Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
abinda la kula dashi dai yawan shan ruwa da Hajara take yi. Ta raka Safiya har soron farko na kofar gida suka yi sallama suna yiwa juna murmushi, Hajara ta juyo domin komawa daki kamar yadda ta saba. "Sannunku." Hajara ta fada daidai lokacin da ta zo wucewa kusa da su Tasalla da sukc zazzaune a tsakar gida suna abin da suka saba yi yau da kullum, tsegumi. "Yauwa." Suka amsa baki daya. "Kai ni wallahi tausayin yarinyar nan nake ji Saude." Tasallah ta fada daidai lokacin da Hajara ta shige daki. "Ni kaina da na tsaneta amma yanzu tausayinta nake ji Kwarai." "Irin wannan salihar yarinyar a dauka a bawa dan iska gashi nan duk ya sai da mata da kayan dakinta gaba daya." "Ke ma kya fada Saude." "Kullum sai ramewa take yi kamar mai cutar kanjamau." "Ke Tasalla ba ki sani ba, ba ko da yaushe take dorå tukunya ba wani lokacin sau biyu take dora abinci wani lokacin sau daya." "Allah sarki wani lokacin sai dare ki ga shegen ya shigo da biredi da dan wani kunshin da ni kaina ba zan tantance ko na menene ba." "Ba zai wuce abincin fulani ba." "Ke bana son iskanci me ye kuma wani abincin mu fulani ban da dai gugar zana, a rinka yi ana jin kunyar ganin ido ban da cin fuska." da "Ai kowa ya san abincinku kosai ne." "Shegiya ba kya rabo da abin dariya." Yayin da su Saude suke hira a tsakar gida Hajara na daki yunwa da tunanin abubuwa da dama sun addabi zuciyarta rabonta ta sa wani abu a bakinta tun kokon safe sai kofin ruwa biyar da sha. Irin maganganun da mahaifanta suka sha gaya mata suka dinga shawagi a kwakwalwarta, suna dawowa garai-garai tamkar yanzu aka tadasu. ta "Wanne zabin kika yiwa kanko....?" Mahaifinta. "Ba wani tunanin da za ki sake yi....?" Gwaggo ta 'Yankaba "Hajara zabin da muka yi miki bai yi ba.....?" Mahailiyarta. 41 Sai dai maganar da ta fi tadawa Hajara hankali idan ta tunoshi."Hajara zan amince da duk wanda kika kawo za ki aura don gudun fadawa wani mawuyacin hali, sai dai abin da nake so dake nake kuma son tabbatar miki duk halin da kika shiga kar ki zargi kowa illa kan kí, ki sani cewa MAZA SAI SANNU...." Muryar mahaifinta. Da zata iya da ta je gidansu an bata abinci, sai dai gudun surutai shi zai hanata zuwa maganar yunwa kuwa ta fara sabawa da ita. "Yanzu menene abin yi? Ina kuma mafita?" Hajara ta jerowa kanta tambayoyi biyu a lokaci guda, kuma sune mafi yawan tambayoyin da take yiwa kanta a kowane lokaci idan bukatar hakan ta taso. "Wankau, aikatau." Sune abubuwan da suke fado mata a rai. ta dade tana ganin mata na yin wanki a biya su, sai dai bata san ko nawa ake biyan su bavita darta ga ana yin wanki, hakika irin wannan wankin shi ya dace da ta dinga yi ko surfe don asirinta dana masoyinta ya samu rufuwa. . Abin ku ma da Hajara taikasa ganewa shi ne ina mijinta ke kaiwa kudın kayayykinta da yake sayarwa? Kuma ina kayan shagonsa suke? Allah sarki abin da Hajara bata sani ba shi ne tuni kayanta da kayan shagonsa Sumoli da sauran 'yan matan da Isma'il yake bi tuni sun lashesu yanzu ka yi na yi yake yi. Hajara ta gama yanke shawara a zuciyarta, abin da ya rage mata bata san yadda zata yi a dinga kawo mata kayan wanki ba, ba abin da ya fi mata illa ta sami su Saude ta yi musu bayanin halin da take ciki. Har yanzu su biyu ne zaune a tsakar gidan suna ta hirarsu na Isegumi kamar yadda ta shiga daki ta bar su bayanta raka Safiya. Hajara ta tunkarosu zuciyarta cike da jin kunyar abin da zai fito daga bakinta. garesu. "Salamu alaikum." Hajara ta yi musu sallama yayin da ta isa "Wa alai kumassalamu.". Suka amsa mata baki daya. "Don Allah Saude wata tambaya na zo muku da ita." "La! Hajara fadi tambarki in dai mun sani to zamu baki amsa ko don yadda kike girmama mu." 42 "Dama....,irin....wan..." Sauran magana ya makale a fatar bakinta. "Dama me?" Ta sallah ta tambaya a zake don wannan shi ne karo na farko da Hajara ta taba zuwa musu da wata tambaya, gwara ma su kwanaki sun tambayeta yadda ake wankan janaba da yadda ake karatun niyyar wankan janaba, don Tasallah ta ce Ayatul Kursiyyu ake karantawa Saude kuwa ta ce Lakad Ja Akum da Lilafi ake karanta wa, sai Hajara-ta warware musu yadda abin yake. Hajara. "Irin wankin nan da matan aure ke yi nake..." "A gidan Delu mai manja ake yi." Saude ta tari numfashin "A'a ba haka nake nufi ba." "To me kike nufi Hajara?" Ta sallah ta tambaya. "Ina nufin idan zan rika samu ana kawo min zan yi." "Za ki yi me 'yar nan?" "Wankau idan zai samu." Hajara ta bata amsa. "Ke! Tasallah meye haka baki san uzirinta ba." "Gaskiya haka ne." Tasallah ta ce. "Zai samu?" "Eh zamu aika makota amma fa duk daya kwandala ake yinsa su za su baki sabulu da kudin ruwan wankin." "Ba komai in dai zan ssamu ku aika." Wannan shi ne mafarin sana'ar wankau da Hajara ta soma don rufawa mijinta asiri, cikin ikon Allah abu kamar wasa kullum wanki baya yanke mata, sai dai abin da ya yi gaba, saboda wanki mai kyau da take. ba kuma bata lokaci dan abin da ta samu ne ta kan sai musu abinci gami da kayan cefane wani lokacin har kudin kashewa take bawa Isma'il. ga zubin dashi da take yi duk sati sai dai sau da yawa ta kan ji kirjinta na yi mata ciwo amma don tsabar Karfin hali haka take daurewa gami da shan kwayoyin gajiya babu abin da take buri irin illa kayan dakinta da Isma'il ya sai da ta maida su. Saboda surutu ya fara vin yawa. *** "Ni fa gaskiya ya kamata mu san wacce muke ciki Isma'il." Sumoli ta fada gami da zukar sigari. "Ban fahimeeki ba?" Isma'il ya bukata yana kallonta. "Abin da nake nufi shi ne na gaji da wannan zaman." 43 "Ban gane kin gaji ha?" "Ka san neman kudi na fito." "Kina nufin duk abin da nake yi miki a baya kin manta? Shi ne yanzu kike wani magana." "Ai ba kyauta ka yi min ba na biyaka saboda haka ka kyaleni na sami kwastomomi sai na fada maka lokacin da zaka rika zuwa kana ziyartata." "Lallai baki da mutunci." "To ai mutuncin kenan, ko kana aure na ne?" Ko ba aurenki nake yiba uban wayc ya sai miki kayan nan da suke dakinki? Da har za ki ce za ki dinga kawo wasu kartin iska. wallahi duk wanda na gani a dakin nan sai na ci uwatar." "Ai wałlahi baka isa ba, ai ba zamanka nake ba." "Dan ubanki duk kayan shago na da kayan dakin matata an gindinki suka kare, baki isa yanzu don bani da komai ba ki watsar dani." "Dan uwarka an gaya maka bariki karya ce. ko da kake kashe min kudin idanu kawai kake zuba min. ba 'dare ba rana kullum kana kan ruwan cikina nawa ka biya kudin sadaki na?" "Ke! Ashe baki da mutunci? Uwar wa kike zagi?" "Kai uban wa kake zagi?" "Ubanki nake zagi." "Ni ma uwarka nake zagi ko an gaya maka..." Kafin ta rufe baki Isma'il ya katse mata hanzari da duka da hannunsa da kafa sai ka ce ya sami kwallo. Hadiza Ciyaledi tana daki tana shirya kudin adashi ta jiyo Karar ihun Sumoli. "Maganinta kenan shegiya." Hadiza ta fada a fili ita kadai. "Bari in je in raba don kar ayi mana kisa a gida 'yan sanda su zo su dame mu da jarabar kame ba san hawa ba bamu san sauka ba." Tana gama magana ta tashi da sauri, tana fitowa tsakar gida ta hadu da Rabi Kwandala a tsakar gidan. "Ke! Rabi zo mu je mu raba 'yan iskan can." 'Rabu da su Hadiza su kashe kansu don ubansu." "A'a yawa ne Rabi." 44 Suna zuwa suka tarar da Isma'il na ta dukan Sumoli kamar wanda aka aiko shi. "Kai Isma'il wai meye haka?" Hadiza Ciyaledi ta fada. "Kullum sai ka yi ta dukan 'yar mutane.' Rabi kwandala ma ta fada don kar ace bata yi magana ba. "Wallahi 'yar akuya ce yarinyar nan." Isma'il ya ce daidai lokacin da ya tsaya daga dukan dayake yi wa Sumoli. "Ubanka ne fan akuya." Ta mayar masa tana kuka. "Isma'il kasan mata sai hakuri." "Wanne irin hakuri Hadiza? Menene bana yiwa yarinyar nan amma kullum sai ta raina min wayo sai ka ce wani dan karamin yaro?" Isma'il ya ce yana huci tamkar kasa. "Abin da nake so da ku shi ne ku zauna lafiya, gaskiya in dai kuna yawan yi mana fada a gidan nan wallahi zan tasheku don kun san duk amanar gidan nan a hannuna take." "Ni yanzu ta kare tsakanina dashi, don ko uwata da ubana basa dukana balle wani Katon iska." "Na ji ba ni ba ke amma duk kayana da kika san na sai miki zan kwashe abina." su. "Ai wallahi karya kake uban kuturu ma ya yi kadan." "Haka kika ce?" "Kwarai ma kuwa." Sumoli ta tabbatar masa. "Ah! To lallai abin naku babba ne." Hadiza Ciyaledi ta ce da "Wallahi sai na kwashe duk kayana don ba ubanki ne ya ba ni kudin ba." "Wallahi baka isa ba ai ba kyauta ka sai min ba, mutuncina na sayar maka." "Haka kika ce, wallahi sai kin gwammace kida da karatu." Isma'il yana gama maganar kalin Sumoli ta bashi amsa tuni ya sa kai ya fice daga dakin, yana fitowa kofar gida ya tare fan асаба. A cikin gida kuma a dakin Sumoli su Hadiza Ciyaledi. "Dama mun gaya miki zaman dadiro kwaruwa za ki yi." Rabi ta ce da ita. "Gara ka rinka kama gaja ki wanki wannan ki wanki wancan. a rana daya sai na hada samari goma wani kwanan gida wani short 45 time, wani kuma na wankeshi na ware,a lokaci guda sai ki ganni da dubunnai." Hadiza Ciyaledi ta fada. "Kai ni abin da nake tsoro Hadiza wannan shegiyar cu tar da take hana mutane sakat." "Ba wata cuta duk wanda ki ka ganshi a duniya akwai hanyar ajalinsa." "Haka ne amma fa dubi yadda Tayi wa Tina sai da ta gama bushewa sannan ta mutu." "Ke da Allah bari tuna wanna tsautsayi ya hau ta." "Allah dai ya kare mu." In ji Rabi Kwandala sai yanzu ta tsoma musu baki a hirar ta su. Suna cikin hira suka ga Isma'il ya shigo tare da wani ramammen dan sanda babu ko sallama. "Ga ta nan yalla6ai." Isma'il ya nunawa dan sandan Sumoli. "Lallai Isma'il baka da mutunci ni ban dauko maka kwal ba sai kai zaka dauko min kwal." "Ke, waye kwal din?" Dan sandan ya daka mata tsawa cikin muryar da yake tunanin zata firgita Sumoli. "A, yallabai ka yi hakuri dan Allah." "To ta so mu je ofis dinmu amma ki fito da duk wani Electronics dake dakin nan akwai mota a waje." "Ban gane in fito da duk electronics ba yallabai?" "Ke! Za ki bi doka ko kuwa sai mun ci ubanki?" Dan Sandan va fada gami da zazzare idanuwansa dake makalae a lungu kamar na maciji. "Yallabai yi hakuri bari mu taimaka mata mu tayata diban kayan." Hadiza Ciyaledi ta ce da dan sandan. "Ke ce Ciyaledin gidan nan?" Dan sandan ya tambaya. "Eh. ni ce yallabai." Hadiza Ciyaledi ta ce dashi daidai lokacin da ta rungumo rediyo sidi da hannu biyu. Rediyo sidi, bidiyo sidi, talabishin da rikoda gami da fanka da dan Raramin dutsen guga tuni aka sa ma musu mazauni a cikin motar da Isma'il gami da Dan sandan suka zo da ita. Har an tada motar Isma'il ya tsaida su "Yallabai akwai katifa." Ya ce da dansandan. "Ba wurin sawa in mun je ma zo mu dauka." "Ke! Shi ge mu je." Dan sandan ya ce da Sumoli. 46 "To yallabai, Hadiza ku hawo mashin ku biyo mu." Suna zuwa ofishin jami'an tsaro suka sauke kayayyakin aka shiga dasu aka ajiyc a bakin kanta, daya bayan daya aka dorasu akan kantar daga ciki na farkon fari ne mai uku-uku wanda ke makale da mukamin insifecta, sai na kusa dashi baki dogo mai makale da jajayen igiyoyi guda uku, hakan ne zai tabbatar ma da cewa sajan ne, mai bi masa kuma shi ne fan sandan da ya gayyato Sumoli sun zama su biyar kenan in ka hada da wasu mata dake gefe. "Ina mai karar?" Dansandan dake makale da mukamin insifecta ya tambaya. "Gani yalla6ai." Isma'il ya amsa. "Me ye Karar ka?" Ya sake tambayarsa a karo na biyu. "Yallabai yau shekara kusan hudu muka yi da yarinvar nan duk dawainiyarta da kudin abincinta gami da kudin haya duk ni ne sannan duk wani kaya da kake gani a gabanka ni na saye su..." "A gaisheka jarumi." Sajan din dake gefe guda ya fada. Isma'il ya kalleshi sannan ya ci gaba. "Yallabai kasan halin yau, duk abin da na ke yi mata a banza ta dauke su, shi ne yau na zo take yi min gargadin kar na kara zuwa wajenta, ni kuma na ga ga kayana a dakinta gara na kwashe tun da ba zan kara zuwa ba ka ga kenan ba karę bin damo." "Ke kin ji duk abin da ya fada?" Insifetan ya tambayeta. "Kwarai yallabai na ji duk abin da ya fada." "Abin da ya fada gaskiya ne? Haka ne?" "Ba gaskiya ba ne yallabai." "To me ye gaskiyar maganar?" "Yallabai kamar yadda ya fada maka mun dade tare da shi muna zaman dadiro amma kullum daga duka sai zagin iyaye ni kuma naga zaman ya isheni haka na ce masa ya kamata mu hakurcewa juna. aure ma in ba zaman lafiya hakura ake yi ballantana zaman dadiro, zaman bariki, kuma yanzu ma katin ya kawo Karata wajenku sai da ya yi min dukan tsiya, da kyar aka kwace ni daga hannunsa da na san zai kawo kKarata da ban wanke jinın da ya zubar min ba." "Wa ye shaidar ki ta cewa ya dake ki?" 47 "Ga su nan yallaßai." Sumoli ta nuna Hadiza Ciyaledi da Rabi Kwandala. "Kai me ye hujjarka ta wannan kayan naka ne?" "Yallafai saboda ni na saye su." "Akwai takardunsu a wajenka?" "Ita na ke bawa ajiya." "Ke ina takardun da yake baki ajiya?" "Yallabai bai taba ba ni ajiyar takardu ba." "Wallahi yallabai na..." "Kai Malam yi mana shiru ba a tambayeka ba, ba ma son musu in kana son rantsuwa ne sai ka bari in an kai ku kotu tukunna.": "To yallabai na yi shiru." "Ke yarinya wannan kayayyakin da kika ce na ki ne kina da takardunsu da za su tabbatar mana na ki ne." "Kwarai kuwa yallafai." Sumoli ta tabbatar masa ta sa hannu a gaban rigar nononta na bangaren dama ta dauko wasu takardu a nannade. Dan sandan dake makale da mukamin Insifeta ya karfi takardun ya warware su, sai da ya bata kusan mintina biyar yana nazarinsu idan ya duba takardar ya kan dauki kaya daya bayan daya ya duba a haka har ya gama da su. Insifectan ya dago kai ya kallesu daya bayan daya dariya ta so ta dan kwace masa da ya kalli Isma'il, ya tabbatar Isma'il ne ya sayi kayan gashi jaraba da soyayyar karya tasa yasa sunan Sumoli a jikin takardun, sau da yawa sun sha yin kes irin wannan ba kuma yadda za su yi dole suke barin 'yanmatan su tafi da kayan da sun tabbatar na mijin ne ke dasu. "Wacece Sumoli Jos?" "Yallabai ni ce." Sumoli ta nuna kanta. "Ok, to a iya binciken mu ko in ce a yadda takardun nan suka nuna sun nuna kayan nan na Sumoli Jos ne, sai dai ba mu sani ba ko kaima kana da wasu takardun wanda za su nuna mana kayan naka ne?" "Haba yallabai ya za ka ce nata ne bayan....?" "Bayan me? Me yasa ka sa sunanta a takardun?" "Lokacin muna shiri." "Tunaninka bai taba baka za ku bata ba wata rana?" 48 "Eh ban taba kawowa a ka ba." "To kun bata sai ka dau kaddara tunda karambanin ka ya jawo maka." "Yallabai ina Kararsa akan dukan da ya yi min." Sumoli ta ce da dansandan. da "Ok, kai kun shaida ya dokcta?" 1Dansan ya tambaya, gami kallon bangaren da su Hadiza Ciyaledi suke tsaус. "Kwarai kuwa yallabai mu muka raba su ma." "To kai me yasa ka doketa?" "Zagi na ta yi." "Me yasa baka kawota kara ba?" "Gani na yi abin bai isa a kawo kara ba." "Ka dau doka a hannunka kenan ko?" "Ba haka ba ne." "To zagayo bayan kanta." "Haba yallabai ni na kawo kara fa." "An gaya ma duk wanda va kawo kara shi ne mai gaskiya? Ba lallai ne idan ka kasance mai kara ka kuma kasance mai gaskiya ba." "Wai ba za ka shigo ba ne?" Daya dan sandan da ba shi da igiya ya dakawa Isma'il tsawa, yana ji yana gani 'yan sandan suka tura keyarsa bayan kanta daya daga eikinsu ya dauko wani katon bakin littafi. "Wanne cajin za a rubuta masa?" Dansandan marar igiva ya tambayi Inspectan. "Criminal force and intimidation za ka caje shi." *** "Salamu alaikum." Mahaifiyar Hajara ta yi sallama. Sallamar da ta fargar da Hajara daga tulin wankin da take yi, dagowar da ta yi suka hada ido da mahaifiyar ta Hajiya Ladi, dogon wando na yarodan shekara biyar rike a hannun Hajara. A hankali ta maida wandon cikin ruwan kumfar, da ta san da zuwan mahaifiyarta da ranar ba zata tsiri yin wankin ba ko don gudun tonon sililin asirin halin da take ciki. "Hajara wankin waye wannan?" Mahaifiyarta ta tambayeta un kafin ta shiga dakin Hajara. 49 Shiru kawai ta yi ta kasa bata amsa har zuwa lokacin da ta shige dakin. Daga kofar daki mahaifiyarta ta tsaya ta karewa dakin kallo gabas da yamma kudu da arewa, alamun mamaki bayyane Karara a fuskarta. "Hajara ina kayan dakin?" Shiru Hajara ta kara yi gami da sunkuyar da kai kasa tana kallon ledar tsakar dakin jikinta a sanyaye ta shige dakin ta nemi waje da kanta bisa dandagaryar ledar dakin ta zauna. Yau ta tabbatar da jita-jitar da take ji, lallai ta zama gaskiya, dama sun tabbatar duk wanda ya saci zanin mahaukaciya dole ya rina, duk wanda ya sai rariya dole ya san zata zub da ruwa. "Hajara tambayarki nake yi kin ki yin magana?" Shiru ya kara biyo baya. "Hajara kayan wa kike wankewa?" Ta kara maimaita mata tambayar a karo na biyu. yi. "Wanki nake." Ta yi magana karo na farko. "Eh. dama na gani wanki kike, kayan waye haka tuli guda?" "Na jama'a ne." Ta ce a takaice. "Ban fahimceki ba?" "Na kudi ne." Magana karo na uku. "Kina nufin wankau kike yi?" Wannan karon Hajara bata yi magana ba gyada kai kawai ta "A'a wannan ba zai yiwu ba, wallahi bayan sai da kayanki da ya yi kuma sai kin yi aikatau za ki ci abinci don kin fi kowa hakuri. damo sarkin hakuri, ina ba zata sabu ba bindiga a ruwa." Har Hajiya Ladi ta dire Hajara bata sa baki ba, ta dai ci gaba da kallon ledar tsakar dakin. "Ki dubi fa yadda kika koma kamar waece ta haifi 'ya'ya goma. wannan ai sai yunwa ta nakasa ki ki mutu, ina wallahi tashi gaskiya mu tafi ba zan iya barinki a banza ya karasa kiba." Ta dan Kara yin shiru ta kalli Hajara wacce kwalla ta ciko mata idanu saboda tausayi, tasa gefen zaninta ta goge. "Dama ba rashin Kaunarki ne yake hanamu rashin yawan zuwan ba, idan aka yi wa yarinya aure yanzu idan mahaifiyarta la cika ziyarta gidanta sai a rika zunden zata kashe mata aure, tun da kika yi aure wannan shi ne zuwa na na hudu sau tari idan na shirya 50 zan zo babanki ne ke hanani zuwa, lokacin ma da ake ta yawan zuwa ana gaya min halin da cike ciki mahaifinki ne ya hanani zuwa, ya ce tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka amma yanzu ina zan iya kyaleki a cikin irin wannan halin haka, maza hado kayanki mu tafi in ya so in ba zai yiwu ba ko auren na a raba ina irin wannan wahala haka." "Mu je ina?" Hajara ta bukata a takaice. "Gida mana." Ta bata amsa a gajarce. "Hajiya Isma'il bai san da fitar ba." "Isma'il din uwaki, mutum da ke neman halaka ki har kina wani neman izinin sa, ni ba mahaifiyarki ba ce?" "Hajiya daidai da soro na biyu ba zan iya takawa ba ba tare da izinin Isma'il ba, ki yi hakuri Hajiya." "Ke! Dan ubanki ban son maganar banza kar ki maida ni wata karamar yarinya mana dole ki bi umarnina ki tashi mu tafi, in ke ba ki san ciwon kanki ba ai ni na tsugunna na haifeki na san zafinki." "Hajiya ki yafe ni ba zan iya fita bada saninsa ba." Hajara ta ce da ita hawaye na zubowa daga idanunta. Kallonta kawai Hajiya Ladi ta ci gaba da yi sai dai ta rasa abinda ke zuciyarta haushi, takaici, ko kuma tausayi ne, cikin uku ta san dai dole a sami guda daya a ciki. *** Jamila na daya daga cikin karuwan da suke ji da kansu a duniyar bariki ta Sabon gari, ba kasafai take kula Kananan masu hannu da shuni ba, duk lokacin da ka ganta da namiji to ka tabbatar ko shahararren mai kudi ko kuma rikakken dan siyasar dake kan kujera. Sau da dama 'yan bariki na yi mata kirari da kara da kiyashi daukar marar sani, reza yanki dan birni da bakauye, kaska rabi mai jini. JAMILA KALA kamar yadda 'yar birni ke kiranta. Ta kai kololuwar da duk yadda tunanin mai tunani bai kai ba, 'yan siyasa da masu gidan rana sun sha yin fada a kanta, akwai shekarar da har kisan kai aka yi saboda ita. Duk da almubazzarancin da take yi da kudi ta mallaki gidajen haya guda uku gami da 'yar karamar motar shiga. Haji biyu 51 ta halatta gami da umara uku duk a irin kudin da 'yan siyasa ke ware don bayin Allah na gari, duk shekara sukan warc wa Jamila kala nata tare da jama'arta 'yan kanzaginta. Zaune take a Burma road cikin wani dan matsakaicin gida da wani kansilan kauye ya kama mata haya inda a nan suke ragargazar kudin tsangsayar tasu wacce ko rijiyar kirki basu da ita a kauyensu. Tirkashi wata shari'ar sai a lahira kullum da yamma bata da wani wurin zuwa da ya wuce Abedi sau tari anan masu neman ta ke zuwa su sameta, ta karbi na karba ta wulakanta na wulakantawa, wani lokacin har tausayin mutum za ki ji idan Jamila ta yi masa wani wulakanci na musamman idan ki ka ga ya share kamar ba a yi masa komai bа. Daga Abedi dare na yi zata murza motarta sai Wazahed (WEATHER HEAD) wato lamba goma don halartar wani shahararren makadin Hausa Boda ko Dan Indo wani lokacin, nan ma na daya daga cikin matattararar 'yan asarar. Tun sati biyu da ya wuce Jamila kala take yawan tari gami da zazzabi mai zafi, ba abinda ya fi damun Jamila kala kamar yawan gudawar da take, ta sai magunguna na zazzabin, gudawar gami dà tarin amma a banza har yanzu shiru, wai Malam ya cі shirwa. "Jamila ki je Lamco Laboratory a auna jininki don a san irin maganin da ya kamata ki sha." Cewar Hauwa daya daga cikin 'yan koren kawayenta. "Ke Hauwa me kike nufi da auna jinina?" "Haba Hajiya Jamila, ba ina nufin komai ba sai dan kısan irin maganin da za ki sha kamar yadda na ce dake a baya." "In dan wannan ne me sai na wani je an auna jinina." "LIkitoci ke bada shawarar haka." "Ke bari in gaya miki duk wata karuwa da take ji da kanta a fadin garin nan ba wacce ta kai ni lafiya, kin ji ko?" "To Hajiya dan dai kin fadi haka ne, amma garin nan fadi gareshi." "Kina nufin karya nake yi kenan?" "A'a wace ni na isa." "Na dauka ko karyata ni kike son yi in ci uban uwarki ta Dutsen ma." 52 Sati dayá da bata shawarar da ta Ri bi ciwukan na ta uku suka ci gaba da addabarta, sai karuwa suke zazzabin gami da ciwon kai, da kanta ta ga cutar na neman kwantar da ita sai ta kudiri niyyar zuwa asibiti domin a auna jinin nata kamar yadda kawarta Hauwa ta bata shawara a satin da ya wuce, abin da Jamila ta tabbatarwa kanta ban da wannan cututtuka uku babu wata 6oyayyiyar cuta da take damunta, tana tabbatarwa da kanta haka duk lokacin data dauki mudubi ta duba kanta musamman ma idan bata ga wata alamar rama daga gareta ba sai ta kara gaskata hakan a zuciyarta. Kirar jikinta na nan kamar yadda take baka doguwa. fuskarta na dauke da tarkace mai ban sha'awa, kirjinta raye yake da malasan nonuwa masu daukar hankalin da kwantar da hankali yayin da duk ka yi ido biyu da su ko ba ka taba ba. Ba wannan ne kadai abin daukar hankali a jikin Jamila kala ba sai ta gifta ta gaban ka zaka sha kallo yadda duwawunta ke kadawa kamar ba like suke jikinta ba. duwawukan dake sa lafiyayyen namiji ya ji kamar an Isikare shi da allurar doki,, sau da yawa in Jamila ta gifta irin jarababbun mazajen nan da basa kai zuciya nesa, ma'ana masu kallon kurilla ina nufin 'yan amshin shaidan za ki ga suna kokarin kokawa da wandonsu yayin giftawar ta, wani sa'in kokawar ta yi nasara wani lokacin asiri ya tonu, sau da vawa idan Jamila ta lura da hakan ta kan yi dariyar keta gami da farin ciki an ganta an yaba. LAMCO LABORATORY na daya daga cikin kwararrun asibitocin awon jini a Kano suna da reshe ko ina a cikin fadin birni da kewaye. Zaune Jamila take a daya daga cikin tsabtatattun bencinan da Lamco Laboratory suka tanada don jiran sakamakon jinin wanda aka daukarwa duk wani mai boyayyiyar larura. Zuciyarta tas take bata wani tunani mummuna game da lafiyarta illa tunanin 6ata mata ciki da abincin wani dan Karamin Restaurant ya yi. hakan ne yasa ba kasafai Jamila kalar birni take son cin abinci a Raramin wajen cin abinci ba. Abin da ke bawa Jamila mamaki zuciyarta na dan bugawa kadan-kadan haka nan gabanta na dan faduwa jifa-jifa tun bayan gama daukar jininta. koda yake a tunanin Jamila kala hakan na da nasaba da huda fatarta da aka yi da allura. 53 Ta maida kallonta ga hannun da aka huda da allura doan daukar jininta, har

Chapter 4 of 5