abba da Gaji ido ya raina
fata, gashi ba batun kudi daga Fiddausi hanya ta toshe, gashi
kuma an ce siyen magani za su dun ga yi, a wannan ranar dai
Abba ido ya yi zuru ga shi ya fada sai ka ce wanda ya yi
rashin lafiya. Haka suka kasance a halin bakin cii da takaicin
duniya mu dai sai mu ce a yi hattara jama'a, kun dai ji yadda
Abba ya fara takawa akasin mugunta futsarin fako, shi dai
Abba da a ce Fiddausi ce ta kamu da wannan cutar to da
babu wanda zai fishi murna da farin ciki to amma da yake
Allah ba azalimin Sarki bane, bai yi nufi ga hakan ba.
Wata rana bayan wani lokaci mai tsaho sai Alhaji
Hamisu ya ziyarci Fiddausi koda ya isa ya y i sallama aka
amsa ya shiga ya ga Abba ya tambaye shi jikin dansa ya ce
da sauki. Alhaji Hamisu ya ce da Fiddaausi daman zuwa na
yi na tambaye ki ko kinna da bukatar kaya, kasancewar ga
shi salla ta gabato, ko na atamfofi haka. fiddaausi ta ce,
kwarai domin bani da kaya yanzu. Ya ce kala nawa, ta ce ko
kala uku ma sunisa. A lokacin Abba da Gaji sai musaayar
kallo suke yi. abba yadda ka san ya buge Alhaji Hamu haka
yake ji, domin su so suka yi ya bawa Fiddausi kudi su karbe
su yi wa dansu magani, ka ji wawaye. Nan dai Alhaji
Hamisu ya yi sallama da Abba da mai dakinsa ya yi
tafiyarsa. Bayan tafiyar Alhaji, sai ga Jamila wasu sun biyo
ta har kofar gida suna sai ta ba su kudinsu in ita 'yar iska ce 14
to sun fita iskanci, ko da Abba ya ji hayaniya ta yi yawa sai
ya fito ya ga an ci kwalar Jamila nan ya ce ko lafiya, ya
tambaye su, wani mara kunya daga cikinsu, ya ce malam
babu ruwanka ko biya za ka yi ka bari sai an nuna mata
cewar ita karamar 'yar iska ce, ko da Abba ya ji ya ce ko ka
sanni k uwa, gayen ya ce ni ba so nake na sanka ba. Ya ce
kai wai me ake jira ne kawai ku tube kayan jikinta mu tafi da
su a maimakon kudinmu domin ba kira babu abin.da zai ci
gawayi, koda Abba ya ji haka sai ya ce Jamila mene ne haka,
me ya hada ki da wadannan 'yan ıskan, ta yi shiru Abba ya
ce nawa ne kudin, sai wannan,mara kunyar ciki ya ce Naira
dari biyu ne, kuma sai ka bamu sannan musake ta. Abba
ransa ya baci ganin Jamila ta soma lalacewa, nan da nan ya
shiga gida, Hajiya Gaji tana cewa lafiya ko kula da ita bai yi
ba, ya dauki kudi ya fita, sai da ya ba su kudinsu sannan
suka sake ta. Nan ba kunya haka Abba da 'yarsa suka shiga
cikin gida to ai dama dan kuka shi ke jawowa uwarsa jifa.
Abba dai abin duniya ya yi masa yawa, daman ka so naka
duniya ta kishi, ka ki naka duniya ta soshi, lalle bahaushe ya
yi gaskiya, bayan sun shiga sai Gaji ta ga Jamila duk a
yamutse, sai ta ce daman dake ake rigima. Jamila ta ce
wallahi saurayin Fauziyya ne sukai min wulakanci akan su n
ba ta kudin shat to ashe ba ta ba su ba, shi ne'daman ni sun
san sanmu tare, kuma ita wai sai ta ce kudin yana gurina.
Kuma yanzu ita Fauziyya din bata nan shi ne suka rike ni a
maimakonta. Kin ji dalili ni kuṁa na ce ba zan ba su ba, shi
ya sa tun da bani suka bawa ba. Ka ji karya amma da yake ta
gagare su, shi kansa Abba kasa yi mata komai ya yi domin
ya san ko ya yi mata fada ba ji za ta yi ba, daman an çe ice
tun yana danye ake tankwara shi idan ya bushe sai an karya
to Allah ya kiyaye mana yaranmu amin kuma ka shiryi
wadanda suka kauce amın.
15
ク
1
Alhaji Hamisu ya ziyarci marainiya Fiddausi don ya kai
mata kayan da ta bukata, wato na Salla, wato a dinka ya
kawo mata wasu atamfofi kala biyu na HOLAND kala daya
kuwa ta ENGLAND. Fiddausi ta ga kayan sai ta yi murna
sosai kuma ta yi wa Alhaji godiya mai yawa, Hajiya Gaji
bayan Hamisu ya yi sallama da su ya yi tafiyarsa ta bishi da
kallo. Sannan abba ya mikawa Fiddausi hannu ba tare da ya
yi mata magana ba ko da ta ga haka sai ta ce don Allah Abba
ka bar mini domin ba ni da k ayan sawa. Sun lalace, wasu ma
sun yage koda ya ji haka sai ya mike ya dauketa da mari ji
kake tas!!! Yayin da ya karbe kayan ya ce ba za ki sa ba, ya
hankada ta daki ya ce duk san da Alhaji Hamisu ya zo ki ce
da shi duk abin da yake hannunsa naki kina son ya dawo
hannuna. Domin na ga kin zama makira kin daina karba ko
bai zo ba ni sai na je na karbo haka dai Fiddau si t ci gaba da
kuka ta koshi inda Abba ya bawa Gaji ya ce ai sai ki bawa
Hajiya mai danyen kaya ta sayar. Sai Gaji ta ce haba gashi
yadda Jamila bata da kayan Salla ai sai a bata, Da yake Gaji
ta gama da Abba ai nan da nan ba tantama sai ya yadda ba
Jare da wani tunani ba, Allah SArki to kun ji fa hakkin
marainiya aka karba aka bawa diya. Babu ko tsoron Allah to
ai wata rana sai labari Allah ya saka mata.
Lamarin Jamilu kuwa da yake kwance a HOSPITAL
kuwa ya dan ji sauki don haka aka sallame shi kasancewar
dama ita wnnan cuta sai ta wulakanta ka tukunna sannan ka
ce ga garinku nan. Haka aka dawo da shi gida amma ba ya iya tafiya koda bukin Salla ya zo, sai Jamila ta caba ado da
kayan marainiya da aka kwace. Ta shiga cikin gari barikanci.
domin shi ne sana'arta. Fiddausi ta yi kukan kayan da ta
gansu a jikinta kamar idanunta zai zube haka ta kasance a
halin bakin ciki da takaici wanda ba zai misaltu ba.
Wata rana su Hajiya da Abba ba sa nan sai Jamilu da abokinsa, don ita kuwa Jaila ba a maganar ta domin sai ta ga
16
dama take kwna a gidan, haka Fiddausi ta hada ya nata-ya
nata amma Jamilu bai sani ba. Ta yi tafiyarta ta je inda
Mustapha yake, wato inda suke kwana, tana zuwa ta yi sa'a ta
tarar da shi, ya ce lafiya Fiddausi na ganki da kaya ko
aikenki aka yi. A lokacin Fiddausi sai hawaye ne yake zuba
daga idonta, Mustapha ya ce ai ba kuka za ki yi ba shin mene
ne yake damunki, ko ba k da lafiya ne sannan ta share
hawayenta ta ce Mustapha ka san dai irn halin da nake ciki,
to ni yanzu na gaji garin zan bari ko na huta don ni na gaji da
irin wannan mulkin kama karya, ka duba inda na koma ko
almajira ma ta fini, don haka idan.dai ba kasheni za su yi ba
ai ya dace a kyale ni na huta. Don haka na bawa kaina
shawarar na tafi ko na huta na murmure, Mustpha ya ce to
yanzu idan kin tafi ina zaki, Fiddausi ta ce ai ni bana
tsammanin zan sake dawo wa nan garin, sai Mustpha ya yi
shiru zuwa wani lokaci Mustpha ya ce to y anzu yaya
maganar aurenmu ko shike nan mun rabu, Fiddausi ta ce
haba Mustapha ai babu abin da zai raba ni da kai, sai dai *
mutuwa don haka in dai har za ka nemi aurena to sai dai ki
bini, Mustpha ya ce to yaya zan yi na biki tun da ban san.
gidan da zaki sauka ba, nan Fiddausi ta bashi address" din
da Abdullahi ya bata da kuma lambar wayar ta
TELEPHONE" Mustpha ya ce to na gode Allah ya kara
soyayya amin. Fiddausi ta ce ni kam na gaji da wahalar da ba
za ta kare ba, Mustpha ya ce gaskiya ina tausaya miki. A
lokacin Mustapha ya kai Fíddau si tasha, a inda sukai
bankwana ya ce sai ya zo, Fiddausi na hawaye Mustpha yana
ba ta hakuri da haka suka rabu suna masu bakin cikin rabuwa
da juna, haka mota ta yi lodi sai K.T., wato Katsina, bayan da
suka yi tafiyar awannı sai suka isa, bayan mota ta tsaya sai
mutane suka sassauka ita ma Fiddausi ta sauka, sannan ta yi
tambaya akan inda za ta sami motar FUNTUWA ta yi sa'a
wani mutumin kirki ya saka ta a mota, Fiddausi ta y i masa
17
e
godiya mai yawa, suka tafi bayan sun isa cikin gari sai
Fiddausi ta yi tambaya, ba ta sha wahala ba da yake shi gidan
fitacce ne a wannan uguwa, nan da nan ta sami gidan, ta
shiga ta yi salama, Hajiya Ni'ima ta amsa mata ta shiga ta
gaida Hajiya sannan Hajiya ta ce ki zauna ga kujera nan, ita
Hajiya tun da Fiddausi ta shigo ta shedata, to amma ta yi
mamakin ganinta a wannan matsay in don ta san mahaifinta
Attajirin gaske ne amma ga shi duk ta lalace kamar wadda ba
a barwa komai ba haka dai Na'ima ta ce da Fiddausi, Ina
mutanen gidan, ta ce sunan nan kalau, Fiddausi ta ce baki
shedani ba ko? Hajiya t ce ba ke ce Fiddausi ba, ta ce E" ni ce
Hajiya ta ce yaya su Baba da Hajiya, Fiddausi ta ce suma
suna nan kalau, a lokacin Fiddausi ta ce ina Baffa Hajiya
Na'ima ta ce yana "OFFICE" amma ya kusa tashi. A lokacin
Na'ima take cewa Allah Sarki yaya hakuri kuma na rashin
Hajiya, Fiddausi ta ce an gode Allah, Hajiya ta ce amma zaki
kwana biyu kafin ki koma, Kano a lokacin Na'ima ta yi
murmushi da yake mai son mutane ce, Fiddausi ta ce i dan
dai Baffa ya bar ni ba zan koma Kano ba. Hajiya ta yi m u
rmushi ta ce saboda me, Fiddausi ta ce haka nan don na gaji
da zaman can. Hajiya ta ce Allah ya sa ya barki, daman na
gaji da zama ni kadai sukai ta yin hira. Abin da ya sa
Fiddausi ba ta fadi dalilin zu wanta ba, don kada Baffan nata
ya zaci ko karya take yi ya dawo da i ta, Alhaji Abdullahi
waħnan mata Na'ima ita ce matarsa kuma su na da 'ya'ya
guda biyu, Fiddausi ba ta dade da zuwa ba sai ga su sun
dawo daga makaranta, su ka yi sallama aka amsa, su ka gaida
yayrsu Fiddausi duk da y ake ba su santa ba, wadannan 'ya'ya
dukkaninsu mata ne ta farin su nanta `BINTA" amma ana
kranta "ZAHARA'U" don sunan mahaifiyar mai gidan
kenan nasan mai karatu ba zai manta ba, ta biyun sunanta
SHEMA'U" kuma daman Allah bai ba su haihuwa da wuri
ba, kuma zancen da ake ma Na'ima tana da ciki tsoho.
18
Bayan sun dans ami lokaci suna hira sai Hajiya ta kawo
mu su abinci suka ci 'ya'yan ma suka ci kowa ya koshi.
Lokacin da agogo ya buga cewar karefe uku, sai Alhaji
Abdullahi ya tashi inda ya nifi gida, koda ya shigo ya yi
sallama, Shema'u ta tashi da gudu ta t ari mahaifinta a
lokacin ta yi masa sannu da zuwa, shi kuma Alhaji ya dauke
ta da yake shi mai son yara ne su ka shiga falo ko da su ka
shiga sai Alhaji ya ga Fiddausi sai ya ce saukar yaushe?
jLokacin Hajiya ta ce, ai kafin a yi sallar azahar ta zo,
Fiddausi ta yi masa sannu da zuwa ya ce yawwa, ya ce amma
fa kin sha hanya, Hajiya ta yi wa Alhaji barka da zuwa ya
amsa, sannan Fiddausi ta sakko daga kan kujera ta gai da
BAFFANTA. Hajiya ta kawo masa abinci ya soma ci, bayan
ya gama sai Alhaji ya tambayi Fiddausi yaya mu tanen gida,
ta ce suna nan lafiya, su ka fara hira ta ce zan dafe, alhaji ya
ce to madalla, ko da Fiddausi ta sami kwanaki a Katsina ta
murmure sosai kamanninta su ka dawo kai ka ce ba Fiddausi
ba ce, don komai na surarta ya dawo kuma hankalinta ya
kwanta. Sai abin da ranta yake so shi za ta ci.
Lamarin Alhaji Abba kuwa da suka koma daga unguwar
da suka tafi shi da Gaji sai ya nemi Fiddausi ya rasa,
hankalinsa ya yi mumunan tashi ba don komai ba sai don bai
riga ya karbi kudin daga hannun Alhaji Hamisu ba, ai da a ce
ya kar6 to da ko Fiddausi mutuwa ta yi to babu abind a ya
dame shi. Nan dai ya shiga nema ba ji ba gani, amma ina ko
duriyarta babu sama ta yi nesa da kasa. Ita kuwa Fiddausi
bayan komai ya dai-daita ta sami nutsuwa sai ta dau
"TELEPHONE" ta bugawa Alhaji Hamisu ta gaishe shi ya
amsa, ya ce daga ina kike dan na je gida ban same ki ba.
Kuma na tambayi Alhaji Abba ko ina kika shiga, ya ce bai
san inda kike ba. Fiddausi ta ce ai na dade rabona da su ashe
Mustpha bai gaya maka ba. Ai na sanar da shi, ai Baba yanzu
gidan wan Hajiya nake a nan Katsina. Kuma wallahi Bab a
19
na gaji da ma na ce wata rana zan bar gidan nan, kuma kayan
sallar nan da ka kawo min Abba karbewa ya yi ya bawa
Jamila, na yi magana ya yi min "DUKAN KAWO WUKA'
ni na fahimci so suke su kashe ni kwanana bai kare ba. Kuma
ta kara da cewa ni dai ba zan kara dawowa Kano ba. Kuma
Baba, Abba ya sani na sa hannu amma ba na gaskiya na sa
ba, don haka ko ka je kada ka ba shi komai nawa don tilasta
ni ya yi, domin a fadarsa yana son wai kudina na banki ya
zama nasa, don haka kada ka bashi komai nawa. Kuma Baba
na gode bisa rike amana ta da ka yi, kuma wata rana zan
kawo maka ziyara. Don duk inda na shiga ba zan manta, da
kai ba,. Alhaji Hamisu ya ce to na ji dadi kuma ya yi kyau da
kika za6i Baffanki kika dawo hannunsa. Kuma Allah ya yi
miki albarka. a lokacin Alhaji Hamisu ya ce ta ba shi lambar
wayar gidan Fiddausi ta ba shi saboda wata rana, nan Alhaji
ya rubuta saboda mantuwa, suka yi ban kwana, ta ajiye, koda
ta fito sai Alhaji ya ce wa Fiddausi wa take yiwa
"TELEPHONE" ne Fiddusi ta ce abokin Babana na yiwa,
Alhaji Abdullahi ya ce na ji kin ce ba za ki koma Kano ba.
Ko me ya sa a nan Fiddausi ta soma ba shi labarin Abba da
mai dakinsa da irin azabar da suke yi mata, ta ce ba ka ga da
na zo na zo ne a rame kuma na koma baka ba to wallahi
Baffa ba komai nene ya mai da ni h aka ba illa wahala da bautar
gidan nan. Kuma a lokacin da ka kawo min ziyara, ina tsoran
ko Abba yana laße ne shi ya sa ban sanar da k ai a halin da
nake ba. Domin hatta kayan da na sa na aro ne do min da
nawa ne amma saboda mulin mallaka aka bawa Jamila, suka
zama in dai bakon lasa ya zo, sai dai a ba ni aro, to a lokacin
da ka zo ma aro aka ba ni. Amma a yanzu da na ga wuya ta
yi wuya shi ne na taho nan. Domin na fahimci so suke su
kashe ni don dukiya ta tsone musu ido. Domin ni na san ba
inda za ni a karbe ni in ba nan ba. Kuma na san ba za ka kore
ni ba. Kuma ka ga duk wani harka dukiyata ya yi ficin-ficin, 20
komai aka ba ni sai ya kwace, ka ga duk sitturana an kwace
an bawa Jamila, Baffa hatta abinci ba a bani sai ya kwana,
kuma hatta makaranta sai da su ka haramta min ita saboda
aikin gida. Amma Jamilu har `AMURKA" aka tura shi Karin
karatu, kuma Jamila ita ma har karatu mai zurfi ta yi. Amma
ni kuwa ko oho, haka Abba zai sa su a mota ya kai su a
lokacin, amma da kafata ya hana ni zuwa. Ire-iren wadannan
wahalhalu su ne gajeru,