na zaune a cikin kuryar turakarsa
yana bincike a eikin hallarar tsafinsa sai kawai
yaga wani abu da ya yi matukar firgitashi ya razana
ainun ya kurma wani uban ihu ya ja da baya.
Adaidai wannan lokacin ne sarki Ridwan ya Karaso
cikin turakar a guje, cikin firgici ya kama boka
Rimasu ya tashe shi zaune ya zauna daf da shi yace
Jarumi da Gimbiya
"Ya kai dirkar birnin kilmaz me ka gani yanzu a
sakamakon binciken da ka yi. Tabbas dama na ji a
jikina wani abu na tafiya ba daidai ba" Boka
Rimasu yace.
"Yarka gimbiya sazira ta ci amanarmu, a halin
yanzu ta sace akushinmu na sihiri ta gudu daga nan
a cikin siffar kuyanga Dulus kuma taje ta hada kai
da dakarun sumame na birnin samhar wadanda
suka zo saceta domin su je can birnin samhar su
sace na su akushin sihirin, suna so ne za su hada
akushin guda biyu su jefasu a cikin wutar ibilisai
dake karkashin dutsen zulus. Idan hakan ta faru
Karshen mulkinka dana sarki muraka ya zo karshe,
masarautun guda biyu duka sai sun fadi, babu wani
sarki da zai sake gudanar da mulki yadda ya ke so a
wannan nahiyar" Koda sarki Ridwan ya ji wannan
jawabi sai ya fusata ya mike tsaye ya kurma uban
ihu. Ihun ya cika gidan sarauta gaba daya.
Kuyanga Dulus na ji wannan ihu na sarki sai
data firgita ainun ta gane cewa asirinta ya tonu.
Don haka sai ta mike zumbur daga kan kujera a
falonta ta fito da gudu tana kokarin ficewa daga
cikin gidan sarautar gaba daya al'amarin dayai
matukar baiwa dukkanin hadiman gidan sarautar
mamaki kenan, kuyanginta suka biyota da gudu a
baya, tana cikin wannan gudune kawai aka ga ta
tsaya cak! Ta kame kamar gunki, kawai sai aka ga
kanta ya cire ya fado kasa daga jikin wuyanta. Jini
ya yi tsartuwa daga jikin wuyanta. Jini ya yi
tsartuwa daga cikin wuyan.
72
Jarumi da Gimbiya
Kan na faduwa kasa sai ya koma fuskar
kuyanga Dulus sarki Ridwan na tsaye a gaban
gangar jikin rike da takobinsa jini na diga a jikin
takobin kawai sai sarlo Ridwan ya dubi kuyangi da
dukkanin dakarun tsaro dake wajen yace.
"Wannan ba 'ya ta bace gimbiya sazira kuyanga Dulus ce ta rikide izuwa kamanninta,
gimbiya ce duk ta shirya wannan al'amarin ina
sarkin yaki kinana yake maza aje a gaya masa ayi
gagarumin shirin yaki zuwa birnin samhar zamu
tunkara yanzu" Yana gama fadin haka sai ya juya
da sauri ya nufi turakarsa domin ya je ya yi shigar yaki.
Al'amarin jarumi Lurwan da gimbiya sazira
kuwa cikin kankanin lokaci suka yi shiri-tare da
yaransa guda shida suka hau dawakansu suka nufi
birnin samhar gimbiya sazira na goye a bayan jarumi Lurwan bisa dokinsa, wato su biyune akan
doki guda.
Lokacin da ya rage sauran baifi tafiyar rabin
saaba su isa birnin samhar sai suka tsaya jarumi
Lurwan ya dubi jaransa guda shidan yace "Abinda
nake so da ku shi ne ku tafi izuwa can dutsen zulus
inda wutar ibilisai take ku jirani a wajen. Zan
sameku a can bayan na sami nasarar sato akushin
sihiri na masarautarmu, kamar yadda na yi muku
alkawari idan har muka sami nasara akan wannan
kudurin ku ne za ku zamo manyan fadawa a
wannan kasa tamu, kada ku manta cewa
kowannanku ya rantse da gemun iyayensa bisa
73
Jarumi da Gimbiya
alkawarin rike amanarmu" Jaruman shida suka ce
tabbbas rayuwarmu fansace akan wannan babban
Kuduri.
Koda jin haka sai farin ciki ya kama gimbiya
sazira ta dauko akushin sihiri na birnin kilmaz daga
cikin jakarta yana nannade a cikin wani jan
tsumma ta mikawa daya daga cikinsu tace "Ku tafi
da wannan ku adanashi da kyau har sai mun zo da
dan uwansa sannan za'a hadasu a lokaci guda a
jefa a cikin wutar ibilisai" Batare da bata wani
lokaci ba dakarun shida sua karbi akushin sihiri
suka kada linzamin dawakansu suka nufi hanyar da
zata kai su inda wutar ibilisai take har sai da su
jarumi Lurwan suka daina hangosu sannan gimbiya
sazira ta dubi lurwan tace da shi.
"Yanzu sai ka daure hannayena ta baya ka
barni akan doki ka kama linzamin dokin kaja ka kai
ni gaban sarkinku a haka" Ba tare da wata gardama
ba kuma sai jarumi Lurwan ya aikata hakan suka
durfafi fadar birnin samhar kai tsaye ba tare da
wata fargaba ba.
Sarki muraka tare da dansa Yarima Andaz na
zaune akan kujerar mulki fadar ta cika makil da
fadawa, dakaru da mutanen gari ana gudanar da
harkokin mulki, kawai sai aka ji takun sawun doki a
cikin fadar. Hankalin kowa ya kai izuwa kofar
shigowa da kakarun tsaro suka bude hanya kawai sai
aka hango jarumi Lurwan rike da dokinsa sun
runkaro inda karagar mulki yake. Gimbiya sazira na
zaune akan dokin an daure hannayenta ta baya kuma
an rufe mata idanunta
74
Jarumi da Gimbiya
Cikin tsananin mamaki da farin ciki sarki muraka
da yarima Andaz suka mike tsaye suna kallon ikon
Allah abinda ya fara baiwa su sarki muraka mamaki
shi ne ta yaya jarumi Lurwan ya sami wammam
gagarumar nasarar ya sato gimbiya sazira cikin sauki
haka?
Sai da ya rage saura baifi taku bakwai a tsakanin
dokin lurwan da karagar mulkin sarki muraka ba sai
sarki muraka ya dakawa jarumi Lurwan tsawa ya
tsaya cak, kawai sai sarki muraka ya yi wa wasu
dakarunsa inkiya su kimanin dari cíkin hanzari
dakarun suka zare makamansu suka ritsa jarumi
Lurwan da gimbiya sazira dake daure akan dkin sarki
muraka ya dubi dansa yarima Andaz kawai sai suka
bushe da dariyar mugunta a lokaci daya.
Sarki muraka ya turbune fuskarsa ya dubi jarumí
Lurwan yace "Kana zaton bansa duk abinda kuka
shirya bane a kaina, Lurwan ka ci amanata ka hada
baki da wannan yar sarki domin ku rushe
masarautunnan guda biyu. Naga komai da kuka
shirya a cikin madubin tsafina, ya ke gimbiya sazira
kiyi sani cewa komai sammakonki ni a tafe na
kwana" Koda jin wannan batu sai gimbiya sazira ta
bude hannayenta, igiyar data daureta ta kwance tasa
hannu ta bude idanunta ta dubi sarki muraka a fusace
tace.
"Ya kai wannan -sarkin kayi sani cewa koda a
yanzu bamu sami nasarar cika kudurinmu a kan ku
ba kai da mahaifina to nan gaba sai an samu wadanda
za su kawar da ku saboda shi zallunci baya dorewa a
doron kasa, bamu da wata damuwa idan ka kashemu
a yanzu kai ma ka jira ranar taka mutuwar Dajin
75
Jarumi da Gimbiya
wannan batu sai yarima Andaz ya bushe da dariyar
mugunta ya dubi gimbiya sazira yace.
"Wannan shi ne iyakar abinda zaki iya fada?
Dakaru ku kama su ku kai su cikin kurkuku ku
kullesu, a daren nan na yau za mu cika burinmu na
amfani da akushin sihiri bayan nan kuma zan cika
alkawarina akanki yake lallai sai na daddatsa wannan
kyakkyawan jikin naki na aikawa da mahaifinki
kanki ya gani da idanunsa, nasan yana gani zai hadiyi
zuciya ya fadi ya mutu" Sarki muraka ya bu she da
dariyar mugunta yace.
"Zancenka dutsene maza dakaru ku hanzarta kai
su cikin kurkuku a je a kirawo mun babban boka
domin mu fara shirin kaddamar da tsafin akushin
sihiri" sarki na gama fadin hakan aka kama jarumi
Lurwan da gimbiya sazira da karfin tsiya tunda
sarkin yawa yafi sarkin karfi aka kai su cikin
kurkuku aka kullesu.
**
Al'amarin dakarun sumame su shida kuwa
lokacin da suka isa inda kogin ibilisai yake suna
dauke da akushin sihiri na birnin kilmaz sai suka
daure dawakansu suka zauna a gefe guda.
Dukkaninsu sai suka yi shiru suna tunani dayansu
baice uffanba. Daga can sai babban cikin su wanda
ake kira da suna barde awaisu ya dube su su duka
yace.
"Kunsa wani abu kuwa? Suka ce "Bamu san
komai ba face ka fadi abinda yake ranka" Yace "Ina
ji a jikina gimbiya sazira da barde Lurwan ba za su
iya gudanar da wannan aikin ba a cikin gidan sarki
face sun samu matsala saboda duk shirinsu sarki
76
Jarumi da Gimbiya
muraka ya fi su, ai duk wanda ya rigaka kwana
dolene ya rigaka tashi, ya zama dole mu rabu biyu
wasunmu su kai musu dauki a yayin da dare ya
raba, dolene mu san yadda zamu shiga cikin gidan
sarautar domin muga halin da suke ciki ku sani cea
nasararsu itace tau. Idan ba su yi nasara ba
dukkaninmu nan sai an kamomu anyi mana kisan
gilla" Lokacin da barde Awaisu ya zo nan a
jawabinsa sai dukkaninsu jkinsu ya yi sanyi suka
gamsu da abinda ya fada awaisu ya sake
dubansuyace.
"Nasan kuna tunanin hanyar da zamu bi mu shiga
gidan sarauta ba tare da asirinmu ya tonu ba to ina so
ku tuna da yadda muka yi muka shiga cikin gidan
sarautar birnin kilmaz har muka isa bangaren turakar
gimbiya sazira ba tare da kowa ya ganmu ba. Dakaru
dari uku muka kashe a wajen kuma muka fito lafiya
to yanzuma irin wannan shirin za mu yi saboda haka
yanzu mutum biyu kacal zamu bari anan wajen kowa
ya yi shiri lallai a darennan za mu ratsa gidan sarautar
garinnan".
Jarumi Lurwan tare da gimbiya sazira na zaune a
cikin kurkuku har dare ya soma yi basu ci komai ba
basha wani abu ba saboda takaicin yadda dukkanin
shirinsu ya wargaje. Tsawon wannan lokaci dayansu
baice uffanba sai dai su kalli juna su kauda kai. Sau
goma sha daya gimbiya sazira tayi kokarin amfani da
sihirin tsafinta domin su kubuta daga cikin kurkukun
amma sai tsafin nata yaki ya yi tasiri, shima jarumi
Lurwan haka ya yi ta jarrabawa sau ba adadi har ya
gaj
Jarumi da Gimbiya
Sai da dare ya raba sosai suna zaune su basu
kwanta ba kuma ba su rufe idanunsu ba kawai sai
gimbiya sazira ta taso daga inda take zaune ta dora
kanta akan kirjin jarumi Lurwan tace "Lokaci ya yi
wanda zamu yi bankwana da duniya"Cikin mamaki
ya janye jikinsa daga cikin nata ya dubeta yace
"Gimbiya ban fahimce ki ba ya za'ayi muyi
bankwana da duniya alhalin ba a zo kashe mu ba"
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubo mata
tace.
"Da dai mu bari wannan azzalumin sarkin ya
kashe mu gwara mu kashe kanmu kawai, idan fa na
mutu tsafin da zai yi da akushin sihirin ba zai yi aiki
ba, ina son ka kashe ni da hannunka nima na kashe ka
da hannuna sai dai su zo su iske gawarmu wannan ce
kadai hanyar da za mu bi mu hana sarkina da
sarkinku cika burinsu na ci gaba da yin zallunci a
wannan nahiyar idan baka manta ba ka daukar mini
alkawarin cewar ranka da jikinka fansane akan
wannan babban kuduri na alkhairi" Sa'adda da
gimbiya sazira ta zo nan a zancenta sai shima hawaye
ya zubo masa yace.
"Tabbas na yi miki wannan alkawari kuma
dolene na cika shi" Yana gama fadin hakan sai ya
zaro wuka a jikinsa, itama gimbiya sazira sai ta zaro
wukar jikinta, duka su biyun suka yunkura za su
cakawa juna. wukaken akan makoshinsu kawai sai
suka ga barde Awaisu ya duro daga sama tsulum! Ya bayyana a gabansu. Nan take yasa mukuli ya bude kofar kurkukun suka fito daga ciki duk su ukun suka
kamatafiyar sanda da labe a cikin gidan sarautar.
78
Jarumi da Gimbiya
A daidai wannan lokacine suka ji an busa kahon
yaki, koda jin hakan sai gimbiya sazira ta yi murmushi tace "Ga mahaifina nan tare da rundunarsa
ta yaki sun iso garinnan, yanzu nan za a yita ta kare,
maza ka nuna mini inda aka ajiye akushin sihiri na
wannan masarauta” Dajin haka sai jarumi Lurwan ya
wuce gaba da sauri suka bishi a baya.
Nan danan gidan sarautar ya hargitse da guje- guje na dakaru suka yi ta debo makaman yaki ana ta shirya dawakai domin tuni labari ya zo cewa ga
dakarun yaki can na birnin kilmaz suna daf da isowa
kofar birnin samhar jarumi Lurwan da gimbiya sazira
tare da barde Awaisu suka tunkari dakin tarihi inda
aka ajiye akushin sihiri amma sai dakaru suka taresu
aka ruguntsume da azababben yaki da karfin tsiya su
gimbiya sazira suka kwaci makaman yaki a hannun
dakarun suka rinka ragargazarsu sai da suka shafe
sama da sa'a uku suna bakin artabu da dakarun har
ya zamana duka su ukun sun samu raunuka a jikinsu
kuma sun sha bakar wuya kamar ba za su rayu ba
sannan suka samu da kyar da sidin goshi suka shiga
cikin dakin tarihin suka dauko wannan akushin sihiri.
A can kofar birnin samhar kuwa yaki ya yi
tsanani sai ragargazar maza ake yi suna zubewa kasa
matattu. Saboda yawan gawarwaki a wajen kai kace
yabanya ce a gona duk inda ka duba jinine ke malala
bisa kan Kasa. Sarki Ridwan da sarki muraka ke
jagorantar wannan yakin. Sai da gari ya waye ana ta
gwabza wannna yaki har rana ta fito sosai sannan
gaba dayan dakarun yakin suka kare aka yi ragas ya
zamana cewa mutum biyune kacal suka rage a tsaye
79
Jarumi da Gimbiya
suna kallon junansu suna haki kamar zakaru. KКо
wannen su jikinsa ya yi kaca-kaca da jini, ba
wadansu bane wadannan mutanen face sarki muraka
da sarki Ridwan ya yin da kowannansu ya dubi
dubun gawarwakin dakarunsa sai bakin ciki ya
turnukesu suka kwarara uban ihu suka yunkura
domin su ruga da gudu izuwa kan juna kawai sai
sukaji an tsala tsawa a sararin samaniya mai matukar
firgitarwa suka daga kawunansu sama suka ga ko
alamar hadari babu hankalinsu ya dugunzuma ainun
ba don komaiba sai saboda sun gane cewa an jefa
akushin sihiri guda biyu a cikin wutar ibilisai.
Koda suka fahimci hakan sai kowannansu ya
kurma ihu suka durkushe kasa bisa guiwoyinsu cikin
matsanancin bakin ciki nan take ko wannansu yasa
takobinsa ya soka a cikinsa suka bingire kasa matattu.
Kamar yadda Gimbiya sazira ta yi alkawari haka
abin ya kasance domin an daura aurenta da jarumi
Lurwan. Shi kuma Yarima Andaz an tsinci gawarsa a
filin yaki anyi gunduwa-gunduwa da ita. An sare
kansa an ajiye shi kusa da gawar mahaifinsa.
Daga wannan rana aka sami zaman lafiya da
kwanciyar hankali a wannan nahiyar gaba daya.
Sarakuna suka rinka tabbatar da adalci gami da
tausayi da jin kan talakawansu.
ALHAMDULILLAH
ABDUL-AZIZ SANI MADAKIN GINI
KARSHЕ
80
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels