An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
SHARRIN
NA
AMINA ABDULLAHI SHARADA
(MRS.AHMED YUSUr
Sharrin Jinni 3
SHARRIN JINNI
3
NA
AMINA ABDULLAHI SHARADA
(Mrs Ahmad Yusif Hadejia)
1
Amina A. Sharada
HAKKIN MALLAKA
Amina Abdullahi sharada
GODIYA
SHEKARAR BUGU
2008
Ga Allah Subahanahu wata'ala da ya bani ikon kammala wannan littafi.
Allah ka karawa Anabi S.A.W. daraja da daukaka. Amin summa amin.
GAISUWA
> Ummi Sulaiman
Hajiya Sulaiman
Nafisa Kawu
Fati Ya'u
Maryam Alhaji
Sakina Tasi
Saude Balarabe
Aisha A. Kurawa
Hajiya Ali
Dukkanku gaisuwa ce daga Zainab Sulaiman (Dangadi)
Zeee Babu Maiduguri. 2
Sharrin Jinni 3
FATAN ALKAIRI
Fatan alkairi gareki.
* Nafisa Muhammad Sheka. (Marubuciyar
Mariyatu)
Wasila Muhammad
Jamila Muhammad
Hadiza Bashir Dandago
Ummi Usman
Hadiza Ciroma
Hadiza Baba
Sagir Muhammad Sheka
Hauwa Muhammad
Binta Muhammad
Nayi muku fatan Alkairi daga Numan
Adamawa State.
GAISUWA TA MUSAMMAN
Ga dukkan Masoyana masu aikon min da
sakwanni tedt ko waya.
Na gode sosai. Allah ya kara kauna Amin summa
amin.
GAREKU KAWAYENA NA KAINA
• Bilkisu H. Muhd (Mrs Auwal by force
Zage (MULKIN MALLAKA)
.
Nafisa Muhd Sheka (ZUHURIYYA)
Sa'adatu Ahmed (SALEEMAT)
3
Amina A. Sharada
Zahra'u Baba Yakasai (TARKON SO)
Safiya Sani Ahmed (DUK ABINDA КА
KE SO)
Bilkisu Garba Maiagogo (IN SHARRANSHARRAN)
JINJINA GARELA KANINA NA KAINA
Shitu Sa'id Cross River State (Calaba)
GODIYA GAREKU
Sumayya Baita Yahaya D/Dutse
Khadija K/Marusa KT
Aunty Sa'a Zuru
Deejat S/Sharubutu
Jamila Zaryya Gamawa
Zabba'u Tambuwal
Maryam (Meran) Tambuwal
Baraka shiru Lawan (Nakirki) Katsina
Maman Fati Katsina
H.M.A. Fagge Kano
Rukayya Y. Adamawa
P.T.O.
Tsara rubutu a na'ura mai kwakwalwa
(COMPUTER)
MUBARAK M.B. GADON KAYA
07039170556-07039034583
Sharrin Jinni 3
SHARRIN JINNI 3
S
adik ya yi matukar karfin hali ya ce "Kai waye
da za ka shigo min gida haka kawai ka hana ni
sakewa.?"
Ya sake jin an cc. "Ni ba ka isa ka san ko ni waye
ba. Amman da sannu nan gaba za ka sani."
Ni ko ina kudundune a jikin Sadik na kasa fito da
kaina ma daga kirjin Sadik.
Sadik ya ce "Koma wayc kai Allah ya fika, domin
mu da shi muka dogara."
Nan ya fara karanto wasu addu'o'i masu karfin
gaske, maganin duk wasu shaidanun aljanu. Ya dinga
tofawa a dakin, kudu da arewa, gabas da yamma, sama
da kasa.
Duk wannan abun abu dake faruwa har yanzu ina
jikin sa a dukunkune.
Ya ce "Zo muje mu kwanta." Na ce "Wa? A ina.?"
Ya ce "Muje dakina." Na ce "Sam ba dai a gidan nan ba,
mu je dai kawai ka maidani gidan Alhaji."
Ya ce "Kar fa ki manta duk inda muke Allah yana
tare da mu.?" Na ce "Duk da haka ba zan iya zama ba.
Haba Sadik kana fa jin abinda aka ce. To kai kuwa
wonne tsautsayine zai sa mu kwana a gidan nan.? Ni dai
uke ka maida ni."
Hankalin Sadik a tashe ya ce "Mu koma falo."
Kememe naki yarda in banbaru daga jikinsa. Ya rasa
yadda zai yi dani, domin kuka nasa masa. A haka muka
je falo ya dauko kaset na karatun Alkur'ani kira'ar Sidi
5
Amina A. Sharada
Abdurraman Madina, da yake dama can Sadik
ma'abocin son wannan karatun nc. Ya kunna tare da Kurc karar rediyon.
In ka fita tun daga get ana jiyo sautin muryar,
sannan ya kuma zauna a falin kan doguwar kujera.
Dangwargwar har gari ya waye babu wanda ya rintsa,
duk abin nan ina jikin Sadik lamo muna ta sauraron
karatun Almur'ani, sannan kuma Sadik na ta faman yin addu'o'i.
Tun assalatu Sadik ya ce in tashi muje muyi sallah.
Na ce ya bari gari ya yi haske. Ya ce "A'a shi zuwa zaiyi
ya yi sallarsa." Na ce "Ai ko ba zai barni ni kadai ba a
falon, sai dai mu tafi tare.
Haka muka shiga toilet. Tare muka yi alwala,
sannan muka yi sallar tare. Kayan namu ma tare muka je muka dauko saboda tsananin tsoro.
A inda muka yi sallar nan muka zauna muna
karatun Kur'ani har gari ya karasa wayewa. Ya san ma
in ya ce inje in hada abin karyawa ba zuwa zanyi ba,
dan haka da kansa ya mike. Zumbur! Na kama gefen
rigarsa na bishi.
Na kasa komai dan tsabar tsoro, shi ya shirya mana
abin karyawa, muka fito falo tare, muka zauna tare,
muka kwashe kayan ma tare bayan mun gama karyawa.
Ya ce "To yanzu in zan fita ya za'ayi kenan.?" Na
ce "Ka fita ina.?" Ya ce "To zanyi ta zama a cikin
gidane? Ai dole ne in fita." Na ce "Ai sai dai mu fita
tare."
6
Sharrin Jinni 3
Ya yi shiru yana tunani. Can ya ce "Kin ga fa
wannan magana ba ta shiru ba ce, dolene in sanarwa
da Alhaji halin da ake ciki." Na ce "Au wai da kai
shiru zaka yi? Ai ba zai yiwu ba. Domin kuwa
wannan bau bana shiru bane. Ta shi mu tafi kawai
gurin Alhajin.?" Ya ce "To muje.'
Muka kukkule gidan, muka fito muka nufi
gidan Alhaji. Da yake ba nisa a kasa muka je,
saboda layi daya muke da shi.
Da zuwan mu muka same shi a zaune a tsakar
gida shi kadai. Muka yi masa sallama ya amsa gami
da duban mu cikin mamaki. Ya ce cikin fada. "Yau
zan ji shakiyancin banza. Daga gama bikin jiyajiyan nan sai ka dauko ta ku fito yawo.? Yanzu ina
za ku je.?" Sadik ya rusuna ya ce "Alhaji ba yawo
muka fito ba, wata matsala ce ta faru jiya." Ya ce
"To me yake faruwa."
Nan Sadik ya kwashe yadda aka yi ya fadawa
Alhaji. Wani mamaki firgitacce ya kama Alhaji. Ya
ce "Yanzu ya ya aka yi." Ya ce "Zuwa mukai domin
mu sanar maka halin da ake ciki." Alhaji ya ce "shi
kenan, muje cikin gidan, gani nan zuwa." Muka
shiga ciki.
Mamy na ganin mu ta bude baki da salatin ta
baki daya. ta ce "Ku kuma ina zaku..." Kafin mu
bata amsa Alhaji ya shigo, ya ce "Wani abun
7
Amina A. Sharada
mamakine kuma ya samu. Anya kuwa Hajiya Lami
babu wani bakon al'amari tare da yaran nan.?"
Takc ya sanar da ita halin da ake ciki baki
daya. Ta dafe kirji gami da salati, ta cc "Hakika
akwai wani al'amari a tarc da su. Anya kuwa ba'a
dajin nan suka kwaso aljanu ba.?" Alhaji ya cе
"Nima dai abin dana ke tsammani kenan. Amma ko
ma mcyc Allah zai mana maganinsa. Yanzu dai ku
zauna ba inda za ku jc. Ma'ana ba za ku koma ba
har sai an tabbatar an tsare gidan naku tukunna, kar
suje su sabauta ku." Takc murna ta kamamu har
Sadik din.
Alhaji fa ya shiga hada Malamai manya domin
su taimaka a tsare gidanmu. Sai da ya hada
Malamai goma sha uku suka dukufa da karatun
Alkur'ani ba dare ba rana.
Sai da suka yi sauka sau uku, sannan suka
dinga bayar da kafin miyagun mutane da Aljanu
shaidanu ana binnewa a gidan. Sannan muma aka
hadamu aka yi mana rukiya, domin ana zaton ko
yana tare da mu.
To ba abinda ya bayyana a tare da mu, sannan aka
tabbatar mana da zamu iya shiga gidan yanzu ba
wani abu. Muka yi matukar farin ciki. Alhaji da
kansa ya rakamu gidan. Muka yi masa godiya mai
tarin yawa, sannan ya zauna a falon gidan. Ya fara
min fada akan abin da ya kamata in dinga yi dan
8
Sharrin Jinni 3
gudun samun mafakar wani shadanin Aljani а
jikina. Dama dai aljani yafi samun sararin shiga
jikin 'ya mace fiye da da namiji, saboda ita mace
tafi sakaci, domin ita aka umarta da ta suturcе
jikinta domin duk wani abu na daga jikin 'ya mace
al'aura ne. Ba'a kuma ce ya suturce dan mazan
mutane kawai ba, har ma da mazan Shaidanun
Aljanu, wadanda bayan sha'awa ma, sukan auri
mace ba da sanin ya ba, kuma suyi ta biyan
bukatarsu da ita ba tare da an ankaraba, sai tura ta
kai bango sannan suke bayyana kansu, azo ayi ta kai
ruwa rana kafinb su bar jikin mace."
Na ce "To Alhaji. Ta ya ya suke shiga jikin
mace.?" Ya ce "Hanyoyin da suke shiga jikin mace
yana da yawa, amma mafi sauki shi ne ta inda 'ya
mace yafi sakaci da wurin. Misalin barin kai a bude
da kitso, ko tsefaffen kai. sannan yawo da daddare a
tsakar gida kafa ba takalmi. Zaman bakin kofa ko
kan turmi. Shiga bandaki kai babu dauri, da surutai
a bandaki, sannan kuma bayyanar da tsiraici ta
hanyar sanya matsatstsun dunkuna. To wannan ma
bayo ga mazan mutane yake tasiri ba, har ma da na
Al anu baki daya, domin fidda tsiraici yana taka
muhimmiyar rawar gani wajen jawo su.
Kuma dan Allah ki dinga yawaita addu'a da
karatun Alkur'ani mai girma. Ta wannan hanyar ma
9
Amina A. Sharada
zaki iya nisantarsu, ba za su sami damar shigarki ba
muddin kina kiyaye wadannan dokokin."
Na yi matukar farin ciki da jin wannan
shawarwari da Alhaji ya bani. Muka yi masa godiya
mai yawa ya tashi, muka rakashi har bakin get ya
tafi.
***
Zama ya kankama tsakanina da Sadik. Ba wata
fargaba ko hayaniya, sai zuba soyayyarmu muke yi
hankali kwance, domin ba wani abu da yake
damunmu barema ya firgitamu.
Muna baiwa fulawowin gidan ruwa ni da
Sadik da tiyo, ta hanyar jonota a jikin fanfon dake
tsakiyar gadin din gidan. Dama abin ban ruwan a a
hannun Sadik yake, yana ta jika fulawoyin. Sai ya
dan watso min ruwa, naji sanyi ya shigeni, gashi
kuma dama lokacin sanyi ya dan fara shigowa.
Na ce "Lala-lala! Ka zuba min ruwa? Wallahi
sai na rama." Ya ce "To rama din."
Na shammace shi na fisge tiyon na feshe shi da
ruwa ina dariya. Sai da na jike shi. Ya biyoni da
gudu muka shoga cikin gida da gudu. Na fada
dakina ina kokarin rufe kofa, sai ya rigani, ya
danno kofar ta bude, na afka kan gadona, shima ya
bini yana cewa "Yau sai kin gaya min wanda kika
jika."
10
Sharrin Jinni 3
Ni kuma ina dariya ina cewa "Dan Allah Yaya
kayi hakuri, wallahi na daina." Ya dauki filo yana
maka min. Ni muma ina kukan kагуа.
Na kukuta na janyo kwalar rigarsa na sabule
da karfi, ni kuma na ware rogar barcina mai tsaga a
gaba.
Kallo daya ya yi min na rikita masa zuciya.
Take ya afka min muka saka labule.
Muna zaune a falo, na ce "Yaya Sadik." Ya ce
"Na'am." Na ce "Ina son in koyi mota wallahi." Ya
ce "Ai ba wani abu, zan dinga koya miki. Kullum da
yamma ma dinga fita." Ina jin haka nayi tsalle da
ihun murnata, na afka masa a jiki ina dariya. Na ce
"Dan Allah Yaya Sadik mu fara daga yau." Ya ce
"To shi kenan, in an jima sai ki shirya mmu fara,
amma fa da sharadi. Ko kin iya ba zan barki ki
dinga tuka kanki ba, domin dai kin san ina da kishi,
shi yasa na ke shakkar koya miki, kar ki sami kafar
yawo. Sai dai muyi da wajewa, in kin fara tuki da
kanki ba shiga ba fita sai in ta kama dole.?" Na ce
"Na yarda." Ya ce "Shi kenan, ki shirya da yamma
zan fara koya miki." Na ce "To."
Kwanci tashi kullum sai mun je da yamma Sadik ya
koya min, har na fata gwanancewa, na kan dan yi
tafiya mai nisa na dawo da kaina. Sadik dan murna
sai ya tafa min, in na fito ya rungumeni yana min
karka. Nima murna a guna b bayani.
11
Amina A. Sharada
Sadik ya ce "In Allah ya sa ya fara aiki ya
sami kudi zai saya min mota tawa ta kaina." Nan
ma murna a guna kamar me.
Yaua dai kauye muka nufa domin mu gaishe
da su Dagaci, su Inna da Babba Tasallah. Alhaji
yana yawan yi mana fada akan cewa mu dinga
yawan zuwa muna gaishesu, shi ne zamu dinga
samun albarkarsu akowanne lokaci, kuma zamu
dinga ganin budi a rayuwa, domin iyaye ba abin
wasa ba ne. Shi yasa a kowanne wata sai munje
mun gaishe su.
Gidan Dagaci muke fara zuwa, sannan muje
gidan Baba Tasallah sai mu karkata gidan Inna.
Bamu taba kwana ba, duk san da muka je a ranar
zamu dawo, sai dai mukan kai dare. Dagaci ne ma
ya ce zuwan da muke yi duk wata ya yi kusa. Ya
deba mana wata uku-uku in ba so muke da ma muyi
ta yawo a hanya ba. Haka muka hakura akan sai
bayan wata ukun ma dinga zuwa.
Rannan ina kwance a dakin Sadik da daddare
muna hira har wani lokaci. Sadik ya fara jangwalata
na son mu kebe. Ni kuma bana bukatar komai a
wannan lokaci. Sai na yi masa karya na ce cikina
yana ciwo. Ya ce "To shi kenan Allah ya sauwake."
Na ce "Amin." Sannan ya mike ya kawo min
12
Sharrin Jinni 3
magani. Ala dole na sha, domin kar ya dagoni.
Haka muka kwanta har kusan asuba.
Da asuba naga ya fara dan lalube-lalube.
Kawai sai na yi fuska, na ce "Nifa ban warke ba."
Ya ce "Wallahi karya ne." Na ce "To shi kenan,
bara in bar maka dakin." Na tashi na yi tafiyata
dakina, na yi kwanciyata.
Sadik na dakinsa, can kusan assalatu sai yaji kamar
an bude get din gidan. Dan haka sai ya yi sauri ya
daga labulen dake windown dakinsa. Yana kallon
harabar gidan ne ya hango wani kamar Ibrahim ya
fita da doguwar rigar barci. Ya fara mamakin meya
kawo Ibrahim gidan sa a asubar nan.
Wuf! Sai ya mike domin ya je dakina ya gaya
min abinda ya gani. Yana shiga ya sameni ina ta
sharar barci. Ya dagani da zummar ya dorani akan
cinyarsa. kawai sai yayi ido biyu da gajeran wandan
Ibrahim a karkashina ina kai a kwance. Ya yi saurin
fusgoshi dan gasgata abinda idon sa ke barazanar
nuna masa. Hakika babu makawa idonsa ba gaibu
yake ba shi ba. Wandonsa ne!.
Juyawar da zai yi sai ga agogon Ibrahim shima
a yashe bisa gadon. Duk abin nan idona a rufe yake,
ban san me ke faruwa ba, dan haka ban ko bude
idona ba ma na sake gyara kwanciyata a cinyar
Sadik.
13
Amina A. Sharada
Ya janyeni a hankali ya dauke wadannan
kayan. Wato agogo da gajeran wandon ya fice
abinsa. A zatona zuwa zai yi ya dawo domin idona a
rufe yake na ci gaba da kwanciya abina ina sauraron
dawowar Sadik.
Shiru bai dawo ba, na tashi na yi sallah, na
koma na kwanta abuna har gari ya yi haske, sannan
na fito na nufi kitchen domin in dora mana abin
kalacin safe.
Har na gama banga Sadik ba, sabanin yadda
ada muke ta aikin tare, muna yi muna wasa da juna.
Na jera mana abincin mu akan daning table na koma
dakin Sadik domin inga in barci yake in tashe shi.
Na jima a tsaye ina kwankwasa kofar, amma
shiru bai ta shi ba bare ya bude. Na yi kira, na yi
kira shiru. Sai na zaci abin da na yi masa a daren
jiya ne ya bashi haushi har ya ki fitowa. Na koma
kan kujerar falo na kwanta ina tunanin lallai ma
Sadik, wato rana daya ta mai kaya, rana dubu ta
barawo, wato dan yau daya na nuna masa haka shi
ne zai yi fushi dani? Ko da yake ta wajen wannan fa
Sadik ba shi da hakuri. Haka zan bashi hakuri in ya
fito, domin ni ce da laifi."
Ina nan kwance sai naji yana bude kofa. Na
tashi da sauri na dubeshi bayan ya fito. A shirye
yake tsaf! Ga alama ma fita zai yi. Ganin fuskarsa ta
sani bugun kirji tafi sau ashirin masaki domin ban
14
Sharrin Jinni 3
taba ganinsa a wannan yanayi ba. Yazo zai giftani
ya wuce. Na yi wuf! Na mike na shiga gabansa. Na
ce "Sadik ina zaka je ko karyawa fa ba muyi ba."
Ya kewayeni. "Kina iya karyawa in kin ga dama."
Ya sa kai ya fice.
Na yi turus dani a tsaye. Na sake binsa kafin
ya kai kofa, na ce cikin sanyin murya. "Sadik ka yi
hakuri, na san na 6ata maka rai. Wallahi ba zan kara
ba." Ya juyo a fusace ya ce "Ya rage naki kuma."
Ya fice abinsa ya barni a tsaye. Ban san cewa
hawaye na zubo min ba sai da na ga ya digo min a
hannu, sannan na lura. Na koma na kwanta akan
doguwar kujera nima na kasa cin komai.
Haka na kwanta ina tunani har azahar tayi ban
iya kulla komai ba. A daddafe nayi abinci na ma,
na ajiye ina jiran ya dawo ko kafin loka a huce
daga fushin da yake yi.
A lokacin da ya dawo ina dakina ina sallah,
dan haka banji dawowarsa ba. Da na gama na fito
domin in duba ko ya dawo. Na duba dakinsa akulle
yake, sai na zaci ko bai dawo ba. Na koma na zauna
na kasa cin komai. Tun safe ban karya ba, na yi
wani rangwam dani kamar mara lafiya. Domin
komai ma ba dadinsa na ke ji ba. Can sai naji shi ya
bude kofa zai fito. Na zuba ido saitin kofar. Ina
ganin ya fito na ce "Sadik ashe ka dawo? Wallahi
ban sani ba, ina daki ina sallah." Ko kallona ma bai
15
Amina A. Sharada
yi ba. bare ya san abinda na ce. Na bishi da sauri
"Sadik na gama abincin rana fa, kai na ke jira mu
ci.
"Bani da muradi."
Wani dunkulallen bacin rai ya tsaya min a
wuya. Na sunkuya a gurin ina kuka. Ya yi ficewarsa
abinsa
Sai da na jima ina kuka a gurin sannan na
tashi. Naji sam cikina ma ya cika bana jin yuwan
bare kishirwa. Na koma dakina na kwanta ina ta
tunanin anya ko wannan laifin da nake ganin na
yiwa Sadik shi ya janyo wannan fushi kuwa? Kai
ina ga dai akwai wanì laifin na daban, domin da ace
wannan ne kawai da yanzu mun shirya, duk kuwa
da cewa bamu taba koda musu da shi ba bare in san
irin fushin zuciyarsa
Dare ya yi, na shiga wanka na shirya tsaf
kamar yadda na saba in zanje gurin Sadik, na feshe
jikina da turare, na sanya kayan dana san Sadik na
matukar kaunar in sanyasu. Na nufi dakinsa a
lokacin ba abinda ya ga cikina sai ruwan shayi,
domin abinci ba zaì ciwu ba a gurina.
Na tsaya a bakin kofar sa na yi ta
kwankwasawa, shiru ya ki budewa. Ni kuma na fi
barin gurin, sai da na kai kamar awa guda ina bugun
kofar har hannuna ya fara radadi Sadik bai bude
min ba. Ina nan tsaye sai gashi ya bude a fusace, ya
16
Sharrin Jinni 3
dubeni sama da kasa. Da dai kamar ya ce in shigo,
to ko mai ya tuna sai kawai naga ya yi wani kicinkicin da shi, ya ce "Wai yama za'ayi ki dinga buga
min kofa haka kin hanani barci? Karki kara!." Na
durkusa ina cewa "Dan Allah Sadik kayi hakuri, na
tuba wallahi ba zan sake ba. Sadik kayi hakuri."
Idanuna hawaye sharab-sharab.
Kawai Sadik sai ya maida kofarsa ya rufe, ya
ce "Zancen ki ke so." Nan na kwanta ina ta kuka."
Nai masa magiya ya bude min, amma ko a jikinsa.
Haka na kwanta a gurin nan har gari ya waye.ban
tashi ba.
Da ya bude kofarsa ya ganni sai ya tsallakeni
kawai ya yi gaba abinsa. Sai kamshin turaren sa ne
ya bugeni. Na yi zumbur na mike ya yin da ya kai
bakin kofar fita. Na bishi da guduna ina cewa
"Sadik ka yafe min dan Allah. Sadik kar Allah ya
kamani da laifin saba makа."
Ko kallona bai yi ba ya wuce yaja kofar da
karfi ya barni tsaye ina ta faman kuka.
Wasa-wasa sai da muka share kwanaki uku
muna haka da Sadik. Duk nabi na rame, na lallace.
Sai kawai na yanke shawarar in hakura in daina
kula shi nima, domin dai duk wani rarrashi da zanyi
ma sa na yi, haka kuma duk wani ban hakuri nayi.
To gara nima in kama kaina tunda abin hakane.
17
Amina A. Sharada
Saboda haka nima sai na shiga boye kaina ba
ruwana da shi, in kuma mun hadu a falo baya kulani
nima bana kulashi, sai dai ya wuce nima na wuce,
ko kallonsa bana yi. Hakan ne ya sa shi matukar
fadawa wani sabon bakin cikin.
In na fito daga dakina yana cikin falon, sai
inga ya yi sauri ya dago kai ya kalleni. Ni ko sai in
dauke kai abina. Haka muka yi ta yi da shi ko zai
sauka. Amma ina! Sai ma abinda ma ya yi gaba.
Rannan ina zuane a dakin, sai naha Sadik ya yi
sauri ya banko kofa ya shigo yana huci. Ya tsareni
da ido da alamar tambaya a bakinsa, amma baiyi
magana ba. Nima kuma ban yi masa magana ba na
kauda kai.
Ya shigo cikin tsananin bacin rai ya cakumeni
ya jijjigani yana cewa "Wato Hamdiyya abin da
zaki dinga yi kenan ko? Dan na kyalki da halinki
shi ne zaki dinga cin amanata ko?"
Take naji yawun bakina ya dauke. Naji ina
jawo numfashina da kyar, domin barazanar
daukewa da yake yi.
Da kyar na bude bakina na ce "Sadik me ka ke
neman doramin.?" Y ace "Kina nufin kice karya
nake? Da fa idona bai gani ba bane. Shi yasa na
bishi da gudu na rasa lungun da ya shiga, wallahi da
sai na sassarashi, in yaso duk abinda za'ayi sai dai
18
Sharrin Jinni 39
ayi. Kuma ai duk kece cikakkiyar munafukar da
kika cuceni kika yaudareni!!".
"Wai Sadik na ce maka me kake zargina da
shi? Kana nufin ina kawo maka mazan banza cikin
gida.?"
Ya yi tsaki da karfi ya ingizani waje, ya juya
abinsa. Ina ban sami damar kuka ba, domin wannan
lamarin yafi gaban kuka. Na bishi da gudu har
dakinsa, na afka na tsaya a gabansa. na ce "Ban fa
gane abinda ka ke nufi ba........."
Kyawawan marirrika guda uku da naji sun
sauka akan fuskata sune suka katseni. Ya zaro belt
ya fara tafkata, ina ihu da neman taimako.
Sai da ya gaji da dukana sannan ya fice ya
barni anan jikina duk ya yi tsami. Na mike da kyar,
na nufi dakina na kwanta. Take zazzabi ya rufeni na
kwanta ina ta jin jiki.
A maimakon jikin Sadik ya danyi sanyi. Sai
lissafinsa ma ya kara dagulewa. Ya fice a hasale
ransa a bace ya dauki motarsa ya fice, ko ganin
gabansa baya yi, ya dauki hanyar air port yana tsula
uban gudu.
Yana cikin wannan hali ne kan motar ya
kwace ya saki hanya (kan titi) ya daki wata katuwar
bishiya dake gefen hanya ya tintsiro.
*** 19
Amina A. Sharada
Ina kwance jikina duk babu dadi. Sai na dan
fito falo domin in dauki magani, in na gama shan
maganin sai in kwanta.
Anan falon ina tunanin abinda ke faruwa a
tsakanina da Sadik. Na ce a raina "Wai Sadik me
yake nufi da ni ne? Ko yana zargina ne da kula wani
namijin? To in ko hakane na shiga uku, ya zanyi ya
gane gaskiyar bana kula kowa.?"
Na yi shiru ina yunno amsar. Sai naji Alhaji na
sallama. Na ce a raina "Shi kenan ta faru ta kare,
wai an yiwa mai dami daya sata. Na san ma zuwa
ya yi ya gayawa Alhaji. Amma ko Sadik bai kyauta
ba, mai makon ya sameni ni da shi ya fuskanci
gaskiya shi ne ya je ya fadawa Alhaji...?"
Ina cikin wannan tunani sai ga shi ya shigo
falin. Na yi masa sannu da zuwa, na tashi zan kawo
masa lemo da ruwa. Sai ya ce in zauna baya bukatar
komai. Na dawo na zauna na gaishe shi kaina a
sunkuye.
Ya ce "Wai ina Sadik ya ce za shi ne.?" Na yi
shiru, domin ban san inda ya yi ba. Na ce "Wallahi
bai ce min ga inda za shi ba."
Ya yi tsaki, sannan ya ce "Shi kenan, tashi ki
shirya, za ku je asibiti dubiya ke da Hajiya Lami."
Na ce "To Alhaji ai baya nan, kar kuma ya dawo ya
yi min fada in ya ga bana nan." Ya ce "Ai nine na
20
Sharrin Jinni 3
cc kije. In ya yi magana ma kicc nina zo da kaina na
ce