kawai ta gyara ni
zanyi mata afuwa."
Alhaji ya ce "To ke kinji, tunda yaki fadar
laifin da kukai masa sai ki kintata ki gyara kinji
ko.?" Na ce "Wallahi Alhaji ba wani laifi da nake
masa, kuma yanzu a gabana ne ya fadi wannan, in
ka tafi ci gaba zai yi. Gara kawai ayi ya kare."
Alhaji ya ce "Kaji abinda tace, kuma ya
kamata ace ka bayyana mata laifinta dan a kori
gaba." Ya yi shiru. Sai Alhaji ya ce da Nusaiba "Ke
tashi daga nan. Ana magana kin tsare mutane da
ido." Sum-sum ta mike ta fice. Sannan Alhaji ya се
"To sai kayi mata bayani."
"Shi kenan kawai Alhaji, zan yi mata bayani,
amma sai ni da ita." Ya ce "To shi kenan, ke kinji,
amma ki kiyaye gaba, in har kinyi masan. Haba
karku bani kunya mana, ku duba fa kuga irin
gwagwarmayar da kuka sha, babu hankalin wanda
baku tasa ba, amma daga baya kuma tun ba'aje ko
ina ba zaku fara raba abin fada? Ya kamata kuyi wa
kanku fada tun kafin ma ace wani ya sani. Kai
Sadik kaine babba, in kaga ba dai-dai ba ba shiru
zaka yi ba ka kullaceta, sai ka sanar mata tunda
38
Sharrin Jinni 3
wuri ta gyara. Gashi Allah ya bada rabo, nan gaba
ba'a san iyakacin ba, in har kuna wanann in kun tara
yara suka yi wayo sai ku dinga rabawa taranku
hankali, in suna ganin bakwa zaman lafiya, suma
kansu ba zai taba haduwa ba, kuma ba za su taба
samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba. Saboda
haka ku saita halayyarku tun daga yanzu, kar kuzo
kuna da kun sani gaba."
Dukkanmu muka yi kasake muna sauraronsa.
Sai da ya kawo nan ya mike. "Ni zan koma. Ina
dada jan kunnenku karku sake." Muka ce munci in
Allah yaso haka ba zata sake faruwa ba." Ya yi
mana sallama ya fita. Sadik ya rakashi sannan ya dawo.
Tun dafa fadan da Alhaji ya yi manalan
yanzu Sadik ya dan sauko kadan, dominn nayi
abinci zai ci, sannan in na gaisheshi zai amsa. Duk dabaya tsayawa ya yi hira dani, kuma baya shiga dakina, Kowa makwancinsa daban ne. Duk da haka ban damu sosai ba, tunda har awo yake kawoni, in
na gama ya daukeni ya dawo dani gida. Kuma da ya
samu aikin gwammanti ya sanar dani har lokadin da zai fara zuwa. Na yi farin ciki sosai.
***
Mutanen da suka tsare Sadik a dajin nan tuni
an gurfanar da su gaban shari'a domin hukuntasu.
39
Amina A. Sharada
Take Alkali ya yanke musu hukuncin dauri shekara
biyar-biyar da tarar kudi ta dubu dari biyu-biyu,
saboda irin tsare Sadik din da suka yi, suka rabashi
da gida kuma suka gana masa azaba.
Suna jin haka suka ce aiko sai dai a hada har
Ibrahim, domin duk abinda ya faru shi ya sa su.
Take kuwa mai shari'a ya bada umarni da Ibrahim.
Aka kuwa zo aka kama shi aka tafi da shi.
Abin bakin ciki, sanadi kadan ya jawo masa
shiga babbar matsala. Alhaji da Mamy damu baki
dayanmu munyi bakin cikin abin da ya faru.
Sabanin Sadik da naga abin ko a jikinsa. Ya dai
jajanta a gaban Alhaji, amma a bayan idonsa murna
ya dinga yi komai ya sa oho.
Kwanci tashi cikina ya isa haihuwa. Dan haka
Nusaiba ta dawo gidana da azma ko da haihuwar
zata zo cikin dare, ta taimaka min mu tafi asibiti.
Haka kuwa akayi, domin dare nayi bayan
zuwanta da kwana biyu, sai Allah ya kawo nakuda.
Da sauri na tasheta. Ta je ta sanarwa da Sadik a
dakinsa.
Ya fito da mota muka yi asibiti. Bamu jima da
zuwa ba Allah ya kawo haihuwar. Nan da nan na
haifi dana sankacece kyakkyawan gaske. Kowa ya
ganshi ya ga Sadik, domin suna matukar kama
sosai. 40
Sharrin Jinni 3
Tun a daren Nusaiba ta gayawa su Mamy.
Kuma a daren suka taho. Anna muka kwana da su.
Shi ko Sadik da ya kawomu gida yayi komawarsa
abinsa. Wannan abu ba karamin bakanta min rai ya
yi ba. Hatta Nusaiba sai da taji ba dadi. To amma
sai taja bakinta ta tsuke gudun kar ta nuna bacin
ranta. Hankalina ya kara tashi fiye da da.
Su Mamy suka zo suka ga jariri har Alhaji ya
tambayi inda Sadik yake. Nusaiba ta ce "Ai tunda
ya kawo mu bai dawo ba har yanzu." Ya ce "To ya
san ta haihu.?" Ta ce "A'a bai sani ba."
Take Alhaji ya yi masa waya ya sanar da shi
haihuwar. Ya ce kuma tun daran suke a asibitin."
Sadik ya ce "To gashi nan yana zuwa."
Shiru har kusan azahar bai zo ba. Shi ko dama
Alhaji tafiya ya yi tun da safen ya bar su Mamy da
Nusaiba. Sai Mamy ta ce "Tunda lafiyata kalau a
sallamemu. Nan kuwa aka bamu sallama muka taho
gida.
Tun a hanya nake ta faman kuka ina rokon
Mamy ta kaini gidanta, ni kar a kaini gidan Sadik.
ta ce "Bani da wannan izinin sai kiyi hakuri in
munje ai za'ayi masa fada ne."
Akan dole na hakura muka isa gidan. Muka
kuw ayi sa'a yana nan a zaune a falo ya yi tagumi.
Yana ganinmu sai ya tashi ya gaishe da Mamy. Zai
shige ciki sai Mamy ta ce ya dakata tana son
41
Amina A. Sharada
magana da shi. Ya komo ya zauna yana sauraron
abin da zata ce da shi Fa ce nima in dakata. Nima
na zauna.
Ta karbi jaririn daga hannun Nusaiba, ta се
"Wai wannan waye.?" Ta tambaye shi. Kallo daya
ya yi wa jaririn ya ce "Jinjiri ne." Ta ce "To dan
waye.?" Ya sunkuyar da kai. Ta ce "Ba za ka fada
ba.?" Ya ce "Danta ne." Ta ce "Dan wa."
"Dan Hamdiyya." Ya yi shiru. Ranta a bace ta
ce "Da wa kuma?". Y ace "To wai Mamy wannan
tsarewa da akai min ni fa ban gane haka ba. Haka
kawai a dinga takurani.?" Yana gama fadin haka sai
ya mike abinsa ya fice.
Ina ganin haka sai na rushe da kuka ina cewa
"Na shiga uku Mamy na lallace! Kar dai ace Sadik
yana nufin wannan ba dan sa bane.?" Ta ce "Haba
ya ma isa? Ya ma soma.?" Ta kirashi, amma ya ki
zuwa. Ta cc "An shiga uku jama'a, wai meke damun
Sadik ne? Gaskiya akwai magana mai karfi ma
kuwa. Barin Alhaji ya dawo sai ayi tufkar hanci tun
kafin iyayen yarinyer nan su zo su san abinda yake
wakana."
*车华
A zaune nake a daki nayi tagumi ina tunanin
abinda ke kaiwa da komowa. Na yi shuru zuciyata
kamar ta tsage dan bakin ciki. A raina na ce "Yanzu
42
Sharrin Jinni 3
irin sakamakon da Sadik zai yi min kenna? Duk
abin da na yi mishi da irin kaunar da make nuna
masa duk bai gani ba? To me yake nufi da nine.?"
Na tambayi kaina. Ba amsa. Na ce "To a gaskiya ya
kamata in san abinyi, ba zan zauna hawan jini ya
kamani a banza ba wallahi." Ban san san da hawaye
ya fara zubo min ba. Na yi ta kuka a hankali dan kar
Nusaiba taji ta tashi asirina ya tonu, gashi gobe
suna, gida ya cika da baki.
Na dauki jariri n na zuba masa ido ina ta
kallonsa. sai naji tausayinsa ya kamani. Na girgiza
kai, wani hawaye mai dumi ya zubo min. Tun da
aka haifi yaron nan Sadik bai taba daukarsa ba ko
sau daya, tun dai sa'adda Mamy ta mika masa shi.
Mamy tayi fadan, Alhaji ya yi fadan, amma abanza.
Alhaji ma har fushi ya yiwa Sadik.
Kayan barka kuwa duk Alhaji ne ya siya. Haka
ragon suna ma sai Alhajin ne ya yi. Shi yasa ma Alhaji ya ce ranar suba ba za'ayi wani taron suna ba
gudun tashin wata hatsaniyar kuma daban.
Haka dai aka yi sunan aka watse ba wani
armashi. Aka sawa yaron sunan Alhaji, wato
Lawansa, sai muke ce masa Daddy. Duk wannan
abu bai dada Sadik da kasa ba.
*** 43
Amina A. Sharada
Ina zuane a falo ni kadai nayi tagumi Daddy
na hannuna yana shan nono. Duk wanda ya kalleni
ya san cewa nayi matukar ramewa sosai, domin
lamarin na Sadik yafi gaban magana sai dai addu'a.
Ina nan zaune ya dawo daga aiki, ya wuceni
kwan-kwan-kwan abinsa. Na bishi da ido, domin
har na gaji da yi masa sannu da zuwan da bana
samun amsa daga gareshi. Na shareshi. Shi kuwa ya
shige dakinsa. Jim kadan ya komi ya shiga kitchen
domin hada abincinsa, yaje ya tarar ban girka ba.
Ya dawo ya tsaya kawai, kamar ya yi magana,
amma ko mai ya gani oho sai yake kawai ya koma
dakinsa gami da dauko dan mukullin motarsa ya
fice. Na bishi da kallo, a raina na ce "Indai ni ce
wallahi yanzu zan fara shirya maka nawa taceccen
rashin mutuncin.
Kwanci tashi har Daddy ya kai kimanin
shekara biyu. Ba shi ba Sadik kama ba dan sa ba. А
koda yaushe gidan Alhaji nake kaishi ko Nusaiba
tazo ta tafi da shi gidan su. Ba zai dawo ba har sai
ya yini. Wataran ma a can yake kwana. Shi yasa ma
Alhaji ya ce ayayeshi sai Mamy ta daukeshi ta
barshi a wajenta, domin suna tsammanin Sadik
haihuwarce baya so shi yasa yake wadannan
abubuwan. Nima dai abinda na ke tunani kenna, shi
yasa ma na hakura aka dauke shi din domin in gani
44
Sharrin Jinni 3
ya zaiyi in baya ganinsa. To da yake dama yasaba
da su sai ya yi zamansa a can din.
Rannan ina zaune ni kadai sai ga Sadik ya
shigo, na yi masa wani kallon sha tara na dauke kai
kawai na buga tsaki. Har ya kai bakin kofa sai ya
tsaya, ya juyo ya kalleni. Na murguna baki gami da
hararacsa na tashi abina zan tafi. Sai ya ce "Dakata."
Sai na tsaya domin inji abinda zai ce. Sai yazo dab
dani ya tsaye, ya ce "Wai wa kike yiwa tsaki." Na
ce "Da kai nake." Ya ce "Karki kara yi min tsaki, in
ba haka ba jikinki zai yi tsami." Na ce "Nayi, kuma
na kara sai kayi duk abinda ka ga dama." Ya ce "To
ki kara ki gani."
Nan take na kuma daka masa tsaki Mst! Sai
kuwa ya sharara min mari. Na dafe kuncina gami da
fadin "Ka mareni. Wallahi sai kayi danasanin
marina da kayi."
Ina rufe bakina, me zai faru? Kawai sai naga
Sadik ya yi kara ta fadı. Ga karar mari ana ta faman
kifa masa. Banga mai marin ba sai dai karar marin.
Shi kuwa yana ta tuntsurawa yana ihu. Kafin kace
meye wannan bakinsa yana ta tsiyayar jini, fuskarsa
kuwa ta kumbura suntum saboda tsananin mari.
Ni kuwa saboda tsananin firgita ban san
lokacin da na nufi gidan Alhaji jikina babu ko
mayafi ina ihu. Da gudu na karasa cikin gidan.
Mamy na zaune Alhaji baya nan ya tafi wajen
45
Amina A. Sharada
Ibrahim ya gano shi ya kai masa wani dan abin
masarufi kamar yadda ya saba duk karshen wata.
Momy tana ganina ta tashi aguje tana tambayar
lafiya? Domin a zatonta dukana Sadik ya yi. Nan da
nan ranta ya бaci. Ta ce "Zauna Alhaji ya dawo.
Wallahi yau sai anyi tufkar hanci." Ta fuskanci a
firgice nake nake. Sai ta kamani ta zaunar tana
tambayata ina Sadik.?" Na ce "Yana gida." Ta ce
"To wai me yake faruwa ne.?" Na ce "Ni dai naga
yana faduwa yana ihu yana wani irin abu." Mamy ta
suri mayafi tayi waje tana cewa "Kice abin ba
karami bane?". Tayi waje, nima nabi bayanta muka
isa gidan.
Da shigarmu muka sami Sadik a kwance shiru
kamar matacce. Nayi saurin zuwa inda yake na
dafashi. Ya dago kai da kyar yana kallona fuskarsa
a kumbure, idanunsa duk sun nutse. Ya tashi da
kyar.
Mamy ta karaso inda yake, ta ce "Sadik me ke
faruwa?". Ya ce "Wallahi Mamy ban san abinda ya
faru ba sai ji nayi ana ta marina haka kawai. Ji bi
yadda fuskata ta kumbura. Amma nafi zaton
wannan abun da muka gani a gidan nan ya komo."
Mamy ta ce "Ai sai a yiwa Alhaji way ayazo a
sake kawo Malaman nan, amma fa ina ganin
lamarin ku akwai wani bakon al'amari. Anya kuwa
rashin jituwar nan taku bata da nasaba da halin da
46
Sharrin Jinni 3
ka shiga yanzu.?" Sadik ya ce "Ba wani nasaba da
wannan, ni bana so ma a dinga yi min wanann
maganar." Ta ce "To shi kenan, Allah dai ya daidaitaku. Amma ai abin akwai mamaki, dole kuma a
dauki tsatstsauran mataki akan wannan abin.
***
Satin Alhaji daya da zuwansa gurin Ibrahim sai ga
Ibrahim a gida. Cikin tsananin rudani Alhaji ya
mike ya ce "Ibrahim me ya akwoka? Ya akai ka
fito? Wato gudowa kayi daga gidan yarin ko?"
Ibrahim ya samu guri ya zauna, ya ce "Alhaji
kwantar da hankalinka in baka labarin abinda ya
faru, in baka yarda ba sai muje da kai a tambaya."
Alhaji ya ce "Kai nake sauraro." Ya ce "Da mai
girma gwamna ya ziyarci gidan maza a irin ziyarar
da yake kaiwa wurare a kasan nan, shi ne yau Allah
ya nufe shi da zuwa inda muke, ya taramu aka dinga
karanto masa laifin kowa. Ma'ana aka dinga
sallamar masu laifuka kananu, yana kuma ragewa
wasu shekarun da aka dibar musu abisa adalci da
kaunar talakawa. Wallahi Alhaji abin ba karamin
dadi wannan abu ya yiwa al'umma ba. Hakan ne ma
ya sa muma muka zamo daga cikin wadanda aka
yafewa shekaru ukun, kuma kasan mun haura biyu
ma.?" Ya ce "Haka ne.? To amma ba zan yarda ba
47
Amina A. Sharada
sai naje ad kaina naga zahiri." Ya ce "Muje tare ma
kaji yadda aka yi."
Alhaji ya tusa Ibrahim gaba har ofishin
Alkalin da ya yi musu shari'a. Alkalin ya tabbatar
musu da wannan magana haka take, sannan
hankalin Alhaji ya kwanta, domin da mai da shi
zaiyi ayi a kuma yi masa hukuncin laifin da ya yi
dai-dai da laifin nasa.
Yanzu tsananina da Sadik abu ya sauya ba
kamar da ba, domin tun daga ranar da ya sha mari
yake dan rangwantamin, domin ya gane dalilin
marin da ya yi min ne aka hukuntashi. Yanzu zamu
zauna muyi hira da shi, zamu ci abinci tare,
makwancin mu daya. Komai dai ya sauya. Nan da
nan zuciyata tayi sanyi. Sai dai abu guda da har
yanzu baya kula Daddy, in ya ganshi sai ya daure
fuska. Haka shima Daddy in ya ga Sadik baya sakin
jikinsa da shi. To irin wannan lamarin ne yake
bakanta min rai. Wai ace kai da danka ya zame
maka abokin gaba. To amma sai in' daure zuciyata
domin gudun kar in yi masa magana mu koma
gidan jiya, inzo kuma ina tada zaune tsaye. shi yasa
ma In na ga muna zaune da Sadik Daddy ya taho,
sai in maza in aikeshi daki dom in kar ya ganshi ko
kuma yazo inda muke. Da yake yaron yana da jin
magana, da na ce ya tafi sai ya juya da gudu ya tafi
ya kwanta shi kadai a daki abinsa har sai sa'ilin da
48
Sharrin Jinni 3
na je. Hakanne yasa nake yawan kai shi gidan
Mamy.
Rannan na tashi bana jin dadin jikina, sai na
fadawa Sadik. Ya ce in shirya to ya kaini asibiti."
Haka kuwa muka yi, ina gama shiryawa ya daukeni
sai asibiti. Anan likita yake sanar dani cewa ina da
shigar ciki na wata biyu.
Anan naga ikon Allah, domin Sadik murna ya
dinga yi kamar ya hadiyeni. Da muka zo gida da
kansa yaje ya gayawa su Mamy. Suma sun yi farin
ciki matuka, kuma sunyi mamaki cikin abin nan
sosai.
Tun daga wannan lokaci na zamo 'yar lelen a
hannun Sadik, domin irin gatan da yake nuna min
ko ada ma bai nuna min shi ba. Da na ce "Wash!"
Yanzu ya kidime.
Daddy kuwa sai kace agola na zo da shi.
Hakan ne yake sani tunanin ko Sadik yana tunanin
Daddy ba dansa bane? Take na kauda wannan
tunani, na sako wani domin ba shi da wani amfani.
A haka har ciki ya isa haihuwa. Mamy ta ce
Nusaiba tazo ta zauna a tare dani tunda batayi
tafiyar ba (da yake za ta tafi Bauchi bautar kasa)
domin tace sai tayi karatu mai yawa sannan zata yi
aure.
Da Mamy ta gayawa Sadik haka, sai ya ce a
barni kawai, shi zai lura da ni. Mamy tayi mamaki,
49
Amina A. Sharada
musamman da ta ga ya dauko wata likita tana
dubani yana biyanta. Dan haka da haihuwar tazo ma
ita ya yi kira ta kar6i haihuwar. A gida Allah ya
saukcni. Allah ya sake bani saurayin kyakkyawa,
shi kuma kamar mu daya da shi.
Da ranar suna ta zo aka radawa yaro sunan
Sadik, wato Magaji da Rai. A wanann karon Sadik
ya yi buduri na ban mamaki, domin irin ta'adin
kudın da ya yi abin ba bayani. Bai bar Alhaji ya yi
komai ba sabanin haihuwar daddy da sai Alhaji ne
ya yi komai. Kayan barka ma sai da na nuna бacin
raina sannan Sadik ya daina jidowa. A wanann
karon kai lamari ya yi sosai, ga kaunar dan da Allah
ya zubawa Sadik. Domin 'yan barka ma idan sun zo
a hannunsa suke karbarsa. Wasu ya bayar, wasu
kuma ya yi bara ayi hakuri a ganshi.
In an kwana biyu abin har kunya ya dinga
bani. Ranar suna kuwa dauke dansa ya yi wai kar
jama'a su jagwalgwalashi yazo yana ciwon jiki. Sai
da Mamy tayi masa fada tana cewa "Wai kai a ina
ka taba ganin irin wannan rashin mutuncin? Ya
mutane za su zo tayaka farin cikin karuwa ka dinga
hanasu suga dan.?" Nan dai tayi masa tatas! Ta cе
ya bata dan ya bar gidan, in ba haka ba ta hada shi
da Alhaji. Sannan aka sami sa'ida.
Bayan munyi arba'in ne naje gida na dawo. Ina
zaune da Sadik little wanda Sadik naji yana kiransa
50
Sharrin Jinni 3
na je. Hakanne yasa nake yawan kai shi gidan
Mamy.
Rannan na tashi bana jin dadin jikina, sai na
fadawa Sadik. Ya ce in shirya to ya kaini asibiti."
Haka kuwa muka yi, ina gama shiryawa ya daukeni
sai asibiti. Anan likita yake sanar dani cewa ina da
shigar ciki na wata biyu.
Anan naga ikon Allah, domin Sadik murna ya
dinga yi kamar ya hadiyeni. Da muka zo gida da
kansa yaje ya gayawa su Mamy. Suma sun yi farin
ciki matuka, kuma sunyi mamaki cikin abin nan
sosai.
Tun daga wannan lokaci na zamo 'yar lelen a
hannun Sadik, domin irin gatan da yake nuna min
ko ada ma bai nuna min shi ba. Da na ce "Wash!"
Yanzu ya kidime.
Daddy kuwa sai kace agola na zo da shi.
Hakan ne yake sani tunanin ko Sadik yana tunanin
Daddy ba dansa bane? Take na kauda wannan
tunani, na sako wani domin ba shi da wani amfani.
A haka har ciki ya isa haihuwa. Mamy ta ce
Nusaiba tazo ta zauna a tare dani tunda batayi
tafiyar ba (da yake za ta tafi Bauchi bautar kasa)
domin tace sai tayi karatu mai yawa sannan zata yi
aure.
Da Mamy ta gayawa Sadik haka, sai ya ce a
barni kawai, shi zai lura da ni. Mamy tayi mamaki,
49
Amina A. Shurada
musamman da ta ga ya dauko wata likita tana
dubani yana biyanta. Dan haka da haihuwar tazo ma
ita ya yi kira ta karbi haihuwar. A gida Allah ya
saukeni. Allah ya sake bani saurayin kyakkyawa,
shi kuma kamar mu daya da shi.
Da ranar suna ta zo aka radawa yaro sunan
Sadik, wato Magaji da Rai. A wanann karon Sadik
ya yi buduri na ban mamaki, domin irin ta'adin
kudın da ya yi abin ba bayani. Bai bar Alhaji ya yi
komai ba sabanin haihuwar daddy da sai Alhaji ne
ya yi komai. Kayan barka ma sai da na nuna bacin
raina sannan Sadik ya daina jidowa. A wanann
karon kai lamari ya yi sosai, ga kaunar dan da Allah
ya zubawa Sadik. Domin 'yan barka ma idan sun zo
a hannunsa suke karbarsa. Wasu ya bayar, wasu
kuma ya yi bara ayi hakuri a ganshi.
In an kwana biyu abin har kunya ya dinga
bani. Ranar suna kuwa dauke dansa ya yi wai kar
jama'a su jagwalgwalashi yazo yana ciwon jiki. Sai
da Mamy tayi masa fada tana cewa "Wai kai a ina
ka taba ganin irin wannan rashin mutuncin? Ya
mutane za su zo tayaka farin cikin karuwa ka dinga
hanasu suga dan.?" Nan dai tayi masa tatas! Ta ce
ya bata dan ya bar gidan, in ba haka ba ta hada shi
da Alhaji. Sannan aka sami sa'ida.
Bayan munyi arba'in ne naje gida na dawo. Ina
zaune da Sadik little wanda Sadik naji yana kiransa
50
Sharrin Jinni 3
da only one ban san me yake nufi da wanann sunan
ba. Sai nima na ke gaya masa hakan.
Muna zaune Sadik na gefen mu shima a zaune.
Ban san yadda aka yi ba sai naji yaro ya tsandare da
kuka. Ashe wai hannun ne ya sarkafe daya daga
jikin hudu jin lessidin dake jikina. Shi kuma Daddy
ya ja a rashin sani. Habawa Sadik na tashi sai ya
kifa masa mari. Yaro ya yi taga-taga a firgice ya
kwala kara. Take naji raina ya yi mugun baci. Cikin
6acin rai na ce "Haba Sadik dan rashin imani me
za'a daka anan.?" Ya ce "An daka ya ya kina
kallonsa yana jamin hannun da sai ya karya ya
cuceni.?" Na ce "Ya za'ayi ya karyashi yana sani ne.
Kar ka kara dakar min da daga yau." Ya ce "To ki
gaya masa kar ya kara dakar min da daga yau."
Nan na dire jaririn, wato only one na dauki
Daddy muka yi cikin daki na bar ma sa shi a nan
zuciyata kamar ta fashe dan bakin ciki. Shi kuma ya
daukeshi suka nufi nasa dakin.
Yauma din dai kamar kullum, muna zaune ni
da yarana muna ta wasa, suna abin dariya ina yi sai
ga Sadik ya fito zai fice. Ya karaso inda yake ya
yiwa only one wasa yana ta bangale masa baki. Shi
kuma Daddy ya koma gefe daya ya yi tsuhu yana
kallonsu. Sadik ya ce da only one "Zanje kasuwa
me zan taho maka da shi.?" Sai ya kara kunnensa
51
Amina A. Sharada
dai-dai bakinsa ya ce "Okey in sayo maka keke da
mota ko...... ?"
"To duk zan sayo maka." Daddy yana jin haka
ya taso da sauri ya ce "Nima za'a siyo min.?" Ya ce
cikin hantara "Da Allah can waye zai siyo maka.?"
Yana jin haka sai ya koma bayana ya boye fuskarsa
abayana saboda tsoro. Yana fita sai ya zago ya sani
a gaba ya zuba min ido ya yi gwalam da shi,
tausayinsa ya kamani. Na ce "In Allah yaso zan siyo
maka kaji Daddyn Umma." Ya gyada min kai. Na
yi shiru ina tunanin irin kiyayyar da Sadik yake
nunawa yaron nan kamar ba jininsa ba. Na ce a
raina "In Allah yaso sai Sadik ya yi dana sanin kin
da yakewa yaron nan. Da izinin Allah sai ya yi kuka
da hawaye sharab-sharab. Domin musgunawar tayi
yawa, sai kace agola ko shege. Yaro shi da gidan
ubansa ba shi da ikon watayawa.? Na ce "Wallahi
da ade agola na zo da shi da tuni na mai da shi
gidansu, domin in huta shima yaron ya huta. Haba
wannan bakin cikin har ina.?"
Sadik karami rarrafensa yake yi. Ya saba da
Sadik. Ko ina 72 shi in ba aiki, to tare suke da only
one dinsa. fa yin da ni kuma nake farantawa
Daddy, domin ko dinkin Sallah Sadik baya yi masa,
52
Sharrin Jinni 3
ni nake saya masa, sai kuma gidan Alhaji, domin
Alhaji na yi masa Mamy na yi. Hakama Ibrahim
nayi masa. Hatta Nusaiba tana yawan daukarsa ta
tafi da shi tayo masa shoping. Kuma wani ikon
Allah sam ba ruwansa da Sadik karami, suyi ta
kyararsa ko kadan bana jin haushi domin na san
suna yi ne dan su kona zuciyar Sadik. Sadik kuwa
yaji haushi sosai, har cewa ya yi in daina zuwa da
shi gidan tun da ba sansa suke yi ba.
53
Amina A. Sharada
TOFA, KARSHEN TIKA-TIKI TIK!
Wata rana ina zaune a falo ni kaďai ina tunanin
abin da yake wakana a rayuwata, duk burin 'ya
mace dai baya wuce gidan mijinta, to ni gashi na
samu, amma na kasa jin dadn zaman gidan miji.
Kuma auren so muka yi da shi bana ki ba, to why?
Na tambayi kaina. "To ashe dai wannan rana ita zata
zame min ranar warwarewar duk wani bakin cikina
da kuma cudewar al'amarin ma baki daya.
Ku biyoni a sannu.
Ina nan zaune sai ga Sadik ya fito sanye da
wani boyen dari tas mai kyan gaske. To ashe iri
daya suka dinka shi da Alhaji. Shima Sadik har da
babbar riga, kuma aikin ma iri daya. Na dube shi na
ce "Daddyn only one ina za'ane aka yi wannan irin
shiga kamar za'a gaisuwar surukai.?" Ya yi dariya
ya ce "Aure zan karo shi yasa yanzu ma gidan
iyayen yarinyar zamu." Na yi dariya "To Allah ya
kiyaye hanya. A gaishe su in sunyi maka maraba."
Ya ce "Au baki yarda ba kenan.?" Na ce "Yarda ma
ai daya ce." Ya yi dariya "Shi kenan tun da baki
karaya ba. Yanzu kyaji inda zanje." Na yi murmushi
kawai. Ya ce "Gidan surukan Ibrahim zamu." Na ce
"A ina ne kuma." Ya ce "Can kauye." Na ce "Wace
matar shi kuma? Duk gayun nan nasa ya rasa inda
54
Sharrin Jinni 3
zai yi aurc sai a kauye?" Ya cc "Ai ba'a can take da
zama ba. Anan Kano take, kin san ma kowace
matar.?" Na girgiza kai "Ban sani ba." Ya ce "Haula
ce fa kawarki." Na rike baki cikin mamaki. Na cе
"Au dama Haula ce yake so.?" Ya ce "Iyi, gashi har
ma zamuje gidan su." Na cc "Au shi ya sa na ce ta
gaya min waye angon rannan da tazo ta ce wai ba
yanzu zan ji shi ba. Ashe ma facala ta ce. Yanzu
kuwa zan yi mata tsiya san raina." Ya yi dariya ya e
"A to ita ku."
Muna cikin wannan hirar ne sai ga Daddy da
gudunsa, ya yin da Sadik ya juya baya zai yi
tafiyarsa, sai ya cakumeshi ta baya yana zaton
Alhaji ne. Habawa! Sai ya gambareshi ya ya kwada
masa mari yana cewa "Haka kawai dan sangarta ka
zo ka bata min kaya.?"
Yaron nan ya gigice, ya taho da gudunsa ya
rungumeni saboda tsananin rudewa da zafin mari.
Ta ke naji zuciyata tana faman tafasa. Namike cikin
bacin rai na ce "Haba Sadik ka gaya min idan
dannan ba naka bane wallahi ayau zai bar gidan
nan, zan fita da shi, duk wanda na samu akan