gidan, hasken dake tsakar gidan ne ya
haskawa mahaifin Hajara littattafan dake rike a hannun Hajara. "Wadanne littattafai ne rike a hannunki?"
"Bulugul Maram da Riyadussalihina Al-Amin ne ya kawo
min su yanzun nan."
Mahaifin nata ya karbi littattafan daga hannunta ya duba na
tsawon dakiku kadan ya yi nazarinsu sannan ya mika mata, tasa
hannu biyu ta karba ta hanyar risinawa cikin halin girmamawa kana
ta wuce dakinta.
"Kai Hajiya Allah ya yi yaron nan da son addini gashi da
girmama mutanc." Alhaji ya ce bayan ya shiga daki. "Alhaji ai ni inda na sallamawa yaron kafin ya fara zuwa
zance wajen 'yar nan sai da ya nemi izinin mu tukunna."
"Ai dama haka yake a addinince."
"Lokacin da ya fara zuwa sai da wasu Kawayena suka zo min
da tsegumin wai dan Izala ne kada na yarda na amince 'yata ta aureshi."
"To don dan Izala ne sai me?"
"Ni ma dai hakan na ce dasu."
"Kin san duk mutumin da bai zabawa 'yarsa miji na gari ba
sai sun tsaya gaban Ubangiji dadyar tasa a ranar sakamako." Alhaji
ya ce da Hajiya.
"Kwarai ma kuwa don idan bai zabar mata miji na gari ba ya
riga ya cutar da ita kenan har abada."
"Hajiya ni zan fita muna da taron iyayen yara."
"To Alhaji sai ka dawo. A dawo lafiya."
"Allah ya sa" Ya sa kai ya fice.
***
Alhaji Isa mahaifin Hajara yana da hali daidai gwargwado.
halin da ba zaka sashi a layin masu hannu da shuni ba, haka nan ya
kuma li karfin a jera shi a sahun talakawa, idan mutum ya kasance
a wannan rukunin yanayin da Alhaji Isa yake ciki Hausawa kan
kira irinsu da mai rufin asiri, Allah ya yi shi mai hakuri gami da
juriya da saukin kai haka kuma Allah ya ba shi mata mai saukin kai
kamar sa gata ita ma da hakuri hakan ne yasa zamansu na shekaru
16
sama da ashirin da 'yan kai babu wanda ya taba jin kansu bare
shiga tsakaninsu.
a
Allah ya albarkace su da haihuwar 'ya'ya biyar uku maza
biyu mata Ali shi ne babba sai Hajara dake bi masa baya ita kuma
Sadiya ke biye da Sani shi ne na hudu sai 'yar autarsu Sakina.
Kamar iyayensu haka 'ya'yan suke sakamakon tasowa da suka yi da
kyakkyawar tarbiyya da suka samu daga wajen iyayen nasu,
kawunan yaran gidan ya yi matukar haduwa akwai jituwa mai karti
tsakaninsu wanda hakan ya sa ba ajin kansu suma. Musamman da
yake ciki daya suke.
a
RANAR JUMA'A 24 DECEMBER 2001
Ranar IHajara wuni ta yi tana tunanin Isma'il wanda ita kanta
ta rasa dalilin kasancewar hakan a zuciyarta, abu daya zata iya
tabbatar wa kanta shi ne tana Allah-Allah Isma'il ya zo domin ta ji
abin da zai zo mata da shi, sai kuma irin yadda ta ji lafazin bakinsa
ya burgeta, a ranar bata iya karanta komai ba daga cikin kowanne
irin littafi, in ka dauke littafi mai tsarki data karanta shima tun da
safe ne. wuni ta yi tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ba
kazar-kazar bata wani kuzari a tare da ita babu hirar kirki da
mutanen, akan kirata kamar sau uku ba tare da ta amsa ba wani
sa'in ma sai an dan tabata kafin ta gane ana kiranta, ko da yake ta
kare kanta a wajen mahaifiyarta da cewa bata da lafiya ne jin hakan
mahaifiyarta ta tashi Sani ta ce ya sayo mata magani a kemis, karya
ta farko kenan a tsawon rayuwarta da ta yiwa mahaifiyarta akan
sauravi.
Ta kan duba agogon dake makale a bangon dakinta a
kowane rabin sa'a, da kyar Azahar ta shiga La'asar ma haka yayin
da a daddafe magariba ta rinka yi mata sanda a nata ganin lokacin
baya tafiya yadda take bukata. Bayan ta idar da sallar magariba ne
ta yi sauri ta shirya bata san dalili ba, atamfar da ta fi burgeta cikin
kayanta wacce kuma ta fi tsada ta sanya a ranar, ta dade rabonta da
ta sanya atamfar. bata 6ata wani lokaci wajen kwalliya ba.
"Salamu alaikum." Ta ji sallamar wani yaro a tsakar gida.
kafin a amsawa yaron sallamar da ya yi ta yi zumbur ta mike da
sauri cikin gaggawa hijabin ta take kokarin sanyawa.
"Wai ana allama da Ali." Yaron ya fada.
17
Hajara dake tsaye a tsakar dakinta tana kokarin sanya
hijabinta ta ji wani irin abu ya tsaya mata a kahon zuci, take ta ji
makogoronta ya bushe kamar ta hadiyi kwatlon yazawa.
"Wannan yaron ko kuskure ya yi? Kai yaran yanzu ba su da
nutsuwa yanzu haka ma ni aka ce ya kirawo ya zo ya ce Ali
maimakon ya сe Hajara." Hajara ta ce a zuciyarta hijabin da bai
sawu ba kenan sai dai har yanzu yana rike a hannunta ranta a bace
zaka gane hakan ne idan ka yi nazarin yanayin da fuskarta take
dauke da alamun 6acin rai karara.
"Ali baya nan amma ka duba waje ko masallaci ba mamaki
ka sameshi." Muryar Hajiya Ladi ce mahaifiyar Hajara ta ke bawa
yaron umarni daga tsakar gida. Hajara daga dakinta ta sake samun
waje ta zauna sai dai abin dake bata mamaki wai menene na yin
hanzari? Me kuma ya sa ta 6acin rai ko Al-Amin ne suka yi
alkawari dashi in baj zo ba bata damuwa haka, to shin yanzu
menene ke shirin faruwa a gareta ne? Mutumin da ko tsayawar
kirki ba su yi dashi ba ta dinga damun kanta a banza.
"Salamu alaikum" Hajara ta sake jin muryar wani yaron
daban a tsakar gida ga mamakin Hajara tun kafin a amsa sallamar
sai ta mike cikin gaggawa fuskarta cike da murmushi.
"Yanzu dai na san shi ne ba musu." Ta ce a ranta. Sannan ta
sake surar hijabinta cikin gaggawa a wannan karon ba ta yi kokarin
sanyawa ba.
"Hajiya don Allah 'a taimakeni da sadakar abinci ko gaya ne
ba miya." Murya yaron ta doki dodon kunnen Hajara. Hajara ta ji
kamar ta ce "Wayyo Allah don haushi.
"Kawo kwanon naka." Hajiya Ladi ta çe da almajirin. Hajara
komawa ta Kara yi ta zauna a karo na biyu ta yi tsaki, hijabin dake
rike a hannunta shi ta mayar abin goge gumin dake tsattsafowa
daga fuskarta. An sami tsawon mintuna akalla goma bata sake jin
motsin kowa ba har ta saduda ta soma kokarin fidda rai da zuwan
Isma'il. Hajara ta rasa abin dake yi mata dadi a ranta gashi dai ba
wata alakar soyayya ce tsakaninta da Isma'il ba amma ga
mamakinta sai ta rasa dalilin kasancewar hakan a gareta maimakon
idan bai zo ba ta dauka a matsayin ba komai tunda dama bai taba
zuwa ba
18
Sallamar 'da ta ji yayanta Ali ya yi ita ce ta katseta daga
dogon tunanin data tsunduma a wannan kuntataccen al'amari.
"Hajara." Aliyu ya kwala mata kira daga tsakar gida.
"Na'am Yaya." Hajara ta amsa kamar yadda ta saba amsawa
in ya kira a koyaushe.
"Akwai wani na jiranki a waje." Ya ce da ita daidai lokacin
da ta fito daga daki hannunta rike da hijabinta, Ali bai kalli inda
take ba, abin da bata taba tsammanin ji kenan ba, nan da nan ta ji
wani irin farin ciki ya mamaye ilahirin zuciyarta, cikin rawar jiki ta
yi waje da sauri a hanya ta gama sanya hijabinta.
Ta sameshi tsaye a gefen wani dakali dake makwabtansu,
murmushin da ya farar tarar ta dashi irin murmushin da idan ya
yiwa duk wata 'ya mace sai ya tafi da rabin imaninta.
"Sannu da zuwa." Ta ce dashi yayin da ta karasa wajensa
bayan ta yi masa sallama muryarta na rawa.
"Yauwa Hajaratu." Ya.ce yanamurmushi.
Yanayin yadda ya kira sunanta cikin nuna salo da tausasa
harshe shi ya fi bata mamaki. ya yi mata kiran da ba wani mahaluki
da ya taba yi mata irinsa a duk tsawon rayuwarta.
"Hajara na daukaikin manta da alkawarinmu."
"Ya za a yi na manta, nifa na zabar maka ranar da zaka zo
da kaina."
"Kin san ku mata wani sa'in akwai saba alkawarі."
"Wasu ko." Ta ce dashi.
"Mafi akasarinku haka kuke."
"Hakan na kasancewa ne da jrin karbar da aka yiwa mutum"
"A takaice dai na karbu a wajenki?"
"Eh to......" Та се tana murmushi.
"Eh to me?" Ya bukata.
Ta yi murmushi.
"Kila waka la kenan ko?" Ya bukata.
"Ni ban ce ba." Ta yi gaggawar fada.
"A gaskiya Hajara tun lokacin dana ganki a ranar nan na ji na
kamu da wani shu'umin shauki a zuciyata, na ji a duk tsawon
rayuwata babu 'yar da ta taba samun gurbin karbuwa cikin
kankanin łokaci kamar ki. kin yi matukar kwantawa a rai na
musamman da na yi nazarin nutsuwar ki. hankalinki da kuma
19
yanayin
kammalallun
kame kanki, na dade ina neman mai irin wadannan siffofin Allah bai nufa na hadu da mukusanciyar hakan ba sai ke da a yanzu Allah Subahanhu wata'ala ya hadani
tara
dake, a gaskiya samun irin ku tamkar tsintsar dami ne a kale sai a
mata sama da dubu ba a sami kamar ki ba don...." "Kai Isma'il kada yabon ya yi yawa." Hajara ta katschi. Tana murmushin jin dadin yabon yaudarar da yake yi mata, hakika Hajara ta hakikance akan Isma'il yana da laffuza masu taushi da bayanai masu kyau a furucin bakinsa. A lokaci kankani ta ji ya soma burgeta.
"Ai Hajara duk yadda na siffantaki kin kai kin kuma zarta wannan matsayi, abin da nake son sanar dake ya Hajaratu na zo ne da Kokon barata akan kaunarki ko Allah zai sa na sami dan wani gurbin da zan makale a cikin mashahurin birnin zuciyarki komai Kankantarsa."
Mamaki da jin dadin kalaman da suka fito daga bakinsa su suka hadu suka dagula lissafin kwakwalwar Hajara har ta kasa samun sukunin yin wata magana da zata maye gurbin nasa maganganun tsawon wani lokaci, kura masa idanu kadai ta iya yi yayin da shi ma yake mata wani irin yaudararren kallo mai tafiya da sinadarin kashe zuciyar wanda aka yiwa.
"Ba ki bani amsa ba." Ya ce cikin sassauta murya. "Mhn me zan ce ma Isma'il?"
"Amsar abin da na fada nake son ki bani."
"Fitowa in saurareka ma gamsasshiyar amsa се."
Kamata ya yi ki fada da bakinki kona sami sa'ida a raina." "Me ka ke son na fada?" Hajara ta bukata.
"Ki ce kina sona." Isma'il ya fada idanunsa kafe bisa yalwataccen kirjinta da yake tasowa duk bayan shakar numfashi da saukewarsa.
"Ki ce kina sona?" Ta ce ta hanyar maimaita kalamin dashi ya furta a farko.
"Abin dana fada kika maimaita."
"Ya kake son na fada?" Ta bukata.
"Ki ce Isma'il ina sonka."
"Ki ce Isma'il ina sonka." Ta sake maimaita daidai da kalamin da ya fada mata.
20
Dariya ce ta kwacewa Isma'il ganin yadda Hajara ke neman
mai dashi wani Karamin yaro ko wani bi ta can.
"Hajara ya kike garani ne kamar wani garc-garen wasan
yara." Ya ce da ita bayan ya tsagaita da dariyar da yake yi da farko.
"Wacce irin garawa kuma?"
"Kin ki ki bani gamsasshiyar amsa."
"Duk abin da ka umarce ni shi nake fada maka."
"Yadda nake so ba haka kike fada ba."
"Ya kake son na fada?"
"Kin fini sani." Ya ce da ita.
Haka suka ci gaba da hira cikin sakewa da junansu tamkar
sun dade da sanin junansu, Hajara bata taba yin hira mai dadin
makamancin wannan ta yau ba. Haka zalika bata taba dadewa a
waje kamar wannan ranar ba, akalla sama da sa'o'i uku suka shafe
suna hira. Sannan daga bisani suka yi sallama da alkawarin zai sake
dawowa rana irin ta yau Juma'a.
Ranar sai data sahfe lokutanmasu tsawo kafin barci ya
dauketa. tunani gami da zancen zuci suka dada taka muhimmiyar
rawa wajen taimakawa barci ya kasa ziyartarta.
Hakika Isma'il ya fi Al-amin iya tsara zance nesa ba kusa ba,
Hajara ta kuma gamsu da irin bayanan da Isma'il ya yi mata, irin
kallon da yake yawan vi mata na matukar burgeta, a kallon nasa
kallo ne da ke tattare da abubuwa da dama wanda a cikin su ta
fahimci kallo daya na so, kauna, yarda gami da aminci. sabanin AlAmin in ya zo kansa a koda yaushe sunkuye baya ko son hada
idanu da ita kamar surukarsa, kullum zancensa baya wuce na karatu
ko da yake ta san karatu yana gaba da komai to amma ai akwai
bırar nishadi da akan dan taba wani lokacin, hakika tana son AlAmin don son addininsa, zantuttukan Isma'il kuma na burgeta, a
nata tunanin shima Isma'il na iya kasancewa mai kamewa da son
addini. Wata tambaya daya data tsayawa Hajara a rai shi ne shin
Al-Amin bai iya zantuttuka irin yadda Isma'il yake yi ba ne? Idan
bai iya ba ya kamata ace ya koya domin ko ba komai ana tą ganin
yanzu zamani ya sauya. Da irin wannan tunane-tunanen barci ya
sadado ya saceta.
A cikin barcinta ne ta yi mafarki mai ban sha'awa da ya dan
dada darsa mata son Isma'il a ranta. Ta tsinci kanta a cikın
21
mafarkin wai gasu a cikin wani irin ni'imtaccen sassanyar lambun
shakatawa mai ciki da yalwatattun kyawawan furanni masu dadin
Kamshi ita da Isma'il suna zazzaune akan shimfidaddiyar koriyar
ciyawar da ta yiwa iya fadin sararin lambu tsinke suma hira cikin
jin dadi da annashuwa suna wasanninsu irin na ma'abota bege da
soyayya, hirar ta yi tsawo har ya fara shafi sabon shamfon dake
kanta sannu a hankali har ya gangaro da hannunsa zuwa gadon
bayanta, ta ji tsigar jikinta ta tashi wani irin dadi mara misaltuwa ya
lullubeta wanda ba zata iya misaltashi ba, ya sake sa hannunsa ya
tallafeta ya matso da bakinsa daidai kunnenta na dama yana mata
wani irin yare a bata iya fahimtarsa ba Larabci ne turanci ne ko
Hausa ita ma ta kasa tantance daya a biyu, kafin ta yi aune
harshensa na bakin kunnenta yana wasa da shi, cak numfashinta ya
dauke bayan tsawon minti guda ya fito da harshen ya bi dashi ta
gelen kunnenta sannan ne numfashinta da hankalinta suka dawo
jikinta, rungumeta ya Karayi yana shafata sannu a hankali lokaci
guda gabobin jikinta gaba daya sukayi sanyi, karfin jikinta ya yi
nusan ba abin da ta iya yi sai langwabe wa a jikinsa yayin da shi
kuma a hankali ya soma sullube mata kayan jikinta....firgigit ta
farka daga nannauyan barcin nata mai cike da daddadan mafarki
cikin fargaba da tsoro kayan jikinta ta soma tabawa ta ji su sanye a
jikinta kamar yadda ta kwanta da su sabani yadda take zato ko
tsammani.
Rashin karfin jikin da ta ji a cikin mafarkinta har yanzu yana
tare da ita. jikinta gaba daya ya canza bata taßa jin ta cikin yanayi
makamancin wannan ba kuma bata taba yi mafarki irin wannan ba,
in ka dauke kasalar da take ji a jikinta zata iya cewa ta ji dadin
mafarkin da ta yi, idan Hajara bata manta ba shekaru biyu baya da
suka wuce akwai wata yarinya a makarantarsu da ta taba tambayar
ya Sayyadinsu kan makamancin mafarkin. amsar da malamin ya
bawa ita ta fara karantowa a zuciyarta kamar yanzu ake yi yarınyar
"Duk wacce ta yi mafarkin tana tarawa da da namiji ko
kwatankwacin hakan yayin da ta farka daga barcin ta ga alamun
wani farin abu mai kama da koko bushe a jikinta ya 6ata mata
zanin ta ko wandonta data kwanta dashi ko kuma a'a gana zama
mafarkin ta farka ta ji danshi ko laima a gabanta hakan shi Ya
tabbatar da balagarta za kuma ta gaggauta yin wankan janaba
22
kamar yadda watannin baya muka koya muku, haka zalika duk
wacce ta tsinci kanta a wannan hali ta tabbata duk abin da ya hau
kan akili ya hau kanta a shari'ance daidai take da mahaifanta duk
abin da ya hau kansu ya hau kanta."
Hajara ta dan shafa gaban wandon dake jikinta sai kawai ta ji
dan laima gami da yauki-yauki a hannun da ta taba da sauri ta mike
zaune ta tashi ta fita tsakar gida cikin sa'a ta tarar ba kowa, buta ta
dauka ta cikata da ruwa ta nufi bandaki.
MAJALISA
LAHADI 25 DECEMBER 2001
"Gaskiya Isma'il ka yi dacen yarinya, ta hadu." Abba daya
daga cikin 'yan majalisar su Isma'il ya fada.
"Sai ma ka kare mata kallo tukunna mugu." Isma'il ya сe.
"Ai nasan alkawari ne a kawota abbatuwa." Nura ya ce.
"Kai Nura wannan yarinya ba ta ſida ba ce ballantana a
kawota abbatuwa ta aure ce."
"Ka fadawa wanda bai sanka ba." Nura ya ce dashi.
"Ya ya zaka yi da yarinyarka Sumoli ta Sabon Gari?" Abba
ya tambaya.
"Ka san mutumin da ba shi da ajiyayyen hatsi a rumbu to ya
zama lallai ya yi awo."
"Kana nufin duk shakuwar da kuka yi da Sumoli kana yin
aure shi kenan?"
"Haba Nura daduro fa suke yi ya za a yi su rabu." Abba ya
ce da Nura.
"Daduro ai ba aure bane."
"Isma'il duk fada kake kana dan samu kana gwada
lakalminka da yarinyar nan warewa zaka yi."
"Rabu dashi Nura sau nawa yana samun yarinya, ya nuna da
gaske ya ke yi aurenta zai yi amma daga zarar ya kawota abbatuwa
da an fedeta shi kenan sai ya fara yi mata wulakanci har zuwa
lokacin da zata gaji ta hakura dashi."
"Tun da nake yin 'yan mata akwai wacce na taba cewa zan
aureta ne a cikin 'yan matan da nake kawowa fida?"
"Ko ba ka ce zaka aura a gabanmu ba ai su 'yan matan da
zummar aure kake zuwar musu."
23
"To Allah ne kadai ya san karatun sallar kurma." Isma'il ya
ce dasu yana dariya.
"Allah ya sa da gaske kake."
BABI NA BIYU
BAYAN WATANNI BIYU
24th FEBRUARY, 2002
U
staz Al-Amin ya fara ganin canji a wajen Hajara tun
tana nuna masa a fuska har ta fara fitowa fili tana fada
masa, daga yazo zance zata soma bata rai, koda ya soma magana
zata ce ta gaji zata koma gida barci take ji. Soyayya tsakaninta da
Isma'il ta soma karfin tun ba a gane ba agidansu har daga baya aka
fuskanci me yake gudana a tsakaninsu.
"Hajara wai yanzu Al-Amin da ya zo sai ya tafi kamar wanda
ake kora me ke faruwa ne?" Hajiya Ladi ce ke tambayar 'yarta
Hajara.
"Nima ban san dalili ba."
"Ko dai wani abin kika yi masa?"
"Ba abin da na yi masa."
Waye kuma wanda yake zuwa wajenki a 'yan kwanakin nan
bayan Al-Amin?"
"Wani ne Isma'il."
Abin da nake son gaya miki shi ne ki rike Al-Amin hannu
bibbiyu kin ga yaro ne mai rikon addininshi, kada wani ya hure
miki kunne ya yaudareki, saboda samarin yanzu abin tsoro ne,
kuma a hankali ake binsu."
"Ni ba wanda zai hure min kunne."
"To Allah ya sa."
Hausawa na cewa abu kamar wasa Karamar magana ta zama
babba, haka soyayya ta ci gaba da ruruwa tamkar wutar daji
tsakanin Isma'il da Hajara har kowa ya sani tsakanin yaro da babba
a unguwar su Hajara ya san Hajara da Isma'il tun iyayenta na yi
mata fada har suka gaji. Yadda soyayyar su take ruruwa da Isma'il
haka soyayyarta da Al-Amin ta ja baya tun yana zuwa daya a sati
ya koma yana zuwa sati bibbiyu daga karshe ya koma zuwa watawata sakamakon irin wulakancin da Hajara take yi masa.
24
"Yanzu Hajara ace tsakaninmu wani abu ya shiga kin kuma
kasa yi min cikakken bayani." Al-Amin ne yake fadar haka a wani
zuwa da ya yi wajen Hajara.
"Babu wani abu da ya shiga tsakaninmu."
"Amma yanzu ba kamar da ba."
"Canjin me ka gani?" Hajara ta bukata.
"Suna da yawa canje-canjen."
"Kamar na me da na me kenan?"
"Idan na yi sallama dake ba kya son fitowa da wuri sabanin
Ja, hakazalika daga kin zo za ki ce min kin gaji barci kike ji ko
niakamancin haka, kowanne lokaci kikan zo min ranki a bace idan
kuma muna hira wasu lokutan hankalinki baya tare da ni ya kan
tafiya ne wata nahiyar tunane-tunane na da ban wanda na kasa
fahimtar ko gane mene..."
"Ya isa haka to yanzu me kake so?" Hajara ta katse shi cikin
tambaya.
"Abin da nake so shi ne ki gaya min gaskiya idan kin sauya
ra'ayi ki fahimtar dani domin na sani."
"Abin da nake son ji kenan?"
"Kwarai ma kuwa." Ya ce da ita.
"To na sauya ra'ayi." Hajara ta tabbatar masa kwayar
idanunta kafe a kan kirgaggen gemun Al-Amin yayin da shi ku ma
ya rasa ta cewa tsawon mintuna, kana daga bisani ya nisa.
"Hajara na ji dadin bayaninki, da ki tsaya kina wahalar da
kanki da kuma ni kaina gwara ki fito ki fadi gaskiya kamar yadda
kika fada yanzu, sai dai nasihar da zan yi miki ta karshe shi ne ki
maida hankali sosai wajen zaben mijin da za ki aura ki zauna da shi
a matsayin abokin zaman rayuwarki kada zakin baki da iya sa hula
ko iya sa riga su rudeki, ya kamata Hajara ki sani mafi yawancin
samarin yanzu mayaudara ne ki yi hattara da hankali gami da
tsantsar nutsuwa kwarai wajen sauraren kowane irin saurayi da
ma'aunin addini ko...."
"Gaskiya ni na gaji da surutan nan barci nake ji." Hajara ta
katseshi cikin hasala daga doguwar nasihar da yake yi mata.
"To Hajara ki yi hakuri idan na bata miki rai amma ina son
ki rike wannan a ranki ko ba dade ko ba jima sai kin san maganata
gaskiya ce akan hanya take daga karshe nake cewa Allah ya hada
25
kowa da rabonsa na alheri" Al-Amin na gama fadin haka bai tsaya
jin abin da zai fito daga bakinta ba kawai sai ya juya ya nufi
motarsa, kasancewarsa mutum ne mai tawakkali da yarda da
Kaddara.
Hajara ta juya da sauri ta shige cikin gida kamar wacce aka
kora, sai dai abin da Hajara ta kasa fahimta haka kawai sai ta ji
gabanta yana faduwa zuciyarta kuma ta yi bakikkirin.
"Ke wai me ke damunki ne?" Ta tambayi kanta bayan ta
shiga dakinta ta zauna a gefen katifarta, Hajara a zuciyarta ta dan
tausayawa Ustaz Al-Amin sai dai kuma babu yadda zata yi ne son
Isma'il ya riga ya yi mata sanda ya mamaye mata kaso mafi tsoka
da ke zuciyarta duk da kasancewar basu dade sosai ba sonsa ya yi
mata kamun da ba zata iya rayuwa in babu shi ba, a yadda take ji a
zuciyarta zantuttukansu masu ratsa zuciya gam da narkar da
kwakwalwa duk ga bisa dukkan alamu rikon addininsa bai kama
Kafar na Al-Amin ba, bata taba jin sa ya yi mata maganar addini ba
ita dai abin da zata iya tabbatarwa game da Isma'il shi ne Musulmi
ne, kamar yadda yà nuna mata da gaske yake sonta kuma tana
ganin idan har ta auareshi to ta yi dacen miji gashi fari dogo kuma
kyakkyawar gaske gashi da yalwataccen gashin baki ga iya magana
mafi karin armashi a gareshi shi ne murmushinsa yana burgeta а
kowane lokaci ya yi matashi. Hajara ta yi murmushi bayan tuno
Isma'il a ranta take ta ji bakin cikin dake tattare fal a zuciyarta ya
soma washewa sakamakon tunanin Isma'il din da ya bijiro mata a
cikin zuciyarta, a hankali ta mika hannu bisa teburin dake gefen katifarta ta dauko wani littafin Hausa mai suna ILLAR MAZA ta
bude don fara karantawa, layi daya kawai ta karanta daga shafin
farko na littafin sai ta ga tamkar fuskar Isma'il take gani a jikin
shafin littafin yana yi mata murmushi hakan shi ya hana iya ci gaba
da käranta littafin sai ta ma ta soma murmushin ita kadai tamkar
mahaukaciya.
***
Isma'il shahararren cikakken dan bariki ne na bugawa a
jarida. kwararren dan giya wanda saboda sabo da ya yi da giya duk
shan da ya yi mata bata bugar da shi sai dan sauyawa da zai nuna
kadan, ya kan sha rabin kiret, kwalba shida na guld a zaman lokaci
guda.
26
Suna zaune a unguwar Gwammaj layin 'Yan Azara mahaifin
Isma'il tsohon dan sanda ne wanda a yanzu yake karbar fansho,
mahaifiyarsa kuma malamar asibiti ce da take gab da ritaya a
asibitin kashi dake Gwammaja.
Isma'il ya taso cikin tsantsar gata da shagwaba gami da
rashin samun cikakken tarbiyya kasancewar shi shi kađai iyayensa
suka haifa, mahaifin Isma'il ya kan raba kudinsa na fansho ya
mikawa Isma'il rabi a kowanne wata, haka zalika mahaifiyarsa
bata son ganin abin da zai bata masa rai komai kankantarsa.
Sun hade gwiwa sun hada masa jari mai karfi wadatacce
suka kama masa rumfa a kasuwar jan bulo, da farko ya soma abin
kirki kamar gaske amma haduwarsu da Sumoli wata karuwar sade
sukezaman dadiro ke da wuya al'amarin ya sauya salo ita ta sa ya
yi gaba ya yi baya don ma Allah ya yi masa nasibi wajen neman
kudi, rumfarsa a kowanne lokaci cike take da kwastomomi, a
kullum karfe biyu yake rufewa ya nufi Sabon Gari, wajen farkarsa
Sumoli, domin kai mata kudin abincin ranar, gami da kudin daki.
"Hajara mahaifinki ya ce na tambayeki dalilin daina zuwan
Al-Amin?" Hajiya Ladi ce ke tambayar Hajara da ke zaune a tsakar
daki, Hajara ta yi shiru ba ta ce komai ba tsawon mintuna yayin da
Hajiya Ladi ta kura mata idanu tana sauraren jin amsar da zai fito
daga bakinta.
"Ko ba ki ji banc, eye?" Ta sake tambayarta.
"Ina ji." Hajara ta ce da ita sannan ta sake yin shiru.
"Ke kika cc ya daina zuwa? Ko ya ya?" Hajiya Ladi ta sake
jeho mata tambaya a karo na uku.
"A'a ni ban ce ya daina zuwa ba." Hajara ta ce kanta a
sunkuye.
"To menene dalilin daina zuwansa? Kwanaki na tambaycki
da ya zo yana tafiya da wuri kika ce ba komai."
"Ni ma gani na yi ya daina zuwa."
"To abin da nake son gaya miki ni ba za ki jawo min fada a
wajen Babanki ba, ba ruwana in ya zo kya fada masa da bakinki.
kuma bari in gaya miki gaskiya Babanki ya rantse ba za ki auri
kowa ba sai Al-Amin."
27
Hajara ta dago da kanta dake sunkuye don kallon fuskar
mahailiyarta don ta gane da gaske ta ke yi ko kuwa fada kawai
take. yanayin da Hajara ta gani a cikin kwayoyth idanun
mahaifiyarta shi ya tabbatar mata da lallai da gaske táke ba alamun
wasa ko tsoratarwa a tare da ita, idan kuwa haka ne lallai
mahaifinta ya yi mata karantsaye, ita kam babu wanda take so da
Kauna take kuma tunanin aura sai Ism'il, don shi take ganin ya