An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
JARUMІ
DA GIMBIYA
ABDULAZIZ SANI MADAKIN GINI
Jarumi da Gimbiya
JARUMI DA GIMBIYA
Su bakwai ne dukkaninsu sun-yi shigar bakaken kaya sama da kasa, idanunsu Skadai ake gani. Kowannnensu yana rataye da takobi a bayansa kuma suna dauke da wadansu taurari na karfe ma
su kaifi da tsini a jikinsu ma su dan yawa. Lokaci guda su bakwai suka dira akan rufin
sama na gidan sarautar suka karewa gīdan gaba daya kallo. A kalla akwai dakaru kimanin guda dari uku a tsaitsaye a ko wanne lungu da sako na harabarr gidan masu tabbatar da tsaro. Jaruman bakwaíu suka kalli junansu sannan suka kalli shugabansu wanda akwai alama ta zanen jar
tsuntsuwa a jikin rawaninsa, kawai sai shugaban ya
nunawa ko wannen su zai nufa da hannu. Nan take
suka dako tsalle kasa daga saman gininn kai kace
fuka-fukai ne a jikinsu duk da cewa tsawon ginin daga saman zuwa kasa ya kai kamu ashirin da biyar.
Lafiya kalau kowannensu ya sauko kasa ba tare
da anji motsin durowarsu ba, nan fa suka fara
watsawa dakarun gidan sarautar wadannan taurarin
na karfe suna zubewa kasa matatta, kai kace wata
guba suke busa musu dan ko motsin kirki basa
iyaye. Abinda zaifi daure maka kai shi ne zafin
naman wadannan jaruman guda bakwai domin ko
gani su ka yi badakare zai fada kan wani abu da zai
3
Jarumi da Gimbiya
samar da kara wacce zata tona asirin zuwansu sai
kaga sunyi sauri sun rukoshi da hannu, sun ajiye
shi kasa a hankali. Haka da jaruman bakwai suka ci
gaba da bazar da dakarun tsaro na wannan gidan
sarauta har suka karar da su, su dari uku nan. Kai
tsaye shugaban na su ya tunkari turakar Gimbiya
sazira.
a
Kofar shiga turakar a rufe take kuma dakaru
biyune tsaye a wajen. Koda suka hangoshi ya
durfafosu sai suka yunkura a lokaci guda. Daya ya
zare takobinsa domin ya tare shi, dayan kuma ya
kai hannunsa izuwa kan wani kaho dake rataye
sama domin ya dauko shi ya busa amman sai
shugaban dakarun sumamen ya yi wuf ya zaro
taurarin Karfe guda biyu, cikin zafin nama ya watsa
musu. Taurarin karfen suka cake akan goshinsu
duk su biyun suka sulale kasa matattu.
Ita dai wannan babbar kofar ta shiga dakin
Gimbiya sazira a rufe take ta ciki da sakatu da
makullai. Shugaban dakarun sumame ya sunkuya
ya leka ciki turakar ta cikin kafar kubar kofar sai ya
hango kuyangin su da yawa a kwance cikin wani
katon falo suna ta sharar bacci. Kofar shiga cikin
ainahin dakin barci na gimbiya sazira na gaba
kadan.
Koda ganin hakan sai ya rikide ya zama haske
ya shige ta cikin kofar. Yana baiyana a falon ya
sake tunkarar kofar dakin gimbiya kai tsaye. Karar
takun sawunsa yasa kuyanginta suka fara farkawa
daga bacci amma duk wadda ta bude ido tayi arba
da shi sai ta kasa mikewa tsaye kuma ta kasa bude
Jarumi da Gimbiya
baki tayi magana saka makon wata hoda da ya rinka busa musu daga cikin wani lofe dake bakinsa
kuma ya toshe hancinsa da rawaninsa. Nanfa kuyangin suka rinka komawa suna kwanciya
sakamakon bacci me nauyi da ya rinka daukarsu.
Da isarsu kofar dakin Gimbiyar sai ya tsaya cak
domin gimbiyar ya hango ta cikin tagar-dakin
zaune akan gado ta kura masa idanu. Babu-alamar
tsoro ko wata fargaba a tare da ita. A wannan
lokaci tana sanye da wata doguwar farar riga barci
me bayyana kyakkyawar surar jikinta.
Gashin kanta a tsefe yake ya zuba har kasan
kwankwasonta. Macece me dara-daran fararen
idanuwa hancinta dogone a kasansa dan karamin
bakine, kirar jikinta ta kalanguce, kaurin jikinta
madaidaici, fatar jikinta mai haskece, sumul sumul
tamkar ko kuda bai taba sauka a jikinta ba, tamkar
ana tabata jini zai fito. Nan take wannan shugaban
dakarun sumame ya dimauce bisa ganin tsananin
kyawun Gimbiya Sazira saboda dama bai taba
ganinta ba, labarinta kawai yake ji.
_Bayan sun yi kallon-kallo na 'yan dakiku
ashirin zuwa-talatin sai Gimbiya sazira ta sauko
daga kan gadonta ta nufo bakin kofar dakin kai
tsaye ba tare da wata fargababa. Tasa-hannunta ta
zare sakatar kofar dakin guda hudu ta budeta ta
dube shi fuskarta da murmushi irin na mugunta
tace "Kaine shugaban dakarun sumamen da ake
bani labari na birnin samhar ko?" mamaki ya kama
shi ya kasa cewa komai.
Jarumi da Gimbiya
"An gaya mun cewa sarki muraka yasa an baku
horo na wata shida kai da yaranka ku shida domin
kawai ku zo nan birnin kamlaz ku sace ni, tabbas
na yaba da kokarinku da kuma kaifin sihirinka na
tsafi tunda har kuka iya ratsowa cikin gidan
sarautar nan harma kai ka sami nasarar shigowa
6angaren turakata. Nasan kun sami nasarar kashe
gaba dayan dakarun dake tsaron wannan 6angaren
da nake kuma ka sakawa kuyangina bacci me nauyi.
Tofa ka sani ba'anan gizo yake sakar ba, idan kana
ganin za ka iya daukata da karfin tsiya ko da karfin
sihirin tsafi ka kaini wajen sarki muraka babban
makiyin mahaifina to ga fili ga mai doki. Daga ni
sai kai mu jarraba mu gani, babu wanda zai kawo
min taimako, taho mana, zo ka dauke ni idan ka
.isa יי
Mamaki ya kara kama shugaban dakarun
sumamen ya dubeta da murmushi na raini ya bude
baki yace "Ya ke wannan 'yar sarki ke kuwa me
kike takama da shi har da kike tunanin zaki iya
kare kanki daga farmakina?" Gimbiya sazira ta yi murmushi tace.
"Ina takama da duk abinda kake takama da shi,
amma kasan wani abu sai an gwada sannan ake sanin bambanci a tsakanin aya da tsakuwa. Kai
nake jira kawai idan kuma ka karayane, to ka juya ka fice mun na yi baccina da ka katse mun" Koda jin wannan batun sai shugaban dakarun sumame ya fusata ya nufo Gimbiya sazira da nufin ya kamata da hannunsa. Cikin zafin nama ta damki hannun
nasa ta murde ta doki gadon bayansa ya tafi taga6
Jarumi da Gimbiya
taga zai fadi amma-sai ya tsaya daram ya juyo suka
dubi juna yana mamakin irin wannan jarumtaka
tata. Kafin ya ankara sai kawai yaga ta dako tsalle
daga inda take tsaye tamkar kibiya aka harbo ta
kawo masa wawan naushi a fuska. Koda ya goce
hannunta ya samu wani gunki me siffarta dake
tsaye sai gunkin ya rushe ya zube kasa. Nan fa suka
kacame da azababben fada suka wanzu suna kaiwa
junansu naushi da bugu hannu da kafa.
Abinda ya yi matukar daure masa kai shi ne
duk irin salon fadan da ya yi sai yaga itama ta iya
irinsa. Zafin namansa da juriyarsa duk sai suka
zamo iri daya. A duk sa adda ya sami nasarar
naushin jikinta sai yaga ta shanye naushin kuma ta
rama nan take cikin dakiku kadan suka hadawa
juna jini da majina. Sai da suka shafe dakiku ma su
yawa suna wannan gumurzu ya kasa kaita kas
kuma ya kasa galabaitar da ita.
Bisa dole duk su biyun suka ja da baya saboda
gajiya suka yi carko-carko suna kallon juna
sakamakon gajiya sai haki suke yi. A wannan
lokacine hankalin shugaban dakarun na sumamen
ya tashi saboda yasan cewa idan ya kara bata
lokaci shirinsu na sace Gimbiya Sazira zai wargaje
saboda daya 6angaren na gidan-sarautar-za su iya
sanin abinda yake faruwa-anan tunda asuba ta kusa.
Kuma har ya hango ragowar abokan aikinsa
dakaru shidan sun iso babbar kofar shigowa turakar
Gimbiya sazira sun tsaya suna jiransa. Bisa dole ya
yunkura cikin zafin nama ya nuna Gimbiya sazira
da hannayensa biyu, wata irin iska mai karfin gaske
Jarumi da Gimbiyа
ta sauka akan ta tana kokarin zukota gareshi.
Kawai sai itama ta nuna iskar da hannayenta biyu,
take wata jar iska ta tari tasa iskar suka kama
hautsinewa. Ya yi iyayinsa amma ya kasa zuko
gimbiya har shi da ita suka jike sharkaf da gumi,
kawai sai ya saki hannayensa kasa, itama ta saki
suka kama haki suna kallon juna kai kace sa'a uku
suka shafe suna yin aikin karfi.
Shugaban dakarun sumame ya juya zai fita
daga cikin turakar sai tace "Idan ka koma birnin
kilmaz ka gayawa sarki muraka cewa tunda ya kasa
satoni to ni zan zo da kaina na sace dansa Yarima
Andaz". dajin haka sai ya juya ya dubi Gimbiya
sazira yace.
"Ba kasa satoki na yi ba, kwanaki goma aka
bani na kai ki can birnin kilmaz kuma yau kwana
biyu kacal don haka zan ja da bayane domin na
sake yin shiri. Ina mai tabbatar miki da cewa kafin
cikar kwanakin goma sai na kaiki gaban sarki" Gimbiya sazira ta bushe da dariya sannan tace
"Duk irin shirin da za ka je kayi nima zan yi irinsa
anan, ba zaka taba samun nasara a kaina ba, kuma
ka sani nima na yi alkawarin da girman gemun mahaifina kafin cikar kwana gomannan sai na shiga har cikin birnin kilmaz na sato Yarima Andaz. Ka
sani na sani a tsakanin mahaifina sarki Ridwan da sarki muraka duk wanda ya sami nasarar sace jinin daya tamkar mallake kasarsane, ba zan taßa bari ku mallake kasarmu ba saboda tsohuwar gabar da take
a tsakaninmu tun iyaye da kakanni. Kafin ka fita daga nan ina so ka bani amsa amsar tambayayona
8
Jarumi da Gimbiya
guda biyu, wane kai a cikin kasar-kilmaz-kuma
saboda me ka siyar da rayuwarka domin ka
farantawa sarkinku rai? Wane alkawari ya daukar
maka har da ka yi wannan kundumbalar haka?"
Shugaban dakarun sumame ya yi kamar ba zai
ce komai ba sannan yace "Ni ba kowa bane a cikin
birnin kilmaz face jarumi me zaman kansa. Ba-zan
iya baki amsar tambayarki ta biyu ba, sai mun sake
haduwa a karo na biyu" Yana gama fadin haka sai
ya juya ya fice daga cikin turakar, Gimbiya ta
biyoshi da gudu amma yana isowa inda abokan
aikinsa suke su shida sai su duka suka daka tsalle
sama suka dira a cikin rufin saman gidan. Nan take
itama Gimbiya sazira ta dako tsalle sama tamkar
daga cikin baka aka harbota ta dire akan rufin gidan
amma sai ta neme su sama da kasa ta rasa.
Cikin tsananin bakin ciki ta diro kasa bisa
kafafuwanta ta koma cikin turakarta. Adaidai
wannan lokacine taji an busa kaho, alamar angane
cewa baki sun shigo gidan. A wannan lokaci asuba
ta kawo kai.
Sarki Ridwan ya na kwance akan gadonsa yana
bacci kawai sai ya ji an busa Kaho. Cikin hanari ya
mike zaune ya sauko daga kan gadonsa ya dauki
alkyabbarsa yasa ya fice daga turakarsa. Yana fita
yaga dakaru suna ta rugawa izuwa bangaren da
Gimbiya sazira take.
Hankalinsa ya tashi ya nufi bangaren da sauri,
kawai 'sai ya hango sarkin yakinsa barde kinana ya
taho gareshi. Kinana na zuwa daf da shi sai ya zube
9
Jarumi da Gimbiya
kasa bisa guiwarsa guda ya kwashi gaisuwa ya
mike tsaye da sauri ya kame kamar gunki.
Sarki Ridwan yace "Ina 'yata Gimbiya sazira?"
Kinana yace "Tananan a turakarta cikin koshin
lafiya".
"Su waye suka kawo mata hari?"
"Wasy dakarun sumame ne su bakwai, sun
gudu amma na tura abi sawunsu, sun kashe gaba
daya dakarun dari ukun da suke gadin Gimbiya,
kuma sun samu nasarar shiga har cikin turakar
Gimbiya amma ba su sami nasarar tafiya da ita ba".
Cikin mamaki sarki Ridwan yace.
"Ta yaya suka kasa tafiya da ita alhalin sun
sami nasarar shiga har cikin turakarta?" Sarkin yaki
kinana yace.
"Banyi bincike akan hakan ba amma ina ganin
cewa Gimbiya ce kadai zata iya bamu amsar
wannan tambayar" Sarki Ridwan ya yi ajiyar
numfashi sannan yace "Sun taba lafiyartane ko
kuma sun yi mata wani abun?" Kinana yace.
"Ni dai naga jini akan hancinta da lebenta wata
kila dai sun dan doketa".
"Ka je ka zo mun da Gimbiya bayan ta kimtsa,
ku same ni a dakin gani" Kinana yace.
"An gama ya shugabana".
Sarki Ridwan ya juya ya koma 6angarensa shi
kuma sarkin ya kira wani badakare ya bashi
umarnin yaje ya sanar da Gimbiya sazira cewar
idan ta kimtsa yana jiranta za sy sami sarki a dakin
gani, Badakare ya juya da sauri ya tafi isar da sako,
10
Jarumi da Gimbiya
shi kuma sarkin yaki kinana ya nufi bangaren da
tasa turakar take.
**
Lokacin da Gimbiya sazira ta koma cikin
wannan babban falo inda kuyanginta ke kwance
suna bacci sai ta nunasu da hannunta. Take wani
farin hayaki ya lullubesu sai suka farka daga baccin
da suka mimmike tsaye zumbur cikin firgici suna
kallonta shugabar kuyangin wacce ake kira Dulis ta
leka waje ta hango dakarun tsaro kwance a kas
matattu ana kwashe gawarwakinsu sai ta firgita ta
rugo gaban gimbiya ta zube kasa tace "Tuba nake
ranki ya dade, na rantse da darajar mahaifinki ba
musan abinda ya faru ba a gidannan" Gimbiya
sazira ta dubeta cikin murmushi tace.
"Ai ba za ku sani ba, ni kadaice naga abinda ya
faru, sarki muraka ne ya turo dakarun sumame
domin su sace ni, don haka maza a shirya mun
ruwan wanka da abincin kalacina" Durus tace.
"An gama ranki ya dade".
A daidai wannan lokacin badakaren da sarkin
yaki kinana ya aiko ya karaso cikin turakar yana
hango Gimbiya sazira sai ya risina ya isar da sako,
Gimbiya sazira ta wuce cikin turakarta, badakare
ya risina ya mike-tsaye ya juya ya tafi su kuma
kuyangin sai kowacce ta kama gudanar da aikin da
ta saba yi.
Sarki Ridwan na zaune a cikin dakin gani shi
kadai yana cin tuffa, sarkin yaki kinana tare da
Gimbiya sazira suka shigo. Yana ganinsu ya mike
11
Jarumi da Gimbiya
tsaye cikin farin ciki ya bude hannayensa Gimbiya
sazira ta fada kan kirjinsa suka rungume juna.
Sarki Ridwan ya sumbaci goshinta sannan ya kama
hannunta suka zauna tare akan kujerar da yake.
Sarkin ya dubi sarkin yaki ya masa wani nuni
ga farantin tuffar dake bisa tebur a gabansu. Kinana
ya dauki tuffa guda daya bayan ya zauna ya fara ci,
sarki ya dauko wata tuffar ya mikawa Gimbiya
itama ta karba ta kai baki kamar zata ci sai ta fasa
ta ajiye tuffar bisa faranti. Sarki ya dubeta cikin
mamaki yace "Me yasa kika ki ci wannan tuffar?"
Gimbiya ta yi murmushi tace.
"Na ci tuffa da yawa a cikin abincin kalacina
da zu kuma a koshe nake sosai".
"To ammma dai kya ci ko dan yaya tunda ni ne
na baki da hannuna" Gimbiya sazira tace "Ka yi
hakuri Abba idan na ci tffarnan koda bata wuce
kwayar zarraba zuciyata ta shi zata yi na yi amai"
Koda jin haka sai jikin sarki Ridwan ya yi sanyi,
sazira ta yi masa wani irin kallo na kurulla domin
ta gano wani abu amma sai ya yi sauri ya kauda
aknsa ya dubi sarkin yaki kinana yace masa.
"Wane sakamako dakarun da ka tura suka bi
yan sumame suka samo?" Kinana yace "Sun gano
cewa sarki muraka na birnin samhar ne ya turosu su
sace gimbiya sazira" koda jin wannan sai sarki
Ridwan ya fusata ya mike tsaye zumbur ya dakawa
sarkin yaki kinana tsawa yace "Ya aka yi kuka yi
sakaki har suka je bangaren da gimbiya take ba tare
da kun sani ba?" Sarkin yaki ya dan sunkuyar da
kansa kas yace.
12
Jarumi da Gimbiya
"Ya shugabana kasani cewa a daren jiya bana
nan ka aike ni kauyen Batur kuma ban dawo ba sai
gefin asuba, kuma wadannan dakarun sumame
suna da karfin sihirin tsafi ni kadaine tsaransu, idan
da ina nan ba su isa su shiga bangaren da gimbiya
take ba, sai bayan sun gudu sannan na iso cikin
gidan sarautarnan Sa'ar da-sarki Ridwan ya ji
wannan batu sai ya yi ajiyar numfashi ya koma kan
kujera ya zauna a kusa da gimbiya sazira ya dubeta
yace.
"Ya ke 'yata-a sanina dake baki taba yi min
karya ba kuma na yarda da ke dari bisa dari, ina
son ki yi mun bayani a nutse kuma ki gaya mini
iyakar gaskiya, mene ne ya hana wadannan
dakarun sumame samun nasarar tafiya dake?" Ya
yin da gimbiya sazira ta ji wannan tambayar sai ta
gyara zama gami da gyaran murya. ta dubi
mahaifinta cikin nutsuwa tace.
"Ya kai Abbana ka sani cewa mafi yawan dare
bana yin bacci domin lokacine da nake zama ina
karance-karance na littafai na tarihin Kasashen da
suke cikin wannan nahiya tamu. Bana kwanciya
bacci har sai gari ya waye na yi kalaci sannan nake
komawa bacci, ba zan farka ba face idan kai ne ka
tura a kirawoni. A jiya-eikin daren ina cikin karantalittafi na tarihin wannan masarautar tamu sai kawai
naji motsin dirar wani abu akan rufin sama na
Gangaren turakata. Hakan ne yasa na rufe littafina
na boyeshi a karkashin matashin kai na gadona.
Kawai na zauna ina kallon kofar shigowa
turakata, tsawon dakiku masu dan yawa ina zaune
13
Jarumi da Gimbiya
a hakan kawai sai na hango wani badakare sanye da
bakaken kaya, fuskarsa a rufe, idanunsa kadai ake
gani ya nufo kofar turakata. Da isowarsa sai muka
hada idanu ta cikin taga, take zuciyata ta buga da
karfi na firgita kafin na yi wani motsi ya ratso cikin
turakata ya bayyana a gabana. Jikina na karkarwa
na dubeshi muryata na rawa nace wanene kai?
Mene ne ya kawoka nan? Badakaren ya bushe da
dariya yace ni manzone daga sarki muraka na
birnin samhar kuma na zo ne na saceki. Na dube
shi a nutse nace shin kana da mata?
Ya dube ni cikin mamaki yace me yasa kika yi
min wannan tambayar? Nace saboda nasan cewa
kowane mutum yana son ahalinsa. Tabbas kana da
mata kuma kana da 'ya guda daya sunanta Yarsik
shekararta goma sha daya a duniya, kana sonta fiye
da komai a duniya, shin idan wani ya zo ya saceta
ya rabaka da ita ya za ka ji? To ka sani idan ka
rabani da mahaifina kaima sai an rabaka da Yarsik.
Yana jin wannan batu jikinsa ya yi sanyi ya kasa
kamani kawai sai naga ya juya ya fice daga cikin
turakata bayan ya nausheni a fuska na fadi kasa.
Wannan shi ne dalilin daya saka wadannan
dakarun sumamen suka fasa kamani domin su tafi
da ni" Sarki Ridwan ya yi shiru yana mai kurawa
Gimbiya sazira idanu yana nazari bayan ta gama
jawabinta sannan ya yi ajiyar numfashi yace.
"Nasan cewa marigayi Boka samasa ya koya
miki ilimin sanin sirrin mutum to amma ai wannan
ilimin ba ya aiki face ka taba tafin hannun mutum
da tafin hannunka, ya aka yi ke kika iya sanin sirrin
14
Jarumi da Gimbiya
rayuwar wannan badakare da ya zo saceki?"
Gimbiya sazira ta yi murmushi tace.
"A daren da boka samasa zai mutu ai kasan
cewar na je bankana da shi,kuma mun kadaita da
shi a cikin turakarsa, a wannan lokacin ne ya kara
kaifin wannan ilimin a gareni ya-tabbatar min da
cewa ko kallon idanun-mutum-na-yi zan iya sanin
komai na sirrin rayuwarsa" koda jin wannan batu
sai hankalin sarki Ridwan ya tashi yace a zuciyarsa
kenan yanzu gimbiya tasan-dukkanin-sirrikana na
rayuwa da nake boye mata? Kai ban yadda da
hakanba har sai na gwadata na gani. Koda gama
aiyana hakan sai sarki ya dubi sazira yace.
"Shi kenan na sallameki za ki iya tafiya, ni da
sarkin yaki za mu tattauna akan yadda za mu
tsananta tsaro a gidannan domin kada a sake kawo
miki hari" Gimbiya ta yi murmushi ta mike tsaye ta
fice daga cikin dakin suka-bita da kallo har ta fita
suka dubi junansu suka yi shiru.
**
Al'amarin wadannan dakarun sumamen guda
bakwai kuwa bayan sun gudu daga cikin gidan
sarautar birnin kilmaz sai suka bayyyana tsulum a
cikin daji inda suka daure dawakansu. Kowannansu
ya yaye rawanin dake kansa. Shugaban na su
saurayine matashi ma'abocin kyawu da kwarjini da
kuma sura irin ta cikakkun jarumai ana kiransa da
suna Lurwan. Kai tsaye ya nufi kan wani dutse ya
je ya zauna ya yi tagumi yana tunani. Suma sauran
dakarun sumamen su shida sai suka zo suka
zazzauna a kusa da shi suka yi jugum! Kai kace
15
Jarumi da Gimbiya
zaman makoki ake yi. Tsawon kimanin dakika
arba'in dayansu baice uffan ba. Sannan daya daga
cikinsu mai suna zainur ya dubi jarumi lurwan yace.
"Ya shugabana gaba dayanmu jikinmu ya yi
sanyi ai bamu taba sanin cewa gimbiya sazira
jaruma bace kamar haka, kuma tana da karfin sihiri
da tun farkoma ba za mu yi gangancin biyoka zuwa
wannan aikin mai hatsari kamar haka ba" koda jin
wannan batu sai jarumi lurwan ya fusata ya dakawa
zaunur tsawa yace "Kada ka gaya mini maganar
banza mana. Gabadayanku ku shidannan kudade
na baku ma su yawa wanda baku taba mallakarsu
ba sannan kuka amince kuka biyoni izuwa wannan
aikin. Kusani cewa mahaifiyata sarki muraka ya
tsare domin na yi masa wannan aikin idan na ki yin
wannan aikin kasheta zai yi don haka ta kowane
hali sai mun koma cikin birnin kilmaz mun sato
gimbiya sazira idan kuma kuna ganin cewa ba za
ku iya sake komawa ba to kowannenku ya biyani
kudina dana ba shi darham dubu goma-goma yanzu
take".
Lokacin da barde zainur suka ji wannan batun
sai duk su shidan hankalinsu ya dugunzuma suka
rasa abinda yake musu dadi a duniya. Lurwan ya
sake dubansu yace "Sauran kwana takwas wa'adin
da sarki murata ya diba mini ya cika. To ni na baku
kwana uku ku gama yanke shawara domin a kwana
na uku za mu koma cikin birnin kilmaz mu sato
gimbiya sazira, so nake a cikin kwanaki biyunnan
na gama tunanin dabarar da zamu yi mu sami
nasara ba tare da mun sake fuskantar wata
16
Jarumi da Gimbiya
matsalarba. Ku tashi ku fara kafa mana tanti ni zan
shiga cikin daji na farauto mana nama da za mu
gasa" Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya
dauki kwari da bakan sa ya nausa cikin daji.
Zainur da 'yan uwansa suka bisa da kallo har
ya kule a cikin dajin sannan zainur ya dubi sauran
abokan tafiyar yace-musu "Anya kuwa jarumi
lurwan bai samu tabin hankali ba? A ina za mu iya
samo dinare dubu goma-goma da ya bamu mu
dawo masa da su alhalin duk munyi bukatunmu da
su a can birnin samhar. To ma wai wane irin sabon
tunani zai yi wanda har zai iya samun nasara sato
gimbiya sazira? Juma'ar da za tai kyau ai tun daga
laraba ake ganeta" Daya daga cikin jaruman shida
me suna komaru yace.
"Mun riga mun siyar da rayukanmu tunda mun
karbi kudinsa akan wannan aiki don haka dolene
mu cika masa alkawarin in ba haka ba kuwa sai dai
mu gudu mu barsa mu bazama zuwa wata nahiyar
ta duniya mu hakura da mahaifarmu da danginmu"
Zainur yace "Hakan ba zata taba faruwa ba, ku
tashi mu fara aikin kafa tanti". Ba tare da wata
gardama ba kuwa sai suka mike tsaye suka fara
aikin kafa tantuna.
**
Al'amarin sarki Ridwan da sarkin yaki kinana
kuwa bayan Gimbiya sazira ta fice daga cikin
wannan dakin gani ta bar su, su biyu rak sai sarkin
Ridwan ya mike tsaye yaje ya bude wata durowa ta
karfe dake jikin bangon ya dauko wani akushi na
17
Jarumi da Gimbiya
sihiri wanda a rufe yake kuma ba a budeshi.
saman akushin akwai kofofi guda biyu rak.
A
Shi wannan akoshin an sasssakashine daga
danyen lu'u lu'u sai sheki yake yi. A gefensa guda bakwai akwai wani bututu wanda inda za'a zuba
ruwa ta cikin wannan kofofin guda biyu to zai iya
zurarowa waje ta cikin bututun. Sarkin Ridwan ya
zo ya ajiye wannan akushin a gaban sarkin yaki
kinana sannan ya zauna ya dubeshi yace.
"Ya kai sarkin yaki shin kasan ko wannan
akushin na mene ne?" Kinana ya yi dan guntun murmushi yace "Ranka ya dade na sani mana,
wannan ai shi ne akushin sihiri na mallakar wannan
nahiyar gaba daya. A cikin waannan kofofi guda
biyu dake samansa kana bukatar ka diga jinin
Gimbiya sazira da jinin Yarima Andaz na birnin
samhar, idan aka diga jinin wani hayaki zai tashi
ya fito ta cikin wannan bututu ya baibaye jikinka.
Da zarar hakan ta faru duk kasar daka yaka a
wannan nahiya sai ta dawo karkashin ka, kai