Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
ba tare da na sa ni ba, sai da na kai cikin wasu sarke-sarken bishiyoyi sa reshina, sannan na yanke shawarar na juya na dawo baya, domin kuwa babu hanya. Allaha ya taimake ni na gani tunda wuri, juyawar da zanyi ni ban sa ni ba ashe akwai wata dankareriyar katuwar mesa saman gurin da nake, kawai sai naji wata irin kara shuu! sai ra fado min a jiki ta nannade ni, gata katuwar gaske, tayi wata irin haniniya kamar kukan katon bijimin sa, ban san sa'adda na kwalla kara ba, gami da kiran "Wayyo Allah! na shiga uku." tsananin nauyinta tane ya kaini kasa, daman ita haka take so kenan, ta sami damar da zata karyamin kasusuwa ta hadiye ni. Nayi lamo dani ina karanta kalmar shahada, domin na debe tsammani ga rayuwa ta. Ta bude bakinta ta dai-daici kaina zata saka kaina a bakinta ta hadiye, ni kuma na rufe idona ina ta faman salati, domin nasan tawa ta kare, daman karar kwanace ta kawo ni dajin nan...." tunanin ya katse sakamakon wani abu da naji ya fashe fus! naji kuma wani danshi mai dumi ya jikani, naji duk dabaibayeni da mesar tayi duk jikinta ya sa ki, ta warwareni, nayi firgigit na bude idona da saurinka, nayi yunkurin tashi, sai naji nauyi, duk abin nan ban lura da kan mesar ba, sai jini da na gani a jikina. ya bani mamaki ya yin da na mike nayi 32 0 A arba da kan mesar can waje daya ya dagargaje saboda tsabar wahala har ya fita daga uwar jikin, na kwallah wata uwar razananniyar kara na fita da gudu, ba koma ta kan kayana ba, wato jakar da ruwan nan na barsu, bukatata dai in bar gurin, domin abuda ya kashe mesar nan hakika ganinsa ba zai yi min kyau ba, duk da cewa bana debe tsammamin gudun da nake yi zai sa na tsira daga wannnan abu, to amma gara ya kasheni bisa kokarina na tsira da rayuwata. Bani na daina wannan uban gudu ba sai da na kai kimanin minti goma sha biyar saboda tsananin razana, wannan ya nuna min kenan ba karamin nisa nayi da gurin ba. Sai da na sami sarari sannan na zauna na huta ina ta faman haki kamar raina zai fita, bakina ya bushe, makogwarona na ta suya, ga wahala da jikaga, ga kuma kayan jikina duk sunyi faca-faca da jinin wannan mesar, abin dai ba kyan gani. na dade a zaune kafin in tashi, lokacin sha biyu ta kusa, na tashi na yi mika gami da hamma, na dudduba ko ina, ba alamar ruwa a kusa, dan haka na dada nausawa can yamma ina tafiya, kafata ba ko takalmi, daman na zubar na zubar, in ma ba wauta irin tawa ba, mai ya kaini saka takalmi mai tsini da zan shiga daji har da wani kashe dauri, to dankwalin atamfar tawa ma acan na baro shi, daga ni sai riga da zani, kaina babu dankwali, gashi babu kitso, tunda ban dade da zuwa saloon ba wannan tafiyar ta sameni. Har yanzu dai zuciyata bata karaya ba, tafiya kawai na ke, ban san inda za ni ba, can sai na hangi wani guri, bisa alama akwai danshi a gurin, domin na hangi tsuntsaye na ta shawagi a sama, kuma gurin yana 33 yanayin da hazo-hazo alamace ta akwai kogi a nan ko wani ruwa na kwarara. Nan na himmantu akan tafiya ta, domin na matsu na Karasa gurin na ga ruwa na sh, domin har ishirwa tagama galabaitar da ni, ba ni na isa gurin ba sai misalin karfe biyu da rabi, tuni kafata ta fara sabawa da tafiya, nayi sa'a ba komai a gurin, wani katon ruwa ne a gurin, yana kwance damkam! ga tsuntsaye na ta faman kai da komowa a gurin. na karasa dab da gabar ruwa duk chakwa-kwali da sawayen namun daji, hakanne ya sa ni tunanin ko akwai namun daji a gurin ta, amma na yi mamakin rashin ganin dabbobi ko daya a gurin, nan dai na nemi gurin takawa mai dan tsananin domin kar na kabe tabo, na hangi wani dan tudu mai wasu irin kusassari kamar kaya-kaya dago na dan taka gudun kar na cace na sunkuya na fara debo ruwan ina sha da tafin hannuna, na ji in da na taka din ya danyi motsi, nayi zaton kasar gurin ce ta sha ruwa, na yi nufin na sauka kar ta rozaye dani, babu zato babu tsammani sai naji wanı irin gurnani da ban fahimci meye ba, kuma ban gane daga ina ake yinsa ba, na mike tsaye ina hangawa, domin kar na koma muyi kicibus da abin da ya ke gurnanin, daga can sai na jiyo gurnanin yana kara kusantar inda na ke. Yo dubawar da zanyi sai na hango wasu garken zakuna manya-manyan gaske sun nufo inda nake, suna ta faman sunsune-sunsune, ga alama kamshina ma su ka jiyo, bayan sun taho shan ruwa. Nan fa na rude, nayi tunanin ina ma mesar nan ce ta kashe ni tun a gurin da ya fiye min sauki, domin babu ko shakka zakunannan watanda za su yi da namana, ba zan ma wadace su ba, domin ina zaton gaba ki daya 34 T1 aa 2 akaап1 aIVA a a1נו family din su suka hadu suka taho shan ruwa...." Ban gama tunanin da na ke yi ba, sai na ga gurin da na ke tsayc ya yi wani irin juyi ya fada ruwa.Shu!!! yana yanka ruwa kamar jirgin ruwa. sai da na dade ina saita kaina sannan na gane ashc akan wani narkeke kadane mai mutukar girman gaske, idansa jawur ko wanne daya ya yi dunkulen hannuna, wannan fa shine gaba kura baya ga damisa, ni dai na zuba ido ina ga inda zai kaini, domin nasan dai in har kadan ya kama mutum to cikin ruwa yake danna shi, su hadu da 'yan uwanshi asha walima, to wannan kadan sai na ga ya nufi bakin gaba dani, hakanne ya sa ni tunanin ko baya so 'yan uwansa su taya shi ci, sai ya yi gaba abinsa. Sai da yaje bakin gaba sannan ya watsa ni waje, ya koma ya dulmiye a ruwa, daga nan ban sakc jin ko duriyar sa ba. Su kuwa garken zakunan nan ban san yaddka suka kare ba da su ka rasa ni ba. Na jima ina jin jiki saboda jifan da kadan nan ya yi da ni. Na mike da kyar na tashi jikina na ta faman tsuma, duk kuwa da cewa na dan fara sabawa da wahala yunwa, kishirwa da sauran makamatan irin su. Bayan na huta na tashi domin na ci gaba da tafiya, jikina duk ya mutu, ina ta tunanin abinda naje nema, wato Sadik. "Anya kuwa Sadik yana da rai kuwa, in kuwa yana da rai to shiko zaman me ya ke yi a wannan bakin dajin.? Au cewa fa aka yi kama shi aka yi aka kulle." To kuma ai ni ban ga alamar ma zan sami wani gida anan ba." na kauda wannan tunani da tambayoyi mara sa amsa da na ke ta jero wa kaina, na ci gaba da tafiya ta kawai. Sai da na yi nisa so sai da bakin ruwan nan ya zama na bana 35 hango sht, sat na iske wasu bushiyoyin kwa-kwn ta ruwa, ga wasu nan sun fado Rasa, sun fhr fashe, na zauna na dauka ina ta barewa ina shanye ruwan cikin su ina cin kwakwar Sai da na Roshi NO ani sannan na tashi na ci gaba da taflyata. Ina cikin tafiya sai na ji ta sama wata aska shuu! ta jefar da ni wje daya, daga kan nan nawa sai naga wata Ratuwar mikiya, tana neman ta kuma kawo min sura, na goce a dai-dai sanda ta kawo surar ta watci kasa, ta sa ke dawowa kaina, ta nufi t cire min ido. da na fahimci nufin ta kenan, sai na ringa kare idanuwa na da hannuwana, hakanne yasa duk ta yayyaga min kayana da faratanta masu kama da reza, duk kuma ta yayyaku sheni, jikina ya yi jona-jina, har na fara galabaita, na kasa karo kaina, nayi shane-shame a kasa, havnayena bisa idanuwa na, domin ka da ta kwaRule min idanuwana. Ta taso da saurinta da niyar ta cake ni, sai na ji wani irin bugu can nesa da ni, ji kake wani jif!" na yi saurin ta shi in ga menene kuma, sai na ga mikiyar can gefe daya kwance ba rai, daga nan sai naga wuta ta kama jikinta. Mikiyar nan ta kone kurmus. Ai nan na mike cikin gigitacciyar razana na runtuma a guje, na Rara nutsatsa can ciki, sai da na gaji da gudu sannan na zauna na huta, nayi tagumi ina ta faman tunanin anya kuwa zan iya abinda ya kawo ni kuwa.? a gaskiya na tafka mummunar wauta ta shigowa dajin nan, domin wani mafarkin ba gaskiya bane." Daga nan na fara tunanin abubuwan da suke faruwa dani a dajin, na fara tunanin anya kuwa ba wani abu da yake taimaka min, amma ban fahimci ko meye ba.?" Na kauda wannan tunani da cewa "Allah ne mai taimawa bayinsa domin da 36 yar darsa ake yin komai." Ina gama yin wannan tunani na tashi dan ci gaba da tafiyar da ban san inda zan nufa ba. a Ina cikin tafiyata sai na dinga hangen kamar mutum a zaune a gindin wata bishiya. nan na kara azama domin ganin ko mutum ne na sami abokin hira, domin rabona da aganin mutum tun da na fita daga mota, har na debe tsammamin ganin wani kuma, ina isa dab da gurin sai na gano bafulatanar mata zaune, jikinta sanye da kayan fulani,amma ba komai a hannunta sai wata 'yar butar ruwa. Na yi ma ta sallama, ta amsa min cikin fara'a. Na cc "Dan Allah ki taimakeni da ruwa zan sha." ta ce "To ai ba wani abu, ungo, ta miko min ruwan da ya ke hannunta. na karba, domin ni duk zuciyata ta dake daga duk wani abin tsoro da zan gani. Sai da na sha wannan ruwa na koshi, sannan na mika ma ta ina ta faman yi ma ta godiya, na ce "Bari in dan huta a nan sannan na ci gaba da tafiya." na zauna a kusa da ita. Ta ce "Ba kya bukatar wani abinci ne, ko da 'ya'yan itatuwa.?" Na ce "Ina bukata, to amma ban san su ba shi ya sa ban ci ba; ko ban sa ni ba ko ba'a cin su, iya ka wadanda na sa ni nake ci in na samu.." Daga nan ta tashi ta nuna min irin wadanda ake ci, na tsaya ina kallonta ina mamkin ta. "Ji bi mace ita kadai a bakin daji nan amma ko alamar tsorata babu a tare da ita, can nace da ita "A nan kike da żama.". "Ke dai kyale ni inda kika ganni." ta ce da ni. na ja bakina na tsuke na zuba ma ta ido ina kallon ikon Allah. Daga can sai naji barci yana neman kamani. Nan na kishingida, abinka da gajiyayyiya, ai nan take barci ya 37 yi awon gaba da ni, daga nan ban san abinda ya faru ba. Acan gida kuwa, tunda gari ya waye Mami ta ga shiru ban fito neman abin karyawa ba, sai ta shiga dakin domin taga ko lafiya.? Tana shiga taga wayam! sai ta zaci fita nayi, dan haka bata damu ba a wannan lokaci, sai da taga har goma na safe ban dawo ba, sannan ta gayawa Ibrahim, shima a wannan lokaci hankalinsa bai ta shi ba, domin babu zato sai ya dauka ko gidan Aunty naje, shima ya tafi domin ya ganni hankalinsa ya kwanta. Yana zuwa tace Ai na jima rabona da gidan ta, sai dai in kauye na tafi." Bai dawo gida ba yana yi ma ta sallama, ya nufi can kauyen domin yaga ko naje can, da isar sa suka karbe shi bannu bibbiyu. Ciki fara'a Inna ta ke tambayarsa muna nan lafiya ince ko.?" ya ce "Inna ai ita na zo nema, domin tun da safe ba mu ganta ba, shine muke tunanin ko tazo nan." Inna fa hankalinta ya ta shi, tace a je gari zanzari a gani ko najc. Nan take ya tashi ya tafi garin gidan Baba Tasallah. Ya je nan ma bana nan, ko gidan Dakaci bai je ba ya dawo ya sanar da Baba, sannan yace "Da Allah abi gida jen 'yan uwa ko tana can." Inna tace "Ni da kaina ma zanje." Daga nan ya yiwa Inna sallama ya komo gida, aka yi ta yawon nemana, amma shiru, hankalin Alhaji da Ibrahim fa ya yi mummunar ta shi, su ka fara bada cigiya ta a cikin kafofin yada labarai. Shiru abu yau har kusan kwana hudu babu wani amo balle labari. Daga nan Alhaji ya shiga yiwa Ibrahim fada da cewa "Duk wannan abu kai ka jawo shi, domin na fuskanci yarinyar nan ba sonka 38 takc ba, kai ka matsa ma ta ta ce tana sonka, abinda ya sa ta gudu shine dan ta ga babu yadda za ta yi ne. Imma ta cc bata kaunarka ba kyalcta za ka yi ba, na fuskan ci kai ba yaron kirki banc, ga shi ka janyo lissafin mutane ya jagwal-gwale, to yanzu ya ya zanyi da iyaycn yarinyar nan.?" Ibrahim ya yi shiru, ransa a bace ya сe "Wai ni Alhaji da za'a dinga yi min fada ni ne na ce ta tafine!.? ba za ka kyale mutum ya ji da abinda ya dame shi ba, sai ka yi ta yi masa fada haka kawai..." "To waye ya jawo.?" Alhaji ya tambaye shi cikin bacin rai. ya ci gaba da cewa "Ai kai ka jawo, fada kuma dole a yi ma ka shi....." Ibrahim ya ta shi ya tafi yana gunagunai. Shima Alhaji ya fice zuciyarsa cike da bacin rai yana fadin "Da ma ya sa ni ya rabu da yarinyar nan ta tafi gidan iyayenta tayi zamanta, yanzu irin wannan me gari ya waya. Ita kanta Mami abin ya daure ma ta kai, ta samu Ibrahim ta ce ma sa "Ibrahim kar fa asirin mu ya tonu, ko aikawa zan yi a kwanto mana Abubakar Sadik, da ya ke yarone mai hakuri mu ba shi hakuri domin kar ya bayyana komai, in ya so sai ya nemo Hamdiyya, in kuma an samu labarin ya dawo, ita ma sai ta dawo.." Ibrahim ya ce "Tab di jam! Mami kenan, wallahi komai za'a baiwa Sadik sai ya bayyana, domin yana shan wahala, na ma fa ce su dauke shi gaba daya ma daga nan su mai da shi dajin nan da yake tsakanin Tagina da Birin Gwari a cikin wani gida da yake cikin kungurmin daji.." Ta dafe kirji "Haka aka ce kayi.? haba Ibrahim, mai ya sa kake haka, kar ka manta fa dan uwanka ne fa, ya ya zaka sa ayi ta gana masa azaba, ni dai ban saka ka 39 ahh abma hahe Thwalh i han tate that IT DE VE ব। কথি suke waga a firge Ahя hakun Kol Lallar Ya kara so a w kuycrun falon ya лша, уа dor Marn aaide Fokarn neman yrwur baknta NA Sabodt tsah sanarn fingici da te ye or "Ragva Lбя sammutn kina da wanma hahn na k ba sa yu Kn бoyс halayvar ka mara kva km o da min kyvа dan tsagata ya had ye ywm ha oika, daga bisa un yva ci gaba da crwa "Tanda nake da ke han taba una za ko sa ni a ma wannan bs sa vanza Wae dama kece mmol abaisim Satam Sadif ko keda danki, t0 Handryva ma kune kukа ут sanadin Satanta don haka san ki ncamo ta" Науa Mami ta dafe kirji "Alhaji walahi bam na Satar da ita ba Ya katseta Yi min sbira mara otunci, wailahi sai kin ffo m da ita" Ya dubi brabin, "Kai kum wallahi Allah kaga dan jinn jane to sai ma bukuntaka dai-dan da larfin da kzyi.. Ina son ma za ka sanar da n mda ka kzi Abubakar.7 Cikin tsanann nadama уа сс, Ya can ckia gr min da..jin Ta gima ya karasa batunsa muryarsa na rawa dim? "Oh. can kka kai shi ko.? 10 mai kayi masa a can "Wallahi ban yi masa komai ba, yana can dai a tsarc? 40 "Zamu je da kai a taho da shi, amma Ibrahim ka bani kunya, kuma ka bata rawar ka de tsalle kuma ka bata wayon ka, ban taba yin tsammanin haka kake ba ai yau, amma kowa ya yi da kyau, zai ga mai kyaı, kun.a abinda ka shika shi za ka girba.." ibrahim ya dur kusa ya kama kafar Alhaji yana kuka yana rokonsa gafara yana cewa, "Wallahi ya daina, ba zai kara ba, warınan ma tsautsayi ne." Alhaji ya ce "Kai jama'a, Hajiya kin cuce mu, wallahi kece kika bata min yara, shi kenan da namiji, amma kina neman samin shi a wani hali ko.?" Ta share hawaye ta cc "Alhaji, wallahi duk abinda ka gani ya baru, ba laifina bane. Laifina daya dai da na biye masa, duk abinda ya ce bana kwabarsa..." "Ai ina jin hirar da kuke yi, za ki bakantawa wani domin ki farantawa naki. Hum walllahi Hajiya Lami kin cucc ni, yanzu dare ya riga ya yi, amma gobe in Allah ya so zamu je a taho da shi. Ni yanzu ma da wacce fuskar zan kalli yaron nan da kuma ubansa Dakaci...?" Ya tashi ransa a bace ya fice, yana tunanin abinda yake wakana. *** Tun da barci ya share ni a gurin wannan bafulatanar, ban iashi farkawa ba sai a kofar wani gida a ciki dokar dajin nan. Na mike ina mai mutukar mamakin abinda ya kawoni nan, domin ni dai na san ba anan na kwanta ba. Ta ke na tuna da wannan mata Bafulatana, na dudduba ban ganta ba, na fara tunanin ba mutum ba ce oho, na ce a raina "Ko ma dai nanne gidan da Sadik ya ke.?" domin a mafarkin da na yi ance a nan dajin yake. 41 Nan ta ta ke naji wani irin gwiwa yazo min gami da Karfi. Na dubi jikina, duk kayana sun yayyage, sun yi wani bakikkirin, kaina ya cukurkude na zama kamar mahaukaciya, da da kitso ne ma da abin ya fi sauki, to amma a tsefe ya ke. Na mike cikin sanyin jiki na nufi kofar gidan, ina turawa sai na ji ta bude, na yi karambanin cusa kaina a cikinsa, na samu ashe ba tsakar gida, dakuna ne kawai da wani katon falo a tsakiyar Sakunan, na samu wsu mutane masu kama da 'yan fashi a kwakwkwance sun sa ki baki suna ta munshari, sai na yi tunanin sune na gani rike da Sadik a mafarki na. Na farko na shiga cikin da karfin zuciya ina duddubawa, sai na bude wani daki, na tarar da wani mutum a daudaure, a haka dai fari ne, amma yanayin wahala da datti sun sa shi ya koma baki, gashi duk ya rufe masa fuska. Sam ban gane ko waye ba, har zan rufe kofar sai na ji ana kirana a hankali ana cewa "Hamdiyya, zo ki kwance ni, Hamdiyya kar ki koma nine Sadik din ki ki zo ki kwance ni." ta ke na ji jikina ya yi wani yarrr! na shiga dakin da sauri na, na fara kwance shi, sannan na girgiza shi na ce "Sadik kai ne ka dawo haka.?" Ya ce cikin da she war murya, "kiyi sauri ki kwance ni, mu fita daga gidan nan, domin naji lokacin da Ibrahim ya yi wo musu waya tunda safe ya ce su kashe ni.!" Na bude baki gami da zare idanu, na yi ma za na kwance shi, na kamo hannunsa muka fito. To fa, ashe baya iya taka kafar, dole tasa na yi masa jagora, ta hanyar jin gina shi a jikin da na yi, muka fito muka fara tafiya yana ta dingisawa, sai da muka bar gidan, sannan na lura da raunikan da ke jikinsa. Take na fashe da kuka. Muryarsa bata fita so sai 42 ya ce "ki yi a hankali, kar su jiyo mu, muyi mu bar gidan nan. Na ce "To." muka nausa gabas. ya cc "Mu yi kudu, domin in muka mike hanya za su biyo sawun mu, su same mu su hallaka mu, kuma muyi azama ba hutawa." na ce "To." muka dinga tafiya baji-ba-gani, sai da muka sami awa uku muna tafiya, sannan muka dan zauna muna hutawa, duk da haka zuciyar Sadik bata amince da mu zauna ba, ni na matsa masa mu zauna, domin na gaji. Ba mu yi awa guda da zama ba, sai ga wani maharbi a tsaye akan mu. Na dube shi a razane na ce "Lafiya malam.?" ya ce "Mai kuke yi a nan.?" na ce "Ва komai, muna hutawa.?" ya ce "To ma za ku tashi ku tafi, domin yanzun nan na ga wata motar 'yan sanda da wasu mutane a ciki sun yi hanyar wani gida da ke cikin dajin nan.".Habawa, ba shiri muka muka tashi muka nutsatsa tare da maharbin nan, muka dinga tafiya maharbin yana taimakawa Sadik, ta hanyar sakale shi da hannayensa kamar yadda na yi masa a farko. Muka dinga tafiya, bamu zauna a ko ina ba sai wani dan gida na itatuwa. A she a nan maharbin nan yake da zama, ya kaimu har cikin gidan, muka zazzauna, ya kawo mana ruwa da gashashshen nama, muka dinga ci, sai da muka koshi muka sha ruwa, sannan hankalin mu ya komo jikin mu. Sai da maharbin nan ya fuskanci mun nutsu, sannan ya fara tambayar mu inda muka je a cikin wannann kungurmin daji da kuma abinda ya kawo mu.?" Sadik muryarsa bata fita so sai ya bada labari, nima na bada labarin 6atan da Sadik ya yi da nemansa da aka yi ta yi, da kuma mafarkin da na yi, game da shida tahowar da na yi da wahalhalun da na sha, da 43 hadarurrukan da na haye, duk na fada musu. ka wai sai na aga Sadik yana hawaye, ya ce cikin sanyayyiyar murya "Ba wani ne ya jawo mana wannan masifa ba, duk Ibrahim ne, be irin ukubar da ban gani ba, Allah ne ma ya yi da sauran kwanana a gaba, domin na debe tsammmani da rayuwa, yanzu ba zan iya ba dda labari ba, amma nan da kwana biyu zan baku labarin halin da na samu kaina har na galabaita haka. Maharbin nan ya shi ya yi wa Sadik gyaran fuska, sai a sannan na ga yanda Sadik ya rame, sai kace wanda yka yi cuta. kai wannan abin tausayi da yawa ya ke, na dube shi na ce "Sadik yanzu kaine ka daw3o haka.?" ya ce "Ninc, wuya meye bata sawa.?" na ce "Haka ne kam." Nan muka yi ta yin hira har dare ya kawo kai, Nan maharbin nan ya kawo mana gashashshen naman zabin daji mai dumi, muka ci muka sha, muka koshi. Sannan muka zauna a 'yar bukkar nan ta maharbin nan muna bira har shi, ba abinda ya damemu, sai hira muke kamar wadanda suke a cikin gidan su, idon mu ya rufe da ganin juna, sai muka manta muna cikin daji, na ce "Kai muna ta hira kamar ba a daji muke ba, kar fa wasu miyagun su far mana, bayn mun sa ki jiki." Sai maharbin nan ya yi dariya ya ce "Ain nan ko tsun-tsu sai na ga dama zai gifta ta wajcn nan." ba mu yi mamakin jin haka ba, domin ba mu san irin shirinsa ba. Nan dai muka yi ta hira, har barci ya dauke mu. ya yinda maharbin ya cе "Zai fita, shi a waje ma zai kwana. 44 *** Al'amarin su Alhaji kuwa, da gari ya waye, sai ya je ya sanar da 'yan sanda abinda ya ke faruwa, ya се kuma a bashin 'yan sanda su tafi domin taho da Sadik. Haka kuwa aka yi, suka ba shi 'yan sanda mota guda da kayan aiki, aka dunguma zuwa dajin, da Ibrahim aka tafi da Alhaji, suka nausa. Ibrahim shine mai nuna musu hanya, aka yi sa'a ba wani bata lokaci suka je gidan, da isar su, tun daga nesa suka kashe motar, suka dinga sanda. Har sai da suka je bakin kofar gidan, sannan suka shiga bayan sun gama shirin ko ta kwana. Suna shiga ciki, suka gansu a kwakwkwance shame-shame suna ta faman sharar barci har da munshari kamar wadanda aka baiwa maganin barci. Su kansu 'yan sandan sai da abin ya basu dariya, domin basu dauki abin da mutukar sauki haka ba. Ta ke suka sassaka musu ankwa, sannan suka shiga gabgabza musu mari, domin su tashi daga nannau yan barcin da su ke yi mai kama da na mutuwa. Su nuna musu inda suka tsare Sadik." a gigice suka farka, suka dubi 'yan sandan cikin mamaki, suka yi waura-wura da su. sai daya daga cikin su ya fara kwarmaton cewa "Wallahi mu ba 'yan fashi bane, oga Ibrahim ne ya kawo musu wani aiki ya kawo mu nan, Sai wani daga cikin 'yan sandan ya ce "Ai dama ba ance ku 'yan fashi bane, a bisa laifin ku aka kamaku. Ina Sadak din.?" Suka nuna dakin da yake. Ta ke biyu daga cikin 'yan sandan suka isa dakin da bindugogi a hannunsu, suka dudduba babu kowa a dakin sai igiyoyi da dan tarkacen da ba'a rasa ba, ga takalmi da agogo wanda ake zaton na Sadik ne. Suka kwashe suka fice, suka tasa sauran a gaba, suka nufi 45 inda 'yan uwansu suke. Suka sami Alhaji suka gaya masa basu sami Sadik din ba. Amma dai ga takalmansa nan da agogonsa." Alhaji ya karba ya duba ya сe "Hakika na sa ne, to ina ya kc.?" Su ka ce "Wallahi su dai ba su san inda ya yi ba..." Alhaji ya daka musu tsawa ya ce "Ina kuka kai min Sadik, ko kun kasheshine.?" Su ka ce "Ba su kashe shi ba, su kafin su yi wannan barci ma sai da suka sa ke lekawa domin su ganshi, kuma sun ganshi a sannan din." Nan aka shiga caje gidan, an caje gidan nan tsaf amma babu Sadik babu alamarsa. Alhaji ya ce "Shi kenan, yanzu abinda za su yi shine, su je can police station din su kai wadanda aka kama su fara tuhumar su tukunna." Duk suka dunguma suka shiga cikinmota suka

Chapter 3 of 5