ba." Da Sadik ya
fahimci maganar babu gaskiya a ciki, sai ya ce "Shi
kenan sai abasu hakkinsu kawai." Ya ce "To ka kira
matar taka muyi maganar." Ya ce "To, amma abari
mutane su wate tukunna, sai tazo kuma tunda su
Inna suna nan sai ayi maganar har da su." Ya ce
"Shikenan babu matsala. A bari sai an watse daga
bikin.
Daga nan ya tashi ya fita. Gida ya dosa, ya
sameni ya fadamin duk yadda suka yi da Dagaci.
Naji dadin wannan abu sosai, domin kuwa dama ina
son in sayawa Inna gida ta dawo birni ta baro
kauye, dan haka sai na yanke shawarar in har ya
bamu gurin mu sai da shi zamu yi kawai.
74
Sharrin Jinni 3
Bayan an gama biki kowa ya watse, amarya ta
tarc a gidan mijinta. Sai Dagaci ya ce mu zo baki
dayan mu yana da magana. Muka zo har su Inna.
Bayan mun gaisheshi ne ya ke cewa, "Dama
abinda yasa ya taramu akan maganar gadon mu ne.
Shi yanzu ya ga ya dace ya bamu komai namu dan
gudun fushin Allah akansa. Saboda haka ya bamu
gonar mu da kuma gidan mu."
Muka yi ta murna sosai. Dama mun yi shawara
da Inna akan za'a sayar in ya bamu. Dan haka muka
ce a sayar da shi akwai a kawo mana kudi, mu za
mu saya anan.
Da jin haka sai Dagaci ya ce zai siya. Nan take
aka yanke masa kudi. Ya dauki alkawarin kawo
kudin nan da sati daya.
Pan kawo kudin ne na sami gida mai
kyan ayaa Inna nan kusa damu. Baba Tasallah
kad na sayaW ri shi yasa ba zan ce ta dawo nan
m ila aure take
din ba.
套
Sadik muna hira.
Ina kwance kaina bisa einуаrn Mamy wai A lekacin su Daddy basa nan suna gida a can za su kwana. n in Na dubi Sadik na ce "Sadik ni ko ma so kara karatu, zaka bari.9" Ya yi mumushi y
"Wacce makaranta kike son zuwa.9" Na cg "F.C.E
75
Amina A. Sharada
Ya yi murmushi. "Ban ki ki je ba, amma kin san ni
mutum ne mai masifaffen kishi, bana son in ga
abinda zai jawo mu dinga kai ruwa rana." Na ce
"Wallahi ba komai. Wai kai dan Allah ba ka yarda
dani bane ko me.?" Ya ce "A'a ba wai ban yarda da
ke ba. Kin dai san halina. Zan barki kiyi karatu,
amma da sharadin sai kin daukar min alkawarin ba
za ki kula kowanne namiji ba sai Malami. Shima sai
ta kai na dole.?"
Cikin doki na ce "Na ji na bi. Amma kaima ka
yi min alkawarin za ka cire zargi daga zuciyarka,
domin bana son ka dinga saka zargi a zo ana ta da,
wai Zabiya ta mance waka." Ya yi dariya. Ya ce
"Ai ni na yarda da ke dari bisa dari. Saboda haka ki
daina tunanin wani abu wai shi zargi. Abin da na ke
miki magana akai kawai ki zama mai maknun kai,
kuma dolene in yi miki wannan fadan, domin koda
a gidan iyayenki kike in za su yi miki fada ba zai
wuce irin wannan din ba." Na се "Hаka ne. To
yaushe zan fara zuwa.?" Ya yi dariya "In sun fara
siyar da form din zan sayo miki." Na rungume shi
sabida matukar farin ciki. Na ce "Shi kenan inna
fara zuwa sai in mayar da su Daddy gidan Mamy
ko.?" Ya ce "Eh, ki dinga kai su tunda sum ma saba
da Mamy dia.
*** 76
Sharrin Jinni 3
Kwanci tashi ba wuta. Tuni na fara zuwa
makaranta abina. Kullum Sadik ne yake kaini ya
aukoni. Ya kuma ajiye min lessing teacher a gida
yana koyar dani. Kafin meye wanann na san
Jubuwa da dama, wanda ada ban sani ba. Kuma
ayin kokarin dai-dai gwargwado. Sadik yana
guna farin cikinsa game da wannan, domin ya ga
tbin dana je nema shine a raina ba wasa ba.
Batun Nusaiba kuwa. Tuni ta kama aiki, kuma
sa mata rana da wani saurayi mai suna Salim,
-wanda suka hadu tun a makaranta suke ta rangada
yayyasu har ya ga,a ya barta da alkawarin in ta
gama za su yi aure bayan ta kama aiki.
Haka kuwa aka yi. Sai da ta fara aikinta aka sa
amar bikin. da lokacin ya yi aka rangada biki na
mamaki. A wannan karon mu biyu da Haula muka
yi ta kankajere gurin bikin. Sai dai ita Haula ba ta
sami sukunin cashe biki ba, asakamakon cikin dake
greta, wanda watan haihuwa har ua kama. Hakanne
ma yasa Mamy ta ce ya dan takaiya yawon domin
kr ta dinha wahala da yawa. To amma ina ba zata
iya ba, domin tana ganin kuma duk abin mu tare
- muke yinsa abin sha'awa. Mamy har cewa take yi
mun hade kai mun ya da ita domin in bana gidana
ia gidan Haula. Haka itama in har bata gidanta tana
gidana. Ko da yaushe muna tare. Duk abin da na
girka da rabonta. Haka itama duk abinda ta girka da
77
Amina A. Sharada
rabona a ciki. Kuma Ibrahim sai yazo gidana ya ci
abinda ya ke so san ransa. Haka ma Sadik sai yaje
gidansu ta bashi abinda duk yake so. Duk da Sadik
yana nuna mata shi sirikine tunda shine wa Ibrahim
ne kani.
Bayan an gama biki da 'yan kwanaki kadan
Haulatu ta haifi 'yar ta kyakkyawa mace. Batun
murna a wajen Sadik da Ibrahim ba magana. Ni
kam murna ba magana, musamman da ta haifo
mana 'ya mace, domin na fi son mu sami 'ya mace.
Shi kansa Sadik cewa ya yi "To Hamdiyya abin
nema fa ya samu ga 'yar budurwar ki nan kin samu."
Na ce "Ai dama wannan tawa ce sai dai ku sake
samo wata, amma wannan ta wace." Aka yi ta
dariya.
Da ranar suna ta kewayo aka rada mata sunan
Mamy na gaskiya. Wato Hauwa, muke kiranta da
Walida.
A sunan ma anyi buduri sosai. Komai namu iri
daya ne ad Haula. Munyi matukar ba da sha'awa
sosai, musamman ma ganin yadda kanmu ya hadu
kamar ba faccalaba.
***
Muna zaune da Haule a falona muna hira.
Walida na ta wasanta akwance. Shi kuma only one
yana kokarin daukarta ina ta faman hanashi, domin
78
Sharrin Jinni 3
bana son ya dinga daukarta domin kar ya ka da ita.
Sai ga Sadik nan a lokacin ina cewa "Only one ba
zaka daina daukar yarinyar nan ba sai ka kayar da
ita.?" Sadik ya ce "Ва па ce ki daina kiransa da
wannan sunan ba ne.?" Na ce "A'a da mai ya sa ka
sa masa. Tun da ka san ba ka so a kira shi sai da ya
zauna abakin mu sannan zaka ce ba za ka ce baka
so?." Ya ce "Ni dai na ce ku daina kiransa da
wannan suna." Na ce "Sai ka fada min dalilin da ya
a ada kasa masa wannan suna sannan zan daina
gaya masa." Ya yi murmushi. Ya dubi Haulatu dake
zaune kanta a sunkuye tana sauraron mu. Ya ce
"Kinji ta ko? Wai ita sarlom wayo." Haulatu ta ce
"Ai Yaya tana da gaskiya. Ni kaina zan so inji dalilin da yasa aka sa masa wanann sunan. Wato
Only one." Ya yi murmushi. "Bakin ku daya kenan
ko.?" Ta girgiza kai ta ce "Ko kadan ba haka
lamarin ya ke, ina son sani ne dai." Ya ce "Shi
kenan dama, ai ba wani abu ne mai zafi yasa na sa
masa ba, tun lokacin da bamu fahimci zaman mu ba
1e. Kin san san da aka haifi Daddy muna cikin
zaman doya da manja, sai bayan wasu 'yan lokatai
nciyata ta danyi sanyi, na dan sami nutsuwa da Hamdiyan aka sake samun cikin Only one don sai aji a rayuwata kamar shi kadai ne dana, a lokacin
na kan ganiyar gagarumin tashin hankalin da ban
san asalinsa ba. Haka kawai naji a rayuwata na
79
Amina A. Sharada
tsaneki ke da dan, ban san wani dalili da bashi da
tushe ayi dana. sanin hakan daga baya. Na gano
cewa ashe duk wannan makirce-makircen da ma
duk wata wahala da muka sha ta a baya sakamakon
SHARRIN JINNI nc." Na daga kaina na dube shi.
Muka yi murmushi. Na ce "Ato, ai kuma, Allah ya
fishi, domin ga yadda ta kare masa."
Haula ta'ce "To Allah Ubangiji dai ya rabamu
da SHARRIN JINNI."
Dukkan mu muka amsa da "Amin summa
amin."
KARSHЕ.
Wannan shi ne Karshen Littafin SHARRIN
JINNI. Sai kuma mu tara a na gaba. Wato wani
sabon littafin nawa in Allah ya so.
Daga mai kaunarku a kullum
AMINA ABDULLAHI SHARADA
(Mrs Ahmad Yusif Haďejia)
Maman Ahmed.
80
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
ZAZZAFAR KAUNA 1, 2 & 3
TALLAFIN KAUNA 1 & 2
SIRRIN JUNA 1& 2
HAKURI DA MASOYI 1 & 2
RASHIN HALACCI 1 & 2
TSAYA KALLON RUWA... 1 & 2
SHARRIN JINNI
PRINTED BY:
AL-AMIN B/PRINTING & PUBLISHING COMPANY
No.; 156 S/TITIN MANDAWARI KANO CITY. 08028411703
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels