Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕 Na MAMUH GEEE🌕 And ZINNIE SMART 1~5 BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM. Motocine guda uku qirar c class 217 baqaqe suna sheqi ke tafiya akan titin airport road bayan sun dauko gimbiyar familyn nasu gaba daya. LAILAH ALI MODIBBO shine cikakken sunanta, Shekara goma kenan rabonta da qasarta Nigeria tana zaune a starling city dake qasar america tareda mum dinta. Mum dinta ba ita ta haifetaba qanwar mamantace data rasu tun tanada qananun shekaru, Zamanta acan yasamo asaline bayan mahaifiyarta ta rasu tun tanada shekara takwas, Mahaifinta justice aliyu modibo yana tsananin qaunarta sbd itakadai matarsa tabar masa, Hakama kakanta alhaji muhd modibo yana tsananin qaunarta fiyeda sauran jikokinsa sbd tsananin qaunar dayakewa mahaifiyarta kafin tarasu., Yayun mahaifanta biyu alh nasir modibo da alh abdulkarim modibo tareda matayensu suna qaunarta sosai sbd tarin dukiyar da mahaifinta yakeda ita. WANNEN KENAN. ******************** Alh muhd modibo shine kakansu yayansa uku rak a duniya,,alh Nasir modibo shine babba yanada 'Yaya uku JABEER,SIYAMA,AYSHAT., sai alh Abdulkarim shikuma yanada 'Yaya biyu ZUBAIR,HAYAT. sai justice aliyu modibo shine qarami shikuma yanada 'ya daya tak LAILAH. gabaki daya iyalan a guri daya suke zaune domin kuwa gidajensu a Jere suke cikin gate daya. *********** Bakin wani katafaren gate motocin suka tsaya motar farko tayi horn har so biyu amma shiru ba a bude gata dinba. Tunda aka daukota daga airport waya take da mum dinta data bari can america datse kiran tayi tana kallon gate din gidan cikeda mamakin yanda ake horn amma maigadin gidan kamar baisan aikinsaba. Siririn tsaki taja tana yamutsa fuska sbd ta tsyay useless and lazy people. Daddynta dake gefenta zaune yana waya ya datse kiran sbd ganin tana yamutsa fuska yakumasan halin yarsa sarai tunda duk bayan wata uku sai ya ziyarcesu acan America. Gyara murya yayi kafin yace, Nuhu kafita ka duba ko YASEER maigadi baya kusa dan na tabbata bata barin gurin aikinsa ba dali.... Bai qarasaba aka wangame gate din gidan. A yangance ta dago kai zuwa ga maigadin amma ga mamakinta saita ga abinda yayi masifar 6ata ranta sbd tsanin kyawu data gani agun maigadin domin kuwa fatarsa had wani sheqi take sbd haske da kyau. Tsaki takuma ja tana dauke kai har suka isa parking space direba yayi parking dinsu. M & 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕 Na MAMUH GEEE🌕 And ZINNIE SMART 6~10 BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM. Dukkanin iyalan gidan sun murna da dawowarta hardai 'yan matan gidan wato siyama da ayshat wainda ke ganin sun samu abokiyar fasowa agari. A part din daddynta ta sauka sbd yayi aure tun da dadewa, Dakinta a can upstairs yake tun kafin tabar qasar. Wanka tayi tareda yin sallah Tana cikin saka Riga siyama tashigo dakin daukeda babban tray. Kallon siyama tayi takuma kalli tray din hannunta dake shaqeda kalolin abinci kafin ta zauna akan dressing chair tana cewa, Am not hungry fa,amma zaki iya ajewa a kitchen idan zanci sai amun worming nasa. Tareda siyama suka sauko palon tana lure da matar daddynta amma tayi kaman bata gantaba ta fice palon sbd daddynta yana part din alh tsoho wato mahaifinsu sbd mahaifiyarsu ta jima da rasuwa itama. Sashen ta nufa kaitsaye tana yamutsa fuska sbd iskan dake kadawa baya mata dadi zafinsa takeji a fatarta. Daidai shiga qofar tayi karo da mutum sakamakon wayarta datake kallo a hannunta. A yamutse ta dago ta kallesa Idan bata manta ba wannan shine Yaya zubair. Kallonta yake yana murmushi sbd yanda take kallonsa batasan mai zatace. Just say sorry broda zubair. Dariya tayi ahankali sbd yanda zacen nasa yabata daria. Shima daria yayi tareda cewa sorry little sis koda akaje daukoki ina gurin wani urgent work daya taso a office. Its alright. Tace tana qoqarin rabasa ta wuce. Hartakai qofar shiga ya dan daga murya cikin sigar wasa yace, Kidaina sauri akan zaki gurin tsoho sbd tuni yace ya yafe dan haka kixo gani sabon jini. Cak ta tsaya tareda juyowa ta kallesa kafin ta saki murmushi ahankali tana girgiza kai dan Zancen nasa yabata dariya. Da sallama tashiga palon fuskarta daukeda farin cikin ganin kakan nata ga kuma sauran murmushin zancen Yaya zubair. Kusada tsohon ta zauna tana gaidasa cikin shagwaba Cikeda farin ciki yake amsa mata yana qara tambayar yanda tabaro mum dinta. Daddynta ya kalleta cikeda qauna yace, Lailah bakiga yayanki a zaunebane ki gaidasa mana. Sam ita bata Masan da akwai wani a palon ba saida daddy yafada. A lalace ta dago kai tadan kalli gefen tace, Sannu ko. Ga mamakinta saitaji ya amsa sbd iya saninta tun tana yarinya Yaya jabeer baya sakewa dasu bare gaisuwar rainin hankalin datayi masa. Miqewa tayi tace, Daddy bara naje mugaisa dasu umma dan haryanxu ban hadu dasuba. OK lailah. Tsoho saina dawo fira ko. Wace fira nidai na yafe saikiyi gaggawar fidda mijinki saikiyi firar dashi. Murmushi tayi tana ficewa daga palondan batada amsar basa sbd zancen aure ko wani fiddo miji baya cikin agendarta Sam Sam. A bangarensu umman siyama tafara sauka Sai rawar jiki umman take tana nan nan da ita sabanin ita da duk a qagare take data koma sashensu. A bangaren ummansu zubair ma hakane hardai data lura kamar zubair dinta ya qyaso lailah. Wani murmushin dadi tasaki tana hangosu idan har zubair dinta ya auri lailah. ************* Karfe goma na safe agogon dakinta ya nuna badan tasoba ta tashi ta fada toilet tayo wanka. Armless gown tasaka blue tareda yane kanta da black vail qarami bayan ta tufke gashinta. A nutse tasauko stairs din tana waya da mum dinta cikeda shagwaba. A dining ta tarar da daddy tareda matarsa Anty basma. Gud morning dad, Morning dear. Ya kewan mominki da kika baro? Dad ina missing mum dasu afra sosai inaji kaman nayi shekara bana taredasu but ganin ina kusa dakai ya yaye 90% of my worries. Batareda ta kalli Anty basma dake sarving dad ba tace, Gud morning. Cikin sakin fuska tace, Lailah ki saki jiki dani am also ur mum so feel free wit me. Suna gama breakfast din ta mike tareda ficewa zuwa sashen tsoho. Ahanya ta hadu da siyama zata taho gurinta A ya mutse take amsa maganar siyama din har suka isa sashen tsoho. Suna shiga zubair na qoqarin fitowa ya tsaya suka gaisa yana tsokanarta Yauma da murmushin suka rabu dan kuwa zubair yafara zama mutuminta. Fira take da tsohon cikin sakewa da shagwaba suna daria Wanda hakan ba qaramin mamaki yakeba siyama ba sbd iya saninsu tsoho baya wasa da jikokinsa kaf, Kullum fuskarnan a tamke umarni yafi iya bayarwa akansu da iyayensu. Mutum 'daya tsoho yake sakewa fuska sosai harda dariya Yakuma yi wasa dashi shine YASEER maigadi. Saikuma yau dataga yanayi da LAILAH. Sallamarsa ce ta dakatar da dariyarsu Tsoho da Kansa ya amsa sallamarsa fuska asake yana cewa, Yaseet ka qaraso mana. A nutse y qaraso ya gaida tsoho cikeda biyayya. Lpia klau yaseer ya aikinka? Lpia klau dama jiya bansamu shigowa na gaidakaba. Bakomai yaseer ngd Allah yayi maka albarka yabaka iyali nagari. Jikata lailah dake qasar turawa ce tadawo a jiyan,kallon lailah yayi yace, Lailah ki gaidasa shima kaman yayankine. Turo baki tayi fuska a kwabe dan dama yana shigowa ta daure fuska bare dataga ko kallo basu isheshiba Danko gefen dasuke bai kallaba. Kai tsaye tace, Sannu ko. Bai kalli gefen datake ba yace, Yawwa barka da dawowa. Mikewa yayi ya fice daga palon bayan yayiwa tsoho a yini lpia. Tsabar haushi har wasu hawaye taji suna taruwa a idanunta sbd yanda yayi kamar sune masu gadin shine mai gidan. Mikewa tayi tafice daga sashen. ******************* Mum pls ki kwantar da hankalinki there's nothing to b worried abt sbd aikin nan nawa yana qara buqatan time. And mum I promise to come bck Dana gama hada information akan case din nan. OK yaseer bt pls daka samu time kazo ka ganni saika koma. No mum banada time din dazanzo har Miami naganki amm.... Ok to ni xanxo naganka. No mum. Mum pls nace kiyi hkr time Kadan yarage,. Shikenan yaseer ka kula da kanka. I will mum, kema ki kula okey? Kashe wayar yayi gaba daya tareda mayar da ita cikin kayansa ya boye kafin yafuto Yakoma bakin gate gurin aikinsa ya zauna yana tunanin mum dinsa danyasan yanda take matukar sonsa dole tayi kewarsa wata hudu baya tareda ita. M & 🌕🌕AUREN RABA GARDAMA🌕🌕 Na MAMUH GEE🌕 And ZINNIE SMART👌 11~15 BISMILLAHI'RAHMANIRRAHEEM. Zaune take a falon part d'insu hannunta ri'ke da wayarta 'kirar IPhone 7+ sai faman danne danne takeyi Wanda kallo d'aya zaka mata kafahimci, Chart takeyi sabida yanayin yadda take doka murmushi, Da sallamarsa yashigo had'i dafad'in, Hy my sister, Hy Tafad'a a ta'kaice ba tareda ta d'agoba Zaunawa yayi a kusa da ita yana mai 'karewa kyakyawar fuskarta kallo Gosh yafad'a 'Dago da kanta tayi a hankali, Any prb tafad'a tana kallonsa, Murmushi yayi,nohp,sister nikam bakibani labarin,America ba, Murmushin gefen le'be tayi tace ai inace kaje American nan yafi sau d'aya, So what are u asking then? To ai ni zuwa nake indawo well kekuma zama kikai acan har na wasu shekaru, Mi'kewa tayi tana d'an murmushi, I have alot to do so byee , Hayewa tayi up stairs d'in Kallo yabi ta dashi mai cike da ma'anoni sai'kudurta abubuwa yake akan, Dariya yayi had'i da fad'in koma meye dai ina sonki LAILAH....... ************* Sanye take cikin riga da sikert yn kanti wanda sukayimata matu'kar kyau, Kasancewarta fara kalar kayan kuwa Maroon Sai tayi wani irin kyau, fitowa part d'insu take 'ko'karin yi, Suka had'u d Siyama itakuma zata shigo, Sis Sai ina haka, kamar bata so tace inaso ne infita inga yanayin garin daganan ind'anje shopping, Bata fuska tayi had'i da fad'in shine ko kinemeni inrakaki, Well koyanzun baibaci ba zaki iya d'auko mayafinki mutafi, Da sauri tafara tafiya zuwa d'aukar mayafin dakatar da ita tayi, ta hanyar kiran sunanta, Siyama, make sure ba kiyi lattin fitowaba, Cox idan kika dade to fa baza kisameni ba, Gyad'a kai Siyama tayi dn tasaba da halin yr mulkin tasu, Zubair ne yazo fita yaganta a tsaye fitowa yayi dgacikin motarsa yace a a Sister Sai ina haka, d'ago da kanta tayi a ta'kaice tace shopping, To waye zai kaiki? Driver, To why not kizomuje ni inkaiki tunda kinga dama fita zanyi, no Kabarshi kawai, Haba dai sister guda zata fita inkasa kaita please kizo muje, Mamakinsa ne yakamata ganin yadda yake ro'konta yakai ta unguwa, Kawar da tunanin tayi tace OK to bara Siyama tafito........ Bata 'karasa ba saiga siyamar tafito, Park yakaisu suka sha ice cream, Sai faman janta wasa yake a 'kokarinsa nason cusa kansa, Sunje shopping mall tayi siyayya itama siyam tad'au abunda takeso, duk zubair ne yayita biya, Basu dawo gida ba Sai guraren magrib, dan haka nema bai shiga dasu ba, ya ajesu a bakin gate, Dan yanaso yatsaya masallaci, Siyama ce ta kwaso musu kayan , Itakuwa wata yr leda kawai tari'ko wacce chocolate ce acikinta, Tura 'karamar 'kofar gate d'in tayi kanta a 'kasa, Daidai lokacin zaifita zuwa masallaci, yana gyara hannun rigarsa da ya nad'e dazaiyi al'wala, Aikuwa karo sukayi wanda yasa ta kusa fad'uwa sabida takalmanta, da suka lan'kwashe, Baya tayi zata fad'i da azama ya kamota madadin ta fad'i Sai tafad'a a hannunsa, Idanuwanta a rufe dn tad'auka tafad'i jin ta jingina da abune yasa tabud'e idonta, Ganin mutumin da takejin haushinsa tun ranarda tadawo ne yasa tayi saurin bari hannunsa, Had'i da nunasa da d'an yatsa, Kai baka da hankaline zaka fito baka sanin inda kake saka 'kafarka tsabar dabbanci, Mts next time kasake bari mukayi,kwatankwacin wannan had'uwar, Saida takad'a yn yatsunta sukai 'kara tace Sai nayi sanadin barinka gidannan, U trashed A zafafe tawuce cikin gidan,ko ledarta bata tsaya d'auka ba Sai Siyama ce tad'auka, wacce duk abunda yafaru gaban idonta, Tunda tafara magana yake kallonta yana mamakin yadda ta ta'kar 'kare tana masa rashin kunya, Kayi ha'kuri yaseer... Maganar Siyama ce ta dawo dashi daga tunanin d yake, girgiza kai kawai yayi yafita, Jin anyi ruku'i M& M&Z [18/01, 22:53] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕AUREN RABA GARDAMA🌕🌕 Na MAMUH GEE🌕 And ZINNIE SMART👌 _Bismillahi'rahmanirraheem_ 16~20 Tana shiga d'aki tashiga cire kayanta, towel tad'auka had'i da fad'awa bathroom, Dan acewarta yau dole ta dirji jikinta kodan wannan matsiyacin da yatabata, Al'wala tad'auro bayan tayi wankan, tana fitowa ta janyo wata doguwar Riga tasaka, sannan ta shimfid'a prayer Mart ta kabbarta sallah, Bayan ta sallame tayi azkar d'inta, Saime kawai hoton abunda yafaru d'azunne yari'ka dawo mata, Wani irin haushinsa d tsanarsa taji, mts tasaki tsaki dn bata son take tunanin useless man d'innan kamar yadda tarad'a masa suna, Wayarta ce tayi 'kara dubawa tayi dn taga waye mai kiran, New number tagani,tsaki takoma ja dn ita ba kasafai take son kira da new number ba, Cigaba akayi da kira saida takusa katsewa sannan tad'auka had'i da cewa, Hello who is on the line, Sister taji anfad'a Wanda koba a fad'amata ba tasan shine dn muryarsa da taji, A ranta tace nifa bnka number naba dnka ri'ka disturbing d'ina ba............. Maganarsace takatseta Hello ar u there Inaji tafad'a a ta'kaice Am sorry sister natakuraki ko?am really sorry, please, Dama kira nayi inmiki ya gajiyar fita dn nasan 'kanwar tawa yr hutu ce, Yadda yayi maganar da zolaya yasa tasaki yr siririyar dariya,had'i da fad'in haba dai yayah zubair, Ai banyi fitar da zangaji ba d'an zoo road d'in da mukaje?? Ke sister kifad'i gskya kedai kind'an gaji badai da yawa bako?? Dariya tasaki sossai, Haka sukaci gaba da fira sai janta da surutu yake, A nufinsa na 'ko'karin cusa kansa gurinta tayadda yakeso tasaki jiki dashi, Koda yatashi bayyna manufarsa bazai sha wahala ba dn shikam sonta yariga da yayi nisa tayyada bayajin kira, ************* Haka kuwa akayi wata irin sha'kuwa ta shiga tsakanin zubair da LAILAH a inda zubair yake ganin cewa tuni laila ma ta kamu da cutar da yakamu da ita tunda dad'ewa, Dan haka shi agurinshi time kawai yake jira yabayyanamata cewa yana sonta Wanda a ganinsa, itama shi take jira, Wanda,a 'bangaren laila kwata kwata batamasan wainar da yake toyawa ba, Dan ita duk abunda ke gudana a tsakaninsu tana kallonsa ne amatsayin yan uwantaka, Kuma da kowani d'an uwanta zata iya haka shima dalilin da tasa sha'kuwar tafi yawa sabida yana yawan kulawa da ita wanda ba yayiwa yn uwansa, Sai ta d'auki hakan akan Allah ne yahad'a jininsu, WANNAN KENAN ************ Yau takama juma'a rana ce da TSOHO yaware domin ganawa da iyalansa baki d'aya, Bayan ansauko juma'a ne kowwa yanufi sashin tsoho dn sunsan da zaman wannan 'ka'idar, Kowwa ya hallara mata gurin zamansu daban haka mazan kuma acikin wannan babban falon nasa, Ake kan kawo abinci da drink's kala2 kowwa yaci ya 'koshi mai abun fad'a yafad'a ko shawara ko 'korafi kodai wata damuwa, To yauma hakan takasance bayan anci abinci an'koshi,tsoho ne yabude guri d addu'a, Sannan yayi musu nasiha kamar yadda yasaba, Nan yabada dama d'aya bayan d'aya kowwa yafad'i abunda ke ransa, Bayan angamane yace to, Saura yn mazan yayanku da ynmata dan haka ina so kowwa acikinku yafito da matar aure, Kuma haka yanuna bangaren da su Laila suke yace duk aurar daku za'ayi, Nagaji da ganinku kunzama tuzurai tunba mazan ba, Dariya zubair yayi yace tsoho kwantar da hankalinka nikam nasamu mata saidai ko jabeer, yafad'a yanawa jabeer d'in dariya, Amma ni dama lokaci nake jira amma mata kam ai tanann nasamu, Ya'karasa zancen nasa yana kallon Laila wacce akayi sa'a itanma shi takallah, Wani kallo taga yasakarmata wanda takasa tantance na meye ??kuma ma me hakan ke nufi?? Kai itafa takasa gane kan yaya zubair kwanann wasu irin abubuwa yakemata dayake d'aure kanta to me yake nufi??? Tunanin tane ya tsaya lokacin dataji jabeer nafad'in to ai nima nasamu mata jira nake musasanta kan infad'a, Dariya tsoho yasaki da iyayensu kowa dariya yayi,tsoho yace, Ja'iran yara d [3/4, 14:04] ‪+234 818 350 7088‬: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕 Na MAMUH GEEE🌕 And ZINNIE SMART 21~25 BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM. Wani irin iska ake kadawa mai dadi Wanda yake hankado labulen windon dakinta yana dukan fuskarta dake kwance kan lallausan pillow dinta. Jan numfashi tayi a hankali sbd yanayin ya tuna mata da America sosai Hardai idan tana tareda mate dinta salman Wanda suka rabu suna tsaka dajin dadinsu,, Mikewa tayi ahankali tazo bakin qaton window din ta tsaya tareda lumshe idanunta iskan na saukar mata ahankali. I really missed you my salman, Da nasan maganan aure za'ayimin daban yarda ko kadan nadawoba sbd am not ready for it., And I promised you Dana dawo zan cigaba da karatu na anan but I don't know wat came over me... I dnt knw if I can do this without you but I promise I will try. Tsaye yake bakin window din dakinsa na bakin gate din gidan yana waya. Ahankali ta bude idanunta dake lumshe sbd wani irin sanyi dake shigarta sakamakon lovely voice din datake jiyowa tana watsa american English a nutse.,dadi da qari kuma kamar muryan salman dinta. Alokaci daya idanunwansu suka sauka akan juna, Ba qaramin mamaki tayiba data ga shine maiyin wannan turanci Wanda zatace yadama ya shanye. Dauke kansa yayi tareda janyewa daga jikin windon sbd yanayi kayan dake jikinta dan kuwa handless vest ce ajikinta da gajeran wando. Numfashi tasauke ahankali tareda jingina jikin window sakamakon mutuwa da jikinta yayi.. She just don't know why but sumtin is telling her that sumtin is not right. Wayarta ta daga ta danna kiran salman ko zataji daidai. ***************** Fira take da daddynta akan zataje Kaduna gurin kakarta ta gurin mamanta saiga jabeer yashigo palon da sallama. Dad da Anty basma ne kadai suka amsa ita kuwa dauke kai tayi sbd Sam bata wani shiri da jabeer din dan girman kansa. Daddy dama Kaduna zani nadawo gobe shine nace bara naxo nayi muku bankwana. Alhmdulillh kaga kuwa saika tafi da lailah dan yanzuma muke maganar tanaso taje Kaduna gurin hajiya babba. Kaje da ita goben idan kagama aikinka saika biya ka daukota kudawo ko. To. Yace yana kallon gefen datake zaune. Badan tasoba ta miqe ta shiryo. A hanya tayi mamaki sosai na yanda ya taqarqare yaringa janta da fira. Sama sama take amsa masa harsuka isa Kaduna. Da gudunta ta fada jikin tsohuwar tana dariya Itama dariyar take dan kuwa ba qaramin farinciki tayiba da ganin jikar tata. Tareda jabeer sukaci abinci dare agidan dan bai bar gidanba sai dare sosai bayan sunsha fira da tsohuwa. Washe gari sai yamma suka baro Kaduna ana kiran magriba suka iso abuja. Salloli tayi bayan tayi wanka kai tsaye bangaren tsoho ta nufa Zaune suke su biyu kadai apalon kan babbar darduma dake shimfide a palon sunacin abinci. Ruwan black tea yake kurba ahankali cikin kwarewa da iya shansu dan har wani lumshe ido yakeyi. Maida kallonta tayi ga tsoho taga shi fruit yake ci ahankali. Siririn tsaki taja Wanda yasa suka lura da shigowarta amma duk da hakashi bai dagoba sbd wani iron masifaffen miskilanci dake cinsa. Alh tsoho hidima kake haka abun ko gayyata. Azumi nakeyi duk ranar litinin hakama yaseer shiyasa duk ranar nake gayyatarsa musha ruwa tare. Ok, tace tana yamutsa fuska dan tuni ta fasa zama ta juyawarta. ********* Yau tacika wata biyu da dawowa kuma yau ne zata fara zuwa school sbd qarasa karatunta na degree da bata qarasaba acan. Ado taci na musamman sai zuba qamshi take Hanbag da wayarta ta dauka ta sauko Palo. A dining ta Tatar dasu dad dinta tuni taja kujera tazauna tana cewa, Gud morning papa. Lailan dady kin tashi lpia? Lpia klau dad. OK my girl kinga yau zaki fara zuwa school so be very careful sbd nan da america is not dsame so be smart and intelligence. Don't worry dad I can handle it. Kallon Anty basma tayi tace, Ina kwana Anty. Lpia klau yar daddy nima INA Jan kunnenki daki lura sosai a school din. OK, tace tana mikewa cikin sbd tafara latti. Key dad ya miko mata Da sauri ta karba cikin murna tace, I love you dad and thank u so much. OK I love u too sbdlittle girl now hurry don't b late and pls tek care. Bangarensu zubair tafara zuwa ta gaida umma da baba kafin ta wuce sashensu siyama nanma ta gaidasu momy da Abba kafin suka fito da siyama dan itama siyama can jami"ar take karatu tuni danma tana gab da gamawa. Tare sukaje shashen tsoho a can suka hadu da zubair suka tsaya shiririta Haryasa suka qara latti. Tana shiga motarta tafara danna horn sbd tun wuri ya bude mata gate din dan. Da wani irin gudu ta fita sbd ganin gayen kawai bata mata rai yakeyi sbd ta tsani yanda yake common maigadi amma yanda wani irin kyawu da wata irin izza. RUBBISH tace tana qarawa motar gudu. M & Z [3/4, 14:04] ‪+234 818 350 7088‬: 🌕🌕 AUREN RABA

Chapter 1 of 7