Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
“The Day Destiny Screamed” Ai kuwa ganin jinin da ya fito daga kan Talatu yasa kowa ya watse! Gaba ɗaya unguwa ta rikice, yara suka rika ihu, wasu kuma suka hau dariya suna cewa, “Indo fa ta yi nasara yau, ta dawo da martabar Mairo” Amma dai ba wasa ba ne, Talatu ta faɗi ƙasa tana riƙe kai tana ihu,“Innalillahi Indo ta kashe ni! Indo ta kashe ni ooo!” Sai kawai Indo da su Dijee suka kwasa da gudu kamar waɗanda aka ce “an zo da keke-napep ɗin police.” A hanya Indo na ta zagin kanta tana dariya, “Kai Indo! Wallahi yau kika kai! Amma dai gaskiya sanyi ne na Mairo ya tashi min, in dai ina numfashi Talatu sai ta gane da wane take wasa.” Suna zuwa bakin titi suka tsaya, suna haki kamar waɗanda suka tsaya da gudu daga tsere. Indo ta dubi su Dijee, ta ɗan girgiza kai tana kwaɓe baki ta ce: “Kuna ji ku? Wallahi da ba sanyi na ƙawata Mairo bane, da na ce sai na kwance mata ƙeyar rigarta gabaki ɗaya. Amma ai ubangiji ba ya barin mai zalunci taji ko da daɗi kullum sai yawa ƙawata duka!” Dijee ta ce tana dariya, “Kai Indo, ai ke fa ba mutuniyar da za a bi a ce a bar rigima ba, rigima kamar sarkin daka!” Indo ta ce “Hmm, ai ba rigima bace, sai dai kare kai! Kullum fa sai ta dake Mairo, ta zage ta kamar ita ta haife ta. To yau Allah ya bata fansa ta hannuna.” Suka yi shiru na ɗan lokaci, hawaye suka fara zubo wa Indo, ta ce cikin muryar tausayi, “Mairo dai ta tafi... Allah ya kiyaye ta. Amma wallahi zan rama mata komai da komai. Ba zan bari ta je birni ta sha wahala ba. Ko da zan bi ta da ƙafa sai na dawo da ita ..” Haule ta ce, “To amma fa Indo, kin manta da mai unguwa ne? Yau dai idan ya ji labari, zai zo ya same mu!” Indo ta ɗan sake murmushi, ta ɗaga kai cikin izza ta ce: “Mai unguwa fa? To in yazo, in dai ba zai bani abincin da zan ci ba, to sai na ce masa inna ce mai kisa. Ai Talatu ce ta fara ni da sharrinta. Mutum ya hana ni numfashi a gida kamar ba na cikin mutane.” Suka kwashe da dariya, su duka suka zauna a ƙasa bakin titi, rana na shirin faɗuwa, iska na busowa daga ɓangaren da motar ta tafi da Mairo. Indo ta ce cikin sanyi“Ku ji dai, wallahi ni Indo, zan tashi, zan bi ta... idan na samu kuɗin mota, ko ma na gudu da ƙafa, sai na ga inda ta je. Ba zan bar ƙawata ta lalace ba.” Ta ɗaga hannuwa sama kamar mai rantsuwa, ta ce “Allah na... kai dai ka sani, Indo ba muguwar mace bace, kawai mutane ne ke ɓata min suna.” Suka yi dariya da hawaye suka tashi tsaye “ Haule tace " ya kamata yau muje gun Mallam Audu ya bamu mangoro musha ", cikin azama Indo tace gaskiya ne mujeeee " Sun shigo kasuwar Modirre kamar yadda rana ke tashi da annuri — mutane na ta zirga-zirga, hayaniyar saye da sayarwa ta gauraya da ƙamshin kayan miya da turaren ganye. Indo tana gaba da su Dijee da Haule, tana taka kamar sarauniya. “Ku tashi ku biyo ni, yau sai na sha mangoron Mallam Audu da kyauta!” Ta faɗa tana dariya, tana karkar da zani kamar wacce ke hawa titi da sabuwar babbar mota. Dijee ta riƙe baki tana dariya — “To ke dai Indo, wallahi sai na yi tunanin kina da asalin birni. Irin yarenki na nuna haka.” “Ai dama birni ke cikin zuciyata.” Indo ta amsa tana dariya Suna cikin tafiya suka ji karar mutane a can gefe — taruwar jama’a, kamar ana raba kayan tallafi. Haule ta tsaya cak ta ce da tsoro, “Ke Indo, wallahi ina jin tsoro, wannan hayaniya ba kamar yau ba.” “Ke dai Haule sai kace wata shaidaniya, muje mu gani — ni ban da tsoro!” Indo ta faɗa tana jan rigar Dijee. Suka shigo tsakiyar kasuwar, suka tarar mutane sun kewaye wani mutum wanda aka daure da igiya a hannu. Mutumin ya rame, yana ta girgiza kai yana cewa“Wallahi ban sace ba! Wallahi na ga jakar a ƙasa ne kawai!” Mutane suna ta ihu — wasu na dariya, wasu kuma suna tsinewa. " a kama shi! Ɓarawo ne wallahi!” “Na ga shi da idona yana ƙoƙarin kwashe jagar matar nan mai tumatir!”“Ku kira ‘yan sanda kafin ya tsere!” Indo ta zaro ido, ta matsa gaba da sauri tana cewa: “Ku tsaya! Ku tsaya mana! Waye ya tabbatar da satar nan? Ko dai ku kalli fuskar sa ne kawai kuna zargi? kuma baga jakar ba ko akaiw abinda ya ɓata a cikin jakar ” ? tana tambaya matar " a'a bai taɓa komai ba " Mutane suka kalleta suna murmushi — domin Indo dai Indo ce: idan ta shiga rigima, sai ta ƙare da labari Wani dattijo ya ce “Ke yarinya, ki tsaya gefe kafin ki samu duka. Wannan dai ɓarawo ne.” Indo ta ɗaga hannu kamar lauya a gaban kotu: “Wallahi sai an tabbatar min! Ai ko shaidar satar ba’a kawo ba, kun riga kun yanke masa hukunci.” Dijee da Haule suna ta ja mata rigar baya “Indo ki yi shiru, ba lamarin ki bane! Ga mutane nan suna harare ki!” “Ni kuwa sai na faɗi gaskiya,” Indo ta ce tana huci. “Kuna zaluntar marar ƙarfi. Waye ya san ko yunwa ta sa shi? Kunga shi ai ma ba kamar masu sata bane, yana da fuskar mai gaskiya.” sai wani daga cikin masu kallo ya ce “Kai ai wannan ba sata bace, kayan sun faɗi ne daga teburin matar nan.” Nan mutane suka fara shiru, daga baya suka fara murmushi. Wani dattijo ya ce da ƙarfi “To ai kenan ashe babu sata! Kowa ya watse! Ku bar shi yaje a kunce sa yayi tafiyar sa .” Indo ta yi sheshsheƙa da dariya tana cewa: “Na faɗa maku! In dai Indo ta shiga, gaskiya sai ta fito fili!” Mutane suka yi dariya — wasu suna tafa mata hannu, wasu kuma suna kiran ta da “Ɗan Lauya” Ta juya tana tafe da girman kai kamar wacce ta ci shari’a a kotun duniya. “Kuji fa, ni Indo ce — ina kare marasa ƙarfi. Wani ne kuma zai zalunci talaka a gabana?” Dijee da Haule suka tsaya suna ta dariya, suna kallon ikon kwatancin Indo “Wallahi Indo, ke da bakinki sai mutuwa.” Indo ta kalli su tana murmushi da izza: “To ai sai da bakina ake sanin Indo. Bari mu je mu samu mangoro na Mallam Audu, ni dai yau nayi abin kirki.” Suka juya cikin dariya suka nufi shagon Mallam Audu, kasuwar ta cika da hayaniya amma har yanzu ana ta maganar “Indo Barrister” — wacce ta ceci mai laifi daga hukuncin mutane. $$$$$$$$$$$$$ Da yammacin Lahadi rana na sauka da sanyi, Dr. Sadeeq ya fito da kwanciyar hankali daga gida. A yau bai nufi asibiti ba — kawai ya fito kasuwa sayen kayan lambu da fruits domin girkin hutu. Jallabiyarsa ta blue sky ta sheƙa haske kamar sabuwar mota, glass nasa yana sheƙin zinariya, hularsa ta larabawa ta sa shi ya zama kamar ɗan Dubai , .utane na binsa da ido, wasu na cewa "Lallai wannan ɗan bature ne fa!" amma da ya ce "Kai Mallam Audu, ka min sauƙi kan mangoron nan mana!" sai suka gane Bahaushe ne kawai mai tsabta da ɗan ɗan burgu . ( lolz) Amma kash! Indo fa tana cikin kasuwa ita da su Haule da Dijee suna magana da Mallam Audu. Sai kawai idanunta suka sauka a bayan Dr. Sadeeq — charraf! Tayi shiru kamar wacce aka manna remote a baki sai ta ɗaga hannu tana kallon sama ta ce: “Wayyo Allah, idan wannan ba Dr. Balarabe bane, to ai ni ba Indo ba ce! wallahi cikin mutane dubu na gane Balarabe nan, har da glass ɗin nan na ban mamaki!” A take ta fara binsa a guje, tana kiran da ƙarfi: “Kai Balarabe! Dr Balarabe!! Kasan Allah ina binka bashin kaza tuna lokacin da buge ne da motar ka ". Mutane suka tsaya suna kallonta, wasu suka. fara dariya. Dr. Sadeeq kuwa yana jin an kira “Balarabe” sai ya fara sauri yana cewa a ransa “Innalillahi, wai ni da wannan sunan kuma? Indo ce wannan?!” Sai kawai ya ƙara gudu, glass ɗin nasa ya kusa faɗuwa, jallabiya sa tana harɗe sa daga gefe saboda sauri sauri . Indo kuma ta ƙara gudu tana dariya tana huci kamar wanda ya ci dambu da yawa: “Wallahi yau sai na kama ka, kasan Allah bashin nan sai ka biya! sai baci naman kaza har da cinyar ƙafa biyu, ka gudu, yau sai ka biya!” Dr. Sadeeq ya tsaya chak! Ya juyo yana fesar da numfashi yana kallonta da mamaki: “Indo? Ke kike kiran ni Dr Balarabe? Ina ruwana da kazarki?” Indo ta ɗaga hannu cikin nishaɗi ta ce: “To kai ai duka likitoci iri ɗaya ne! Kaza ɗaya dai aka ci fa!” su Dijje suka watse da dariya, Mallam Audu yana riƙe ciki saboda dariya yana cewa: “Indo, wuce ki, kin hanani cin abinci wallahi!” Dr. Sadeeq ya juya yana tafiya cikin gajiya, yana cewa a ransa: “Wannan yarinya idan ta ci gaba da haka, sai na nemi transfer zuwa London.” Indo ta riƙe hannun Dr. Sadeeq da ƙarfi, ta watsar da hannunta a kansa kamar wacce ta gano mazugi. Idon ta na yawo, baki na ci, murya ta ƙara ƙarfi kamar wacce za ta yi kasuwa da zargi: “Are you mad seriously? " yace da alamar fusata " kaine ka buge ne da mota, kaban kaza ɗaya ko dubiya ba ka zo ba, kuma ka kira ni wawiya? Ko ka siya mini kaza da lemo ko na maka tsirara a cikin kasuwar nan!” Dr. Sadeeq ya tsaya cak — da farko ya yi mamaki, ya ɗan yi murmushi, sai ya gane Indo ba ta jin Turanci sosai. Yana so ya yi ta gaggawa ya yi magana cikin English don ya kashe rigimar, amma Indo ta ci gaba da Indo ta lean ɗauranci a ciki: “Don't even talkin' to me again in my life!” Indo ta lean ɗan gaba, baki a faɗi da ƙarfi: A wannan lokaci Dr. Sadeeq ya fahimci cewa a gaske Indo ba ta fahimci duk maganar Turancinsa ba — kuma wannan ya sa shi ɗan sassauta fuskarsa. Ya buɗe aljihunsa, ya cire canji da hannu ɗaya sai ya bada ₦8,000 cikin hanzari, yana cewa a hankali “Take this. Just—please—leave me, and don’t cause trouble.” Indo ta karɓi canjin, idonta na walƙiya kamar ta samu zinariya. Ta ɗan matsa gefen mutane, ta daga hannunta kamar jaruma “Don't ever talk to me again in my life!” ta maimaita — to amma da zuciya a buɗe. “To ko ka’ifaa, Balarabe! Sai ne Indo gata! Ƴar hallak! Allah ya maka albarka Dr. Balarabe har abada — bazan manta da kai ba!” Ta juyo ta durƙusa kamar mai bada waya, idonta cike da ruwan ido: “Kuma idan kana da matsala anan garin, kawai kawo layin mu — kace wacece Indo, za a kawo ka gidan mu, zan tare ma faɗa da kowa , mai unguwa yayan Baba nane!” Wasu mutane a kasuwa sun tsaya cak suna kallon al’amarin, wasu suna fashe da dariya, wasu kuma suna ƙoƙarin rikicewa su rarraba. Wani mutumin gefe ya ce da dariya: Dr. Sadeeq ya ɗan yi shiru, ya ɗaga hannu kamar wanda ya gama shawo kan wani gajiya. Sai ya yi saurin juya, yayin da zuciyarsa ke bugawa: “Headache… and this smell…” — ya furta a ransa, yana tafiya da sauri, yana nemo iska mai tsabta. A kowane mataki, ƙamshin sabulu + dusty village ya ci gaba da shawagi a ƙuruciyarsa — yana sa shi girgiza kai da yin addu’a cikin ransa: “Allah ka jikani.” Indo kuwa ta tsaya a tsakiyar kasuwa, canjin a hannunta, fuska cike da alfahari: “Balarabe! Na mallake ka — wannan ba karamin abu ba ne!” ta yi dariya mai ƙarfi, sai ta juya ta nufi Dijee da Haule, suna rawar murna kamar sun lashe shari’a. A bayan su, Dr. Sadeeq ya nufi mota, zuciyarsa cike da haɗakar gajiya, dariya (a ransa), da ciwon kai. Ya koma gida tare da tunanin cewa wannan rana, Modirre ta ba shi ƙarin labari da ba zai taɓa mantawa ba. To be continued....... https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM 🩺 DR SADEEQ 🩺 by NARNAH KANWAR SOJA ✍️ MY 15th Novel Comedy love drama. 08101235739 CHAPTER 0️⃣9️⃣ *06/ 11/ 2025 “The Day Destiny Screamed” Dr. Sadeeq yana shiga wanka da tawul ɗinsa a waje, ruwan sanyi yana kwarara a jikinsa, yana jin zafi da gajiya. Ya fito, ya zauna a bakin gadon sa, ya jawo phone ɗinsa daga aljihun riga — yana ganin calander “One month remains… one whole month of this…” Ya huci, yana girgiza kai, yana cewa a ransa: “Wallahi, na gaji da garin nan… musamman wannan village girl ɗin.” Bai ji komai ba sai ya kira Kamal, abokin sa mafi kusa, wanda suke best friends tun makaranta, Dr. Sadeeq: “Kamal, kai fa… wallahi wannan Indo ta wuce gona da iri. One month kenan… amma ina jin kamar na tsufa nan take! " Kamal ya ɗaga kai, yana dariya ta cikin waya: “Hahaha! Sadeeq, kai dai ka fara kuka kenan? Wacce irin village girl ce haka ta sa ka haka? Ai kowa na san ba sauki ke ba!” : “Kai Kamal… ba kiɗa bane! Ta fi duk wanda na hadu da shi… voice ɗinta na jima ina jin sa a hancina, kuma wannan drama ɗinta — wallahi, I don’t know whether to laugh or cry!” Kamal ya ƙara dariya, yana ɗaukar lamarin a wasa: “Hahaha! Kai Sadeeq, wallahi na san yanzu zan fara kiranka ‘Doctor of Drama’! Wannan ba ƙaramin village girl bane, wannan kai tsaye ta shigo film industry! ” “Kai dai ban san ko na tafi ko na tsaya ba… I can’t take it seriously anymore! Gaba ɗaya garin nan ya zama mini ciwon kai. Amma ina so ka ji: wannan Indo wallahi ta fi kowa girma a ‘trouble-making’!” Kamal ya yi tsaki, ya ce da nishad: “Sadeeq, kai dai ka kwantar da hankali. Ki yi hakuri — ka ɗauki wannan a matsayin lesson watarana, zakaga farin ciki na drama ɗin nan.” “Lesson? Kai, Kamal… wallahi na fi son lesson a cikin littafi, ba a real life ba! Amma dai na yarda… zan yi haƙuri. Amma ina bukatar shawara: ya ya zan magance wannan village girl ɗin?” Kamal ya amsa da dariya mai tsanani “Simple Sadeeq… kai dai ka tsaya ka yi natsuwa. Kada ka damu da drama, ka tsaya kan aikinka. Amma idan ta sake bugunka… to ai ka dauki photo ka tura min, sai mu yi commentary tare!” Dr. Sadeeq ya saki dariya da ƙuruciya, yana cewa: “Wallahi Kamal, kai dai friend na gaskiya ne. Sai dai ina fatan wannan village girl ta barni lafiya kafin wani abu ya faru!” Ya rufe waya, ya jawo tawul ɗinsa ya share fuska, yana jin cewa duk gajiya ta daina — amma zuciyarsa har yanzu tana cike da one month of village drama! $$$$$$$$$$$$$$$ Indo ta kumawa gida, tana dariya da ƙawayenta Dijee, da Haule, suna tsalle-tsalle kamar suna biki. Sun shiga ɗaki, suka zauna suna cin kazar da suka saya, suna murna da farin ciki. Bayan sun gama cin abinci, Indo ta ja sauran kuɗin da suka rage, ta kawo wa Mama: “Mamaaa, ga sauran kuɗin da muka samu!” Mama ta ɗauka, ta dubeta da mamaki, ta ce: “Ina kika samu wannan kuɗin, Indo? Wallahi sai na ji mamaki!”Indo ta yi murmushi, tana cewa: “Dr. Balarabe ne ya gani… ya kira ni, yace na saya kaza, ko? Ai shi ya bani kuɗin, Mama.” Mama ta tsaya tsaye, tana kallon ta shiru. Ta girgiza kai, ta ce: “Allah ya shirya ke, Indo. Sai na ga wannan yarinyar… gaskiya ko karya, Allah ya shirya.” Dukansu suka fashe da dariya, Dijee da Haule suna ta dariya har kowa ya ji nishadi. Indo kuwa ta zauna tana cin kazar, tana tunanin cikin ranta “Wallahi, idan duk zan haɗu da Balarabe sai na cuce sa ya saya min kaza da lemo kawai nake so!” “Mama, ki bar ta mana! Indo ta zama ta birni yau, tana hulɗa da doctor!” Mama ta saki tsaki tana komawa cikin ɗaki tana cewa: “To Allah ya huta min da ke, Indo! Da gaske wannan yarinya ta sa ni a tunani.” Indo kuwa ta koma ta zauna tana ta cin ragowar kazar, ta lumshe ido tana tunanin Dr. Balarabe cikin ƙirjinta tana cewa: #$#$$#$$$$$$$$$$ Washegari gari bai waye sosai ba, rana ma bata fito ba, amma ana ta hayaniya a unguwar Modirre. Kowa da abinda yake faɗi. Ana jin muryar Talatu tana ta tsine-tsine daga bakin kofarta kamar wacce aka rage wa rai. “Wallahi yau sai yan sanda sun tafi da ita! Sai an ɗauke ta ni da ita fa! An kusa bani ciwon kai saboda waccen yarinyar mara mutunci, Indo! Ina ta kwance a gida, sai kawai ta fasa min kai da dutse!” Tana magana tana ta huci kamar wacce ta sha barkono. Makwabta kuwa suka fito, wasu suna dariya, wasu suna faɗin: “Ai Talatu yau ma kin samu labari fa! Ke da Indo ba kwanciyar hankali!”wasu kuma suna tausaya mata, musamman ganin bandage a goshinta. cikin daƙilewa da jin haushi ta cigaba da faɗa tana kai hannu: “Idan ba a ɗauke ta ba, ni da kaina zan ɗauki doka a hannuna! Wallahi sai an ɗaurata!” Sai ta kama kunne kamar wacce ke rantse da gaske, ta cigaba da zagin Indo har tana hura majina. Da wannan hayaniyar sai ‘yan sanda suka iso da motar patrol, motar su cike da ƙura, tukunyar biredi da ke kan cap ɗin ɗaya daga cikinsu na rawa da iska. Talatu ta gani sai ta fara tsalle: “Yauwa! Gashi nan sun iso! Allah ya kawo gaskiya yau yau Indo sai kin ɗanɗani sabo!” Wasu yara suka fara ihu suna cewa “Yan sanda sun iso! Yan sanda sun iso!” wasu kuma suna gudu saboda tsoro. Unguwar ta koma hayaniya. Kowa na magana, wasu suna tafi, wasu suna tsokanar Talatu. cikin wannan hayaniya kuwa, Mama tana cikin gida tana girki, zuciyarta babu dadi. Tunda aka ji hayaniyar, hankalinta ke ƙaruwa. Tace da kansa:“Ya Allah, kada wannan yarinyar ta sake jawo min matsala yau. Indo! Indo fa barci take yanzu, ko?” Sai ta fito da sauri daga ɗaki, tana sanye da hijabi, ta dubi ɗakin Indo. Sai taga Indo kwance tana barci, ranta cike da nutsuwa kamar wacce bata san duniya tana hayaniya a kanta ba Mama ta girgiza kai, ta ce a hankali: “Wannan yarinya ba zata taɓa gyaruwa ba wallahi. Duk duniya tana magana, ita tana bacci kamar wata sarauniya.” sai ta juyo ta fita ta leƙa kofar gida — nan kuwa ta ga ‘yan sanda, Talatu, da maƙwabta cike kamar kasuw , Duk suka juya suka kalli Mama Ɗaya daga cikin ‘yan sandan ya ce: “Madam, muna neman wata yarinya mai suna Indo… sun ce tana tare da ke?” Mama ta ɗan juyo, ta riƙe gefen hijabi nata, tace da rawar murya “Eh… Indo ce fa ‘yata, amma lafiya dai?”Sai Talatu ta katseta da ƙarfi tana ihu: “Lafiya fa kika ce? Wannan yarinyar ta kusa kashe ni da dutse jiya! Har jini na kwarara kamar ruwa! Ni fa ba zan yi shiru ba sai an ɗauke ta!” Yan sanda suka juya suka kalli juna, ɗaya ya yi dariya, ɗaya ya turo baki. Sai babban ofisa ɗin ya ce:“To madam, kiran ta mu yi, mu ji da kanta.” Mama ta koma cikin gida da sauri tana ta kiran Indo. “Indo! Indo fa, fito nan da sauri, wai ‘yan sanda ne suna neman ki!” Indo a cikin bacci, ta juya kamar wacce ake taɓa da sanyi, tana cewa cikin bacci: “Mamaaa... na rantse ban kai kaza ba yau... duk dai kuɗin na Dr Balarabe zan saya lemo ne …” Mama ta ce: “Wai kin ji kuwa Indo? ‘Yan sanda sun zo, kin jiyo suna ne ko?” sai Indo ta tashi chak! Ta zauna kamar wacce aka zuba ruwa a kanta. Idonta a bude, gashinta a warwatse, ta dubi Mama da tsoro. “Wai me kika ce? yan sanda? to Mama ban ɗauki komai ba fa!” “Ni ma ban san me suka kawo ba, amma sun zo suna neman ki!”Indo ta zaro ido, ta fara girgiza kai. “Ni wallahi ban yi komai ba Mama! ko kadan! In akwai wanda ya ce na yi masa laifi to karya yake! Karya ne Mamaaa!” Sai ta fara kuka, tana bin bango. Mama kuwa sai ta ce “Ai ni ma ban sani ba Indo. To ki fito su ganki.” “A’a Mama! Ba zan fito ba! ni dai ina tsoron su! ni fa ban son rigima!” sai ta rufe kanta da zane ta shige bayan labule da wannan halin, Mama ta fito ta ce: “To dan Allah kuyi haƙuri, bari ta shirya ta fito.” Yan sanda suka tsaya suna jiran ta, yayin da Talatu ke ta huci kamar wacce aka cinye mata buhun wake. Daga ciki kuwa ana jin Indo tana shirin fitar da hayaniya kamar kullum: “Mama! Ni dai ban fita ba! Idan sun kama ni ai sai su fasa kai na kamar Talatu!” Wani yaro na gefen gida ya ce da dariya: “Wai ita ce Indo? Waccan mai ihu da gudu? Ai fa yau sai an ɗauke ta da hannu!” Sai dariya ta kaure. Yan sanda suka kalli juna suna murmushi, ɗaya daga cikinsu ya ce “Wannan yarinyar da take ihu kamar ta sha kayan maye ce kuwa?” Da ƙyar Mama ta shigo da Indo, tana riƙe da hannunta da ƙarfi. Indo ta fito da ƙyalli, zani daban, riga daban, gashin kai a kwance kamar wacce aka taso daga kasuwa. Sai ta dubi ‘yan sanda, ta ɗan matsa baya tana cewa da fargaba: “Don Allah, kuyi haƙuri! Na rantse ban fasa wa Talatu kai ba, itace ta fara zagi na!” “Shiru ki yi!” inji ofisa. “Za mu je ofis mu ji duk bayanin.”Indo ta kalli Mama tana kuka: “Mamaaa! Kice musu fa! Ni dai ban yi komai ba! ni da raina!” Mama ta share gumi tace: “Kuyi haƙuri, malamai, ku ɗan tausaya. Yarinyar nan da alama ta raina ne kawai ta ke.” Sai Talatu ta tsalle ta ɗauki dariya, tana cewa: “To ai da raina ake fara aikata laifi. Ai yau sai taji! Da sa hannun ‘yan sanda taji!” Daga nan ‘yan sanda suka ja Indo zuwa mota. Indo na ihu kamar wacce ake yankan rago: “Wallahi ba ni neee! ba ni neee Mamaaa! Mamaaa ki bi su ki ceto ni!” Unguwa ta kaure da hayaniya. wasu suna ta dariya, wasu suna cewa:“Ai Indo ta shiga uku yau!” Kamar wasa, mota ta ɗaga ƙura ta tafi, Indo a ciki tana ta ihu, yayin da Mama ta tsaya bakin ƙofa da hawaye. Sai ta kalli sama ta ce “Ya Allah, kai ka san halin wannan yarinya, ka kawo mata mafita.” Me yake shirrin faruwa ...? https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM 🩺 DR SADEEQ 🩺 by NARNAH KANWAR SOJA ✍️ MY 15th Novel Comedy love drama. 08101235739 CHAPTER 1️⃣0️⃣ *10 / 11/ 2025 Monday morning iska mai sanyi ke kadawa, rana kuma na fitowa a hankali. A yau Dr. Sadeeq ya farka tun da wuri, ya shiga bathroom yana wanka da ruwan sanyi saboda

Chapter 4 of 5