tayi adaki tanaji wayarta na ringin taqi dagawa sbd tasan cewa xa'ayi take ana kiranta.
Har bacci yafara janta Anty basma tashigo dakin tareda zama bakin gado tace,
Lailah ana kiranki a palon alh babba.
Ba Indi zani ni sbd gskia ni bansan dalilin dayasa ake son shiga life dinaba.
Yi hkr lailah muje kiji koma meyene kadaki manta daddynki na wajen.
Miqewa tayi tana 6ata fuska suka tafi.
Zama tayi tana yatsinar fuska sbd kowama batason gani.
Gyara murya yayi yafara fadin,
Lailah inason ki sanar damu wa kika zaba akan zancenmu na last week.
Turo baki tayi tace,
Nifa gaskia nafada banason kowa acikinsu barema wani aure.
Jinjina kai yayi yace,
To kisani kinyi wasa da damarki dan kuwa bazan janye zancenaba na aurar dake ga duk Wanda naga damaba matuqar baki fidda daya acikinsuba.
Dan haka kowa ya shirya ranar juma'a zan aurar da ita ga duk Wanda nasama,
Haka kuma jabeer da zubair Ku fiddo da mata tare duka za'a hadaku Dana ayshat.
Da gudu tabar palon tana fasa ihu
Sauran jama'ar palon ma da dai dai suka fita sbd hukuncin baima kowa dadi ba bama kamar dad dinta dayakeso tafara gama karatunta.
***************
3 days later,
Lallashin dunia dad da Anty basma sunyi mata amma taki daina kuka.
Yau maryam tazo tasamu ta lallabata dakyar suka fita yawo.
Sosai taji dadin yawon sbd tamanta matsalarta kuma maryam ta tabbatar matada wasace tsoho ke mata dan ba yanda za'ayi ayi mata auren dole
Hakan yasa ta sake suka hau chilling dinsu.
Ta 6angaren su zubair kuwa sunga ba kowa sai Allah sun fidda matayensu har ankai komai anfara shirye shirye.
Gida yacika maqil da 'yan biki domin kuwa hidima tayi nisa
Su lailah da siyama tareda maryam ba abinda ya damesu sbd lailah tuni tayi watsi da komai dan tasan ba abune mai yiyuwaba auren dole agareta.
Duk gyaran da akewa ayshat amarya itama sai anyi mata nata bare ma Anty basma data dage gurin gyaranta.
Anyi kamu da walima ana gobe daurin aure suka fita itada maryam da siyama harda ayshat zasu karbo sauran dinkunan ayshat.
Basu dawo gidaba sai maraice.
Agajiye suke dan haka suna shiga daki ta fada toilet tayo wanka sbd tana period ne.
Doguwar sleeping dress tasaka baqa sbd black shine best colour dinta.
Cornflakes tasa safiya takawo mata tasha tana gamawa saiga hayat brothern zubair yashigo dakin.
Zama yayi akan stool yana cewa,
Lailah kunada baqo a qofar gida tun dazu yazo yaseer maigadi ya hanasa shiga yace saiya kiraki yace yanata kira baki dagaba.
Wat" tafada da qarfi tana miqewa sbd tasan bilal ne brothern maryam Wanda shi take dating 'yan kwanakin.
Miqewa tayi ta 'Dora gyale akanta ta fito.
Tana isa bakin gate ta tarar dashi yana alwala fizge butar tayi tareda wankesa da ruwan.
Dagowa yayi yana mata kallon ido cikin ido wayar hannunta ta jefesa da ita tana nunasa da yatsa tace,
Kai ko acikin dabbobi bansan kai wayeba sbd daqiqancin yayi yawa.
Wani wawan kallo ya jefeta dashi
Hannu ta 'daga zata kai masa mari
Hannunta taji anriqe riqon daya razanata sbd taji maza.
Kallonsa tayi tareda fizge hannunta tafara zazzaga masa rashin mutunci agaban mutane har hkr ake bata amma bata saurara masaba.
Daga qarshe dai shigowar alh tsoho daga masallaci yasa kowa watsewa.
Kallon yaseer yayi yace......
M & Z
[3/4, 14:04] βͺ+234 818 350 7088β¬: ππ AUREN RABA GARDAMAππ
Na
MAMUH GEEEπ
And
ZINNIE SMART
56~60
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.
Yaseer ina tsananin jin kunyar cewama kayi hkr sbd yau 'da ne ka haifesa amma baka haifi halinsaba,
Nayi baqin cikin ganin abinda lailah tayimaka yanxu a bainar jama'a,
Haka zalika tun ba yauba ina lure da sane da rashin mutuncin datake tafka maka.
Qara kallon yaseer din yayi cikin wani nazari daya shigesa yanxun yace,
Yaseer kadaka damu insha Allah zanyi maganin abin nasan matakin dazan 'dauka.
Cikin qoqarin danne 6acin ransa yace,
Alh basai ka mata komaiba sbd ni ban dauki abin da mahimmanciba.
Girgiza kai yayi cikin qara tabbatar da tunanin da yayi ya wuce.
Cikin tsananin 6acin rai da wani irin tiririn zuciya ya shige dakinsa na gate din yana fidda wani irin huci.
Rigarsa ya farke daga jikinsa yayi wurgi da ita tareda kaiwa bango duka,
Duk baimasaba saida yasa qafa yayi ball da laptop dinsa dake charging.
I hate her,
I hate her so very much,
I despise her,
Infact I hate this house and every one in it.
Wayarsa yaciro yana huci ya danna kira.
Ringing biyu aka dauka tareda cewa,
Barka da yini sir.
Bar tsaya amsawaba yace,
Lawal ka sanar da isowata office gobe sbd na rufe case din binciken alh naseer modibo,
Sannan kayimin booking ticket gobe zan wuce Miami.
Cikin son cika umarnin ogansa yace,
Yes sir but.....
No buts just did wat I said.
OK sir.
Wurgi yayi da wayar tareda fadawa toilet din dakinsa.
******************
WASHE GARI
Qarfe goma za'a daura aure dan haka tuni gida ya kaure da hayaniyar jama'a.
Kowa ka gani ya shirya sai shirin daura aure ake.
Qarfe Tara da Rabi kowa ya shirya banda lailah dan har lokacin barci take bata tashiba
Hattasu maryam da siyama harda amarya ayshat sungama shiryawa cikin ado na musamman.
Anty kubra ce tashigo dakin da kaya a hannunta tana cewa,
A'a maryam harkun shirya Baku tada mutuniyar takuba ta shiryaba har an fara daurin auren.
Janye bargon da lailar ke ciki tayi tana cewa,
Daughter maza tashi kiyi wanka ga kaya na musamman nakawo miki.
Tashi tayi tana duba agogo kafin ta kalli su siyama dake faman daura dankwali ayshat kuwa turare take fesawa taci ado sai qyallin amare takeyi.
Lallaima 'yan Matan nan shine kuka shirya Baku tadani ba.
Tura toilet Anty tayi tana cewa,
Bari anjima kya musu wannan.
Tana fitowa wanka tahau shiri.
Dark blue lace ne Anty basma takawo mata Wanda daddynta ya siyo matasu cikin tsadadden lefen dayayo mata kasancewar alh tsoho ya sanar dashi wazai aura mata.
Mai makeup na gama mata makeup ta suka sauko qasa gaba dayansu.
Palon cike yake da mutane anata hidima.
A gurin daurin aure kuwa ba qaramin tashin hankali da mamaki jama'a sukayiba jin an daura auren LAILAH ALI MODIBO da YASEER.
Iya kaduwa su zubair da jabeer sun shiga sai dai sunsan akwai rigima da tashin hankali gurin lailah.
Ana gamawa batareda kowa yashigo gidanba aka 'dunguma zuwa gurin 'dauro nasu jabeer da zubair gidan matayensu.
Ana watsewa bilal yakirata yace,
Bby gani nazo daurin aure amma ba kowa har an watse inaga nayi latti.
Ok Ai ba damuwa bari nazo ko fira muyi kaga adon danayi.
Ko gyale bata yafaba sbd rigar jikinta fitted gown ce data kar6i jikinta ta zauna mata sosai gashi rigar Nada tsawo sosai amma heels din qafarta sun taimaka gurin rage tsawon rigar.
Tun daga nesa ya kafeta da ido yana hade yawu da qyar yana ayyana kota halin qaqa sai ya mallaki lailarsa.
You luk fabulous.
Thank you my.....
Bata qarasaba taji qarar wurgi da kaya tareda wani irin hucin 6acin rai mara misaltuwa na tasowa daga 'dakin yaseer.
Gabantane ya buga da qarfi haka kawai amma saita daure zata kuma magana motocinsu dadynta dasu alh tsoho dasu abbah tareda angwaye suka parker.
Qarar lasifikar maroqi ce tasayi firgifit amma ga babban tashin hankalinta saita taji yana fadin,
Yau dai min shaida 'daurin auren 'yayan gata da aka 'daura na,
JABEER DA SALMA,,,
ZUBAIR DA KHULSUM,,,
AYSHATU DA ANGONTA AHMAD,, SAINA GIMBIYA LAILAH ALI MODIBO DA ANGONTA YASEER.
Kasa tantance mezatayi tayi saita qurawa daddynta ido don son tabbatarda abinda taji..
Sunkuyar da kai yayi cikin jin wani irin yanayin tausaya mata.
Yanayinsa ya tabbatar mata da hakan gaskiyane.
Juyawa tayi gurin alh tsoho ta 'daga hannu ta.........
M & Z
[3/4, 14:04] βͺ+234 818 350 7088β¬: ππ AUREN RABA GARDAMAππ
Na
MAMUH GEEEπ
And
ZINNIE SMART
61~65
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.
Hannu ta 'daga ta dora akai tareda kurma wani mahaukacin ihu daya ratsa ko ina cikin gidan Wanda hakan yajawo hankalin kowa yayo harabar gidan.
Ganinsu Anty basma da kowa na gidan bikin sun fitone yasa tafara ganinsu dishi dishi kafin idonta ya rufe ruf ta sulale qasa a sume.
Anty kubra da maryam,siyama,ayshat da umman jabeer ne sukayi kanta da sauri suna salati.
Umman zubair kuwa tuni ta kawo ruwa ta antaya mata amma ko motsi batayiba.
Qara zuba mata ruwa akayi still ba alamar zata motsa.
Zubair ne yayi saurin kallonsu Anty basma yace,
Anty ku kamota da sauri muje asibiti.
A gigice suka kamata aka saka motar jabeer suka 'dunguma zuwa asibiti.
A emergency aka karbeta tareda fara bata taimakon gaggawar datake buqata.
Laidar ruwa biyu tasha kafin ta farfado,,
Idonta akan Anty basma da maryam ya sauka duk da daddynta na 'dakin amma saita samu kanta da qin kallon gefensa dan wani zafinsa takeji sbd ya tabbatar mata da baya qaunarta.
Anty basma aure aka dauramin da maigadin gidanmu sbd anga banida uwa,
Dama uwa itake son danta fiye da duk wani Wanda zai nunama soyayya.
Yau na tabbatar da banida mahaifiya a duniya,
A rasa waza'a dauramin aure dashi sai maigadin gidanmu.
Anty basma mum ta gargade ni da zuwa Nigeria na Dage akan zanzo sbd ina tunanin dad da alh tsoho suna sona fiyeda komai,
Ashe rashin sanine,duk wannan soyayyar a dah ne....
No lailah ki daina fadar haka dan ina tabbatar miki ba wani mai sonki da qaunarki a duniya sama da daddynki,
Daddynki yana qaunarki haryanxu kuma ya amince da wannan auren naki ne sbd kawai yiwa alh biyayya.
Kema kuma ina roqonki tareda baki shawarar kiyiwa naki mahaifin biyayya.
Girgixa kai tahauyi tana kuka mai qarfi tanacewa,
Bazan iya ba,
Bazan iya aurensa ba,
Bazan iya rayuwar awa daya dashiba bare rayuwar har abada.,
Bazan iya ba,
Na tsanesa wlh....
Kuka take rerawa cikin tsananin baqin ciki da tausayin kanta.
Dafa kanta dady yayi yace,
Sai hakuri lailah sbd bamuda wani zabi daya rage banda kiyi hkr ki kar6i qaddarar nan
Kuma ina tabbatar da zakiji dadi arayuwa lailah ko bayan raina ne muddin kikayimin wannan alfarmar ta kar6ar wannan hukunci na alh babba.,
Lailah ni mahaifinki haryanxu banida kamarki kuma ina roqonki lailah kiyimin wannan biyayyar dan.....
Jikinsa ta fada da sauri tana sakin wani sabon kukan tareda cewa,
Dady kadaina roqona.
Ki yarda dani lailah ina qaunarki fiyeda komai danake dashi arayuwa.....
Dady nasani kuma na yarda kana sona..
Lallashi tareda kwantar mata da hankali yayi har Dr yashigo tareda basu sallama suka kamo hanyar gida.
A hanya shiru tayi tareda jingina kanta ajikn window ta qurawa hanya ido tana tunanin rayuwarta ta lalace gabaki daya batada wani Abu daya rage mata najin dadi.
Runa isa bakin gate gabanta ya buga da qarfi sai alokacin ta tuno da tajiyo karar fasa kaya adakin yaseer kenan shima bayason auren.
Zanyi maganinsa dansaiya yabawa aya zaqinta.
Hayat ne yabude musu gate sbd yaseer din baya kusa.
Sunayin parking hayat ya matso yayi mata sannu da jiki yace kuma alh tsoho yace su wuce gurinsa yana buqatar ganinta itada dad dinta.
Suna shiga suka Tarar da ayshat tareda jabeer da zubair sai uwayensu.
Nasihar aure yayi musu sosai sbd a Daren ayshat zata tare hakama su zubair zasu tare a sabbin gidajensu da matayensu.
Kallon lailah yayi a natse yace,
Lailah nasan kina cikin damuwar auran da 'aka daura miki to batareda da 6ata lokaci ba dai ina baki umarni dakuma nasihar kiyiwa iyayenki da mijinki biyayya sbd ina hango miki kyakkawar Rayuwa da kwanciyar hankali a tattareda yaseer,
Nasan yaseer tun tuni nakumasan waye yaseer dakuma iyayensa hakan yasa na 'daura miki aure dashi.
Abba naseer ne ya dora da tasa nasihar kafinsu dady daganan aka dauki amarya ayshat zuwa gidanta suma su jabeer da abokanansu suka dunguma zuwa nasu gidajen.
M & Z
[3/4, 14:04] βͺ+234 818 350 7088β¬: ππ AUREN RABA GARDAMAππ
Na
MAMUH GEEEπ
And
ZINNIE SMART
66~70
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.
Tunda tashiga dakinta dake zaune gaban mirror tana kallon fuskanta.
Tunani take ta ina zata fara?
Abu daya dayayi mata dadi shine babu alamar yanxu za'ayi maganar tarewarta ko wani Abu daya danganci auren.
Toilet ta fada tayo wanka tana fitowa su siyama da maryam nadawowa daga kai ayshat da'akayi.
Mamaki sukayi ganin tayi shirin bacci tana qoqarin kwantawa.
Maryam tayi qarfin halin fadin,
Lailah ya jikin naki?
Hummm my friend dnt worry abt me am fine now,in fact I will be fine every day.
Hmmmn wat a miracle my frnd,meya canxaki lokaci daya?
Babu abinda ya canxa ni kawai dai nayi wani tunani naga meye abin damuwa ga auren da ni ban dauka aure ba,hakama Wanda aka daura dashi shima bai daukesa aureba.
So inaga wannan ba aure bane daxan ringa damun kaina akai.
Tana gama fadar haka taja bargo ta lullubewarta.
***************
Tunda aka gama daurin auren haryanxu zuciyarsa bata gama tafasaba domin kuwa wani irin tiririn wuta yakeji tana masa dan ba qaramar shammatarsa alh tsoho yayi ba daura masa aure da abinda yafi tsana.
Duk kayan dakin yayi faca faca dasu amma har alokacin bai dainajin tsananin 6acin ran dayakejiba saima qaruwa da baqin cikinsa yakeyi.
Wayarsa ce tayi ringin yanaji yaqi ko dubawa bare ya daga.
Qara kira akayi ya dan kai dubansa
Sunan mum dinsa yagani da sauri ya duba agogo yaga qarfe hudu na asuba yasan yanxu can Miami bakwai na safe yayi.
Daga wayar yayi cikin dasashshiyar murya yace,
M..u.m,
Mum I'm doomed.
Mum I hate her.....
Yaseer kwantar da hankalinka komai zai daidaita insha Allah,ni dama kira nayi nacama inason next week zanzo Nigeria.
A'a mum kada kixo inanan dawowa cikin week dinnan so pls mum kadaki zo kibari nadawo.
Kashe wayar yayi yayi wurgi da ita yana tunanin dole yabar qasar nan dan gwara tun wuri su nemawa 'yarsu miji.
**********
Washe gari tun safe tashirya tanada lecture itada maryam kuma daga can maryam zata koma gida sbd angama biki kowa ya watse.
Straight skirts ne ajikinta purple colour da free shirt light purple sai black Vail data yafa dan siriri.
Handbag da keys din motarta ta dauka suka fito suna fidda wani sanyayan qamshi.
Kallon Anty basma tayi zatayi magana maryam tayi saurin cewa,
Anty pls don't spoil her mode.
Cup din freshmilk kawai tasha ta mike itama dai maryam ba wani abincin kirki taciba suka fice.
Key tasa zata bude motarta kenan hayat yazo yace,
Alh babba yace kada ta kuskura ta fita batareda ta nemi izinin mijintaba.
Kallon hayat tayi dakyau tace,
Are you really telling me this?
Juyawa yayi yana cewa,
Zaki iya zuwa ki tambayi tsohon da kanki dan naga kunfi kusa.
Bayansa tabi da kallo kafinta maido kallonta ga maryam wadda ita ma mutuwar tsaye tayi dajin wannan sabon alamari.
Wani mummunan 6acin Raine ya dibeta a fusace ta bude mota zata shiga taji muryar alh tsoho na cewa,
Kadaki soma.
Dama nasan bazakiyi abinda na aiko afada mikiba shiyasa na fito da kaina.
Da qarfi ta tura qofar motar tana cewa,
Yanxu school dinma bazaniba saina tsaya 6ata lokacina gurin wani tambaya.
Tsawa ya daka mata wadda ta ka'da hantarta harsaidata ja daga baya.
Daga yau duk inda zaki idan baki tambayesaba to wallahi bazakijeba.
Da sauri ta kalli daddynta dasuka fito tareda tsohon tace,
Dady ka.......
Daga mata hannu yayi yace,
Son danake miki bazaisa nabari kiringa haduwa da fushin ubangijiba,
Nadai roqeki kiyimana biyayya kiyiwa yaseer biyayya amma kinqi dan haka nima daga yanxu tsaurara miki zanyi.
Wucewa sukayi suka barta tsaye
Da gudu takoma cikin gida tana hawaye.
YASEER. Dadynta yakirasa cikin nutsuwa.
Yaseer harga Allah na yaba da nutsuwarka dakuma yanayin kamalarka.
Yaseer alh babba ya yarda dakai shiyasa yabaka lailata,
Cancantar da yayi dakai ita tasa na yarda dakai.
Ayau yaseer ni mahaifi kuma uba dayake son 'yarsa tazaka tagari kamar 'yar kowa ina roqonka dakaji tausayin manyancina ka karbi 'yata da amana.
Hakika lailah nada rauni sosai ta 6angaren sanin Rayuwa dakuma rashin sanin darajar komai na Rayuwa.
Yaseer ga amanar 'yata nan inason ka 'doramin ita akan hanya ta sanin meye Rayuwa.
Nasan kaima bakayi na'am da wannan aureba sbd na lura da yanda kake cikin rashin nutsuwa.,
Zan baka gida da mota tareda aikinyi mai ma'ana,
Nidai roqona ka daramin lailah ahanya harzuwa lokacin dazaka samu mace daidai zabinka saika qara da iya..
Ajiyar zuciya yayi ahankali yace,
Alh bana buqatar gida,mota da aikin yi sbd zan dora lailah akan hanya ta gari.,
Alh ni bana qarya ko 6oyon zance dan haka kayi hkr,
Maganar gaskia ni banada ra'ayi da lailah bare aurenta,
Haka nima sanin alh babba da girmansa aguna yasa na yarda nayi masa biyayya.,
Alh alh yasa nayi masa alqawarin tarbiyantar da lailah
Na amince sbd girmansa aguna.,
Alh kaima girmanka aguna babbane dan dai baka sani bane,
Na yarda dazan Dora lailah a hanya tagari kuma zanyi sbd Allah dakuma girmanku aguna.
Maganar kudi da gida kuma bana buqata inason abari ahakanma zan iya.
Nagode yaseer Allah yayi maka albarka yakuma baka ikon daurewa da halayenta.
Amin yace afili yana miqewa amma a zuciyarsa cewa yayi saina tabbatar 'yarka tayi kuka arayuwarta harsaita roqi mutuwa da kanta.
*****************
Sati daya lailah bata zuwa ko ina sbd batasan yama za'ayi ta tambayi maigadi ba,ita batamasan ya ake cewa maba idan za'a fita.
Wayartace tayi ringin tana dubawa taga bilal ne ke kiranta.
Tsaki taja ahankali kafin ta 'daga.
Hello bby gani nazo ina qofar gida.
Harzata kashe saikuma tayi tunanin gwara taje ko yawo yakaita tasha iska.
Miqewa tayi tareda Dora jacket akan handless gown dinta ta fito.
A waje yayi parking dan haka gate ta nufa kai tsaye ta fita.
Wayam tagani ba kowa.
Kiransa tayi awaya rai bace tace,
Meye haka zakacemin kazo....
Sorry lailah rashin sani yasani zuwa sbd maigadinku ya fito ga ganni nace masa gurinki nazo yacemin kada nakuma zuwa gurinki wai ke matarsace an daura muku aure.
Wat"" tafada da qarfi,
Are u sure haka yafada maka?
Kashe wayarsa yayi cikin tsananin damuwa.
Har tuntube take sbd tsananin 6acin rai,
Kai tsaye 'dakinsa tayi sbd baya bakin gate din.
Fitowarsa wanka kenan yana daure da towel a quguns,
A fusace tayi kansa da jefo masa waya tana fafin I will teach u a very gud lesson today,
Hannu ta 'daga zatakai masa duka ya damqe duka hannuwanta biyu tareda matseta a bango yayi mata runfa........
M & Z
[3/4, 14:04] βͺ+234 818 350 7088β¬: ππ *AUREN RABA GARDAMA* ππ
Na
Mamuh geeeπ
&
Zinnie smart
71~75
Jikintane yadau rawa sbd haduwar jikinsu gashi yaseer din bashida kaya itakuma basu kayan arziqine ajikintaba.
Shikuma kallonta yake cikin kyama yace,
Ki tattaro hankali da juriya kisawa empty brain dinki sbd am going to make your life a living hell,
I will become ur worst nightmare.
Cikin tsananin mamaki ta kallesa sbd abinda yafada ya bata mamaki sosai.
Ya akayi yake iya wannan turancin na qwararrun turawa.
Wurgi yayi da ita yana cewa,
Get out foolish girl.
Baqin ciki ya danne mata zuciya Allah ya isa tace da qarfi tareda miqewa ta fice a fusace.
Kaida kawo tahauyi a dakinta tana tunanin irin cin mutuncin dazatayi masa dazaisa ya gudu da kansa yabar gidan.
2 days Ltr
Zaune take a kan dinning tana qoqarin kai pancake bakinta dad yace,
Lailah meye saqonki gurin mum dinki yau zantafi Kaduna acan zanhau flight zuwa Lagos gobe na wuce can.
Saurin aje spoon din tayi tace,
Dad pls zani.,
No my girl bakisan yanxu kingirma ba,
Kinzama matar aure.
6ata fuska tayi tace,
Dad ni kadaina fada.
Murmushin manya yayi yace,
Lailan dady learn to be a gud wife and daughter,
Sake kwa6e fuska tayi
Dad din ya shafa kanta yace,
Just give it a try my girl,
Trust me you'll experience sumtin new in life.
Safiya ce tazo cikin ladabi tace,
Alh ga yaseer nan dakace akira.
Ok kice yashigo.
Cikin nutsuwa yashigo palon tuni qamshinsa yacika palon,abinda yakeba kowa mamaki da yaseer din shine fitinannan qamshinsa da Kwarjininsa.
Dauke kai tayi tana 6ata fuska.
Shikuwa gaida dady yayi cikin girmamawa.
Lpia kalau yaseer,
Bismillah zauna muyi breakfast.
Ba musu yaja kujera cikin wayewa ya zauna tareda gaida Anty basma.
Cikin salon yaudara yace,
Lailah kintashi lpia?
Sosai ita kanta tayi mamaki sbd tafi kowa sanin girman kansa duk da yana maigadi.
Murmushin jin dadi dady ya yana cewa,
Lailah kece yakamata ki gaidasa bashi yakamata ya gaidakiba.
Toh. Kawai tace tana turo baki.
Coffee ya kur6a yana wani irin murmushin qeta.
Sbd yasan duk wannan iskancin takusa dainasa.
Dady dan Allah kaje dani naganosu mum dasu afra nayi missing dinsu sosai kuma banaso tasan da wani zancen aure sbd ranta zai 6aci.
Miqewa dad yayi yana cewa,
Baxaki ko inaba sbd yawo baikacekiba yanxu
Kaikuma yaseer mutafi ko.
Kallon Anty basma tayi alamar tambaya.
Antyn tayi saurin cewa,
Yes tareda yaseer zashi Lagos sbd yanaso yafara koya masa business.
Dan qaramin tsaki taja kafin ta miqe tayi hanyar hayewa stairs tana cewa,
Nidai dady bara na shiryo kobaka tafi dani America ba saiku barni Kaduna nayiwa hajiya babba kwana biyu.
Kallon yaseer dady yayi zaiyi magana
Yaseer yayi saurin cewa,
Ba komai zata iya zuwa idan nadawo daga Lagos saina biya nataho da ita.
To shikenan tunda ka amince.
Motar dady suka tafi da ita Kuma yaseer ne ke tuqin
Lailah na gefensa dady na baya.
Suna isa Kaduna kai tsaye gidan haj babba suka nufa.
Suna pakawa maigadi yataso da sauri yana musu barka da zuwa kafin yasanar dasu yau dinnan hajiya babba tayi tafiya gidan bakowa arufe yake.
Shiru dady yayi kafin yace,
Lailah kinga rashin jinki abinda yaja tunda dakinyi zamanki dashikenan gashi yanxu bamusan yazamuyi dakeba kuma lokacin tashin flight dinmu yakusa.
Yi hakuri dady bansan bazamu sameta bane.,amma ai ba matsala muje airport din Ku wuce zan iya kai kaina abuja tunda ba dare neba.