shekaru Ashirin a
duniya.
Alhaji Ahmad na da tarin arziki
amma bai taba haihuwa ba, ya dan yi
aure aure mata kala kala har ya zamo ya
fitar da rai da samun haihuwa, mutum
ne mai matukar neman mata kamar
wani dan akuya duk matar da ta yi masa
sai ya yi kokarin wajan mallakarta, baya
jin kyashin kashewa mace kudi ko nawa
ne.
Bai yi kauran baki ba wajen
bayyanawar Lawai bukatarsa, shi kam
Lawan ji ya yi kamar an tsunduma shi a
aljanna saboda farin ciki, godiya ya
116
Garari Hadiza Ado Yalwa
dinga yiwa Alha Ahmad kamar shine ya
bukaci wani abu a wajensa, shi ma
Alhaji Ahmad ya nuna masa cikin
gaggawa zai yi abin a cikin sati uku
kadai ya ke son Umaima ta zamo
matarsa, ya daice masa zai je wajen 'yan
uwansa su yi magana ba wai dai yana
son ja da maganarsa ba ne sai dai ya na
son samun wani abu a waje.
Ya kuwa sami yanda yake domin
kuwa Alhaji Ahmad dubu ashirin ya ba
shi sannan ya yi masa alkawarin cewa
tsintisya baya bukatar asaiwa Hansa'u
ya na da komai a gidansa.
Lawai bai taba hango amfanin
haihuwa mata ba irin wannan lokacin ba
dare ya yi amma bai iya rintsawa ba,
yana tunanin abin farin ciki da yanda za
a gudanar da shi sai dai duk inda ya
hanga ya hango sai yaga dole sai da
117
Hadiza Ado Yalwa Garari
Harira abubuwan za su tafi yanda
yakamata iyaye mata su ya dace su yi
irin wadannan maganganun da yayansu
don haka washe gari ya yi sammako
zuwa doka dan ya lallaßa Harira ta
dawo dakinta su shirya yoeda bikin zai
kasance, ya na zuwa kuna sai ya tarar
da mutuwa yayan Harira nan fa ya
zauna zaman makoki.
Har sai da yamma bayan mutane
sun rago ya aika aka kira masa ita suka
zauna a soron gidan, bai damu da
yanayin da fuskarta ke ciki ba, ya suma
da yi mata gaisuwa ta amsa ashe kuma
ba shi da lafiya ki ka taho baki gaya min
ba, kin ga ai dana biyo ki Allah ya raba
ganawarmu".
Ta gyara mayafi ni bama wannan
ne ya kawo ni ba, na dai zo ne na tarar"
118
Hadiza Ado Yalwa
Garari
Ya yi murmushi "Koma mene ne
ya dace a ni me iznina kafin a fito Allah
ya ji kanshi da rahama"
Ta amsa da amin. Ya mike "Ni
zan koma gobe idan an yi sadakar uku
sai ki taho gida in ya so ranar bakwai
din ba baki kudin mota ki dawo saboda
yara su kadai sai su yi ta abin da su ka
ga dama"
Ashe ina da rana ta fada a
zuciyarta ya yin da ya fito da kudi daga
aljihunsa har naira dubu uku "Ga
wannan ki shiga mota".
Ba ta da wani zabi dole ta sa
hannu ta karfa kudin domin ba ta da
zabin da yafi haka, ko da ta koma gida
ta kirga kudi ta yi matukar cika da
mamaki rabon da Lawan ya bata irin
wadannan kudade har ta manta ta san
baya yi ne don bikonta ba, lallai akwai
119
Hadiza Ado Yalwa Garari
wani dalili haka ta yi ta tunani cikin
ranta don haka ta dokanta gari ya waye
a gama komai ta taho gidan.
Dukkansu suna yin sallar
magariba a cikin daki, su ka ji sallamar
Ummansu aikuwa suna yin sallama suka
zagayaeta ita kuma fuskarta cike da
murmushin ta rungume Sayyada take
binsu da kallo. Ta fada musu rasuwar
wanda duk suka jimanta duk da ba wani
shakuwa su ka yi da shi sosai ba, tunda
bakasafai take zuwa da du doka ba, in
ma zata a a daren ranar Lawan ya
bayyana mata duk yanda abubuwan
suka faru.
Abin da ya fadar mata da gaba sati
uku da ya bukaci asa ranar bikin.
"Amma Lawan kamar an yi
gaggawa a cikin lamarin nan kuma
gaggawa na daga shaidan"
120
Hadiza Ado Yalwa
Garari
Ya katse ta "Ni tsiyata da ke
duhun kai, na gaya miki mutumin nan
ba mace a gidansa yanzu haka mutuwa
ta yi kin ga kuwa dole akwai bukatar ya
ajiye mace a gidansa da gaggawa a
matsayinsa na babban mutum kuma ma
ban da abinki ai talaka ke bukatar shiri
me kudi kuwa a shirye yake ko yaushe
ya ke da bukatar yin abu ya kawai zai yi
kawai ki gawa Umaima na yi mata miji
kuma gobe ya ce zai so su yi hira
Harira ta yi shiru amma zuciyarta
bata gama kwanciya da maganar auren
nan na gaggawa da kwadayi, ta ma
shiga zargin anya kuwa Lawan ba tallan
'ya'yanta ya ki ga masu kudi ba.
Aure irin wanda su za su yi komai
daga karshe in da zai girbi wulakanci da
kaskanci a saboda kwadayi ka dauka
masa farin ciki har karshen rayuwarsa,
121
Hadiza Ado Yalwa Garari
duk cikin yaranta tana jin auradda
Hansa'u yarinya ee da bata da wayo ga
ta da zurfin ciki kuma bata da hakuri
tana da taurin kai a kan abin da bata so
shi yasa take ciki da fargabar fada mata
har zuwa yammacin ranar zuwan Alhaji.
Sai da ta bari suna zaune duk su
ukun suna ta hira abinsu sannan ta
zauna a cikinsu ta yi shimfida da
gabatar da abubuwan da suke ciki na
damuwa da suke ciki sannan, ta sako
maganar da ta ta so wadda ta ke nuna
musu alkairi ce ga Hansa'u tun kafin ta
karasa ta saka kai cikin goyoyinta ta na
rasgar kuka fuskar mutumi kadai ta ke
hangowa da ta kaicin wai ita ya ke so
babansu ya fi shi kuruciya ga muni.
Wai ma ga Asiya a ce ita za a urar
dukkansa suka zube mata ido kukanta
ya tabbatar musu da cewar bata so dole
122
Hadiza Ado Yalwa
Garari
Harira ta shiga lallashinta Asiya kamar
ta hadiye zuciya ta mutu don bacin rai
ita kan ta tsani ganin abin da zai sa.
kannenta duk sai duniya tai mata zafi.
Da kyar suka shawo kanta da lallami
abin da tasa a ranta za ta yi komai don
farin cikin Ummansu kin amincewa
auren nan tamkar rugaza farin cikin
Ummanta ne kamar ta tunsar da ita.
Shiryen shiryen biki ya kankama a
cikin shiri har da na barin gidan domin
Alhaji Ahmad ya basu wani gida su
zauna a ciki a cewarsu baya son 'yan
uwansa su zo kawo lefe su ga wannan
kazamin gidan da suke ciki, ba lawan
kadai ba, hatta Hansa'u wannan barin
gidan ya yi mata dadi gida ne mai
dakuna cike da flour guda biyu da
kichin da bandaki gida mai kyau, sun
123
Hadiza Ado Yalwa Garari
tarar ya sa an shimfide musu leda da
labulaye har da gado.
Sabuwar duniya inji Uwani dake
shafar ledar tsakar dakin.
Yau ne ranar kawo kayan manyan
akwatuna da set cike d akaya na gani na
fada. Bayan 'yan kawo kaya sun tafi.
Jama'a sun rago Umma na idar da sallar
magariba,w asu mata gud abiyu suka yi
sallama Umaima ta basu masauki suka
zauna duk da bata gane su ba ta karbe su
da fara'a sannan ta basu tabarmar da ke
shimfide wadda baki suka ta shi daga
kai suka zauna kallo take musu na son
sanin daga ina ko su waye domin bata
tuno inda ta taba ganin fuskokinsu ba,
matar daya dattijuwa ce domin ko
bata haifeta ba, yanayinta ya nuna ta
soma manyanta.
124
Hadiza Ado Yalwa Garari
Dayar kuwa yarinyar mace ce da
alama amma bushewar da ta yi da
ramamman jiki yasa bata fahimci
wanda zai iya girmewa wani
tsakaninsu ba.
"Ba ki san mu ba kamar yanda
mu ma ba mu sanki ba, dattijiwar ta
katse mata tunani, "Eh wallahi ina
fatan ke ce mahaifiyar yarinyar da
Alhaji Ahmad a huta ya kawo yake
neman aurenta".
Gaban Harira ya yi wata irin
faduwa. Ta ce "Ni ce na haifeta".
Dattijuwar ta nuna yarinyar kusa
da ita "Kin ga wannan ni ma 'ya ta ce,
ta cikina kuma matar da Alhaji
Ahmad Ahuta ya aura ya saki,
shekarunta basu wuce sha takwas ba
yanzu ita ce ta tara da na haifa ita
125
Hadiza Ado Yalwa Garari
autata take bi, abin da ya kawo ni
shine sanin darajar haihuwa domin
kuw ana haifa kuma na san darajar da
kamar kowace uwa à takaice dai kin
ga yarinya rnan. tawa shekarunta
shidda kacal a duniya Alhaji Ahmad
ya aureta, bata cika shekaru biyu ba
ya sake ta
Labari ya yi ta zuwar mana yana
dauke da cutar kanjamau, don haka
muka kaita asibiti a ka yi mata gwaji
take likitoci suka tabbatar dacewar ta
kamu da ciwon shekaru biyu ke nan
da suka wuce tana jinya duk da
magungunan da ta ke karba a Asibiti,
wannan ya sa na yi tattaki don fada
muku gaskiya yanzu ya shafawa 'yan
mata sama da biyar da ya aura masu
Kanannun shekaru kamar na 'yarki".
126
Hadiza Ado Yalwa Garari
sharar Yarinyar ta soma
kwalla,"Wallahi son zuciya ya kai ni ga
aurensa, ga shi yanzu ya cuce ni, labarin
ina da cuta ya baza gari,kuma ku yi
bincike sosai, za ku ji a bakin jama'a
yawan aure -aurensa ya sa an gane don
Allah mama ki cici rayuwar 'yarki."
Harira ta sauke ajiyar zuciya daga
suman zaunen da ta yi, zuciyarta kuma ta
shiga rarraba mata maganganu tsakanin
gaskiya ne ko karya. Ta dai yi musu
godiya daga nan suka bar gida ta zabga
tagumi yanda ta ji labarin auri-sakinsa a
bakin Lawal da yadda ya ke son a yi
komai cikin gaggawa da yadda ya ke ta
nanata mata sai son tushe kuma daga
surutun mutane lokacin da ya zo gaishe
ta.
Duk sun nuna mata akwai abin da
yake son boyewa,in kuwa ma ga shi
dama yarinyar sam ba ta so ita da kanta
hankalinta ya kasa kwanciya da
127
Hadiza Ado Yalwa Garari
al'amarin,lallai ya kamata ta yi bincike
sosai don tabbatar da gaskiya.
Shin idan ta binciki gaskiyar Lawal
zai yarda da maganarta a fasa auren.
In kuma ya yarda da ina su ke da
kudin da za su biya shi wahalar da yayi
ta neman aure, ciki har da zamansa a
wannan ni'imataccen gida. Shin haka za
ta aura wa 'yarta me cutar kanjamau,
saboda yana da kudi?
Shin yaya aka yi Asiya ta samu
cikin jaririn hannunta? In gararin rayuwa
zai kai su ? duk amsoshin tambayoyin na
gaba mu hadu a cikin littafi GARARI na
2 wanda suka fito tare da na dayan nemi
naka ba jira. Yanzu labarin ya soma.
Daga mai debe muku kewa Khadija
Ado Yalwa(Khadija Adamu Shitu) don
yabo ko ba da 'shawara 09065291030 sai
na ji dga gare ku.
128
IBB BOOKSHOP
NOJ, SABON GARI MARKETKANO
07037690966
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
1. KOFAR RAGO
2. KARSHEN KIYAYYA
3.GARARI 1-4
4. AUREN DANGI
5.AUREN MATSALA
6. AUREN GATА
7. DA WALAKIN...
8. BAGIDAJIYA
9. BAKUWAR FUSKA
10. KARAR KWANA
11.BA HUJJA
12. DA BAMBANCI
13. DA RABON WANI
14. DINKIN KWALBA
15. BAKON AL'AMARI
Graphics And Computer Services 08099685635
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels