dace
da tsarin rayuwar aurenta, hakika ta hakikance akan tabbatarwa
kanta da Isma'il ya shiga ranta ba ta jin zata iya auren waninsa
sabani shi, tunda take bata taba sabawa iyayenta ba amma wannan
karon kam sun yi yamma ne ita kuma ta yi gabas miji kam ita zata
aura ta zauna dashi ba su za su zauna mata da shi ba saboda haka a
nata tunanin kamata su kyaleta ta zaba ta darje da wanda ya yi mata
va kuma kwanta mąta a rai ta zauna dashi zaman soyayya, ba ta ce
Al-Amin ba mai son addini bane amma bai yi mata ba, baya kuma
daya daga cikin tsarin irin mijin da take son zama da shi. Isma'il
take so ko ya kasance mai son addini kö ya kasance marar damuwa
da addini ba wannan shiriya ce ta Ubangiji tunda dai Musulmi ne ai
shi kenan sai dai abin da Hajara bata sani ba shi ne ta tafka
mummunan kuskure mafi muni a rayuwarta ta duniya...
"Kin fahimci abin da nake gaya miki ko?" Hajiya Ladi ta
bukata ta hanyar katse mata dogon tunanin da ta tsunduma.
"Na fahimta amma Hajiya gaskiya....."
"Gaskiyta me?" Ta katse ta.
"Gaskiya Hajiya Isma'il neke so."
"Oh! Na shiga uku yanzu Hajara da bakinki kike gaya min
wannan maganar wai wani Isma'il kike so don tsabar rashin
kunya?"
"Hajiya babu yadda zan yi da zuciyata..."
"Zuciyar uwarki har wata zuciya ce da ke? Tashi ki bani
waje yarinyar banza yarinyar wofi marar kunya kawai." Hajiya
Ladi ta daka mata tsawa.
Hajara ta tashi jikinta a sanyaye ta doshi dakinta jikinta babu
Kwari idanuwanta cike da hawaye kafin ta Karasa kofar dakinta ta
ci tuntube da wata Karamar kujera sakamakon rashin gani
hankalinta ya gushe baya tare da ita, saboda tsantsar cikowar da
kwayoyin idanunta suka yi da kwalla.
28
Ta shiga dakinta ta zube kan katifarta zuciyarta cike da
kuncin irin maganganun da mahaifiyarta ta fada mata.
Hajara ta sake kafa sabon babin kuka.
A
"To dan nan Allah ya sa kada ka ba ni kunya don a shekarun
baya haka ka gano wata yarinya kamar gaske kace kana so zaka
aura mun je mun shirya magana daga baya ka zo ka zame ka bar
mu duk gidan sunan da muka je ko gidan biki sai an nunmani da
girma na da komai har a asibiti wasu mata ba su bar ni ba, kasan
mu mata da tsegumi." Mahaifiyar Isma'il ta ce dashi.
"Haba Hajiya kada ki damu wannan karon wallahi da gaske
nake yi sonta nake da aure ba wasa ba."
"To ba komai idan mahaifinka ya shigo zan shaida masa
halin da ake ciki." Ta fada da alamun farin ciki a tattare da
fuskarta, ta dade tana yiwa dan nata sha'awar yin aure ko don ta
sami jikoki kasancewar Isma'il kadai Allah ya bata, ya sha kawo
'yan mata kala-kala yana nuna mata da zummar zai auresu, amma
ita abin da bata sani ba hakan wata hanya ce ta yaudara da samarin
zamani suka shigo da ita mutum ya dau yarinya rimi-rimi har
gidansu wajen mahaifansa don ta amince dashi ta kuma saki jiki
dashi daga baya daga ya dan gwada takalminsa sai ya ari takalman
kare ya arce, wasu yaudarar tasu har ta kai su kai kudin zance ko
kayan na gani ina so don kawai su biya bukatarsu da ita, wani
lokacin har ciki sukan dura wa 'yan mata su gudu su bar su da
kudin NA GANI INA SO da ciki wata daya ko wata biyu, shi yasa
duk soyayya kada yarinya ta yarda da saurayi sai ta ji an shafa
musu fatiha.
"Hajiya zan fita na ji an soma kiran sallah."
"Oh! Isma'il yanzu dai ka soma tsayar da sallah akan lokaci."
"Kwarai kuwa Hajiya yanzu sallah bata wuce ni."
"In da da gaske kake fada wallahi za ka daina duk wani
shashanci da kake yi."
"Da gaske nake lajiya." Ya fada yana kokarin zaro wani
abu daga cikin aljihun gaban rigarsa.
"Gama carbi na na addu'a." Ya ce da ita yana nuna mata
wani koren carbin roba mai beza-beza.
29
"Lallai Isma'il ka soma samuwa, Allah ya dada shirya min
kai." Ta fada tana murmushi, yayin da shi kuma Isma'il ya mike ya
fice daga gidan yana dariyar cin nasarar karyar da ya shiryawa
mahaifiyarsa, shi dai ya san in bai manta ba rabonsa da sallah tun
wata Juma'a da sallah ta ritsa dasu a masallacin Juma'ar Rijiyar
Lemo da suke sallaha karfe daya a lokacin sun dawo daga ziyarar
wasu 'yan mata a makarantar kwana shima a lokacin gani ya yi
sauran abokansa sun sauka ya tuna shima fa Musulmi ne ya sauka
ya yi sallar ganin ido.au kusd shekard biyy kenan
Haka Isma'il ya karasa majalisa yana tunane-tunanen bara da
bana.
***
"Hajarar! Hajara!!" Alhaji Isa mahaifin Hajara ya kira
sunanta har sau biyu a hankali, tana zaune a gabansa bisa
shimfidediyar dardumar tsakar dakin. Hajiya Ladi kuma na zaune
bisa doguwar-kujerar da Alhaji Isa ke zaune akai, Hajara ta dago
kai a hankali ta kalli mahaifiyarta suka hada idanu Hajara ta mayar
da kanta da sauri ta sunkuyar sakamakon ganin irin sauyin yanayin
da fuskokin mahaifanta suka yi. Alhaji Isa ya ci gaba da bayaninsa.
"Hajara ki sani mune mahaifinki har abada babu sauyi komai
dadi ko wahala. Hajara ki sani kamar yadda Manzon Allah (SAW)
ya sanar damu, tun kina maniyyi a cikin mahaifiyarki, ki zama
gudan jini, kika zama gudan tsoka a haka a haka har Allah ya busa
miki rai kika rayu zuwa wata tara cur a cikin mahaifiyarki ita kadai
ta san irin wahalar da ta sha, sai dai dan abin da ni na gani zahiri, a
lokacin da take dauke da cikinki ne takan ji, babu abin da take
sha'awa ko take bukata illa ta shaki tsururin warin dake fitowa daga
masa, tun ina fada har na gaji na hakura wannan kenan. bayan
haihuwarki kuma ban da shayarwa da goyaki Allah ya yiyo ki mai
yawan rashin lafiya kullum tana kan hanyar asibiti dake ko wajen
masu bada maganin Hausa, ba zan taba mantawa ba saboda yawan
zirga-zirga kafarta har kumbura ta yi, akwai wani lokaci ma da ta
dawo daga Kurna wajen mai bada maganin gargajiya wani yaro ya
kadeta da keke ta karye a kafa sai da ta yi akalla wata daya tana
fama da jinya, haka aka yi ta shan wahaloli da dama dake har zuwa
lokacin da aka yaye ki. Makaranta babu irin wacce bamu saka ki ba
ta addini da ta boko har gashi Allah ya sa kin gama sakandiren ki.
30
ba ki taba neman wani abu a wajen mu kin rasa ba, saboda so da
kauna irin ta da'da mahaifa, ke ki sani Hajara ban yi niyyar fada
miki ba amma ya zama lallai, duk cikin 'ya'yana ba wanda nake
kauna kamar ki, ki sani Manzon Allah (SAW) ya koyar da mu duk
wani tsarin rayuwa, yadda zamu zauna, yadda zamu tashi, cin
abinci, sa riga, kwanciya, tashi daga kwanciya shiga bandaki, ke
komai da kika sani a rayuwa balle uwa da uba a kan harkar aure
wanda kowa kika gani ta wannan hanya ya samu. ki sani Hajara
Manzon Allah (SAW) ya gaya mana irin matan da zamu aura ko
irin namijin da mace ya kamata ta aura Manzon Allah (SAW) ya ce
akan auri mace don kyanta, danginta, kudinta ko na iyayenta ko
don iliminta wato ta bangaren addininta sai Manzon tsira ya ce na h
ore ku da mai addini. Ki sani Hajara haka yake ga 'ya mace
iyayenta su zabar mata mijin aure, Hajara ba zamu taba zabar miki
mijin da zamu yi dana-sani da shi ba kuma ki sani hakkin mu ne
zabar miki miji na gari Hajara mu muka haifeki muma kuma
kaunarki, wallahi-wallahi Hajara Al-Amin shi ne mijin da ya fi
dacewa da ke shi ne irin mijin da Manzon Allah (SAW) ya yi horo
da a aura idan kika bi umarnin Manzon Allah (SAW) ba zaki taba
tabewa ba, idan kika saba kuma za ki sha wahala, wallahi yaron da
kika zaba a matsayin wanda kike son ya aureki sam bai dace da
rayuwarki ba, ba kuma mijin aure ba ne."
gaba.
Ya yi dan shiru, gami da kallonta na dan lokaci kana ya ci
"ba zamu yi miki auren dole ba amma ki sani idan kika ce sai
wanda zuciyarki ta amince take so to zamu zuba idanu ne kawai ba
wai muna fatan wani abu ya faru ba ni abin da na tabbatar duk
wanda ya sabawa maganar iyayensa sai ya yi dana-sani...."
"Ya isa haka." Hajiya Ladi ta katseshi. Ganin yana daukar
zafi.
"Kin dai ji duk bayanin da mahaifinki ya yi? Saboda haka ki
e nan da kwana biyu ki yi tunani ki kuma auna da maaunin
unaninki akan maganganun da mahaifinki ya fada miki. kamar
yadda ya ce ba zamu yi miki auren dole ba sai dai ki sani son
zuciya....tashi ki je..." Hajiya Ladi ta umarceta.
Hajara ta tashi jikinta a sanyaye kafafunta sun yi mata nauyi
ankar ba za su iya daukar 'dakon gangar jikinta ba, kunya tsoro
31
gami da nauyin maganganun da mahaifinta ya yi mata na neman
kada ita a Kasa, haka ta lallaba ta bar dakin ta nufi dakin ta kirjinta
dankare da damuwa.
yi
Maganganun da mahaifinta ya fada mata gaskiya ce tsantsa,
maganganun suka rika shawagi a cikin kwakwalwar Hajara. Ta
hakikance gaskiya ce tsagoronta sai dai ita kam son Isma'il ya
Karfi a zuciyarta, Karfin da babu wata nasiha ko wa'azi da za su
ruguza shi, son Isma'il ya yi mata kanta a zuciya ya mamaye kaso
mafi tsoka da rinjaye a birnin zuciyarta, hakika ta san Al-Amin
mutum ne kamili nitsattse sai dai ba ya daga cikin tsarin mazajen da
take so..
"Salamu alaikum." Sallamar da wata kawarta Safiya ta yi ita
ta kaste mata tunaninta.
"Safiya." Ta kira sunanta ba tare da ta dago kai ta kalleta ba.
hakan shi ya tabbatarwa da Safiya cewa Hajara na cikin wani
Kuntataccen yanayi marar kyau.
"Hajara lafiya na ganki a cikin wannan irin hali?"
"Mhm ke dai bari kawai Safiya wallahi wannan matsalar ce
ta kara tasowa."
"To ke yanzu wanne zabi kika yiwa kanki?"
"Gaskiya Safiya na fi son Isma'il."
"Kina ganin zabin iyayen naki bai yi miki ba?"
"Ni ban ce bai yi min ba, amma dai na fi son Isma'il."
"Bai yi miki ba kenan?"
"Eh...to."
"Hajara ni ina ganin ko makaho iyayenki suka zabar miki
kawai sai ki hakura, don shi ne zabin da zai iya zama mafi alheri a
gareki."
"IHaka ne Safiya amma menene illar Isma'il?"
"Ni ban ce yana da illa ba, kin san MAZA SAI SANNU 1
amma kuma a gareki menene illar Al-Amin?"
"Bashi da wata illa sai dai bai yi min ba ne."
"Zuciyarki bata amince da shi ba kenan?"
"Eh, tabbas wannan haka yake." Hajara ta tabbatar mata.
"Hajara Hausawa sun ce son zuciya facin zuciya."
32
"Ba lallai ne duk abin da malam Bahaushe ya furta ya zama
gaskiya." Hajara ta ce da ita ranta a bace domin ta soma kosawa da
hirar da Safiya ke yi mata.
"Sau dayawa ya kan zamo hakan."
"Son da lsma'il yake yi min babu alamun samun matsala a
tattare da ita."
"Haka kika ce?" Saliya ta bukata.
"Eh, haka na ce ko kema kina daga cikin masu yi min
hassada ne gami da mugun fata?"
ne?"
"A'a Allah ya baki hakuri, yaushe zamu dubo rizol din mu
Safiya ta sauya akalar darasin hirar sakamakon hangowa da
ta yi al'amarin na neman ya 6acі.
"Kin sami labarin fitowarsa ne?"
"Eh na sami labari shi ne ma dalilin da ya sa na zo domin ina
tunanin ko kc ba ki ji labarin ba ne."
"Me zai hana mu je ranar Litinin."
"To Allah ya kai mu."
Haka suka ci gaba da hirarsu har iokacin tafiyar Safiya,
Hajara ta rakota har kofar gida sannan suka yi sallama suka rabu a
kan zasu hadu ranar litinin.
***
Kwana biyu ya zamowa Hajara kamar awanni biyu, yau ne
cikon ranar ta biyu da iyayenta suka debar mata, jira kawai take
dare ya yi mahaifanta su kirata domin jin sakamako daga bakinta,
sai dai har yanzu zuciyarta tana nan kafe kan Isma'il tunaninta.
hankalinta, jin ta da ganinta gaba daya sun karkata ne kan Isma'il ta
riga ta bashi ragamar mulkin zuciyarta. ta yi kokarin ta dan yi
tunanin Al-Amin ko da na dakika daya ne, amma abin ya faskara
zuciyarta ta vi zurfi da tunani gami da begen Isma'il, zuciyarta ta ci
gaba da ingizata kan bijirewa umarnin iyayenta.
Ba kamar yadda ya saba dawowa ba yau karfe uku na rana a
gida ta yi masa ba mamaki hakan nada nasaba da cikar kwanaki
biyun daidai da suke debarwa Hajara.
A daddafe ta yi sallar La'asar saboda zulumi da tunanin irin
amsar da zata bawa mahaifanta ita dai ta tabbatarwa kanta ko za a
dakata a turmin karfe sai Isma'il.
33
"Hajara wai ki zo.' Karamin Kaninta Sani ya ſada bayan bankada labulen dakinta da ya yi.
"In ji wa?" Hajara ta tambayeshi.
"In ji baba, Hajiya ma tana dakinsa tare da Gwaggo ta 'Yan Kaba."
Das!! Gaban Hajara ya buga da karfi Gwaggo ta 'Yankaba
wata masifaffiyar yar Babansu ce bata wasa ko wargi koda da
jikanta ne, ga saurin fushi gami da rashin hakuri, maganar da bata kai ta kawo ba yanzu saj ta maidata babba.
Haka Hajara ta lallaba ta je kiran da mahaifanta suke mata, ta yi sallama a kofar dakin kafin ta daga labule. "Shigo." Hajiya Ladi ta ce da ita muryarta ciki-ciki. Hajara ta shigo ta sami wuri gefe guda ta takure tamkar wata mai jin sanyi.
Dakin ya yi shiru na tsawon dakiku, idon Gwaggo la 'Yankaba kafe a kan Hajara.
"Hajara" Gwaggo ta 'Yankaba ta katse shirun ta hanyar kiran
sunan Hajara sannan ta ci gaba..
"Wanne zabi kika yiwa kanki?"
Hajara ta yi niyar furta wani abu haka kawai sai ta ji bakinta
ya daure tamkar wata wacce aka yiwa asiri. Shiru kawai ta yi gami da sunkuyar da kai ta kurawa ledar tsakar dakin ido.
"Ba ki ji tambayar da aka yi miki ba ne?" Mahaifiyar ta ce take tambayarta.
"Na ji." Ta amsa da kyar.
"Ku kyaleni da fitsararriya, wanne zabi kika yiwa kanki?" Gwaggo ta kara tambayarta a karo na biyu.
"Isma'il." Bata san lokacin da bakinta ya subuce wajen furta
sunan Isma'il ba.
"Babu wani tunani da za ki kara yi Hajara?" Mahaifinta ya tambaya muryarsa a sanyaye. Hajara ta yi shiru zuciyarta na bugawa kamar zata fasa kirjinta ta fito waje.
"Hajara zabin da muka yi miki bai yi ba?" Mahaifin ta ya kara tambayarta yana kallonta muryarsa Kasa-kasa kamar mai
shirin yin kuka. Abin tausayi ga duk mai tausayi, ita kanta Hajara
sai da ta tausaya masa, sai dai son Isma'il ya fafari komai daga zuciyarta.
34
"Hajara." Ya ci gaba "Zan amince da duk wanda kika k
min a matsayin mijin da zaki aura don gudun fadawar ki wani
mawuyacin hali, sai dai abu guda da nake son tabbatar miki shi ne
duk halin da kika tsinci kanki a dangane da zaman rayuwar aurenku
da Isma'il kar ki zargi kowa ki zargi kanki, ina fata kin fahimta?"
Shiru ta yi don bata tunanin zata iya bawa mahaifin nata
amsa.
CI GABА
21 JANUARY, 2004
A
guje dan acaba ya shiga dashi Abedi ta Sabon gari, đan
Lacabar ya dan taka birki a wata 'yar kwana sakamakon
wata karuwa da ya hango ta tsallako titi kanta babu dankwali cikin
rashin zato.
"Banza sokuwa ki rika kula.' Dan acaбar ya сe.
"Ubanka ne soko ta maida masa da karfi ganin idan ta fada a
hankali ba zai ji ba, saboda ya dan gotata kadan, ya dan rage wuta
sabowa wani rami dake gabansa, ya kaucewa ramin daidai lokacin
ne ya isa No 32 NIAGARA ya caki burki da karfi kamar matukin
da ya ci karo da jirgin kasa a gabansa, Isma'il ya sauka daga kan
mashin din sanna ya mikawa dan acabar kudinsa.
Kai tsaye ya shige gidan kamar kullum.
Hadiza Ciyaledi ya tarar a tsakar gida Gambo Dan Daudu na
mata tsifar kai, ta yi daurin kirji zanin kuma tattare yake har
matsematsinta hakan shi ne zai baka damar hango sa6ar-sabar din
cinyoyinta.
"Barka da zuwa Sama'ilan Sumoli." Gambo Dan Daudu ya
fada cikin wata lalatacciyar murya.
"Yauwa Gambo sannu da aiki." Isma'il ya mayar masa da
martani yayin da yake kokarin tsallake mikakkun cinyoyin Hadiza
Ciyaledi, ta bishi da harara shi kuwa gogan naki bai ma san tana yi
ba. ya bankada labulen dakin Sumoli ba tare da ya yi sallama ba,
hayakin taba sigari ya soma yiwa hancinsa maraba.
"Waye?" Sumoli ta tambaya bata ganeshi ba, saboda hayakin
da ya rufe bakin kofar dakin a kokarinsa na neman hanyar ficewa
waje ya baje ya bi iska.
"Ni ne." Isma'il ya ce yayin da ya shigo ciki.
35
yau?
"Dama tun dazu nake jin yunwa, me ya hanaka zuwa da wuri
"Naje unguwa ne."
"Gaskiya ka dinga kawo min kudin abinci na akan kari."
"In na samu ko."
"Ko ka samu ko ba ka samu ba dole ne ka kawo tunda
zamanka nake yi."
"To na ji ni dadi na dake duk san da aka zo wajenki sai kin
so ki fadawa mutum da fitina."
"Fitina ai kai ka jawo shi."
"To ta wuce tashi ki sayo mana abincin."
"A ina?"
"A wajen Marka Dan Daudu."
"Kai ni na gaji da cin abincin wannan shegen, gwara na sayo
a wajen Esta."
"Ko ma wajen waye ki je ki sayo." Isma'il ya ce yayin da
yake zira hannu a aljihunsa domin ya dauko kudi,
"Ka san fa satin da ya wuce idan baka manta ba na karbi
bashin leshi." Sumoli ta ce dashi ganin irin kudin da Isma'il ya fito
da shi masu yawa daga cikin aljihunsa.
"Ke bana son iskanci a wajen wa kika karbi leshin?"
"Haba Isma'il da gaske nake fa ba da wasa ba a wajen Dan
Sakkwato na karбa."
ne."
"Nawa ne kudin leshin?"
"Dubu uku da dari biyar kuma na ankon galar Fati 'yar Gwal
"A ina Fatin zata yi GALA?"
"A Lale Sinima, su Ciyaledi tuni suka sayi nasu ni kadai ce
na rage a gidan nan ban biya ba."
Kai tsayc Isma'il ya kirga dubu uku da dari biyar daga cikin
kudin firjin Hajara ya ba wa Sumoli sannan kuma ya kara mata dari
biyar a sayo musu abinci.
本本
"Kai gaskiya Tasallah yaron nan na zaluntar yarinyar nan ki
duba fa har yanzu bai dawo ba."
"Haba Larai mu mazajen mu sun shigo ne?
36
"Ai gara mu manya ne suna zaune a kofar gida, ko banzа
muna jin muryoyinsu."
"Larai kina da gaskiya." A cewar Saude sannan ta ci gaba
"Ki duba ki gani irin biyayyar da take masa amma in ya fita baya
son dawowa wani lokacin ma sai an kulle gida ya zo ya damemu da
bugawa kamar wani 6arawo."
"Wai ku idan ya zo zai gifta ba kwa jin kaurin taba sigari a
jikinsa." "Ni ina jin wari
ba." amma ban san ko na menene
"Oh! Ni Tasalla ashe shi yasa lokacin da nake da ciki in ya
gifta sai na yi hararwa."
Gaba daya suka bushe da dariyar munafurci.
"Daga ganinsa dan ba..."
"Mhm' Gyaran muryar da suka jiyo shi ya katse hirar da
Tasalla ta dauko.
"Ga gogan naki nan Saude don shi ne mai ırin wannan
gyaran muryar."
Saude ta mike cikin gaggawa, ta dauki yaronta dake kwance
bisa yagaggen tsohon zani.
"Sai da safen ku." Saude ta ce da su.
"Tó Allah ya tashe mu lafiya." Suka amsa mata a lokaci guda
tare tamkar hadin baki.
"Kai wannan mijin nata da jarabar tsiya yake yana riga kowa
shigowa gida." Larai ta ce daidai lokacin da Saude ta shige daki.
"Kai! Larai baki da dama."
"Allah Tasallah. ba kya ganin kwanika take yi."
"Gaskiya duk shekara sai ta haihu sai ka ce tinkiya."
"Shekaran jiya wajen Karfe dayan dare fitsari ya kamani na
zo wucewa ta kofar dakinta sai na ji kara har na firgita zan koma
da baya a tsorace sai daga baya na fuskanci ashe gadonta ne ke
Karar kin san gadon karfe da isabar tonon silili sai ka ce gyare!"
"Ni ma da irinsa aka kawo ni gidan miji amma daga baya a
hankali na sake nawa na yanzu."
"Ina Saude zata iya zare dubu goma ta sayi gado a wannan
shegen son kudin nata na tsiya."
"Gaskıya fa wannan haka yake."
37
A daidai lokacin da suke hirar Hajara kuma na daki zaune
zugum tunanin abubuwa da dama sun cika sun addabi zuciyarta,
tun bayan wata biyu da daura aurenta da Isma'il baya dawowa gida
da wuri, kullum idan ya shigo a makare da hujjar da yake zuwa
mata na musamman a matsayin madogararsa, sau tari idan ya dawo
ta kan dan ji tsami-tsami a jikinsa gami da kamshin alawar tomtom, koda yake ba mamaki alewar ta zamar masa tamkar goro ko
al'ada in bai sha ba ba zai ji dadi ba, to amma abinda ke bawa
Hajara mamaki shi ne tsami-tsamin fa na meye? Menene dalilin
samuwarsa? Wannan tambayar ita ta shigewa Hajara lungu sai dai
yau kam ta kudiri niyyar tambayar Isma'il dalilin daren da yake
kaiwa da tsami-tsamin da take ji a jikinsa.
Ta kalli agogon dake makale a bangon dakin daga bangaren
gabas maso kudu na dakin. Tsinken agogon dake nuna awanni ya
tsaya akan sha biyu yayin da tsinken dake nuna mintuna ya tsaya
daidai saitin lamba uku, hakan ne ya tabbatar mata da karfe sha
biyu da kwata daidai.
Lokacin da tsinken dake nuna awanni ya kusa zuwa kan daya
dan uwan nasa dake nuna mintuna saitin sha daya ta ji bugun kofar
gida,. Kamar kullum yau ma ta tashi da sauri ta nufi tsakar gida don
zuwa taryar makararren mai gidan nata. Hajara ta bude masa kofa.
"Dalin Hajara." Isma'il ya fada gami da yake hakora isamitsamin data saba ji yau da kullum gami da kamshin tom-tom din da
ya zame masa al'ada ya biyo bayan abin da Isma'il ya kira da
murmushi.
"Isma'il." Hajara ta kira sunansa daidai lokacin da ya fada
kan kujera bayan ya shigo daki.
"Yes Hajara kina da magana ne?"
"Ina da magana Isma'il." Ta ce dashi.
"Fadi maganarki in ji."
"Wai Isma'il ina kake zuwa ka ke kaiwa dare haka?"
"Hajara manya wajen tafsiri nake zuwa."
"Wanne irin tafsiri ne ake kawai dare haka?"
"A cikin gari ne."
"Me yasa baka zuwa dani, sannan baka kuma taba karar dani
abu daya daga cikin abubuwan da kake koyowa daga can ba."
"Ai mata ba sa zuwa."
38
از
"Me yasa baka sanar dani?"
"Babu wadataccen lokacin yin hakan."
Hajara ta dan yi shiru ta zuba masa idanu tana kallonsa na
dan wani lokaci, ta lura duk maganar da suke fitowa daga bakinsa
babu alamun gaskiya a tattare da shi sannan kuma yana magana
idanuwansa a rufe, wani sa'in kuma yan yin maganar ne kamar dan
koyo sanyi-sanyi ko barci-barci yake ji ne? Tambayar da Hajara ta
yi wa kanta kenan a zuciyarta.
"Me yasa ba zaka sani a makaranta ba tunda baka da
wadataccen lokacin koya min?"
"Makarantar matan aure?" Isma'il ya tambaya.
"Abin da nake nufi kenan." Hajara ta tabbatar masa.
"Ina! Allah ya sauwake haramun ne.'
"Lallai Isma'il rikakken jahiline kai." Abin da Hajara ta so ta
fada kenan amma sai ta hadiye kayanta.
"Oh! Allah sarki Al-Amin." Hajara ta ambaci sunan Al-Amin
amma a zuciyarta.
"Isma'il kullum idan ka dawo na kan ji dan tsami-tsami gami
da kamshin tom-tom a jikinka wanda na lura hakan ya zame maka
tamkar al'ada me ya ke kawo hakan?"
Tambayar ta girgiza Isma'il yadda Hajara ta lura lokacin ne
ya bude idanunsa suka firfito.
"Eh! Me kika ce?" Ya bukata a firgice.
"Sau da yawa in ka dawo na kan ji tsami-tsamin gami da
kamshin alawar tom-tom a jikinka."
Isma'il ya kama rigarsa a firgice ya sansana, inda akwai
abinda Isma'il ya tsana a rayuwarsa bai wuce Hajara ta gane irin
halin da yake ciki na zamantakewar rayuwar duniya ba, ko banza
zata iya hana shi sai da kayanta idan har ta gane abubuwan da yake
yi da kudin kayayyakinta idan ya karba ya sayar.
Ya dago da kansa ya kallo Hajara, har yanzu idanuwanta
kafe suke a kansa, shiru kawai ya yi yana kallonta a mamakince.
"Ba ka bani amsa ba har yanzu." Hajara ta ce dashi ganin irin
yanayin da ya shiga irin na mara sa gaskiya.
"Iye na'am." Isma'il ya furta a rude.
"Na ce baka ban amsa ba." Ta maimaita masa.
39
Hajara wani maganin basir nake sha mai daci da tsami,
dacinsa ne yake sa nake shan tom-tom a duk lokacin da na sha kin
san basir mugun ciwo ne yanzu sai ya kai mutum lahira."
"Allah ya sauwake." Hajara ta fada har zuci.
"Amin masoyiyata." Isma'il ya ce yana mai bayyanar da
murmushin samun nasarar bata gano shi ba, kai tsaye ya tashi ya
rungume ta. Tsamin ya kara bugar hancin ta, duk da bata so ba
vadda zata yi yau da kullum tafi karfin wasa.
21 DECEMBER, 2004
H
ausawa sun ce zara bata barin dami, a hankali dauki
daidai kayan dakin Hajara suka kare, in ka dauke gado
da katifarta sai sif, dibaida ba komai a dakin hatta tibi da bidiyonta
Isma'il ya hada ya kadar dasu tun 'yan uwa da abokan arziki na
kaiwa mahaifan Hajara labari gami da suka har suka gaji ganin ba
wani mataki da suka dauka.
Shekara uku baya idan kasan Hajara in ka ganta a halin da
take ciki yanzu sai ka rantse ba ita ba ce, irin ramewar da ta yi zai
iya tuna ma da irin mutanen da ake nunawa a CNN yayin da yaki
ya ci kasar su.
cewa.
A yanzu da kawarta ta kawo mata ziyara suke hira take
"Hajara gaskiya ramar da kike yi ta isa haka, wai me ke
damunki? Ko ba ki da lafiya ne?"
"Lafiyata kalau Safiya me kika gani?"
"Kullum ramar ci gaba take yi."
"Amma ya kamata ki je asibiti a dubaki domin a halin da
kike cikin na ramewa ba lallai ne ki san me ke damunki ba."
"Haba Safiya wallahi lafiyata kalau na ce miki."
"Hajara ya naga kayan dakinki duk sun kare babu?"
"Mhm Safiya wasu nake son sakewa."
"Allah ya buda."
"Amin Safiya."
Abin da ya daurewa Safiya kai tun karfe goma na safe ta je
gidan har zuwa karfe biyu bata ga Hajara ta dora girki ba, haka
suka gama hirarsu da yake ba abinci ne ya kaita ba bata damu da ta
tambyi dalilin rashin yin girkin ba har lokacin da zata tafi suka yi
40
sallama