yanzu dafe take da audugar da likitan ya lika
mata bayan ya dauki jinin. A hankali ta dan daga audugar sai
audugar ta dan taso sama amma bata gama rabuwa da inda aka
likata ba. hakan na da nasaba da dan jikewar da ta yi da ruwan
dettol.
Sannu a hankali Jamila ta daga audugar sai audugar ta fara
bin hannunta dake rike da ita yayin da kadan daga cikin audugar ta
manne a jikinta, zafin da Jamila ta ji ya yi daidai da zafin da za ki ji
yayin da kiyashi ya cijeki, ta dan yamutsa fuska kadan irin na
karuwai.
"Jamila kala." Aka kira sunanta daga ciki.
ta Ta tashi cikin yanga da gwalli tana kwarkwasa irin na
karuwai ta soma wasa da duwawunta kamar yadda ta saba idan
san ana kallonta. Tana zuwa ta daga labulen kofar ofishin likitan ta
shiga cikin yanayin yanga babu ko sallama. Ta sami kujerar dake
gaban teburin likitan ta zauna a kwarkwasance.
"Gani." Ta fada cikin kalmar raini bayan ta zauna.
"Na ganki." Likitan ya ce da ita daidai lokacin da yake
rubutu bisa takardar dake gabansa.
"Likita wai me ke damuna ne?" Jamila ta bukata tana fari da
idanunta.
"Za ki ga komai a rubuce." Likitan ya fada yayin daya dago
kansa daga rubutun da yake yi.
"Yi sauri ka sallame ni dan Allah Honarabil na can yana jira
na kada na 6ata lokaci." Ta fada maganar taso ta bawa likitan
dariya. amma sai ya kanne gami da miko mata wata 'yar doguwar
takarda mai dauke da rubutu.
Ta karbi takardar da hannun hagu a wulakance lokaci guda
kuma ta mike tsaye ta soma tafiya tana kada duwawukanta da ta
saba. ta tabbatar a zuciyarta dole ne likitan ya kyasa. sai dai kuma a
nata tunanin wutsiyar rakumi ta yi nesa da Kasa.
Likitan ya kallo duwawukan nata dake rawa kamar mazarı.
ya dan yi murmushi kana ya soma magana a fili amma Kasa-Kasa
bayan fitar Jamila kalar birni.
"Da in kusanceki gwara na rungumi tiransifomar da ruwan
sama ya jikata ba mamaki ta kasance ba wuta."
54
...
Honarabil ya yi kwance rigingine yana lunanin satar da zai
shirya bayan gama masha'ar da ya yi da Jamila. kusan satin sa daya
bai je tsangayarsu ba.
"Gaskiya Honarabil ya kamata ka canza min mota, haba
wannan motar tawa naga an fara yin tasi da irinta kai har daukar
kayan miya ake da irinta a 'Yankaba."
"Eh, gaskiya dole a canza miki wata, domin na ga akwai
wata sabuwar ya yi mai suna 'KIA' da ta shigo ita zan saya miki."
"Yauwa daling ko kai fa." Ta fada yayin da ta yi isalle ta
fada kansa tà fara yi masa wasannin dake sawa ya manta da
kauyawan matansa, irin wasannin da take yi masa ne yasa yake
bata kyauta kowacce iri ce, wani lokacin cikin hankalinsa yake bata
kyautar wani lokacin kuma hankalinsa a gushe yake kyautar.
"Jamila....." Ya kira sunanta cikin wani irin sassanyar murya
kamar muryar yaron da kyanda ta kama makogoronsa.
"Na'am Honarabil." Ta amsa a yangace.
"Allah ya tsinewa matana na kauye."
"Haba Honorabil me yasa kake tsine musu?"
"Ba su iya komai ba shegun."
Dariya ce ta biyo baya gami da kara mikewa jikinsa sun fi
mintina biyar a haka.
Sannu a hankali Honarabil ya sabule gajeren wandon dake
jikin Jamila, ita ma ta sabule na jikinsa suka soma bin umarnin
shaidan bayan ya yi sa musu hijabinsa.
"Kar fa ka manta da maganar motar Honarabil." Jamila ta ce
dashi a shagwabance ta hanyar yaudara da kisisina, irin ta matan
bariki
"Haba Honey ya za a yi na manta." Ya fada yana kokarin sa
farin gajeren wandonsa, bayan sun gama sharholiyarsu, yana gama
sa gajcren wandonsa ya ci gaba da magana.
kan "Akwai wani korafi da na yi ga karamar hukumar mu
gyaran wata gada, 'in kudin sun fito duk abinda zai faru sai na saya
miki mota a ciki."
"Kai Honorabil kada fa 'yan kuayaen ku su yi maka tawaye."
"Haba Jamila kamar ba ki san halin mutanen mu ba, daga an
zagemu za ki ji wasu sun fito rediyo suna karemu."
55
"Su masu kare kun kudi kuke ba su?"
"Ba wani kudi in dai matar mutum ta haihu ka kawo goro da
alewa ka ba shi ko ka saya masa dan ramammen rago shi kenan ka
gama masa komai."
"Wato kowa dai matsalar kansa yake kawowa?"
"Kwarai ma kuwa, akwai wani ginin asibiti da ni da ciyaman
dina da sauran mukarrabai muka hau kansu har yanzu shiru kike ji
kamar an aika bawa garinsu."
"Au Honarabil har ka tuna min da ka ambaci asibiti na manta
dazu fa na je Lamco Lab sun auna jinina saboda yawan zazzabin
dake damuna, bari in dauko maka takardar ka duba tun da ka san
kan magunguna, sai mu je Kemis mu sayo magungunan da suka
rubuta."
Honarabil ya karbi takardar yana dag kwance ya fara duban
takardar yana nazarinta. Firgigit ya mike zaune akan katifar ya
mutsuttuke idanunsa da hannun hagu yayin da takardar ke hannun
damansa a rike.
"What!" Ya fada da karfi.
Ganin irin firgitar da ya yi gami da zazzare idanunsa da ya yi
yasa Jamila ta firgita.
"Typoid ne Honarabil?" Ta bukata daidai lokacin da jikin
Honarabil ya fara karkarwa yana tsima tamkar wanda ake kadawa
gangi. Bai yi magana ba, duban takardar kawai yake yi har yanzu
kwalla ta cika masa idanunsa.
"Ko Maleriya ce." Ta sake tambaya karo na biyu a zake.
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'una, lahaula wala kuwwata.
na shiga uku na lalace, wayyo Allah na..."Shiru ya yi ya kasa ci
gaba da maganar yayin da ita ma Jamila ta fara firgita domin bata
taba ganin Honarabil a cikin irin wannan yanayin ba..
"Allah ya tsine miki Jamila, shegiya azzaluma kin cuceni kin
cuci rayuwata kin cuci matana, Allahya isa tsakanina dake ashe
cutar kanjamau ce a jikinki shegiya lyarwuta azzaluma, wayyo
Allah. wayyo Allah na shegiya na shiga uku wayyo Allah." Ya fada
a razane yana kuka.
"Ni cc nake da cutar Kanjamau? Sai dai in kai ka sa min
shege macuci..." Kuka ya subucewa Jamila. sauran maganar ta
56
makale a fatar bakinta ta soma birgima a kasa gami da fargaba sun
yi, dirar mikiya a cikin zuciyarta.
"Honarabil wai me ye rubuce a jikin takardar...?"
"Ki duba mana ba Positive ne rubuce a jikin takardar ba..."
Ya fada muryarsa na rawa.
"Wayyo Allah na shiga uku na lalace..." Jamila ta kwala ihu
cikin firgita yayin da muryarta ke sassarkewa sannan ta yi shiru.
Shirin da Honarabil ya tabbatar masa suma ta yi cikin rashin
kwarin jiki ya mike ya karasa sa kayansa a rude sannan ya fice
daga dakin ya bar ta anan sume da farfadowarta da rashin
farfadowarta uwarsu daya ubansu daya, shi dai ya tabbatar tasa ta
Karc.
Kwanan Isma'il biyu garkame a ofishin' yan sanda, daya
daga cikin abokan barikin Isma'il ya yi belinsa bayan Sumoli ta ce
ta hakura.
A gida kuwa Hajara nata zulumi ko wani abu ne ya sameshi
don duk daren duniya Isma'il ya kan komawa gida tun da suka yi
aure sau uku kawai ya taba kwana a waje shima ya gaya mata
dalilai, in ka dauke wannan kwana ukun da kuma 'yan tafiye-tafiye
da ya saba yi lokacin-lokaci, bai taba kwana a waje ba.
Abinda Hajara bata sani ba shi ne tafiye-tafiyen da yake yi
duk na karya ne yana yin su ne a dakin Sumoli suna shake a yarsu.
"Isma'il ya aka yi kwana biyu ban ganka ba baka kuma
kwana a gida ba?" Hajara ta tambaya cikin takaici bayan Isma'il ya
dawo gida daga tsarewar da aka yi masa a ofishin 'yan sanda.
"Wallahi Hajara wata tafiya muka yi muna zaton zamu iya
dawowa a ranar sai kuma aka samu akasi mota ta lalace mana а
hanya, ni kuma ba kudi a wajena ballantana ace na yi dawo wata."
Isma'il ya fada yana kokarin cire rigar dake jikinsa.
"Ya aka yi ka juya rigarka bai bai?"
"Saboda kar ta faci."
"Allah ya kyauta." Ta fada har zuci.
"Amin." Isma'il ya ce "Kina da ragowar abincine?" Ya
lambaya duk da ya san bai kawo ba. ya tabbatar zai samu tun da
Hajara ta fara wankau bai ta6a sayan abinci ba.
"Akwai." Ta fada gami da mikewa tsaye lokaci guda.
57
Ta miko masa abincin ya fara ci a gaggauce saboda irin
yunwar da ya sha a ofishin 'yan sanda, abin da Sumoli ta yi masa ba
zai taba mantawa ba, mata ba 'yan goyo bane, a lokacin da Sumoli
ta zo garin nan bata da kowa bata da komai shi ya zama kowanta ya
kuma zame mata komai amma yanzu dan ta ga bashi da komai ta
maidashi ba komai ba.
Isma'il ba zai taba mantawa da ranar da ta sauka ba, duk
karuwan Sabongari, hanata masauki suka yi, shi ne ya taimaka mata
ya kai ta DEMIKELA HOTEL ta dinga kwana cinta da shanta duk
shi ne amma a banza jiran kare a Rorafi ba rini ba matsa ba
sakamako ba lada.
ba.
"Kai Allah ya tsinewa bariki." Ya ſada a fili ba da saninsa
"Mc ka ce Isma'il?" Hajara ta tambaya tana kallonsa.
Ya dago kai ya kalleta, sai a lokacin ne ya san cewa a fili ya
fada ya dan yi murmushi gami da kara maimata abin da ya fada.
"Allah ya tsinewa bariki da 'yan bariki."
ba."
"Addu'a za ka yi Allah ya shiryesu ba ka rinka tsine musa
Hajara bata son zargi mummuna, amma yanzu kam lallai
tana zargin miji nata.
"Isma'il shekaran jiya mahaifiyata tazo, tun dadewa tana jin
surutun jama'a a gari na dangane da irin halin da muke ciki bata
taba yarda ba amma ranar da ta zo ta sameni kace-kace cikin
wankin kudi da nake yi mu na samun abinci, ta duba dakin nan ba
kaya ta yi min fada sosai ta kuma bukaci da mu tafi gida amma na
ki yarda daga baya dole ta tafi ta bar ni." Ta yi shiru tana maida
numfashi, sannan ta ci gaba.
"Isma'il sau da yawa na kan dan ji magana a tsakar gidan nan
duk da ba yadda nake ba to amma idan magana ta yi yawa zaka
samu akwai kamshin gaskiya a tattare da lamarin, Isma'il ina son ka
ina kaunarka don Allah ka rufa min asiri ka kame kanka'daga duk
abin da ka san za a zarge ka ko a yi da kai, Isma'il iyayena basa
sonka aureni ni na dage sai kai amma kai kuma kake neman ka bula
min kasa a idanu don Allah Isma'il kar ka ba ni kunya, ka sani
Isma'il yanzu fa duk wanda ya san tarihin aure na da kai ya zuba
mana ido ya ga yadda zamu karke amma kai kuma kamar naga
58
baka damu da haka ba, ka yi tunani tun lokacin da na fara aikatau
baka Kara kawo min abinci ba ka ta'allaka ga abinda nake samu ba
wai ina yi maka gori ba ne, a'a a matsayin ka na namiji ya kamata
ka rika kokari saboda gaba."
"Hajara ki sani karayar arziki na iya fadwa kan kowa babu
wanda ya fi karfin kaddara kuma in sha Allahu kwanan nan komai
zai warware ki kara hakuri."
"To Allah ya sa." Hajara ta ce a takaice.
Bariki ta gama shiga jikin Isma'il irin shigar da ko yana da
kudi ko bashi da komai sai ya yi giya dai ya tabbatar zai sha ko
kyauta ne, yana gama cin abinci ya zuba wanka ya sauya kaya ya
fice Sabongari ta diba.
***
a
lta kadai ta farfado daga gajeren suman da ta yi sannu
hankali ta tashi zaune ta duba ko ina na bangon dakin Honarabil
baya nan sai wasikar da mutuwa ta iyo musu ita da Honarabil kafin
ta karaso, ko da yake ba Honarabil ne kaďai meneminta ba suna da
dama.
ta
Tana son mikewa tsaye amma fargaba da tsoro suka hanata
kuma rasa abin da yake yi mata dadi, take ta ji ma ta tsani
rayuwa duk duniyar ta yi mata kunci.
Ta tabbatar idan mu tane suka sami labarin abin da take
dauke dashi gudunta za su yi, gashi dama ita ba kowa take gani
kansa da ganshi ba, mutanen da za su yi farin ciki sun ninka
wadanda za su yi bakin ciki ribi goma, yau kimanin shekarunta
biyar rabonta da kauyensu Magarya domin halartar iyayenta duk da
cewa ba nisa ke gareshi ba, sau uku yayyenta na zuwa tafiya daita
tun farkon fitowarta bariki amma tana sawa a yi musu rashin
mutunci daga karshe har kanin mahaifinta tasa aka doka a tsakiyar
Sabongari don kawai yazo tafiya da ita.
Auren dole ta yi gudu, gata ta zo Sabongari tana karuwanci
mijin da i yayenta suka zabar mata bata yadda dashi ba. amma a
yawon ta zubar din da take yi da wanda suka kai shi da wanda ba
su kai shi ba tana saurarensu, a takaice dai ta zama kazamar rijiya
wacce ake samata kowacce irin guga.
"Mutuwar yawa ka ka ce." Abin da ya fado a zuciyar Jamila
kala kenan lallai kam ba zata mutu ita kadai ba.
59
"Dole ne na sami abokin tafiya ko ta halin kaka." Ta facfi
haka a fili
Iludubar da shaidan ya yi mata kakagida ya sake karfafa
mata gwiwa duk da akwai wani abu da ya tokare mata makogoro.
Cikin dan Kankanin lokaci ta zabga wanka gami da
kyakkyawat shiga da kwalliya mai bayyana surar jiki karara a fili.
irin shigat da za ki ga karuwan da ke tsayawa a Lodge Road da
daddare sun yi.
Ta kalli kanta a cikin dogon mudubin dake like a bangaren
hagu na bangon dakin. Har yanzu kyakkyawan jikinta na nan
kamar yadda yake da sai dai ja da idanuwanta suka yi sakamakon
kukan takaici da bakin cikin da ta yi. Ta mika hannu don daukar
'var Karamar jakarta da take ajiye mukullin motarta a ciki. har
yanzu farar takardar nan inda take bata motsa ba. ta sa hannu ta dau
takardar ta Kara dubawa sannan ta yi tunanin ya kamata ta boyeta.
Karfe hudu daidai ta isa Abedi ko ina ta bi sai Kananan
karuwai ke mata kirarin da suka saba yi mata 'The Senior Class' ita
kuma tana daga musu hannu sai dai yau ba walwala da annashuwa
kamar kullum. ita kadai ta san abin da ke damunta in ka dauke
likita da Honarabil da yanzu bata san inda ya yi ba.
Zaune ta sami Isma'il kusa da wani mai snooker shi kadai
sigarin Benson a hannunsa na dama ya kusa zuketa. Jamila kala ta
dade da saninsa ta kuma san sunansa, sai dai magana bata taba
hadasu ba.
"Sannu da hutawa Isma'il" Ta ce dashi bayan ta yi fakin din
motarta a kusa da shi. Isma'il ya dago fuska ya dubeta, tunaninsa ya
bashi ko batan kai ta yi.
naku."
"Yauwa Jamila sannúnki da zuwa." Ya.ce yana murmushi
Ta sami waje kusa dashi ta zauna.
"Ya kake zaune kai kadai?"
"Ina dan hutawa ne kawai." Ya ce da ita.
"Ina Sumol dadironka?" Jamila ta bukata tana kallonsa
"Mun 6ata da dadewa."
"Duk Sabongarin nan ba dadiron da ya yi tsawon kamar
"Jamila mu yi mata maganar bana son tunanin wannan
maganar."
60
Ran Jamila kala ya yi fari saboda maganar da ta ji Isma'il ya
fada, abin da take son ta samu, ta tabbatar baza ta sha wata wahala
ba wajen sadashi da ajalinsa.
"Isma'il za ka yi mamaki idan na ce ma dama na dade ina son
ka a cikin rai na amma ganin irin kulluwar bakar alakar ku da
Sumoli ya sa ban taba fada ma ba."
Isma'il yayi mamakin maganar da ta fito daga bakin Jamila
kala kamar a mafarki, sai dai ya san ba wani mamaki idan ya yi
la'akari da maganar malaminsa dake bashi rubutun maganin farin
jini. Ya dade yana shan maganin farin jini a wajen wani malami
kuma sau da yawa malamin kan cewa.
"Isma'il wannan maganin zai yi maka amfani wata rana ko ba
daďe ko ba jima."
Yau ga amfaninsa ga Isma'il ya kama.
"Ya na ji ka yi shiru Isma'il?" Jamila ta bukata.
"Jamila nima na dade ina sonki, abinda ya hanani sanar da ke
sai na kanne ganin ba kya kula kowa sai masu akwai da matsayi."
Ya bata amsa sai dai abin da ya bawa Isma'il mamaki yana bata
amsar gabansa ya fadi kamar wanda aka sanar masa mutuwar
mahaifinsa.
"Ka manta da wannan ai so wani abu ne da ban."
Sun dauki lokaci mai tsawo suna hira, Isma'il farin ciki ya
lullußeshi saboda tunanin irin wulakancin da Sumoli ta yi masa
gashi yau ya sami wacce ta damata ta shanye, shi dama ya san
Allah ba azzalumin bawansa ba ne, sai dai abin da Isma'il bai sani
ba da ya kusanci Jamila kala a halin da take yanzu gwara ya je ya
lunkari gaban jirgin kasa ya markadeshi ya mutu lokaci guda shi ya
fi ye masa sauki sai dai rashin sani ya fi dare duhu.
"Isma'il ya kamata mu je MR BIGG's na New Road mu ci
abinci." Ta fada.
Isma'il ya ji gabansa ya fadi sanin cewa bashi da ko taro.
"Kar ka damu Isma'il akwai kudi a wajena." Ta ce dashi
kamar ta san tunanin da isma'il ya ke yi.
Gaban motar ya shiga ransa fari tas MR BIGG's ta diba, sun
share kamar awa daya a MR BIGG's, sun ci abinci irin na alfarma
rabon Isma'il da cin irin wannan abincin tun a wani fati da ya taba
halarta shekaru biyu baya da suka shude.
61
Daga nan kai tsaye suka wuce gidan Jamila kala don
shakatawa.
"Gaskiya gidan naki yana da kyau ya hadu." Isma'il ya се
yana murmushin jin dadi, ya ci abinci a iska zai kuma gwada
takalmi al banza.
kallo.
BLUE FILM ta fara samu su irin na kasar China suka fara
Hankalin Isma'il ya tashi kololuwar tashi ba abin da yake so
illa ya ganshi yana kwatanta abin da suke kallo;. A hankali Jamila
ta soma tube suturunta tsirara ta yi daga ita sai fant rigar nonon ma
kwabewa ta yi, Isma'il ya kalli Jamila sama da kasa har yanzu
nonuwanta a tsaye suke kamar na budurwa 'yar shekara sha hudu
ya kai kallonsa ga fant din dake saye jikinta mai dauke da
kyakkyawan hoton malam bude mana littafi shima hudubar shaidan
ya bi ya soma sullube kayan dake jikinsa.....
KASH
Masu karatu mu hadu a littafin MAZA SAI SANNU na biyu
don jin ci gaban labarin.
Taku
Binta Walee
(Mrs Auwalu Garba Danborno)
HANKALI DA SAMARI
"ai wane irin zance ne haka, nesa-nesa, "Waikamata ya yi ki matso kusa don ki dinga
fahimtar abinda nake cewa" Ya fada yana nazarin
kirjinta.
"Haba Musa wannan tsayuwar tamu ma ai ta yi
haka, ba ka gudun surutun mutane, ga kuma abokan mahaifina can suna hira."
"Ina ruwana da wasu abokan mahaifank, ke yanzu
fa duniya ta canza ba wani wanda ya isa ya sawa mutum
ido in dai yarinya tana sonsa ko ba kyà sona?"
62
"Ina sonka fiyc da yadda kakc zato." Ta fada tare
da yi masa kallon INA SON KA HAКА
"Abin da za a yi mu shiga daga soro don ya fi
sirri."
Hankali da samari na nan fitowa daga 'yar autan
marubuta
BEENTA A. WALEE 64 942941
SOMIN TABI DAGA
MAZA SAI SANNU 2
"Wai Hajara wacce irin rashin lafiya ce ke damunki haka? Ni
fa gaskiya ba zan iya zama dake kina irin wannan tarin ba."
"Haba Isma'il ai Allah ne yake dorawa mutum cuta shi kuma
yake yaye masa, ka yi hakuri tunda ina shan magani zan samu
sauki, in Allah ya yarda." Hajara ta bashi amsa tana hawaye.
tarin gashi kullum "Ba wani sauki yau watanki nawa kina sai
ramewa kike, in ba dama kawai ki tafi gidanku ni ba zan iya zama
dake ba haka, in kin sami sauki a dawo da ke, don ni lafiyarki na
aura.
"Don Allah Isma'il ka rufa min asiri. ka ji tausayina ka
taimakeni. Wayyo Allah! Na shiga uku...." Kuka mai karfi ya hana
Hajara Karashe maganar ta.
Yana nan fitowa daga 'yar autan marubuta
BINTA WALEE
63
SAKO DAGA AUWAL G. DANBORNO
Assalamu alaikum
Na dan ari fili a wannan littafi na mai dakina don in bawa
dimbin makarantan littattafaina hakurin rashin Titowar
KATANTANWA 2 da MUTUWAR TSAYE ci gaban SHARADI 2
da MUGUN ABOK1 2, Rubutun littafi abu ne mai wahala, don
Allah ku dan kara hakuri suna nan fitowa duka ba da dadewa ba.
Sannan mutanen da suka rubuto min wasika da kuma wanda
suka turo min sako ta email da wadanda suka bugo min waya.
musamman mutanen KADUNA, ZAMFARA. SOKOTO, NIGER.
BAUCIII, GOMBE, MAIDUGURI, YOBЕ, КЕВВІ kai har da
mutanen kasar NIJAR na gode kwarai da gaske, kuma ku dan kara
hakurin rashi fitowar littattafan nawa kamar yadda na fada a bawa.
sau tari nakan dan hada gudu da susar duwawu shi yasa.
NAKU HAR KULLUM
Auwalu Jibril Garba (Danborno)
SHIN MATAR WANE NE?
Sama da shekara biyu zuwa uku suna tare a matsayin mata da miji.
Almustapha da matarsa Lajja suna matukar so da kaunar junansu. kuma
suna alfahari da hakan, suna gamsuwa.
Abubuwa biyu ne kadai ke damunsu, ke sanyasu tunani, da shiga
ravuwarsu. Rashin haihuwa shi nc abu na farko da ya kc shiga ravuwarsu.
ya ke kasafta tunanin ma'auratan, sannan kuma sai wani firgitaccen hali
wanda ya danganci mamaki da gusar da hankali wanda matar ke fuskanta,
bangare guda kuma ko kadan mijin bai san wannan abu ba. bai san
dalilinsa ba, bai san yadda zai san shi ba bare wanda ya sani.
a
Kwatsam wata rana tsaka a cikin irc-iren ranakun babi-babi na
rayuwarsu, wani mutum wanda ya amsa suna ALHAJI HAMMAD уа
bayyana. ya bayyana ne tarc da tabbatarwa duniya cewar Lajja fa matarsa
cc!
Hujjoji kwarara da ya kawo su súka tabbatar da abin da va fada
haka ya ke. Bayan shige da fice, kutsawa da bullewa, hange da hangowa,
shaidu da dalilai, hujjoji gami da hukunci. aka karba matar daga hannun
Almustapha aka ba shi.
Shckara daya da faruwar wannan al'amari Allah ya vi wa Lajja
haihuwa. To a wannan lokaci ne kuma wasu hujjoji suka tabbatar da
kansu, kuma suka tabbatar wa duniya Lajja ba matar Alhaji Hammad ba
сс!
Nemi
KUSHEWAR BADI..... Daga Kabiru YusifAnka
64
2
DANBORNO BOOKSHOP
RUMFA MAI LAM A 145, LATIN MA) IA HADEVA
LAM NA HUDU, KUFAR GADAR YAM KUHA, KALUWAR E/GAR, KANо
080288811624
Sai Watoreие
Ayube isyako Danzaki
TSARIN BANGO:
ANKA-G RAPHICS FAGGE
08028182666
AUBINS PUBLISHERS, KURNAY 08028811674
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels