gansu ya kawo musu dan
abin da ya sauwaka kamar yan da
suka saba, basu dogara da shi ba, ta ci
gaba ne da siyar da gasarar a kadai
amma aikin awara a gidan mutane ba
36
Hadiza Ado Yalwa Garari
zai yiwu ba, da kwanaki suka soma
turawa Lawan sai ya daukie kafarsa
gaba daya daga gidan, ta koma fitar
da rai da zai nema musu wani gidan
tunda ta samu labarin a dakin
abokinsa yake kwana kuma har abinci
matar abokin nasa take ba shi, ya
mike kafa sosai a gidan abokin nasa
ga shi su duk ranar da a ka yi ruwa
basa iya bacci abincin ma ya zama sai
uwani idan ta yi ta sama musu jarin
awara tuni ya karye.
Dole ta fito nemar mus hayar da
kanta saboda idan har suke cinye
ragowar kudin hayan to fa bata san in
da za su samu ba, don haka ta dinga
fita ba ji ba gani nema musu gida duk
in da ta je sai a ce mata babu, sai da ta
yi sati guda ta na yawo ba a dace ba,
37
Hadiza Ado Yalwa Garari
ranar kwana na takwai ta na dawowa
take fadawa Uwani ba a samu ba,
Uwani ta nisa.
"Maganar gaskiya Harira samun
haya a nan kusa zai yi muku wahala
saboda yanda ake yamididin bakwai
biyan kudin haya, sai dai ki yi can
wajejen Remin kebe nan ne ba
sanku sosai ba kila a dace".
a
Wani irin nauyi kirjin Hairara ya
yi tabbas ita ma ta yi tunani haka don
ta samu dakunan da babbu kowa
amma tana zuwa sai a ce wai an ba da
su.
Shawara Uwani ta dauka ta sake
fita sannan ta samu dakin ga matsalar
rashin cikon kudi ta yi burinta fita
idan rana ta yi sanyi ta nemo Lawan
duk in da yake ya taimaka ya bada
38
Hadiza Ado Yalwa Garari
cikon kudin sai ga shi ya shigo da
bala'in da ta kasa yi masa ko wacce
magana.
Wai yaushe ne Lawan zai ji
kanta yaushe zata burge shi a rayuwa
yaushe ne zai kyautata mata.
Wannan tunani take yi tana fitar
da kwalla zuciyarta na sake daukar
zafi ba don tausayin 'ya'yanta ba da
ta gudu ta bar Lawan ta nuna masa ita
ma fa babu digon kaunarsa a
zuciyarta, to amma yaranta ta san in
ta bar masa su haka zai barsu su watse
su lalace tunda kaf danginsu babu mai
daukar masa babu ma wanda ya
dauka da mutumci da kima balle a
rabe su.
A soron gidan Kamar ba mutum
a cikinsa sai yawan ajiyar zuciyar da
39
Hadiza Ado Yalwa Garari
suke yi daya bayan dayan Uwani се
ta fito daga dakinta wadda kusan duk
hayaniyar da yake yi babu wani abin
da bata ji ba, abin da yafi konawa
Uwani rai yadda yake wa Harira a
gaban yaranta.
Ya leko sorön gidan "A'a
'yammata duk kuna nan kuna shan
iska"
A tare suka dago kai dan duk
sun ji motsin fitowarta. Umaimata ta
dan yi yake "Muna nan".
"Ga wannan ku dan taba kuma
bari na kaiwa Ummanta ku, wannan"
Ta meka musu robar hannunta
da 'yan farantin kuma ta nufi dakin
Ummansu. Da shi danwake ne, da ya
sha ya ji yana ta kamshi man zallar
Kulikuli duk da yunwar da ke
40
t
Hadiza Ado Yalwa Garari
addabesu babuw adda ta yi gigin
dauka, takaici da tunani kadai ke
yawo a tsakiyar kansu, har sai da su
Ahmad da Muhammad suka shigo
sannan Asiya ta ce su dauka su ci
batare da ta yi shawara da kowa a
cikinsu ba, kallo daya ta yi waa
Kannen nasu ta tabbatar sun fisu jigata
da jin yunwa, ga shi ba shi da yawan
da zai ishe su, ma gaba daya.
Kudin kitson da Umaima ta
samu shi ta cire ta meka wa Asiya
"Ga shi yaya me za mu yi da
daddare?"
Asiya ta ja ajiyar zuciya tana
juya kudin hade da tunanin sai
lokacin Hansa'u. Та се "Akwai sai a
yo cefane faten tsaki kawai".
41
Hadiza Ado Yalwa Gararf
Har lokacin da suka gama girki
Harira bata nukurkusarta wanda ya
hadda masa ciwon kai mai tsanani.
Dama tuni 'yanmatan sun
sabarwa kansu aikace-aikace gidan in
har Ummansu tasa musu hannu to, ita
ta so taimaka musu.
Har washe gari da yamma
Lawan bai dawowa ba kuma bata
hangi wata hanyar da za ta bi ta samu
kudin ba ga wani abin da yafi tayar da
hankalinta a yau ruwan ranar da a ka
yi tun safe ake kwara ruwa har sai
wajen sallah azahar sannan ruwan ya
soma raguwa daga ita har yaran sai da
suka je ke sharkaf saboda feshin
ruwan da yake shigowa dakin duk da
asabarin da suka sake a bakin kofar.
42
Hadiza Ado Yalwa Garari
Ga a zababbiyar yunwa dake
addabarsu saboda babu wannda ya
samu damar fita bare ya samo musu
dan abin da za su saka a bakunanus,
garin kwakin da bai wuce gwangwani
biyu ba ta jikawa yaran suka karya da
shi har zuwa rana ana idar da sallar
la'asar ta fito daga gidan duk da ana
dan yin yayyafi.
Ba kuma yanke shawarar in da
yakamata ta soma nufa iska mai sanyi
ce take kadawa cikin sararin
samaniya ruwa ya jika ko ina, ni'ima
ta sauke har lokacin babu alamun rana
sai haduwar saboda hadari ta sauke
kanta daga kallon yanda gabas take
dada duhu hadiye ajiyar zuciya.
Take ta yanke shawarar neman
Lawan a wajen abokansa ta san zai zo
43
Hadiza Ado Yalwa Garari
har gida ya ci mutumcinta saboda
abin da za ta yi masa, amma tana da
tabbacin zai iya nemo kudi duk in da
suke ya yi mata duk yanda ta so ko
don karta sake biyo shi wajan
abokansa ta ba shi kunya sai dai
rashin sa'ar da ta yi ta samu duk in da
yana zam ata je bata same shi ba.
Jikinta a sanyaye ta juya da
nufin komawa gida har ta soma tafiya
sai kuma ta canza shawara ta nufi
rumfar mai icce in da a nan ne wanda
zai basu hayar gidan yake sana'arsa ta
sai da icce.
Koda ta isa bata same shi a cikin
rumfar ba bata yi mamaki ba saboda
tasowar hadari da iska mai hade da
digowar kwayayyen yayyafi ta
zubawa iccen ido kamar wadda ke
44
Hadiza Ado Yalwa Garari
jiran amsar in da mai su ya shiga daga
gare su.
Katuwar rumfar kwano ce idan
ka dauke tabarma da bencin da ke
cikinta, to fa babu komai sai iccen
tana da girman gaske akwai itatuwa
masu yawan gaske duk wadanda aka
faskara da wadanda aka daure aka
kasa ne a cikin rumfar gunguma
gunguman daba a faskara ba, kuma
suna daga wajen rumfar.
"A'a barka da zuwa Hajjaju"
Ta ji an fada daga bayanta tana
juyawa ta ga mai iccen bota ce a
hannunsa "Ke ce da hadarin nan?"
Ta dan yi murmushin yake
"Wallahi dole ce ta fito da ni".
Ya zauna a kan bencin dake
cikin rumfar ita kuma ta durusa a kan
45
Hadiza Ado Yalwaа Garari
tabarmar shifede bayan sun gaisa
shiru ta ratsa na wasu 'yan mintuna,
tana juya kalaman da ya kamata ta yi
amfani da su dan bayyana masa
matsalar da take ciki, har dai ya kosa
da shurin nata idanunsa na kanta
"Kudin kika kawo?"
Sai sannan ta girgiza kai "Har
lokacin kanta na kasa dama na zo
neman alfarma ne.
"Alhaji Baban yaran ne baya
gari kuma a takure muke a inda muke
zaune saboda yanayin nan nadamuna,
shine na zo a taimakamin; ka karbe
rabin kudin nan in ya dawo zan kawo
cikon insha Allahu a taimaka dan
Allah Alhaji".
Ba ta kula da irin kallon kurullar
da yake yi mata ba, saboda har ;
46
Hadiza Ado Yalwa
Garari
lekacin kanta Rasa yake har ta kai
karshen maganarta.
"Wannan ba zai gagara ba kawo
abin da yake hannunki".
Kamar ta yi rawa don murna
farin cikinta ya kasa 6oyowa take ta
yi murmushin da har hakoranta suka
bayyana takwanto kudin daga cikin
bakar ledar da ta daure su, a ciki ta
kirga sannan ta mika masa.
Sai a lokacin ne ta kula da irin
kallon kurullar da yake mata har sai
da gabanta ya fadi take fara'ar dake
fuskarta ta dauke.
Cikin muryar kasa-kasa ya cе
"Ai ba girmanki ba ne, kina
yarinyarki da ke kina neman alfarma"
Ta dago da sauri kafin ta ce
wani abu. Ya mike "Babu damuwa,
47
Hadiza Ado Yalwa Garari
ko yau ne ko na iya shiga, babu
damuwa, ko yaune ko na iya shiga ga
mukullin nan ya a jiye mata mukullin
a gabanta.
Wannan kalmomin na shi su
kasa cewa komai sai godiya sai dai a
cikin zuciyarta na cike da tambayar
me yake nufi da furta su a gare ta har
ta isa zuciyarta bata gama amince
mata cewar ba shi da wata manufa a
cikin kalamansa ba.
Addu'a ta shiga yi ta Allah ya
tsare ta daga dukkan wani mugun nufi
ba karamin farin ciki yaran suka yi
ba, da ta zo musu ba labarin ya karbe
kudin da sanyin safiya ma za su tare a
gidan, cikin dare suka kammala
dukkan shirinsu guri na wayewa, ta
shiga yiwa Uwani sallama da dimbin
48
Hadiza Ado Yalwa Garari
Godiya Uwani taya su murna sosai ta
ce," kuma taimakon wani ai taimakon kai
ne." ta kuma dora da addu'ar Allah ya
hore.
Nan da nan suka dora tarkacen
kayansu a kura suka dauki hanya. Daga
'ya'yan suke bin Ummansu da ta san
gidan,jikinsu a sanyaye yake har babu
wacce ta ke iya Magana cikin 'yan
matan.
'ya'yan nata ban da su Mahmud da
suke ta yin wasanni goge-goge a kan
hanyar ita kuma Umman Harira tafiya
kawai ta ke yi zuciyarta cike da sakesake da addu'a.
A bakin wani lungu mai siririyar kofa
suka tsaya Harira ta kuma sauke kayan
suna taya ta said a suka shiga lungu
sannan suka gane kofar gida ne
49
Hadiza Ado Yalwa Garari
ba lungu ba, ba su yi tafiya mai nisa
ba sai ga su a tsakar gidan.
Ba su shiga gidan sosai ba, katuwar
rumfa suka shiga wadda ta ke dauke da
dakuna har guda takwas hudu na kallon
hudu.
Kowane daki daya iyali ne a cikinsa,
suka yisallama har sau uku, amma babu
wanda ya amsa musu..
Matasan 'yan mata ne suke casar fada
kamar za su yaga naman jikinsu. Fada
suke yi,su Umaima suka kalli juna har
Harira ta fara bude kofar dakinsu sannan
wata mata ta fito daga daki da buta a
hannunta,ga mamakinsu ko inda 'yan
matan suke bat a kalla ba,kamar ma bat a
san wani abu na faruwa ba.
Da fara'arta ta, ta ce," a'a, baki muka
yi sannunku da zuwa."
50
Hadiza Ado Yalwa Garari
Ta karasa fitowa da Sanda a
hannunta "To kar na kuma jin bakin
wata a cikinku"
Su ka gaisa da matar cikin
fara'a sannan Harira ta ture kofar
dakinta ta shiga ba lefi dakin yana
da dan girma, sauran yaran suka
dinga shigowa da kyar suka barsu
wajen shirya kayansu, duk basu
wuce tabarmi da katifa guda daya
ba,s ai wani tebur da gwandon
kwanika da jakunkunan kayansu.
Nan da nan suka kammala
shirya komai. Dukkansu suna
kwance a tsakiyar dakin ba wacce
ke iya magana, kuma ba wacce ta
rintsa a acikinsu, kowacce da abin
51
Hadiza Ado Yalwa Garari
da ke sakawa a ranta, ta yanda za su
fuskanci zaman gidan.
Sun saba da zaman gidan haya
tun tasowarsu, amma sun gaza
sabawa da fargabar kalubalen da
duk gidan da suke zama su kan
zamo baki. Musamman irin wannan
gidan da ya tara yawan al'umma
ban da su Mahmud da tuni suka fice
suna murnar samun sababin abokai.
Rana na dagawa gidan ya dume da
zafi hayaki, dole ce ta sa dukkansu
fitowa ko don shekar daddadar
iskar bayan gidan, in da anan suke
tsammanin samin inuwar da za su
tsugunna ba su yi mamakin ganin
daukacin gidan wajen ba sai dai
kowacce ba a zaune take ba kamar
52
Hadiza Ado Yalwa Garari
yadda suka zo shan iska duk suna
aikace aikacen kayan siyarwasu,
wasu dambu wasu danwake, shi ya
sama hayakin ke komawa
dakunansu.
Wata 'yar budurwa ce ta fito ta
kalli Umaima ta sheke da dariya
"Kunji turaren hayaki ko, ku ne
kuka kunshe kanku a ciki daki".
Asiya ta yi dariya "Akwai
hayaki kam sannunku da aiki".
Yarinyar ta soma gabatar da
sunanta dana kannensu, abin da
suka rike shine Laila wadda ke
gabatar da kansu, wadda bata wuce
sa'ar Asiya ba.
53
Hadiza Ado Yalwa Garari
Daga nan ta fara musu hira
wadda yawanci bugar ciki ne da
tambayoyi mara alaka da ita.
Su kam daga murmushi basa
iya kara wani abu domin Ummansu
me kwabarsu ce akodayaushe basa
iyawa manya na magana suna sa
baki ko shiga cikin maganar da bata
shafe ka ba, wanda abin da suka
lura da shi a wannan zamani sami
yaran basa shayin fadar kowace irin
magana gaban iyayinsu, wani
lokacin ma suke kara musu haske a
takaice kusan tare ma ake hirar.
Wadda rabinta duk żancen
mutane ne da batsa, wani lokacin su
kan ji kunya kamar su nutse amma
iyayen babu abin da ya dame su,
54
Hadiza Ado Yalwa
Garari
yaran kuwa dariyarsu suke yi ba
wani alamun kunya ko damuwa a
kan fuskokinsu.
Haka suka ci gaba da zaman
wajan ba don zaman na musu dadi
ba, sai dan rage wahalar zafi da
hayakin cikin dakinsu,w anda babu
shi, sai ma iskar bishiyar dake
makota ke kaďo musu.
Suna zaune har zuwa lokacin
da kowace ta mike ta wanko kafafu
da hannaye sannan aka zo ana саба
kwalliya.
Iyayensu na zuba musu abinci
siyarwa a roba da suke fita da su,
tallah.
Sannan ne fa Asiya ta mike
dukkansu ma suka bi bayanta don
55
Hadiza Ado Yalwа Garari
komawa cikin nasu dakin,
Ummansu tunda safe ta fita nemar
musu abinci za su ci duk da sun
baro gurin duk wacce ta gama
abinci ta zubo musu ko da suka ki
karba sai su ajiye musu a dakin na
su, sai su yi godiya,
Asiya na sallaha Umaima na
yiwa Sayyada tsifar kanta Hansa'u
na wanke musu kwanuka.
Ummansu ta ji sallama ta
shigo Umaima ta amsa ta dube su,
duka ta nisa ina so Muhammad
yanzun nan su ka ci abinci suka fita
ina kuka samu abinci Umaima ta yi
mata bayani a takaice ta dauko
ledar da ta shigo musu da ita Jalop
din shinkafa ce a cikin cikin
56
Hadiza Ado Yalwa Garari
zuciyarta ciki da tunanin yanda za
ta yi ta samarwa su Mahamud
makaranta, domin ta tsani yawon
nan nasu tana ciki da farbar kada su
zame mata yan da yayansu ya
zama, duk yanda take son kulle su a
daki abin gagararta yake yi ba
kamar yaranta ba, ga shi dai a cikin
idon ta ma har ta manta rabon da ta
ga wansu ba ma ta tsammanin
yasan zamansu gidan Uwani tun
wani lokaci suna wancan gidan da
ya shigo mata daki kamar
mahaukaci yana layin buguwa ta
matan gidan suka dinga gudawa
suna rufe dakunansu da kyar ta tura
shi waje ta kuma gargafe shi kada
ya sake shigowa cikin idan
57
gidan
Hadiza Ado Yalwa Garari
ita yake son ga ni ya tsaya daga
waje ya tura a kirata. Bai yi magana
ba ya juya kawai ya tafi bata sake
ganinsa ba a idanuwanta.
Duk zancen zucin da take yi
tana juye musu abincin a cikin
kwanika, da ddadan kamshin abinci
ya gauraye dakin wanda rabon da
su ji irinsa har sun manta.
Hansa'u će ta kasa hakuri ta ce
"Umma ina kika samu wannan
abincin me yawa haka, ga kamshi"
Dukkansu suka sa dariya. Ban
da Umma da tunanin da ta ke yi ya
sauke mata da dakin zuciya ta dai
sauke ajiyar zuciya.
"Tun bayan fita ta gidan Kubra
na nufa yayar Yahanasu" (Yayar
58
Hadiza Ado Yalwa
Garari
wata ce da suka taba zaman gidan
haya da ita)
Tun da na ga ba mu da abin da
za mu ci na soma tunanin sai ta
fadomin a rai, na santa macece mai
tausayi da kara, kuma daga nan zan
iya zuwa gidan akafa ta na can Jaba
gidajen 'yansanda nan, wallahi ira
ce da wannan aikin abincin har
kudi wai na yi jari"
Gaba daya suka yi mata
addu'ar Allah ya biyata da
aljannah.
Sun gama cin abinci suka fara
shawara sana'ar da yakamata su yi
don neman tudun dafawa. Sun tsaye
ne a kan shawara da Umaima ta
kawo wato yin Awara da safe da
59
Hadiza Ado Yalwa Garari
rana kuma wake da shinkafa da
Kunun tsamiya tunda akwai masu
yin awara a gidan basu 6ata lokaci
ba wajen siyo kayayyakin da niyar
gari na wayewa za su tashi da aikin.
Misalin karfe tara na dare
Hansa'u na yiwa su Mahmud
shimfida, Umaima da Asiya na dafa
Awara, Ummansu na zaune da
sauran matan gidan ana taba hira,
suka ji gyaran muryar hade da
sallama. Harira ta dauka mijin daya
ne daga ciki ne ya dawo ta dan
janye jikinta don tafi kusa da hanya
ga mamakinta sai ta ji kamar
muryar Lawal ya na nanata sallama
ta dago ido babu tantama shi dinne
60
Hadiza Ado Yalwa Garari
ya soma duru-duru na rashin sanin
ina ne dakinnasu.
Muryar Hansa'u ta ji ta fito
daga dakin ya yi saurin shiga dakin,
ba don a bakon guri suke ba babu
abin da zai sa ta biyo shi, fushi take
yi da shi sosai, amman gudun kada
'yan gidan su gane akwai matsala
yasa ta mike ta shiga dakin amma
ta tsaya a bakin kofar bata iya furta
masa kowace kalma ba.
Shiru ya ratsa tsakaninsu ya
dai kula da yanda ta hade fuska, ya
yi kasa kasa da muryar "Na je can
gidan Uwani ta hada ni da yaro ya
rako ni nan ashe an samu dakin
amma baki neme ni ba."
61
Hadiza Ado Yalwa Garari
Duk kame kamen da yake yi
tana jinsa bata iya cewa komai ba
saboda kalmar da zata fada ba mai
dadi bace, kafin su fara raba abin
fada a bakon waje.
Ganin ba zata tanka mushi ba
ya soma kiran Hansa'u ta shigar da
sallama. ya mika mata ledar
hannunsa "Ga wannan ku je ku ci
ke da kannenki".
Kawunan kifi ne da gyada me
gishiri. Hansau'u na fita Umman ta
bi bayanta ta koma gun matan
gidan su ka ci gaba da hirarsu.
Lawan ya rage kayan jikinsa
sannan ya haye katifar ya yi
kwanciyarsa ya na jero tsaki na jin
62
Hadiza Ado Yalwa
Garari
haushin yanda ta tafi ta bar shi shi
kadai a daki.
"Ke su Mahmud ma ba wanda
ya leko bare ya yi musu 'yan
tambayoyin da suke ransa.
Asiya ce ta shigo don dibar
tabarmin shimfidarsu kamar yanda
ta ga ni kowacce mata na shifida a
koafar dakinsu, ta ji magana ta juya
ta ji wanda ke makotaka da dakinsu
na cewa "Ai sai kin fara shimfida
kwali, yanda rumukan nan ba za su
hanaku bacci ba"
"Asiya ta sauke ajiyar zuciya
yanzu ina zamu samu kwali?"
Yarinyar d ahar a lokacin Asiya
ba ta rike sunanta ba ta ce "Siyarwa
63
Hadiza Ado Yalwa Garari
ake yi kantunan dake kusa da gidan
nan
Dole Asiya ta aje shimfidar ta
koma ta gayawa Umma don ta hango
matsalar da 'yar budurwar ke fada
mata.
Harira ta shiga dauko kudi a
daki tana kallon yanda Lawan ya yi
dai-dai akan katifa ta dinga jin kamar
ta rufe shi da duka, haka ta hadye
takaicin ta fita ta bawa Ahmad kudin
ya tafi siyowa.
Duk yanda Lawan ya yi ya
shawo kan Harira abin ya gagara don
haka shima ya dau gaba da ita, sai dai
hakan bai hana mishi kwanan gidan
ba da cin duk wani abinci da ya ga ni
a dakin bai canza ba, duk da ya samu
64
Hadiza Ado Yalwa
Garari
aikin tuka wani babban mutu a mota
wato driber.
A cikin 'yan kwanakin duk da
bai fadawa Harira ba ta dai lura da
yanda yake canza kayan sawarsa da
daduwar tsabtar jikinsa ta yi tunanin
akwai in da yake zuwa koma dai me
ya ke ciki bata damu da tunanin halin
da yake ciki ba.
Harkokin sana'arta yanda zata
taimaki yaranta shi tafi mai da hankali
a kai musamman cikin 'yan kwanakin
nan da take hada kudin da zata sa su
Mahmud a makaranta da Islamiyya.
Ga dai shi anata ciniki sosai fiye
ma da zatansu sai dai hidimar
gabansu tana da yawa.
Umaima da kudin da take
tarawa na kitso ta biyawa Asiya kudin
65
Hadiza Ado Yalwa Garari
jarabawar shiga aji shida (qualifying).
Daga ita har Hansa'u kuma basa zuwa
saboda ba su biya kudin makaranta
ba, ganin wannan ne ya sa ta dagewa
don neman kudi har wankau take
zuwa duk sati ake biyanta ko yaran
nata ba wanda ta gayawa tana yi, don
ta san halinsu karshe su matsa a kanc
ewa su za su yi ita kuma bata san
yaran su dinga shiga gidajen masu
hali saboda tsoran abin da zai je ya
ZO.
Daga ita har yaran ba wanda ya
fadawa Lawal halin da suke ciki
saboda sun manta ranar da Lawal ya
magance musu matsalarsu.
Wata ranar Lahadi Alhaji
Manman tafiya zuwa Abuja sai ranar
litinin za su dawo, cikin dare yake
66
Hadiza Ado Yalw a
Garari
sanarwa Harira tafiyarsu, ta yi addu'a
da fatan alheri.
Sai lokacin ta san Lawal yana
wannan aikin shi ma don lawal ya na
tsoron hanya kada wani abu ya same
shi, su ce basu sani ba, aibunsa ya fito
sarari, shi yasa ya yi shawarar fada ya
kuma shigo musu da shinkafa kwano
daya manja gwangwani daya ya bata
dari biyu wai ta yi cefane, ragowar
kudin ya adana abinsa sannan ya yi
musu sallama suka dauki hanyar
Abuja.
Washe gari litinin da safe
Hansa'u ta gama awara da safe ta
shigar da ragowar tana irga kudin,
Umaima ta gamaiwa sayyada wanka
tana shaifa musu mai Ummansu na
67
Hadiza Ado Yalwa Garari
kan sallaya tana lazimi bayan ta idar
da sallar walha.
Lawan ya yi musu sallama gaba
daya suka amsa tare da yi masa sannu
da zuwa, suna kokarin ta shi ya ce
"Yau me ya hanaku zuwa
makaranta?"
Saboda rashin sabon jin irin
wannan tambayar daga bakinsa yasa
ya rasa me fara ba shi amsa a cikinsu
sai kallon juna da suka yi na mamaki
har sai da ya maimaita musu
tambayar.
Duk da murmushin a fuskarsu
Umaima ta ce "Kudin makaranta ne
ba mu biya ba"
Ya ci gaba da taku zuwa kan
katifar sannan ya kalli Harira dama
aurar da su ki ka yi kika huta".
68
Hadiza Ado Yalwa
Garari
Saboda takaicin maganar Harira
ba ta iya cewa komai ba, su kuwa
kowacce ta yi nadamar tsayawa don
jin kalaman nasa, nan da nan annurin
fuskokinsu suka gushe, kamar
walkiya suka fice daga dakin.
Ya zauna yana nanatawa "Ke
Harira wataran rashin daukar
shawararki ce take sawa na ke rabuwa
da ke, amma ban da haka kya sa yara
a gaba kuna kallon juna ai gwara ki
aurar da su ita fa babbar Asiya sha
bakwai ta ke Hansa'u sha biyar
Umaima sha huďu ko ke sanda na
aure ki ai shekararki basu fi na
Karamar ba"
Gudun ka da ya ce bata bi
shawararsa ba ya sa ta tankawa duk
da wani abu ya zo ya tsaya mata a
69
Hadiza Ado Yalwa Garari
cikin shakewar murya ta ce "To wa
zan aurarwa su, tunda ba su da ma
nemi kuma in ma suna da mane min
da me zan aurar da su".
Ya mike kafafuwansa "Ke dai
Harira ki dinga godewa Allah ko da
kudin da suke neman miki ai kya yi
musu kayan daki."
"Da shi mu ke ci mu ke sha har
na biya kudin haya"
Ta fada a zafafe, domin ya gama
kaita makura.
"To ni na zame hoto ke nan ba
nayin komai".
Wani kallo ta watsa masa
maimakon amsar ya janyo robar
awara ya soma ci "Ke dai ki dinga
godewa Allah".
70
Garari
Hadiza Ado Yalwa
Ta dauke kwanan awarar ya bita
da kallo ai kuwa aiki na gabanki"
Zuciyarta na kuna ta shiga cikin
matan gidan wadanda suka rage a
wajen duk yanda ta so goge takaicin
maganganun nasa sun kasa fita daga
ranta.
ke yi Duk hirar da matan gidan
sai dai ka ga murmushinta da yawa
bata gane abin da suke fada ba jinsu
kawai take yi, abin da bata sani ba
kuma shirunta ba karamin bakanta
ran matan gidan ke yi ba, suna mata
wani irin kallo ne mai girman kai,
kamar tana nuna ta fi karfin yin
magana da su, ko tafi karfin yin
mu'amala da su, daga ita har yaranta
basa sakewa da kowa a gidan in ka ji
hirarsu isu isu ne kawai, in ko suna
71
Hadiza Ado Yalwa Garari
cikin yaran gidan sai dai murmushin
in ko a ka yi abin dariya su yi dariya,
na jaje su ce Allah ya kyauta.
Ga karatun bokon da suke yi
wanda duk cikar gidan da batsewarsu
babu wanda yake zuwa makaranta sai
su.
Wannan yasa suka sa musu ido
sosai cikin al'amuransu da haka har
suka gano ba fa wani abu suka fisu da
shi ba tsabar girman kai ne a tasu
fahimtar.
Wannan ya janyo muguwar
tsanar ya zamo ko magana suka yi a
gidan ba mai tanka musu.
Da farko abin ya da mu Harira ta
same su cikin tausasawa take
tambayarsu ko ta yi musu wani laifi
ne ko yaranta sun bata musu ba
72
Garari
Hadiza Ado Yalwa
wadda ta yi magana saboda ba
takamaimai abin fadar sai tsabar
hassada.
Tun daga wannan lokacin ta fita
daga sha'aninsu za dai ta gaida kowa
da safe haka ma yaranta za su gaishe
su daga nan basa kara shiga sabgar
kowa harkokin gabansu kawai suke yi
duk da hakan ma bai rage ko da digon
abin da suke yi musu ba, sai ma abin
da ya dadu.
Wani yammaci ta dawo daga
gidan da take yiwa wanki agajiye take
sosai saboda yau wanki mai yawa ta
yi tafiyar ma kamar dole take yi ga
ciwon kai, sai ta dinga jin kamar kira
daga bayanta sai ta juye ta tabbata ita
din ake kira, tabbas ita din yake kira
da murmushi a fuskarsa a gabanta ya
73
Hadiza Ado Yalwa Garari
yi wata irin faduwa tun ranar da ta
baro rumfår shi ko hanyar bata kara
bi ba, Alhaji Mai ice ne ta dan rage
tsaho don ta gaida shi gaba daya
fuskarta babu walwala.
"Kin buya ina ta cigiyarki"
Ta dan dauke kai ta ci gaba da
tafiya "Wallahi ban yi ta wajejenku
ba ne".
Ganin tana tafiya ne yasa ya се
"Harira tsaya magana nake son mu
yi".
Ta dan tsaya tana kallon kasa,
"Haba Harira kamar baki gane abin
da nake nufi ba, bakya nuna min
kulawa.".ta dago da sauri ta watsa
masa wani irin kallo irin na kyama
"Ban gane abin da kake nufi ba Alhaji
Ina tsammanin an fada maka ina da
74
Garari
Hadiza Ado Yalwa
aure, in ma ba a gaya maka ba to ka
sa ni ina da aure na, ya dago hade da
sauke ajiyar zuciya, na sani amma irin
aurenki ba zai hanamu soyayya ba
Harira"
"Zuciyata ta kamu da son ki tm
ranar da na ganki, shi kuma mijinna
ki ai bai mai da ke mace ba, idan har
kin ba ni dama ni zan hana zuciyarki
da hannuwanki wahala zan mai da ke
macen so ke maida aurenki yanda ya
mai da shi".
Maganganun suka dinga yawo a
kanta zuciyarta na dada tafarfasa ta
dai kasa magana har ya kai karshen
maganarsa. Ya sa hannu a aljihu ya
zaro kudi ya mika mata, sannan ta
samu karfin fara tafiya batare da ta
kallo kudin ba, hawaye ne suka zubo
75
Hadiza Ado Yalwa Garari
mata duk wannan tozarcin lawal ne ya
ja mata, kafinta isal gida haki ya fara
ta so mata saboda 6acin rai. Ranar
haka ta wuni ta na juya abin a ranta
tana kuma tunanin abin da yakamata
ta yi don dakatar da wannan al'amari.
Hanyadaya ce wadda zata samu
sauki barin gidan Alhaji mai icce sai
dai matsala daya kudin da zasu kama
hayar wani gidan daga karshe ta
yanke shawarar fadawa Lawal ko ya
samar mata mafita a cikin wannan
BAKON AL"AMARIN.
Cikin darre bayan ya kammala
duk abin da zai yi ya kwanta, ta same
shi ta fada masa tun kafin ma ta
karasa ya katse cikin fada.
"Wai me ki ka dauki kanki
Harira indiya ko balarabiya mai
76
Garari
G
Hadiza Ado Yalwa
Alhaji Zai yi da ke, kawai salon ki
janyo abinda za ki ce muta shi daga
wannan gidan tunda