hanya
zan ba shi kyautarsa wallahi."
Shima a fusace ya juyo ya ce "Banawa bane,
gara ma ki nemi ubansa tun dare bai yi miki ba." Ta
ke naji wata irin tsima ta kamani. Na ga falon na
juyawa, na fara juyi ni kadai. Tuni Sadik ya zuro da
55
Amina A. Sharada
gudu dan karfe only one daga hannuna domin in na
fada kansa sai ya yi mugun jin ciwo. Kafin ya iso
tuni an yi jifa da dan waje daya, ya yin da ni kuma
na kifc kasa baki a datsc, ban san meke faruwa ba,
domin bana cikin hankalina sam-sam.
Sadik ya suri dansa cikin bacin rai. Bai lura
ma da halin da na shiga ba ta dansa yake yi. Ya tafi
gidan Mamy dan gaya mata abin da na yiwa dan
domin a zatonsa nina ya da shi ina sani.
Ni kuwa Daddy ne kife bisa kaina yana kuka
"Umma ki tashi! Umma ki tashi!!" Ina ban san me
ya ke fada ba.
Mamy na jin abinda Sadik ya ce ta fada shi da
fada tana cewa "Ai kadan ma tayi maka, inda ace ni
ce abinda zan yi sai yafi haka. Kai yanzu in kana da
kunya ka zo ka ce min wani abu? Haba Sadik, wai
yaushe za ka yi hankali ne? Ace baka da wani
abokin gaba sai matar da ka ke aure? wallahi anyi
bitir!"
Nusaiba ta karaso ta ce "Yaya tana ita kuma
Hamdiyyar.?" Ya ce "Tana can akwance."
"Akwance.!?" Inji Mamy.
"Dukanta kayi.?" Ta kuma tambaya. Ya се
"A'a ni ban taba ta ba, gani nayi kawai tayi jifa da
shi ta fadi." Ta ce "Ai idan Hamdiyya batayi
hankali ba sai bakin cikin ka ya kasheta wallahi."
Ta dubi Nusaiba ta ce "Maza ki gani min abinda ke
56
Sharrin Jinni 3
faruwa." Nusaiba ta fisgi mayafi tayi waje da gudu,
ya yin da shi kuma ya zauna Mamy tana ta yi masa
fada akan abinda yake yi na rashin kyautawa.
Akwance ta sameni rigingine bakina na kumfa,
idona a tsaye kuma a juye. Da gudu ta fice bayan ta
janyc Daddy ta koma gida a rude tana kiran "Mamy
kizo kiga abinda take yi. Mamy ko mutuwa za ta ta
yi?"
Mamy ta fisgi hijabi ta fice, ya yin da shima Sadik
yabi bayanta a hanzarce. Nusaiba ita ma ta dafa
musa baya.
Suna zuwa suka tsaya a kaina suna sallallami.
Nan da nan Mamy ta yiwa Alhaji da Ibrahim waya
suzo maza gida babu lafiya."
Ba'a fi minti biyar ba sai gasu, domin dama
suna tare, kuma a hanyar zuwa gida suke. Suna
ganina Alhaji ya ce "Garin ya ya haka ta faru.?"
Mamy ta ce "Gashi nan shi ya jawo. Ina gida yazo
yake gayamin."
Alhaji ya ce "To jiran me aka yi, sai a tafi
asibiti. Suka dauk i sai mota. Daddy na ta kuka. A
lokacin shekararsa audu, muka dunguma gaba ki
daya.
Ta ke aka bani gado gami da sanya min karin
ruwa. Bayan gwaje-gwaje da aune-aune da aka yi
min, amma ko kadan ban dawo hankalina ba.
57
Amina A. Sharada
Likitoci sun kai bakwai akai kowa yana
kokarinsa, amma lamarin yaci tura. Haka suka yi
iya bakin kokarinsu, amma lamarin ya ci tura. Haka
suka yi iya bakin kokarin su suka barni, domin hankalina bai dawo ba, kuma har wani lokaci bakina bai daina fitar da wannan farar kumfar ba.
Ba wanda bai zubar min da hawaye ba har Alhaji. Shima Sadik a zaune yake ya yi tagumi yana tunani da dana sanin abinda ya yi min.
Kwana bakwai a asibiti, amma kullum gobe ya jiya babu sauki babu dalilinsa. Dan haka Alhaji ya yanke shawarar aje can kauye a fadawa su Inna domin in ma cutar ta tafiya ce sa ganni ba sai dai suji mutuwa kwatsam ba.
Dole Ibrahim me uake domin Sadik ba zai iya
zuwa ba, shima a 'yan kwanakin nan har ya rame, ya jeme, ko abinci baya iya ci. Kullum sai kuka, a
lokacin ne nadama ta zi masa, ya dinga tunanin wai
me ya sa ma yake min irin wannan halayen ne. Shifa bai ga abinda na ke masa ba. Da abin ya yi
masa zafi sai ya sa kuka kawai.
Ya nufi gadon da nake ya fara sambatun cewa "Hamdiyya dan Allah ki yafe min kar ki mutu. Wallahi na daina." Ya dan girgiza ni wai lallai sai in tashi mu koma gida shi, ya daina bata min rai. Alhaji ya rarrasheshi yana cewa abinda nake gudun maka kenan kaki ji Sadik, gashi baka ki gani
58
Sharrin Jinni 3
ba. Lokacin da na ke maka fada gani ka ke kamar
ba sonka nakc yi ba, gashi yanzu ka gani da
idonka."
Da kyar ya rarrashe shi ya fidda shi daga
dakin.
Da Inna da Baba Tasallah da gidan Dagaci
gaba dayansu suka zo dubani. Suna ganina abin ya
basu mamaki.
Inna ta ce "Ya kamata amai da ta gida ayi mata
maganin gargajiya." Alhaji yaki ya ce "A sauya
wani asibitin dai."
Hakja suka hakura aka sauya min asibiti. Can
ma din haka aka yi ta fama, kullum kamar da dai.
A haka har sati biyu suka shude, aka ga dai ba wani
sauyi da aka samu. Sai aka yanke shara akan akoma
dani gida kamar yadda Inna ta ambata.
Aka koma gida. Nan ma sai da su Alhaji suka
yi da gaske sannan Inna ya bari aka kaini gidan
Sadik. Alhaji shi ya bada shawarar asamo Malamai
masu rukiya, domin suna zaton wannan abu akwai
hannun mutanan 6oye, domin sun nuna tun farko ba
a sauraresu ba ne.
Haka aka samo Malamai su hudu suka dukufa
da karanta ayoyin rukiyya akaina, sai da suka yi
kwana uku suna aiki ba tsayawa, sai ko sallah da cin
abinci. Wani lokacin ma da dai-dai da dai-dai suke
zuwa basa barina su tafi baki dayansu.
59
Amina A. Sharada
Har izuwa yanzu babu wata alama da ta nuna
cewa akwai Aljanu a tare dani. Abun ya bawa kowa
mamaki, bar ma aka fara shawarar a hakura kawai
asake wata hanyar.
Sai daya daga cikin su ya ce muje mu gayawa
Malam yazo da kansa, domin a zaton da muke yi
akwai aljanin, kuma yana da matukar taurin kai,
shaidanin gaske ne."
Aka yarda da hakan, aka sami daya daga
cikinsu yaje ya gayawa babban Malamin nasu suka
taho tare
Da zuwansa ya kura min ido. Sai ya yi
murmushi ya ce "Zaka yi bayani yanzu, domin
kuwa GABA DA GABANTA." Daga nan ya cafki
dan yatsana babban na kafa ya matse da karfin
gaske, ya ce da sauran yaran nasa "Ku ci gaba da
karatu maza."
Ta ke suka dinga kwararo ayoyin rukiyya.
Suna cikin yi sai kawai aka ji wata irin kara da ta
firgita duk wanda ke gurin. Amma banda Malam,
domin su sun saba, kuma aikin su ne.
Take Malamin ya ce "Kayi magana me ya
kawo ka nan,?" Ya yi shiru. Ya ce "Kayi magana
mana.?" Nan ma shiru. Malam ya dubi sauran
Malam ya kauda kai. Tuni sun gane abinda yake
nufi. Suka fara kokarin kona Aljanin. Da yaji azaba
ta isheshi sai ya fara kara yana ihu. Malamin nan ya
60
Sharrin Jinni 3
ce "Ku kona shi in har ba zai yi magana ba. Suka
hau aikinsu.
Tuni ya ce su tsaya zai yi magana. Malamin ya
ce "Su dakata." Sannan ya ce "Daga ina ka ke?
Kuma kai waye.?" Ya yi shiru. Ta ce "Au raina
mana hankali zaka yi? Za fa mu kona ka yanzun
." Ya dubi sauran. Su kuma suka ci gaba da nan.
karatu.
Ya kuma kwala ihi mai razanarwa. Ya ce "Su
tsaya zai fada. Suka ki dakatawa. Sai da ya jigata
sosai sannan suka yi masa magana. Sannan ya amsa
musu a wahale. Karshe ma kawai sai ya fice ba tare
da sun ji wani cikakken bayani a wajen sa ba.
Malamin ya ce "Ya fa gudu da ya ga halaka."
Alhaji ya ce "To fa lafiyar ita yarinyar.?" Malamin
ya ce "Ai shine, kuma zamu binciketa yanzu mu
gani domin bamu tantance ta inda ya fita ba."
Suka sa Sadik yajo ya jijjigani da karfi. Ya
kira sunana a hankali. Na bude ido gami da
amsawa. Na jima ina jujjuya ido kafin in shaida
mutane. Daga can na gane Sadik. A firgice na tashi
na matsa daga inda yake, na ce cikin kuka "Ina
Daddy.?" Aka ce gashi. Na kama Daddy na
rungume ina kuka kawai. Ba wand abai tausaya min
ba. Su Mamy cewa suke yi "Kiyi hakuri Hamdiyya,
in Allah yazo za'a rabaki da wannan alakakai din.'
Na yi saurin dago kaina na kalli Mamy, na ce
61
Amina A. Sharada
"Wayc.?" Ta ce "A'a ba komai, kije ki kwanta ki
huta baki da lafiya." Na ce "To." Na koma kan
kujera. Malaman suka ce za su tafi, da zarar anga ya
komo sai a sanar da su da wuri."
Su Alhaji suka yi musu godiya mai tarin yawa,
aka sallamesu suka tafi. Suma sun jima a gidan
sannan suka tafi ba tare da sun sanar dani abinda ya
faru ba.
Sadik na zaune ya hada kai da gwiwa yana ta
tunani. Sai naje kusa da shi na zauna, na kalleshi
idanuna taf da hawayc, na ce "Yanzu Sadik haka
zaka yi min? Irin sakamakon da zaka yi min kenan?
Ka tuna fa saboda kai na kusa na salwantar da
rayuwata, amma ka rasa wanda zaka yi wa sharri sai
ni. Wai ka ce Daddy ba danka bane? Kai ko wanne
irin laifi nayi maka haka har da zaka yi min irin
wannan mummunan sharri.?"
Kansa a sunkuye ya ce "Kin ga ni dai ban ce ki
sake tayar da wannan maganar ba. Ya ya abu ya
wuce sai ki dinga tada shi.?" Na ce "A wajen kane
ya wuce, amma a wajena bai wuce ba" Ya ce
"Haba Hamdiyya, na ce kiyi hakuri kın k, to ya ya
kike son in yi miki ne.?" Na yi shiru (an na ce
"Wannan fa magana ba ta shiru ba ce, saboda haka
sai na bari gani ga ka ga Mamy sannan in fada." Ya
ce "To shi kenan. Ni kuma zan ce sharri kika yi
min." Na ce "Koma mai zaka ce sai na fada in Allah
62
Sharrin Jinni 3
ya so." Ya yi murmushi. "Su ma ba za su yarda ba."
Na ce "Ai sun ga alama tun daga farko."
Ya lakuce min hanci. "Baki da hankali, kina so
ki kuma jawo mana wata rigimar daban." Na cе
"Wacce rigima ce kuma." Ya yi murmushi "Ai ke
sai dai a lalla6a ki, domin duk wanda ya takura miki
na fuskanci ba zai ga da kyau ba." Na tabe baki na
ce "Na fahimci kaima ka shiga canfe-canfen nan na
tsofaffi." Ya ce "Wanne irin canfi kuma banda
wanda na gani da idona? Wannan ai ya wuce tunda
har jikina ya gaya min." Na ce "A'a ba zancen wasa
ba Sadik, wai dan Allah akwai wani abu da yake
faruwane da ni sabanin wanda na sani.?" Ya cе
"Akwai kuwa."
Take ya warware min komao na dangane da
zuwan Aljanin nan kaina, da kuma yadda aka yi ta
fama da shi.
Na yi matukar mamaki, na yi tagumi kawai
zuciyata cike da fargaba. na ce "Wato dai tana kasa
tana dabo kenan ko.?" Ya ce "Ato daga dai yanzu
ko wanne lokaci zai iya dawowa, domin guduwa ya
yi bai tsaya ya yi magana ba."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un." Abinda na
ce kenan. Take hawaye ya zubo min. Na ce "Kai ni
dai na shiga uku. Take mafarkin da nayi ya fado
min a lokacin da ina asibiti. Na yi shiru kawai ina
tunani. Sadik ya rungumeni ta baya, ya ce "Ki
63
Amina A. Sharada
manta da komai, Allah zai yi mana maganinsa ne."
Na yi murmushi, "To Allah gamu gareka."
Yanzu komai ya zame mana kamar da,
tsakanina da Sadik kamar wata husuma bata taba
hadamu ba. Ya dawo da al'amuransa gareni. Nima
kuma na watsar da komai, tunda naga yanzu Sadik
yana son Daddy fiye da kowa, kullum suna tare
kamar ya hadiye shi. Yanzu sun ma fi rigima da
Sadik karami, domin in mun shiga dakinsa zai masa
ta'adi sai ya koreshi, kuma sai ya gudu waje yana
dariya, in kuma barna ya yi masa ya dan dakeshi ya
yi kuka sai in ce "Kayi hakuri, ka san sha'anin
mulki hawa da sauka ne. Wannan karon Daddy ne
ya dane kujerar."
In na fadi gaka Sadik ya yi ta dariya. Hatta
unguwa tare suke tafiya, dinki iri daya, hula iri
daya, kai komai nasu iri daya. Tun Daddy bai saba
da shi ba har yazo ya saba. A yanzu kwanciya ce
kawai take rabasu, itama din sai ya yi barci nake
daukeshi in kai shi makwancinsu. A takaice dai shi
ya komo mowa, ya yin da little ya dawo bora.
***
Kwanci tashi ba wuya, domin dai an kusa
daura aurer Tbrahim da Haulatu. Ana ta shiryeshiryen biki, duk da ta zama faccalata kawancanmu
sai abin da ya yi gaba, domin a yanzu ne ma muke
64
Sharrin Jinni 3
Eawance, duk abinda ta saya na auranta dangane da
wanda zata saya da kanta yana gidana, tare muke
fita kasuwa ta siyo, in sayo, mu hadu mu Soye ba
wanda ya sani. Lefenta ma tare muka hado, ta kuwa
tubure nima sai an hada min lefe, na ce "A'a bena
so." Ta ce "Wallahi baki isa ba." Ibrahim ya ce "Ai
uwargida ce sai a hada mata."
Suka yi ta zolayata shi da Sadif. Da yake duk
inda za su suna tare, muma muna tare abinmu. Sai
tazo tayi kwanaki a gurina ba tare da gidan s
Ibrahim din sun sani ba ma
Yau ce ta kasance ranar daurin aure. Dangi
daga ko ina sun hallara maza da mata. Da yake
zarcewa zaayi da biki duk mutanen Kauye sun zo
mazansu da matansu. Da yake gidan Alhaji na da
girma, sai ya kasance komai a wadace ba matsuwa.
Mata suna bangaren su, mazama haka. Ni kuma ina
can gida da tawagata muna ta faman namu sha'anin
a nawa Gangaren. In kuma mun gaji da nan sai in
debosu mu dunguma gidan Mamy.
Sadik ma ba zama shi da ango, suna ta faman
shirye-shiryen daurin aure. Duk abin nan Daddy na
manne da shi, in na ce ya kawo min shi baya baya
yarda. Sai na kyalesu suna tare, ko yana gurin
Ibrahim ko yana gurin Sadik. Har nake tsokanar
Ibrahim ma da cewa sun sami dan zaman daki
Ibrahim ya ce "Yaushe za ku yarda ku bani, yadda
65
Amina A. Sharada
kuke makale da su ba kwaso ya matsa daga gareku."
Muka kalli juna da Sadik muka yi dariya muka tafa.
Ya ce "Rabu da shi maga yadda zai yi nasa kawa zucin."
Shi ko Sadik karamin yana gurin Mamy, duk
wannan kujiba-kujiban da shi take yi. Shi yasa nake
yawo na zagargar abina. Hatta su Inna da Baba
Tasallah suna gidana sun zo bikin.
Yau ranar lahadi, ita ce ranar da aka daura
auren Ibrahim da Haula a can garin mu, wato
Kauyen Zanzari.
Bayan an dauro auren an dawo su Dagaci suka
biyo bayan angwaye. Jerin gwanin motoci kuwa
abin ba magana, har nan gidan Alhaji. Falon Alhaji
cike da manyan baki 'yan uwa da abokan arziki
masu zuwa taya shi murnar auren dansa da ya yi.
Mu kuma muna falin Hajiya ana ta faman shagalin
biki da murnar daurin auren, mun cika makil,
domin su Inna ma nan suka taho. Su Aunty da
kawata Safiyya ta gudo daga gidan kawaye wai
wallahi ta gaji da zirga-zirga. Inna tayi mata tsiya.
Na ce "Ashe ba zaki fatin ba gashi a Hotel din da
kike so za'ayi. Wato CONG COНТ НОТEL." Ta ce
"Zuwa kai. Ta6dijam! Ai damu za'a rabashi." Na ce
"Yar iska, ko ki fidda miji abu ya gagara." Та се
"Wa ya ce miki ban fidda miji ba.?" Na ce "A gidan
uban wa kika fitar.?" Tayi dariya. "Sorry Aunty na
66
Sharrin Jinni 3
yi miki karya." Na ce "Wacece Auntyn ta ki.? Ke fa
baki da mutunci." Ta cc "Ai gani nayi har kinyi
haihuwa biyu ni ko auren banyi ba. Nan gaba kuka
kara ta uku wallahi Mama zan ce miki."
Na kai mata duka. Muka fito falo da gudu
muna dariya. Sai ga Sadik yace "wanna wanne irin
abune wannan kuma? Sai ka ce yara.?" Na ce "Wai
ce min take Aunty." Ya yi dariya. Ta ce "Wallahi
Sadik ta tsufa, gara ka sami wata 'yar shana-shana
ka aura." Ya ce "Haka ko za'ayi Safiyya. Ki samo
min yarinya karama." Tayi dariya, "An gama
Sadik." Na ce "Za ki ci ubanki wallahi. Ki
kiyayeni." Suka kwashe da dariya. Na ce "Na san
irin zaman da zan yi da ke." Ta ce "Afuwa kawalli
da wasa na ke." Na ce "Kin tsira." Muka yi dariya
baki dayan mu. Ta karbi Daddy daga wajen Sadik
tayi gaba ta barmu a gurin. Na nemi guri ha zauna
na ce "Wash Allah Sadik! Kaina ciwo yake yi." Ya
ce "To tashi mu koma gida." Na ce "A'a, ai da nan
da can din duk daya ne." Ya ce "To muke wurin
Mamy ki karbi magani." Na ce "To." Muka fito
tare.
A sako muka sami Mamy a zaune tana lallaба
Sadik karami yana son yin barci. Sadik ya ce
"Baiwa Hamdiyya maganin ciwon kai." Tа се "Anya kanki ne ke ciwo? Sannu Allah ya sauwake.
Wallahi hayaniyar bikice. Bari in kawo miki
67
Amina A. Sharada
magani." Ta mike ta tafi dauko maganin. Ni kuma
na kwanta ina hutawa. Sadik na zaune, sai ji ya yi
na kwala Kara. Ya zaburo da guru gurina ya ga
abinda ke faruwa.
Tuni na koma gidan jiya. Wato bakina ya datse
yana kumfa, idanuna a kafe. Nan da nan dakin ya
cika da jama'a dan jin karar da na kwala.
Mamy kuwa bata san ma yadda aka yi tazo
dakin ba, ko maganin bata dauko ba. Nan da nan ta
tura aka fadawa Alhaji, ya taho da sauri. Yana ganin
halin da na ke ciki sai ya fita da sauri. Bayan ya kira
Sadik.
Basu fi minti arba'in da biyar ba sai ga su da
Malaman nan da suka taba yi min rukiyya. Suna
ganina sai suka ce a dawo dani falo. Cak Sadik ya
daukeni ya ajiyeni a tsakiyar falo.
Nan suka dukufa kan yi min rukiyya. Amma
Aljanin nan ko gezau bai yi ba. Hasalima sai ya fara
bugani da jikin kujerun falon yana gurza kaina a
kasa. Kafin ka ce meye wannan? Ya yi min jinajina. Hankalin kowa ya tashi a gurin. Mata sai kuka.
Sadik ransa ya 6aci, idanunsa suka yi jajawur
kamar gaushin wuta. Ya dubi Aljanin ya ce "Kai
sakarai mara zuciya, ai wannan abin da kake yi ba
so bane, kuma yanzu na tabbatar kai matsoraci ne.
In þa dan haka ba ka yi magana mana a san ko kai
waye, kuma daga ina ka fito? Kuma meye hadinka
68
Sharrin Jinni 3
da ita, in ma fafatawa ne sai mu yi domin aga mai
karfi tsakanin ni kai." Ya yi shiru yana ta huci
kamar kububuwa.
Aljanin ya yi dariya, ya ce "Yauwa jarumin
maza, yanzu na san cewa kai namiji ne, kuma zamu
kara da kai akan Hamdiyya."
Malaman nan suka ce "Ba za ka fita ba
kenan.?" Ya ce "Ai gurin zamana ne nan." Suna
cikin haka sai ga daya babban Malamin nan da ya
taba zuwa ya fara illata Aljanin a wancan karon.
Yana zuwa ya damki goshina ya fara karanto ayoyi
masu zafin gaske. Ya ce da sauran suma su kifu
akansa." Nan da nan sai ga Aljanin nan ya fara ihun
wahala yana jin azaba. Gashi duk sun toshe wata
kafa da zai gudu.
Da dai yaji zai hallaka, sai ta ce da su su
dakata zai yi bayani." Sai da suka kara wahalar da
shi sannan suka tsaya. Ya yin da shi kuma ya soma
bayani dalla-dallah kamar haka.
"Ni sunana Shu'umanu dan Shaidanatu. Ina
zaune ne a wani daji mai suba Darbuba akan dutsen
Jal'ura. Ina da shekaru dari bakwai da arba'in da
biyar a duniya. Asalin haduwa ta kuwa da wannan
yarinyar ba ita na taba so ba. Akwai wata kakarya ta
bakwai a cikin iri-irin danginsu wandanda suka
gabata tun zamanin da can kimanin shekaru dari
69
Amina A. Sharada
uku da sittin. Ita wannan mata Allah ya bata baiwar
kyau da babu kamarta a wannan lokacin.
Tun da na ganta na jarabtu da kaunarta, ya yin
da wani dan sarkin wannan zamanin shi ma ya
kamu da ciwon sonta. Ba yadda banyi ba in raba su
na kasa, domin irin tsarin dake jikin su. Haka itama
na yi-nayi in shige jikinta na kasa, domin mutanen
wannan lokaci basu da shagalalliyar zuciya kamar
na wannan zamanin, dan haka har ta koma ga
mahaliccinta ban sami damar rabar jikinya ba.
Na yi bakin cikin wannan abu. Tun daga
wannan lokaci nake bibiyar danginsu daya bayan
daya ko zan dace a cikin irinsu in sami kamarta.
Ban samu ba sai akan Hamdiyya. Tun tana
jaririyarta nayi ta lura da ita domin naga ta debo
yanayi da ita waccan tsohuwar budurwar tawa.
Na shiga lura da ita sosai gudun kar wani abu
ya taba min ita. Tana girma kamaninta na kara
fitowa. Sai da ya kasance babu wani banbanci a
tsakaninsu. Nan zuciyata ta afu akan ta. To itama na
auna babu damar shiga jikinta saboda akwai yanayi
na wancan tsari a nata jikin. Dan haka na kyaleta
ina dai lura da ita har lokacin da ta isa munzalin
mutane. Shi ne na shiga bayyanar mata kaina a
yanayin dan Dagaci, wato Abubakar (Sadik).
Dukan da ake yiwa 'yan matan nan ma na kauye ba
kowa bane face ni. Domin na sha alwashin hukunta
70
gharrinJinni 3
wani mai sha'awar tabata. Ko da wasa ma uwar
ta haifeta ma in zata iya yunawa a duk lokacin da
doketa in tayi mata ba dai-dai ba sai taga ba daiiba. A takaice dai duk abin daya faru a garin nan
ne ummul'aba'isi. Ni nayi sanadin kulla siyayya
akanin Sadik da Hamdiyya domin su shagala in
mi damar shiga jikinta. Amma ban samu ba,
Jomin iyayensu suna tsaye a kansu har soyyyarsu ta
ama gaskiya, wadda ba zata kankaru ba. Ni ne
Juma na taimaka mata a lokacin da ta tafi nemansa
akin dajin nan ta shallake hadura. Shi kuma ni na
uro wannan micijin ya sareshi domin rama mata
vahakar da ta sha a wajen nemansa. Ni ne wannan
maharbin da ya taimaka musu, kuma nine na
daukosu amota na kawo su gida. Bayan anyi auren
anaga zama ya yi dadi, sai na shiga hadasu, domin
gu bata tunda naga suna more rayuwarsu ba abin da
ya damesu, ni kuma ina fama da bakin cikin
ashinta. Sai na dinga kammanni da Ibrahim domin
inyi amfani da wannan damar in jefa zargi a zuciyar
Sadik. Na kuma yi nasarar yin hakan, bayan kuma
n farkon tariyarsu na hansu kwanan farin çiki a
wannan ranar.
Da ta haihu sai na cusa kiyayya da zargi a
uciyar Sadik domin ya ki dan da ya dinga
sammanin na Ibrahim ne. Haka kuma aka yi,
l'amarin da ya haddasa musu tsananin 6acin rai da
71
Amina A. Sharada
rigima. Na yi sa'a na sami yadda na ke so suka
dinga tafka rigima tun ba'a sani ba har aka sani.
Kuma ya mareta na rama mata. Na kuma dinga
tunzura masa zuciya domin kar su sami zaman
lafiya bare su dinga farantawa junansu. Nan ma nayi
nasara samun haka, har ya ce da yaron ba dansa
bane adai-dai lokacin da na samu damar shiga
jikinta.
Wanna shine takaitaccen tarihina da dalilin da
ya sani shiga jikinta. Kuma ina rokonku da kar ku
konani ku kyaleni, ku kyaleni zan fita, kuma na yi
alkawarin ba zan kara shiga jikinta ba. Kuma na
dau alkawarin in har wani ya musguna mata zan
dau mataki akansa."
Malaman nan suka ce "A'a ba wannan ake so
ba, sai dai ga mugaye masu muguwar manufa
akanta ba kowa ba." Ya ce "To naji nabi." Suka ce
"Kayi alkawari ba zaka sake shigarta ba." Ya ce
"Nayi." Sai da suka nanata sau uku. Sannan suka ce
ya fita ya kyaleta ta huta domin ta galabaita." Ya ce
"To zai fita." Suka ce "Ta ina?". Ya ce "Ta baki."
Suka ce "To kafin ka fita muna so mu san wanne
addini ka keyi.?" Ya ce "Ni bani da addini." Suka ce
"To muna so ka karbi addinin musulunci, domin
shine addinin gaskiya wanda Ubangiji ya yi umarni
da abi." Ya ce "Naji ina so a shigar dani cikin
wannan addini na musulunci."
72
Sharrin Jinni 3
Ta ke suka biya masa kalmar shahada ya
maimaita. Suka ce ya sauya suna, domin wan can
sunan nasa ba suna ne da musulunci yazo da shí
ba." Ya ce "To ai shi bai san irin sunan da za'a sa
masa ba. Amma in Sadik ya yarda tun da ya zama
abokinsa ya zaba masa suna." Take Sadik ya ce
"Sunanka Usmanu." Ya cc "Yaji ya karba." Sannan
ya yi musu sallama.
Da zai fita ya dubi Dagaci ya ce "Ka mikowa
Hamdiyya gadonta da ka cinye, domin ba halak
cinka bane. In kuwa kaki ji ba kaki gani ba." Yana
gama fadin haka ya fita. Suka ji shiru. Guri ya yi
tsit ana ta mamakin abin da ya faru.
Ni ko nayi shiru ina tsakiyar mutane ban san
me yake faruwa ba. Naji dai ana yi min sannu. Na
mike da kyar zan fita. Sai Sadik ya ce in koma
gidan maza yanzu yana zuwa." Na ce "To." Na tafi.
Anan na bar su Inna.
Ina zuwa gida nayi wanka na shirya nayi
kwanciyata. Jim kadan sai ga Sadik ya shigo da
Daddy ya ce "Dama binda yasa nake son mu kaďai
ce shi ne. A bayanin Aljanin nan na karshe, ya ce
wai Dagaci ya biya ki hakkin ki na gado, shi ne
nake son jin dama akwai wani hakki naku da
Dagaci ya karba.?" Na yi murmushi, na ce "Ya fi
kyau dai kaje ka same shi ya yi maka bayani cikin
nutsuwa." Ya ce "Shi kenan bara inje." Na ce "A'a
73
Amina A. Sharada
ka kyaleshi sai an gama biki kaje har gida ka same
shi ya yi maka bayani." Ya ce "Ina ai ba zan iya
jurcwa ba. Ni yanzu zanjc." Yana gama fadar haka
sai ya tashi ya fita.
Ya yi sa'a kuwa dakin da Dagaci yake ba
kowa, daga shi sai Alhaji. Ya gaishesu, sannan ya
ce "dam abinda yasa na zo, naji aljanin nan ya yi
maka magana ne ban fahimce ta ba." Da Dagaci yaji
haka sai ya ce "Maganar gadon nan ce fa ta bayan
gari. Kai ma ka san da maganar." Sadik ya ce "Ai ni
cewa dani kayi siyar maka suka yi." Dagaci ya ce
"A'a ni ban gaya maka haka