na ma lura bakin
halinki ya hanaki sabo da matan
gidan".
Ta inda ya ke shiga ba ta nan
yake fita ba. tana jinsa ya na ta miota
a haka har bacci ya dauke shi. ita kam
bata rintsa ba a haka har a ka yi sallar
asuba.
**
Da sanyin safiya dai-daikun
mutane ka ke ga ni Umaima cikin
kayan makaranta, A nutse suke
tafiyarsu saboda tabbacinsu na cewar
sammakon da suke daka na iya kaisu
mkaranta ba tare da sun makara ba,
duk kuwa.
77
Hadiza Ado Yalwa Garari
Nisan da ke tsakaninsu da
makaranta. 1
Asiya na tsokanar Umaima da ta
zama sabuwar dalibar ajin farko na
babbar Secondary (SS1) rawar
kannan na ki ke damu na Umaima,
satin nan sam kin hana ti baccin safe
da asuba, kin fara shirin makaranta ni
na rasa me yake dibanki ko dokin
sabon kayanne oho".
Ta dubi farin hijab din Umaima
da yake daukar ido ga gurgar da
yasha, su ka yi dariya gaba daya.
Umaima ta ce "Ba za ki gane ba
ne yaya shigata ss 1 din nan kuma
ajin da na fi so (Science class), yanda
na fitar da rai da karatun nan kuma na
same shi ai dole...
78
Garari
Hadiza Ado Yalwa
Ta kasa karasa abin da take fada
idanuwanta na kan Hijabdinta da
wani mai mota ya watsa wa
jikakkiyar jar kasa.
Allah ya isa ba za mu taba taba
yafewa ba, mugu, yanda ka bakanta
mana ka cutar da mu a sanyin safiyar
nan Allah ya hada ka da mummunan
bakin ciki, Asiya ke nan da take ta
jerowa me motar manyan alkaba'i
wadanda ita ma bata san ta na fadar
su ba saboda Gacin rai.
Umaima dai kasa magana ta yi
saboda takaici sai ga hawaye na
silalowa daga idanunta, jar kasa ce ta
yi face face a jikin farin jijab din,
ganin hawaye a idon Umaima ya sake
nunka bacin rai a wajan Asiya ta
dago kai don ta nuna masa wata mai
79
Hadiza Ado Yalwa Garari
dacin, ga mamakinta sai ga ni ta yi
yana ja da haya, "Wallahi bazan
saurara maka ba kama dawo din”.
Ta zubawa motar ido har ya
dawo dai dai in da suke kakin dake
jikinsa kadai ya isa ya yi mata
kwarjini, bare shi kansa, kwarijin da
ta hanga a idonsa bai sanyaya
jikintaba, shirye ta ke ta gaya masa
koma menene in dai shi ma zai ji zafi
a ransa.
Ya sauke ajiyar zuciya ya jima
bai ga wanda ya dubi tsabar idonsa ya
yi masa irin wannan kallon ba bare
wannan muguwar addu'ar da bai taba
cin karo da ita a rayuwa ba, wannan
dalili ya sa shi juyawa kalma daya ya
yi niyar fada musu ku yi hakuri, to
80
Hadiza Ado Yalwa Garari
amma yanayin kallon da take masa
cike da tsiwa da tsana.
"Ke ashe ba ma ke na bata ba
kike wa mutane tsiwa da surutu
kamar tabaбbiya".
Cikin dakiyar murya ta cе
"Gwara ka 6ata ni da ka 6ata Umaima
a sabon Hijab dinta dubi abin da kai
mata, ita kam Umaima tunda ta
ganshi kwarjininsa ya firgita ta
wannan ko dan sandane babbane, ko
custom ne ko dai wane ne me
damarar me kuma babban matsayi, ga
yanayinsa da ya nuna hutu zalla ne a
jikinsa, tun tsayawarsa wani kamshi
da yake ta shi, gaba daya kwarjininsa
yasa tsoro ya kama Umaima ta ja
hannun Asiya da take ta zazzaga masa
81
Hadiza Ado Yalwa Garari
masifa "Dubi abin da kai mata haba
malam".
"Kyale shi Yaya Asiya kin san
masu mukami a kasar nan ba adalci
gare su ba, kada ya samu abin da ba
zamu iya fitar da kanmu ba".
"Ko ma me zai mana sai dai ya
yi mana amma ba zai yiwu ya yi
mana laifi mu ja baki mu yi shiru ba,
saboda muna tsoron sharrin da zai
mana agaba".
Umaima ta share kwalla da
bayan hannunta don Allah ki yi shiru
yaya kada hankalin mutane ya koma
kanmu wallahi duk gaskiyar da muke
da ita şhi za a bawa hakuri, mu kuma
duk abin da zai faďa a kan mu dole a
yarda.
82
Hadiza Ado Yalwa Garari
Asiya ta yi shiru ita ma share
kwallar take, har lokacin yana tsaye
ya kuma tsira musu ido yana kuma
juyo maganmganun Umaima da take
yi kamar rada, ya dinga jin wani irin
yanayi na shigarsa wanda yasa ya
gaza kowane irin tunani komansa ya
tsaya cak!, kalaman yaran kadai ke
yawo a tsakiyar kansa, sai zuciyarsa
dake tsananta da ci, yanayin kasala
kuma na hana shi yin wani katabus.
Da nannauyan jiki ya soma
tafiya cikin motarsa har zuwa gidansa
da ke kan titin Airport road cikin
rukunin gidajen 'yansanda yana shiga
harabar gidan ya hango yaransa a
shirye tsaf suna ta tsalle tsallensu tana
taku kadan kamar wadda jiri ke
dibarta ya fito daga mota da sauri ya
83
Hadiza Ado Yalwa Garari
taro ta hade da fadin "Subhanallah
kamar dole Jidda ba ki da lafiya dole
ne fitar. Amir Abba".
Ya kwalawa yaransa kira "Ku zo
99
nan.
Ya rungume ta a hankali ya
rada mata "Is ok."
Za ta yi magana ya dora
danyatsanshi a a kan leßanta "Ki yi
shiru na ce miki mu shiga ciki ko".
Ba ta musa masa ba amman sai
ga hawaye a fuskarta, bai hana su
zuba ba saboda ya san yanda take ji a
yanzu ko da kukan bakin ciki har da
nå farin cikin don bata taba
tsammanin dawowarsa yanzu ba, basu
tsaya ko ina ba sai akan gadon
baccinta. Da kanshi ya janye mayafin
da ta yi lullubi da shi ya gyara mata
84
Hadiza Ado Yalwa Garari
filo ya kwantar da ita, kamar dama
kwanciyar take bukata ta takure ta
rukunkume pillow hannunta daya a
kan goshinta.
"Ciwon kan da yake addabarta
bai saurara mata ba, su Abba suka
shigo suna cewa "Mama ki zo mu je
unguwar"
Ya dora hannunsa kan lebansa
alamar su yi shiru sannan ya nuna
musu kofar fita, suka fita daga dakin.
Ya riko hannunta "Yunwa ko?"
Ba ta ba shi amsa ba, sai ido da
ta bi shi da shi na tsananin mamaki
wai Muktar ne wannan ko mafarki
nake.
Ya san abin da ke damunta don
haka bai jira amsarta ba ya mike hade
da cewa "Ina zuwa".
85
Hadiza Ado Yalwa Garari
Yana fitowa ya hadu da yaran
sun nutsu a kan kujera suna murza ido
alamun kuka suke ya duruksa а
gabansu ya rike hannun Abba, wanda
shine babba zai kai shekaru shida,
wanda shine Babba Umar shine
ainihin sunansa saboda ya ci sunan
mahaifinsa yasa ake kiransa da Abba,
sai Amir Kaninsa dake shekararsa uku
wanda ya ci sunan kawunsa Usman.
Ya ce "Haba Abbana kai ne
babba kuma kasa. kanninka a gaba
kuna kuka"
Ya mike "Ina ku ke son zuwa?"
Da sauri suka hada baki "Gidan
gwaggo".
"To na ji kirawo min driver, ya
kai ku".
86
Hadiza Ado Yalwa Garari
Nan da nan suka fita suna tsalle.
Ya bi bayansu yana murmushi Bilya
direba ya kara so suna rike da shi
Abdul ya mika masa mukullin bude
store.
"A debo shinkafa buhu da mai
roba daya ka shigo nan a daukiw asu
kayan a kai gidan Gwaggo tare da
yara nan.
Bilya ya sara masa "To ranka ya
dade".
Sannan ya juya shi kuma ya
koma ciki dauko lemoka ruwa da
sauran kayan bukata ya sa kudi a
embelope ya bawa Bilya ya kaima
Gwaggon.
Wani rin dadi ya dinga ji rabon
da ya yiwa gwaggo wata kyauta irin
haka har ya manta. Kichin ya koma
87
Hadiza Ado Yalwa Garari
ya dafa indomie sannan ya hada mata
tea mai kauri.
Har baccinta ya soma nisa ya
zubowa fuskarta ido ba karamar rama
kyakkyawar fuskarta ta yi ba, sai
wani irin haske. Gashi kwance a
gefean fuskarta dan karamin bakinta
a tsoke ko cikin bacci Jidda
kyakkyawar gaske ce mai matukar
hakuri.
Ya sauke ajiyar zuciya sam ta
rasa kulawa daga gare shi lokuta da
dama anya kuwa bata yi masa
mummunar addu'a cikin ranta kamar
yanda yarinyar dazu ta yi masa karara
yake hangen rashin adalcinsa, a kanta
lallai Allah na karbar addu;ar wandá
aka zalunta. Yanayin da yake ji ya ci
88
Hadiza Ado Yalwa Garari
gaba da mamayar sa irin yanda bai
taba ji ba.
Ta so ta dan juya jikinya ya bata
kamar akwai mutum kusa da ita ta
dan bude ido dan tuni ma ta manta da
Muktar a a gefe ya na gidan domin
rabonta da ya shigo ya zauna tare da
ita tsayin lokaci har ta manta.
Ta dora idanuwanta a kansa
yanda ya zuba tagumi yana kallonta
sai ta ji har gabanta ya fadi. Anya
kuwa ba wani abu ya faru da Muktar
ba, sai ta ji ba ta iya komawa bacci ta
mike zaune ya dan yi murmushi hade
da sauke ajiyar zuciya "Dama dai ba
bacci ki ke yi ba, gara ma da ki ka
mike wannan ramar da ki ka yi haka,
duk na san rashin cin abinci ya janyo
ta, ba ainihin ciwo ba".
89
Hadiza Ado Yalwa Garari
Ya so ma hada mata tea da
kanshi ya dinga bata har sai da ya
tabbatar da ta koshi bai bar gidan ba
har zuwa karfe biyar na yamma da
ma aikin dare ne da shi cikin
kwanakin nan wanda ko ita Azimar
bata san da haka ba, duk kowa da tana
matsayin matarsa ya haranta mata
shiga dukkan cikin wasu al'amura
nasa.
Yau rana ce da a rayuwarta da
ba zata manta da ita ba ita rana ce da
ta dade da fitar daren za ta sake
dawowa a rayuwarta da. Ranar da ta
samu kulawa daga Muktar kulawa da
soyayya abin tamkar almara haka a
office din sama din sama jama'a da
yawa kė mamakin laushinsa a yau
wanda har wasu ke kasa hakuri garin
90
Hadiza Ado Yalwa Garari
canjin daga gare shi su ce "Oga yau
kuwa kana lafiya".
Amsa daya ya ke basu ta lafiya
kalau. Shi da kansa ya tantance da
cewar lafiya yake, wannan yanayi da
ya ji jinin da tsoka gabоbinsa da
ilahirin jikinsa yake sanyaya shi yafi
masa kama da shigar ciwo sai dai bai
jin wani ciwo a cikin jikinsa, wanda
zai dauka ya zama ya tabbatar da
cíwo ke damunsa..
Abu daya ya san na yawo a
tsakar kansa nadamar rashin bawa
yaran nan hakuri bayan sun yi masa
miyagun addu'o'i, ba wai girman
laifin da ya aikata musu ne ke
damunsa ba, usili shi mutum ne da
kansa kadai ya sa ni baya daukar
matsalar wani a matsayin abin da zai
91
Hadiza Ado Yalwa Garari
dame shi mutum ne wanda ya dauki
tausayi ba a matsayin abin yinsa ba in
har ka ga murmushinsa a kan fuskarsa
to ba karamin abu ne ya faru ba, abu
daya yake bawa muhammanci a
rayuwarsa aikinsa. Sannan abu daya
ya fi so a rayuwa a yi masa addu'ar
alkairi.
Sannan abin da yafi tsana
zalunci bai da abokin hira ko me ba
shi shawara yana dauka tunda ya rasa
iyayensa bai da sauran gata shiru shi
kadai ne ba wanda zai tausaya masa
shi ne gatan kansa shine dangin
kansa, shi kadai ne kansa, ka dan ya
sa ni da rayuwar da ya ta shi ke nan
tun farko shi yasa wadannan akidu
suka zama hallayarsa.
92 4
-
Hadiza Ado Yalwa Garari
Abinda ya faru a yau ya dinga
hasakaka masa wasu abubuwa da
suka zamewa rayuwarsa duhu ya kas
agane shi yake ta tafiya cikin duhu
fitilar da ta haske su, kalaman yân
matan nan, rayuwarsa ta baya ta zame
masa rayuwar da komai ya yi ba dai
dai ya yi ba, makusantanshi kan
aibata shi laifi da nasa da ba na sa ba
duk akansa a ke dorawa ya zama abin
har tara abin kyama ba dai ya na da
wani aibu ba na rashin kyawun hali
gudun da ya yiwa Illa maraici da
talauci.
Dalili talauci neya mai da shi
maraya maraici kuma ya mai da shi
mara galihu wadannan abubuwan
suka kangarar da shi suka tafi da
murmushi da dariyarshi suka dauke
93
Hadiza Ado Yalwa Garari
tausayi daga zuciyarsa ya zamo bai
ganin girman kowa har lokacin da ya
kawo wannan matsayin wanda a
yanzu wadanda ma ba jininsa ba suke
son kasancewa da shi danginsa suke
alfahario da shi bakunan kowa ke
fadar alkairinsa duk a yau ya hango
aibiunsa da mutane sun san da shi sun
kuma san yana munana musu amma
saboda matsayinsa ba wanda zai
tunkare shi da fada masa gaskiya, ko
nuna 6acin ransa bare har ya gyara
duk abin da yake yi. Addu'ar
alkairice ake masa a gaban idonsa a
bayan idon kuma fa mai duniya ta
dauke shi?
Duk wannan bai da sani ba
kuma ya tunanin sanin sai a yau da
94
Hadiza Ado Yalwa. Garari
haske ya haskaka duhun da yake
tafiya a cikinsa.
Lallai akwai abin da ya kangara
zuciyar 'yammatan da suka dinga
zazzaga masa masifa batare da ganin
girmansa ba, karshe suka raka da yi
masa mummunar addu'ar, to mene ne
ya tunzuro su haka?
Wane kuncin ne wanda ya tuno
da ta shi rayuwa haka. Su ma nan
gaba in sun girma suna iya zama
masu halayya mara kyau saboda
kangarewar zuciya, sun dauki dukkan
masu mukamin mara adalci, ćiki har
da shi, kuma ba karya su ka yi ba,
aikata rashin adalci ya zamo
dabi'unsu da hannu biyu ya ja tagumi
bai san lokacin da hawaye ya soma
zuba daga idanunsa ba, adadin
95
Hadiza Ado Yalwa Garari
mutanen da za su yi masa Allah ya isa
da mummunar addu'ar bai san
yawansu ba, bai kuma san inda zai
gansu ya nemi gafararsu ba, ina zai
kai tarin hakkin. Da yake kansa ya zai
yi da munana ayyukansa
Gaba daya zaman office din ne
ya ji yana neman gagararsa yanayin
da yake ji na neman kwantar da shi
mike wa ya yi yana sharar hawayen
fuskarsa ya dauki rigarsa da ke jikin
kujera ya kira wani Sajan "Zan wuce
gida bana jin dadi ne in akwai wata
matsala ka kira ni a waya".
"To Oga".
Ya sara masa haka ya dinga
wuce su suna sara masa shi ma yana daga musu hannu suka cika da
96
Hadiza Ado Yalwa Garari
mamakin don abin da bai taba yi ba
kenan.
Kyautarsa ce ma ke sawa suke
ganin kimarsa dan shi mutanne mai
yawan kyauta amma ba shi da sauki
ko kaďan zafi ne da shi kamar zazzabi
baya jin ban baki ko magiya Sajan
din su biyu da suka kame suka kalli
juna bayan ya wuce.
"Oga Allah yasa ciwon nan nasa
na yau ba kamun mala'iku ba ne"
Dayan ya kwashe da dariya
"Mala'ikun ka ga ni tare da shi ko
me?"
Ya sake fadin haka sajan Bala
na kokarin zama akan benci kamar
dai yana tare da su "Ka ga yanda ya
yi laushi har yake iya daga mana
hannu abinda ban taba gani ba tunda
97
Hadiza Ado Yalwa Garari
na zo wannan gidan kuma ai yana
cuta katuna kwanaki har kwanciya ya
yi a Asibiti amma fuskar nan ta shi
bata sauya da komai ba, in ka ga ka yi
masa magana sau dubu wacce bata
shafi aiki ba ko da kuwa gaishe shi
kake yi ba zai saurare ka ba, dayan ya
ce "Na yarda da maganarka. In dai
hake ne kila saukin mutuwar ne ya zo
masa.
"Ni dai addu'ata koda koda ya
mutu Allah ya kawo mana mai dan
sakin fuska duk walwalar da na ke
ciki da na ga fuskarsa sai na ji ta kau,
lallai ne murmushi ga dan uwanka
musulmi shi ma sadaka ne manzon
Allah ya yi gaskiya"
"Kuma shimfidar fuska tafi ta
tabarma" in ji Bala
98
Hadiza Ado. Yalwa Garari
**
Lokacin da su Umaima ke tafiya
ba ta fasa sharar kwalla ba, ita kuwa
Asiya nata dudduba inda za su samu
ruwan da za ta wanke wa Umaima
domin a ganinta har da ma ganin da
take yiwa Jijab din yake kara tunzura
zuciyarta take ta faman kuka, ita
kuma da ta tsani ganin ta na yi a
zuciyarta na tafarfasa hanyar titi ne
sosai.
Daga kamfanoni sai shaguna
sam ba ta hangi wani gida ba, don
haka bata hangi inda zata sami ruwa
ba, wata mota ta hango ta tsaya kusa
da su ta nata horn, sam basu kawo
mai motarsu ya tsayawa ba, sai da
suka zo daf da motar sannan suka ga
glass din motar na sauka a hankali".
99
ر
Hadiza Ado Yalwa
"Ke sarkin makara”.
Garari
Sannan ta juya sai kuma ta yi
murmushin ganin principal dinsu cе
wadda saboda tsabar yawan
makararta ta gane ta har tasa mata
suna Sarkin makara, ta kuma yi
bincike a kan yarinyar ta gane tafiyar
kasa take yi da kuma halin yau yasa
take yawan makaran, yanzu ko ta
makarama ta hana a tsaida ita sun
durkusa don gaishe ta ta ce "To ku
shigo mu karasa".
Nan fa suka shiga kokawar
yanda za su bude motar don wannan
karo na farko da suka fara shiga
karamar mota, Asiya ta yi nasarar
budewa ita kuwa Umaima ta zauna a
gaban inda Hajiyar ta bude mata.
100
Hadiza Ado Yalwa Garari
Hajiyar na tuki "Ke kuma me ya
same ki ki ke kuka”.
Ta kalli Umaima da har yanzu
yanayinta na mai kuka ne ta ware
Jijab dinta inda ta cukuikuye inda ya
baci "Ba wani ne ya 6ata min sabon
hijab di na ba".
Hajiyar ta kalli Hijab din sannan
ta mai da kanta kan titi
"Saboda ke kuma 'yar sarkin
shagwababа6бuce shine ki ke kuka".
Bata sake magana ba har sai da
suka isa makaranta ta dubi Asiya "Mu
je office ki karbar mata wani, ke
kuma wuce ki wanke a wancan
famfon".
Ta dauko sabon Hijab ta bawa
Asiya tare da cewa "Kanwarki cе”.
101
Hadiza Ado Yalwa Garari
Nan da nan annurin fuskar Asiya
ya bayyana "Knwata cсе"
Sannan ta durkusa ta nanata
godiya. Principal ta ce "Ba komai ku
yi maza ku je aji kar a fara darasi"
Ta window ta mika wa Umaima
sabon Hijab din saboda kiran da
monitar ajinsu ke yi mata a yau ita ce
da sharar aji.
Sai da aka fito sannan suka hadu
nan fa hirar dadin motar principal da
karamci da ta yi musu duk da tsabar
kwarjininta da ya yanda take dakawa
yara tsawa, mamakin yanda ta yi
musu suke yi, tuni ma sun manta da
takaicin da suka hadu da shi a hanya.
orSu dawo gida suna bawa
Ummansu labarin abinda ya faru, duk
yanayinta ya koma tamkar na mara
102
Hadiza Ado Yalwa Garari
lafiya duk tambayar da suke damunta
da ita na mai yake damunta ba komai
shine amsarsu sai dai abin da ke cin
zuciyarta yanda suka yi jiya da Lawan
kan maganar Alhaji mai icce, sai
yanzu ne ta gama gane Lawan sam
bai dauketa a macen aurensa ba,
tunda ba zai ma iya kare mata
mutumcinta ba, shawara daya ta gama
yankewa gobe da safe ta je garinsu
kawai ta fadawa yayanta ta gama
gajiya da aurensa 'ya'ya kuma zata
bar masa su in ya so ya dafa ya cinye
su ai 'ya'yansa ne.
Da sanyin safiya ta shirya ranar
Asiya ce bata je makaranta ba, tana
ganin Ummansu nasa kayanta a leda
duk jikinta ya bata akwai wata
damuwa tana son tambayarta, amman
103
Hadiza Ado Yalwa Garari
ba ta ga fuskar hakan a wajenta ba,
don ko magana bata son yi babu
walwala kwata kwata a tare da ita.
Zargin Asiya bai gama tabbata
ba sai lokacin da ta ga har sun kwanta
Ummansu ba ta dawo ba sun kasance
cikin tashin hankali wanda ya hana
kowacce su rintsawa sabanin Lawal
da ya yi baccinsa har da munshari.
Bai yi tsammanin wannan 'yar
magana zata iyasa Harira ta bar gidan
ba.
Duk da ba wannan ne karo na
farko da suka fara samun sabani tana
kai kararshi ga iyayenta ba, amma dai
wannan karon ransa ya yi matukar
baci abin da ya dauka rashin godiyar
Allah ne kawai iri nata yasa ta gaza ta
biyo masa ta wannan hanyar don haka
104
Hadiza Ado Yalwa Garari
ya dauki alkawari shi ba zai taba bin
bayanta ba bare wan nan nata ya cika
shi da surutu na rashin kan gado duk
ranar da ta gaji da zama ta dawo.
Washe gari da safe haka suka
gudanar da duk abubuwan da suka
saba yi amma dukkaninsu jikinsu a
sanyaye, Lawan kuwa da sanyin
safiya ya fice ya bar gidan, yau da
Hansa'u da Umaima ne kadai suka je
makarantar, a hanyarsu ta dawowa
sun shagala sosai wajen hirar matsalar
tafiyar Ummansu wadda suka
tabbatar cewa ba tafiyar shiri ba ce,
Umaima ce ta hango lawal tare da
wani babban mutum a tsaye a kofar
wani gida da ake gini ma aikata nata
kai kawo suna aikinsu, Umaima ta ce
105
Hadiza Ado Yalwa Garari
"La kin ga kamar Babanmu a can
gurin tsaye shi da wani mutumi".
Hansa'u ta kai dubanta gurin
"Tbbas shine to ko Baba me ya zo yi
nan gurin?"
Ta fada a sarari. "Dago kafa mu
tadda shi ko Allah ya ci da mu ya ba
mu wani abu mu kai gida".
Umaima ta dan 6ata fuska "In
kuma ya yankwanamu a cikin mutane
ke kika jamana".
Hansa'u ta ce "Ke kin fiya tsoro
wallahi kawai daga mun ganshi mun
gaishe shi sai ya yi mana wani abu ai
ba cewa za mu yi ya ba mu wani abu
ba".
Suna kara tunkarowa gabansu.
Suka kara tattara nutsuwarsu har
106
Garari
Hadiza Ado Yalwa
magana suka kowacce na tsoron
yanda zai amsa musu gaisuwar ta su.
Tun daga nesa Ahmad Ahuta ya
hango 'yan matan da ke tunkaro su.
Gaba daya ya shagala da kallansu, har
bai san lokcin da suka kara sa idowa
ba, sai ji ya yi suna cewa "Baba ina
wuni".
Ya dubi Lawan da ya hada fuska
"Ku makarantar ce sai yanzu kuke
dawowa tun dazu nake ganin yara na
wuce
Ya yi sauri yas abaki "Ai ba
jima da tasowa ba"
Sannan shima suka soma gaishe
shi ya ams ayana murmushi "Yaranka
ne wadannan Lawal? Don na ga
kamanin musamman wannan babbar".
Ya nuna Hansa'u.
107
Hadiza Ado Yalwa Garari
Nan da nan Lawal ya washe baki
"Eh wallahi alhaji ai ita babbar ita се
Hansa'u wannan kuma Umaima".
"To madallah"
Inji Alhaji yasa hannu a
aljihunsa ya dauko kudi ya mika
musu.
"Aka karasa mai karba tsakanin
Umaima da Hansa'u sai kallon juna
da suke yi daga karshe suka ce mun
gode Alhaji suka bar shi da kudin a
hannunsa.
Lawal da ya kurawa kudin ido
yaga cewa tafiya za su yi sai ya yi
maza ya daka musu tsawa "Ke ya za
ku dinga jayayya da Alhaji".
Hansa'u ce ta juya da sauri ta
durkusa ta karba sannan ta yi godiya.
108
Hadiza Ado Yalwa Garari
Suna tafiya amma a rude suke
da tsawar da babansu ya daka musu.
Ba su bar fargabar ba har sai da
suka tabbatar sun yi masa. Nasa baya
iya gane su, saboda tsoron kada ya
kira su ya balballasu da fada sun yi
masa laifi dan su a iya tsawon
rayuwarsu da Lawan basu tantance
mene ne in an yi mas alaifi ne mene
ne ba laifin ba sai dai idan bai gansu
ba.
Kusan a tare suka sauke ajiyar
zuciya Hansa'u ce ta dubi Umaima a
Hijab dinta ya karkace idanuwanta su
ka yi muzu muzu ta yi dariya "Kin
ganki ke kuwa lallai kin rikice.
Ita ma ta kwashe da dariya "Na
rikice ko mun rikice kin ga yand
109
Hadiza Ado Yalwa Garari
amuke gwara kai kuwa kai Baba ba
shi da dama komai fada".
Hansa'u ta bude hannunta da
kudin suka cike sababbin kudi ne
takardar dariyar biyar biyar har guda
shida.
Tu ni idanuwansu suka firfito na
mamaki sam ba su yi zaton kudin sun
kai haka ba, nan da nan suka kara
sauri sai gidan gaban Asiya suka zube
kudin lokacin da take daurin gyada
mai 6awo
"Yaya kin ga wani mutum da
suke tare da Baba ya ba mu".
Asiya ta ajiye gyadar hannunta
tana kirgawa suna bada labarin abin
da ya faru kawai sai jin muryar Lawal
su ka yi yana sallama Umaima ce ta
yi saurin dibar kudin biyu suka zube
110
Hadiza Ado Yalwa Garari
a farantin gyada suara kuwa ta daga
tabarma ta cusa suna amsa sallama
wadda ya yi ta hade da shigowa
dakin.
"Ina kudin da mutumin nan ya
ba ku? Maza ku miko minsu".
Nan ya zuba dubu dayan dake
kan farantin gyadar ido Umaima ta
dauka ta mika masa ya kirga "Sunfi
haka munafukai ku fito min da sauran
duk wahalar ta ku ba a kaina take ba,
maza ku fito min da su".
Umaima ce ta dake zuciyarta
wajan iya furta masa "Duka abin da
ya ba mu ke nan yanzu ma muka
ajiyewa Yaya ko tabawa ba mu yi
ba"
"Yaran banza to da kuka kawo
mata me za ku yi da kudi har haka?
111
Hadiza Ado Yalwa Garari
Cefane zan je na yi muku tunda ita
uwar ta ku ta watsar da ku ta tafi ta
barku yana wannan gorin ya fita".
Dukkansu suka kalli Umaima
yand ata iya wannan karfin hali.
Asiya ke cewa "Amma fa ba ki
kyauta ba ni dai zan ajiye masa kudin
tunda ya bukata ba ko abin da zai yi
mana da su ba, tund akin ga yanzu ya
יי
san Umma ma bata nan".
Umaima ta sauke ajiyar zuciya
"Ni yaya gani na yi da zai yi wani abu
da bai ma bukaci mu ba shi kudin ba
sai dai ya ce mu siyo abin da muke
bukata kawai amma me ye amfanin
karyar da ki ka yi yanzu ai da mun ce
masa ya ba mu mu siyo yafı karyar'.
In ji Asiya ranta a bace.
112
Hadiza Ado Yalwa Garari
"To ki yi hakuri Yaya idan ya
kawo sai mu ba shi ko haka su ka yi
ta zuba idon ya aiko musu da wani
abu har dai Asiya da kanta ta fitar da
tsammani ta dauko kudin ta bayar
suka yi cefane da goyawa wannan
bayan ba za su ba shi ragowar kudin
ba, har sai dai idan ya kawo musu
abin da za su ci.
Tun kafin Harira ta gama shiga
cikin garinsu mutane ke ta jajanta
mata rashin lafiyar wanta wadda bata
sani ba, jikinta ya yi sanyi kalau
domin ta kula da cewa ciwon ba
karamar kwantarwa ya yi masa yanda
kowa ya sani ita ce dai labarin bai
jewa ba, haka ta shiga cikin gida sai
kusan hudu tana sallama ba wanda ya
amsa mata sai can ta jiyo muryar inda
113
Hadiza Ado Yalwa Garari
matarsa a shake da sauri ta shiga
dakinsa Indo. Na bakink ofar tana
sharar kwallah yayin da abokansa
guda biyu ke zaune a gefansa dayan
na tallafe da kansa dayan na shafa
masa ruwa a fuska saboda sau biyu
yana suma ta kara gabansa tuni
muryarta ta soma rawa na son yin kuka.
"Yanzu jikin nasa har ya kai haka
ba a gaya min ba, da banzo ba shi ke
وو
nan.
Yana jin muryarta ya dan bude ido
"Harira" ya fadı sunan a wahale.
"Yaya Allah ya ta shi kafadunka"
Ya riko hannunta da kyau "Ina
tausayinki Hararia ki yi hakuri da
rayuwa ki zama jarumar kanki mai
dogaro da kanki kafin ya karasa tari ya
turnokeshi. Daga nan kuma sai shakuwa
nan da nan numfashinsa ya soma kaiwa
114
Hadiza Ado Yalwa
Garari
da komawa, sai kuma bacci ya dauke
shi haka suke zaune a gabansa masu
tofa masa addu'a na yi masu kuka na yi
kamar Harira da ta kasa jurewa kallonsa
ta fito tsakar gida ta hada kai da gwiwa
tana rasgar kuka lokacin sallah azahar
ne ya yi don haka duka suka fita yin
sallah, sai dai ashe ciwon bana tashi
bane kafin ma, su idar rai yayi halinsa
..dukkan mai rai mamaci ne wannan
mutuwar ba karami kada Harira ta yi ba,
domin shi ne wanta daya tilo kuma
marikinta da
.
ya rage mata a rayuwa
wannan ya dakusar da kudirin da Harira
ta taho da shi domin ta kasa bayyanawa
wani ma abin da ke cikinta.
Alhaji Ahmad kani ne ga Alhaji
Madu wanda Lawai ke tukawa a mota.
Tun ranar da ya dora idon a kan
Umaima ya ji yarinyar ta kwanta masa
115
Hadiza Ado Yalwa Garari
ya na son ya mai da gurbin matarsa da
ta rasu tsayin lokaci yana zaune babu
aure.
Kudirinsa kuma na son yarinya ne
karama sam baya sha'awar ya auri
yarinyar da ta kai