salo’! Wannan iskanci ne fa Rahama, wallahi jan rai ne! Don Allah ki duba mana idan akwai complete, ko dai marubuciyar nan tana wasa da zuciyarmu ne?”
Dariya Nabila ta yi tana girgiza kai.
“Ke Rahama, da gaske kin cikka rake. Kowa da sanin sa, ai marubuta su ma mutane ne. Ki yi haƙuri, wani lokacin dole ana musu uzuri gun rarraba littace shiyasa haka ya faru Amman idan ban samu complete ba akwai number ta a cikin book one sai mu gwada kirar ta ".
Rahama ta murmusa kaɗan ta ce,
“Hmm… to shikenan, ki bani number ɗinta kawai, zan tura mata tambayar ta WhatsApp.”
Sai ta juyo ta tambayi Nabila cikin murmushi:
“Amma wai Nabila, ya labarin ƙawarki Atika wacce take Yola? Na ji wai ta rame saboda Dakon soyayya! ”
Nabila ta fashe da dariya har tana hawaye, ta ce:
“Ke dai bari. Wancan soyayya ta Atika da Dr. Sadeeq ai kamar film ne. Ita kawai ta haukace, shi kuma ma bai san tana haukarta ba. Ai sai dai soyayya ɓangare ɗaya, ke kalli yadda take jarraba kanta don kawai ta ganshi , kin kasan cewa suna na ya fito zan tafe dashi , Amman ta shiga ta fita sai da ta sauya da sunan ta , barazana nasani ba kawai na barta ne , yaushe zan zauna inason masu wani !”
Suna cikin wannan gulmar ne kawai aka kira su daga speaker “Emergency work! All nurses on duty, report immediately!”
Sai suka yi tsit suka kalli juna, Nabila ta ce:
“To ga gulmar ta tashi kenan. Soyayya sai an dawo!”suka yi dariya suka watse — gulmar ta mutu.
YOLA MODIRRE APARTMENT
A hankali ta fara cire kayan jikinta, ta daura tawul a kirji, sannan ta tsaya gaban madubi.
Idanunta suka sauka kan shape ɗinta — cikakke, daidai, mace ce da Allah ya halitta da kwarjini da kyan jiki.
Ta ɗan murmusa cikin hawaye tana cewa:
“Dr. Sadeeq… ko duniya zata tsaya, sai na mallake ka. Duk wannan kyau na, duk wannan surar da Allah ya bani, me yasa baka kallona matsayin mace ba? Me yasa baka taɓa ganin ni kamar yadda nake ganin ka?”
Sai ta daure fuska, ta share hawayen da hannunta , nan take ta ce da kanta:
“To shikenan, daga yau zan canza salo. Idan har kai namiji ne — to, wannan karon zaka san wacece Atika!”
Ta shiga wanka, ta fito da sabon ƙamshi mai daɗi da ke cike da ɗakin.
Turaren Amber Oud da ta shafa ya gauraye da ƙamshin sabulun vanilla musk, yana fita kamar na wata ƙaramar sarauniya.
Ta sanya wando da guntuwar riga, cibiyar ta a waje bata saka bra ba gashinta ta zuba baya, ta ɗan shimfiɗa gyale a kafaɗa, sannan ta ɗaura abayarta , ta tsaya gaban madubi, ta yi kallo ɗaya daga ƙasa har sama, ta murmusa da salon da ke ɗauke da jarumta da girman kai.
“Daga yau, sai kai Dr. Sadeeq ka fara soyayya da sunana sai ka fara jin shaukina
domin idan ka ga surata — dole ne zuciyarka ta kwanta min.”
Ta yi dariya mai sauti, ta ɗan janye gyalen, ta ce cikin murya mai cike da daɗi da nishadi:
“Sai na mallake ka… saboda ina sonka!” ........
Tana zuwa a cikin saɗa da rigima Irrin ta goggaggiyar ƴar makaranta a hankali ya tura kofar sai taji a rufe yaye knocking a lokacin ya fito wanka kina yana GOGGE jikin sa nan yazo dafff kofar " who " cikin rawar murya tace it's me sir Atika ". tsaki ya dan ka kaɗan " okay what do you want now " cikin kasallalliyar murya ' sir it's about the assignment"
" then go I don't have time for this and next time kar ke sake zuwa da dare kina Min knocking " ya faɗa yana juyawa Daman ko ƙofar bai buɗe ba, cikin jin haushi da takaice ta juya tana iso wa ɗaki taye hurge da pillow Cinderella tace mata " i hope is fine like u love ur oga " ta faɗa tana murmushi ƙefen baki , ko kullata Atika bataye ba taye ruff da ciki ta kwanta Asuba ta gari ...
TO BE CONTINUED. .......
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
🩺 DR SADEEQ 🩺
by
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739
CHAPTER 0️⃣6️⃣
3/ 11/ 2025
“The Day Destiny Screamed”
" Wallahi yau sai an yi wa Indo wanka, ko da da karfi ne! wai ko kunyar shiga mutane bazakije Na haba Indo ta
Mama ta ce tana hura hanci, “Haba Indo! Bazaki ji tausayin kanki ba? ki kalli jikinki fa, kamar an shafe ki da mai daddawa da ƙura!”
Indo ta fara gudu tana ihu,
“Mamaaa! Wallahi ban ƙazantu ba, jikina yana da natural colour ne kawai!”
Amma Mama ta kama ta da gudu suka shiga drama Indo na cizgar ruwa kamar maciji, tana ihu kamar ana yankar ta “Mama zafi! Mama zafi! Ruwanka kamar acid!”
su Dijee suka tsaya bakin ƙofa suna kallo, suna faɗin: “Kai yau fa, Indo ake yi wa wankan dole!”Mama na zuba mata ruwa akanta , Mama tana faman watsa ruwa tana cewa,
“Yau ko da dole ne Indo sai an gama wanka!”
Indo kuwa ta fara ihu tana birgima kamar ana yi mata fasa kai.
“Mamaaa! Ruwa kamar wuta! Wallahi zafi ne!”
Sai Mama ta ɗaga bokiti ta juye mata gaba ɗaya. Indo ta tashi da wani ihu da dariya lokaci guda, tana ta birgima a ƙasa, Indo ta saki katon tusa mai amo — booommm!
Warin ya mamaye wurin, Mama ta ɗaga zanin ta da gudu ta fita tana faɗin, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! Indo yau za ki kashe ni da wari! Haule ta leƙo tana dariya,Tusa ta farko ta fito da sauti mai amo, ta girgiza har bangon bandaki!
“Mama, ku rabu da ita kawai. Wanka ba zai tafi da wannan warin ba!”
Indo kuwa ta tsiri da dariya kamar ranta zai fita, tana ta faɗin: “Ni dai Mama, kaɗan aka yi! Tusa ta ce ba ruwana abu ko wari babo !”
r ta lafa — sai kuma aka ji wata tusa ta biyu, Wannan karon sai ta fi ta farko ƙarfi, wari ya mamaye gidan gaba ɗaya!
Mama ta tashi da gudu tana dafe hanci tana cewa: “Innalillahi Indo! Wannan ba wanka bane, azaba ce!”
Mama ta fita a guje tana kallon Indo da mamaki, kafin ta iya cewa komai
Sai ta zame a ƙasa!
Indo ta kalli yadda Mama ta faɗi, ta fara dariya ba ƙaramin dariya ba! Ta na ta tsiri kamar zata shaƙe kanta, tana faɗin “Mamaaa! Kinyi kama da wanda ruwa ya ci!”
Amma kafin dariya
Da kyar Mama ta shige ɗaki, tana rawar sanyi da gajiya. Ashe a cikin wannan cunkoson faɗuwa ta kwana da masifa — hannunta ya buge da bango, goshinta kuma ya fashe, jini ya fara zuba kamar ƙaramin rijiya.
Nan take ta saki ƙara — “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! Indo kin kashe ni yau! Indo! Indo!!”
Cikin firgici Indo ta fito da hanzari, tana tafiya kamar wacce aka yi wa bulala. Doguwar rigarta ta manne a jikinta saboda ruwa da sabulu, gashin kanta dogo ne mai tsanani Amman yayi dungule dungule ya chunkushe sai ɗiga da baƙin ruwa yakiye ga ɗan banza wari saboda an zuba mai ruwa yana manne da kumfa, sai ta rufe kirji da hannuwa tana ihu.
“Waiyo Mamaaa! Mama jini! Na shiga uku yau! Wallahi ban yi da gaske ba!”
Kafin su Dijee su fito daga ɗaki suna ihu, maƙwabta suka taru a ƙofar gida. Mai unguwa kuwa ya iso da serious face, yana kallon Indo cike da mamaki.
“Ke Indo, wai har yanzu baki daina wannan wankan wahala ba? Wace irin halitta ce ke haka?”Amma Indo bata ma saurare shi ba — ta ruga kanta wajen Mama tana kuka kamar ƙaramar yarinya .
“Wayyo Mama! Ki tashi ki yi magana mana, kin barni ni kaɗai!”Mai unguwa ya girgiza kai, ya ce, “Ku kira napep kafin ta suma nan gaba ɗaya.”
Da hanzari aka kawo napep, aka ɗora Mama, Indo kuma tana bi a baya da gudu, ga rigar ta ta manne, ga kumfa, ga dusty slippers ɗin ƙauye — abin ma dariya yake.
Yaran layi suna ta dariya suna ta mata dariya
Ana cikin haka suka shige MODIRRE SPECIAL HOSPITAL. Indo na ta ihu a bakin ƙofar asibiti kamar wacce aka zo da gawa, ga yawu yana fitowa saboda ihu, jikin ta kuwa ruwa da yauƙin dirty.
“Waiyo ku taimaka, Mama zata mutu! Ni Indo ce! Indo ‘yar gidan Mama!”
Nurse ɗaya ta fito tana kallonta da mamaki, ta ce da sauran nurses:
“Ku duba, wannan ai ba patient ba bace wannan drama patient ce!”
$$$$$$$$$$$$$$$$$$
A cikin nutsuwa da kamala yake zaune, Dr. Sadeeq ɗaya daga cikin likitocin da ko turare sai ya yi breaking news a wajen nurses.
Yau kam ya sanye ƙananan kaya masu launin sky blue — shirt ɗin sa ta manne da jikinsa kamar an zana shi da brush. Trousers ɗinsa kuwa ta kama shi daidai da ƙafafun sa masu tsayi, sai agogon silver a hannunsa yana walƙiya.
Gashin kansa kuwa sai luff-luff yake kamar wanda aka yi masa brushing da iska mai sanyi. Yana zaune cikin ofishin sa, ƙamshin turaren Bleu de Chanel yana yawo cikin ɗakin kamar iska ta Aljanna.
Hankalin sa kwance, murmushi a gefen baki, yana danna laptop ɗinsa a hankali, yana ɗan cizza lebensa da salo irin wanda ke sa nurses su manta suna aiki.
Babu hayaniya, babu wahala yana hutuwar sa yau Sai kawai… “PRIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIING!!!”
Emergency bell ta buga da ƙarfi har sai da ya ɗan firgita, ya dago da sauri yana kallo.
Cikin seconds kaɗan, nurse Atika ta shigo da gudu tana haki “Doctor! Doctor! Emergency room one — female patient, bleeding! It looks serious!”Ya ɗan janye kujerarsa a hankali, yana gyara murya. “Who’s on call dutty ?”
“You, sir!”
Ya ɗan ja dogon numfashi, ya miƙe, suit ɗin sa da ya rataye a kujera ya ɗaura a kafaɗa.
Ya dubi madubi a bango, ya ce cikin salo:
“Emergency again? Modirre people won’t let me rest... Let’s save another life.”
Sai kuma murmushi ya yi — mai cike da kwarjini da doctor’s confidence.
Ya fita a nutse, ƙamshin turarensa na biye da shi har zuwa corridor ɗin asibitin...
Cikin gaggawa nurses suka shigar da Mama ɗakin emergency, ana jin ihun “wayyo ni Mamaaa!” daga Indo har a waje.
Mutane sun taru, wasu na tsaye suna kallo, wasu kuma na rarrashin ta:
“Haba ƙanwata, ki bari likita ya duba ta mana!”
Indo kuwa kuka take, ihu da ihu sun haɗu, majina na fita, hawayenta na rige da juna.
Sai kawai ƙofar ɗakin ta buɗe da ƙarfi —
Dr. Sadeeq ya shigo da sauri, hannunsa cikin gloves, Atika tana bayansa da emergency box.
Turarensa ya cika ɗakin, ƙamshi ya yi karo da wari. Idon Indo ya faɗa kansa, numfashinta ya tsaya kanta ya buga — “Shikenan! Shi ne dai wannan kyakkyawan Balarabe ɗin da suke ta cewa!”
Sai kuma ta ji wani abu ya tsaya mata a wuya — muryarta ta ruɓe, zuciyarta na dukan guga.
Gashin kanta ruwa yake, yana digar da ruwa kamar an tsiyaye mata ruwa a kai, ya kwanta da salo kamar coiling hair ɗin da ake yi a saloon — amma ba saloon bane, wankan dole ne Mama ta yi mata
Sai kuma wani wari mai sa hawaye ya tashi — wurin daga jikinta ne, saboda wahalar wankan da ba ta gama ba.
Sai dai duk da haka, idanunta suna haske, cike da wani irin tsoro da bege.
Dr. Sadeeq bai ankara da ita ba, yana duban marar lafiya, yana cewa “Nurse Atika, check her pulse… we’re losing time.”
Kafin kace “Injection”, Indo ta tashi da sauri — ta faɗa jikinsa wuffffff!
Ta kama rigarsa da karfi, ta jingina kanta a ƙirjinsa, tana rawar jiki tana faɗin:
“Kai ne za ka ceci Mama, don Allah ka taimake muoo!”
A lokacin Atika ta tsaya cak, ta zuba mata ido,
Dr. Sadeeq kuma ya yi shiru yana kallon Indo da mamaki…......
ƙamshin turare da warin sabulun ruwan wankan dole suka haɗu — abun ya zama kamar sinadarin ban dariya da tausayi lokaci guda!
How Indo a jikin Dr Balarabe........?
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
🩺 DR SADEEQ 🩺
by
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739
CHAPTER 0️⃣7️⃣
05/ 11/ 2025
“The Day Destiny Screamed”
Numfashin Dr. Sadeeq ya kusa barin gangar jikinsa gaba ɗaya zuciyarsa na bugawa da sauri kamar ana buga ganga wari irin wari da dirty wanda bai taɓa jin Irrin sa ba a rayuwarsa duk da kasancewer sa likitn mata !
Idan iska ta shigo hancinsa — sai jikin sa ya ɗau rawa.
A cikin sakan kaɗan, shi da kamshinsa na Versace suka fara rikici da warin sabulun Indo da wari na ruwan wanka da datti.
Ya ɗan ja da baya yana dafe ƙirji da hannunsa, idanunsa sun firfito “Oh my goodness! What… what is this smell!?”
Mai unguwa wanda ya kawo su, da sauri ya kamo Indo yana jan ta daga jikin likitan.
“Ki fito ki fita ki je waje kafin a kore ku da sanda!”
Indo na kuka tana juyi, “ka taimaka ma Mama ta! Don Allah kai ne kaɗai zaka iya!”amma duk wanda ke ciki, sai suka yi shiru suna kallon yadda likitan ya kasa numfashi.
Dr. Sadeeq ya yi saurin nufar toilet — yana rike ciki kamar mai gudawa.
A can cikin ɗakin, sai aka ji “wuuufff!” ya yi amai da ƙarfi,
kamar zai mayar da hanjinsa waje “Ya Allah, I can’t breathe!”
Atika da ke wajen ta riƙe ciki tana dariya, tana ɗan boye fuska saboda ba ta son a gane tana dariya — amma abun ya gagara!
Tace a hankali:
“Doctor Sadeeq dai ya hadu da bala'e daga yau sai dai ya saka mask kafin ya fita!”
Da ƙyar ya fito daga toilet ɗin, rigarsa ta jiɗe da ruwa.Da ya fito daga toilet ɗin, rigarsa ta jike, ya cire suit ɗin, ya kifa shi bisa kujera yana huci.
Sai kawai ya zauna, ya rufe fuska da tafin hannunsa yana cewa a hankali“Oh God... what a smell of destiny!” ya cire court suit ɗinsa ya rataye a gefe, yana numfasawa da wahala,
fuskar sa cike da gajiya da tashin hankali.
Sai ya kalli Atika da yanayin disbelief, ya ce cikin murya mai sanyi amma cike da haushi:
“Next time, don’t ever… ever allow such smell near me again.”
Ya girgiza kai, ya ɗan share gumi sannan ya ce:“Now, where is the patient?” ya gyara glass dinsa, ya jingina da bango — har yanzu idanunsa suna ruwan hawaye saboda masifa
A can cikin dakin, Mama Indo an riga an tsaftace goshinta, an daura mata bandage.
Indo kuwa tana zaune a gefe tana rera waka cikin kuka da dariya “Mama ba za ki mutu ba, ko da wari ya kashe Dokta
Bayan awa biyu aka sallame Mama daga asibiti, aka ba ta magunguna da shawara.
Sai dai kafin su fita, mai unguwa ya shigo da tsawa “Ku fita daga nan, Indo! Wallahi sai kun gyara halinku, wannan ihu da rashin kunya naku ya isa!”
Kafin Indo ta tanka, Mama ta ja ta da hannu suna ficewa.
Indo na daga murya tana cewa: "Dr Balarabe Nagode "
DR. SADEEQ
by
Narnah ƙanwar soja
08101235739
Da ya koma gida, Dr. Sadeeq ya jefa suit ɗin cikin laundry basket kamar wanda aka jefar da jikin gawa ya tsaya a gaban madubi, yana kallon kansa da takaici.
Ya ɗan dafa hanci yana furta da ƙasa:
“Oh Lord... I’m a doctor, not a warrior. What kind of creature was that girl?” yana shiga wanka tamkar zai ƙarar da ruwan toilet da sabulu yana fitowa, ya buɗe wardrobe ya ɗauko turare, ya feshe jiki gaba ɗaya kamar zai tsabtace tunaninsa ma.
Amma duk da haka, har yanzu yana jin wani ƙamshi — haɗin Dettol, sabulun local da turaren wanka — yana yawo a cikin hancinsa.
Yana murmushi da kansa cikin takaici, ya ce:
“Ko dai zuciyata ce ke tunanin wannan ‘yar kauyen? Indo...? that's her name ”
Sai ya girgiza kai da sauri, ya ce da ƙarfi “No way! Never! I can’t be thinking about that noisy... smelling... drama queen!”
Amma a zuciyarsa sai wani siririn dariya ya biyo — kamar yadda yake yi idan ya ga jarirai suna dariya a asibiti.
Wani flashback ya dawo masa: yadda Indo ta faɗa jikinsa, yadda gashinta ya tsaya, yadda take kuka tana cewa “Mama ba za ta mutu ba, ko da wari ya kashe Dokta!”
Sai murmushi ya ƙwace masa, ya dafe kansa yana cewa “kai! Wannan yarinyar ai bala’a ce. Amma... tana da wani abu daban.”
Wannan ne karon farko da Dr. Sadeeq, wanda yake tsananin tsabta, ya kasa mantawa da mutum saboda wari ,
A daidai wannan lokaci kuma, a can Modirre, Indo tana ta bada labari ga ƙawayenta cewa:
“Wallahi Dokta ya kusa suma! Na ce muku ni Indo, ba kowa ke jure kamshina ba!”
A cikin gida, bayan sun dawo daga asibiti, Indo ta zauna a gefen gado tana ta murmushi tana kallon sama.
Mama tana kwance, tana bacci bayan ta sha magani.
Indo ta ɗan dafe kumatu, ta ce a hankali cikin sanyin murya:
“Hmm… wannan Balaraben ai ya ban tsoro, amma kuma… yana da kyau. Muryarsa ma kamar wadda ke dariya ya iya magana masifar da kamar hira sam bashi da murya a sama .”
Ta yi murmushi, ta ɗora hannu a kirjinta, tana jin wani abu da bata saba ji ba “Kai Indo, kina dariya da kanki fa,” ta ce tana wasa da yatsunta.
“Toh ai babu laifi ko da dai ni ‘yar kauye ce, ashe ina da guntun basira!”
Sai ta fashe da dariya tana riƙe ciki, tana tuna yadda Dokta ya fita da gudu daga dakin saboda wari
“Wai ko saboda ni ya fasa aiki? Ai da ya dawo sai in ce masa sorry Doctor, it’s my natural body !” a hankali bachi ya kwashe ta da tunanin kala kala ...
$$$$$$$$$$$$$$$$$$
Yau kwana ba'kwai kenan da faruwar wancan abin dariya a asibiti, amma Indo har yanzu bata daina ba. Kullum sai taje asibiti da fatan a yau ne za ta sake ganin “wanan kyakkyawan Balarabe likita” ɗin da zuciyarta ke bugawa da sauri idan ta tuna da shi.
Amma kuma kash — kullum sai a hana ta shiga a yau ma, tun da asuba Indo ta tashi cikin annashuwa, tana ta waka tana shara.
“Yau Mama zata kuma asibiti… yau fa dole sai na tafi da ita!”
Mama kuwa ta fito daga ɗaki, fuska a haɗe.
Indo ta biyo bayanta cikin wani shigar ban dariya , rigar daban, zanin daban, gashin kanta duk a waje, ta ɗaura kallabi kamar mai niyyar hawa rijiya!
Zanin kuma ta ɗaura shi sama kamar mai neman ɗaukar kogi akanta Mama ta tsaya tana kallonta sama da ƙasa, ta dafe kai:
“Wallahi Indo, ba za ki tafi ba yau! Ai kullum ke da asibiti sai fitina.”
Indo ta rike kirjinta, ta fara birgima a ƙasa tana ihu kamar wacce ake yi wa allura “Wayyo Mama! Wallahi sai na tafi! Idan ba na tafi ba, zan mutu a nan!”Mama ta zaro ido:
“Mutuwa kuma Indo?”
Amma Indo ta ƙara juyawa a ƙasa, ta kama ƙafafun Mama tana faɗin:
“Sai na tafi Mama, wallahi sai na tafi — ni da likita saina gansa yau!”
Mama ta dafa kanta da ta gaji da fitsaran Indo, ta ce cikin gajiya: “Toh, zamu tafi kawai, tunda ke da shaidaninki kun yi ƙawance !”
Indo ta tashi da sauri, tana dariyar nasara “Na san za ki dawo hayyacinki Mama, yau fa Modirre Hospital sai ni da Dr Balarabe kawai!”
Tace, “Na ji za ki bini, amma sai da yamma ake cewa zanje, ba da safe ba…” nan da nan fara’ar da ta cika fuskarta ta tsaya cak!
Duk burinta dai, taga likita mai ƙamshin ƴan aljanna i ba wari kamar taƙin Indo Tana ta gunguni tana fita daga gida, bata ma sa mayafi ba — sai gidan su Mairo kai tsaye!
Da ta ƙarasa, ta hango su Dijee da Haule suna ta rusa kuka, kamar an musu jana’iza. Indo ta tsaya daga nesa tana dubansu da mamaki, sai ta ɗaga hannu ta dafe ƙugu tana tambaya da murya mai taushi amma cike da zolaya:
“Wayyo Allah! Waye ya taɓa min ƙawayena? ku gayyamin yanzu nake kwance masa fantari cikin jama’a!”
Kallon juna kawai suka yi sannan suka rungume ta cikin kuka.
Ta sake dafe ƙugu tana ƙara murya “kai nifa ku faɗa min me ya faru? Tsimin na har na tashi haka?!”Sai Haule ta girgiza kai, cikin kuka tace “Za su tafi da Mairo birni aikatau, Indo... wai yau za su ɗauke ta!”
Ai kafin ta gama magana Indo ta rufta da gudu kamar wadda aka saki daga kulle , ta nufi gidan su Mairo, tana rera ihu:
“Wallahi ba za ku tafi da Mairo ba sai dai ku ɗauke ni ma! yaran unguwa kuwa suka fara biye mata suna dariya, wasu kuma suna faɗin:
“Indo ta sake hauka ne ko?”
Halin Indo dai — ko da kuka ne, sai ta saka dariya a ciki!
Duk hankalin maƙobta ya dawo kan Indo. Ta na ihu tana ta daddage murya har unguwar ta tsaya cak — kowa na kallonta da dariya da mamaki. A gefen titi, Mairo na zaune a motar, idonta cike da hawaye; hannu a hannun Haule da Dijee, amma zuciyarta na nufin tashi su tafi birni. Indo kuwa ta cika da tashin zuciya, ta yi ihu da ƙarfi kamar wacce za ta ƙarye duniya:
“Wallahi ba za ki tafi ba! Ke barmu?!”
Nan ne suka tashi suka ja su Mairo cikin mota — kamar an yi wa rai kwashe. Suka rungume juna tsananin, wasu suna ta yi musu tausayawa, wasu kuma suma hawaye suka zubo saboda rabuwa. Motar ta ƙara motsi, ƙarar taya da tukin ta na ƙara nisa, amma har yanzu bakin titi sai ihu da kururuwa.
Sai kuma kishiyar maman Mairo ta fitowa kamar wacce ta cika da zafi a fuska, kai har da bakin magana: “Ke tafe? Ai baza mu maye a hannun kura ba! Ke tafe chan, ke nemu min kuɗi — ba zan ciyar da ubanki ba! na chiryar dake ba tunda uwarke ta mutu ” Ta ce haka tana nuna ƙyar da fushi. Indo kuwa, da zuciyarta ta ƙara zafi, ta ɗauki dutse a ƙasa — idanuwanta cike da zafin rai — ta jefa dutse da ƙarfi kai tsaye kan ƙiyarta. kawai sai ta faɗi akan bakin ta sai ga haƙurinta ya zube gida biyu saboda akan Dutse ta faɗi Dutse ya buge ta, sai ihu da ƙara ta ɓarke daga makobtan unguwa.
Mutane suka yi ta dariya da hanzari; wasu suna ta magana, wasu na ta ce “Ai wannan kuwa ta wuce gona da iri!” Amma gidan dariya ya tashi ne saboda yadda Indo ta jefa dutsen — abin ya yi wa maƙiyarta kyauƙaƙen zafin rai, kuma har an ce an tura yarinya ƙarama don aikatau zuwa wani gari.
Indo yau ta jawo magana fan's ya kuga wanan page in......... Sha...................
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
🩺 DR SADEEQ 🩺
by
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739
CHAPTER 0️⃣8️⃣
06/ 11/ 2025