kijc." Na cc "Shi kenan bari in shirya."
Ya tashi ya ce "In zo yanzu fa." Na ce "To."
Na shiga na dauki mayafina da mukullan gidan na
fito na kukkule gidan ina ta faman tunanin abin da
yake faruwa tsakanina da Sadik."
***
Hajiya Lami ce (Mamy) ta ke tukin. Ni kuma
ina gaba a zaune. Na dubeta na ce "Mamy wai waye
bashi da lafiya ne.?" Ta ce "Wani ne." Na се "Mе
ya same shi.?" Ta ce "Nima ban sani ba sai in munje
ma gani."
A haka muka isa asibitin, muka shiga gurin
mara lafiyar. Da isarmu sai na ga wani a kwance a
nannade kansa da bandeji har fuskarsa. Ban shaida
kowaue ba, domin idanunsa ne kawai a waje, kuma
suma a rufe suke.
Na sami guri na zauna na ce da Mamy
"Wannan shi ne marar lafiyar.?" Ta ce "Shi ne."
Na yi shiru kawai ina kallon dakin. Gado daya
ne tak, sai kujeru biyu na maziyarta, wadanda suke
dab da gadon.
Shiru marar lafiyar bai farka ba, muna zaune
kawai ni da Mamy. Na dubi Mamy na ce "Mamy
wai waye ne.?" Ta kalleni kawai ta kauda kai, ta ce
21
Amina A. Sharada
"Ai yanzu zai farka, ina jin in ya farka za ki gane ko
wayc." Na yi shiru kawai ina tunanin ko waye oho.
Mun fi awa uku a zaune bai farka ba. Na mike
na ce "Mamy zan tafi gida, na san yanzu Sadik ya
koma, kuma zai tarar bana nan." Ta ce "Ba wani
abu zauna, in muje na yi masa bayani." Na се "То
shi kenan." Na koma na zauna.
Jim kadan sai naji wannan marar lafiyar yana
wasu sambatu. Na ce da Mamy "Lah! Kin ga zai
farka." Ta ce "Eh, dama a yadda likitan ya gaya
mana sai wannan lokacin zai farka."
"Hamdiyya!." Ta kira sunana a hankali.
"Na'am." Na amsa mata ina tattara hankalina
kanta.
"Ina so duk a irin halin da kika sami kanki,
walau na bacin rai ko tashin hankali, ki kasance mai
tawakkali, ki saka Allah a al'amuranki kin ji ko.?"
Na ce "To Mamy. Me ya ke faruwa.?" Ta ce "Ni dai
na gaya miki kawao domin ki zama mai yadda da
kaddara mai kyau da mara kyau..........
Ta ci gaba "Ina son in gaya miki wata magana.
Amma fa sai kinyi min alkawarin ba za ki tashi
hankalinki kan abin da zan fada miki ba."
Tun daga lokacin naji gabana ya fadi ras! Na ce "Na
yi miki Mamy, fada min."
Ta ce "Kin san ko waye wannan akwance.?"
Na dafe kirji cikin firgici na ce "A'a." Ta ce"To ai
22
Sharrin Jinni 3
kinji irinta, tun kafin in gaya miki har kin tsorata,
shi yasa ma Alhaji ya ce kar in fada miki."
Na matsa kusa da marar lafiyar na kare masa
kallo sama da kasa. Ta 'yan yatsun kafarsa na gane
ko waye, domin da ban lura ba sosai.
Ai ina gane ko waye sai zuciyata ta buga dum!
Numfashina yana fita sama-sama. Da kyar na
kakalo sunansa.
"Sadik!" Na ambata da karfi, na yi baya.
Mamy ta rafka salati. A dai-dai lokacin da Alhaji ya
turo ya shigo. Yana ganin abin da ke faruwa ya
karaso da gudu yana cewa "Hajiya me ya sa kika
gaya mata? Ai kinga irinta ko? Abin da akc gudu ya
samu." Mamy ta ce "Alhaji taimaka ta suma, ayi
kiran likita."
Da gudu Alhaji ya fita, ya nufi ofishin lıkitan.
Sai ga su tare cikin gaggawa, tare da wasu Nas guda
biyu suna tura dan keken daukar marar lafiya.
Suka karaso inda nake har Hajiya suka kamani
suka dorani akan wannan keken. Nas din nan biyu
suka tura shi suka nufi wani daki da ke kusa da
dakin Sadik.
Anan Likita ya auna, sannan ya bani gado.
Shima dakin gado daya ne da shi tak, sai toilet. Ba'a
dau wani lokaci na na farka. Bayan agajin hahawa
dana samu. Hajiya tana wajena, shi kuma Alhaji
yana wajen Sadik.
23
Amina A. Sharada
Na dubi Mamy na ce a hankali. "Mamy me ya
sami Sadik.?" Ta ce "Hatsari suka yi."
"A ina.?" Na sake tambayarta kwalla na zuba
daga idanuwana. Ta ce "Ban san a inda suka yi ba
Na lumshe idona ya yin da barci ya yi awon
gaba da ni sakamakon allurar barcin da aka yi min.
Wani irin tafkeken dajinc, ba gida gaba ba gida
baya, sai rukunan bishiyoyi da suka taimakawa
dajin matuka wajen kara masa duhun gaske, gami
da jerin duwatsu manya-manya da suke kewaye da
dajin.
Wasu maka-makan duwatsu sun kewaye wani
katon tafki sun masa kawanya, sannan ga wani irin
yanayi bai ban tsoro. Kallo daya zakaiwa dajin
kasan cewa yana dauke da miyagun namun daji da
aljanu.
Adai-dai wannan lokaci ina tsaye a bakin tafki
ina haki sakamakon gudun da naci. Zuciyata a bace
ina kokarin taka dutsen dake gefen tafkin da nufin
in zunduma ciki in huta da bakin ciki.
Yunkurawar nan da zan yi na buga wani uban
tsalle da niyyar in zunduma ciki. Sai naji wani shuu!
Tik! Na jini a ksa maimakon inji ni a ruwa. A
firgice na bude ido inga me yake faruwa. Sai na yi
tozali da wani kyakkyawan saurayi baki, jikinsa
24
Sharrin Jinni 3
babu riga, sai wani warki na fata da ya daura,
sannan da wata jaka ratayc a jikinsa.
Na dube shi a firgice na fara ja da baya. Ya yi
murmushi ya ce dani "Na ga har yanzu ba ki gane
waye ni ba ko." Ban iya ce masa komai balle har ya
samu amsar tambayarsa.
Ya ci gaba "Yanzu ne naga ya dace in bayyana
miki gaskiyar kaunar da nake miki. Allah ya saka
min kaunarki. Tun kina yarinya ina biye da ke, ina
lura da ke, bana bukatar duk wani abu da zai taba
ki. Kowa ya bata miki sai na bata masa. Shi yasa
kuka ga mutane suna shiga matsala a kanki. Ko
uwar da ta haifekice ta ce za ta batamiki sai na nuna
mata kuskurenta. Saboda haka ki jawa mijinki
kunne. Wannan hadarin da ya yi kadan ne na taba
shi, duk lokacin da ya kuskura ya dakeki sai na
wulakanta rayuwarsa. Sannan kuma in kasheshi in
daukeki."
Duk wannan bayanin da ya ke yi ina jinsa
kawai. Sai da ya kawo karshen bayanin nasa,
sannan na ce "To kai waye?"
"Ni ba mutum bane aljani ne. Tun da kina da
dakakkiyar zuciya zan nuna miki asalin surata
yanzu."
Yana rufe baki sai ya yi wata irin girgiza gami
da haniniya da kugi. Baki daya nan take suffarsa ta
sauya daga ta mutane ta koma ta wani irin bakin
25
Amina A. Sharada
maridin Aljani, wanda acikin aljanun ma shi irin
bakaken shaidanun nan nc. Girmansa kuwa ya kere
duk bishiyoyin da ke gurin. Kansa irin na miciji ne,
sai dai yafi na miciji girma sosai.
Ina ganin wannan halitta ban san sanda na
fadi kasa sumammiya ba.
Wuf! Na tashi daga barcina, gami da kwala
wata razananniyar kara. Mamy ta tashi da gudu, ya
yin da na ke ta kokarin dirowa daga kan gadon da
na ke kai. Na fiske robar ruwan da akai min karin
ruwa. Na nufi hanyar fita ina kiran "Sadik!"
Mamy ta jawoni iya karfinta. Na tureta can
gefe ta fadi. Ina kokarin ficewa sai ga Alhaji da
Ibrahim. Suna ganin abin da yake faruwa, sai Alhaji
ya rikeni yana tambayar me yake faruwa.?"
Mamy da take kokarin tashi cikin tsamin jiki
na kayan da nayi mata, ta ce "Wallahi Alhaji tana
kwance tana barci sai naga ta tashi a razane tana
kara, shi ne fa ta diro tana ihu."
Ba dan Alhaji ya yi min rikon tsauri ba, da tuni
na fisge. Ya dubeni yaga ba acikin hayyacina na ke
ba, ina ta faman sambatu. Sai ya fara yi min addu'a
yana tofamin. Mamy ma na yi. Alhaji ya ce Ibrahim
ma ya taso ya yi min. Shima ya taimako.
Haka dai suka dinga yi min addu'a, da haka har
na fara nutsuwa. Da na komo cikin hayyacina, sai
na mike kyam na koma kan gado. Na yi tagumi ina
26
Sharrin Jinni 3
tunanin abinda na gani a mafarki. Ban san lokacin
da hawayc ya fara zubo min ba. Alhaji ya matso
kusa dani, ya ce "Kiyi hakuri, Sadik din ya farko,
yanzu ma daga gurinsa nake, yana shaida nautanc,
har ma yana magana. Dan haka Ibrahim zai zzauna a
wurinsa, ke kuma ga Nusaiba nan zata zauna tare da
ke."
Na ce "Alhaji nifa lafiyata kalau." Ya ce "Ai
na sani, so na ke ki huta tukunna sai kije gurin
nasa." Na koma na zauna, ina mamaki, wai lafiyata
kalau amma ace wai bani da lafiya.
A zaune Sadik yake, domin ya fara samun
sauki, ya yi tagumi kawai, ya yin da Ibrahin yake
gefensa a zaune shima yana kallonsa, zuciyarsa cike
da mamakin irin tsanar da Sadik ke masa. Shi kuma
baiga abinda ya yi masa ba, amma a yadda ya
daukeshi, sai ka ce abokin gaba. Ko dai a hatsarin
da ya yi ya samu buguwa a kansa ne? Irin tunanin
da Ibrahim yake kenan. Ya yin da ya ke zaman
jinyar Sadik.
"Ibrahim na gaya maka bana son zaman ka,
gara ka koma gida a turo wani. Kai ni a kyaleni
haka ma, ni kadai ma zan iya komai da kaina."
Ibrahim ya ce "To na ji, ka baro Alhaji yazo,
yau sai in gaya masa ya kawo maka wani."
Sadik ya yi tsaki ya juyar da kansa gefe daya
kawai. 27
Amina A. Sharada
"Nusaiba zo muje in ga jikin Sadik." Ta се "То
taso muje tun da kin na ce sai mun je din." Na mike
muka fita, muka nufi dakin Sadik.
Yana kwance Ibrahim na gefe daya. Na karasa
inda yake na kira sunansa a hankali "Sadik!". Ya
bude ido ya kalleni. Sai naga ya tashi zaune ya
Kurawa Ibrahim ido. Ya sake maida kansa gareni ya
girgiza kai kawai, ya koma ya kwanta ya rufe
idonsa.
"Sadik ya jikin.?" Na ce da shi cikin sanyin
murya. Ko kallona bai yi ba, ya ma juyar da kai
kawai. Na zauna kusa da shi, na sa hannu na dafa
shi, na cc "Sadik ka daina saka bacin rai a zuciyarka
kar wan i ciwon ya kamaka." Baice dani kala ba. Na
dubi Ibrahim na ce "Ibrahim ko baya magana ne.?"
Ya ce "Wallahi nima haka yake min. Amma yana
magana." Na girgiza kai kawai. Na zauna na yi
tagumi, banda hawaye ba abinda ke zubo min daga
idanuna.
Haka muka yi ta zama a asibitin har Sadik ya
samu sauki baya mun maganar komai, sai dai yasa
Nusaiba tayi masa wani abun idan yana bukata.
Baya sani, baya sa Ibrahim. Abin yana bamu
mamaki, amma sai muka zuba masa ido kawai,
domin in mun ce zamu tambaye shi dalili ma ba
magana zai yi mana ba, sai dai akwai ya zubo mana
na mujiya. 28
Sharrin Jinni 3
A haka aka sallamomu gaba dayan mu, domin
Sadik ya samu lafiya.
*
Tunda aka sallamemu muka dawo gida ba
abinda ya sauya dangane da fushin da Sadik ya ke
yi dani. Idan abinci nayi baya ci, in gaisheshi nayi
baya amsawa. Duk abin da na yi masa baya
saurarona. Hakan ne ya sani matukar damuwa, koda
yaushe ina zuane nayi tagumi, ko barcin kirki bana
iyawa.
Muna nan a haka rannan sai na tashi da jiri da
ciwon kai. Ina kwance a dakina ban fito ba, ko
karyawa ban yi ba, domin ba zan iya cin komai ba.
Wajen sha daya da rabi na rana na samu jirin ya dan
sakeni. Sai na fitoa falo domin in danji dadin jikina.
Sai na sami Sadik a falon azaune yana shan tea.
Anan na tabbatar shima sai yanzu yake karyawa. Na
sami guri na zauna, na dubeshi na ce "Ina kwana.?"
Ya dan kalleni. "Lafiya." Ya amsa min a ciki da
gajeriyar amsa.
"Dan Allah ko zaka je ka ce da Nusaiba tazo ta
dan tayani wasu abubuwan. Wallahi bani da lafiya."
Bai ce dani komai ba, ya ci gaba da abinda yake yi.
Hakan da yake min ba karamin kona min rai yake
yi ba. To amma dolene in yi hakuri har Allah ya
kawo karshen wannan lamari, domin dai na san ba
29
Amina A. Sharada
AUREN KI aka yi mana, AUREN SONE tsakanina
da shi, bare yace dole aka yi masa auren.
Ina nan kwance sai kamshin dankali da kwan
da ya soya ya ke karyawa da shi ya bugeni. Take
amai ya fara taso min. Ina kokarin tashi in fita da
gudu sai aman ya rigani. Anan na fara kwara amai.
Yana kallona kawai ba abinda ya ce da ni har na
gama aman. Ciwon ciki kuma ya ce gani nan. Na
dinga birgima ina rike da cikina ina kiran "Wayyo
Allah! Sadik ka taimakeni. Wayyo Allah Sadik zan
mutu!"
Kawai sai ya yi tsaki ya dauke flet din da kofin
shayin ya nufi kitchen ya barni a kwance anan ina
juyi da kiran Wayyo Allah na zan mutu!.
Ya dawo ya yi shigewarsa daki abinsa. Haka
na yi ta murkususu, ga ciwo ga bakin ciki. Can
jimawa sai ga Nusaiba ta shigo da saurinta. Ta
karaso inda nake kwance tana cewa "Sannu
Hamdiyya. Tun yaushe baki da lafiya." Da kyar na
bude baki na ce "Da safen nan." Ta ce "Oh Allah ya
sauwake, dama nima yanzun nan Yaya Sadik ya yi
min waya, ya ce inzo baki da lafiya."
Duk da nayi mamakin abinda tace. Sai na
6oye dan kar ta gane, na ce "Uhm." Kawai. Nan ta
taimaka min nayi wanka, ita kuma ta gyara falon.
Bayan na sauya kaya ina kwance sai gata ta
gama, ta ce "Hamdiyya Yaya Sadik ya ce wai ki fito
30
Sharrin Jinni 3
muje asibiri." Na ce "Shi zai kaimu." Ta ce "A'a ya
bani mukullin motarsa, ya cc in kaiki." Na cc "Au
an gyara motar nc." Ta cc "A'a baki san Alhaji ya
sauya masa sabuwar mota bane.?" Na yi shiru kawai
ina tunani, dan ban san Alhaji ya sauyawa Sadik
wata motar ba sam-sam. Amma dan kar ta ganc sai
na cc "A'a dama ina a tsohuwar ta da yake fada." Та
ce "A'a."
Na tashi na shirya muka tafi. Na ce "To kin
karbo kudi ko haka zamu tafi." Tа сс "Ya ce muje
can Hospital din da akc zuwa."
"Kin san wurin." Na tambayeta.
"A'a ba kin sani ba.?" Ta ce dani. Na ce "Ke
dai in kin sani kawai muje." Ta ce "Ban sani ba sai
dai in tambayeshi. Ya dai ce Privete ne asibitin." Na
ce "Kije ki tambayeshi." Na fita, ita kuma ta wuce dakin Sadik.
Ta juyo ta kalleni, sannan ta maida hankalinta
ga tuki, ta ce "Niga mamaki kika bani, gashi dai
kina a halin rashin lafiya, amma sia naga kina
murna bayan kinga likita. Wai me ke gudana ne.?" Na yi murmushi na ce "Sauki na smau shi ya sa kika ga ina ta murna." Tayi dariya, "To Allah ya karo sauki." Na ce "amin."
Adai-dai lokacin da muka yi parking a kofar get dinmu, ya yin da Maigadi ya ke kokarin bude
mana get. Muna shiga cikin gidan sai ta tsaya, na
31
Amina 4. Sharada
fito ina yamutsa fuska, Daga k "an nan da zanyi sai
muka yi ido hudu da Sadik yana kallona ta
windownsa dake fuskantar harabar gidan. Na yi
saurin dauke kaina nayi shigewara ciki na bar
Nusaiba na kukkule motar.
Ta sameni a falo a zaune, ta ce "Ungo ki kaima
sa key dinsa." Na ce "Ba zan iya tashi ba, kai
masa." Ta shiga ta kai masa. Ta dan jima sannan ta
fito, ta ce "Hamdiyya ya ce ki bani katin in kai
masa." Na yi kamar ba zan bata ba, amma dai sai na
mika mata kawai, na sami guri nayi kwanciyata,
Anan ta dawo ta sameni ina kwance da katin a
hannunta ta miko min. "Gashi." Na ce "To." Na
Каrба. Та zauna kusa dani, ta ce "Hamdiyya ina son
in yi miki wata tambaya, amma ina gudun kar kice
nayi miki shishshigi a lamarinki." Na yi murmushi,
na ce "Nusaiba kenan, ai tsakanina da ke ba
maganar shishshigi, gaya min duk daya ne." Ta ce
"Dama so nake inji, wai me yake kaiwa da komowa
a tsakaninki ke da Sadik ne.?" Na kalleta na yi
murmushi. "To ke me kika gani.?" Ta ce "Ba komai,
gani na yi dai ba kamar da ba." Na ce "To ai ba
wani abu. Ke ce dai kika ga hakan." Ta ce "A'а
Hamdiyya kar fa a dinga wahalarmin da Yayana."
Na yi murmushi, na ce "Ko dai shi ya wahalar dani,
domin in shi ba'a wahalar da shi ba ai shi ya
wahalar." Tayi dariya, ta ce "Ki gode Allah
32
Sharrin Jinni 3
muje asibiri." Na ce "Shi zai kaimu." Ta ce "A'a ya
bani mukullin motarsa, ya ce in kaiki." Na ce "Au
an gyara motar ne." Ta ce "A'a baki san Alhaji ya
sauya masa sabuwar mota bane.?" Na yi shiru kawai
ina tunani, dan ban san Alhaji ya sauyawa Sadik
wata motar ba sam-sam. Amma dan kar ta gane sai
na ce "A'a dama ina a tsohuwar ta da yake fada." Ta
ce "A'a."
Na tashi na shirya muka tafi. Na ce "To kin
karbo kudi ko haka zamu tafi." Ta ce "Ya ce muje
can Hospital din da ake zuwa."
"Kin san wurin." Na tambayeta.
"A'a ba kin sani ba.?" Ta ce dani. Na ce "Ke
dai in kin sani kawai muje." Ta ce "Ban sani ba sai
dai in tambayeshi. Ya dai ce Privete ne asibitin." Na
ce "Kije ki tambayeshi." Na fita, ita kuma ta wuce
dakin Sadik.
Ta juyo ta kalleni, sannan ta maida hankalinta
ga tuki, ta ce "Niga mamaki kika bani, gashi dai
kina a halin rashin lafiya, amma sia naga kina
murna bayan kinga likita. Wai me ke gudana ne.?"
Na yi murmushi na ce "Sauki na smau shi ya sa
kika ga ina ta murna." Tayi dariya, "To Allah ya karo sauki." Na ce "amin."
Adai-dai lokacin da muka yi parking a kofar get dinmu, ya yin da Maigadi ya ke kokarin bude
mana get. Muna shiga cikin gidan sai ta tsaya, na
31
Amina A. Sharada
fito ina yamutsa fuska. Daga k "an nan da zanyi sai
muka yi ido hudu da Sadik yana kallona ta
windownsa dake fuskantar harabar gidan. Na yi
saurin dauke kaina nayi shigewara ciki na bar
Nusaiba na kukkule motar.
Ta sameni a falo a zaune, ta ce "Ungo ki kaima
sa key dinsa." Na ce "Ba zan iya tashi ba, kai
masa." Ta shiga ta kai masa. Ta dan jima sannan ta
fito, ta ce "Hamdiyya ya ce ki bani katin in kai
masa." Na yi kamar ba zan bata ba, amma dai sai na
mika mata kawai, na sami guri nayi kwanciyata.
Anan ta dawo ta sameni ina kwance da katin a
hannunta ta miko min. "Gashi." Na ce "To." Na
Karba. Ta zauna kusa dani, ta ce "Hamdiyya ina son
in yi miki wata tambaya, amma ina gudun kar kice
nayi miki shishshigi a lamarinki." Na yi murmushi,
na ce "Nusaiba kenan, ai tsakanina da ke ba
maganar shishshigi, gaya min duk daya ne." Та се
"Dama so nake inji, wai me yake kaiwa da komowa
a tsakaninki ke da Sadik ne.?" Na kalleta na yi
murmushi. "To ke me kika gani.?" Ta ce "Ba komai,
gani na yi dai ba kamar da ba." Na ce "To ai ba
wani abu. Ke ce dai kika ga hakan." Ta ce "A'a
Hamdiyya kar fa a dinga wahalarmin da Yayana."
Na yi murmushi, na ce "Ko dai shi ya wahalar dani,
domin in shi ba'a wahalar da shi ba ai shi ya
wahalar." Tayi dariya, ta ce "Ki gode Allah
32
Sharrin Jinni 3
Hamdiyya, irin yadda Yaya Sadik ya dauke ki, in
kika ce haka kinyi masa butulci, domin babu
yarinyar da yake kauna fiye da ke." Na ce "To in
ma cutarsa nake yi ai zaku gani ne yau da kullum
ko.?"
Ta yi murmushi, ta ce "Amai da wukar, Allah
ya huci zuciya, ban fada dan rai ya baci ba, na fada
ne dan a gyara." Na ce "Nima ai ba ran nawa ne ya
baci ba, gani nayi za'a fidda min kokon usuli, wato
ke mai dan uwa.?" Tayi dariya "Kema tawa ce ai."
"Yo ba dole be. Ni kinga ki kyaleni inji da
abin da ya dameni." Tayi dariya, "Ai abinda ya
dameki ba wani abu ne na bacin rai ba, dan haka sai
ki san yadda zaki alkinta mana dakon da ko 'ya." Na
yi murmushi "Ku kai ku alkinta."
Ta mike, "Kinga ni yanzu ma zuwa zanyi inb
kaiwa Mamy albishir." Na harareta. "Kin ga ni fa
bana son gunzugulu."
"Koma me zaki ce nayi sai na fada." Na се
"Kanki ake ji."
Tayi waje tana dariya. Har ta fita ta dawo. "Au
na manta zan dawo in dora miki girki ne Aunty
Hamdiyya." Na ce "Kya santa dai."
"Allah ba da wasa nake ba." Na ce "Ke ni ba
zan ci ba."
"To in bakya ci Yayan fa.?" Ma be "Jeki ki
tambaye shi, in yana da bukata." Ta nufi dakin
33
Amina A. Sharada
Sadik. Ta dawo ta ce "Ke in mun gama na gida a
kawo masa." Na ce "Ke kika sani sautin
mahaukaciya." Ta fice ta barni anan akwance.
***
Yau watan cikina shida, har ya bayyana, kowa
ya san da shi. Amma Sadik tun ranar da aka kai
masa katunan nan har kawo yau bai taba cemin ashe
ciki gareki ba.
Na karaci laulayina na gama yana ji yana gani
kamar wanda ba na saba. Hakane yake firgita ni.
"To wai meye nufinsa ne? Hakuri dai iya hakuri
nayi shi, koma ince ina kanyi, domin duk halin nan
da muke ciki ba wanda na taba gayawa. Nusaiba ma
dan ta fuskanta ne da ba zata san me ake ciki ba,
kuma gidan mu gurin zuwanta ne yau da kullum.
Irin wannan tunani shi ne abokin hirata kullum.
Yauma kamar kullum ina zaune ni kadai a fali,
duk na saki labulayen, da yake lokacin sanyi ne, irin
hunturun nana. Na kwanta gami da jan tattausan
bargona bayan na duba agogon da ke manne a falon.
Daya saura minti biyar na rana. Na yi lami kamar
mai barci. Can sai na mike kamar an mintsineni,.
domin bin umarnin abinda tunanina ya
sana'antamin. Na nufi dakin Sadik kai tsaye, na
sameshi shima a kwance, duk da yake fuskarsa a
34
Sharrin Jinni 3
bude idanunsa na kallon sama, ya tsurawa silin din
dakin ido kawai yana tunani.
Na je kansa na tsaya da jiki tirtsitsi, fuskata a
daure. Ya juto a hankali ya zubo min ido. Sai da
muka share mintina kusan uku muna kallon-kallo da
ni da shi, sannan ya ce cikin sanyin murya. "Me ya kawo ki dakina.?" Na ce "Eh kace mai ya kawoni
mana tunda ba aurena ka ke yi ba. Ni dama zuwa na
yi in shaida maka cewa na gama hada kayana zan
tafi gida, na gaji da zaman da bashi da amfani. Ban
san cewa baka aurena ba sai yanzu."
Ya mike zaune a hankali "Wa ya ce bana
aurenki.?" Na ce "Oho! Kai ka sani." Na juya zan fice. Ya ce "Zo nan Hamdiyya."
Da dai kamar ba zan koma ba, sai dai na koma
dan inji abinda zai ce min. Na tsaya a gabansa. Ya
kalleni sama da kasa, ya ce "Yanzu baki ji kunyar
tsayawa a gabana kina fadamin wannan maganar
ba.?" Na ce "Kunya!? Kana wasane da abin da bana
wasa ba? Kar ka manta wannan cikin fa dake jikina
naka ne, amma duk irin wahalar da na ke sha akansa
baka taba saurarena bama bare ka tausayamin.
Hasalima tun lokacin da Allah ya bayar da cikin
baka taba cewa yau banzar nan cike gareya ba bare
in san ka san da shi. Ai ko zuwa nayi da shi ka
tausayamin bare kuma naka."
35
Amina A. Sharada
Ya yi shiru kawai yana saurarona. daga can
kuma ya ce "Yanzu to ya kike son inyi miki." Na ce
"Kawai gida zan tafi, in na haihu a aiko maka da
jaririnka ko jaririyarka. Ban zaci baka kaunata ba
sai yanzu!!".
Ina gama fadin haka na saka kuka na fice daga
dakin na barshi ya kasa katabus.
Ina shiga dakina na hau hada kayana a cikin
akwati ina ta faman kuka. Sai ga Nusaiba ta shigo
sanye da riga da wando na sanyi masu kaurin gaske,
ta sanyo hijabi. Da hucinta ta fado dakin, ta dauka
na tafi, ta sameni a zaune hawaye na shatata daga
fuskata. Tayi turus ta ce "Haba Hamdiyya, wai
menene na tada hankalinki ba, ke kuma baki
kwantarwa da Sadik nasa ba. Wai ya kuke son nayi
muku ne.?"
Sai da ta gama maganganunta, sannan na dago
kaina ina share hawaye, na ce "Wato dai ku laifina
ma kuke gani. In haka ne ke da Sadik din ya yi
muku wayar ba sai ya fada miki abinda na yi masa
ba. Ni wallahi tafiyata zanyi ba zan iya zama ba a
cikin bacin rai." Ta ce "ni dai wannan lamari naku
ban gane masa ba. Wallahi Alhaji zan gayawa."
Nan da nan ta bugawa Alhaji waya. Yana
amsawa ta ce "Alhaji kazo gidan Yaya Sadik, ina ta
fama da Hamdiyya wai sai ta tafi gida. Nayi-nayi ta
gayamin abinda ya faru taki...."
36
Sharrin Jinni 3
"Yauwa to muna jiranka......" Ta kashe
wayar.
Ta kalleni "Alhaji ya ce ki jirashi yana zuwa
yanzu." Ko kallo bata isheni ba, na ci gaba da hada
kayana. Itama kuma bata yi min magana ba. Daga
nan ta koma falo ta zauna.
A falo na samesu zaune tare da Sadik, nazo
zan giftasu, sai Nusaiba tayi saurin kamo akwatin
dake hannuna ta rike, ta ce "Ke yanzu in ance ki tafi
sai ki tafi a yadda kike din nan.?" Na ce "A'a sai in
tafi mana tunda ba'a Kaunata."
Ta mike ta kama akwatin ta ce "Alhaji ya ce ki jirashi zai zo yanzu."
Tana rufe 6aki sai Alhaji ya yi sallama ya
shigo. Muka amsa masa baki dayanmu, ya sami guri
ya zauna, ya dubeni ya ce "Zo nan Hamdiyya in ji
me ke faruwa." Na koma na zauna bayan na
sakarwa Nusaiba akwatin. Na sunkuyar da kaina, ya
yin da hawaye ke zubo min kamar ruwa.
Alhaji ya nisa ya ce "Ya aka yi ne.?" Cikin
kuka na ce "Wallahi Alhaji ban san abinda na yi
masa. Kusan watanni takwas baya min magana,
kullum sai haushina yake ji."
Alhaji ya ce "Sadik me yake faruwa har haka
ta samu.?" Ya yi shiru kawai. Alhaji ya ce "Da kai
nake magana kayi shiru." Kansa a sunkuye ya ce
37
Amina A. Sharada
"Alhaji yarinyar ce dai kawai bata da kirki, shi yasa
naga ya dace in daga mata kafa."
Alhaji ya ce "Kamar yaya bata da kirki? Ai ka
bani a rufe."
"Alhaji ai ita ta san laifinta,