wadannan
mutane biyu da suka rage face sarki muraka na
birnin samhar da kuma sarki Ridwan na birnin
kilmaz.
Kowannansu ya yi gagarumar shigar yaki suna
zaune bisa ingarmun dawakai dokin sarki muraka
bakine shi kuma na sarki Ridwan farine. Sarki
Barluza ya dubi wadannan sarakai biyu ya yi musu
jinjina. A wannnan lokacin gimbiya falmin na tsaye
daf da mahaifinta kuma a yaune ta fara ganin
wadannan sarakuna guda biyu, don haka sun kura
mata idanu itama ta kura musu idanu zuciyartana yi
mata wasu-wasi akan wanda yakamata ta zaba ya
zamo abokin rayuwarta.
Duk da cewa tasaon cewa bata isa ta yiwa kanta
zabi-ba tunda wanda ya lashe wannan gasa shi ne
zai aureta. Sarki barluza ya dubi gimbiya falmin
cikin murmushi yace "Ya ke 'yata yanzu a cikin wadannanjaruman sarakunan wanne ne yafi
kwanta miki a rai?" koda jin wannan tambayar sai
ta maida masa da martanbin murmushi tace.
"Ya kai Abbana ka sani cewa ni mace ce me
son tausayi da jin kai ga talakawa don haka nafi
36
Jarumi da Gimbiya
son ace sarki Ridwan ne zai zamo ango na saboda
yafi sarki muraka saukin zallunci, duk da cewa dai
shima din ma'abocin danne hakkin talakawane da
kuma son dukiya" Sa'adda sarki barluza ya ji
wannan batu sai fuskarsa ta sauya zuwa yanayi na
damuwa yace.
"Nima na fi sonki da sarki Ridwan amma kuma
baka safai muke samun abinda muke so ba a
rayuwa Yana gama fadin hakan sai ya bar
gimbiya falmin ya nufi inda su sarki muraka suke
ya je har daf da su ya dube su yace "Ya ku
wadannan zaratan jaruman sarakuna a cikin
jaruman gasa guda dari uku da sittin ku biyune
kacal kuka sai da ranku domin zuwa tsaunin
mutuwa to kusani lokacin fara gasarku ya yi, sai ku
hanzarta zuwa kogon dukiya ku debo zinare da
lu'u-lu'u duk wanda ya kawo wannan dukiya kafin
rana ta fadi daga cikinku tamkar bayar da sadakin
auren 'ya tane gimbiya falin kuma nan take zan
daura masa aure da ita” Sa'adda sarki muraka da
sarki Ridwan suka ji wannan batu sai suka dubi
junansu suka yi murmushin mugunta sannan suka
juya baansu suka dubi bokayensu wadanda suma
suna zane bisa dawakansu. Kawai sai bokayen biyu
suka kada linzamin dawakansu suka juya suka nufi
kofar fita daga cikin gidan sarautar. Sarki muraka
da sarki Ridwan ma sai suka bi bayansu, gimbiya
falmin da mahaifinta suka bisu da kallo har suka
bace musu da gani.
3-7
Jarumi da Gimbiya
Haka dai wadannan mutane hudu suka ci gaba
da tafiya akan dawakai suka nausa cikin daji inda
wannan tsaunin mutuwa yake. Boka samasa da
sarki Ridwan ne akan gaba. Sarki muraka da
bokansa Aryan na biye da su kuma tazarar da take
tsakaninsu bata wuce kamu goma ba sarki muraka
ya dubi boka Aryan yace "Ta kowane hali fa nine
zan lashe wannan gasa" Cikin mamaki Aryan yace.
"Ya shugabana dame ka dogara ka fadi haka?".
"Abinda na dogara bisa binciken da ka yi shi ne
zan shiga çikin koğon kuma zan fito a raye to idan
har shima sarki Ridwan ya samu wannan nasara to
ba zan bari ya koma fadar su gimbiya falman ba"
Boka Aryan yace.
"To yaya zaka iya hana shi zuwa?" Sarki
muraka yace "Kashe shi zan yi saboda gimbiya
falman tawace ni kadai ba zan taba bari wani na ya
mallaketa ba" Yana gama fadin hakan ya juyo baya
ya hada idanu da sarki Ridwan. Ridwan ya yi masa
murmushi amma shi sai ya daka masa harara ya
juya yaci gaba da tafiyarsa. Sarki Ridwan ya dubi
boka samosa yace "Maganarka gaskiyace akwai
mugun nufi a cikin zuciyar wannan abokin
hamaiyar tawa domin naga hakan a cikin idanunsa"
Boka samosa yace.
"Nima naga hakan sai ka kula".
Nan dai aka ci gaba da tafiya ana ta ratsa daji
batare da an fuskanci wata matsala ba har rana ta
take, bisa dole suka yada zango. Sarki Ridwan da
Boka samasa suka sauka a karkashin wata katuwar
bishiya suka daure dawakansu suka yi shimfida
38
Jarumi da Gimbiya
suka zauna kuma suka bude jaka suka fito da abinci
guzuri suka fara ci. Sarki muraka da boka Aryan
kuwa sai da suka yi nesa kadan da su sannan suka
soma yada zango a karkashin wata bishiyar daban
suma suka yi shimfida suka zauna suna cin abinci
kuma suka fara hira inda boka Aryan ya dube shi
yace.
"Ya shugabana daga nan inda muke fa tafiya ce
ta zango daya da rabi kacal mu isa tsaunin mutuwa.
Kasani cewa idan muka isa can ni da bokan sarki
Ridwan a kasan tsaunin za mu tsaya mu jira
saukowarku, don haka duk taimakon da zamu iya
baku daga nan zuwa bakin tsaunin mutuwa ne"
Cikin mamaki sarki muraka ya dubi boka Aryan
yace "Ashe duk bala'in da za mu tunkara a cikin
tsaunin mutuwa babu ruwanku da shi?" Boka
Aryan yace 'Kwarai kuwa tunda tsafi baya tasiri a
cikin wannan kogon abinda zai ceceku kawai shi ne
karfin damtsenku, jarumtakarku da kuma irin
nasibinku a rayuwa kai dai kawai duk yadda za ka
yi kayi domin tabbatar da cewa ka debo wannan
dukiya kuma ka fito a raye" Sarki muraka ya yi
ajiyar numfashi yace.
"Wannan kamar anyi an gamane lallai sai na
sami nasara debo wannan dukiyar kuma sai na fito
a raye daga cikin kogon dutsen na tsaunin mutuwa".
A can bangaren su sarki Ridwan kuwa hirar da
ta karke a tsakaninsu da Boka samaso ya dube shi
yace "Ya shugabana babban tashin hankalina shi ne
idan ka rasa rayuwarka a cikin tsaunin mutuwa ba
Jarumi da Gimbiya
zan iya komawa birnin kilmaz na kai wannan
labarin ba domin wasu za su yi zargin na akan ni na
hallakaka domin na gaje kujerarka don haka na
hakura da rayuwar can sai dai na tafi wata kasar na
zauna na karasa ragowar rayuwata" Sa'ar da sarki
Ridwan ya ji wannan batun na boka samasa sai ya
kyalkyale da dariya sannan yace "Ya kai wannan
boka ka yi sani cewa ba'a iyawa mutum a cikin
wannan duniyar, ko ka koma ko kar ka koma hakan
ba zai saka aki yin zarginka ba bisa mutuwata.
Abinda na ke so ka sani shi ne ba zan mutu ba a
cikin wannan tafiyar haka kuma babu tabbacin zan
sami nasarar lashe wannan gasa" Cikin mamaki
Boka samosa ya dube shi yace.
"Ya shugabana kai kuwa mene ne dalilin da ya
sa ka fadi haka?" Sarki Ridwan yace "Saboda duk
abinda zai sameni a rayuwa nakanga
kwatankwancinsa a mafarki kafin wannan abin ya
faru-a zahiri, yanzu yaushe ne za mu ci gaba da
wannan tafiya?" Boka samosa yace.
"Ai da zarar rana ta danyi sanyi kadan za mu ci
gaba da wannan tafiya tunda kafin ranat ta fadine
ake so akai sadakin Gimbiya falman" Sarki Ridwan
ya yi murmushi gami da jinjina kansa yace "Lallai
yau akwai gwagwarmaya wacce zata zamo abar
tarihi a wannan nahiyar gaba daya".
**
Kamar yadda boka samasa ya fada haka
al amarin ya kasance wato rana na soma yin sanyi
sai duk su hudun suka mike tsaye suka yi shiri suka
hau dawakansu suka ci gaba da tafiya suna masu
40
Jarumi da Gimbiya
tunkarar tsaunin mutuwa ko tafiyar sa'a guda basu yi ba suka iso wani babban fili wanda babu bishiya ko guda daya a wajen.
Kasar wajen gaba daya yashi ce kuma wurin ya yi tsit! Tamkar babu wani abu me rai da ya taba wanzuwa a wajen. Sarki maraka da boka Aryan ne suka fara isowa wannan wurin don haka sai suka tsaya cak suna nazarin wajen koda ganin haka sai sarki Ridwan da boka samosa suka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak! Boka Aryan da boka samosa suka sauko daga kan dawakansu suka damki wannan yashi suka shinshinashi domin su gano ko akwai wani mugun abu a wajen amma sai suka kasa ganokomai. Kowannansu sai ya fara amfani da sihirin tsafinsa domin ya gano sirrin wajen amma sai dukkaninsu sihirin tsafin na su
yaki ya yi aiki.
Al'amarin da ya matukar basu mamaki kenan
kawai sai boka Aryan ya dubi sarki maraka yace
"Ya shugabana ba zan iya ketare wannan wajen ba
face ka fara ketare shi saboda bansa irin bala in
dake cikin wannan yashin ba".
Shima boka samosa sai ya yi wa sarki Ridwan
irin wannan bayani, koda jin hakan sai sarki
Ridwan ya sauko daga kan dokinsa ya zare
takobinsa ya nufi cikin wannan yashin kai tsaye ba
tare da jin tsoron komai ba. Da ganin hakan shima
sarki muraka ya sauko daga dokinsa ya nufi wajen
da sarki Ridwan ya nufa. Boka Aryan da boka
samosa suka zama 'yan kallo.
Jarumi da Gimbiya
Muraka da Ridwan suka shiga cikin wannan yashi kowannansu na rike da takobinsa suna taka
sawayensu a hankali cikin tafiya cike da nutsuwa irin ta jaruman da suka yadda da kansu. Kwatsam
sai su kaga hannayen wasu mutane ya fito daga
cikin karkashin kasa ya kama kafafuwansu, cikin
zafin nama kowannansu ya kaiwa hannayen da
suka rukoshi mugun sara amma sai sukaji kamar
Karafa suka sara ba hannun bil'adama ba domin
wata irin kara ce ta tashi kal! Gami da tartsatsin
wuta.
Ko gezau hannayen ba su yi ba kuma ko
kwarzane ba su yi ba, maimakon ma su saki
Kafafuwan sarki maraka dana sarki Ridwan sai
suka sake rikesu gam suka fara jansu da karfin
tsiya izuwa cikin karkashin kasa, kafin su ankara
kafafunsu sun shige cikin kasa tsawon guiwoyinsu.
Koda ganin haka sai sarki Ridwan da sarki maraka
suka saki takobinsu suka kama hannayen da suka
rikesu suka rinka janyosu da dukkan karfinsu, nan
fa kwanjinsu ya tashi dukan jijiyoyin jikinsu suka
tashi suka kumbura, kawai sai gani akai sun cisgo
hannayen daga cikin gangar jikin dake cikin kasa,
sai ga jini na zuba a jikinsu. Faruwar hakan ke da
wuya sai wasu samudawan mutane su kimanin dari
suka suka faso ta cikin karkashin Kasa suka yiwa
sarki maraka da sarki Ridwan kawanya.
Koda ganin wadannan samudawan mutanen
sai boka samasa da boka Aryan suka firgita ainun
saboda kwarjinsu da kuma kirarsu ta karfi babu
komai a jikinsu face warki na fata, kafafuwansu
42
r
Jarumi da Gimbiya
babu takalma a wuyansu akwai wata sarka wace
aka yita da kashi, su dai wadannan mutane sun fi
kama da masu cin mutane domin kamanninsu ma
ya fara fita daga hayyaci na bi'adama su kansu su
sarki muraka duk da kasancewarsu gwarazan
jarumai sai da suka firgita bisa ganin wadannan
mutanen amma da yake idan mutum yaga mutuwa
murara sai ya tareta domin neman matsera sai ko
wannansu ya gyara tsayuwarsa ya dunkule
hannayensa biyu domin fara gumurzu. Lokaci guda
sai samudawan suka yi ca akansu aka ruguntsume
da azababbane fada ya zamana cewa samudawan
na kai musu naushi da bugu suma suna kai musu.
Babban abinda ya dagawa su sarki Ridwan hankali shi ne duk basamuden da suka nausa sai
suga ya shanye dukan tamkar shafarsa suka yi shi
kuma idan ya naushe su sai kaga sunyi layi suna
neman faduwa saboda karfin naushin. In ba don ma
suna da tsananin juriya ba da na ci da cikin kankanin lokaci za su zube kasa. Cikin kankanin
lokaci aka hadawa sarki muraka da sarki Ridwan
jini da majina. Tun suna iya kare naushi da bugu
gami da maida martani har takai cewa an kai su
kasa ana ta yi musu luguden duka. Tuni sarki
muraka ya galabaita har ya fara aman jini, idanunsa
sun fara warkalewa alamar zai suma, koda sarki
Ridwan yaga halin da sarki muraka ya shiga sai
ransa ya baci ya kurma wani uban ihu mai tsananin
firgitarwa wanda yasa su kansu samudawan suka
dan ja baya
Jarumi da Gimbiyа
Kawai sai sarki Ridwan ya daka tsalle sama tamkar daga kan sifirin aka wurgo shi kawai sai ya dira akan kawunan samudawa biyu da kafafunsa
kawai sai ya ji kawunan na su sun gurma suka sulale kasa matattu. Nan take ya gane cewa ashe lagon samudawan shi ne tsakiyar kansu cikin zafin
nama Ridwan ya ci gaba da naushin tsakiyar kawunan samudawan suna faduwa tamkar ana
sassabe a gona.
Adaidai wannan lokacine sarki muraka ya
dawo cikin hayyacinsa koda yaga yadda sarki
Ridwan ke ta dukan samudawan a tsakiyar
kawunansu suna zubewa matattu sai shima ya mike
tsaye wuf! Ya tashi ya kifa kan samudawan. Kafin
cikar rabin sa'a sun kashe gaba dayan samudawan
dayan su bai tsira ba. Faruwar hakan ke da wuya
sai sarki Ridwan ya durkushe kasa yana haki kamar
ransa zai fita, shima sarki muraka sai ya zauna a
kasa yana numfashi saboda jikinsa gaba daya ya yi
tsami,sakamakon naushi da bugun daya sha.
A daidai wannan lokacin boka samasa da boka
Aryan suka rugo da gudu izuwa garesu suka kama
yi musu jinjina bisa ganin irin gagarumar
jarumtakar da suka yi. Boka Aryan ya yiwa sarki
muraka rada a kunne yace.
"Baka yiwa sarki Ridwan godiya ba alhali
badan shi ba da yanzu tuni ka dade da mutuwa a
lokacin da kuke yin gumurzu da wadannan samudawan” Koda jin haka sai sarki muraka ya
murtuke fuskarsa ya bude baki a fili yace "Tsakanin abokan gaba babu taimako ko godiya
Jarumi da Gimbiya
Yana gama fadin haka sai ya mike ya dubi Boka Aryan yace.
"Bamu da lokaci ka zo mu ci gaba da tafiya
tunda so ake a kawo sadakin gimbiya kafin rana ta
fadi" Dajin haka sai boka Aryan ya mike da sauri yabi sarki muraka suka haye dawakansu sua
zaburesu da gudu. Koda ganin haka sai sarki
Ridwan da boka samaso ma suka ruga izuwa wajen
na su dawakan suka haye suka bi bayansu sarki
muraka da gudu.
Har su sarki muraka suka isa bakin tsaunin
mutuwa ba su sake haduwa da wani mugun abu ba,
da zuwansu sai suka ja linzamin dawakansu suka yi
carko-carko suna kallon tsaunin.
Shi dai wannan tsaunin na mutuwa tsawonsa
daga kasa zuwa sama yakai kamu tamanin koda
sarki muraka da sarki Ridwan suka kalli tsawon
wannan tsaunin sai hankalinsu ya tashi domin ba sy
ga yadda za su iya haye saman wannan tsaunin har
su shiga ciki kogon dutsen ba tare da amfani da
karfin sihiri ba tunda tsafi baya amfani a wannan
dajin.
Idan takamar mutum ya iya hawa saman dutse
to ai kafin ya kai karshensa hannunsa zai gaji idan
kuma ya gaji to subutowa zai yi ya fado kasa ya
mutu a banza.
Boka samasa da boka Aryan suka koma gefe
daya suka zauna a waje guda suka yi tagumi duk da
cewa tunda aka fara wannan tafiya ba su yi wa
junansu magana ba ko sau daya amma sai
kowannansu ya ji yana so ya yi maganar. A
45
Jarumi da Gimbiya
wannan lokacin sarki muraka da sarki Ridwan sun
tsaya a gaban tsaunin mutuwan sun kura masa
idanu kawai kowannansu yana tunanin dabarar da
zai yi ya hau kan wannan tsaunin ba tare da ya
fuskanci wani hadari ba da zai zamo sanadin
ajalinsa.
Boka Aryan ya dubi boka samasa yace
"Abokina ashe duniya abar tsoroce?" Cikin
mamaki Boka samasa ya dube shi yace "Kai kuwa
mene ne dalilin da yasa ka fadi haka?" Boka Aryan
yace.
"Bomai mulkin mutum da daukakarsa komai
tarin dukiyarsa yana ji yana gani wani abun zai
gagareshi. Yanzu dai gashi sarakunan nan biyu
babu abinda suka rasa a wannan duniyar amma sun
rasa ta yadda za su hau kan wannan tsaunin,
wannan ya isa babban darasi akan kowa. Babban
abin hadarin ma shi ne saboda kawai su mallaki
mace guda daya suke so su hau kan wannan tsaunin
kuma babu tabbacin za su iya isa karshen tsaunin
har su debo dukiyar da ake bukata kuma su sauko
lafiya a raye" Koda jin wannan batun sai boka
samosa ya bushe da dariya yace.
"Na rantse da gemun mahaifina ni dai idan ni
ne daya daga cikinsu hakura zan yi da wannan
gasar tunda ina da sarauta kuma ina da kudi duk
وو irin kalar macen da nake so na aura zan iya samu
Boka Aryan ya yi murmushi yace
"Ai shi dan adam da buri yake mutuwa saboda shi buri baya karewa, tunda a nahiyarnan kaf babu wata budurwa mai kyawun gimbiya falman tofa
46
Jarumi da Gimbiya
duk wanda ya mallaketa a wannan zamanin ya
zama zakaran gwajin dafi kuma ya ajiye tarihin da har abada ba za a taba mantawa da shi ba" Boka
Aryan na gama fadin haka, sai suka hango sarki
Ridwan ya gyara zaman takobin dake rataye a
gadon bayansa sannan yasa hannayensa biyu ya
kama tsaunin ya fara hawa kansa. A hankali yake
hawa tsaunin idan ya yi taku uku zuwa saman sai
ya tsaya cak ya dan huta. Ya yin da sarki muraka
yaga yadda abokin hamaiyarsa ke hawa kan
wannan tsaunin sai shima ya yi koyi da shi ya kama
hawa tsaunin.
Haka dai suka ci gaba da hawa kan wannan
tsaunin suna hutawa har suka kai rabin tsawon
tsaunin. Koda suka kallo kasa suka ga tsananin
nisan kasa sai hankalinsu ya tashi saboda sun
tabbatar da cewa ko yaya suka subuto kasa sunansu
gawa. Abu na biyu kuma shi ne idan ba su hanzarta
isa saman wannan tsaunin akan lokaci sun debo
wannan dukiyar ba to rana zata fadi su fadi a
wannan gasar. Koda suka tuna da hakan sai suka ci
gaba da hawa kan tsaunin. A wannan lokaci sun
nannade tafin hannunsu da tsumma amma saboda
zafin ranar da ya daki dutsen tsaunin tsumman ya
fara farfashewa kuma tuni tafin hannayen nasu ya
cika da kanta.
Dama sun cire takalman kafafuwansu don kada
santsi yasa su subuce su fado kasa. Ai kuwa nan
danan 'yan yatsun Kafafunsu suka kumbura kuma
47
Jarumi da Gimbiya
suka yi bakikirin kamar kuna saboda zafin ranar
dake jikin dutsen tsaunin.
Dukkaninsu sun jike sharkaf da gumi tamkar a
cikin kogi aka tsomasu, sai da suka shafe kusan
rabin sa'a suna ci gaba da hawa wannan tsaunin
wani lokacin idan daya daga cikinsu ya zame ya yi
kamar zai fado kasa sai kaji abokinsa ya kurma ihu
amma bisa mamaki sai aga bai fado din ba ya ci
gaba da hawa can saman tsaunin. A haka dai suka
sami nasara hayewa can karshen tsaunin bayan sun
sha bakar wahala.
Da isar su saman tsaunin suka yi arba da katon
kogon dutsen dake kasan sai hankalinsu ya
dugunzuma ainun, zuciyoyinsu suka karaya suka ji
nadama ta zo musu bisa shiga wannan gasa da suka
yi. Ba komaine ya haddasa hakan ba face ganin
wasu irin halittu masu kama da dodanni kimanin
guda dari uku wadanda suka lullube kogon dutsen
samansa da kasansa.
Su dai wadannan dodanni kawunansu irin na
batoyine, idan suka wangame bakunansu sai kaga
ai zasu iya hadiye karamar giwa, hanayensu da
kirjinsu sirarane amma cikinsu babbane tamkar an
hura balan-balan. 'yan yatsun kafafuwansu da
hannayensu dogayene cike da jijiyoyi babu kyan
gani dauke da zakwa-zakwan farata masu kaifi da
tsini tamkar karfe aka fike, sannan kuma suna da
fuka-fukai a jikinsu.
Duk da cewa sarki muraka da sarki Ridwan a
matukar galabaice suke sakamakon tsananin
wahalar da suka sha a wajen hawan kan wannan
48
Jarumi da Gimbiya
tsaunin suna yin arba da wadannnan halittu sai kowannansu ya yi wuf ya mikezaune aka fara kallon-kallo a tsakaninsu da su. Ga shi dai kofar kogon dutsen a bude take kuma su sarki Ridwan na
iya hango tarin dukiyar zinare da lu'u-lu'u tsubi
guda a ciki amma kogon ba zai shiga ba.
Ridwan da muraka suka kalli junansu, a karo na
farko tunda suka fara wannan tafiya dayansu bace
uffan da abokin tafiyarsa ba face kallon harara da
tarin kiyayyar zuci da zahiri amma sai sarki
muraka ya bude baki yace "Ya kai abokin
hamaiyata kayi sani cewa ba zamu iya shiga cikin
kogon dutsenan ba face mun hada karfin da karfe"
Ridwan yace.
"Ta yaya kenan kake nufi?" Muraka yace "Za
mu rike garkuwoyinmu a sama, sannan mu hade
jikinmu waje guda daya a gaba, daya ya fuskanci
baya muna rike da takobbanmu. A haka za mu
tunkari cikin kogon dutsennan da gudu suna kawo
mana hari muna mai da martani cikin zafin nama
da jarumtaka. Idan har muna da rabo da sa'a to
lallai zamu sami damar shiga cikin kogo a haka
amma fa komai zai iya faruwa, idan ba mu yi
nasara ba dayan mu ba zai tsira da ranyuwarsa ba"
Sa'adda sarki Ridwan ya ji wannan shawara wacce
sarki muraka ya zo da ita sai ya yi shiru yana tunani
da nazarinta.
Abu na farko daya fado masa a rai shi ne anya
kuwa sarki muraka ba so yake ya yi amfani da
damarsa wajen taimakon kansa ba? To idan ma ba
haka bane ai zai iya yaudararsa a lokacin da ya
49
Jarumi da Gimbiya
bashi hadin kai suka sami nasarar shiga cikin kogon ya yaudareshi ya cutar da shi, wata zuciyar kuma sai tace da shi to ai kuma wannan dabarar da
sarki muraka ya zo da ita, tabbas ita ce kadai
hanyar da za su iya bi su shiga cikin wannan kogon
dutsen koda gama aiyana hakan sai sarki Ridwan
ya mike tsaye shima muraka sai ya mike tsayen
suka kalli junansu,Ridwan yace "Kawai mu yi hakan"
Nan take kowannnansu a ciro garkuwarsa daga gadon bayansa ya riketa da hannun hagu sannan
suka zare takobbansu da hannayen dama suka hada
bayansu. Ridwan ne ya fuskanci gaba shi kuma
muraka ya fuskanci bayansu.
A daidai wannan lokacin mugayen halittun
masu kama da dodanni suka fara yin wani-irin
gurnani mai matukar firgitarwa kuma faratan
hannayensu da kafafuwansu suka fara kartar dutsen
kogon. Nanfa tartsatsin wuta ya fara tashi
sakamakon haduwar faratansu da dutsen.
Al'amarin daya dugunzuma hankalin Ridwan da
muraka kenan ganin idan faratan suka karci
wannan dutsen sai ya murmushe, kenan idan suka
taba jikin mutum mene zai faru? Kawai sai sarki
Ridwan ya kurma uban ihu irin na manya jarumai
wadanda ba su san tsoro ba, ai kuwa shima sarki
muraka sai ya kurma ihu. Lokaci guda suka falfala
da gudu izuwa kofar kogon dutsen.
Kaico,bala'i ba a sa masa rana, gobara daga
kogi maganinta sai Allah. Lokacin da wadannnan
gwarazan jaruman sarakai biyu suka nufi kofar
50
Jarumi da Gimbiya
kogon dutsen sai gaba dayansu wadannan halittu guda dari uku suka bude fukafukansu suka taso a
sama suka lullubesu suka rinka kai musu sara da
suka da faratansu na hannu da kafa. Sarki Ridwan
da sarki Muraka suka wanzu suna kare kansu da
garkuwoyin hannunsu kuma suna kade wasu haren
da takubbansu kuma ba su fasa kutsawa ta cikinsu
ba da gudu da dukkan karfinsu. Nan fa wuri ya
yamutse in banda karar haduwar faratan halittun da
garkuwoyinsu da takubbansu babu abinda kunne ke
ji sai kuma karar rurin halittun.
Duk da kasancewar su sarki Ridwan gwarazan
jarumai masu zafin nama, karfin damtse da juriya
sai gashi halittun sun takurasu harma sun fara
samun nasarar uankar sassan jikinsu da sukarsu da
kaifin faratansu da tsininsa. Sarki Ridwan da sarki
muraka suka rinka kurma ihu sakamakon tsananin
zafi da zogin da suka ji a jikinsu a lokacin da jini
ya rinka zuba a jikinsu, harma jiri ya debe su amma
saboda bakin na ci da juriya amma ba su fadi kasa
ba.
A hakan suka ci gaba da bakin artabu suna
banke halittun har suka samu suka shige cikin
kogon da karfin tsiya, suka zube kasa cikin
matukar galabaita. Suna shiga sai halittun suka јa
da baya suka daina binsu kuma suka bace bat
tamkar ba su taba wanzuwa a wajen ba.
Da kyar sarki Ridwan da sarki muraka suka
bude idanunsu suna ganin dishi-dishi koda suka ga
jini na zuba a sassan jikinsu kuma jiri bai daina
dibansu ba sai kowannen su ya yi sauri ya kama
51
Jarumi da Gimbiya
yagar tufafin jikinsa yana daure raunin dake jikinsa
domin tsayar da jinin dake zuba cikin matukar
sauri. Ba komai ne yasa suke wannan saurin ba
face kar rana ta fadi kafin su kai wannan dukiya
birnin soman a matsayin sadaki na auran gimbiya
falman.
Cikin hanzari kowannansu ya dauko damin
dukiyar dinare da lu'u-lu'u dake cikin buhu guda
alhalin dukiyar dake wajen tafi buhu dubu dari
biyar, cikin takaici duk su biyun suka kalli tarin
dukiyar saboda babu damar su kara daukar koda
buhu dai-dai domin ba zata dauku ba sakamakon
nauyinta. Kowannansu a zuciyarsa yace to wai shin
ma wannan dukiyar bata fi gimbiya falman daraja
bane a wajenmu? Ko shakka babu wani sarki a
wannan nahiyar daya mallaki wannan tarin dukiyar.
Suna ji suna gani suka hakura da wannan tarin
dukiyar suka fito daga cikin kogon dutsen suka nufi
Karshen tsaunin domin saukowa kasa.
Anan fa suka tsaya cak suka kalli junansu cikin
mugun nufi, kowannensu yana goye da dukiyar
daya debo, lokaci guda kowa ya kai hannunsa kan
marikin takobinsa amma sai suka kasa zaro
takubban. A zukatansu kowa so yake ya kashe
abokin gabarsa domin ya zamana cewa shi kadaine
zai sauko daga kan wannan tsaunin a raye, bisa
mamaki sai duka su biyun suka bushe da dariya.
Sarki muraka yace "Ya kai abokin hamaiyata ka yi
sani cewa idan muka ce zamu yaki juna bayan duk
wannan bakar wahalar da muka sha ta dauko
wannan dukiyar to tabbbas ragas za mu yi,
52
C
Jarumi da Gimbiya
dayanmu ba zai cika burinsa ba, zai fi mu sauka kasan tsaunin sannan mu raba wannan gardama"
Sa'adda da sarki Rudwan ya ji shawarar da sarki muraka ya zo da ita sai ya yi guntun murmushi a
gareshi yace.
"Tabbas na aminta da wannan shawarar taka"
Yana gama fadin hakan sai kowannansu ya bude
jakar guzurinsa ya dauko igiya mai karfi da
matukar tsawon gaske cikin sauri suka daddaure
igiyoyin a jikin dutsen tsaunin suka ziraro su kasa
suka iso har can inda su Boka samasa suke, koda
Boka samasa suka ga igiyoyi guda biyu sun fado
kasa daga saman tsaunin sai farin ciki ya lullubesu
domin sun tabbatar da cewar sarakunansu sun samu
nasarar dauko abinda suka zo nema a tsaunin
mutuwar cikin hanzari Boka samasa da Boka
Aryan suka mike tsaye kowannensu ya daga kansa
sama domin ya hango sarkinsa amma saboda nisan
tsaunin daga can saman basa iya hang komai.
Sarki Ridwan da sarki muraka suka kama
igiyoyin guda biyu suka fara saukowa kasa daga
saman tsaunin kowannansu na goye da buhun
dukiyarsa ta zinare da lu'u-lu'u a matsayin sadakin
da zai bayar na auren gimbiya falmin. Sai da suka
shafe sa'a uku suna saukowa kasa daga saman
tsaunin sannan su Boka samasa suka fara hangosu
nan fa farin ciki ya kara turnukesu suka soma
kyalkyala dariyar murna. Haka dai su sarakunan
biyun suka ci gaba da kama igiyar suna ta saukowa
kasa. Ko wannansu sai da hannayensu suka dade
suka rinka yin kara saboda rike igiya amma saboda
53
Jarumi da Gimbiya
jarumta da naci basu saki igiyarba suna ta kara
saukowa kasa.
Tsayin daya rage bai fi sauran kamu ashirin ba
da kasa sai kaiwa sarki muraka ya shammaci sarki
Ridwan ya zaro wata wuka mai kaifin tsiya ya
cillata izuwa kan igiyar sarki Ridwan take wukar
taje ta yanke igiyar da yake rike da ita ya suboto
kasa, shi kuma Boka Aryan ya shammaci Boka
samosa ya daki kirjinsa da kafarsa, boka samosa ya
fadi