ka'ajiyeni anan cefane aka aikeni nayo ''
'Cefane yamai maita cikin wani sabon mamaki 'kyadamasa kai tayi alamar eh
'Agidan ba'a san bakida lafiya bane'
Shiru tayi danbatasan mezatace masaba ganin hakan yasa yayi parking ɗin motar yamayarda hankalin sa kanta Maryam!
Yakirata cikin sanyin murya tace ansamasada
''Na'am'' bawandake yin aikenne saike? ''Eh '' ta amsa masa tambayar cikeda ƙosawa shiru yayi naɗan wani lokaci yajuya akalar motar zuwa kasuwar habu bene wata sassayar ajiyar zuciya tasauke batare data kalleshiba tace
''Nagode, Allah yasakamaka da mafificin alkairi, yabiyamaka buƙatun kana allkairi yasakagama da duniya lafiya''
Sosai yaji daɗin waɗanan addu'oin nannata ammakuma yayi mamakin yadda tajidaɗi ganin yakama hanyar kasuwa
Parking yayi sannan yadubeta yace 'dame dame zakisaya '' kifi kilo ɗaya, madara ma kilo ɗaya''
Jintayishiru yasa yace shikenan kyaɗa masa kai tayi alamar ''eh''.
F🌹A🌹K Batool Kamba
More comments more typing
{🖤Batool kamba 🖤}. ALKA LAMI YAFI TAKOBI 🗡️
https://chat.whatsapp.com/Gn6wOkxz4N6KBN3JbMkPiZ?mode=ems_copy_c
💋*SON KI NE ƘADDARA TA*💋
{🌹 Your love is my destiny 🌹}
STORRY & WRITING
BY
FATIMA ABDULLAHI
{Batool Kamba}
Dedicated to my lovely mom ALLAH yaƙara tsawonrai da rayuwa mai albarka
* 1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣
___________________________✍️wai papane dakansa yakoreta, tome tayi masa hartakusa shiga ɗakin mamma tace hijab kawai zaki ɗauko
Batareda ta amsaba tashige ɗakin wani kukane yasake kufcemata
Kukane irin wandake fitowa tun ƙasanrai , kukane maihaɗeda ƙunar zuciya
Kukane mai cinrai,
Kukane narasa mafita,
Kukane na neman dauki awan maha licci,
''Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un! ''
''Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un! ''
Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un''
''Alhamdu lillahi ala khulli halim ''
''Alhamdu lillahi bini imaathihi thathi mussalihun ''
''Alhamdu lillahi wakhhafa ''
''Alhamdu lillah ''
''Alhamdu lilah''
''Aljamdu lilah''
Abinda take nanatawa kenan afili jinzuciyarta take tamkar zatafashe
''Wayyo! Allah nashiga ukuna ni Maryam inazansa kaina Allah yakawomin agaji nibaiwarkace mai tsananin rauni Allah natuba ''
''Astaqfi rullah ''
''Astaqfi rullah''
''Astaqfi rullah wa'atubu ilak''
Jin anfara kwala mata kirane yasa tayi saurin fitowa bayan ta ɗauko hijab ɗin kallon motar papa tayi kasancewar atsakae gidan suke, nufar motar tayi cikin sanyin jiki papa naganinta yayi saurin ɗauke kai durƙusawa tayi agaban papa bayan ta isa wajan cikin murya mai rauni tafara magana
''papa bansan dawacekalma zangodemakaba, bansan dawane harafi zan godemakaba, haƙiƙa kazamomin wani jigo arayuwata , wanda bazan taɓa mantawaba, kazamomin bangon jingina alokacinda narasa majin gina, kazamomin tudun dafawa alokacin da narasa madafa papa Allah yabiyaka bazan gushe dayimaka addu'a ba, zantafi kamar yanda kabuƙata nabarmaka gidanka amma kasa aranka bazan taɓa mantawa dakai ba arayuwa katallafeniii ''
Kasa ƙarasawa tayi saboda wani irin kuka daya tasomata, dasauri tamiƙe tayiwaje mamma takalli matar tace kuɗinfa? Murmushi matar tayi sannantace Hadiza bakida sauƙi akan kuɗi
Kallon bakida hankali mamma tayi mata tace ke awannan zamanin kuɗi ai sune rayuwa malama kibaninkawai
Buɗa jakarta tayi taɗauko damen kuɗi tamiƙawa mamma washe baki tayi kafintakarɓa tanafaɗin yanzun naji zance hajiya sa'ade karki manta ƙasararda nabakifa maitsadace dan Allah kisamomata gurri mai gwaɓi kindaigane taƙarasa maganar tanamai kashe mata ido
Murmushin ƴan duniya hajiya sa'ade tayi, karkisamu damuwa Hadiza wannan yarinya aisai manya kumanasan baƙananun kudi za'a samu akantaba .
Nandai sukayi sallama papa najikuma yana gani amma yakasa cewa ƙala shifa acikin ransa tausayin Maryam yake amma yarasa dalilin dayasa yace tabar masa gidansa shidai yasan bahakane aranshiba , jiyake bakinsa yayimasa nauhi hakanyasa yakasa magana har matar tabar gidan wani abin haushima lokacinda Maryam keyimasa magana yasu yaceda Ita wani abu amma yakasa
Fitarsu daga gidan kaitsaye sukaɗau hanyar barin garin neimey Maryam tatsorata sosai dan itadai bata taba ganin irin wannan tafiyaba gashi kuma ba'itakadai bace sunfi su talatin amotar kuma duk mata bawanda yakulata itama bawanda takula saikuka datake matar dake gaban motarce ta juyo amasifance tafara magana
Ke Malama kiyimana shiru kowaye kikaga yana kuka a nan dazakidami mutane
*MARWAN*
Guduyake shara rawa kantitin garin abuja kaida ganin wannan kasa tuƙin gangancine dubada yanda yake draving baya damuwa dawanda ke kan titin burinsa kawai yakai inda yake so jamil dake gefensa duk atsorace yake Allah ne sheda yayi danasanin biyosa dayayi, yasan waye marwan bai iya fushiba cikin shakkar sayace
''please, marwan come down mana karka kashemu abanza naga ai gaskiya suka faɗa da tana sonka aibazata gudu ajajibirin ɗaurin au.....'' Wani irin birki dayajane yahana jamil ƙarasa maganar
Cikin wani maɗaukakin ɓacinrai yace ''stop Please jamil ''yafaɗi atsawace wandayasa jamil ɗin jan bakinsa yayi shiru
Yashiga bashi haƙuri kosau raronsa marwan baiyiba yafita daga motar yana huci Allah mayasa lokacinda zai jabirkin yagan gara gefe da anyi ɓarna, tsaye yayi yama rasa mezai yiwa jamil dasu haroun yahuce
Shima jamil fitowa yayi
''please marwan kafahimta ada inagoyon bayanka kaci gabada son yarin yarnan amma ayanzu nadawo daga rakiyar ka dama ai anfaɗa tsintacciyar mage aibata mage ''
Baikula dayanayin dayashigaba yacigabada cewa
"Marwan sanin kankane bawanda zai ɗauke hotu nanta inhar ba itaba wamaysan inda suke? Kuma aiii''
Wata muguwar shaƙa marwan yakai masa, nan yafara dukansa baji bagani Wani ikon Allah jamil baya ramawa saidai yana ƙoƙarin kare kansa da dukkanin hanna yensa wani mai motane yatsaya ganin abinda ke faruwa nan yafara rabasu dayake shi Jamil baramawa yakeyiba faɗan yayi saurin rabuwa kallon marwan yayi cikin zaro ido da maɗaukakin mamaki yace marwan!
Haba yallaɓai dagir manka meyayi zafi? Ko kallonsa marwan baiyiba yagiftashi yashiga mota A 360 yabar wajen kallonsa mutunan yamayar kan jamil yace yalla ɓai meyahaɗakada yallaɓai baka gudun abinda zaije ya dawo kasan masu kuɗin nan basada mutunci
Barinma wannan shakwa ɓaɓɓen yaro waye bai san shiba? Kab garin abuja dakaceee
''abokinane'' Jamil yakatse shi
Yanafaɗin haka yabar wanjen Allah mayasa ba mutane ke yawan wucewa kan titinba hanyace hara hayaniya
Kaga inazakije tunda shi yawuce loko ESTATE jamil yafaɗa kaitsaye
Muje na saukeka Allah ya ki yaye gaba
Bamusu Jamil yabishi ganin yakama hanyar ganinzasu wuce gidansu yasa yadakatar dashi fita yayi
''Nagode ɗan uwa ''
Jamil yafaɗa haɗida juyawa yashige gida
Marwan tun barinsa wajen yake jinsa wani iri, magan ganun haroun da jamil ke faɗomasa arai
Shifasam bayaganin guduwa my soul ɗinsa tayi yafi yarda da saceta akayi kowani abun badai guduwaba duk cikin kalaman jamil bawanda yayiwa marwan ciyo kamar tsintacciyar mage kenan ma gori yake mata
''No never wallahi my soul bazatayimin hakaba mema zaisa tayimin haka, tana sonafa haba kai bazai yiyuba ''
Shikaɗai yaketa magana tamkar wani zararre harya isa bakin gate ɗin katafa ren gidansu hone ɗaya yayi saiga gate man yazo dasauri yabuɗe
Kaitsaye parking space yanufa ko parking arziƙi baiyiba yafito direct yanufi part ɗin mom
''Mom!
Mom!!
Mom!!''
Yashiga kwalamata kira tamkar zaifasa gidan
Mom dake farlou tamiƙe tanafaɗi lafiya dai? Wani irin rungumeta yayi tare dafashewa da kuka tamkar ƙaramin yaro
Sosai mom hamkalinta yatashi ,zaunardashi tayi sannan tamiƙe taɗauko masa ruwa maisanyi a freg saidayasha sosai
Yafara magana ''mom wai dagaske my soul batasona shiyasa tagudu, mom dagaskene dan Allah kiga yamin? Yanamagana hawaye na tsiyaya a idanunsa
Daman tatsuniyar gizo ai bata wuce ƙoƙi sosai ran mom yaɓaci
Kaga banason wannan tayar da hankalin dayake
A'a bagaskiya bane kamanta dawacece my soul ɗinkane? Yazakayimin wannan tambayar Please ka kwantar da hanka lin ka kaji
Shiru yayi yana sauke zazzafar ajiyar zuciya
Miƙewa yayi yanufi part ɗinsa kaitsaye haban wadrop yanufa yaɗauko wani allon zane wani irin zaro idanu yayi waje 👁️👁️ cikin tsananin tsoro yajefarda allon yana ja da baya tamkar wanda yaga mala'ikan zare masa rai
Too masukaratu aganinku me marwan yagani dahar yabashi tsoro haka?
Amsarku nanan a page 14 & 15
Inhar banga ruwa comments ba sainan da One monch zakusa ke gani post inkuwa kun shirya nima ashirye nake
SON KI NE ƘADDARA TA
🌹your love is my destiny🌹
STORRY & WRITING
BY
FATIMA ABDULLAHI
{Batool Kamba}
Wannan shafi sadaukar wane ga duk wata marubu ciya dake faɗin duniya ina sonku writters
*1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣
___________________________✍️ma gana yake son yi amma yakasa
''Mom!''
Yakwala wa mom kira afir gice yana mai miƙewa yanufi fita waje yana mai mai ta kiran mom
Tun aharabar gidan yadinga faɗi yana tashi abun mamaki securiti's zuba masa 👁️sukayi dan basu taɓa ganinsa ahakana gashidai bai daɗe dashi ga part ɗin nasaba mom dafe kai tayi ji kiranda yake yimata, lamari marwan nabalain bata mamaki mutum kamar ba namiji ba
Mom! Yasake kiranta lokacin daya shigo part ɗin akiɗime
Lafiya marwan? Ta tambayeshi ganin yanda yake zaro ido kamar tsohon kwarto
''Mom dan Allah wa yashigar min part ɗina daba nanan? ''
Kallon mamaki tayi masa cikin halin ko inkula tace
Wakasan yana shigar maka part ko wayasan password ɗinka?
''Mom dan Allah zo ki gani Please yafaɗa out of control''
Ganin kamar baya hayyacin sa yasa mom binsa , koda suka isa part ɗin bedroom ɗinsa suka nufa kaitsaye gurin allon zazen yakaita ɗagoshi yayi
''mom kinga sauran maganarce tamaƙale saka makon ganin wayam .
Menene?
Kasa maga yayi saboda ɗimauta saida yaɗau dogon lokaci sanan yaja numfashi
"Mom kinsan menazana?
A'a
Mom face ɗin my soul nazana amma natarar yakoma kwaran kwal
Yanzukuma bakomai Please mom meke shirin faruwa ne?
*MARYAM*
Sunyi tafiya takai ta 5 hours suka huta sannan suka cigaba daga nan bazatace ga abinda yasake faruwaba saida ta buɗa ido taga duhu yamutsa fuska tayi ganin suna ƙoƙarin tsayawa yasa duk jikinta yayi sanyi
"Niyanzun inane za'akaini gunsuwa zan zauna Allah kajikaina ka agazamin Allah karkabarni na wulaƙanta aduniya "
Tsawarda aka dakamatace tadawo da ita hayyacin ta
Fito malama kinwani zaunawa mutane amota inajin bakitaɓa shiga motabane
Wasu zafafan hawayene suka wankemata fuska jin irin tsawarda yakemata aka
"Yihaƙuri" tafaɗa cikin muryar kuka
Tsakiyaja kafin yayi gaba abinsa,
Shin yanzun ita menene makomar rayuwar ta
"Ya Allah kajiƙaina "
Wani gida tagani da alama nanne masaukinsu domin sauran yanmatan duk sun shige ragiwar kuma suna ƙoƙarin shiga itama hanyar tanufa.
Gidane da ɗakuna ajere barandace doguwa yawan ɗakunan mayasa bansan adadin suba
A tsakar gidan suka tsaya, wasu ƴan mata kusan su goma wasukoma suka shige ɗakunan da'alama sunsan yanda gidan yake wata matace dafito dagawaniɗaki dake gefe ɗaya, hannunta ɗauke da sigari tana busawa, jan sigarin take irin nakwararru kuma ta tattun ƴan bariki, kallon wula ƙanci tayimusu tareda yatsina baki
Kune baƙi annan dafatar kunsan meyaka woku nibana ɗaukar iskanci dole gobe kufara aiki danbazan baku ɗakuna kushare kuzaunaba .
Cire glas ɗin idanun tatayi tabisu da kallo ɗaya bayan ɗaya idanutane yasauka kan Maryam saida taƙre mata kallontsaf yafito ta da hannu
Cikin ɗari ɗari dajiki tanufi inda matar take sake kallon sauran tayi bangaya muku sunanaba ko?tatambaya cikeda iskanci
Taɓebaki tayi da alama hakan yazame mata ɗabi'a
"Zaku iya kiranada uwar gida ko anty kundai gane ?"
Jinjinakai sukashigayi itadai Maryam duk atsorace take kasan cewar bata sababa. kallon Maryam tasakeyi cikin iskanci tace my love yasunanki?
"Mar r y a m" tafaɗa cikin rarrabewar harshe murmushin ƴan duniya tayi
Dagayau sunanki qutty kinji? Kyadakai tayi alamar Ehm
Nan akashiga bawa kowa ɗakinsa har maryam ɗin ɗakine maiɗaukeda madaidai cin bad, Waldrop sai mirror dakujera two sitter, da bathroom .
bathroom ɗin tashiga taɗauro alwala cike da damuwa tafara sallah.
Harta idar taci gabada tunanin makomaer rayuwarta, taɗau alƙawarin dul wuya bazata sayar da mutuncin taba, danta soma gano wani abu dangane da wannan gida
amma zata bi ahan kali tagani har Allah yasa tasamu hanyar gudu.
Washegari tunda tayi sallar asubahi tarinƙajin hayaniya dataso tayi zamanta saigawata matashiyar yarinya taahigo waitafito waje inji Uwar ganta lalli hijab ɗinta tasanya
tafito ganin gidan yacikada mutane daban daban yasata fara tambayar kanta "wannan wane irin gidane? "
Muryar Uwargida ce taji tafara magana. qutty zonan. Dakar kartaje saikuma tanufeta, matsawa tayi ta zauna cikin ladabi tace "ina kwana " lafiya cewa uwar gifa
Sannan tace da alama ke bakisan wannan inaneba amma zakisani naga kowa ya fahinta kece kawai kikeson bamu problem amma You don't worry qutty zaki gane, yanzun jekiyi wanka natanada miki costomer yananan zuwa zaki tayashi kwana baƙone kisaki jikinki kikwashi rabonki karki kuskura kimai musu komaiyace
Saurin katseta Maryam tayi dacewa "hajiya kiyi haƙuri ban fahimtaba , wani kuma? A ina yasanni nida nazo jiya wana sani, waya sanni dahar zaizo wurina . kuma naji kinazancen costomer nida bana kasu wanci meya haɗani da costomer?"
Sosai wurin akashiga dariyarta ciki kuwa harda waƴan dasukazo jiyan
Kumin shiru cewar uwar gida kinga qutty aiki bata ƙananun mutane bace so karkidami kanki cos kinada abinjan hankalin ɗa namiji karkiyi wasa da damar ki wanna dakike ji nace zanhaɗaki daahi babban mutunne a Nigeria so kiyi amfani da damar ki wajen sa
Kan Maryam yasake kullewa itafa bagane wannnan kurman zance takeba "Please hajiya let me go to the streat point zanfi ganewa " tafaɗa cikin yatsina tana son tabbatar wa dagaake wannan gidain karuwai ne
Cikin ɗanjin haushinta uwar gida tace jeki kiyi wankan zan aiko miki da kaya idan kunje zaki gane nufina ok yamutsa bakitayi kamar tayi magana kuma tafasa
, kamar yanda uwar gida ta, Umar ceta wasu ƴan isan kaya takawo mata taso taƙisakà kayan amma saita tuna karfa tayi ƙoƙarin ja inja da ita takoreta Allah mashaidane wani abu takeji maikama samun freedom, wato ƴanci .
sosai kayan yakarɓi jikinta kasancewarta Black beauty kayan kuma golding colour kamar dan ita akayisu the best colour ɗin ta kenan .
Ridane dawando rigar iya gwuiwa shimadai wandom baikai ƙasaba.
"zuwa yanzu tacire komai daga ranta zatata fuskanci rayuwarta tayanzun.
Motsin mutum taji dasauri tajuya ganin wani tayi atsaye yana mata wani irin kallo data kasa ganesa, tarigada taranfo uwar gida zata yarda tabishi daganan zatasan abinyi..
More ✨comments ✨ more ✨ typing
F🌹A🌹K 🖤BATOOL KAMBA 🖤}forever
SON KI NE ƘADDARA TA
{🌹 Your love is my destiny🌹}
STORRY & WRITING
BY
{🖤 Batool Kamba 🖤}
Wannan littafin kacokan sadaukar wane ga mahaifiyata abar alfaharina
Allah yabani ikon kyau tatamiki ameen
*1️⃣5️⃣ &1️⃣6️⃣*
_______________________________✍️
Ganin baiyi mata sallamaba yasa tacigaba da sabgo ginta,
baƙarya taji haushisa sosai, ƙato dashi bai iya sallamaba.
mtsuu taja tsaki saida yaƙare mata kallo off and down sanna yayi kyaran murya, batakula shiba yazo inda take yazauna dab da ita yazauna ,
matsawa tayi saboda tafara jin tsoro "Allah yasani taso tadaure amma bazata bari wani gardi yataɓamata marta bartaba basadaki.
Tashi tayi takoma ɗayan kujerar dake ɗakin dama bakin katifa tazauna .
juyawarda tayi shiya fallasa asirin manyan hips ɗinta,
Aiko yana tozali dasu yawu yasar ƙeshi yahau tari baƙakƙau tawa, taso tashare saikuma ta ga rashin dacewar hakan
Amma ai baiyimiki sallamaba wata zuciyar tagaya mata hakan yasa tashare ,
Ganin yafita yasa tasake kallon jikinta, bazatace garanar datasanya kaya masu kyauba irin wannan.amma tanaji kamar dama tasaba sanya kalar kayan.
Sake shigowa yayi yazo inda take, baizaunaba sai cewa yayi
"Am dafatar hajiya tayi miki bayani,
"Bayanin me kenan"
Yanda tayi da bakinta yafi komai riki tashi.
Kinada kyau wannan yarinyar Allah yazuba miki kyau,
uwar gida batayi ƙaryaba keɗin tadabance kizo kibini zakiyi mamaki dan zan sakar miki kuɗi,
zan baki duk abinda kikeso aduniyar nan matuƙar zaki yimin abinda nakeso.
Awannan karonma taso shareshi amma takasa azafafe tafara magana "waikai kanada addini kuwa? Murmushin ƴan duniya yayi yace me kika gani?
Nantake zuciyarta takwaɓeta
"Ambakomai zanyi maka yanda kakeso ɗin. "
Yaji daɗin amsarda tabashi hakan yasa yazauna kusada ita yace "kinga yanzun rana tasomayi dan ana neman ƙarfe 11:30 ne kozaki bini muje hotel "
Yaƙarasa maganar yana kanne mata ido ɗaya
Abin dariya mayabawa Maryam "gashida girma kamar buhun masara kumawai soyake na aminta dashi kamar wani mijina,
kutt Allah bazai yiyuba wannan kan ai zan iya mutuwa"
"Kina kallona kobazakije bane
Saurin saita kanta tayi sannan tace
"Bakomai muje "
Tayi maganar cikeda tsoro haryasoma ganewa yace
Kisaki jikinki baby akwai kuɗi
"Shiwai atunanin sa kuɗene nazo nema uhumm , ko zannemi kuɗi bata wanna hanyarba "
duk wannan maganar tanayintane azuciyarta.
Miƙewa tayi tanufi ƙofa, shima bin bayanta yayi suka fita, sosai gidan yasake cika damutane.
"ikon Allah sai kallo "
maryam tafaɗa cikin maɗau kakin mamaki, ganin ƴan daudun dasuke kwasar rawa ana musu liƙi.
Jin ankama hannun tayasa tayi saurin juyowa, karaf suka haɗa ido yayi saurin kauda nasa idanun.
"Kinga kidaina kallona da kwala kwalan ida nunnan naki😃, nitsoro suke bani."
yayi maganar da iya gaskiyarsa.
Sosai wannan karon takasa ɓoye dariyarta saida ta murmusa
Wow kunga wani irin kyau da dariyar tayi mata
Ahankali tacire hannunta daga nasa tayi gaba ƙirjinta nawani irin bugawa narashin sabo tanaso ta ƙarfafa zuciyarta sosai tayanda zata cimma manufarta.
"Allah kajiƙaina kasa wannan shine ƙarshen shiga ta wannan baƙin gidan "
Wata arniyar mota tagani a fake daidai motar tatsaya ,
Saurin ƙarasowa yayi yabuɗemata.
Shigar ta motar yayi daidai da saukar hawaye akuncinta, lokacin dayashiga bailura dahalinda take cikiba yatayarda motar
Baby bangaya miki sunanaba ko,
"Uhumm" kawai tace saboda wani ɗacin rai dake ɗawai niya da ita
"Sunana Alhaji surajo, Amma ana kirana da Alhajin manya danni bakowace mace bace nake kulawa saiwadda tasan kanta acikin mata,kamardai ke ɗinnan ,
Nibaƙone daga Nigeria nake ina zaunene a Abuja nida iyalina.
Yaɗan tsagaita dacewa "kinsan komeyasa nake yimiki wannan bayanin inason inhar zaki amin cemin na aureki
*Abuja Nigeria*
Damisalin 9:20 nadare marwan nezaune a parlourn sa mom na tsaye da alama magana take yimasa
"Nidai Allah yasani bazan iya zuwa koinaba, Please mom kuje kawai inya iso gida ai zan gansako? " cike damamaki mom take kallonsa.
Marwan dady nefa za'a tarba bawaniba, kumakace bazaka je tarbarsaba.
" Mom dan Allah kuje kawai banason haya niya wallahi"
Mom ko aranta cewa take kodai yafara zaucewane bamada masaniya.
Kamar yasan metake faɗi yace
"Nifa dahankalina kawai banajin ƙafafuna zasu iya kaini airport ne".
"Uhumm Allah yashige managaba" kawai mom tace tajuya .
Airport babban farin dattijo maijikar kamala da da Dattaku , cikeda natsuwa yake saukowa daka ma tattakalar jirgin,
tunlokacinda yafara saukowa yake baza idanunsa dangani ta inda zai hango farin cikinsa kuma sah lelensa,
Bamaya takan ƴan jarita dasuke son yin magana dashi, gamamakinsa mom kawai yagani itada securiti's.
"Momyn boy inaɗan naki? ". yafaɗa daidai yaƙaraso inda suke .
Uhumm marwan Sarkin rigima yana gida waibazai iya zuwaba, inaji bayajin daɗinji kinsane.
Afirgice dady yace "what, bayajin daɗi kuma kika barmin shi agida
Haba momyn boy kinsan kalar ciyonsafa sokike natarar yamutu kome "
yafaɗa da ɗanjin zafinta ganin yafara masifa kuma agaban securiti's yasa tashige Mota batare data tamka mishiba.
Shima motar yashiga tareda kallon ta yace
" sorry momyn boy naman ta a inda muke kinsanfa boy shikaɗaine gareni dole na tashi hankalina."
Bakomai kanada gaskiyar ka.
dady baigane wace gaskiyar take nufiba yace yawwa momyn boy .
Tunda suka baro airport yake jin badaɗi yamatsu yaje gida yaga wane hali boy ɗin sa yake ciki
Allah mayasoshi yau duk kwakkwafin yanjarida basu samudamar magana dashiba dan basuma ƙaraso inda yakeba,
hakan yasa ya isa gida da wuri kaitsaye pat ɗin marwan yanufa buɗe ƙofarda dady yayi
Yasa yayi daidai da lokacin da marwan kecewa
"Wallahi nikam nagaji da wannan rayuwa haba my soul, mena miki dakika zaɓi cutarda bawan Allah, wallahi na azabtu fiye da tina ninki , dan Allah kidawo gareni zuciyata daf take da bugawa muddin nakasa samunki arayuwata
sosai yake kuka kamar mace , numfashinsa na ƙoƙarin tsayawa yana fizgarsa jirine yafara ɗibansa aiko yatafi luuu.
Dasauri dady yaƙaraso indayake amma inaa jiri yaɗaukeshi nan yazube yana dafe zuciyarsa
Sosai dady yashiga tashin hankali da ɗimuwa ganin tilon ɗansa naneman rasa rayuwar sa...
Menene ra'ayin ku awannan page?
Anya Maryam zata amince da buƙatar Alhaji surajo nason aurenta kubiyoni a next page danjin yanda zata kayaaaaa
Kunason ganin post duk bayan kwana uku
Kubiyoni a facebook group na maisuna
BATOOL KAMBA NOVEL'S✍️
Taku har kullum
Fatima Abdullahi
Please share
https://chat.whatsapp.com/Gn6wOkxz4N6KBN3JbMkPiZ?mode=ems_copy_c
SON KINE ƘADDARA TA
🌹 Your love is my destiny 🌹
STORRY AND WRITING
BY
F🌹 A 🌹 K Batoool kamba
Dan Allah masoya kumin afuwa page 17&18 tabata nayi nema ban samuba dafatar hakan bazai rage muku kar sashiba
_________________________________________________________________________________________________________✍️
*1️⃣9️⃣& 2️⃣0️⃣*
_________________________________________________________________________________________________________✍️wanan shine sanadin canzawar rayuwar su Khadijah domin doctor sadiq yayi musu gata yabiyawa Sani kuɗi yaje London dansamun karatu mai inganci Khadijah ma tacigaba dazuwa school, Dantana ss2 ne
Matar doctor sadiq hajiya Habiba macece mai karamci dason mutane, tariƙi su Riƙayya tamkar ƴaƴanta tanada ƴaƴa uku Umar shine babba yanada shekaru 28 ya kammala degree ɗin sa da master's a ɓangaren low yanzun haka yana aiki agarin Kano sai Hajara mai shekaru 10 sai ƙaninsu Haruna mai shekaru 7 kasancewar lokacin da ta haifi Umar tasha wahala saida akayimata aki doctor's sun tabbatar bazata sake haihuwa ba saboda tasamu matsala amahaifa,
Saida wani ikon Allah Umar nakai shekara 18 taɗanyi zazzaɓi doctor sadiq na dubata yaga ciki bai gamsuba hakan yasa yayita aunata harso babu adadi ganin dan dagaske cikin ne yasa yafara muurna bayan ta haifi Hajara da shekara Uku saiga cikin Haroun daganan kuma har yau dayakeda shekaru 7 batasake ko ɓatan wataba.
Soyayya ce ta ƙullu tsakanin Umar da Khadijah lokacin da doctor sadiq yaji yayi matuƙar farin ciki bai tsaya wani kace naceba yagayawa Sani, shima yayi farin ciki, doctor yaso yagayawa ƴan uwansu na mahaifi amma Sani yace ai su basada wasu ƴan uwa sai shida mamee ( hajiya Habiba kenan ) ba'a ɗauki dogon lokaci ba aka sanya rana wata ɗanya.
Ƴan uwan malam Muhammad sunyiwa doctor tijara lokacin da sukaji labarin zai aurar wa ɗansa Khadijah batare da izinin suba ,
Maganafa ta girmama dan har kotu saida suka je nan Sani yasha yardasu mamaki , agaban alƙali yace,
"Ni Sani nine waliyin Khadijah domin nine yayanta bamada wasu ƴan uwa sai baba doctor dan haka anan nakeson alƙali yazama shaida nabawa Umar auren Khadijah , kuma anan nakeson aɗaura auren matuƙar shi Umar ashirye yake "
"Kallonsa alƙali yayi yace bakada wannan dama saboda kanada ƙan nen mahaifi "
"Yamai girma mai Shari'a nagayama bamada wasu ƴan uwa "
Cikin ƙunar rai yashiga karantowa alƙali duk abinda aukayimasu yaƙara dacewa "tundaga ranar nayan ke alaƙata dasu yamai Shari'a ayimana adalci so suke su salwan tarmin da rayuwar