can gefe daya yana murginawa da kasa, kafin
ya tashi tsaye tuni Boka Aryan ya zaro wuka ya
lumawa dokin boka samosa dana sarki Ridwan nan
take dawakan suka zube kasa matattu.
Lokacin da Boka samosa ya mike tsaye ya
hango sarki Ridwan na fadowa kasa daga saman
tsauni sai ya kurma ihu ya ruga da gudu gareshi
domin ya sa hannayensa biyu ya tareshi karya fado
kasa amma kafin ya isa wajen tuni sarki Ridwan ya
fado kasa tim! Bisa kasa nan take jini ya zubo ta
cikin hancinsa da bakinsa. Boka samos ya fada kan
sarki Ridwan ya tasoshi zaune ya rungumeshi akan
kirjinsa ya kurma ihu kuma ya fashe da
matsanancin kuka domin a zatonsa sarki Ridwan ya
mutu.
A daidai wannan lokacin sarki muraka ya gama
saukowa kasa daga saman, yana kyalkyala dariya
mugunta da farin ciki a guje boka Aryan ya zo da dawakansu guda biyu suka kama suka hau suka
juya da gudu suka nufi birnin saman suka bar Boka
samosa rungume da sarki Ridwan yanba ta faman sharar kuka
Jarumi da Gimbiya
Tsawon dakiku masu yawa Boka samasa yana
ta faman rusa kuka cikin matsanancin bakin ciki sai
ya yunkura domin ya mike tsaye ya dauki gawar
sarki Ridwan ya dorata a kafadarsa kawai sai ya ji
sarki Ridwan ya yi tari gami da furza da jini daga
cikin bakinsa. Koda ganin haka sai farin ciki ya
kama boka samosa ya dubeshi yace "Ya shugabana
bari nayi sauri na yi maka magani sannan na ruga
na bi bayan su sarki muraka, ka sani ina barin
dajinan karfin sirrin tsafina zai dawo don haka zan
riga su Boka Aryan isa birnin soman naje na tona
musu asiri bisa ha'intarmu da suka yi a wannan
gasar da kuma yunkurin kasheka da sarki muraka
ya yi. Sa'adda sarki Ridwan ya ji wannan batu na
boka samosa sai ya girgiza kai yace "Ai ko kaje ka
tona musu asiri a banzane tunda sarki muraka ne
zai rigani kai sadakin gimbiya falman wannan itace
kaddarata. Ba zan taba mallakar gimbiya falman ba
amma ka sani da raina sarki muraka da ransa sai
shima ya rasa gimbiya falman kamar yadda nima
na rasa yanzu.
CI GABAN LABARI
Wannan shi ne asalin abinda ya haddasa
kiyayya a tsakanin sarki Ridwan da sarki Muraka
bayan an haifi Yarima Andaz da shekara uku-ne
sarki Ridwan ya yi aure aka haifi gimbiya sazira.
Sai dai kowannansu ya girma ya balaga wata rana
aka wayi gari gimbiya falman ta tashi da wani ciwo
me tsanani wanda aka kasa gane irinsa da kuma
musabbabinsa
55
Jarumi da Gimbiya
Babu irin likitocin da ba'a taraba domin su yi
mata magani amma abu ya faskara dagananne aka
fara tuntubar bokaye domin neman maganin cutar
da kyar wani boka dake can birnin sin ya gano
matsalar ya sanar da sarki cewar sarki Ridwan ne
ya yi wani sihiri ya binneshi a karkashin tsakiyar
teku cikin rami me zurfin kamu dubu, aljanun da
suka yi wannan aikin kuma duka an hallakasu
kuma duk duniya sune za su iya ciro wannan sihiri
su lalata shi. Gimbiya falmin ba zata wuce sati uku
ba a kwance tana jinya zata mutu.
Lokacin da sarki muraka ya ji wannan jawabi
sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya fashe da
matsanancin kuka. Daga wannan rana sai kulluum
cutar gimbiya falmin ta rinka kara tsanani babu
alamar sauki, sarki muraka ya tare a cikin turakar
gimbiya falmin dare da rana yana kallonta yana
kuka tare da dansa Yarima Andaz, haka suka
kasance har tsawon sati uku sannan rai ya yi
halinsa.
Bayan an binne gawar gimbiya falmin ne sarki
muraka tare da dansa Yarima Andaz suka kadaita
da wannan boka na birnin sin wanda ake kira da
suna boka linjolin sarki muraka ya dube shi yace
"Ya kai boka linjolin ka sanar da ni abinda zan yi
na murkushe sarki Ridwan na yi masa kisan gillah
kuma kasarsa ta dawo karkashin mulkina?" Ya yin
da boka linjolin ya ji wannan batu na sarki muraka
sai ya yi doguwar ajiyar zuciya sannan ya dago kai ya kalleshi sannan ya kalli Yarima Andaz yace "Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa a wannan gidan
Jarumi da Gimbiya
sarauta naka akwai wani akushi na sihiri hakane?"
Sarki muraka ya gyada kai yace.
"Hakane akwai shi" Boka linjolin ya се
"Wannan akushi ya kai shekaru dari uku da goma
sha daya ajiye a cikin dakin mahaifinka a samansa
akwai kofofi guda biyu kuma agefansa akwai wani
bututu wanda zai iya fitar da hayaki. To kasani
cewa akwai irin wannan akushi a can fadar sarki
Ridwan, a cikin ku duk wanda ya samu nasarar sato
jinin daya daga 'ya 'yanku ya diga a cikin kofar
akushin guda goma wani hayaki zai tashi daga
cikin akushin ya lulluße shi, da zarar hakan ta faru
zai samu nasara-kashe abokin -hamaiyarsa-ya
mallake Kasarsa".
Koda jin wannan batun sai sarki muraka yace
"Na rantse da darajar gemun ubana da kuma
kabarin kakana sai na tura an sato mun gimbiya
sazira 'yar sarki Ridwan sai na debi jininta dana
dana na diga a cikin wannan akushi domin cikar
wannan burin nawa". sa'adda da yarima Andaz ya
ji wannan batu na mahaifinsa sai farin ciki ya kama
shi yace "Ya kai Abbana ni kuma na yi maka
alkawari bayan ka sami wannan nasara sai na yi
gunduwa-gunduwa da sassan jikin gimbiya sazira
na zuba shi a cikin akwati na aikawa da mahaifinta
ya gani domin daukar fansa kisan daya yi wa
mahaifiyata".
Sarki muraka ya yi murmushi ya rungume
yarima Andaz yace "Babu shakka sai mun cika
wadannan burika na mu
Jarumi da Gimbiya
Sarki muraka na tsaye a cikin turakarsa yana kai kawo cikin alamun tashin hankali sai ga boka Rimasu ya shigo cikin turakar da sauri ya zube kasa ya kwashi gaisuwa. Sarki muraka ya kama kafadarsa ya tasheshi tsaye suka dubi juna yace
"Ya kai Rimasu da ga amintacce na Boka Aryan ka
yi sani cewa jiya da daddare na yi wani mugun mafarki wanda ya yi matukar girgiza hankalina. Tunda na farka daga bacci kafin ketowar alfijir har
kawo yanzu ban sake rintsawa ba" Sa'adda boka
Rimasu ya ji wannan batu sai ya yi guntun
murmushi ya kama hannun sarki muraka ya ja shi
izuwa kan wata doguwar kujera suka zauna ya tashi
ya dube shi a nutse yace.
"Ya haba ya shugabana yau shekara dari uku
kenan da kafa wannan masarautar, tunda aka kafata
kakannin nakane suka malketa har abin ya zo
kanka, tsawon wannan lokaci ba'a taba cinka da
yaki ba, akan wannan dalilin wani mafarki na
banza zai sa hankalinka ya tashi" Yana gama fadin
haka sai ya dubi wata kuyanga da ya hango a can
kusa da kofar turakar zata wuce ya "Maza aje a
kawo wa sarki abincin kalacinsa" Nan fa Boka
Rimasu ya daukewa sarki muraka hankali da hira
me dadi har aka kawo abincin kalaci suka ci suka
sha tare suka yi hani'an sai da boka Rimasu yaga
hankalin sarki ya kwanta sosai ya saki jikinsa da
shi sannan ya dube shi yace.
"Ya shugabana bani labarin mafarkin da ka yi
jiya da daddare koda jin wannan tambaya sai
58
Jarumi da Gimbiya
fuskar sarki muraka ta sauya izuwa damuwa ya yi
gyaran murya yace.
"Ya kai amintaccen bokana kuma dirkar birnin
samhar kayi sani cewa mafarkin da na yi shi ne
wata kyakkyawar barewa ta shigo har nan cikin
fadata ta ci abincin da nake ci a cikin kwanukan
abincina mai albarka, kowa na kallonta amma an
rasa wanda zai dakatar da ita ko ya kasheta, ina ji
ina gani ta juya ta fice daga cikin fadar amma kafin
ta tafi sai da ta zo gaban dana yarima Andaz ta
cijeshi a hannu Yarima ya kurma ihu ya fadi kasa
yana karkarwa tamkar maciji ya sareshi. A daidai
wannan lokacin na farka daga bacci a firgice,
wannan shi ne dalilin daya sa na aika a kiraka
domin nasan fassara wannan mafarkin" Boka
Rimasu ya bude baki da nufin ya yi magana sai
yarima Andaz ya shigo cikin turakar fuskarsa cike
da alamun damuwa.
Sarki muraka ya tareshi suka rungume juna
sannan ya janye jikinsa daga cikin nasa ya dube shi
yace "Ya kai dana menene ya faru naga babu
annuri a fuskarka?" Yarima Andaz ya numfasa
yace "Ya kai Abbana yau kwana biyu kenan da
muka tura jarumi lurwanu tare da dakarun sumame
guda shida izuwa birnin kilmaz domin sato gimbiya
sazira amma shiru kake ji kamar maye ya ci
shirwa.nifa na yi wani mafarki wanda ya yi mini
nuni da ba zamu sami nasarar cikar burinmu-ba
akan sarki Ridwan" koda jin wannan batu sai boka
Rimasu ya yi caraf yace.
59
09
Jarumi da Gimbiya
"Wannan mafarkin naka ba gaskiya bane, ya
kai yarima ka yi sani cewa nasara tana tare da mu a
wannan masarauta domin bamu taбa samun
akasinta ba, ka je ka kwantar da
hankalinka,kwanaki goma ba za su cika ba face
jarumi lurwan ya zo da gimbiya sazira, yana kuma
kawota za mu dauki akushin sihiri mu diga jininka
da nata a ciki domin hayakin daukaka ya rufe
mahaifinka mu sami damar cika burinmu" Lokacin
da yarima Andaz ya ji wannan batu sai farin ciki ya
lullubeshi ya rungume boka Ramisu yace "Da zarar
ka fita daga nan zaka iske kyauta ta musamman
יי
saboda wannan kyakkyawan albishir da ka yi mini"
Yarima na gama fadin haka sai ya juya ya fice daga
cikin turakar yana mai farin ciki mara misaltuwa.
Sarki muraka ya dubi boka Rimasu yace "Maza
ka sanar da ni fassarar mafarkin da na yi da wannan
barewa" Boka Rimasu ya yi ajiyar numfashi gami
da sunkuyar da kansa kasa sannan ya dago ya dubi
sarki yace "Wannan mafarkin ba zai fassaru ba a
yanzu dole sai naje na yi bincike a kansa kuma
binciken zai iya daukata kwana shida, ka huta
lafiya ya shugabana sai na sake dawowa
gareka"Boka Rimasu na gama fadin hakan sai ya
juya ya fice daga cikin turakar shi kuma sarki
muraka sai ya bishi da kallo cikin matukar
mamakin dalili kuwa shi ne boka Rimasu bai taба
jinkirta yi masa fassarar mafarkinsa ba sai yau. Duk mafarkin da ya yi indai ya sanar da shi to
nan take yake fassarashi mene ne dalilin da yasa
Jarumi da Gimbiya
boka Rimasu yaki fassara mini wannan mafarkin
yanzu? Sarki muraka ya tambayi kansa.
Lokacin da Yarima Andaz ya baro turakar mahaifinsa sarki muraka sai ya wuce kai tsaye izuwa cikin turakar mahaifiyarsa marigayya gimbiya falman.
Ita dai wannan turaka an kawatata ainun- da
kayan alatu na kyale-kyale duk da cewa ba a
gudanar da komai a cikin wannan turaka amma kullum sai an tsaftaceta tamkar me turakar na nan a
raye, daga safe zuwa dare zaka iske an kunna
turaren wuta a cikinta me kamshin gaske kuma
zaka ga kuyangi suna ta kai kawo a cikin turakar
suna gabatar da hidimominsu.
Da shigowar yarima Andaz-cikin wannan
turakar sai gaba daya kuyangin da suke hidima
suka fice suka ja kofa suka rufe. A tsakiyar wannan
turaka akwai gunkin gimbiya falmin wanda ya
kasance kato kuma dogo, gunkin ya sassaku ainun
kamar zata bude baki ta yi magana kamanninta sun
fita sosai, kawai rai ne da babu a jikin gangar jikin.
Yarima Andaz ya karaso daf da wannan gunki na
mahaifiyarsa ya daga kai ya kura masa idanu
tsawon 'yan dakeku sai hawaye ya zubo masa ya
bude baki yace.
"Ya ke ummina kiyi sani cewa a wannan
duniya babu abinda nake so sama dake, an kashe ki
a lokacin da nafi bukatarki a rayuwata, baki da buri
face na ganin aurena amma babban makiyinmu
sarki Ridwan ya yanke wannan burin naki, na
61
Jarumi da Gimbiya
rantse da soyayyar da nake yi miki ba zan taba yin
aure ba face na saro kan sarki Ridwan na zo da shi
gabanki a sannan ne zan cika miki burinki na yi
aure. Ina mai tabbatar miki da cewa sauran kiris
wannan al'amarin ya tabbata da zarar gimbiya
sazira ta fado hannunmu" Yana gama fadin hakan
sai ya sake matsawa jkin gunkin ya rungumeshi ya
fashe da kuka.
Wannan shi ne abinda ya faru a birnin samhar
bayan sarki muraka ya yi mafarkin data dugunzuma
hankalinsa.
**
A can birnin kilmaz kuwa bayan tafiyar
gimbiya sazira cikin daji a cikin siffar kuyanga
Dulus sai ita kuyangar Dulus din ta ci gaba da
zartar da komai kamar yadda gimbiya ta saba
aiwatarwa batare da kowa ya gane a itace ba.
Amma fa hankalin kuyanga Dulus a tashe yake tun
daga lokacin da sarkin yaki kinana ya taba
kafadunta taga ya yi mata wani irin mugun kallo
alamar bai yadda da ita ba, sai dataga an shafe
sama da sa'a uku bai sake dawowa gareta ba
sannan hankalinta ya dan kwanta.
A farkon yammaci ne sarki Ridwan ya turo aka
sanar da Dulus cewa yana so ta sameshi a cikin
lambu na gidan sarautar domin su yi gani na
musamman. Koda jin wannan sako sai hankalin
kuyanga Dulus ya dugunzuma ta rasa abinda yake
yi mata dadi a duniya. Dalili kuwa shi ne bata taba
e
62
Jarumi da Gimbiya
raka gimbiya sazira lambun ba bare taga irin
abubuwan da suka saba yi da sarki a can ba.
Tunaninta shi ne idan fa har bata yi abubuwan
da gimbiya ta saba yiwa sarki ba to tabbas zai gano
ba ita bace kuma idan ya gano hakan hkuncin kisa
ne zai tabbata a gareta, gashi a wannan lokacin jakadiyar sarki ce ta zo da kanta ta tsaya tana
jiranta su tafi tare don haka babu damar da Dulus
zata iya shiga cikin daki ta dauko tsuntsuwar sihiri
ta karfe ta aiketa izuwa wajen gimbiya sazira
domin samo mata mafita. Zuciyar kuyanga Dulus
na bugawa ta mike tsaye tabi jakadiya suka fice daga cikin turakar suka nufi cikin gidan sarautar Gangaren da lambun yake.
Suna cikin yin wannan tafiyar ne jakadiya ta
lura da gimbiya cewar tana cikin alamun damuwa
ko fargaba, don haka sai ta dubeta tace "Ya
shugabata wai shin me kike tsoro ne akan fuskantar
sarki yanzu a can lambu?" koda jin wannan
tambayar sai zuciyar kuyanga Dulus ta buga da
karfi amma sai ta basar tace "Ya ke jakadiya ba
wani tsoro nake ji ba face bana son sarki ya bijiro
mini da maganar aure, kinsa na yi alkawari ba zan
yi aure ba face idan tsufane ya riski sarki yadda ba
zai iya tafiyar da mulki ba, to lallai ba zan hau kan
karagar mulki ba face ina da miji" Jakadiya tace.
"Ai kuwa sarki ba zai taba lamintar wannan
uzuri naki ba" Gama maganar ke da wuya suka
karaso kofar shiga lambun kawai sai suka hango
sarki Ridwan tsaye a cikin lambun yana jiran
karasowarsu fuskarsa cike da annuri ita kuwa
Jarumi da Gimbiya
kuyanga Dulus zuciyarta ce ta ci gaba da bugawa
da karfin gaske akai-akai kai tsaye sarki Ridwan ya
tunkaro kuyanga Dulus da nufin ya rungumeta
kamar yadda suka saba kawai sai yaga ta kauce
masa ta nufi izuwa inda kujerun lambun suke ta
zauna akan kujera me daukar mutum daya ta
sunkuyar da kan kas tayi tagumi.
Cikin tsananin mamaki sarki Ridwan ya taho
gareta ya tsaya a lokacin da tazarar dake tsakaninsu
takai taku uku ya dubeta yace "Ya ta yau kuma
mene ne ya faru naga kina guduna? Kuma babu
walwala da annuri akan fuskarki? Jikinki babu
kwari tamkar baki da lafiya, mene ne yake
faruwa?" Kuyanga Dulus ta daga kai ta dube shi
fuskarta cike da alamomin damuwa tace.
"Na yi mafarki ka aurar da ni ga mijin da bana
so, shin gaskiya ne kana da wannan tunanin a cikin
zuciyarka?" Koda jin wannan tambayar sai mamaki
ya kama sarki ya dubeta ya kauda kai sannan ya yi
ajiyar zuciya sannan ya je ya zauna akan wata
kujera dake fuskantar tata suka kurawa juna idanu
yace "Kafin mahaifiyarki ta rasu ta nemi alfarmar
kada na aurar da ke ga mijin da ba kya so, na yi
mata alkawarin hakan kinga kenan mafarkinki ba
zai taba zama gaskiya ba, nasan alkawarin da kika
daukarwa kanki cewa cewa ba za ki yi aure ba har
sai na yi tsufan da bazan iya tafiyar da harkokin
mulki ba to kasancewar wannan alkawari naki ba
zai taba cika ba saboda ba haka Kaddararki take ba,
tabba nan ba da dadewa ba za ki auri dan sarkin da
babu kamarsa a wannan nahiyar tamu Koda jin
64
Jarumi da Gimbiya
wannan batu sai mamaki ya kama jakadiya da
kuyanga Dulus suka kalli junansu sannan Dulus
tace.
"Ya kai Abbana a nahiyar nan gaba daya babu
wani dan sarki wanda yafi Yarima Andaz na birnin
samhar, tsakaninmu da su kiyayyace ta tsawon
daruruwan shekaru ta yaya zan aure shi ko kuma
akwai wani 6oyayyen dan sarkine wanda-ya
fishi?sa'adda sarki Ridwan ya ji wannan tambaya
sai ya bushe da dariya sannan yace "Babu wani
boyayyen dan sarki wanda yafi Yarima Andaz,
lallai shi za ki aura amma wata kila a wannan
lokacin ni da sarki muraka duk ba ma raye" Koda jin haka sai hankalin Dulus dana jakadiya ya tashi suka kurawa sarki idanu sarki Ridwan ya yi
murmushi ya mike ya nufi wajen da- Gimbiya take,
itama sai ta mike tsaye yana zuwa daf da ita sai ya mika mata hannunsa da nufin ta kama ta rike
domin su fice daga cikin lambun.
Nan take zuciyar Dulus ta yi mugun bugawa da karfi fiye da koyaushe ta yi kamar ba zata ba shi
hannunta ba amma sai ta mika masa hannun, yana
dora hannunsa akan nata sai shi da ita suka ji
kamar an jona musu wutar lantarki ba shiri
kowannansu ya janye hannunsa kuma suka kurawa juna idanu cikin alamu na rashin yadda, kawai sai taga sarki Ridwan ya yi murmushi yace "Gimbiya
baki da lafiya akwai zazzabi a jikinki, wannan gadone kika yi a wajen mahaifiyarki saboda itama idan bata da lafiya a hannunta nake ganewa, maza ki koma turakarki zan turo likitana ya duba
65
Jarumi da Gimbiyа
lafiyarki" Yana gama fadin haka sai ya juya ya fice daga cikin lambun ya nufi bangaren tasa turakar, jakadiya ta bishi da sauri a baya ita kuma kuyanga Dulus ta bisu da kallo kawai, har a sannan
zuciyarta bata daina bugawa da karfi kuma tana ji a
jikinta asirinta ya gama tonuwa.
**
A can daji kuwa lokacin da jarumi lurwan tare
da Gimbiya sazira suka isa inda abokan aikinsa
suke dakarun sumame shida yana dauke da naman
damisa akan kafadarsa sai jaruman shida suka cika
da tsananin mamaki sakamakon hango shi da sukai
tare da bakuwar mafauciya daga can nesa ya yin da
suka matso kusa da su sai daya daga cikin yaran
nasa wanda ake kira karzim ya kurawa gimbiya
sazira idanu yana yi mata wani irin kallo mai nuna
alamun rashin yadda, jarumi lurwan ya jefawa
karzim wannan naman damisar ya cafe ya dubeshi
yace.
"Maza a gasa mana wannan nama domin tarbar
babbar bakuwata" Yana gama fadin hakan ya wuce
cikin tanrinsa ba tare da wata fargaba gimbiya
sazira ta bi jarumi lurwan cikin tanrin. Lurwan ya
kwanta akan shimfida ya mike Kafafuwansa domin
ya huce gajiya. Ita kuwa sai ta zauna a gaban wata
butar ruwa, ta dauki kofi ta zuba ruwan tasha ta dubeshi tace.
"Kafin mu gama yarjejeniya akan harkallar da
zamu kulla ina so ka ban amsar tambayata" A cikin
mamaki jarumi Lurwan ya dubeta yace "Wacce
amsa kike so na baki?"
66
Jarumi da Gimbiya
"Ina so ka gaya mini dalilin da yasa ka siyar da rayuwarka ka zo nan birnin kilmaz dmin ka sato gimbiyata? Ka sani cewa fada mini gaskiyarka shi
ne kadai zai sa na aminta da kai mu yi wannan harkallah. Duk da cewa na dade ina da burin samun
'yancin bauta da kuma samun tarin arziki zan iya
hakura da su muddin na fahimci cewa ka boye mini gaskiyarka" Lokacin da jarumi lurwan yaji wannan
batu sai ya mike zaune ya dubi gimbiya sazira cikin
wani irin yanayi na rashin yadda sannan yace.
"Kinyi mini tambaya bisa abinda ya shafi sirrina wanda idan na saran dake shi bani-da
tabbacin anan gaba ba za ki iya ha'intataba"
Sa'adda gimbiya sazira ta ji wannna batu sai tayi
murmushi ta ce "Ai sarkinka ya gama ha'intarka
tunda ya yi garkuwa da wacce kafi so a duniya-ya
yi maka dole ka taho sace gimbiyata" Koda jin
wannan batu sai jarumi Lurwan ya-yunkura cikin
bakin zafin nama ya zaro wuka daga cikin jakarsa
ya dorata akan wuyan gimbiya yace "Wacece ke?
Ya aka yi kika san wannan sirrin?" Tayi murmushi
ba tare da tsoron komai ba tace.
"Ni ce wacce ka zo ka sace Gimbiya sazira, za
ka dauke kaifin wukarka daga kan wuyana ko sai
ka hallakani na zama gawa yadda naka aikin zai
lalace sarki muraka ya kashe mahaifiyarka" Koda
jin haka sai jarumi Lurwan ya yi sauri ya janye
wukarsa daga kan makogwaron gimbiya ya kura
mata idanu cikin tsananin mamaki, jikinsa na tsuma
kawai sai gimbiya ta rikide ta dawo izuwa ainihin
siffarta koda ya yi arba da ita sai zuciyarsa ta buga
67
Jarumi da Gimbiya
da karfi fiye da lokacin daya ganta jiya da daddare
a cikin turakarta, nan take ya ji ya kamu da
tsananin sonta a cikin zuciyarsa amma daya tuna
cewa wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa sai ya
danne zuciyartasa ya yi mata dole akan ta manta da
abinda ta aiyana masa.
Jarumi Lurwan ya dago kai ya dubeta yace
"Amma fa ina mamakin abinda ya hana mahaifinki
ya turo dakaru su biyo sawunki alhalin bakya cikin
gidan sarautar yanzu" Sazira ta yi murmushi me
taushi a gareshi wanda ya sake dimautashi a karo
na biyu tace "Wacce na zo maka da siffarta itace
take wakiltata a cikin tawa siffar acan fadarmu don
jaka babu yadda za'a gane cewa bana nan, ya kai
wannan jarumi ni nasan abubuwa da yawa wanda
kai baka sani ba kuma a shirye nake na taimakeka
domin ka kubutar da mahaifiyarka daga hannun
azzalumin sarkinku wato sarki muraka amma sai
idan nima zaka taimakeni" Ya dubeta cikin mamaki
yace.
"Wane irin taimakone zan iya baki?"
"Ina son da zarar ka kai ni wajen sarkin ku
yaga ya mallakeni, hankalinsa ya kwanta a cikin
dare kai kuma sai kabi daren ka sace wannan
akushin sihirin wanda aka ajiye shi a cikin dakin
tarihi na masarautarku tsawon shekaru dari uku da
suka gabata, lallai ina son ka tafi da wannan
akushin sihiri izuwa cikin wutar ibilisai da take ci a
Karkashin dutsen larzo a bayan birninku".
Saadda da gimbiya
jawabinta sai hankalin
sazira tazo nan
jarumi Lurwan
a
ya
68
Jarumi da Gimbiya
dugunzuma ainun saboda dalilai guda biyu, dalili
na farko shi ne yasan cewa wannan aiki da take so
ya yi mata yana da mugun hatsari, babu tabbas zai iya tsira da rayuwarsa kafin ya sami nasara. Abu na biyu shi ne idan har ya sami nasarar jefa wannan akushin sihiri a cikin wutar ibilisai dake cikin dutsen larzo to tabbas sai masarautarsu -ta fadi
kuma har abada mulkin kasar ya bar hannun zuri'arsu sarki muraka.
Ya yin da gimbiya sazira taga jarumi Lurwan
ya yi shiru yana ta tunanin wannan babbar harkallah da ta zo masa da ita sai ta katse masa
tunanin tace "Nasan ba komai kake tsoro ba face
rushewar masarautar ku to ka sani a yanzu haka nima na sato akushin sihiri na tamu masarautar
kuma can zan kai-shi cikin wutar ibilisai na jefa shi
ya narke ba domin komai ba face ina son kawo karshen zalluncin mahaifina sarki Ridwan da kuma
karshen zalluncin sarki muraka, idan ba haka muka
yi ba har abada ba za'a sami zaman lafiya da adalci
a wannan nahiyar-gaba daya ba, lallai ina son ka
bani hadin kai dari bisa dari domin mu ceto
rayuwar al'umma yakin gaba daya".
Lokacin da Gimbiya sazira ta zo nan a
jawabinta sai jikin jarumi lurwan ya yi sanyi ya
sake yin shiru yana tunani. Ya mike tsaye ya kama
yin kai kawo a cikin tantin ita kuma sai ta mike
tsaye ta kura masa idanu kawai. Daga can sai ya
juyo ya dubeta yace "Rai na fansane ga al'ummar
da zata ta so nan gaba a wannan nahiyar, na rantse
69
Jarumi da Gimbiya
da soyayyar da nake yiwa mahaifiyata na baki raina da jikina domin tabbatar da wannan batu" Jin haka sai farin ciki ya lullube gimbiya sazira don haka bata san lokacin da ta ruga izuwa ga jarumi Lurwan ta rungume shi ba, mamaki ya
turnuke jarumi Lurwan ya kasa riketa da
hannayensa biyu yace a cikin ransa ya aka yi
wannan 'yar sarkin mai daraja da daukaka haka ta
hada jikinta da nawa alhalin naji ance in banda
mahaifinta da sarkin yakin garinsu babu wanda ya
taba hada jikinsa da nata.
Kawai sai yaga gimbiya ta janye jikinta daga
cikin nasa ta dubeshi cikin murmushi tace "Kai ne
namiji na farko da na yi gumurzun fada da shi, tun
a daren jiya da muka fafata jarumtakarka ta burgeni,
a yanzu kuma dana zo na ji yadda ka sallama
rayuwarka don ceto ta mahaifiyarka da kuma yadda
ka sake bayar da rayuwarka domin gyara rayuwar
'yan gobe sai na ji na kamu da matukar kaunarka,
idan har mun rayu a cikin wannan kyakkyawan
kuduri to lallai kai ne mijin da zan aura, maza ka
fita ka baiwa yaranka umarni su yi shirin tafiya
domin mu isa birnin samhar kafin dare ya raba"
Tana gama fadin hakan sai taje ta kwanta akan
shimfida tana kallonsa cikin murmushi, wani irin
farin ciki mara misaltuwa ya lulluße jarumi Lurwan
gami da mamakin wai yau shi ne gimbiya sazira ta
kaleshi ido da ido tace tana son sa. Mutumin da shi
a rayuwarsa bai taba ganin wata 'ya mace ya ji
yana sonta ba alhalin da yawa sun ce suna son sa
yaki.
Jarumi da Gimbiya
To ya aka yi yanzu ya ji ya kamu da tsananin
son gimbiya sazira farat daya alhalin har yanzu
zuciyarsa tana tabbatar masa da cewa wannan fa
abune wanda ba zai taba yiyuwa ba domin
tazararsa da gimbiya sazira tamkar tazarar sama da Kasane.
Wannan shi ne abinda ya faru a daji tsakanin
gimbiya sazira da jarumi Lurwan bayan sun hadu a
wajen farauta.
A can fadar birnin kilmaz kuwa tun sa'adda
sarki Ridwan ya rabu da 'yarsa gimbiya sazira a
bayan sun hada hannu ya ji kamar wuta ta jashi sai
zuciyarsa ta cika da wasu-wasi ya fara zargin anya
kuwa wannan 'yarsace sazira. Dalili na farko da ya
sa masa wannan shakku shi ne gimbiya bata taba
kin rungumarsa a duk sa'adda suka hadu koda
kuwa haduwa ce ta dari a rana.
Dalili na biyu shi ne me yasa ya ji kamar wutar
lantarki ta ja shi a lokacin da suka hada hannu?
Tunanin wadannan abubuwane guda biyu suka sa
sarki Ridwan ya rasa sukuni, kawai sai ya sa aka
kawo masa doki ya yi hawa shi kadai cikin batar da
kama ya nufi gidan boka Rimasu kai tsaye.
Boka Rimasu