ce "Kin sa ni tun farko ki yi
min worning." Na ce "Ai yanzu ma bata baci ba, ga shi
na yi maka wannan din." Ya ce "Daman ni bani da ra'ayi
tara mata in dai da zaman lafiya. To daya matar ta
isheni." na yi dariya na ce "Ka dawo hanya kenan..." Ya
damki hannuna. "Taso mu zaga gidan nan kiga yadda ya
ke." Na ce "Ai dare ya yi, ka bari sai gobe." ya ce "A'a
mu dai zagaya yanzu." na ce "To muje."Muka fara
zagayawa, da ya ke ko ina yana da haske, duk sai da
muka zage dakunan nan kaf, sannan muka dawo falo.
Na ce "Hakika Sadik gidan nan ya tsaru so sai." Sadik y
ace "Inda kika ga wannan to haka na Ibrahim ya ke ba
banbanci." na ce "To yanzu aiki yake, ko sai ya yi aure
sai shiga.?" Ya cc "A ciki ya ke da zama. Tun da Alhaji
ya bamu mukulli ya koma can da zama." na ce
"Ibarahim kenan, dan rigima yanzu fa ya yi nadama." ya
ce "Ibarahim fa da gaskiyarsa." Na yi saurin dubansa
60
"Kamar ya ya.?"
"Ai ba wanda zai ga zukekiyar kyakkyawar
yarinya ga kyan diri ya kyalla, ai sai inda karfinsa ya
Kare. Wallahia haduwar kice ta rikita shi, haka kawai
yana son zai yi min kwance." na yi dariya na ce "Kai dai
zuga kake." ya ce "A'a ba zancen zuga bace, zo muje mu kalli mudubi mu gani." ya kama hannuna, na yi kokarin
kwacewa na kasa sai na ce "Dan Allah Sadik ka cika ni,
ni ba sai na je ba." Ya ce "Wallahi sai munje ki gani.
Yana gama fadar haka ya sure ni, sai dakin barcinsa. A
she kofar dakin a kulle ta ke, tun sa'inda muka gama
kewayawa dakunan gidan ya rufe, don haka sai ya zama
dole sai ya dire ni zai bude kofar. Ni ko yana direni na
fita da gudu, na barshi yana kokarin bude kofar. A
bayan kujerun falo na buya, ina jinsa yana ta faman
nemana. na yi shiru, dariya ta kusa ta kwace min, na dai
cije, shima sai ya sami guri ya laße. Nima sai na yi zaton
ya gaji ne ya koma fakin shi. sai na fito ina dariya a
gadarance. Haba ai kuwa sai na kicubus da shi a wajen
dakina a labe. Haba sai na juya da gudu. Ina tuni ya caf
koni, muka fadi muna dariya, Ya ce da ni cikin rada
"Wallahi a duk sakwan daya, miliyoyin kaunar kine
suke shigar min zuciya." Na yi murmushi, ya yin da na yi shiru ina sauraron irin bugun da kirjinsa ya ke yi, a
jikinsa na sa ke murmushi domin na dago, na dan zame
na dube shi na dan rausayar da manyan fararen
idanuwana na ce "Ka je ka kwanta, barci ka ke ji." Ya mike gami da ruko hannuna ya ce 'To ta so mu je mu
kwanta." na ce "Jeka gani nan zuwa, zai je dakina
'tukunnan ya ce "Ina jiranki fa." na ce "To ka jirani." na
61
mike na zaga na je na shiga bandakin cikin dakina na
fesa wankana, na zauna a gaban dressing mirrow na shafa mayuka masu mutukar kamshi da taushin fata, har
sai da na ji fatata tayi limis tukunna, sannan na saka rigar barci mai shara-shara mai kyan gaske dafaffiya, na
saka, nan takamani so sai, sannan na sami
turaremaikamshi da jan hankali na feshe jikina da shi.
Na gama shiryawata tsaf. na cire 'yan kunnayen na da
sarka da abin hannu, dama tunina saka silifa, na fita da
niyar inje dakin Sadik, sai wata zuciyar ta hanani da
cewa "Lallai ma Hamdiyyar nan, kina 'ya mace za ki
fara zuwa wajensa.? Ka wai yi zamanki, in kumaya ji
shiru ya zo da kansa, sai na juya da nufin in je in kwanta
sai na ji an cafke min hannu na. na yi saurin juyawa a
razane cikin tsananin kaduwa. Ashe Sadik ne. Na се
"Yau she ka shigo.?" Ya ce "Ai na jima a dakin nan."
Na ce "Amma ban ganka ba." ya ce "Hankalinki bai je
kaina bane, amma na jima a dakin nan." na yi
murmushi. Ya cc "Amma fa kin hadu, ya fara shakar
kamshin turaren da na fesa, ai sai ya rikice sai dafin kis
take, tun ina kokarin kwatar kain,har ya fara galaba a
kaina, to dama ya abu ya hadu da mtsanaiciyar kauna,
ban san lokacin da na fara mayar masa da martani ba Ta
ke na kara rikita shi, gaba daya idonsa ya rufe
hankalinsa ya kifu a kaina, ya riga ya yi nisa. A hankalı
na ringa jansa da baya zuwa gado, domin hankalinsa ya
riga ya gushe, anan na dada sakankancewa, na yi dace
da masoyi maitsananin kaunata. Nan fa na fara raa
masa kalaman kauna tsan-tsa masu faranta ran mai bege,
musamman ma a irin wannan daren da ma'abota
62
soyayya kan kira shi da daren bayyanar da kauna. Duk
kuwa ma'abocin soyyya yana cin burin riskar wannan
dare. To mu ma dai a kwadaice muke, dan gann mu raya
wannan daren. don haka muka dauki aniyar farantawa
juna, A wannan lokaci Sadik na daga baya, ma'ana
bayansa na fuskantar gado, ya yin da ni kuma ina manne
a kirjinsa muka isa gadon.
Wata kara da na kwala, na fisge dan gudun kar ya
Karasa gadon, ita ta mai da shi cikin hankalinsa, muka
zube a kasa cikin kaduwa da firgita, cikin karaji na ce
"Sadik duba kan gadon nan ka gani, meye wannan ?" ya
juya da sauri, ya yinda ya yi ido biyu da wani katon miciji mai sauya launika, in ya yi baki, bakinsa ya kan yi ja, ko kuma ya juya ya zama kore ko yalo ko blue, kaurinsa kuwa ya yi kaurin cinyar kato, sai wani irin murmurdewa ya ke a gadon. Da gudu muka kai bakin kofa muna haki, muka sake juyowa muka kalle shi, yana
nan a inda ya ke. Na dubi Sadik wanda mamaki ya hana shi yin magana, ya dubi a gogon bango dake sakale a
daki, karfe biyun dare saura kwata, ya girgiza kai ya dubeni "Mu rufe wannan kofar mu koma dakin ki mu kwanta har sai da safe a zo a fidda shi. Ha! Ha!! Ha!! Muka ji dariya, kamar daga sama. "Ina son ka gaya min inda aka taba yin aure akan aure, kuma ni nafi karfin ka fidda ni daga cikin gidan nan, in kuma har kana ganin za ka iya ka jarraba in gani........" "To fa mai karatu, tsugunne bata kare ba,wai an sai da mage an sayi biri, domin suna ganin sun yi aure sun tsallake duk wata gwagwarmaya da suka sha. to abin ba haka yake ba, rikici na gaba, dan sanin yadda aka yi
63
kuma za'a kaya sai a nemi littafin SHARRIN JINNI 3 na
uku don jin yadda zata kasance.
Daga mai Gaunarku a kullum
'Yar mutan Sharada
AMEENA ABDULLAНІ
(Mrs Ahmad Yusif)
Hadcjia
08085389470
64
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
ZAZZAFAR KAUNA 1, 2 & 3
TALLAFIN KAUNA 1 & 2
SIRRIN JUNA 1 & 2
HAKURI DA MASOYI 1 & 2
RASHIN HALAC GI 1&2
TSAYA KALLON RUWA... 1 & 2
SHARRIN JINN
PRINTED BY: AL-AMIN B/PRINTING & PUBLISHING COMPANY No.; 156 S/TITIN MANDAWARI KANO CITY. 08028411703
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels