An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
INNIJ
NA
AMINA ABDULLAHI SHARADA
(MRS. AHMED YUSUF)
SHARRIN JINNI
2
NA
AMINA ABDULLAHI SHARADA
(MRS AHMADYUSUF HADEJEA)
1
Hakkin Mallaka (H) Amina Abdullahi Sharada Copy Right (C) Amina Abdullahi Sharada
GODIYA
Ga Allah subahanahu wata'ala da ya bani ikon kammala wannan littafi na biyu, Allah ka kara Annabi Muhammad daraja da daukaka. Ameen summa ameen.
gadi)
GAISUWA GAREKU
Ummi Sulaiman
Hajiya Sulaiman
Nafisa Kawu
Asama'au Murtala
Fati Ya'u
Maryam Alhaji
Sakina Tasi
Saudc Balarabe Darki
Safiya Balarabe
Aisha A. Kurawa
Hajiya Ali
Dukkan ku gaisuwa ce daga Zainab Sulaiman (Dan
Zee Baby Maiduguri
Fati Abdullahi
FATAN ALHERI GAREKU
Nafisa Muhammad Sheka. Marubuciyar Mugun
Yanayi.
Wasila Muhammad
Jamila Muhammad
hadiza Bashir Dan dago
Statc.
Ummi Usman
Hadiza Ciroma
Sagir Muhammad Sheka
Hauwwa Muhammad
Binta Muhammmad
Na yi muku fatan Alhcri, daga Nuaman Adamawa
GAISUWA TA MUSAMMAN
Ga dukkan masoyana, masu aiko min da sakonni
text ko waya, na gode Allah ya bar kauna. Ameen
summa ameen.
BUGAWA A COMPUTER
Mubarak M.B. Gadon kaya
07039034583
3
SHARRIN JINNI 2
"Hamdiyya" LAbubakar." Abinda ya fito daga bakuna
mu kcnan ya yin da muka yi arba da juna, ji muke
tamkar mu rungume juna, don tsananin so da kauna, tuni
mun mance da wadanda ke gurin, sai da Alhaji ya yi
gyaran murya. sannan muka dawo daga duniyar shaukin
Kauna.
"Ku zauna a yi maganar a nutse." In ji Alhaji. Ta
ke muka cika umaminsa muka zauna.
"Hamdiyya ya ya akai kika zo nan.?" Tambayar da
Abubakar ya yi min. Na ce "Ka bari mu nutsu na fada
maka, domin nima ina da tambayar da nake son na yi
maka."
"Daman kun san junanku.?" Inji Alhaji. Abubakar
ne ya fara magana, wanda suke kira da Sadık, ya ce
"Alhaji, ai wannan itace yarinyar da nake son, sanadinta
Dagaci ya ce in komo garinka da karatu ko lamarin ya
wuce." Ibrahim, wanda tuni zuciyarsa ta fara yamustewa
tun san da ya fahimci abinda ke tsakanina da Sadik, ya
ce "Ai wannan da kenan, domin a yanzu Hamdiyya ta
sauya masoyi." gani Alhaji ya daka masa tsawa da cewa,
"Kai wannnan mutumin banza ne, baka da kunya, Sadik
ba yayanka bane.?" Nan da nan ya yi kicin-kicin. Shiko
Abubakar ji ya ke, da wasa Ibrahim ya ke yi, sai ya
kama dariya ya ce, "Haba Yaro, na gaba ya yi gaba,
baya sai tsintar hala." Nan aka yi ta dariya. Shi ko
borahim kamar an yi ma sa mutuwa. Na dubi Sadik na
-tik ga Haule fa." ya ce, "Au Haule yaus he kika
4
zo.?" ta ce, "Ai tunwannan sakon da ka bani na kawowa
Hamdiyya, ban sami kowa ba, sai wannan karon, shine
ban koma gida ba, saiyau dai nake son komawa.
Nan aka ci aka sha, aka yi ta raha cikin farin ciki,
musamman ma Sadik, shi da farin cikin ya zame masa
kashi biyu, ga murnar gama karatu, ga ta ganina.
Bayan komai ya nutsu, sai Alhaji ya fara mika
sakon taya murna ga Sadik, gami da mika masa
mukullin mota, amatsayin nasa gift dinna murnar
kammala karatun shi da ya yi, kuma ya saıni
kyakkyawan sakamako. Haka kuma Mami ta yi masa
dunkuna masu kyan gaske, kamar su shaddodi, yaduka
masu tsada biyu, ga boyil da sauran su kananun kaya,
kamar su,sabbin jeans da t,shart. da sauransu. Shi kuma
Ibrahim ya mike cikin nunku furuci ya ce, "Ni a da
takalma na nawa gift din da huluna da agogo masu tsada
kala uku, to amma yanzu na janye tunda ka furta ka
kwace min budurwa, aka kwashe da dariya. ya ce. "Ва
fa abin dariya bane, domin da gaske nake yi ba da wasa
ba." Alhaji ya ce 'To kai duk abinda ake baka ji ba,
kamar wanda ke zaune, da ka cewa yana gida suna
soyayya, shine ma sanadin barinsa gida, naje na hada shi
na sa shi a makaranta yaci gaba da karatunsa, to kuma
ya ya za'ayi sama ta kai kazo kace wai kana sonta,
bayan kuma akansa ne ga yadda lamarin yake." Ibrahim
ya mike a fusace, yana cewa, "Tunda aka gaji da
bayanansa, wallahi ba za'ayi auren ba." Alhaji ya ce, "Ai
kuma ba ka isa ba, kaga sakaran yaro, ashe haka ka ke.?
Sam albasa ba tayi halin ruwa ba, kai duniya ka lalace,
wai ace danka na cikin ka, kana gaya masa magana yana
5
mayar maka? Sadik ya cc. "Alhaji kayi hakuri, zai
daina ne, yarinta ce."
"Haba kamar wannan in bai girma ba sai yau she.?
Yaron da ya kai ashirin da takwas, kawai dai dan ya
samu ba 'ayi masa fada ne shi yasa ya ke abinda ya ga
dama, amma da ga yau na dinga tsawa ta masa Mami
ta yi murmushi ta ce, "Zancen yaushe, ai yanzu ya riga
ya zama saurayi, kadai kawai kace ya nemi wata
yarinyar, sai kayi masa auren in auren yake so." Alhaji
ya сс. "Нaka ne kam, abinda za'ayi kenan.
Muna zaunc ni da Sadik muna hira, acikin hirar
tamu nc ya kle tambayata yada akayi nazo nan gidan da
aiki Ta ke na kwashe duk abinda ya faru tun daga
farko har karshe na sanara masa, ya yi matukar
mamakin abin, har ma ya kc cewa "Wata rana ya taba
zuwa gidan, sai ya ji Mami na tambayar Nusaiba
"Hamdiya ta fita ne. Sai Nusaiba ta ce, "Eh. Yayа
labrahim ne zai kaita." Toni ban gane kc ake nufi ba, na
dauka wata daga cikin 'yan uwan Mami, domin ance
suna linzamí, don haka na dai yi tunanin ki, amma ban
kawo kece a gidan ba, da ba abinda zai mai da ni ba tare
da na ganki ba." Na cc, "Nima fa wata rana na tabа
ganin ya zo suna tafiya da Alhaji, daga nesa kamar
Dagaci,amma naga Nusaiba da Ibrahim da Mami sun
shiga can sun gaisa. Da na tambayi Nusaíba, sai ta ce
min wani wan Alhaji ne yazo daga kauye, bai ma faye
zuwa so sai ba." sai na cc,"Amma kika ki yi min
magana nace na gaishc shi.? Shine ta ce, "In bari in ya
fita zai tafi, sai muje mu gaisa." To alokacin da ya fita
Mami ta sa na yi ma ta aranging din dakinta, shine ban
6
samu ganinsa ba, da tun a lokacin zan gane komai." Ya
yi murmushi, sannan ya ce, "Allah ne bai so ki sa ni ba
sai yanzun."
"Hamdiyya." Ya kira sunana a sanyayc.
"Na'am." Ni ma na amsa masa a sanyaye. ya ce
"Yanzu Hamdıyya ya ya zamu yi da maganar auren
mu.? Kin san dai yadda mutane suka tsane
mu,musammman ma iyayen mu, sun ki banu goyon
baya akan wannan lamari." na ce, "Ai tunda Alhaji ya sa
baki komai zai zo da sauki, shi zamu je mu samu akan
maganar, in ba haka ba kuwa sai dai muyi ta zama a
haka, domin iyayen mu ba zasu yarda ba......"
"Shima Alhajin ba zai bada goyon baya ba." Muka
ji murya ta bayanmu, mu jiya sai muka ga Ibrahim tsaye
ransa a bace. Sadik ya ce, "Saboda mai kace Alhaji ba
zai bayar da goyon baya ba."
"Saboda ni na dace da a baiwa Hamdiyya, shine
kawai zaka shishshige ka hanata, wallahi ka bar gani
Alhaji yana daka ta taka yana yi maka komai, wannnan
karon sai na bata ka a gurin Alhajin, kuma in har baka
rabu da Hamdiyya ba sai na sa Alhaji ya kore ka daga
gidan nan, kuma kora ta wulakanci." Nace, "Dakata
Ibrahim, shin wai duk wannan abin da kake ba dan ni
kake ba.?" Ya ce, "Da kene, kuma sai kince kina sona
kin rabu da shi zan gyale shi." Na ce, "Ni na ce bana
sonka, bana kaunar ka. sai ya ya.?" Ya ce, "Ai kin yi ta
banza, shi din da kike so ba za ki aure shi ba muddin ina
raye." Zan sa ke magana sai ya daga min hannu, alamar
in dakata, ya ce da ni, "Ta shi mu bar masa gurin." Haka
na tashi muka bar masa gurin yana ta faman fadar
7
maganganu akan Sadik, ko waiwayen sa ba mu yi bam
sai ma danya da muke masa, don muna ganinsa kamar
wani zarare
Tun da Sadik ya dawo, shine ya ke yiwa Alhaji
duk wasu abubuwa, kamar su aike da ya shafi harkar
aikinsa, da sauransu, su shigar da kudi banki da fito da
su. Dakin Alhaji kuwa kamar na Sadik ne, domin Alhaji
ya riga ya yar da da Sadik, domin yaro ne nutsatstse,
gashi ba ha'inci ko son zuciya a lamarinsa, don haka
Alhaji ya ke mutukar son Sadik, ko fansa Ibrahin bai
amincewa ba kamar yanda ya amincewa Sadik ba.
Wata rana Alhaji yana gida, sai ya kira Sadik
domin ya kai masa wasu kudi banki. Sadik ya amsa,
sannan ya ce, "Zaije ya shirya, sannna ya zo ya tafi."
Alhaji yace, "To." Ya fita shi kuwa ya shirya ya fice ya
bar kudin nan a ajiye, duk abin nan Ibrahim na labe
yana jin duk abinda ake cewa, don haka yana ganin
Alhaji ya fita sai ya yi wuf! ya shige bayan ya faki idon
mutane ya dauki kudin ya fita abinda, ya kai dakinsa ya
boye ya ja bakinsa ya tsuke abinsa.
Sai da Sadik ya gama shiryawa, sannan ya taho da
hanzarinsa zai dau kudi. Kudi su ka ce, "Dauke mu inda
ka ajiye mu." Ya yi neman duniyar nan bai gansu ba, sai
ya hakura ya fita da zaton ko Alhaji ya fasa zai kai da
kansa, don haka shima sai ya fice abinsa bai damu ba.
Yamma na yi sai Alhaji ya dawo ya sami Sadik a
gida ya ce, "Ince ka kai min kudin nan da wuri.?" Ya ce.
"Ah. na dauka ka kai da kanka, da na duba ban gansu
8
ba " Alhajı ya yi salati, ya ce, 'Wanc irin ka duba baka
gansu ba, anan nan fa na ajiyc ma ka jakar kudin fa."
Sadik ya yi tsila-tsila da shi, domin abin mamaki abin da
ba'a taba yi a cikin gidan ba sai ga shi yaua ya faru, ya
cc, "Wallahi Alhaji ni ma nayi mamakin rashin ganin
kudaden nan, domin tunda na shigo na duba ban gansu
ba, na ke ta tunanin yadda aka yi, to amma a lokacin sai
nayi zaton kaine za ka kai da kanka." Ya ce, "Da ni zan
kai ai zan ce ma ka ka barshi na kai. Jeka ma za ka yi
min kiran Hajiya." Ya fita da sauri, yana mamakin
wannan abu. Jim kadan sai gasu, su ka zauna, Alhaji ya
dube mu ya ce, "Ba wani abu bane ya sa na kiraku ba
illah, tunda na ke a gidan nan ban taba ajiye abuba na
rasa shi ba sai yau. Na ajiye kudi Sadik zai kai min
banki, sai yazo bai gansu ba." Sai Ibrahim ya cе,
"Wanda aka aika ai shi zai daukar ma ka, tunda mu dai
nan ba mu taba daukar maka komai ba." Alhaji ya cе
"Ya ya akai kai ka san cewa shine ya dauka.?" Ya cе
"Ai gani nayi shi aka aika ya kaimaka banki,lokacin da
ma ka aike shi ba bu wanda ya sa ni ba dan yanzu kudin
sun 6ata ba." Ya cce, "Ai ba wannanne karo na farko da
na taba aiken sa ba, mai yasa duka bai taba daukar min
ba sai wannan karon." ya cc, "Ka sa ni ko daman so
yake ka amince da shi daga baya kuma sai ya cuce
ka...."
"Dakata Ibrahim, in za ka so wanda za ka likawa
sata, amma ban da ni, domin sata ba sana'a ta bace, haka
kawai sai ka ringa neman doramin sata banji ba bangani
ba......?" Alhaji ya tari numfashinsa da cewa, "dakata
Sadik, ai shima akwai ayar tambaya akansa, domin ina
gan n yana da hannu dumu-dumu akan wannan
lanrarm Marmi ta yi farat tace, "A'a Alhaji, Ya ya
za'avi ka dorawa danka sata, ai gaskiyar Ibrahim, da sun
taba yi maka ne ? Alhaji ya kalleta cikin mamaki ya ce,
"Kar kı zama mai son kanki da yawa mana, abinda ban
taba zatonki da shi ba, kar ki manta, wannan din ma
danki netunda dan wanane amma ai gurbin ido ba ido
ban..'ya ci gaba, "Amma kin ban mamaki wallahi..."
Tacc. "A'a. haka kawai a cutar min da dana, ni ba
zan yarda bà wallahi" Yace, "Shi kenan, ku tashi ku
tafi" muka tashi zámu fita, sai ya dubi Nusaiba ya ce,
"Nusaiba zo in dan sa kí wani aiki." ta ce, "To." Тake
ma ta žauna, ya dubeta, "Aikin da nake son in sa kaki
shine, "Ki sakawa Yayanki ido, ki gani zai kai Jakar
Kudin han dakin Sadik, domin nasan shine ya dauka, ba
dan komai ba kuwa sai don adawa da yake yi da Sadik
din akan wannan yarinyar." Ta ce, "Alhaji ai ni nake
masa gyaran dakinsa, in naje zan dubba in gani,in dai
tana nan zan dauko maka ita." ya ce, "Yauwwa, Allah
ya yi miki albarka, ma ża ki sa himma.
Muna zaune da Sadik muna hira, can na dube shi
nace, "Wallabi Sadik badan karatuna ba da tuni na koma
gida." ya ce, "Sabodá mai fa?" na ce, "Sabida takurawar
da Ibrahim ke mäka bana so." ya ce "Ba komai,wata ran
sai labari, ita kanta Mamin tun daga sanda kudin Alhajin
su ka 6ata, sai na ga taja baya da ni, tana dauddaure min
fuska!" yace, "Ai ba ke kadai ta ke wa haka ba, har ni,
domin in na gaishe ta bata amsawa." na yi shiru, can
nace "Allah sarki ba ruwansa, wallahi ina ma halinsa su
ka yi wo, da anji dadi da su." ya ce, "Su ma da ba haka
10
su ke ba, maganar mu da ke ne ta janyo mana wannan
bakın jinin." na ce, "mu ci gaba da hakuri, ba komai,
kamar yadda ka ce, wata rana sai labari.
Muna cikin wannan hirar nan sai ga Nusaiba a
sukwane, ta yi birki a gaban mu ta ce cikin murna
"Albishirin ku.?" muka ce "Goro." ta cc. "To anga kudin
a dakin Yaya Ibrahim." muna jin wannnan maganar
muka mike cikin farin ciki muna cewa ."Alihadulillah.
gaskiya ta bayyana." ta ce "kuzo inji Alhaji." muka tashi
muka bita da sauri, muka tarar da su Mami a zaune a
gaban Alhaji, muma muka zauna muna jiran abinda
zaice. Ya dubi Sadik ya cc. "Sadik an ga kudin nan fa."
Sadik ya ce, "To madallah da aka gansu." ya ce "V
dakin Ibrahim Nusaiba ta gano su...." Mami ta katse shi
ta hanyar cewa, "Wai kai Alhaji sai ka ringa cewa a
fakin Ibrahim, ka sani ko kai masa akai."
"Wa zai kai masa.?" Alhaji ya tambaya.
"Oho. wa ya san wanda ya sata, kasan dai sata ba
halin Ibrahim ba ce, sai dai dora masa aka yi."
"Haba Lami, ki dai na irin wannan magana, wai ba
ki san adawar da ke tsakanin wanann yaron da lbrahim
ba ne, ni fa na riga nasan abinda ke tsakaninsu, ba wai
ya dauka da sunan sata bane, ya dauka ne domin ya bata
shi a gurina.... To na gane don haka wannan shinc na
karshe kar ka sa ke. Kai kuma Sadik dan Allah ka yi
hakuri akan abinda ya yi maka na son kala maka sharrin
sa...."
Sadik ya katsa Alhaji. "Alhaji ba komai, wanna
duk ya wuce a wajena, ni Ibrahim dan uwana ne, bani dr
tamkarsa, don haka bazan taba gudunsa ba ko da dai-dai
11
da rana daya ne."
Alhaji ya cc, "Shi ya sa na ke sonka kana da hankali da tunani mai kyau, Allah ya yi maka albarka. ku tashi ku tafi na sallame ku.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah Yau dai inun kammala akaratun mu na makarantar sakandare, murna
gun Sadik abin ba'a agana, domin har karamin fati ya hada min domin taya ni murna, ya kuma ce, "Ya kamata
muje mu sanar da Alhaji batun aurėn mu ko.?" na ce "To
ai kai ya kamata ka yi masa maganar, kaji abinda zaj
сс."ya сс "zan yi masa ne, amma in tsoron kar Ibrahim
ya kulla mana kisa a wajen Alhaji, domin ya sha
alwashin ba zai bari mu yi aure ba." na ce "Kasan Alhaji
baya da karbar zuga, sai dai Mami, ban sa ni ba ko ita ce
zata zuga Ibrahim dan ya ga ko ta wacce hanya an raba
mu da kai: Na fuskanci tunda na ce bana son danta
shikenan take nuna min wasu halaye, dan ma karatun
nan ya tsai da ni, da tuni na koma gida." ya ce "Ke kuma
in kika koma gidan ai lamari ya baci, kin san dai Alhaji
ne zai jagoranci auren mu, in kuwa kika tafi kin san ba
zai sake saurarar mu ba." nace. "Shikenan sai dai mu
zaunaa a haka din har Allah ya kawo lokácin
rabuwarmu,amma sam abinda Mami take min bana jin
dadin shi ke kadan."
da ni
"Ki ci gaba da hakuri komai yana da iyaka." ya ce
12
***
A gaskıya Mami ki san yadda za ki yi ki raba su,
nifa sai na auri yarinyar na."
"To ya ya kake so Ibrahım.? Ka san dai Alhajiba
yarda zai yi ba dai, kana jin yanda muka yi shi jiya."
"Haka ne, to amma na gano mana wata dabara ko
zata yiwu.?"
"Fadi in ji." ta ce da shi.
"Wai daman so na ke yi muna jin yanda Alhaji zai
kori Sadik din daga gidan nan, in yaso sai in ja ra'ayinta
bisa dole."
"Wannan gurguwar shawara ce, kai ma kasan ba
zai kore shi ba, domin yadda Alhaji yake son Sadik ko
kai baya so haka." Mami fada.
"Abinda naga yati kawai shine mu takurawa
Sadik din har ya gwammace ya koma gida abinsa, kinga
sai musan yadda zamu yi mu hada a yi auren."
"Yawwa, ka kawo shawara mai kyau, ka barni ma
ni kadai na ishi, ka barni da shi kawai.
Yana zaune shi kadai yana faman tunani, sai ga
Ibrahim nan da fara'arsa da komai, ya zauna kusa da shi
ya ce, "Sadik Alhaji ya ce ka zo, ka rani zamu karбo
masa wasu takardu a wani kamfani."
"Yana ina Albajin.?" Sadik ya tambaya.
'Ya fita dazun nan." Ibrahim ya се.
"Ina cewa ya yi tafiya." Sadik ya cе.
"Ai kafin ya yi tafiyar ya ce mujc, amma yaje in baza ka je ba kayi zamanka ni naje." Ibrahim ya ce yana kallon Sadik yana murmushi.
"Yaushe zance ba zani aiken Alhaji ba, ka shiga ka
13
mu tafi, in kuma ka shirya tashi mu wuce.
"A'a ban shirya ba, yanzu dai nake son shiryawa
In ji Ibrahim.
"To ina jiranka anan." Sadik ya ce da shi. Ya yinda
shi kuma ya sa kai ya wucc, yaje ya samu Mami ya ce
ma ta "Ya yarda zai bini." ta ce "Ma za kujc, zan y
musu waya kafın kuje.
Tunda suka shiga motar ba wanda ya sa ke
magana, gudu kawai ya ke kamar zai tashi sama, sai da
Sadik ya dan tsorata da gudun, anan ne ma ya ke cewa. "Ka dan rage gudun mana ya yi yawa." Ko kallonsabai
yi ba. shima kuma ya ja bakinsa ya yi shiru, sai da su kaci gaba da tafiya mai nisam sannan ya karya kwana
cikin, wani daji, bayan sun rabu da mutanc kimanin
tafiyar mil uku, sai suka doshi wani dan gidan gona
karami, wanda Sadik ya kasa tantacewa ko gidan
gonanc ko kuma hakannan aka gidana shi. Ya yi parking
din motar a kofar wannan guri. Nan ya fito ya ce da
Sadik ya fito. Sadik ya cc. "Ba rakiya kace in yi maka
ba, na kuma yo maka ba shike nan ba, ko ko dole ne sai
na shiga gidan.?
"Shiga gidan kam ya zame maka dole, kamar yanda
mutuwa ta zama tilas akan kowa, kwankwacin haka kai
ma shiga gidan nan ya zame ma ka dole. tunda har ka
yarda ka biyo ni kayi mai wuyar." Yana gama fadin
haka ya ciro wani usur daga aljihunsa ya sa a baki ya
busa da karfi. Yin haka ke da wuya, sai ga wasu karti
samari majiya karfin gaske, ko wannen dantsensa a
murde şaboda tsabar karfi. Su kimanin su goma suka
dinga fitowa daga cikin wannan gida, suka zagaye motar
14
da Sadik ya ke cíki. Ko wannen su hannunsa rike da 'yar
Karamar bindiga.
Ibrahim ya yi dariyar mugunta, sannan ya ce
"Yanzu idan kana da sha'awar ci gaba da rayuwa а
doron kasa ka iya fitowa, in kuma baka da muradi а
aikaka yanzun nan."
Sadik cikin tsananin mamakin da bai taba yin irin
saba a rayuwarsa, ya fito bakinsa a bude hannaycnsa
bisa masa. ya dubi Ibrahim ya cc, "Ibrahim tsakanina da
kai daman da irin wannan......" Bai ma kai karshen
abinda ya ke son ya fada ba, sai yaji an dake shi da wani
abu a ka. Tuni idanunsa yaga wasu taurari, daga bisani
kuma duhu ya bayyyana a garcsu, take ya kife a gurin.
Su ka ja shi a kasa suka shigar da shi cikin wannan
gidan, sannan su ka kulle. Kartin su ka tsaya gadin
gidan. shi kuma Ibrahim ya taho gida.
Tunda na idar da sallar azahar ina zaune ina jan
carbi, kamar yadda na saba, har la'asar tayi, na yi sallar
ya yin da garin ya dinke da hadari, iska ta taso, nayi
sauri na nufi dakin Sadik domin inga ko ya dawo na kai
masa abincinsa na rana. Na tarar kofar a kulle, nayı
turus da ni ina mamakin abinda ya hana shi dawowa, na
duba harabar gidan ga motarsa nan a ajiye, na koma
daki, a raina na ce, "Ai duk inda ya ke tunda ya ga
hadarin nan ya dawo gida in yaga ruwa." Nayi kwanciyata da tunanin inda ya tafi bai kuma sanar da ni ba.
Magariba ta yi, nayi sallah, sannan na ci abinci
domin har wannan lokacin bai dawo ba. Isha tayi; nan
ma nayi sallah, kai har kusan sha daya na ji shuru ban
15
gan shi ba, sai Ibrahim ne ke shige da ficen sa shi kadai.
Sai kuma ni da Nusaiba.
Nan na kwanta kwanciyar barci ina tunani. Ban
san lokacin da barci ya dauke ni ba. ban farka ba sai
kusan asuba n atashi, na yanke barci na na nufi kofar
Sadik ko ya awo, cikin daren ma amma gam take tana
kulle, sai nayi ta tunanin ko kullewa ya yi ta ciki. Na
koma na kwanta, ina ta tunanin. har gari ya waye na ga
Abubakar Sadik ya shigo, amma shiru ka ke ji wai
malam ya ci shirwa, na sake komawa dakinsa, nan ma a
kulle ya ke, kawai sai naji hawaye yana zubo min kamar
ruwa. na koma daki na yi wo alwala na yi sallah, na fara
addu'ar neman Allah ya kare sadik, ya kasance ba a
wani mummunan hali yake ciki ba.
Kusan takwasa na safe, na shiga dakin Mami
domin in gaisheta kamar yadda na saba. Bayan na
gaisheta ne na ke ccwa "Mami ko Sadik ya yi tafiya
ne.?"
"Mai kika gani.?" ta ce da ni.
"Gani nayi tun jiya da safe rabonsa da gida...."
"Au bai dawo ba.?" ta tambaya a hanzarce, fuskar ta
tabayar da alamar mamaki.
"Bai dawo ba." na ce ma ta idon cike da hawaye.
"Shi kuwa ina yaje.?" ta kuma tambaya ta.
"Oho. wallahi ban sa ni ba, kuma naga motar sa
tana nan."
Eh. to, ai shine abin mamakin da da motar ya
fitane ma ace ko kauye ya tafi ko kuina Alhaji ya aike
shi kafin ya yi tafiyar nan, to gashí shi baya garin."
"Ko za'aje gidajen 'yan uwa ko za'ayi dace a same
16
shi.?" nace da ita cikin tashın hankali
Ja kuwa hantaro ni da cewa,"To har yaushe ya yı
6atan da za'a shiga nema.? Ni bana son shishshigin
tsiya, ko ya ya kuke da