An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
IBB PUBLISHERS
GARARIHADIZA ADAMU SHITU (Matar Muhd.Nuhu Namarwa)
Hadiza Ado Yalwa
GARARI 1
Garari
maima ta fito cikin Utashin hankali da
tsananin 6acin rai, sauri
sauri take tafiya har ta iske Asiya da
jaririnta a hannun wadda dama tafiyar
tata kamar ta me sanda takeyinta.
Shi yasa Umaima bata wahala
ba wajan tadda ta. Shesshekar
kukanta kawai ka ke iya ji cikin sanyi
asubar "Yaya yaya Asiya".
'Umaima ta kirata cikin dakusasshiyar
murya da ta doshe sabodakuka.
Ta na jin muryar ta gane ta
kanwarta Umaima ce, amma sai ta
kasa juyowa ta hada ido da kanwar
tata inda wanda zai fahimce ta bai
4
Hadiza Ado Yalwa Garari
wuce kannen nata ba, amma sai ga shi
a yau tana jin kunyar hada ido da
Kanwarta Umaima tana matukar jin
kunyar kannenta da abin da ta aikata
ina ga sauran mutanen gari da wanne
ido zata kalle su yayin da gari ya
waye mata da jaririn shege a
hannunta, abin kunya ga al'adarta
babban zunibi ga addininta. Ta ci
gaba da sharar kwalla Umaima ta ci
gaba da binta tana sharar tata kwalla
tafiya suke yi ba mai wa wani
magana, ba kuma wanda ya san
takamaimai in da za su dosa a
tsakaninsu.
Abin da yafi tsayawa a kai Asiya
abin da ta aikata ba laifinta ba ne
amma babu yanda za ta yi ta kare
kanta, duk duniya ta san ba wanda zai
5
Hadiza Ado Yalwa Garari
gamsu da cewar ba laifinta ba ne, ba
itace a bar kyamarba ba mugun
halinta ba ne, ba rainuwa ko son jin
dadi, ko shi wanda ya aikata mata
bata hanglaifinsa a cikin faruwar
wannan babban al'amari ba,, to wa za
a dorawa laifin?
Ta dubi kanwarta ta wadda duk
in da ta sa kafa nan take mayarwa da
alama ba da niyar komawa ashirya take ta bita duk in da ta nufa.
Tana son ta yi maganā amma
wani abu mai daci ya nauyaya bakinta.
Ta sake dauke kanta zuwa daya
gefanta iska mai sanyi na ratsa
dukkan kofafin jikinta ta sake
rungume jaririn hannunta.
6
Hadiza Ado Yalwa Garari
..Ta dinga jin kamar daga ita sai
Umaima dake biye da ita sai kuma
jaririn hannunta suka rage a fadin
duniya iskar da sanyin asuba na sake
horowa ta sauke ajiyar zuciya tana
kallon hanyar da zata sa da su da titi.
Tunaninta ya lola can baya abin
da yafi tsaya a ranta.
**
Ga Umma ga umma yara biyu
suka shigo da gudu suna fada Aisya
dake kwance a tsakar daki ta mike da
sauri ta fito. ta shigo gidan da
sallama cikin sanyin muryar yanda ba
me iya jin sautin muryar tata sai dai
la66anta da suke motsa.
Uwani dake tankade a tsakar
gidan ta daga kai ta kai dubanta
7
Hadiza Ado Yalwa Garari
bakin kofar tana murmushi dai dai
lokacin da Harira ke cire mayafinta.
"Sannu kunsha hanya" in ji
Uwani ganin yanayinta kadai ya nuna
halin gajiyar da ta yi Asiya dake tsaye
ta ce "Umma Sannu da zuwa?"
Bata amsa ba saboda wani irin
jiri da yake dibarta ta zube a kofar
dakin.
Asiya ta juya da sauri ta debo
ruwa a randa ta mika mata ba musu ta
karba ta shanye tana sauke ajiyar
zuciya ko bata fada ba yunwa da
gajiya sun rufar mata.
Zaman da ta yi da ruwan da ta
sha ya saukar mata da 'yar nutsuwa ta
dubi Uwani "Tun safe da na fita nake
gararanba”.
8
Hadiza Ado Yalwa Garari
'Ai ko ba ki baďa ba ice ko an
dace?"
"An dace, mun samu daki daya
a gangaren 'yan garuwa".
'Kai madalla"
Asiva dake jinsu sai ta washe
bakin tana murmushi, yanda Asiya ta
karanci fuskar ta san akwai wata
damuwar shi yasa bata fadada
fara'arta ba, burinta su kebe da
mahaifiyarta ta ji mene ne damuwar,
tana alwala ta ce "Ina su Umaima,?"
Asiya ta ce "Sun je gidansu
Rabi'a".
Tana cikin maganar sai ga
Umaima ta shigo tare da karamar
kanwarsu sayya sayya ta tafi wajan
Umma da gudu tana cewa "Mun je
gidansu Aunti Rabi'a ta ba ni"
9
Hadiza Ado Yalwa Garari
Masarar da take ci ta mika mata.
Na ga Umma ta shigo An dace
kuwa?"
In ji Umaima.
"An dace Asiya ta bata amsa a
takaice.
Hamdala Umaima ta yi
"Wallahi na gaji da zaman gidan
nan musamman idan aka yi ruwa
babu mai rintsawa a cikinmu"
Asiya ta ja ajiyar zuciya "ni ina
ga ba mu ma taba zaman ukuba irin
wannan ba a hakan me kin ga tausaya
mana aka yi ita kanta uwani fa a
takure take kawai dai babu yanda ta iya ne ga zafi, musamman in an yi
ruwa bata da in da za ta yi girkinta fa
sai a daki”.
10
Hadiza Ado Yalwa Garari
Uhm "Yau da gobe sai Allah ni
dai na ji dadi da a ka samu dakin
nan.
Umaima ta sake maimaitawa
"Amma fa da sauran rina a kaba
tunda ba a gama biyan kudin ba
akwai ragowar kuma Umma ba ta da
su".
Nan da nan fara'ar da Umaima
take yi ta dauki "Baban fa har yau bai
zo ba"
"Bai zo ba?"
Asiya ta bata amsa a takaice.
Shiru ya gilma na tsawon lokaci
kowacce da abinda take sakawa a
zuciyarta har Hansa'u ta yi sallama
dukkansu babu ji ta ba ta sake
maimaitawa sannan Umaima ta dago
tana amsawa Hansa'u ta dubi
11
Hadiza Ado Yalwa Garari
fuskokinsu da gani akwai damuwa
gabanta ne ta ji ya fadi amma bata iya
tambayarsu ba ta dai ce "Umma ta
dawo ne?"
"Еh".
Asiya ta amsa mata "Tun
yaushe, bata jima da dawowa ba ta
shiga ciki.
Da sauri fargabarta kar a ce yau
ma basu samu hayar gidan ba, tana
shiga ta hange Ummansu na
gyangyadi a kan buhun da take sallah
don haka ta juya wajan 'yan uwanta.
Yara marasa mafadi ku kadai
kun damu mutane da guje gujen
banza da na wofi.
Muryar mahaifinsu ce ta karade
soron gidan su Ahmad da Mahmud
suka shigo da gudu ko wanne ya
12
Hadiza Ado Yalwa Garar
rakuße jikin koafar soron jikinsu ya
yi budu-budu kamar wadanda aka
tono daga rami, sai raba idanu suke yi
kan yayyensu dake soron cikin
tsananin tsoro da firgitar fadan da
mahaifinsu ke yi. Ko sallama bai
samu damar yi ba fada yake yi kamar
ya ari baki, yana kwalawa Hairara
kira kamar ba cikin dakin zai shiga
ba.
Tana cikin gyangyadinta
wannan sababin na shi ya farkar da ita
kafin ta yunkura ta ta shi ya karasa
shigowa ya tsaya dai dai kanta.
"Barci ma ki ke yi? kowa ya yi
abin da ya ga dama, kowacce uwa na
kokarin koyawa 'ya'yanta tarbiya ke
kina kwance kina barci kin bar duniya
su wancan dan banza Aminu yana can
13
Hadiza Ado Yalwa Garari
ramin da 'yan iskan abokansa suna
shaye shaye su kuma wadannan 'yan
kananun na kan yashi mutane suna
musu ta adi, wadan nan kuma da suka
koshi da rashin tarbiyar har na shigo
ban samu wadda ta iya daga baki ta
gaishe ni ko yi min sannu da zuwa ba,
yanda ki ka raina ni haka kika koyar
da su su raina ni"
"Haba Lawan ai dukkansu ka na
da ikon yi musu fada kai ma a
matsayinka na mahaifinsu, ba sai ni
kadai ba”.
"Ka da ki zage ni Harira ki iya
bakinki, kin ji ko”.
Ya ajiye bakar ledar da ya shigo
da ita yana gunagunin.
'ya'ya mata Gare ki abinda
kake yi min shi za su je suna yiwa
14
Hadiza Ado Yalwа Garari
mazajensu ba namijin da zai iya zama dasu".
Takaici ya hana ta sake yi masa
maganar har ya fita. A soro
dukkaninsu suna iya jiyo maganganun
da yake basu kadai ba duk ma wanda
yake cikin gidan yana iya ji.
Ya zo wucewa kamar kobubuwa
Umaimace ta iya cewa "Baba a dawo
lafiya".
Ko kallo bata ishe shi ba ya fita.
Gaba dayansu suka nufi dakin
da Umma take ciki ta hada kanta da
gwiwa kuka take mai sautin ban
tausayi.
Su duka suka duruksa a gabanta
Umaima da Asiya take su ma na su
idanu ya fara zubar da kwalla ban da
Hansa'u. Ita dai ta hada rai ne kamar
15
Hadiza Ado Yalwa Garari
bata taba dariya ba ko magana bata
iya yi muryar Umaima na rawa ta cе.
"Umma dan Allah ki yi hakuri
mu kukan nan naki muka fi tsana".
Umma ta dago kai idanuwanta
cike da kwalla cikin muryar kuka
"Kuntsani kukan nawa kuke jamin
magana".
Su duka suka kalli juna cike da
mamakin wacce magana kuma suka
ja mata.
"Yanzu ban da rashin mutumci
ace mahaifinku ya shigo kun kasa ko
da gaishe shi, in ba son kuja min
magana ba me zai sa ku yi haka so
kuke yi a dinga zagina a gari ana
cewa duka 'ya'yana basu da tarbiyya
kun min adalci kenan ta sake fashewa
da kuka."
16
Hadiza Ado Yalwa Gararf
Asiya ce cikin raunin tata
muryar ta ce "Ki yi hakuri Umma ba
nufinmu kenan ba wallahi ya shigo
yana fada ne shine duka muka ji
tsoron yi masa magana amma ki yi hakuri ba za mu sake ba"
"Ku ta shi ku ba ni waje"
Ta fada akagauce ba wadda ta iya yunkurin ta shi ganin har yanzu
Ummansu kuka take yi
"Ku ta shi na ce
Ta sake maimaita musu.
Umaima ce ta ce "To Umma kin yafe
mana
Ba wannan ke cin ranta ba tana
dai so ne kawai ta nuna musu
kuskurensu duk abin da ubansu yake
yi mahaifinsu ne ba ta son Allah ya
kama su da rashin yi masa biyayya.
17
Hadiza Ado Yalwa Garari
Kalaman Umaima na yanzu ya dada
karyar da zuciyarta hade da godiyar
Allah daya bata su a matsayin yaya
musu biyayya.
Ta dube su "Dukkansu na yafe
muku Allah ya yi muka albarka ya
inganta rayuwarku".
Cikin sauri suka amsa da Amin
Ummanmu. Asiya ta yi saurin
amsawa ta goge idanuwanta da bayan
hannunta, duk suka mike cikin sayin
jiki suka bar Sayyada da ke gefanta
tana sharar barcinta da guntuwar
masararta a hannun.
Komawa ta yi kan buhuta ta
kwanta wannan karon babu alamun
bacci a idonta sai kuna da radadinn
da zuciyartą take yi ta dora hannu a
saman fuskarta tunanin alamuran
18
Hadiza Ado Yalwa Carart
bayan suka ci gaba da kai komo
cikin zuciyarta
Hamisu yayan lawan shi ne
mazaunin cikin garin Kano, unguwar Yakasai Usulin dalilin zamansa a
cikin kano almajiranci aka kawo shi
ya yi karatu sosai daga karshe ya
soma taba 'yan sana'o'i Allah ya sa
mishi albarka a sana'ar sai da kayan
miya yana da babban teburi dinsa na siyar da danyan kayan miya wani lokacin ma har da busassu da sanar'a
ya yi aure 'yar nan unguwar ce
Habiba.
Ganin ayyukan na yi masa yawa
kuma Lawan kaninsa ya na zaune a
kauye ba abin da yake yi yasa ya
dauko shi ya ci gaba da taya shi
19
Hadiza Ado Yalwa Garari
harkokin sana'ar shi kuma ya sa shi a
makarantar Islamiya da Boko tun
kafin lawan ya baro kauyen sun hadп
da Harira a lokacin ya na da shekaru
goma sha takwas da Haihuwa ita
kuma bata fi shekaru sha biyu zuwa
sha uku ba, Lawan da Harira suna
matukar kaunar junansu, ya zamo
dukkan kauyen ba wanda bai san
wannań soyayya ba, ta kasance
marainiya da ba ta da uwa da uba tun
tana wata bakwai mahaifinta ya rasu,
aifiyarta ita ce ta shayar tana da
ckara biyu, mahaifiyarta ta rasu wanta
ya ci gaba da rikonta.
Dawowar Lawan birni bai sa ya
manta da Harira ba domin duk wani
marin neman aurenta an ci gaba da yi
Hamisu kuma shine ya dauki dawainiyar
yin komai tun daga karatu da neman auren
20
Hadiza Ado Yalwa Garari
lawan ci da shansa da suttura duk ya
na masa. Shi ma kuma yana kokarin
taimakon 'ya'yansa da matarsa wadda
ya ke cewa Adda har yau lokacin
Allah bai bawa Hamisu Haihuwa ba
shi yasa yake jilawan da kuma kani a
ransa.
Abu daya yake damun Hamisu
da Lawan shi ne shigewa masu kudin
unguwar, duk abokansa masu kudi ne
ya ke harka da su ga shi da karya da
son nuna shi ma fa wani ne, Hamisi
yasha nuna masa illar wannan dabi'a
amma ya gagara dainawa.
Kodayaushe cikin kawowa Hamisu
bukato yake yi shi kuma baya iya
hana shi kudi sai dai yana yawan yi
masa nasiha daga karshe da ya ga ba
ya jin nasiya kawai sai ya yi shawarar
21
Hadiza Ado Yalwa Garari
aurensu da Harira Yana ganin idan ya
ajiye iyali zai yi zuciyar neman na kai
da rage buri.
Wata bakwai aka saka rana
dakin da yake kusa da na shi yasa
aka fete shi tsaf bayan an gama biki
amarya ta tare a cikinsa, komai na
gidan Hamisu ne ke yi yawan abokai
wajan lawan abin sai Kara gaba da ya
yi idan a hanya ka gan shi za ka yi
zaton dan wani hamshakin mai kudi
ne a yanzu har mota lawan ya iya
yana kumawa hawa ta abokansa sosai
ya kan yi musu rakiya duk in da za su.
Yamma na yi ya ta shi daga
siyar da kayan miya zai dawo gida ya
dau wanka a shiga gari a dole yake
ma zaman siyar da kayan miyar
22
Hadiza Ado Yalwa Garari
domin idan bai zauna ba bayan da za
a yi ya dan samu kudin kashewa.
Harisa hankalinta a kwance
saboda bar a shi ci bare na sha sam
yawon maigidanta ma bai cika
damunta ba saboda kodayaushe tana
wajan Habiba idan ya zauna ma a
gida gwaliyarsa ke 6ata ranta komai
ta yi sai ya nuna mata ta cika
kauyanci bata iya ba ko Habiba da
take haifaffiyar birni ba ta gwale ta
kamar yanda yake yi.
Kwanci ta shi watan Harira
bakwai sai gata da karamin cikin wata
hudu wanda ita kanta Harira bata san
da shi ba, sai da ya bayyana kansa, ta
yi wani irin haske fatarta ta muje ta yi
wata irin cika daga kasa duk da dama
tana da dirin jiki. Ga ta da shegen
23
Hadiza Ado Yalwa Garari
kwadayi sabanin da da ba ruwanta
komai ci take yi. Habiba ce ta gano
nan da nan ta fadawa malam Hamisu
farin ciki a wajensa abin ba a magana.
Haka su ka yi ta yi ta kula da
Harira har Allah ya sauke ta lafiya ta
samu da namiji.
Lawan ya so a sama masa sunan
Hamisa amma sai ya yi dariya ya ce
sai dai a gaba, amma wannan dai
sunan mahaifinsu z a asaka masa
Mustafha. Haka kuwa a ka yi
Mustafha ya sha gata kulawa a
tsakanin iyayen nasa Habiba da Hamisu,.
Suna kiransa da Dan baba watan
dan Baba goma a ka samu cikin Asiya bai sha wahala ba saboda dama
24
Hadiza Ado Yalwa Garari
shan mama bai dame shi ba, ga shi
yana gudunsa ko ina.
Asiya na da wata uku wata rana
ta ame musu bakar rana da la'asar aka
shigo musu da Hamisu a galabaice
yana ta kwara a mai, Lawan ya na can
wajen abokansa bai dawowa sai
wajan tara na dare yana zuwa ya ga
yanda jikin yayansa ya ke ya samo
mota sai asibiti nan aka ba su
kwanciya saboda yagalaibata har ya
suma fita daga hayyacinsa, kafin
wayewar gari ya ce ga garinku
Hamisu Allah ya yi masa cikawa.
Ba karamin dokan Lawan
mutuwar Hamsiu ta yi ba, sai bayan
an yi arba in Habiba ta kira shi ta yi
masa nasiha sosai sannan ta dauko
jarin kayan miyar da su kadai ne
25
Hadiza Ado Yalwa Garari
Hamisu ya mallaka ta ce "Ga shi
Lawan ka ci gaba da kasuwancin nan
kamar yanda ka saba saboda ka samu
ka kula da iyalinka kullum Malam
zancensa ke nan na kamai da hankali
kan iyainka in mu ne yau watarana ba
mu ba ne.
Ashe malam ba zai tsahon rai ba
ta soma goge kwalla ta na kuka yana
yi da haka yakarbi kudin yana
godiya.
Ita kam ta hada yan komatsanta
ta koma ga iyayenta tun da babu da
bare jika a tsakaninsu. Lawan ya
maida hankali ga sana'ar yana kuma
samun rufin asiri sai dai burinsa ya
dinga kara yawaita yana daukarwa
kansa abin da yafi karfinsa.
26
Hadiza Ado Yalwa Garari
Sam bai damu da iyalansa ba, duk abin da ya
samu a harkar karya da abokai kawai suke karewa.
Rayuwa ta yi wa Harira kunci, daga ita har
yaranta, Lawan bai damu da su ba, balle sauran
al'amura na yau da kullum.
Harira ta yi rama, ta yi baki, ga karamin ciki
Harira. fada hantara da kyara a wajen Lawan sai
abin da ya yi gaba, domin babu mai tsawata masa
yanzu ma ji yake ya fi karfin zama da Hansa'u
saboda yadda 'yan matan birni ke matukar son shi,
shi ma yake kasha musu kudi,kamar bai san zafin
neman suba.
Abin na dada zuga shi,da sannu ya kwashe 'yan
kudadensa da yake Tarawa ya sayi sabuwar motar
hawa.
Al'amura suka kuntata wajen Harira, ba ta da
damar ta fada masa gaskiya da abin ya ishe ta,sai
ta kwashe yaranta ta tafi kauye wajen yayanta.
Ta shafe kimanin watanni biyu, Lawan bai zo
ba,dole ta sa yayanta ya je wajen kanin mahaifinsa
ya fada masa,idan ya saki auren Harira ne ya sani.
Hankalinsa ya tashi sosai,ya ba wa yayan Harira
hakuri, sannan ya tashi da kansa ya je har wajen
Lawan yayi masa fada sosai,ya kuma nemi lalle ya
zo bikon Harira da kansa.
Bayan ya gama cinikinsa na yamma suka tafi tare
da karya da gaskiya Lawan ya tsara, amma ba
27
Hadiza Ado Yalwa Garari
wanda ya goyi bayansa,saboda su ma sun fara
ganin halin Lawan na rashin daukansu da daraja.
Ba kamar dan uwansa Hamisu ba,nauyi ma yake
ji ya kalle su a wajen wadansu, shi ya sa ko zuwa
digansu ba sa son yi saboda yadda yake nuna musu
halin ko-in-kula da nuna rashin jin dadin zuwansu
Kiri-Kiri.
Sun dai yi masa nasiha, ya yi kamar ya ji, saboda
shi da kansa ya ji jiki a rashin Harira a kusa da shi.
Yayanta yayi mata nasiha sosai ya kuma ba ta kudi
da kayan amfanin gona masu yawa, matarsa ta
hada mata su Kuka, Daddawa, Kubewa suka dawo.
Da farko kamar da gaske Lawan ya dinga kulawa
da su amma ko wata biyu ba a yi ba ya watsar.
Ba ma ya dawowa cikin gidan,sai ya raba dare,
haka da Assuba yake fita sarin kayan miya.
Zara ba ta barin dami, tuni jarin kayan miyar ya
karye, ya soma haya da motar da ya saya.
Nan ma ba a jima ba ya siyar da motar haka
kudin suka lalace. Lawan rayuwar manyan masu
kudi ya dora kansa a kai,ko hularsa da agogon
hannunsa sun isa jarin wani mai karamin karfin.
Bayan haihuwar Hansa'u Umaira ta ga lamari
Lawan ba na kare ba ne, hatsin da yayanta ya aiko
mata da shi na gonakinta na gado, ta siyar da buhu
daya jari ta ja jarin basassun kayan miya,dayan
kuma ta soma sayar da gasara.
28
Hadiza Ado Yalwa Garari
Nan da nan ta samu saukin
al'amura ta shiga kula da kanta da 'ya'yanta ba ji ba ga ni. Har ta haifi Umaima matsalar da tafi damun
Harira tun wancan lokacin har zuwa
yanzu bai wuce yawon haya ba, saboda dai lawan tun bayan rasuwar
Hamisu biyan kudin hayar gidan ma
ya gagare shi saboda dama can
Hamisu ne yake biya masa wannan ya
zama dalilin da yasa a ka tashe su, daga gidan ke nan ya zama dalilin da
yasa aka tashe su daga gidan ke nan
bayan barinsu gidan zuwa yanzu sun
zauna, a agidajen da ban daban sama
da kusan goma sha daya, domin wani
gidan ma basa rufa shekara saboda
basa iya biyan kudin shekara sai dai
naw ata shida shi ma idan watanni ya
29
Hadiza Ado Yalwa Garari
cika basa iya biyan wani sai dai a
tashe su.
Jarin kayan miyan lawan tuni ya
dade da rushewa har gonar Harira ta
gado ta matsawa wanta sai da ya ba
da gonarta aka siyar kusan har fushi
ya yi da ita mai tsananin saboda siyar
da gonar da ta yi ko watanni shida
kudin basu yi a hannun Lawan ba ya
cinye su tsaf.
Yawan cudanya da yara marasa
tarbiya Dan Baba yake yi shine ya
gurbata rayuwarsa tun yana dan
shekara goma sha uku ya soma shaye
shaye hankalin Harira ya yi matukar
ta shi amma babu yanda ta iya saboda
daki daya suke iya kama haya, da
'yammantan yayanta dole shi sai dai
ta nemi alfarmar kwananshi a shagon
30
Hadiza Ado Yalwa Garari
makota ko gidajen abokan arziki da
haka tarbiyarsa ta gurbata a yanzu
haka sai ta shafe wata guda ma bata
sa shi a idonta ba, irin ma ta ganshi
gani ne na bakin ciki da takaici
saboda kullum yana cikin maye.
Bola ta zame masa gida da
sunan sana'ar jari Bola yake yi baya
iya tsinanawa kansa komai kayan
maye ne abokin rayuwarsa.
Wannan rayuwar ta dan Baba ita
ce ta tsorata da ita wajan dagewa a
akan karatun sauran yara da anta ta
saka su a makaranta boko da islamiya
duk da yanayin rayuwar da suke ciki
baya barinsu zuwa makaranta kullum
kamar sauran yara amma suna cikin
dalibai kuma suna maida hankali 'yan
mata yaran sun zame mata sanyin
31
Hadiza Ado Yalwa Garari
idaniya suna matukar yi mata biyayya
da tausayin da kaunar. junansu ta
tsaya tsayin daka wajan kula da
tarbiyarsu daga makaranta sai
sana'arsu suna da juriyar da jarumta.
Suna tsara komansu ta yanda zai
yi dai da da rayuwarsu.
Mutum biyu ne ke fashin
makaranta na kwana biyu saboda
suyar awara da ta yi kwana biyu tana
zuwa sannan wata ta zana kwana biyu
da haka sukan kare satin karatunsu
basa zuwa makarantar yamma sai ta
magariba da ta dare saboda aikin
awarar yamma.
Bakaramar tangarda suke samu
ba saboda canje canjen wajan zama
wani lokacin a wannan dalili sai jarin
32
Hadiza Ado Yalwa Garari
ya kare tas sun yi zaman neman sabo
sannan su dora.
Umaima ce ta iya kitso sosai a
cikinsu yara na zuwa ta na yi musu ko
ta je har gida ta dan yiwa matan aure
ta na samu sosai wani lokacin ma d
kudin kitson suke ta da jari.
Sun so zama sosai a gidan da
suka baro saboda sana'arsu ta
bunkasa sosai a gidan har suka samu
faragar su ma tara kudin haya.
Sai dai kudin bai cika ba har
lokacin karbar kudin ya yi dama suna
da labarin rashin mutumcin mai gidan
don haka Ummansu ta je da kanta ta
kai masa rabin kudin ta ba shi hakuri
a kan za a ciko kamar gaske ya nuna
mata ba koma da kudinta idan ta ciko
ta kawo masa. Ta ji dadin hakan ta yi
33
Hadiza Ado Yalwa Garari
ta yi masa godiya yanda ta ke
tsammaninsa ba ta taba tunanin sauki
haka daga gare shi ba, amma me ta na
komawa gida ta tarar da ya datsawa
dakin wani katon kwado gaba daya
yaranta na tsakar gida ta rasa in da za
ta saka ranta dan bakin ciki da takaici
daga karshe dai ta kira me yanke dan
mukulli ya yanke suka shiga.
Washe gari kuwa sammako ya
yi da manyan mutane suka fitar musu
da kaya titi.
Lawan yana gidan a lokacin ya
yi ta ba shi hakuri bai saurare shi ba,
sannan ya ce da Harira su tsaya anan
yana zuwa, ya tafi Lawan bai dawo ba
har rana ta tarar da su sai asoron
makotansu suka zauna ganin yanda
garin ya yi bakikkirin wani
34
Hadiza Ado Yalwa Garari
gangamemen hadari na tasowa ya sake ta da hankalinsu ta soma kaiwa
da komawa a cikin unguwar ga yara
sun yayyame kayan sunata tsallae
tsallaensu a kai, a nan ne suka hadu
da Uwani wadda sun taba zaman haya
da ita a wani gida danta a yanzu ya
gina mata gida mai dakuna biyu da
kichin da bandaki, ita ce ta tausaya
wa Harira ta kwashe kayan kichin
dinta ta hada a daki daya suka zauna
a kichin din da yake ya na da dan
girma makota kuma suka yi mata
alfarmar ajiye kayanta a soron gidan
su kafin su samuw anda za su zauna.
Komai da sauri suka yi shi
saboda ruwa ya soma sakkowa sun
haďu a cikin dakin da aka basu ruwa
ya tsoge sai dai babuw anda ya samu
35
Hadiza Ado Yalwa Garari
zama c ikinsu saboda yan da ruwa ke
shigowa dakin cikin ta jikin kofa gara
shi wadatar gurin zaman a hakan sun
cika da godiyar Allah saboda ruwan
bai sauka a kansu da kayansu ba.
Lawan ba shi ya shiga in da suke
ba sai washe gari ya yiwa uwani
godiya sosai ya zauna har ya ci abinci
ya na ta nunawa Harira shi ma ajiyan
yana can ne ya na nema musu in da
zasu zauna ruwan jiyan nan ma a
kansa ya kare.
Kwanan gida ba zai yiwu a gare
shi ba sai dai lokaci zuwa lokaci ya
shigo ya