Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MAZASAI SANNOINTA A WALI Mrs Auwal G. Danborno) BABI NA DAYA 21 JANUARY, 2004 Hajara gari ya yi gari, kunci ya yi kunci tun da nake ban taba shiga wahala irin wannan na lokacin ba babu kudi, aikin yi ya gagara samuwa, ko ina mutum ya shiga sai kuka, talakawa kuka masu kudi kuka haba!" "Maigida kowane irin yanayi ka sami kanka sai ka kasance cikin godiyar Ubangiji." "Hajara dama dole ne dan adam a ko yaushe ya kasance cikin godiyar Ubangiji, amma kuma yanayin nan da kasar nan take ciki a wannan lokaci na mulkin kama karya, al'amura sai dada tabarbarewa suke komai ya baci." "Komai hakuri ake yi don gudun kamuwa da ciwon zuciya." "Wacce irin wahala ce ban gani ba a cikin wannan surkukin yanayin da muke ciki." "Allah ya kyauta." Ta ce a hankali cikin sanyin murya a kokarinta na kwantar da hankalin mijinta abin kaunarta. ""Yan sarkokin da kika zo da su duk mun sayar mun ci abinci da kudin domin mu rufawa kanmu asiri." Ya ce da ita yana kallonta gami da nazarin kyakkyawar fuskarta. "Haba-haba maigida kar ka damu kanka haka Allah ya Kaddara, ka sani fa babu wanda ya kamata na yi wa hakan da ya wuce kai, domin idan na bi ka sau da kafa to babu makawa aljanna ce sakamakona matukar na bi sharadin aure kamar yadda shari'a ta tanadar." Hajara ta ce da shi. "Allah ya yi miki albarka ya kuma saka miki da alheri." "Amin maigida." Ta amsa. "Wannan shi ne zaman aure na gaskiya mafi yawan mata yanzu burinsu su sami na zuba dashi ko ta halin kaka, idan kuma miji ba shi da shi sai ki ji kańsu, idan yana dashi kuma matsala ta taru la yi masa yawa a cikin gida." "Wadannan ba sa tunanin yiwa miji biyayya da kokarin rufa masa asirinsa, yana daga cikin abin da ya zama wajibi a rayuwar zaman aurce, kuma Manzon Allah (SAW') yana cewa duniya wani dan wajene na jin dadi amma fiyayyen jin dadin shi ne samun mace L ta gari Manzon Allah (SAW) ya yi gaskiya." Hajara ta ce muryarta a sanyaye. "Allahu Akbar, yanzu dai ba wannan ba Hajara firjin nan naki nake son na kadar na shiga kasuwa da kudin domin yin jari kin san kasuwa sai da jari." "Na riga na fada ma kayana kayanka ne duk abin da ka ga damar dauka a fakin nan ka fauka, babu bukatar sai ka kara tambayata." ""Yan uwanki nake gudu kar su rika tambayarki." "Kayana ne ba na wani ba, ba kuma wanda ya isa ya tambayeni ya ya na yi da kaza ko kaza." "Koda mahaifanki ne?" a "Kwarai kuwa ka sani fa ka fi mahaifana matsayi da daraja, wajena domin za ka yi min abin da mahaifina ba zai taba yi min shi ba matsawar rayuwa saboda kimar ka ta haura ta sa a idanuna." "Haba Hajara ba sai kin fada ba na sani." Ya ce da ita yana murmusni. *** Hajara na matukar son mijinta kamar ta hadiye shi, gashi dai shekarar su biyu cikin halin kunci, gidan da suke zaune gidan haya ne dake dauke da dakuna akalla takwas. Zaman da Hajara za ta iya kira ta yi zaman jin dadi da mijinta ba zai wuce na tsawon wata biyun da ya biyo bayan aurensu ba. sauran watannin kuma da suka hadu suka bada shekaru biyu kai tsaye za a iya kiransu da zaman kunci da tsantsar talauci duk da cewa suna zaune sumul da mijinta Sama'ila a zamantakewar 1 aurensu Ba wata soyayya a duniyar nan da za ta yi armashi ba wadataccen abinci, muhalli gami da 'yan sauran abubuwan da ba a rasa ba. Sau uku yunwa gami da tsantsar wahala na zubar mata da juna biyu. hakan bai sa ta damu ba saboda so da Kaunar da ke Isakaninta da Isma'il. Gwala-gwalan da ta tare da su tunı Isma'il ya ci kasuwarsu, yanzu ku ma ya dawo kan firjinta. ko da yake Hajara na zaune dashi zaman Allah da ma'aiki. "Assalamu alaikum." Muryar Isma'il ta kwararo zuwa cikin dakin shi ya dawo da Hajara daga dogon tunanin da ta tsunduma, 5 Hajara ta cira kanta gami da amsa sallamar cikin nutsuwa. Isma'il ne hade da yaro suka shigo don daukar firjin, cikin gaggawa ya shigo dakin. tare. "Shigo mana." Isma'il ya umarci yaron da suka shigo gidan "Hajara dauko min rasit din firjin nan." Ya ce da ita yayin da ya sauke wata tsohuwar fitilar kwai gami da wani karfen maganin sauro da suke zube akan firjin, ta miko masa takardar gami da durkusa wa lokaci guda, Isma'il ya karba. Yaron ya kama masa firjin suka rabashi da jikin katakon da aka dora firjin akai, ruwa ya dan zubo ta gefen da murfin firjin yake, Isma'il ya daga labulen da ya yiwa dakin hijabi da tsakar gidan. Wasu mata biyar da ke zaman gulma suka dan matsa gefe guda gami da bin Isma'il da kallo, yayin da suke kokarin fita shi da yaron dauke da firjin, wata mata baka gajera mai kiba ta kiftawa farar mace ramammiya da ke zaune a gefenta idanu, gaba daya mata suka kyalkyale da dariya irin ta magulmatan mata yayin da suka tsinkayi wani abin tsegumi. "Ni da bita zai-zai" Watamai daurin kirji daga cikinsu ta fada. suka sake Kyalkyalewa da dariya gaba dayansu. "Wa ya ga damo sarkin haküri." Daya daga cikinsu ita ma ta tofa. albarkacin bakinta sannanisuka cisigaba da hirarsu bayan ficewar Isma'il daga cikin gidan "Kai Saude wannan yarinyanwacce iri ce ita?" Matar da ke da daurin kirjiitautambaya. "Oho! Aiidukawacce tancewnamiji uba ne to sai ta mutu marainiya, maza kuma saisannu wallahi." Ta salla ni nataba jinirin wannan:don tsabar rashin hankali wai ita tsantsar soskenanawaiamiji ya rinka sai da kayan dakin matarsa? Wa ya gausahorama." "Ke ma daikya fadasarai, ai ni wallahi ko kudin cefane bana bari in zai shekara bashi da shia kullum sai na tuna masa." "Ke Larai niiba kima sani ba dahyake na dan yi firamare dan littafi ne dani komai na biyoshi bashi sai na rubuta, yanzu haka har ya gane daga ya dawo daga kasuwa, sai ya dauki littafin ya duba in da bashi sai ya brya ni kuma saj na soke, da yake shi ma ya dan yi 6 Islamiyya, in bai biya ba kuma na cashe masa ke wani sa'in ma don tsoron gudun surutuna agogonsa yake bani kafin ya samu ya biya ni in ya so daga bisani kuma, sai va karbi agogonsa tabdijan ai maza sai sannu kamar yadda kika "Ahayye ayyuriı" Matan suka sheke da shewa a lokaci guda tamkar hadin baki kamar suna gıdan biki. "Ni abin haushi na da ita shi ne bata son fitowa cikin jama'a domin ayi hira a kullum tana kumshe a daki kamar shirgi a sito." "Wai nan karatu take yi, wa ya ga ałhuda-huda." "To wata fi karatu? In ma ita ce gafaka." Sarai ta ce tana sosa isefaffan cakurkudadden gashin kanta. "Ni wallahi mugun haushinta ma nake ji banza sakariya kawai santoluwa." "Sai dai kuma tana da ladabi, komai kankantar mutum zata gai da shi." Larai ta ce da su. zaune take gefe guda tana tsintar kwarkwata akan 'yar Karamar 'yarta dake durkushe a tsakanin cinyoyinta tana kashewa a bayan wani kwano ga duk kwarkwatar da abincinta ya Kare a jikin yarinyar. "Ke gafara can! Ba wani ladabi Larai ki kiyayi irin wadannan lumfun-lumbun matan duk...." Hirar tasu ta katse a lokaci guda, sakamakon hango Hajara da suka yi ta fito daga daki hannunta rike da buta. "Sannunku." Hajara ta ce yayin da tazo dab da su. "Yauwa Hajara." Suka amsa gaba dayansu. ta nufi bandaki, suna ganin 6acewarta suka sake bude wani sabon faifan hirar tasu. "Ko wata fi son shiga aljanna?" Sarai ta ce, muryarta kasaKasa gami da kallon sashin bandaki bayan shigewar Hajara. "Wai wacce ma irin sallah ba kirgawa." "Ni dai biyar na sani a rana, ko akwai wata?" "Biyar ne cif-cif." Sarai ta ce yayin da take kokarin kwatantawa da 'yan yatsun hannunta na dama. "Wa ya ga sallau. irin wadannan matan ne ake kira da muminin karc baka haushin sai cizo." "Kwarai ta sallah wannan haka yake irin wadannan ne idan suka sanya mijinsu gaba sai ya raina kansa sai dai......" IHirar tasu ta Kara katsewa a daidai lokacin da suka hango Hajara ta fito daga bandakin, ta tsugunna a gaban wasu tarin 7 kwanuka dake zube a gurin da aka tana da don yin wanke-wanke bataliyar kudaje sun kafa sansaninsu a wajen, tsungunnawar Hajara ke da wuya kudajen suka baje lokaci guda kowanne ya nufi 6angaren da yake tunanin anan matserar sa take tamkar wadanda aka umaria, illa wasu kalilan daga cikinsu da suke yawo bisa tsantsaman ruwan dake zube a cikin wani kazamin kwano wanda hakan ya tabbatar da sun rigamu gidan gaskiya. Cikin dan kankanin lokaci Hajara ta gama alwalar da take yi sannan ta mike tsaye. "Sai an jiman ku." Ta ce da su yayin da ta Karaso kusa da inda suke zata wuce su a kokarinta na zuwa dakinta. "Yauwa sannúnki, unguwa za ki ne?" Sarai ta bukata shakiyance. "A'a karatu nake shirin shiga." "To Allah ya ba da sa'a." Sarai ta cе. "Amin, don hasken Annabi da Alkur'ani." a "Haba Kayode wannan firjin fa da kake gani mai kyau ne domin bai sha wata wahala ta a zo a gani ba, amma kuma kai kake neman ka yiwa mutane cinikin yara, haba Kayode ka duba mana ai don gaba ake wankin tukunya." "Na sani amma baka ganin ba kudi a gari ne? larka ta yi wuya. ai na yi ciniki mai kyau dubu biyar fa ba naira biyar ba." "Ka duba rasit din dubu sha biyar fa aka sayc shi, a ajiye yake ba wani amfani ake dashi ba." "Ni dai dubu biyar zan saya in kuma ba zaka sayar min akan hakan ba to mai kurar bai yi nisa ba sai ka dawo dashi ya dauke maka." Isma'il ya yi shiru yana nazarin kudin a zuciyarsa wanda ya ke ganin tamkar almara ko shirin fim. Ya ja numfashi ya sauke. "Kawo kudin ba komai." Isma'il ya ce. Kayode ya mika masa 'yan Naira dari biyar-biyar guda goma bayan ya Kirgasu, Isma'il ya tisa kudin kana ya soke su a aljihun wandonsa bayan ya tabbatar sun cika. "To sai wani jikon." Ya yiwa Kayode sallama. Ya nufi bakin titi. ya tsaida wani dan acaßa da ya yi dankwali da yadin tutar Amurka a kansa. 8 "Kai yare Sabon Gari." Isma'il ya ce. "Wanne layin?" "ABEDI." Isma'il ya shaida masa. "Lamba nawa?" Dan acaban ya tambaya. "NIYAGARA HOUSE, lamba talatin da biyu." "Naira hamsin." Dan acaban ya fada. Isma'il ya dare mashin din ba tare da ya taya ba. Sabon gari ta diba. FARKON HADUWARSU DA HAJARA 21 DECEMBER 2001 3:00 S anye take da farin dogon hijabi har kasa wanda ya suturce duk ilahirin gangar jikinta hakan ya yi matukar taka muhimmiyar rawar gani wajen, fitowa da tsarin shigar tata, а hannunta na dama rike da littafi mai tsarki, tana tafiya cikin nutsuwa kanta a sunkuye bata kallon ko ina sai gabanta daga ganinta ka ga nutsattsiya kuma kamilalliya a fuska. Daga can wani bangare wasu samari na zaune. Sun tsurawa hanya ido, ba abinda suke sai kallo gami da gulmar matan mutane da 'yan mata masu wucewá sau da yawa a haka ne suke şamun 'yan matan da suke lalata da su. "Kai ka ga wata cika, masifa ta hadu." Sule ya ce. "Daga ganinta za ta yi hankali." Cewar Isma'il. "Gata kuma da kirar da ake so." "Wankar tarwada ce." Sule ya ce dashi. "Ba wata kala wankan tarwada, ka kirata da baka kawai, amma ba can ba." "Amma.Suleiman ai bakin nata ba sosai ba ne da dan haskenta." "Ya! Mutbita mana, ai a rashin kira karen bebe ya bata kuma a rashin tayi akan bar araha." "Gaskiya ne maganar ka sai dai ni wulakanci ne bana so. domin ina gudunsas ka san 'yan matan zamanin nan na yanzu da muke ciki. suci maka mutunci ba wani bakon al'amari bane a wajensu, basu dauke shi a bakin komai ba." Wani mai suna Nura ya ce dasu. 9 "Menene kuma ya kawo zancen wulakanci, anan imma ta yi wulakancin yana fitowa a goshi ne idan ta tsinka mu sai mu juyo mu shareta kawai." "Ka ce wani abu Isma'il Allah dai ya sa kada ta yarfamu." Su biyu suka bi bayanta tun daga layin 'yan azara dake unguwar Gwammaja har zuwa layin Malam Bala Maiyafe, sun cimmata tana kokarin tsallaka titi daidai wani katon ginin bane dakc dama da hanya. ""Yanmata sannunki." Isma'il ne ya soma yi mata magana yana yake hakoransa wadanda hayakin sigari da taba wiwi suka yiwa illa. Hajara ta yi banza da su ta dan kara gaba cikin sauri akan tafiyar da take yi farko. "Ai ka ji tsiyar." Nura ya ce yana dariya. "No! Ba komai wannan ba wani abu bane ai mai nema yana tare da samu." Samarin suka Kara sarsarfa domin su sameta. ""Yan mata don Allah ba ki ji ba muna son yin magana dake ne. A wannan karon ma shirun ta Kara yi musu a karo na biyu yayin da ta tsallaka titin ta ci gaba da tafiyar ta tamkar ma suna magana ne da gunki. "Ji mana Isma'il mu rabu da ita kawai." Nura ya shawarci abokinsa muryarsa kasa-kasa. "Ka koma ka jira ni a bakin titi zan ci gaba da jarrabawa ko na dace ka san jirgin sama ma da jarrabawa ya som a tashi sama." Isma'il ya ce dashi. "Ta ſi nono fari." Nura ya ce ya juya ya tafi Isma'il kuma ya ci gaba da bin ta shi kadai. "Haba 'yan mata ki ji tausayi na mana ki saurareni domin ki ji bayanin dake tafe dani." Hakan da ya fada shi ya dan raunanar da zuciyarta ya sa jikinta ya dan yi sanyi ta ja ta tsaya. "Tausayi kamar ya ya?" Ta bukata gami da juyowa fuskanceshi. ta "Ba shakka yadda kike da kyau a fuska haka nan ma muryarki take da dadin amon sauti mai inganci." Isma'il ya сс а ransa. A fili kuma ya ce. "Tausayi kamar na nisan tafiyar da na yi saboda bin ki." 10 "Ni na cc ka biyo ni?" "A'a ni nasa kaina." "Ka ga kuwa ai sai kai ya fi bauta ciwo." Ta ce dashi tana mai ci gaba da kallonsa, hakan ya sa ta yi nazarin shigar da ya yi na doguwar farar shadda tazarce har kar kansa da hula ita ma fara. hakika ta yaba da tsarin shigar tasa tabbas ta yi masa kyau. Isma'il ya kaucewa wani dan acaba da yake kokarin bugeshi. "Kin san Hausawa sun ce in ka ga kare na shinshina takalmi..." "Malam ban saba tsayawa a titi ba." Hajara ta katse shi ganin Isma'il na neman wuce gona da iri. "Nima ba mutunci na bane na tsayar dake akan hanya, sai dai ba yadda na iya hakan ya zame min dole ne kasancewar rashin sanin takamaiman inda zan sameki ban san gidanku ba haduwar yau daya се." "Daidai wancan darbejiyar da yara ke wasa a Karkashinta. nan ne kofar gidan mu." Hajara ta nuna masa wajen da hannunta. "Suna fa?" Ya bukata. "Hajara." "Naka fa?" "Isma'il." Ya sanar da ita sunansa. "Yaushe ake samun ki a gida?" "Ranar da ba makaranta." "Alhamis da Juma'a kenan?" "Kwarai kuwa." Hajara ta tabbatar masa. Wacce rana kika zabar min daga cikin ranakun biyu?" Ya sake bukata. "Ka zo ranar Juma'a." "Haji babbar rana kenan amma ni nafi sha'awar Alhamis." "Me ya sa ka fi sha'awar zuwa Alhamis?" "Na fi jin dadin zance a ranar." "Ranar ina da bako na musamman." "Bako na musamman?" Ya tambaya baki bude. "Na musamman kamar yadda na sanar da kai da farko." "To shi kenan ba wani abu Allah ya kaimu Juma'ar." "Amin don Rabbil-Arshi." "Sai an jima:" Ya ce da ita 11 "Yauwa na gode." Suka yi sallama. Hajara ta juya ta nufi gida, Isma'il kuma ya juya ya nufi bakin titi zuciyarsa fari fat don bai taba ganin yariyar da ya ji a lokaci guda ta kwanta masa a rai kamar Hajara ba. Ya hango Nura zaune a gindin wata bishiyar dorawar turawa yana zaman jiransa. "Kai banza ne baka da hakuri." "No! Ba haka ba ne ni bana son wulakanci ne." "Su dama mata ai haka suke sai an yi hakuri da su domin dole ne su nuna maka halin nasu sai sun ja maka rai da nuna jan aji don kar su nuna saurin bada kai ace sun wulakanta." ka ce?" "Amma fa yarinyar ta hadu matukar haduwa." "Sai ma ka ji muryarta." Isma'il ya ce. "Ji mana tawa ce ko taka ce?" "Wacce irin taka kuma? Kai da ka kasa jurewa?" "Tun da komai ya daidaita sai ka gabatar da ni kawai. ko ya Isma'il ya kyalkyale da dariya. "Ina haba mugu kaya na ne." Isma'il ya ce dashi. Nura ya mike ransa a Gace sannan suka doshi bakin titi domin komawa layinsu 'Yan Azara, zuciyar Isma'il cike da tsantsar farin ciki da annashuwa yayin da fuskarsa ke cikin wani irin yanayi mai nuna walwala. *** "Sannunku da gida." Hajara ta ce bayan ta shiga cikin gidan gami da sallama. "Yauwa Hajara sannu har kin dawo?" Hajiya Ladi mahaifiyar Hajara ta bukata. "Na dawo Hajiya." "To sannunki da zuwa." "Yauwa." Ta ce daidai lokacin da ta nufi wata kwaba da aka tanada don ajiye littattafai masu tsarki, ta sa dan mukulli a gurbin sa kana ta murza ta bude Rofar kwabar sannan ta sa littafin dake rike a hannunta a ciki, ta mayar da kofar a hankali ta rufe. "Ga abincinki nan ki dauka kafin ya huce." 12 a "To Hajiya." Hajara ta ce daidai lokacin da ta mika hannunta bisa kan kwanon silbar, shinkafa ce dafa-duka hade da kifi sadin, hankali Hajara ta soma cin abincin kamar bata so. "Anti Hajara dazu Al-Amin ya yi waya ya..." Sani. ba. "To na ji sarkin surutu." Hajara ta katse shi. Wani kaninta ne "Ya ce zai zo bayan sallar isha'i." Sani ya ci gaba bai hakura "To na ji sai ya zo." Ta ce yayin da ta kai cokalin dake dankare da shinkafa bakinta. Tana gama cin abincin ta mike tsaye ta nufi dakinta dake kusa da kafar bene. Dakin karami ne da yake dauke da 'yar Karamar lotsattsiyar katifa, gefen katifar wata 'yar Karamar durowa ce dankare da littattafan addini gefe guda kuma ga littattafan Hausa. Kamar kullum yau ma tana zaune bisa kujerar kushin kwaya daya dake dakin, ta mika hannunta sannu a hankali cikin nutsuwa littafin Kur'ani mai tsarki dake ajiye a bisa durowar tsakar dakịn kana ta somå karantawa bayan ta bude shalin da take bukata. Kiran sallar Magariba shi ya katse mata hanzarin karatun da take yi, a hankali ta rufe littafin bayan ta yi addu'a sannan ta maida shi ma'ajin da tanadar masa ta mike da niyar zuwa ta yi alwala. Jam'in da ta bi masallacin dake makwabtaka da gidansu ya dauketa tsawon mintuna sha biyar da 'yan tsirarun dakiku har zuwa addu'o'in da ya samu a gareta ta gabatar ta shafa fatiha, kai tsaye ta koma dakinta: Wannan karon littafin Hausa ta dauka mai suna 'YAN MATA na wani marubuci Kabir Y'usuf Anka cikin nutsuwa ta soma nazarin shafin farko na littafin. "YAWA NE" "КАМAR YA FA?" "KA ZUBAWA YARINYAR MUTANE IDANU..." Abin da ta soma cin karo dashi kenan a littafin wanda hakan ya sa tamkar inkiya ga kwakwalwarta sai tunanin Isma'il ya fado zuciyarta. "Shin ko sune irin samarin dake cikin wannan littafin 'Yan mata?" Hajara ta tambayi kanta. "Kai ba zai yiwu ba." Ta musa kanta. 13 "Gaskiya saurayin yana da laffuzai masu dadi." 'Ta ce sai dai wannan karon a fili ta fada maimakon a zuciyarta kamar yadda ta yi ba tare da tunanin wani zai iya jin ta ba. Ta dan yaba masa, koda yake a ganinta yabawa ba so ba ne, saurayinta AI-AMIN da iyayenta suka amince dashi gaskiya bai gama kwanta mata a rai ba, sai dai wasu abubuwa biyar ne ke sawa ta saurareshi. ADDINI SANIN YAKAMАТА HAKURI DA JURIYA HANKALI DA NUTSUWA KAWAICI DA KUNYA GAMI DA ASALI Duk da cewa ba son Isma'il take ba a haduwarsu ta farko wato yau din nan bata ji sonsa ya darsu a ranta ba, amma za ta so ace ta hada wadannan dabi'un guda biyar data lissafasu, ko dayake basu dauki tsawon lokacin da zai wadacesu suna hira ba a tsaiwar tasu ta yau, ana ta tunanin kamar tana ganin zai kasance da wadannan dabi'un da ta ambata. Duk kuwa macen da ta samu mai wadannan halayya to ta yi matukar sa'a a rayuwar zamantakewar aurenta. Bata ankara ba littafin dake hannunta ya fadi, sannan ne ta tuna ashe karatu take yi. Kana ta maida hankalinta wajen duba littafin. "TO SAI ME KUMA....?" "SHI NE AI ZAKA...." Littafin ba zai karantu ba sakamakon tunanin da take yi a baya, ya kara durfafar zuciyarta ya rika fisgarta, Alhamis, Juma'a sune ranakun data lissafa wa Isma'il cewa ana samunta a gida, sai dai tana jin a zuciyarta kamar ranar ta yi nisa ita da kanta ta yi mamakin kasancewar hakan a tare da ita, kuma ba wai don tana sonsa ba. a'a sai don ya zo ta ji abin da zai ce ta ga iya gudnu ruwansa. lallai kam za ta so jin abin da yake tafe dashi, zata iya tuna wani irin murmushi da ya sakar mata. murmushin ya fan burgeta, kasancewar murmushin ya samu muhalli mafi da cewa da fuskar da ta yi shi, tsawon dan saurayin Isma'il ya zo daidai da irin Isawon da ita take son ta ga saurayi ya mallakeshi, kasancewar a rayuwarta duk wanda ta ga yana da tsawo irin wannan ya kan 14 burgeta matukar burgewa duk inda haduwa take Isma'il ya kai, kenan hakan na nufin Isma'il na iya samun gurbin zama a zuciyar Hajara, sai dai kuma wani hanzari guda daya a gareta shi ne saurayin da iyayenta suka zabar mata a matsayin abokin zamanta Ustaz Al-Amin wanda kasancewarta dashi ta kara zama mai rikon addini sannan kuma shi mutum ne mai nuna mata tsantsar so a koda yaushe suka kebe, so na hakika, soyayya irin wanda Allah ya tanadar a addinance ba irin soyayyar samari da 'yan matan zamanin nan na yanzu da muke ciki ba gurbataccen zamani. Dadin dadawa yana da hali daidai gwargwado yana da 'yar motar shiga karama mai saukin kudi sannan ya gama ginin gidansa a unguwar Dorayi. "Anti wai ki zo in ji Al-amin." Kaninta Sani ya ce daidai lokacin da ya shigo dakin hannunsa rike da gwangwanin madara yana wasa dashi. "Ka ce masa ina zuwa." Ta umarci yaron. Duk ranar da ta kasance akwai makaranta ya kan ziyarceta ne bayan magariba don gudun kashe mata lokacin karatu. Ta sameshi jingine da jikin motarsa wayar G.S.M kirar Sony Erikson rike a hannunsa na dama yana wasa da ita, sallama ta soma yi masa kamar kullum Sannan suka gaisa a takaice. "Hajara ya mutan gidan? Ina fatan kowa da kowa lafiya?" "Lafiya kalau." Koda yake a kurarren lokaci na zo babu wadatar lokacin da zamu tsaya tsawaitar hira, wasu littattafai ne na kawo miki BULUGUR MARAN da RIYADUSSALIHINA." "Kai Al-Amin na gode baka gajiya da dawainiya ne a kullum? Allah ya saka maka da alheri." "Amin Hajara." Kiran sallar da ladanin wani masallaci dake makwabtaka da gidansu Hajara ya kwala shi ya katse Al-Amin da ci gaba da magana. "Maza je ki kada mu yi asarar jam'i sai na zo ranar Alhamis idan mai komai ya kai mu" "To sai ka zo na gode." Hajara ta ce dashi sannan suka yi sallama ta shige gida da sauri, a daidai tsakiyar soron gidan suka hadu da mahaifinta. "Sannu da zuwa Abba." Hajara ta ce dashi. 15 "Yauwa llajara, sannu Amin ne ya zo?" "Eh, shi ne Abba." Hajara ta tabbatar masa kanta a sunkuye. Tare suka shige cikin

Chapter 1 of 5