tafi.
Bayan sun je can police station din, sai da suka ci
uban duka, amma sun kasa bayyana inda Sadik ya ke.
Sai Alhaji ya ce "A hada da Ibrahim a tsare, har sai sa
inda aka ga Sadik sannan za'a sake shi." Habawa,
Ibrahim ya dinga rokon Alhaji akan ya yi hakuri ya
kyale shi zai tafi neman Sadik din da kansa." Amma
ina, Alhaji ya ce "Ina, sam ba za ta yiwu ba." ya dubi
wani sajen Kabir yace "Yalla6ai,a kama shi mana, me
ake jira da shi.?" Su ka damkeshi suka ja shi. Yana ta
rokon Alhaji ya yi masa hakuri a kyale shi." Alhaji ya
ce "ban haifi dan iska ba, amma idan mutum ya ce zai
mai da kansa zai ga ba dai-dai ba." Yana gama fadar
haka ya shige motarsa ya nufi gida, zuciyarsa cike da
bacin ran abinda su Ibrahim da Mahaifiyarsa suka yi
masa.
Yana zuwa gida, ya sami Mami tana zaune bisa
46
kujerar falo ta tayi tagumi. Tana ganin Alhaji a fusace ta
mike cikin fargaba ta ce "Alhaji ya ya aka yi.?" ya се
"Ban sa ni ba, ke in kina da hankali ma kya tambayc ni
abinda ake ciki.? To bari ma in gaya miki. "Na sa an
tsare IBrahim, domin ba'a ga Sadik ba." ta fora hannu a
ka cikin razana ta ce "Alhaji ka sa aka tsare 1Brahim,
dan kane fa na cikin ka.?" ya cc "Kema in ba ki yi a
hankali ba sai kin bishi, shashasha kawai mara tunani.
Ya ya za'ai ki bata min dan, na san duk wannan abin da
ya yi ke kika sanya shi, ga shi nan kin jawo masa abin
da bai zata ba. Kuma kema sai na hukunta ki, domin ya
zama darasi a gaba, domin kar ki sake gigin yi min
makamancin wannan." yana gama fadin haka ya sa
hannu a aljihu ya ciro wata peper ya fara rubutu a jiki.
bayan ya gama ya mika ma ta ya ce "Ga shi nan ki je
gida, sai na ne me ki." ta karba a sanyaye tana dubawa,
tana ganin saki daya ne, sai ta dora hannu a ka ta fara
kururuwa. Ya ce "A'a. kin ga ma za ki fice kar ki tara
min mutane a gida, ki sa a zargeni da laifin duka. Alhali
ba hali na bane." Gaba daya ma gidan ya bar ma ta, ya
fice abinsa da ya ga ta dame shi da ban hakuri, ya ce "In
ta gaji ta fice, shi dai kar ya dawo ya same ta, in ba haka
ba kuwa zata fuskanci wulakanci.Haka ta hada kayanta
tayi tafiyarta, zuciyarta cike da da na sa nin abinda ta
aikata, a lokacin da da na sanin bata da wanin amfanin
yinta.
47
Yanzu Sadik yana iya tattakawa so sai, kuma yana
iya magana so sai, ma'ana muryarsa ta bude so sai,
sakamakon wani magani da wannan maharbi ya ba shi.
Har ya fara samun sauki, har dan fita muke yi ni da
Sadik muna zaga dajin, dan kusa-kusa muke zuwa, mu
samu 'ya'yan itatuwa mu wanke mu ci.
Wata runa, minje mun sami 'ya'yan itatuwa kamar
yadda muka saba, sai muka zauna hira, na ce da Sadik
"Yaushe ne zamu koma gida ne.?" ya ce "Sai sanda
wannan tsoo ya ce mu ta fi, kin san shi zai nuna mana
hanya.?" Na ce "Shi kenan." Ya ce "Wallahi har bana
son komawa.?" Na ce "Saboda mai Sadik."
"Iya abinda Ibrahim ya ke min ya isa, ko kin san
cewa "Shine sanadin bari na gida kuwa.?" Na dafe
Kirjina na ce "Ban fahimce ka ba.?" ya ce "Wallahi wata
rana ina zaune ina hutawa, ya zo ya ce "Wai Alhaji ya
aike shi, kuma ya ce na raka shi." ni kuma da na ji
Alhaji ne ya aike shi kuma har ya ce ya zo ya same ni na
raka shi. sai kawai na tashi na ce muje. A she shi akwai
abinda ya kula a zuciyarsa, shine fa ya kaini wani daji,
da farko ma ba nan suka kawo ni ba, daga bayane su
suka mai da ni nan gidan da kika zo kika sa meni, domin
suna ganin asirin sune zai tonu, oho. Shine fa suka shiga
gana min azaba iri-iri. Wallahi Hamdiyya ban zaci za su
barni da rai ba, kuma fa duk a kanki ne fa." Na share
hawayen da ya zubo min, na ce "Ba yadda bai yi da ni
ba, akan na yarda ya aure ni, ni kuma naki. Wallahi
Sadik, ko dai-dai da sakwan daya bana Kaunar Ibrahim,
48
ko ganin sa ma na tsani nayi, ni fa wallahi in muka
koma gida ba zan kara zama a gidan su ba, gidan mu
zan koma." Ya cc "A'a." na ce A'a na mec.?" ya ce "Ki yi
zamanki, a yanzu an gane sbarrin su, Alhaji ma ba zai
bari ba, na san ma zai sa idlo akan mu yanzu." Na ce
"Haka ne, amma ni gara in koma gida, in ma auren ne a
auro ni a gidan mu yafi dazaja." ya yi murmushi "Ai ni
duk inda kike mai daraja ce ke a gurina, domin irin
Kaunar da na ke miki ba zan iya fadar ta ba a baki.
Mun jima muna hirı, sannan Ya ce "Ya tashi muje
mu samo kwa-kwa." na ce "Kai Sadik, na gaji." Ya се
"To shi kenan, mu koma gida." na ce "A'a muje din." ya
ce "A'a tun da kin gaji, nima na hakura." na ce "To shi
kenan, sai mujc." ya yi dariya "Shi kenan, duk abinda
kika ce shi za'ayi." Na ina gama fadar haka naja hannun
shi muka tafi can ciki daji, muna ta samo kwa-kwar da
ta faffado kasa, muna fasawa muna ci, muna shanyc
ruwan cikin ta, sai da muka koshi sannan muka kama
hanyar kornmawa. Sai na hango watka bishiyar lemon zaki, nace "La-la-la, Sadik kaga wata bishiyar lemon
zaki a can." ya duba ya gano sai ya ee "Tsaya a nan in je
in debo, domin gurin ya faye surkukı so sai." na ce "A'a
sai dai mu tafi tare." ya ce "To shi kenan, amma sai dai
ki tsaya daga baya, ni kuma in tsınko." na ce "Na
yarda." muka rankaya, muna zuwa sai Sadik ya dinga
tsiko mana, ni kuma ina tara mana. Sai na hango wasu
manya-manya nunannu,na tashi zumbur domin in tsuko
su. Sadik ya ce "Ke da na ce ki tsaya a sarari,me ya
kawo ki nan.?" na ce "Wasu na gani nunannu." ya ce
"Bari in zaga, akwai kaya za ki soke hannu."
49
na ce "Don
Allah so na ke in dan tsikowar." ya ce "To ga shi nan,
sai ki tsinka." na mika hannuna zan tsinka, shima ya
tsaya yana kallo na yana cewa "In fa kika soke da kaya
kar ki yi min kuka.............." Kawai sai naga ya sa
hannusa da karfi ya tare wani abu, ya yin da naji sautin
bugun wani abu. babu kafa a hannun nasa ya fisgeni
baya da iya karfinsa, na fada can bayansa baki abude,
ina mamakin mai nayi kuma.?" Sai ya juyo yana rintse
ido gami da cije baki, ya ce "Mu bar gurin nan
Hamdiyya." na tsaya ina masa kallon rashin fahimta. ya
ce cikin tsawa "Mu bar gurin nan mana na ce miki!!!."
Ban san lokacin da na fita da gudu ba, ya biyo bayana,
muka dafo aguje. Sai da muka fito sarari sai naga Sadik
ya fadı,-ya yin da wani katon dankareren miciji ya
nannade masa kafa.Nan take na nayi tunanin shine
dalilin faduwar tasa. Na dawo da baya na tsaya ina
ganin yadda suke ta faman kokawa da Sadik. Allah ya
baiwa Sadik sa'a ya damke kansa, ya tattara karfinsa ya
karya, sannan ya zubar da shi. Ya mike ya nufo gurina,
sai na ga yana layi kamar dan giya. Cikin karaji na ce
"Innalillahi wa'innalillahi raju'un, Sadik ya cije ka.?" Ina
ba magana,kif ya kife a gabana. na yi wani ihu da sai da
dajin ya amsa kuwwa, na cakumi Sadik na juya shi,
idonsa babu baki sai fari tas! zatona Sadik ya mutu,na sa
ke kwala kara, gami gurin ya dinga juyawa dani. Kif
nima na kife kan Sadik. Nima daga nan ban san meye ya
biyobaya ba.
A hankali na bude idona, ya yin da na ji sanyin
wani a bu ya bigi fuskata, na dan juya kaina. Sai na ga
Sadik a waje daya daga shi sai gajeren wando. Maharbin
50
nan na shafa masa wani abu a jiki. na yi wuf! na mike na
dubi Sadik amma ba rai. Na ce da Maharbin nan "Ya
mutu?." ya ce "A'a bai mutu ba, wuyta ce kawai." N ayi
a jiyar zuciya n ace "Zai warke kuma.?" ya ce "Zai
warke, yanzu ma kuwa." Sai na ji wani sanyin dadi ya
kwarara a raina. na ce "Alihamdulillah." daga can sai
naji Sadik yana atishawa,sannan sai ya kuma motsa
kafa, ya dan bude idonsa a hankali, ya bude baki
le66ansa suka motsa ya fiddaharafin magana, amma ban
fahimci abinda ya ce ba. Sai da ga can na dan matsa
kusa da shi, na kasa kunnena a bakinsa, sai naji yana
kirana "Hamdiyya! Hamdiyya!! Hamdiyya!!!" na ce, a
dai-dai kunnensa a hankali "Na'am. Sadik. Ina tare da
kai." wuf ya bude ido yana kokarin ta shi, amma ya
kasa, na ruke shi ya tashi na jingina shi da jikin dakin na
ce "Sadik sannu, ya ya jikin.?" ya gyada kai kawai. Na
dubi Maharbin nan dake murza mai magani a koko na
ce "Bai yi magana ba." ya yi murmushi Zai yi ne." n ace
"To." Ya daura masa maganin, bai dade ba ya fara aman
wani bakin abu mai kama da karan wari. Na cc da Baba
Maharbi "Wannan kuma meye.?" ya ce "dafin miciji
ne,ai har guri uku ya sare shi." Na ce "Kaga fasa kan
farko ni ya yi niya, sai Sadik ya kare da hannunsa." ya
ce "A'a, daman ba ke ya yi niya ba, domin da ke ya yi
niya da ba zai bari har Sadik din ma ya gan shi ba." na
ce "Au miciji baya saran mata ne.?" ya yi murmushi ya
ce "Ko jinjiri ma in akwai tsautsayi ma yana saransa."
na ce "To saboda mai ni bai taba ni ba.?" Ya ce "A to
kinga ba ki sha wahala ba ke kadai ba shima sai ya
dandana ko." Ina jin ya fadi haka sai na yi murmushi,
51
domin duk ban fahimci abinda ya ke nufi ba, a zatona
zolayata kawai yake yi, domin na fuskanci mai son raha
nc. Sadik na gama aman wannan, sai na ga ya fara
dawowa hayyacinsa. Na yi masa sannu ya amsa
idanuwansa cike da hawaye, ya ce "Hamdiyya ina ce ke
wani bau bai same ki ba.?" Na ce "Ba abinda ya same
ni." ya ce "Alihamdulillah, daman ke na ke ta tunani,
domin ka macece." baba Maharbi ya fita ya barmu. Na
ce "Sadik gaskiya ka yiwa nutumin nan magana ya
samu a hanyar da zata sada mu da bakin titi mu tafi gida,
domin kar mu rasa wani daga cikin mu a cikin dajin nan,
ni fa hankalina ya gama tashi da gurin nan fa." Ya ce
"Ko mai kika ga ya sami bawa, to mukaddari ne daga
Allah." na ce "Duk da haka bana son zaman nan din,
haka kawai ga mutane can a gari, sai mu dawo daji da
zama.?" Ya cc "Ai dole ce ta kawo mu, amma zan yi
masa maganar in ya shigo, gara ya mai da mu gida ko
kuma ya samu a hanya, na san yanzu hankalin kowa ya
ta shi, musamman na rashin ki. domin ni kila ma an
manta da ta tawa da ya ke ni dadaddene, sai ke sabuwar
tafiya.
Da baba Maharbin nan ya zo muka yi masa
magana muka ce Ya samu a hanya za mu tafi." Sai ya ce
"To babu laifi, mu bari sai gobe, shi zai kai mu titi da
kansa." Mukai ta yi masa godiya, shima har da hawayc,
wai baya son rabuwa da mu.
Da gari ya waye ya ce "Mu shirya." To dama ba
wani abu zamu dauka ba, sai dai mu da kayan jikin mu,
wanda ni nawa a yayyage suke, ga kaina ba ko
dankwali, kuma ga shi gashina a cukurkude na zama
52
kamar wata mahaukaciya. Na cc "Ka wai mu tafi, mai
muka dauka zamu ajiye." Sadik ya dubi rigar jikina ya
ce "Gaskiya Hamdiyya ba za ki shiga gari da wannan
kayan ba." Na ce "To ya ya zanyi.? kasan dai kayan da
na zo da su na watsar da su a dajin nan. Ni yanzu ma ba
zan iya ccwa ga inda na yar da su ba ma." Ya ciro
rigarsa ta jeans, da ya ke iri daya ce da wandon jikinsa
ya ce In sa rigar, in ya inyi dan kwali da tawa
yagaggiyar rigata." na ce "TO kai kuma fa." Ya сс "Ai
ni akwai t.shirt a jikina, na iya tafiya haka, duk da dai
kayan sun yi datti." Na ce "Shi kenan mu tafi." muka ce
da Baba Maharbi "To mu tafi." ya dubi Sadik ya ce "Sarkin kishi lallai akwai aiki a gabanka." Bamu fahimci abinda ya ke nufi ba. Muka yi dariya, na ce "A"a. to ya
kamata ai ka yi masa fada dai." ya ce "Ya yi wa kansa fada dai.Domin na fuskanci akwai LUGUDEN KAUNA
a kanki,in ba haka ba kuwa ya sha kaunar zuci." Muka
sa ke yin dariya, domin duk bamu san mai yake nufi ba. Na ce da shi "Haba wai kai baka da aure ne." ya ce "Haba. aure kai, ni nine ma kuwa mai aure, nima tawa matar jira nake su gama nasu LUGUDEN KAUNAR а
kanta, sannan in yi nawa, kun san manya-manya maganin kanana-Kanana, namu daban ne, in muka sa kai kuma sai hakuri." Muka ce "Haka ne kam Baba." Na ce "Wallahi Baba sai naga daman kamar tare muke da kai, ka san komai game da labarin mu." ya yi murmushi ya ce "Ai a hirar da na kanji kuna yi a nan nake fuskantar wasu abubuwa."
A hankali muna tafe, in mun gaji sai mu huta, a
haka har muka kai bakin titi, tun kusan karfe biyu muke
53
tsaye a titi, har karfe hudu da rabi bamu samu inota ba,
domin duk motar da muka tsayar bata tsaya wa. Da
Baba maharbi ya gahaka sai ya ce "To shi zai koma, kar
dare ya yi masa a hanya, domin abai taho da makami
ba." Maka ce masa "To." muka yi masa godiya so sai,
muka yi sallama ya wuce, mu kuma muka tsaya a nan
mina jiran mota. Bacewar Baba ke da wuya, sai ga wata
mota kirar marsandi sabuwa dau, sai sheki ta ke yi,
muka ringa daga ma ta hannu. Muka yi sa'a kuwa ta
tsaya. Direban ya leko ya ce "Ku shigo muje, ba kano za
ku je ba." Maka cc "Eh. Kano zamu je."
"To ku shigo mu tafi." Muka shiga muna mamakin
ganin yasan inda zamu dosa.
Sanda muka shiga misalin biyar na yamma ne,
amma abin mamaki kafin shida munje gida. Ku duba ku
ga tsakanin Tagina da Kano, wannan abu ba karamin
mamaki y abamu ba. Amma muka ja bakin mu muka
tsuke. To ashe abin mamaki yana gaba, domin muna
zuwa Kano hanyar Norman Sland ya nufa da mu. Bai
zame a ko ina ba sai a kofar Gidan Alhaji. Cikin
dumbin mamaki Sadik ya ce "Au dama ka san mu ne.?"
Ya ce "I mana. tsiyata da ku mantuwa, yanzu har
kunmanta ni.?" Sadik ya ce "Wallahi ni dai ban gane ka
ba." ya yi dariya ya dube ni ya ce "Ke ma fa ba ki
shaidani ba ko.?" Na ce "Uhm Sadik ma bai sanka ba
bare ma ni.?" ya ce "Lallai sannnun ku, to ku fita ni zan
koma." Muka dage akan sai ya sanar da mu ko wanene
shi, domin kar a gaba mu kara haduwa kaga kamar
wulakantaka muka yi." Ya ce "A'a. ni ba komai, ni ba
zan manta ku ba." Mu ka ce "To barimu karbo ma ka
54
kudin motarka a gida." Ya ce "Ni kyauta na kawo ku,
domin ba haya na ke yi ba." Ya yi baya abinsa,ba tare da
ya sa ke saurarar muba, ya yi gaba ya bar mu nan a tsaye
muna mamkin wannan abu.
Nusaiba ce tsaye da wani saurayin ta ya zo zance,
ta rako shi zai tafi gida, sai ta ga mun turo kofa mun
shigo. Ai ko muna yin ido biyu da ita, ta zabga wani
uban ihu, tay cikin gida da gudu, ta mance da saurayin.
Ta yi dakin Alhaji, shima yana shirin tafiya masallaci,
suka yi karo da shi a bakin kofasa. Ta ce cikin tsananin
kidima da murna da karaji. "Alhaji ga Yaya Sadik da
Hamdiyya nan!!!!!!."
Alhaji dake jan carbi bai san inda carbin ya kubce
masa ba, ya tsinko da gudu yana fadin "Suna ina!!!!"
tuni mu kuma mun karaso ciki. Mu ka yi tozali da
Alhaji, yana ganin mu ya bude hannu cikin tsananin
farin ciki, muka fada jikinsa ya rungumemu yana ta
faman murna.
Muka shiga ciki, Alhaji ya ce "A kawo mana ruwa
da abinci. Nan dai Alhaji a gida ya yi sallah bai je
masalllaci ba, Carbin sa ma sai Nusaiba ce ta tsinto
masa. Ya yi wa Allah godiya iya son rai, sannan ya ce
"Mu jemuyi wanka mu nutsu tukunna da safe ma bashi
labarin ko mai nene tukunna.
Na shiga bandaki na fesa wanka gami da wanke
dankararren curarren kaina, na yi sallah na shafa
mai,kana na sauya kaya na masu kyan gaske. Sai ga shi
na dawo Hamdiyya sak!na nade gashin kaina na daure
shi da ribom. Na fito na sami Nusaiba a falo, na ce "Ina
Mami.?" ta ce "Uhm ke dai zauna, sai dai goben kyaji
55
komai. Muna zaune muna taba 'yar hira na yaushe
gamo, sai ga Sadik nan ya shiryo tsaf, in ka ganshi ba za
ka ce mune muka dawo dazu ba, tanıkar daman can a
gida mukc, sai dai rama gata nan kam.
Da gari ya waye, Alhaji ya tara mu, bayan mun
karya ya sanar damu abinda ke faruwa game da Ibrahim
da Mami da irin bukuncin da ya ſaukar musu, sannan ya tambaye mu abinda ya faru da yadda aka yi, muka
gamu. Sadik ya fada masa labarin sa,sannan ya sanar
masa cewa "Duk ya san Ibrahim ne ya shirya masa
haka,sabida kaunar da ya ke yiwa yarinyar nan
Hamdiyya......" ya ci gaba da cewa amma yanzu duk
wata batun kauna da ya ke ma ta ta kau, domin kuwa
duk wannan sai da ran da Hamdiyya ta yi a kan Sadik
saboda ceton ran Sadik, hakan shine ya nuna mana
matsanaiciyar kaunar da ke tsakanin su." nan muke
tambayarsa Mami.? ya ke cewa "Ai dalilin wannnan abu
da suka yi w Sadik ya sashi ya yi ma ta sakin jan kunne.
Sai da Alhaji ya tara 'yan uwan Mami, ya kira
Dagaci, ya kira su Inna da Baba Tasallah, ya hada 'yan
uwa kaf, sannan ya bayyana musu abinda ke faruwa,
domin da basu da labarin komai, a zaton su dai bata ne
Allah ya kawo. To ga sanadi abinda ya sa ya sanar da su,
kuma shi baya son rashin gaskiya, ba kuma ya san
goyon rashin gaskiya, yanzu ma zancen nan da akc yi
Ibarahim yana can tsare a hannun 'yan sanda, domin ya
ce "Kar a sak e shi har sai sun bayyana inda Sadik da
Hamdiyya su ke." Nan da nan Dagaci ya tashi da fada
ya ce "Amma kuwa Alhaji ba ka kyauta ba, ta ya ya za
ka sa a tsare yaro, baka san kuruciya banc.? Ai rashin
56
bali irin na yara maza, ka sa a sake shi ya dawo gida.
Wannan aikin banza kenan." Alhaji ya ce "Toban ki ta
taka ba, amma ai ya kamata a ja masa kunne, domin bai
isa ya kawo karan tsaye a zumuncin mu ba, haka ya taso
ya ga muna zumun cin mu ba, in dai yace haka zai yi to
ba dai a gidan nan ba, sai dai ya nemi wani gidan uban,
amma ba dai nan ba." Dagaci ya ce "To ai ya horu, ba
zai sake ba, ayi afuwa." Sadik ya ce "Baba Mami ma fa
tana gida, ya kamata a ce ya dawo da ita." Dakaci ya ce
ita kuma ai ba sakinta ya kamata kayi ba, sai ka tsawatar
ama ta, in taki ji ne za ka dau kwakkwaran mataki."
Nan dai Dakaci yasa yaje yasa aka saki Ibrahim, su
kuma wadancen ya ce A kyale su sai ya waiwaye su in
ya nutsu." ya kuma je gidan su Mami ya taho da ita,
akan yarjejeniyar in ta kuma ko makamancin wannan ne
to bayan ya sake ta sai ya sa an daure ta. Sannan ta
yarda da sahardain,suka taho.
Suna zuwa gida, Ibrahim ya yi tozali da Sadik, sai
ya fashe da kuka, yana neman gafararsa. Ta ke Sadik ya
gafar ta masa, sannan ya baiwa Dakaci hakuri, shima ya
yafe masa, duk da dai yana nemi gafarar kowa a wajen
nan. Sannan ya nemi ta mahaifinsa, shima ya yafe masa.
"Amma in ya kara ba zai ga da kyau ba, haka dai guri ya yi tsit! Sannan Alhaji da kansa ya labarta musu irin
wahalhalun da muka sha da Sadik a wannan tafiya, ya
kuma ya ce "A cikin su waye ya kama ta ya auri Hamdiyya ta aura tsakanin Sadik da Ibrahim.?" Ta ke aka hada baki a ka ce "Sadik ya kamata ta aura!!!." Nan
murna ta kamamu, amma muka boye murnar, gudun kar
a agane, sai aga rashin kunyar mu kuma gashi da manya
57
a wajen. Nan Alhaji ya nemi aure a wajen Dakaci, da yake ba maza a 6angare na, sai mijin Ba ba, shi kuma
bai zo ba, sai aka wakilta Dakaci, domin shi Alhaji
daman shine waliyin Sadik.
Dakaci ya amince, aka sa ranar daurin aure. Kowa
ya watse ya tafi yana farin ciki da abinda ya faru a
wannan rana.
Daga sannan na zama 'yar lele a wajen Mami, ta
dauke ni tamkar Nusaiba 'yarta, shi kuwa Sadik shima
hakannc.
Da ranar daurin aure ta zo, aka yi gagarumin
daurin aure, aka sha shagalin biki, wanda ba'a taba yin
kamar sa ba a dangin su Sadik.
Gidan da Alhaji ya bayar a ka ginawa Sadik da
Ibrahim biyu iri daya, kusa-da -kusa shine gidan da aka
kaini. Alhaji shine ya yi komai na game da kayan daki,
to daman gidan ba abinda ba'a sa ba a ciki. Gidan kam
ya hadu so sai, ba abinda ba'a saba a ciki.
A nan gidan Aunty muka sha shagalin biki, amma
a can kauyen mu aka dauko amarya. Kun san kauye da
tsaraba, wai a dauki yarinya a gidan su ya fi mutunci, To
nima nayi farin ciki da wannann lokacin da aka kaini
gidan Sadik, na yi mamakin irin dumbin dukiyar da ya
kashe, domin sai da na dinga tunanin ko dai mafarki na
kc yi ne.?" Domin abiun ya so ya firgita ni, nan dai ya
kai amarya suka gama shewe-shewen şu da gude-guden
su suka tafi suka barni ni takk a cikin gidan, ba yadda
aban yi da su Haulatu da Safiyya ba akan su zauna
amma su ka ki kememe. Ita kuwa Nusaiba cewa ta yi In
ta zauna yaya zai ce ta yi rashin kunya in sun zo siyen
58
baki. Haka na kyale su ba'a san raina ba suka tafi.
bayan sun fan jima da tafiya, sai ga gayyar
angwayc nan sun dumfaro, na yi saurin lullube jikina
duk da Katon mayafi, na zauna nayi shiru d ni, kaina a
sunkuye, suka shigo suka gama barkwancin su, Rarshe
suka yi addu'ar Allah ya bada zuri'a ta gari, suka tafi. Ya
yin da shi kuma ya yi musu rakiya. Jim kadan ya dawo
ya same ni a zaune, shima ya sami guri ya zauna ya
dube ni ya yi murmushi ya ce "Amarsu ta ango mai
dadin mai dadin tuwo da miya." na yi dan murmushi na
ce "Uhin." ya ce "Ya ya hidimar biki.?" na ce
"Alihamdulillah." ya ce "kai munasha kacaniya, wallahi
tunda aka fara bikin nan ban zauna ba." Na ce "Ai nima
haka." Ya ce "To an dai gama komai ko. ya yi kyau,mun
godewa Allah,yanzu sai mu tashi muyo alwala mu
gabatar da nafula ta godiya da farin cikin wannann rana
da Allah ya nuna mana." Na ce "Haka ne."
Bayan mun idar da sallah, ya fara mana da tsarabar
da suka zo da ita domin mu ci. Muka zauna muka ci
muka sha. Bayan mun gama na kwashe kayan, muka je
muka yi wo brush, muka dawo muka zauna muka fara
hira, da yake dare bai yi ba so sai. Can Sadik ya dube ni
ya ce "Hamdiyya Allah ya cika mana burin mu." Na yi
murmushi na ce "Hakika." ya ce "Gaskiya abinda kika
yimin har in koma gamahaliccina ba zan taba mance shi
ba, bani da abin da zan saka miki da shi...... Na katse shi
ta hanyar cewa "A'a kana da shi." Cikın doki ya сe
"Menene shi, fade shi ko meye shi in ba ki in har ina da
shi. Na ce "Ai ba komai bane ilah kishiya, domin na san
ko badade, ko ba jima sai ka karo aure, kaga kuwa ai ka
59
yimin kyakkyawan sakamako." Ya yi murmushi ya
lakuci hancina ya ce "Kin ganki, ba ki da dama.?" na ce
"Ai sanin halin ku na yi na maza." Ya ce "Ya ya akai
kika sa ni.?" na ce "Ai halinku ba boyayc bane, kowa ya
san shi, kuma in kun kai dubu halin ku daya ne." ya ce
"Na alheri ba.? Ai kuma matan haka kuke, ku waye ma
ya kaiku halin tsiya." Na ce "Uhm. Yanzu fa ka gama
yabona, amma tun kafin a je ko ina ka far kushe mata"
"Ai wannan hali na ku sai dai a ganki da shi a
kyale."
"A'a banda sharri, domin mu ba mu da wani hali sai na
alheri.?" Na yi dariya "Haka ne yabon kai." Ya ce "A'a.
ba yabo kai bane." na ce "A'a to. ni dai maganar kishiya
babu ita." ya yi dariya ya