Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
shi, ai ba kamar mu ba, da za ki damu mutanc da a nemo shi. to anki a nemo shi din,sai ki dau zani ki tafi nemansa." bansan lokacin da hawayc ya zubo min ba, na yi wajc ba shiri, zuciyata cike da kunci, na rasa abinda ya ke yimin dadi, na rasa abin yi, kawai sai na shiga dakina na sa kuka, Wasa-wasa, 6atan Sadik ya yi sati biyu, ba shi babu dalilınsa, in kin ganni sai ki tausaya min. duk na rame ra lalace, kullum ina cikin halin tunanin ko wanne hali Sadik ya ke ciki oho. Na rasa wanda zai taimake ni akan wannan lamari, ga Alhaji baya nan. Ko kaďan abinda ya faru bai damu Mami da Ibrahim ba, ko ajikinsu ma, sai da su ka ga na tada hankalina, nane ma su ka ce za su yiwa Alhaji waya su sanar da shi abinda ya ke faruwa. Shiru kusan kwana uku ba su yiwa Alhaji waya ba, na sami Mami na ce "Ko kun yiwa Alhaji wayar.? Tace da ni "An yi masa, yace ba zai samu damar zuwa yanzu ba." Ina ji nasan wannan karya ne, domin da Alhaji ya san wannnan zancen da tuni ya bayyyana a garin nan, komai yake yi." Na ce "Ko inje in sanarwa da Dakaci.?" "Wai ke meyc naki ne a cikin wannan lamarine.? Daga yau in kika kara yimin zancen Sadik sai ranki ya yi mummunan baci wallahi." Mami tace cikin fada. Abin ba karamin mamaki ya bani ba, sai na yi tunanin kawai tana yin kishin Sadik ne saboda danta Ibrahim, da 17 na kiya in aure shi. Don haka sai na tattara komai na barwa Allah, na shiga yawaita addu'a a kan Allah ya bayyana min shi. Ina zaunc gaban Alhaji, carbi a hannuna. Kallo daya za ki yimin ki tausaya wa rayuwata, domin na kode na jeme, na zama tamkar mai yin takaba, idanuna kuwa ja, saboda tsantsar kuka. Alhaji ya rtinga kwararo min tambayoyi kamar haka.:- "Lokacin da ya tafi ba kowa a gurin." "Ni dai bana gurin, ina da niyar zuwa dai, domin in je in same shi a gurin, sai da na tsaya shiryawa, da na isa gurin bayan na gama shiryawa, sai na ga banga kowa ba, sai nayi zaton ko yajc wani wajen ne yanzu zai dawo, sai na zauna har na gaji sa zama bai zoba, do haka na yi komawata daki na yi zamana da niyar in yazo ya yimin magana. To shine dawowar da bai yi ba kenan har yau." Alhaji ya ce. "Nayi iyakacin bincike na an rasa gano inda ya shiga, wannan abu ba karamin abin mamaki bane, domin shi Sadik yarone da ba ruwansa da harkar mutane ma barc wani abu ya haďa shi tashin hankali, barc ya yi fada da wani, gashi yaro mai girmama na gaba, bare a ce ko ya yiwa wani rashin kunya ne. Ni na rasa ta yadda wannan lamari ya faru, kuma ba fada ku ka yi ba ya yi fushi.? na cc "Wallahi ni bamu taba yin fada da shi ba." "Shi kenan na yarda, yanzu zanje can kauyen na sanar da Dakaci abinda ya faru, kuma dama tuni nasa ayi ta rokon Allah akan wannan lamari mai ban mamaki. 18 Abu fa ya zame min kamar cuta, kullum kuka, har su Mami sun fara jin haushina, sai wulakanci take yi min iri-iri gashi Alhaji ya hanani komawa gida. In nace zan koma garinmu sai ya ce In Kara hakuri dai, ana nan ana bincike akan lamarin, kai karshema cewa ya yi ba maganar komawa, domin shi a yanda ya dauke nitamkar 'yarsa ta cikinsa, domin duk abinda zai wa Nusaiba sai ya yimin, a cewarsa ai ni marainiyace. Ranan ina zaune a harabar gida nayi tagumi ina kallon inda nake yawan zama da Abubakar muna zance da irin dadadan kalaman da yake fada min, sai naji hawaye na gangaromin na fara kuka ina kiran Sadik, sai na ji kamar daga sama an ce min "Wahalalliya sai kiyi tayi, haka ki nacewa abinda ba samu za ki yi ba." tuni tun kafin ma Hajiya ns fahimci mai muryar, dan haka nayi saurin juyawana dubeshi raina a bаce паce masa "Tsaya kaji Ibrahim duk abinda za ka ce dani sai dai kace, Kunar Sadik kuwa yanzu ma na soma, kuma misali a ce Sadik mutuwa ya yi to ba ni ba aurc, duk fadin duniyar nan banga wanda ya yi min ba sai shi." ina rufc baki naji wasu kyawawan mari guda biyu tas!tas!tas! har su uku. Na dafe kunci na na fara kuka. ya ce, "Ko kin ki ko kin so Auren ki kamar na na gama ne domin babu fashi." yana gama fadar haka ya yi tafiyarsa ya barni a gurin ina ta kuka na, sai da na gaji sannan na tashi na koma ciki, na same shi a falo, muna hada ido wani irin harara ya doka min, sai da gabana ya fadi, na karasa ciki zuciyata cike da takaici. Ina kwance a daki, can kusan asuba barci daukeni domin kullum bana barci sai na gama sallolina 19 da addu'o't ina neman Allah ya bayyanar da Abubakar Sadik, ya komo gida a duk inda ya ke. Ban dade da fara barcina ba sai nayi mafarki ina cikin dokar daji ni kadai, ina gudu ina kiran sunan Sadik, sai na gamu da wani gida a kulle, na tsaya a Rofar gidan nayi kiransa, sai naji ya amsamin a sanyayae alamar yana cikinmawuyacin hali, sai nayi kokarin bude kofar, na ko yi sa'a Rofar ta bude, na shiga na sami Sadik a daddaure, duk ya rame ya vi baki, kamar ba shi da lafiya. Ina gann haka sai na fada jikin shi na saka kuka. Ya bude ido a hankali ya dubeni, ya girgiza kai cikin mutukar tausayawa ya ce da kyar. "In kwance shi." na shiga kwance shi ina ta faman sauri, nayi sa'a na kwance masa igiyar ya warware sauran. Na kama hannunsa muka fito muka fara gudu, sai ga wasu samari majiya karfi suka biyo mu a baya da bindigogi a hannunsu suna harbinmu, mu kuma muna gocewa. Can sai wani daga cikin su ya tsaya ya saita Sadik a baya ya sakar masa, ya yi sa'a kuwa ya same shi a baya. Sadik ya yi kara gamıda kiran sunana ya fadi. Ina ganin haka nima na kwala wata kara mai tsanani na akansa "A dai-dai wannan lokaci na farka, bansan cewa karar da nayi ta fito sarari ba, sai gani nayi su Mami da Alhaji da Ibrahim sun shigo da gudu suna tambaya ta "Lafiya.?" Cikin tsananin razana da kuka па сс, "Alhaji Sadik!Sadik!!Sadik!!! Alhaji......." "Ina yake.?" cikin kidima Alhaji ya ke tambaya. Nace. "Ya mutu, wayyyo na shiga uku, Sadik ya mutu." "Wa ya fada.?" Alhaji ya tambaya cikin tashin hankali. 20 "Mafarki na yi.?" na bashi amsa. "Au. ai mafarki ba gaskiya bane, addu'a ya kamata kiyı, alherin da yake cikin mafarkin Allah ya tabbatar da shi. Sharrin da yake cikin sa kuwa Allah ya kauda shi." Alhaji ne ya yi wadannan ınaganganu domin ya kwantar nin da hankali. Nan nayi ta jero addu'o'i, shima Alhajin yana taya ni. Su Mami kuwa ficewa su ka yi da suka ji abinda ya faru. Ibrahim tun da ya shigo ya ji nace mafarki nake sai naji ya yi tsaki ya fice abinsa. Shi ko Alhaji sai da ya ga na nutsu sannan ya tafi dakinsa, bayan ya yimin fada akan in yi hakuri In ina yawan sa abun a raina dan kar wani ciwon kuma ya same ni." Na dai amsa nasa da to ne, amma ba zan iya ba, domin kaunar Sadik ta zamar min tamkar mahadin rayuwata. Alhaji da kansa ya je ya sanar da Dakaci abinda ya faru. Dakaci ya yi mamakin wannan abu matuka, kuma ya yi bakin ciki so sai, sai ya dinga addu'ar Allah ya bayyanar masa da fansa kwaya daya tilo. Da zance ya bazu a kauye, kowa ya ringa mamakin wannan abu, wasu suka yi bakin ciki, ya yin da wasu suka dinga addu'ar Allah ya kara, domin iyayine irin na Dagaci ya fauki dan ya kai can birni wai ya yi karatu, to ai ga irin tanan, ya bar dansa a gabansa yaki ya kama ya kaishi wani gari. haka akayi ta 'yan tsegungumi a garin. *** Ibrahim na zaune shi da Mami a dakin Mamin suna tattaunawa, ya yin da Mami ke cewa "Abinda naga 21 ya kamata ayi Ibrahim kawai shine A hada Alhaji da Malamai, kawai ya amince a hada auren naku." "Au dà kika je mai ya ce miki.?" Ibrahim ya tambaye ta. "Cewa ya yi wai ai wannan ma ba mai yuwu wa bace, suna sa ran dawowar Sadik, ya ya ma za'ai wai ace kai ka aurcta, sai dai in Sadik din mutuwa ya yi, kuma ko hakannne sai in tana sonka ne za'ayi, in bata sonka shikenan sai ta fidda wanda take so a aura ma ta." "Wallabi íami sai insa a kashc Sadik muga ta tsiya...." Cikin tsawa Mami ta katse shi. "Kar ma ka soma, baka da hankali ne.? Wallahi sai in daina gaya ma ka baya, ya ya za'ai kasa a kasheshi, kai kayi ma sa ran nasa." "To Mami ai gani nayi ina neman rasata." "Ga shawarar da na kawo maka, muje mu hada su da Malamai, sai kaga komai ya yiwu cikin sauki." Mami tace masa. "Shi kenan Mami na bar miki wuka da nama. Yau kusan wata uku kenan da 6atan Sadik. Ina zaune ina tunanin anya kuwa za'a ga Sadik dina kuwa, ni fa wannan zaman ya fara damuna, ya ma za'ayi ace wai ba zan koma gida ba, bayan kuma na riga na gama karatuna na sakandire. Ga Nusaiba ta tafi makarantar gaba da sikandire. ni ina nan ina nan ina farma da tunanin da ba shi da amfan: !na nan zaune ina tunani, sai ga Mami ta shigo ta same ni. "In kin gama abinda kike yi kizo ina son ganin ki." "To.na ce da ita, sannan mike na fita na sameta a dakinta tana faman daddanna waya, ko wa take so kira 22 oho. "Gani." na ce da ita bayan na durkusa. "Zauna mana so sai, magana nake son yi da ke." Ta juyo da fara'arta ta ce dani. Na zauna, nan ta dubeni tace, "Hamdiyya, wata shawara nake son na ba ki." "To. na ce da ita." Taci gaba da cewa "Mai zai hana ki auri yaron nan Ibrahim tunda Sadik bai dawo ba, ko ince ba'a ganshi ba........ ta dan dakata ta hadiyi yawu, sannan taci gaba da cewa "Wallahi yaron nan yana kaunarki so sai." "To Mami zanyi tunani akai." na ce da ita. "A'a. ba wani batun tunani,ni yanzu nake son jin amsar. "Eh." ko "A'a." "Mami ina son Sadik, kuma ina mutukar Kaunarsa fiyc da yadda kike zato,ina sa ran dawowarsa, kin ga kuwa batun ince na yarda da auren Ibrahim abune mawuyaci......" Ta katseta "Au irin sakayyar da za ki yi mana kenan.? Mun daukoki daga kauye mun kawe ki birmi, mu gyaraki, mun ba ki ilimi, muu maida ke mutum, mun nuna miki soyayya kamar da da iyayensa,amma za ki nuna mana kiyayyar ko ince kin riga kin nuna mana ma, to wallahi ba ki isa ba, aurene kamar anyi shi an gama, wa za ki wulakanta.?" "Maini da Sadik da Ibrahim duk daya ne a wajen ki, to meyc abin bacin rai.....?" Ta katseta. "Kin ga ma za ki fice min daga daki na duk denyan ubanki.? Za ki yi mamakin wallahi, za ki gwammace kida da karatu." Na tashi na fice, zuciyata cike d bacin rai, bansan lokacin da na fashe da kuka ba, har na hada kayana zan bar 23 gidan, sai na tuna da Alhaji,naga in na tafi zai ce banyi masa mutunci ba, sai na hakura na ajiyc kayan ina ta kuka bar wani lokaci. A bankali aka turo kofa, ya yin da na daga kai sai muka yi ido biyu da Ibrahim, gabana ya yanke ya fadi, na mike tsaye da sauri dami da dora hannu na a kan kirji па па сс, "Ibrahim mai ya kawoka dakina a cikin wannan darc.?"!!! "Shecet! abinda yace kenan ya yinda ya dora danya tsansa akan lebensa ya Karso inda na ke, ya tsaya daga shi sai gajcran wando; ya sa hannu ya janyo ni jikinsa da karfi, sannan ya ce, "In kikai min kuka saina wulakantaki a dakinnan." Na sa hannuna na rufe bakina, idoa cikc da hawaye, zuciyata tana barazanar tsaga kirjina ta fito." "sai ki zabi dayan biyu. Ko ki yarda ki aurc ni, ko kuma na 6ata miki rayuwa yanzu-yanzun nan." "Na yar..da za.n a..ure ka." Na fada masa cikin shashshekar kuka, muryata na sarkewa. Ya yimurmushi. "In gari ya waye, zan kira Alhaji ki bayyana masa a gabansa, in kuma kika sabamin sai kinyi nadama, domin zan nuna miki nima kwararre ne, kar kuma kiyi tunanin guduwa, domin in kinje gidan naku ma, iyayenki ba yarda za su yi da maganar ki ba, domin na riga na toshe bakinsu da kudi, in kuma kina shakka ki jarraba ki gani." yana fadin haka ya sa keni ya juya. Na yi ajiyar zuciya gami da komawa na zauna ina ta tunanin abinda ya faru. gaskiya gara in bar musu gidan su tun kafin in gama wulakanta a hannun Ibrahim, afuskanci duk abinda ya yi ba'ayi masa fada, 24 kuma ma ko dukansa za'ayi ya riga ya gama wulakantani, in na sa ke Mami ma ccwa zata yi sharri zan yiwa danta, gidan kawai zan bari shine mafita a gareni, domin na tsaira da mutunci na, ko da yake ya ce innaje gidan ma ba goyon baya zasu bani ba, domin abinda yace, gaskiya suma suna goyon bayan in auri Ibrahim, daman ba son Abubakar suke yi ba. Nan na fara tunanin lokcin da muka je gaishe da Inna, Ibrahim dinne ya kai ni, bayan ba tun Abubakar. Inna tacc "In har ban bar maganar Abubakar Sadik ba zata tsine min in lalacc." To ita kenan ma ta fadi haka, balle kuma Kubra Baba Ta sallah da ko sunan Abubakar bata son na ambata, in na ambata sai tayi kamar ta shake n, yanzu ma abinda ya sa basu ce shi Ibrahim din ya fito ba shine, Dan dai Alhaji bai bayar da goyon baya bane shi yasa har yanzu ba'a sa ranar bikin mu da Ibrahim ba. Da gari ya wayc, tun da safe, sai ga Ibrahim ya shigo ya same ni a zaune ina jan carbi a hannuna ina ta faman hawaye, ya a fusace, "Ki zo inji Alhaji, kuma wallahi ki tabbatar kin fada masa abinda kika ce da ni jiya, in ba haka ba sai kinyi mamaki." Na mike ban ce da shi komai ba na mike zan fice, sai ya sa hannu ya kamoni ya dawo da ni, "Haka za ki tafi kin kukan kalen, Alhaji yace tilasta miki nayi na yi.? To koma sai kin share hawayen za ki fita." Na sa mayafina na share sarai, sannan na fice ya biyoni a baya. Muka tarar da Alhaji da Mami zaune a falon Alhaji, na durkusa na gaishe shi." "Naji wata magana daga bakin Ibrahim, kuma nayi mamakin jinta, shine nace a yi kiranki domin inji haka ne.? In hakan ne shikenan, in kuma ba hakan bane to. 25 daman magana a bakin mai ita tafi da di. Wai da gaskc za ki auri Ibrahim din kin hakura da Sadik.?" Alhaji ya yi wadannan maganganu bayan ya amsa min gaisuwata. Na sunkuyar da kai, hawayc na gangaro min daga idanuna. Dukakan su idanuwansu na kaina, suna sauraron abinda zance, sai nace Eh. kawai, domin in nace A'a shima kansa Alhaji a nawa ganin zai ji haushin irin kiyayar da na kc yiwa dansa bayan irin abin alherin da ya ke yi min, kuma sannan babu makawa Ibrahim zai keta min mutunci na." Alhaji yana jin abinda na ce sai ya yi murmushi ya ce, "Shi kenan daman nayi masu gida a jere ma'ana kusa da kusa shida Sadik, yanzu saura shirin biki kenan ya rage min. "Kai Ibrahim sai kaje ka fara shirye-shiryen ka ba wani bata lokci za'a dauka ba." Cikin tsananin murna Ibrahim ya mikc ya fita yana farin ciki, nima na tashi na bar su da Mami na shiga dakina na fada gado ina ta faman kuka kamar raina zai fita, nace bana sonka Ibrahim bana kaunar ka. Wallahi-wallahi ba zan zauna ba ko anyi auren mu. Tuni Alhaji ya je ya sami su Inna an tattauna maganar aurc, kowa ya yi farin ciki da wannan lamari. Baba Ta sallah ta ce. "Alhaji kaine wuka kaine nama, saboda haka mun bar maka duk komai a hannunka." Alhaji yace "Ai babu komai, shi da duka na kowa ne." Haka ya yi sallama da su ya tafi zuciyarsa cike da farin cikin ganinsu yake kamar 'yan uwansa na jini. Suma su Inna sun dauke shi tamkar dan uwansu. 26 Wata guda kacal aka sa bikin mu, bakin ciki a gurina ba'a magana, na rasa yadda zanyi da rayuwata, na je na sami Ibrahim a dakinsa alokacin Mami ta fita unguwa, na sa masa kuka akan ya janye maganar auren mu." Nan yace "Wallahi in har kinga an fasa auren nan sai dai in mutuwa na yi ko kika mutu, amma ba bu fa shi." Na rasa yadda zan bullowa masa, sai nace "Dan Allah Ibarahim ka ceci rayuwata, ka taimake ni kayo hakuri ka janyc." Ya cc "Wallahi ba zan janye ba, kamar fa mayunwacine yaga lafiyayyen abinci sai yawunsa ya gudana yana shirin a janyc kwanon ace ya hakura ya bawa wani, kinsan abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa." yana gama fadin haka ya janyo hannuna gami da lallatsawa, nayis aurin fusge hannuna na tashi zan fice daga dakin, ya yi saurin tare kofa. "Au ina za ki.? Ba hira kika zo muyi ba." Nace "Ni ba hira na zo muyi ba, rokonka ne zanyi akan ka hakura ka gyale ni in ba haka ba........." na yi shiru. ya ce "To ke nake saurare in ba haka ba meye.?" A "Ba komai." Na ce masa. "Wallahi sai kin fada." ya ce da ni. "Na ce maka ba komai, to mai kake son in fada.?" ya ce "Bari ki gani, yanzu za ki fađa, ya yi wuf ya saka mukulli ya kulle dakin, ya zarc ya sa ka a aljihun wandonsa na jeans, ya koma ya zauna ya ce "In Mam ko Alhaji in wani ya zo zance kince ba za ki fita badaga dakin nan kinzo kenan tunda aka sa bikin mu ya yi nisa har tsahon wata guda." Na cc, "Shi akansa Alhajin ya san ba zan ce haka ba." "Kar ki cika baki, ahannuna kikc.' 27 "Ko ma amc na ke baka isa kayi min abinda Allah bai yimin ba." na ce da shi. "Au ni kike gaya wa wannan maganar, zan yi maganin ki yanzun nan." "Ni dai kawai ka tashi ka bude min kofa in fita." na ce masa. "To ko yanzu aikin kin taya ni hira....." na katse shi. "Ni dai na ce ka bude min ko." ya je ya bude min yana dariya gami da cęwa "То sai na zo hira ko.?" Na ce "kaji da shi, anayi tafiyata daki ina ta tunanin wadda zata fishsheni. Dare ya raba, ya yinda na farka daga nannauyan barcin da nake, tunanin mafarkin da na yi, amsa kuwwar kalaman mai maganar yana ta dawo min cikin kunnena kamar ido biyu na ji su. "Ma za kiyi ki taimakawa Sadik din ki kafin ya hallaka, yana can a dajinan dake tsakanin Tagina da Birnin Gwari, in kinje ki sa fuskarki yamma, ki shiga dajin zan dinga nusar da ke hanya, in kin tashi daga barcin kiyi azama ki fita daga gidan karki gaya wa kowa, ki taimaki Sadik, domin yana cikin mawuyacin hali." Wuf! na mike ina kiran Iannalilahi wa'innalillahi raju'un. mai yake shirin faruwa kuma.? Wane irin mafrkine wannan kuma.? Wane hąli Sadik ya ke ciki.? Duk wadannan tambayoyi ne da bani da amsar su. Nan ta ke na yiwo alwala na yi sallah raka'a biyu, na yi addu'ar Allah ya sa mafarki nan ya zamemin alheri, domin abin nan ya tsoratani, bayan na idarne na koma na kwanta, amma fa barcin bai yuwu ba, a haka har gari ya waye idona biyu ina tunanin wannan mafarki. Kashe gari, tun da sanyin safe na tashi bayan na yi 28 sallah na zauna ina tunanin mafarkin da nayi, tunanin wannan mafarki da nayi. na yi tunanin ko in watsar da shi domin abin ya fayc tsoratanni, wata zuciyar ta kara ta ce, "Anya cewa fa aka yi ki tashi da safe, gwara ki tafi din,. in ma ajalin ki ne haka Allah ya so, da wannann auren ma ba gwara kiyi tafiyar ki ba!." na daga kaina na dubi agogo biyar da rabi. na ce "To yanzu zan tafi wannan tafiya tawa, Allah ya sa alkairi a cikinta." na tashi na nemi hijabi na na sa ka, na dan hada kayana a karamar jaka, na sami wata 'yar roba na dura ruwa, sannan na dauki jakar, sai da na faki ido sannan na fice abina, ba wanda ya gannni, na kama hanyar tasha, na ko sami motar da zata yi lodin legas zata bi ta tagina da birniņ Gwari, na shiga, bayan na biya kudin motar sannan na shiga na zauna, da aka gama lodi, mota ta dau hanya, muka dinga tafiya ba ji ba gani, masu hira nayi, masu shiru nayi, masun gyangyadi na yi, masu barci na yi, ni ko idona kuru ina tunanin abinda yake wakana, hakika mafarkina da akwai kamshin gaskiya a cikinsa, domin zuciyata na dada karfafamin gwiwa cewa zan samu abinda na ke nema. to ma ji dai ma gani, wai an binne tsohuwa da ranta. A farkon dajin na ce zan sauka, mutanen cikin motar suka hauni da banbamin fada. "Ke kuwa wannann yarinya me a sameki haka.? kina da hankali kuwa, za ki ce a wannan dajin za ki sauka, dajin da yake da miyagun kwari da namun daji da kuma gagaruman 'yan fashi.?" wasu suka ce "Ko dai makuwa ki ka yi ba ki san inda za ki sauka bane.? Ga garuruwa mun wuce, amma kice wai a nan za ki sauka.?" Na kalle su na yi murmushin karfin 29 hali na ce, "To wai ku meye na ku a cikin wannan lamari ne.? nan din na yi niyar sauka." Na dubi karen motar. "Malam ka yiwa direban magana ya tsaya ka bude min tunda na shigoi, ai na gaya maka inda zan sauka, kuma ka amsa min ka dauko ni, to yanzu idan ka wuce da ni ina za ka kaini." ya daki kofa gami da cewa. "Akwai mai sauka." Dareba ya ja ya tsaya, wani tsoho da da muke tare da shi a kujera daya da bai magana ba tun sa'inda mutane ke ta faman batun, ya ce da kwandastan "Da Allah yaro yi ma za ka bude ma ta ta fita, nan ba gurin tsaya wa bane." Kwandastan ya bude min na dauko jakata na fito na ce, "Na barku lafiya." ya yin da wasu suka amsa,wasu kuwa cewa su ka yi "Ni kunga yarinya kamar nutsatsiya, amma kila yarinyar 'yan fashi ce tacje gari ta yi musu siyayya ta dawo." Na yi dariya kawai, na suri jakata ya yinda su kuwa suka ja motarsu su ka yi gaba. Na tsaya na kalli kudu da arewa, gabasa da yamma, babu kowa a dajin nan sai ni daya kwal! nace a raina "To yamma aka ce in yi, yanzu gashi na kasa gane yammar tunda kaina ya juye, na dubi agogon hannuna sha biyu saura minti goma, na ce "Kai amma mai motar nan yana zuga gudu, har mun zo.? na tsaya saitin rana nace zan gane yamma, ta hanyar ganin inda ranata dosa, take kuwa na fahimci yamma, na sa kai kawai cikin daji zuciyata a dake. Tafiya kawai nake yi ba tare da na san inda za ni ba, tun sa'adda na sauka har yamma ligis ina tafiya ban gamu da komai ba, sai dai gajiya, domin rashin sabo da tafiyar, na dinga wuce kwazazzabai da bishiyoyi. Na 30 ciro wani fanke da na zauna a gindin wata bishiya na siya a kan wata yarinya tun a tasha, na fara ci, domi yunwa ta soma addabata, na dauki ruwan da na duro a butar roba wata 'yar jarkar nono babba, na sha ruwan, sannan naji dama-dama, na dauki kayana na kara gaba, ko kadan babu alamar wata hanya da mutane suke bi, ni dai kawai duk inda na ga sarari sai inbi, in kuma naga guri ya yi sarkakiya da yawa sai na kewaya, haka nayi ta tafioya har magariba ta gabato, na sami wata bishiya wadda bata da girma so sai, na haye na bar kayana a kasa, nayi zamana. Da haka darc ya yi, dajin ya yi tsit babu wani motsi komai, sai wani irin matsanaicin duhu, wanda ko tafin hannunka baka gani. Haka nayi zamana dan gwargwar akan bishiya nan, idona kuri har gari ya waye, na duro na fara neman inda ruwa yake inyi alwala. na nema babu, sannan na tuna da taimama, nayi, na gabatar da sallah, na ci gaba da tafiya, hantsi na dagawa na fara jin wata irin yuwa, na rasa yadda zanyi, sai ruwan nan da ya dan rage min nake kurba, da kadankaďan, a haka har naje wani wajc inda na sami gwandar daji, da yake na saba da su tun a kauyen mu, na fara sha, ga shi na yi sa'arta manya-manya da yake ba mai zuwa ya diba dajine, sai da naji na koshi, sannan na dauki hanya, kuma sai na dinga jin barci da kasala tana dauka ta, domin na koshi, in banda kwanciya ba abinda nake so, don haka sai na fara hangen inda zan dan kwanta in huta, gashi dama jiya ko rintsawa ban yi ba. na ko yi sa'ar samun wani guri a gindin wata bishiyar dorav'a mai yawan ganye babu ciyawa da yawa, na nufi gurin na dan tatare gurin da zan kwanta, da yake ba damuna 31 bace, du ciyawar ta bushe, na ciro zani a jakata na shimfida na kwanta, tun ina lumshe ido inyi sauri na budes har barci mai nauyi ya dauke ni, bani na tashi ba sai da azuhur,nayi saurin mikewa nayi taimama nayi sallah, sannan naci gaba da tafiya abuna. Ina cikin tafiya, sai nabi ta wata hanya da baza ta fiddani sarari ba,

Chapter 2 of 5