da
sarki muraka ne kadai kuke da irin wannan akushi
na sihiri a wannan nahiyar, kuma wannan ne dalilin
da ya saka yake son a sato masa 'yarka gimbiya
sazira, kuma kaima shirinka kenan ka saka a sato
maka Yarima Andaz, a yanzu haka ma ka tura
sarkin barayi na wannan nahiyar gaba daya ya tafi
birnin samhar domin ya sato maka Yrima Andaz
harma ya tabbatar maka da cewar kafin kwana
bakwai zai kawo maka shi, ka basa rabin ladan
aikinsa darhami dubu dari da hamsin bisa
18
Jarumi da Gimbiya
alkawarin idan bukatar ta biya zaka cika masa
ragowar darhami dubu fari da hamsin".
Lokacin da sarkin yaki kinana ya zo nan a
jawabinsa sai sarki Ridwan ya kamu da tsananin
mamaki ya dubeshi yace "Ya kai kinana ya aka yi
duk kasan wannan sirri alhalin tun da na gaji
sarautarnan ban taba gayawa kowa batun wannan
akushin sihirin ba kuma duk abinda zan yi ni kadai
nake yinsa a sirrance. Wannan fa burine wanda
mahaifina ya mutu da shi kuma ya bar mun wasiyar
na cika shi koda zan rasa rayuwata" Sarkin yaki
kinana ya sake yin murmushi a karo na biyu sannan
yace.
"Kada ka manta cewa kamar yadda ka gaji
sirrin wannan gidan sarauta namu haka nima na
gaji sarautar sarkin yaki na wannan birnin namu.
Babu abinda mahaifina bai sani ba na dangane da
mahaifinka amma shima sai ya yi shiru bai nuna
yasan komai ba. Nima yanzu in ba don ka
tambayeni ba da ba zan taba nuna maka na san
wani abu ba, ina son ka sani cewar sarkin barayi ba
zai taba iya sato maka Yarima Andaz ba, kuma duk
duniya babu wanda zai iya sato maka shi face
mutum daya" Cikin matukar mamaki sarki Ridwan
yace.
"Wanene wanda zai iya sato mun Yarima
Amdaz? Na rantse da kabarin mahaifina ko nawa
yake so zan biya shi" Kinana ya yi ajiyar numfashi
yace "Wanda zai iya sato Yarima Andaz yafi kowa
kusanci da kai kuma baya bukatar sisin kwabo
daga hannunka to amma kai ba zaka bari ya je ya
19
Jarumi da Gimbiya
kai kansa birnin samhar ba" Koda jin wannan sai
sarki Ridwan ya mike tsaye cikin tsananin mamaki
ya nuna kinana da hannu yace.
"Kana nufin kace da ni 'yarta gimbiya sazira се
kadai zata iya zuwa birnin samhar ta sato mini
Yarima Andaz?" Kinana ya gyada kai cikin
murmushi yace "Tabbas ko shakka babu itace
kadai zata iya yin hakan saboda abinda baka sani
ba shi ne boka samasa ya bata horon yaki dana
jarumtaka a sirance kafin ya mutu ba tare da kasani
ba haka kuma ya tsumata a cikin sihirin tsafi da ko
ni da kai bamu da irinsa, duk maganar data gaya
maka da zu karya tayi maka. Jarumin da aka aiko
daga birnin samhar domin ya saceta bakin gumurzu
suka yi shi da ita aka rasa mai samun nasara a
tsakaninsu saboda jarumtarkarsu da karfin sihirinsu
ya kusan zuwa daya".
Koda jin wannan batun sai mamaki ya kara
turnuke sarki Ridwan ya yi shiru yana tunani
sannan ya dubi kinana yace "Me yasa tuntuni duk
baka sanar da ni komai akan 'yata ba sai yanzu?"
Kinana yace.
"Saboda kai ma kana boye mini komai naka,
baka yarda da ni ba kamar yadda mahaifinka ya
yarda da mahaifina, kuma ba komaine ya janyo
hakan ba face kai kafi son kanka da kowa" Sarki
Ridwan ya bushe da dariya yace "Tabbas kafi kowa
sanina a garinnan kuma nima nasan cewa ba zan
iya gyara halina ba amma tunda ka fito mini a
mutum me zai hana muyi wani abu guda?" Kinana
yace.
20
Jarumi da Gimbiya
"Me kake so muyi?"
"Ka taimaka mun na cika burin mahaifina ni
kuma na yi alkawari da kabarin mahaifina zan baka
kasata biyu na baka rabi ka mulketa" Sarkin yaki
kinana ya yi murmushi yace.
"Ni a rayuwata ban taba jin ina sha'awar mulki
ba, kuma bana sha'awar na tara dukiya mai yawa.
Burina guda dayane jal a duniya, matata bata taba
haihuwa ba amma kafin boka samasa ya mutu-ya
fada mun ba zata taba haihuwa ba face an hada
jinin 'ya'yan sarakuna guda biyu na wannan
nahiyar an bata ta lasa da harshenta. Ka yi mun
alkawari cewa idan aka sami nasarar kawo maka
Yarima Andaz zaka ciri jininsa da na Gimbiya
sazira ka hada a waje guda a baiwa matata tá lasa,
sai munje da kai gaban kabarin mahaifinka ka dafa
kabarin da hannunka kayi rantsuwa bisa cewa zaka
biya mini wannan bukatar sannan nima zan
taimaka maka ka cika wannan burin naka ina
tabbatar maka da cewa nasan yadda zamu iya sato
yarima Andaz ba tare da Gimbiya sazira taje da
kanta ta sato shi ba, hakan shi ne zai fiye maka
kwanciyar hankali domin kada garin neman gira a
rasa idanu gaba daya. Tura gimbiya izuwa birnin
samhar domin sato Yarima Andaz ba karamin
ganganci bane"
Lokacin da sarkin yaki kinana ya zo nan a
jawabinsa sai hankalin sarki Ridwan ya dugunzuma
fiye da koyaushe ya mike tsaye ya kama kai kawo
yana tunanin mafita. Abu na farko dai shi ne boka
samasa ya gayamasa cewar duk matar data
211
Jarumi da Gimbiya
dandani jinin 'ya 'yan sarakunan biyu na nahiyar
akan harshenta sai ta haifi sarkin da zai mallaki
Kasashen nahiyar gaba daya. To ya za'ayi kuwa ya
bari wannan damar tabar ahalinsa ta koma ahalin
sarkin yaki.
Yanzu kuma ya tabbatar da cewa idan bai yiwa
sarkin yaki abinda uake so ba to shima bukatarsa
ba zata biya ba. Yanzu ina mafita a gareshi? Yana
cikin wannan tunanin zuciyarsa ta bashi mafita tace
da shi kawai abinda za'ayi shi ne ya je ya yiwa
sarkin yaki wannan alkawari a gaban kabarin
mahaifinsa amma da zarar tasa bukatar ta biya sai
yasa a kashe matar sarkin yaki a sirrance tunda ai
sai tana raye sannan ma zata iya haifar dan da zai
mallake nahiyar gaba daya. Koda zuciyar sarki
Ridwan ta kimtsa masa wannan dabara sai farin
ciki ya lullubeshi. Cikin hanzari ya dubi sarkin
yaki yace.
"Na amince yau da yamma za muje da kai
gaban kabarin mahaifina na daukar maka wannan
alkawarin" Koda jin haka sai farin ciki ya lullube
sarkin yaki kinana ya mike tsaye suka rungume
juna yana yiwa sarki Ridwan godiya, yana ta
murmushi amma shi sarki Ridwan fuskarsa a
murtuke take cike da guzurin mugunta.
**
Gimbiya sazira kuwa lokacin da ta baro dakin
gani wajen sarki ta koma turakarta sai itama ta rasa
sukuni. Ta kasa zama da tsayuwa zuciyarta ta cika
kakil da tunani gami da damuwa da kuma fargaba.
2.2
Jarumi da Gimbiya
Bisa wannan daliline ta shige can cikin kurya
turakarta ta kulo kofa ta zauna ita kadai tana
tunanin mafita. Abu na farko da ya fara fado mata a
rai shi ne ta sani cewa mahaifinta azzalumin
sarkine wanda yake matsantawa talakawansa akan
haraji da sauran al'amura na rayuwa. Tun tana
karama da ta taso taji bata son wannan dabi'ar ta
mahaifinta, a duk sa'adda ta nuna masa kyamatarta
akan hakan sai yace.
"Shima haka ya taso ya gani mahaifinsa ya na aikatawa"
Sarki Ridwan baya taimako kuma baya jin kan
talakawansa, kuma duk abinda ya gani a hannun
talakansa ya ji yana son abun walau dukiya ko
mace tofa ta karkashin Kasa a sirrance zai rabashi
da shi. Idan ma bai rabasa da ransa ba duk tasan
irin wannan mugayen dabi'un da sarki Ridwan
yake aikatawa domin haka sai taji bata son ya kara
samun karfin mulkinsa bisa wannan dalilin ta fara
tunanin taje har cikin birninsamhar amma ba
domin ta sato Yarima Andaz ba sai domin ta kashe
shi kawai tunda idan ta kashe shi ai shi kenan burin
mahaifinta ba zai taba cika ba saboda sai yana-raye
sannan jininsa zai iyayin aiki a cikin wannan
akushin sihirin. Abinda gimbiya sazira ta aiyana a
cikin ranta shi ne idan har bata samu nasarar kashe
Yarima Andaz ba to tabbas ita zata kashe kanta don
kada burin mahaifinta dana sarki muraka ya cika
tunda dukkaninsu azzalumaine babu wani sarki da
ya fisu cutar da talakawa a nahiyar.
23
Jarumi da Gimbiya
A yanzu kowannansu kasa yake mulka, idan
kuma suka mallaki nahiyar gaba daya, shi kenan
zalluncin sai ya ninka na da fiye da kima. Batare da
bata lokaci ba sai gimbiya sazira ta yanke hukuncin
cewa zata kai kanta wajen wadancan dakarun
sumame da su ka zo domin su saceta, ta hakan
kadai zata samu damar da zata kusanci Yarima
Amdaz ta kashe shi. To amma ya za'ayi tabar cikin
gidan sarauta ta tafi har birnin samhar ba tare da
mahaifinta ya sani ba? Koda ta zo nan a tunaninta
sai hankalinta ya tashi ta ci gaba da kai komo ta
fara sabon tunani.
Sai da ta shafe kusan rabin sa’a sannan mafita
ta zo mata, nan take farin ciki ya kamata ta mike
tsaye ta bude kofar turakarta ta kwalawa shugabar
kuyanginta kira Dulus. Dulus ta amsa kiranta ta
rugo da gudu izuwa cikin turakar Gimbiya ta
dubeta tace "Ki rufe kofofin za mu yi ganin sirri"
Dulus ta juya da sauri ta rufe kofofin turakar
sannan ta dawo wajen gimbiya ta durkusa kasa bisa
guiwoyinta biyu. Cikin hanzari Gimbiya ta sunkuya
ta kama kafafunta biyu ta jata izuwa kan babbar
kujera suka zauna tare. Gimbiya ta dubi dulus cikin
nutsuwa tace "Kin sani cewa a cikin kuyangina
duka babu wacce na yarda da ita sama da ke, na
sani cewa idan nace ki fada wuta sai kin fada, baya
ga haka tsawon zamana dake baki taba cin amanata
ba kuma baki taba furtawa wani sirrina ba, ina son
zan yi tafiya ta sirri izuwa birnin samhar kuma kece
za ki wakilceni a ya yin da bana nan domin kada
24
Jarumi da Gimbiya
sarki ya gano cewar bananan" mamaki ya kama
baiwa Dulus tace.
"Ranki ya dade ta yaya zan iya wakiltarki
alhalin kama da wane bata wane na sani cewa idan
na sanya suturarki na boye fuskata kowa zai dauka
cewa kece amma kuma da anga fuskata shi kenan
asirina ya tonu" Sa adda gimbiya sazira ta ji haka
sai tayi guntun murmushi sannan tace.
"Ai wannan karon ba a iya jikinki za ki yi kama
da ni ba, fuskarki ma irin tawa zata koma" Mamaki
ya kara kama baiwa Dulus tace.
"Ta yaya kenan hakan zata faru?".
Maimakon gimbiya ta bata amsa sai ta mike
tsaye taje ta bude durowar da kayan sawarta suke ta
nuna mata wadansu dogayen riguna na musamman
masu tsananin kyau wadanda sun kai kala ashirin ta
dubi Dulus tace.
"A duk sa'ar da kika saka daya daga cikin
wadannan tufafin kamanninki za su rikide ne izuwa
nawa sak! Idan kina shakka ki jarraba sawa yanzu
kije gaban madubi ki tsaya ki kalli kanki" sa'adda
baiwa Dulus taji wannan batu sai ta mike tsaye
cikin sanyin jiki da fargaba domin zuciyarta cike
take da fargaba tana bugawa da karfi. Abu na farko
shi ne wai yau itace zata sanya irin suturar da
gimbiya ke sawa a matsayinta na baiwa kuma wai
zata ci gaba da rayuwa a matsayin gimbiya sazira
har tsawon kwana ashirin, lallai kenan zata shiga
daula da irin jin dadin da gimbiya ke samu har
tsawon wannan lokaci. Koda baiwa Dulus ta tuna
25
Jarumi da Gimbiya
wannan al'amari a cikin zuciyarta sai taji wani irin
farin ciki ya shigeta mara misaltuwa.
Dulus ta isa inda daya daga cikin dogayen
rigunan take ta dubi dauki daya daga cikin dogayen
rigunan wata shudiya me haske da kyalkyali ta
dauko ta. Nan take ta ajiye rigar akan gadon
gimbiya ta cire wacce ke jikinta ta dauki wannan
din ta sanya.
Kawai sai ta nufi inda madubi yake, ai kuwa
tana isa gaban madubin sai ta fara kallonta daga
kan kafafunta a hankali har zuwa kan fuskarta, tana
yin arba da fuskar tata kawai sai taga ta zama
gimbiya sazira. Mamaki ya turnuke ta Gimbiya
sazira ta taho gaban madubi ta tsaya a kusa da ita
sai suka zama kamar Hassana da Usaina Gimbiya
ta yi murmushi tace.
"Daga yanzu kin fara aikin ki saboda
yanzunnan zan yi shiri na bar gari, kinsa komai a
dangane da dukkanin gari, kinsa komai dangane da
motsina a gidannan kinsan yadda na saba yi zan
baki manzo wanda za ki iya aikensa izuwa ko ina
nake da zarar kin fuskanci wata matsala". Dalus
tace.
"Manzo kuma? Ai babu wani mutum da zai iya
yin wannan aikin". Gimbiya sazira ta yi murmushi
tace "Ai ba mutum bane tsuntsune na sihiri” Tana
gama fadin haka sai ta bude tafukan hannunta, take
wani tsuntsu na karfe ya bayyana akan hannunta
me launin ruwan kwai Gimbiya ta mikawa Dulus dan karamin tsuntsun wanda ko kaďan ba shi da
nauyi, Dulus ta karbi tsuntsun tana dorashi-akan
26
Jarumi da Gimbiya
tafin hannunta sai-ya zama-na-gaske ya juya-ya
fuskanci gimbiya sazira ya bude fukafukansa ya
risina a gareta alamar girmamawa, ya sake kamewa
ya zama gunki mamaki ya kama baiwa Dulus ta
dubi Gimbiya tace.
"Ya shugabata ya zanyi da wannan tsuntsun"
Gimbiya tace.
"Anan kusa da tagar gadona za ki rika ajiye shi,
a duk lokacin da za ki aiko shi gareni sai ki dauke
shi ki dora shi akan tafin hannunki, take zai zama
na gaske sai ki bashi sakon da-zai kai mini sannan
ki bude wannan tagar za ki ga ya fice ta cikin tagar,
kar ki bar bakin tagar kuma kar ki kulleta har sai
kinga ya dawo. Lallai zai zo miki da amsar sakon
da ya kai min” Gimbiya na gama fadin haka sai
taje ta dauki takobinta da kwari da bakanta ta
ratayasu a bayanta sannan ta dauki wata jakar fata
da kaya a ciki ta ratayata a kafadarta suka yi
bankwana bisa cewar sai bayan kwana ashirin zata
dawo. Gimbiya tana janye jikinta daga jikin baiwa
Dulus sai ta rikide ta koma kamannin baiwa Dulus
din ta juya ta fice daga cikin turakar Dulus ta bita
da kallo kawai cikin tsananin mamaki kuma
zuciyarta ta ci gaba da bugawa da karfi sakamakonwani tsoro da ya shigeta bisa tunanin idan asirinta
ya tonu aka gane cewa ita ba gimbiya sazira bace
sarki zai iya sawa a kasheta.
Lokacin da Gimbiya sazira ta fito daga cikin
turakarta a cikin siffar baiwa Dulus kuma gata
dauke da jakar fata sai kowa ya zata cewa gimbiya
27
Jarumi da Gimbiya
ta aiketa cikin gari domin tayi mata siyayya kamar
yadda aka saba don haka duk kofar data isa sai
kaga Dakaru sun girmamata sun bude mata kofa da
sauri ta wuce. A haka sai data wuce ta cikin kofofi
goma sha daya na gidan sarauta hankali kwance.
Koda ta iso kofa ta sha biyu wacce itace ta
karshen fita daga gidan sarautar, tana zuwa sai taga
anki bude mata kofar ta dubi dakarun fuskarta a
murtuke tace.
"Baku gani bane za ku ki bude mini kofa
alhalin gimbiya ce ta aikeni kasuwa?" Daya daga
cikin dakarun yace "Kiyi hakuri Dulus sabuwar
dokace ta zo daga wajen sarkin yaki yace duk
wanda zai fita daga gidannan sai da izininsa" Koda
jin wannan sai zuciyar gimbiya sazira ta buga da
karfi domin tana ji a jikinta cewa babu wanda zai
iya gano shirinta face sarkin yaki kinana. A
yanzuma da ta rikide izuwa siffar kuyangarta Dulus
yana yin arba da ita zai gane ba ita bace, kwatsam
sai taji muryar sarkin yaki kinana daga can
bangaren yana cewa.
"Dulus juyo ki taho nan za mu yi magana"
Koda jin haka sai zuciyar gimbiya ta sake bugawa
da Karfi sosai a karo na biyu, cikin sanyin jiki da biyayya ta juyo da baya, kanta na sunkuye ta
tunkaro sarkin yaki ta tsaya cak! A gabansa.
Mamaki ya kama sarkin yaki kinana yace "Yau
kuma ko gaisheni ba za ki yi ba" Koda jin haka sai tayi sauri ta durkusa kasa bisa guiwarta guda ta
kwashi gaisuwa. Kinana ya yi murmushi ya kai
hannunsa bisa kafadarta zai tasheta tsaye sai ya yi
28
Jarumi da Gimbiya
sauri ya cire hannunsa daga jikinta kuma ya dan ja
baya cikin alamun tsoro kadan. Ba komai ya jawo
haka ba face tsananin laushin jikinta da ya ji, ta
yaya jikinta ya kasance a haka tana matsayin baiwa.
Wannan itace tambayar da sarkin yaki kinana ya yi
wa kansa kuma ya kasa baiwa kansa amsa.
Gimbiya ta mike sunkuye da kanta ta kalleshi
kadan ta sake sunkuyar da kanta kas, kinana yace
"Wane irin sako gimbiya ta baki izuwa cikin gari?"
"Aikena tayi na sayo mata kayayyakin hada
miya ta gargajiya" Kinana ya yi murmushi yace
"Tabbas na sani cewa gimbiya kullum sai ta ci
miyar gargajiya, akwai wani abu na kayan marmari
wanda sau daya gimbiya take siyansa a sati, idan
aka sayo mata wannan abun sau nawa take cinsa a
rana?" koda jin wannan batu sai gimbiya ta yi shiru
tana tunani ta kasa bashi amsa, can sai ta dago kai
ta dube shi tace.
"Babu wanda zai iya baka wannan amsar sai
gimbiya da kanta saboda babu wanda ya taba ganin
lokacin da take cin wannan-abin marmari" Sa'adda
sarkin yaki ya ji wannan amsar sai ya yi murmushi
ya dubi dakarun tsaron kofar yace musu.
"Ku bude mata kofa ta fita" Cikin hanzari sukа
bude mata kofar ta fita, suka janyo kofar suka sake
rufewa, sarkin yaki ya yi shiru yana tunani, ba
komai yake tunani-ba face yana zargin ko-gimbiya
ta rikide ta zama baiwa Dulus domin ta sami damar
fita daga gidan sarautar amma daya yi mata
wannan tambayar ta biyu ta kasa ba shi amsa sai
hankalinsa ya kwanta, saboda yasan idan gimbiya
29
Jarumi da Gimbiya
ce mancewa zatai ta basa amsa kasancewarta mace
mai yawan mantuwa akan al'amuranta nan take
sarkin yaki kinana ya juya ya koma can cikin gidan
sarautar.
Da fitowar gimbiya sazira daga cikin gidan
sarautar birnin kilmaz sai ta ci gaba da tafiya har
sai da tayi nisa sosai ta daina hango bayanta sannan
ta bace bat tamkar bata taba wanzuwa ba a wajen.
Bata bayyana a ko ina ba sai a can cikin
kungurmin daji inda mafarauta ke zuwa neman
dabobbin daji. Tana bayyana a wannan wurin sai ta
hango wata katuwar damisa kawai sai tayi sauri ta
zaro kibiya a bayanta ta dana akan baka ta saita
damisar da nufin ta harbeta a lokacin da damisar ta
juya baya tana tafiya. Kawai sai taga damisar ta
tsaya cak a inda ta ke kuma ta juyo gareta suka
kurawa juna idanu har izuwa tsawon 'yan dakiku.
Daga nan kuma sai damisar ta tunkaro Gimbiya
sazira kai tsaye tana tafiya a hankali.
Koda gezau gimbiya sazira bata yi ba kawai sai
ta kara tabe bakarta ta saita kan damisar da
kibiyarta. Koda ganin hakan sai damisar ta falfalo
da gudu har tana tashi sama da nufin ta zo ta
murkushe gimbiya sazira baifi taku goma ba a
tsakaninsu sai gimbiya ta sakar mata kibiya, kibiyar
ta huda tsakiyar kan damusar rabinta ya lume a ciki.
Maimakon damusar ta fadi a kasa sai ta dako tsalle
a sama ta kawowa gimbiya wawusa da faratan
hannayenta biyu tamkar kibiya bata soketa ba,
cikin bakin zafin nama gimbiya sazira ta kaucewa
30
Jarumi da Gimbiya
harin damisar ta sunkuya ta karkashinta tayi sufa
izuwa can gefe daya, bayanta ya bugu a jikin wata bishiya ita kuma damisar ta diro kasa akan
kafafunta guda hudu ta karci kasa da faratan ta kura ta tashi ta yi tirjiya sannan ta juyo da baya suka sake kallon-kallo a ya yin da gimbiya sazira ke zaune a kasa jikin bishiya.
Wannan karon sai da suka yi nazarin juna sosai
kowannansu ya kudure mugun nufi a ransa domin
samun nasara akan abokin gabansa. duk da cewa
wannan kibiyar da gimbiya sazira ta harbi damisar
na nan a cikin kan damisar jini na zuba kuma dafin kibiyar ya fara sata jin jiri-jiri amma tana yin wani
irin gurnani mai ban tsoro kuma tana wangame bakinta, hakoranta ma su kaifi da tsini na firgita
duk wata halitta dake wajen.
Cikin shammata sai damisar ta dako tsalle mai
karfi a sama daga inda take da nufin ta dira-akan
gimbiya ai kuwa itama gimbiya sai tayi wuf ta zaro
takobinta ta doki kasa da hannunta guda sai gata a
sama cikin sararin samaniya tamkar harbota akai
daga cikin baka suka yi mugun gamo ita da damisar
a saman. Damisar ta wangame bakinta da nufin ta
hadiye kan gimbiya cikin zafin nama ta kaucewa
bakin damisar ta soka mata takobinta a tsakiyar
gadon bayanta takobin ta 6ollo ta cikin Damisar
suka fado kasa tim!. nan take Damisar ta zama
gawa ko shurawa ba yi ba.
Takobin gimbiya ta nutse a cikin kasa a cikin
Damisar Gimbiya na ruke da takobin tata da hannu
biyu kawai sai gimbiya ta ji ana-yi mata tafi daga
31
Jarumi da Gimbiya
bayanta. Ta waiga da sauri tayi arba da wanda yake
yi mata tafin ba wani bane face jarumi lurwan
shugaban dakarun sumame wadanda suka zo saceta.
Yana tsaye rike da kwari da bakansa ya kura mata
idanu yana mamakin wannan gagarumar jarumtaka
da ta yi a yanzu ta kashe wannan Damisar farat
daya.
Jarumi Lurwan ya karewa gimbiya kallo sama
da kasa yaga tana rataye da jaka ta tafiya a bayanta
Gimbiya ta mike tsaye ta zare takobinta daga cikin
Damisar ta goge jinin dake jikin takobin akan
gawar Damisar sannan ta zurata cikin kufenta. A
sannanne jarumi Lurwan ya dan matso kusa da ita
yace.
"Na so na gane wannan fuskartaki daga cikin
kuyangin dake kwance a babban falon Gimbiya
sazira jiya da daddare" koda jin haka sai ta dube shi
a fusace tace "Wato kaine shugaban dakarun
sumamen da ya shiga har cikin falon Gimbiyata
domin ya saceta ko?"Lurwan yace.
"Tabbas ni ne ke kuma wacece kuma me yasa
kika baro cikin birnin kilmaz kika shigo wannan
daji, ina kika nufa daga nan?" Gimbiya ta sake
murtuke fuska tace.
"In ba don akwai aikin da na fito yi ba yanzu da
sai na kamaka da karfin tsiya na kaika gaban
gimbiyata na gurfanar da kai domin ayi maka
hukunci bisa laifin da ka aikata na yunkurin satar
gimbiya" Koda jin wannan batu sai jarumi Lurwan
ya kyalkyale da dariya yace.
32
Jarumi da Gimbiya
"Ya ke wannan kuyanga ta gimbiya sazira kiyi
sani cewa uwargidanki ma na yi gumurzu da ita
bata sami nasara akaina ba bare ke 'yar karamar
alhaki. Tabbas jarumtakarki ta burgeni da za ki
amince ki taimaka mini na cika burina akan
gimbiyarki da na kai ki birnin samhar kin sami
daukaka daga kuyanga-zuwa ga attajirar da babu
kamarta" Lokacin da Gimbiya ta ji wannan batun
sai tayi sororo ta sunkuyar da kanta kas tana tunani
sannan ta dago kai ta dube shi tace.
"Ta yaya zan iya tabbatar da cewa idan na
taimake ka naje na sato Gimbiya na kawo maka ita
har nan zaka cika wannan alkawarin ba tare da ka
yaudareni ba?" koda jin wannan batu sai farin ciki
ya kama jarumi Lurwan ya dubeta cikin murmushi
yace "Idan har kika kawo mini Gimbiya nan inda
nake zan tura birnin samhar a dauko miki dinare
cikin buhu goma. Idan kuma muka isa can birnin
samhar da gimbiya sazira lafiya zan kara miki buhu
arba'in na dinare, yaya kin yarda da wannan
sharadin?" Gimbiya ta kada kai tace.
"Ban yadda ba sai ka fara bani kafin alkalami
sannan zan yarda-na-ci amanar gimbiya naje na
satota na kawo maka ita nan” Jarumi Lurwan yace
"Shi kenan na yarda da hakan muje cikin tanti mu
zauna ki huta sannan mu daddare wannan babbar
harkallah" Yana gama fadin haka ya je ya sari
naman Damisar ya juya ya nausa eikin daji. Cikin
hanari da murna gimbiya sazira tabi shi a baya ba
tare da yasan cewa itace wacce yake nema ba ruwa
Jarumi da Gimbiya
a jallo saboda a cikin siffar kuyangarta Dulus ya
ganta.
**
A can birnin samhar kuwa sarkin muraka na
kwance a cikin turakarsa da tsakiyar dare yana
bacci sai ya farka a firgice ya mike zaune zumbur
sakamakon wani mugun mafarki da ya yi mara
dadi. Hakanne yasa idanunsa suka bushe, bacci ya
kaurace masa ya mike tsaye ya kama kai komo.
Har alfijir ya keto bai sake rintsawa ba.
Tun kafin gari ya yi haske ya kirawo bafadensa
ya aike shi da yaje ya kirawo abin dogaronsa wato
boka Rimasu nan danan kuwa bafaden ya cika
aikinsa. Kafin Boka Rimasu ta iso tuni sarki
muraka ya yi wanka ya kimtsa kuma sai ya yi
gagarumar shigar yaki ya zauna a cikin fadarsa shi
kadai babu dogarai da fadawa sai huci yake yi yana
muzurai cikin alamun tsananin fushi. Ba wai
mutum ba ko aljan a wannan lokaci ko wacce irin
halittama sai tayi shakkar tunkarar sarki muraka
saboda kwarjininsa da kuma fushin da fuskarsa ke
nunawa. A wannan rana tunda sarki ya farka daga
bacci hatta matansa da kuyanginsa babu wacce ta
kusance shi saboda shi idan yana cikin fushi kana
rabarsa zai iya yi maka mugun lahani koma ya
hallakaka. Boka Rimasu ne kadai yake iya zuwa
kusa da shi ya kwantar masa da hankali.
Sarki muraka ya kasance gawurtaccen jarumi a
nahiyar domin a tarihin jarumtakarsa ya ajiye
tarihin da babu wani. jarumi daya ajiye irinsa.
Abinda ya faru a lokacin daya nemi auren matarsa
34
Jarumi da Gimbiya
mahaifiyar Yarima Andaz wacce a halin yanzu-ta
samu shekara bakwai da rasuwa.
Ita dai mahaifiyar Yarima Andaz sunanta gimbiya Falmin kuma ta kasance 'ya ga wani sarki
da ake kira Barluza me mulkin kasar soman a
kudancin Kasar samhar A wannan lokacin a
nahiyar gaba daya babu-wata budurwa wacce ta kai
kyawun gimbiya falmin don haka sai sarakuna, jarumai da matsafa suka yi caa akan neman aurenta
bisa wanan dalilin mahaifinta sarki Barizu yasa
wata gasa me tsananin wuya hadari bisa cewa
wanda ya samu nasara lashe gasar shi ne zai auri gimbiya falmin.
Yanayin gasar shi ne akwai wani tsauni wanda
aka yi masa lakabi da tsaunin mutuwa. Shi dai
wannan tsauni a samansa akwai wani kogo babu
komai a cikin kogon face tarin dukiya ta zinare da
lu'u-lu'u ance wannan dukiyar tafi shekara dari
uku a wajen amma duk wani mahaluki da ya shiga
cikin wannan kogo domin ya dauko wani abu a
cikin dukiyar baya dawowa a raye. Da yawa
wadanda suka shiga wannan kogon basa dawowa
kuma ko duriyarsu ba a sake ji. Bokaye da-yawa
sun tabbatar da cewa ba aljanune suke hallaka
mutum ba a cikin wannan kogon wadansu irin
halittu ne masu cin naman mutum sai dai aga sun
watso kasusuwan mutum waje sun cinye naman,
kuma an tabbatar da cewa tsafi baya tasiri a kansu
sai dai tsagwaron karfin damtse da iya yaki.
Mutane dari uku da sittine suka taru a kofar
gidan sarautar kasar soman domin neman auren
35
Jarumi da Gimbiya
gimbiya falman amma da mahaifinta sarki Barluza
ya fito ya yi musu bayanin cewa sadakin 'yarsa shi
ne zuwa tsuburin mutuwa a shiga cikin kogon
dukiya a debo zinare da lu'u-lu'u duk wanda ya zo
da wannan dukiya gaban sarki Barluza kafin rana ta
fadi to shi ne zai auri gimbiya falmin sai mutanen
nan suka fara janye jikinsu daya bayan daya suna
hakura da shiga wannan gasa har sai da ya zamana
sauran mutum biyu kacal ba wasu bane