zuciyarsa cike da nutsuwa ya zauna a kujera mai taushi, ya buɗe laptop ɗinsa yana duba emails sai idonsa ya tsaya a kan email mai taken “Emergency Work.”
Aikin gaggawa ne na tsawon watanni biyu, wanda zai tura shi zuwa wani gari mai nisa:
Adamawa State, Yola ƙauyen Modirre Local Government.
Ya ɗan tsaya, yana nazarin sakon.
Wannan aiki ba kawai tafiya bace sabuwar jarabawa ce.
Zuciyarsa ta karɓi aikin da natsuwa, domin yana jin kamar akwai wani abu da Allah ya nufa da wannan tafiya ya shanye coffee ɗinsa, ya fara tsara shirin tafiya.
Duk motsinsa yana cike da daidaito, kamar mutum mai sanin me yake nema.
Yayi booking na jirgin safiya zuwa Yola, sannan ya fara tattara kayansa cikin tsari.
yana cikin shirye-shiryen tafiya, sai ya ji knock a ƙofar office ɗinsa Ya ɗaga kai a hankali —
Atikah ce,mace mai kyau irin wacce ake kira middle-class beauty — fara, mai kyau, kuma ɗauke da murmushi mai haɗa natsuwa da raha.
Ta tsaya tana murmushi a hankali, tana cewa da ladabi“Sir, na samu transfer a ƙarƙashinka zuwa Adamawa State ,yaya zamu tsara shirye-shiryen tafiya, kuma a wanne lokaci zamu tashi?”ya ɗan ɗago kai kadan, amma bai kalleta sosai ba ya ce da murya mai sanyi:
“Get ready... for your own way.” ya rufe kofar, ya barta tsaye, kamar wacce aka kwashe da iska .
Ta jingina da bangon corridor tana lumshe ido, tana haɗiye baƙin ciki “wannan mutumin fa, wai me yake ganin kansa ne?”
ta furta cikin murya mai sanyi amma cike da fushi.
“Get ready for ur own way? To ai zamu gani, Doctor Perfect.”
Takalmin heels ɗinta suna bada sauti kamar gangar tafiya ta jaruma.
Duk ma’aikatan da suka gan ta sun san akwai drama a zuciyarta.
Atikah kuwa — mace ce mai ƙarfin hali, ba ta jin janye kai.
Cikin dare, Dr. Sadeeq ya zauna a gadonsa yana duba laptop ɗinsa haske daga screen ɗin yana haskaka fuskarsa mai kyau, idanunsa suna sheƙi.
A gefensa, coffee cup yana fitar da ƙamshi, da ɗan ƙanshin Arabic perfume yana yawo cikin ɗakin “Two months away from Abuja to Yola, Modirre village.”ya furta cikin murya mai natsuwa.
“This isn’t just a journey — it’s a test.” ya ja numfashi mai zurfi, zuciyarsa tana tunanin abubuwan da ke jiran sa.
☀️ Next Morning
Dr. Sadeeq ya fito cikin white shirt, black trouser, da sunshade.
A hannunsa akwai passport da bag ɗinsa — tafiyarsa cike da class da natsuwa, yana isowa parlour ya zauna a ƙasa nan ya gaida Mommy cikin girmamawa " to Son Allah ya taimaka ka chigaba da riqon addini gaskiya banso ace kayi nisa har wani gari ba but tunda aikin ka ne is normal Allah ya tsare min kai " Ameen Mommy in Sha Allah zan kula Layla ce ta fito cikin wando jenz da top shirt tasa earphones a kunne kai ba kallabi tana hango sa raye saurin cirewa " gd morning brother" mrng yace bai sake waiwaye ba nan ya fito farfajiyar gidan driver da ne zai kaisa airport kai tsaye yayi addu'a ya shiga
Filin jirgin sama na Abuja cike yake da hayaniya da motsin mutane.
Rana tana haskawa, jirage suna tashi, kuma iska tana cike da ƙamshin sabon safe.
Atikah kuwa ta bayyana cikin sky blue hijab da simple gown, fuskarta ta yi haske da ɗan light make-up.
Ta tsaya daga nesa tana kallonsa, zuciyarta na bugawa kamar gangar drama.
“Oh my God… how can someone look this perfect this early?” ta furta a hankali, tana murmushi mai ɗan ɗaci.
Sai idonsu suka haɗu.
Kallon da Dr. Sadeeq ya yi mata ya sa ta kasa magana “Ready?” ya tambaya da murya mai sanyi. ta ɗan gyaɗa kai,
“Yes, sir…”
Sun shiga jirgi cikin natsuwa.
Lokacin da suka zauna, iska mai sanyi ta cika cikin jirgin Atikah ta juya ta kalle shi daga gefe, yana duba tablet ɗinsa “Sir,” ta faɗa cikin murya mai taushi,
“Are you always this calm?” Ya ɗago kai, ya ɗan murmusa, “It’s called discipline, Nurse Atikah. You should try it.”
Ta ɗan tabe baki tana murmushi, zuciyarta na tafarfasa tsakanin soyayya da haushi.
“We’ll see, Doctor Perfect,” ta furta a hankali tana jingina da kujerar jirgi.
✈️ The Journey Begins...
Jirgin su Dr. Sadeeq ya tashi daga Abuja → Yola → Modirre Village.
Ba su san cewa wannan tafiyar ce da zata sauya musu rayuwa gaba ɗaya ba.
To be continued........
Sometimes, destiny brings you love in the most unexpected way
When a doctor heals with love, even pain becomes laughter.” 🩺
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
🩺 DR SADEEQ 🩺
by
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739
CHAPTER 0️⃣4️⃣
1/ 11/ 2025
Wanan page in naku ne mu fan's ina jin daɗin sharhin ku da addu'ar ku a kaina Allah ya bar ƙauna , much love to you guy's..
“The Day Destiny Screamed”
ADAMAWA STATE AIRPORT
Jirginsu na leading ya sauki cikin tattaki ya ɗaga kansa sama ya shaƙe iska mai sanyin safiya ya furzar da cewa " Alhamdullah"Mota ce neavy blue ƙirar taxi ta tsaya a gaban su nan driver ya fito yana ganin sa yace Dr Sadeeq right " miƙa masa hannu yayi sunaye sallama nan ya shigar da Bag's nasu bayan mota shi da driver suka zauna a gaba nan suka fara tafiya direct Doctors’ Apartment, inda za a basu takardar part ɗinsu.
Da suka isa, aka bashi upstairs flat, mai ɗakuna biyu da toilet da karamin kitchen — clean, well arranged, sai ka ce an shirya shi don mutum mai tsabta.
Ita kuma Atika ta samu part ɗin ƙasa, wanda yake na nurses. Daki ne mai kyau, suna zaune su biyu; ta samu sabuwar roommate mai suna Cindra inya mura mai barkwanci sosai.
Dr. Sadeeq yana kammala karɓar key ɗinsa, sai ya tsaya kallon wajen, ya taɓe baki cikin sanyi, sannan ya shiga toilet, ya yi alwala, ya yi raka’a biyu. Bayan ya idar, ya fesa turarensa mai sanyi, ya gyara jikin sa, ya fito cikin nutsuwa.
Sai driver ya tsaya yana kiransa,
“Sir, this car is for you. You can use it — it’s free for doctors like you. Let’s go for your first drive to the hospital. The name is Modirre Special Hospital, under the government.
Ƙauyukan Yola South gaba ɗaya anan suke zuwa. We can go now, sir.”
Atika tana gefe, tana tsaye da waya a kunnenta, tana wani murmushin da ita kanta bata gane dalilin sa ba.
Shi kuma ya shiga gaba tare da driver, ita kuma ta shiga baya cikin nutsuwa.
Motar na tafiya a hankali, iska tana busa gashin kanta, tana jin wani irin strange feeling — ba ta san me yasa zuciyarta ke bugawa haka ba, amma tana jin kamar tafiyar ta fi kowane tafiya daɗi...
Driver mai ɗan iskan surutu ne — irin waɗanda idan suka kama magana sai dai ka fasa kunne ,yana faɗa kamar rediyo yana cewa, “Kai Doctor, ai Yola fa, mata da ruwa suke! Ko maza sai suyi musu gasa. Kuma ka sani Modirre akaiw kyakkyawan mata Fulani ”
Kafin ya kai ƙarshen maganarsa, Dr. Sadeeq ya ɗaga hannu a hankali, cikin sanyin murya ya ce “Please, focus on driving.”
Muryarsa ba ta da tsawa amma tana da nauyi, wanda ke sa mutum ya yi shiru.
Driver ya yi tsaki da ƙasa, bai fi minti biyu ba sai wata yarinya ta wantsalo da gudu ta fada gaban motar! KWAaaaaaaa! — motar ta tsaya da ƙara.
Suka fito da hanzari.Dr. Sadeeq cikin farin rigarsa ya ɗaga hannuwa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”
Driver yana kallon sa da tsoro, yana fargabar kada likitan ya ce shi ne ya yi ganganci.
Sai suka ga yarinyar ta tashi tsaye kamar wadda aka kunna maɓallin drama Tana riƙe guiwa tana ihu:
“Wayyo ubanaaa! kai! waye wannan makahon? ni kake so ka kashe? Allah ya isa tsakanina da kai! mugu! zaka iya baka tafiya ganin mutane ne?”
Sai ta ɗaga hannu tana nuna motar:
“Ku duka a mota ɗaya! Wallahi yau sai dai a kira ‘yan sanda. Da kun ganni yar talaka sai kun ce ku fi ni komai ai ko?!”
Ma’anar maganarta ya tsaya a fili, ko ba ta san turanci ba, harshen zuci ya isa Dr. Sadeeq ya gane ta cike da fushi da jin haushi.
Ya ce cikin sanyi, yana kokarin kwantar mata da hankali:
“Excuse me, Miss, you were the one running across the road without looking.”
Ta daka masa tsawa:
“Ka yi shiru kai ɗan boko Balarabe ba kai ka isa ka ce min magana ba! Kai ne kake cikin mota fa!”
Driver ya kasa daurewa, yana dariya yana cewa “Oga Doctor, wallahi ka haɗu da bomb!”
Indo ta juyo da sauri, ta ce:
“Kai kuma sai dariya kake? ni a nan na kusa mutuwa kake dariya?! uban meye dariya a ciki?”
Dr. Sadeeq ya juyar da kai don dariya ta kusa kubce masa , yarinya ƙarama Amman sai shegen baki ya ce a hankali,
“Alright, let’s take you to the hospital. I’ll make sure you’re okay.”Ta ce da rawar murya:
“Hospital kuma? to kai ka duba ni nan — ai kai likita ne ko ba haka ba ga kayan likita? Ga guiwa nan, duba mana"
Tana buɗe yaggaggen zanenta, sai ta hango cewa faɗuwar da tayi ta gurje. Jini kaɗan kaɗan yana fitowa a guiwarta, fatar ta d'aga amma saboda irin masifar nata, bata ma lura da zafin ba sai yanzu. Ai kuwa ta kurma uban ihu, ta faɗi tana birgima a ƙasa, tana fitar da hawaye kamar an sareta da wuka.
A take mutane suka fara taruwa, wasu suna dariya wasu kuma suna faɗin “Subhanallah! an bugeta da mota!”
Shi kuma Dr. Sadeeq ya tsaya gefe yana kallon ta da fuskar da ta cika da gajiya da takaici, sannan ya ja numfashi yace cikin rashin natsuwa, “Driver, put her in the car, we can move to hospital. I hate unnecessary drama, I swear.”
Ya kammala maganar da wuya saboda ya gaji da hayaniyar da take yi, tana birgima tana ihu kamar an kashe mutum.
Kafin a ce komai, sai ga wata yarinya ta ƙaraso tana gudu, Dijee, tana ganin Indo a cikin mota sai ta kurma ihu da ƙarfi:
“Mun shiga wallahi! An kashe Indo! Za a kaita asibiti!”Takalmi a hannu, gashi a warware, ta tsere tana kiran mutane. A gefe kuma Indo tana cigaba da yiwa mutane masifa: “Ku gani da idonku! Makahon direba! zai kashe ni a hanya saboda shegen girman kai! Ƴan bakin ciki kawai!”
Jama’a kuwa sai dariya suke yi, wasu suna cewa “Wannan ba ciwo ba ne, film ne kawai!”
##########
Motar su kafin ma ta isa asibiti, Dr. Sadeeq ya kusa fita hayyacinsa saboda ihu da ƙamshin wari da Indo ke ɗauka. Yana ta juyi a kujerarsa yana murmushi da ɓacin rai lokaci guda, sai ya kalli driver ɗin cikin gajiya yace,
“Wallahi, I don’t know which one is louder her voice or her smell!”
Driver kuwa sai dariya yake yi har idonsa suka cika da hawaye, yana cewa, “Sir, calm down… ai yarinyar nan drama ce ta gari!”
Dr. Sadeeq ya ɗan ja numfashi, ya buɗe glass ɗin motar a hankali, ya fitar da kansa yana toshe kunne kamar wanda ke guje wa ƙarar generator, yana hura iska kamar yana neman sabuwar rayuwa
Atika kuwa?
Ai ta kusa suma saboda wari! Ta rufe hanci da tissue, tana juyi a baya tana cewa a ranta,
“Ya Allah, ka bani haƙuri da wannan posting ɗin Adamawa, idan ba haka ba sai na koma Abuja!”
suna isa farfajiyar asibitin, kafin kowa ya ce komai, Dr. Sadeeq ya buɗe ƙofa da sauri ya fito kamar wanda aka sake daga gidan yari, yana sauke numfashi da sauri:
“Finally! Fresh air… thank God!”
An shigar da Indo cikin room zuwa wajen wanke ciwo, yayin da shi kuma aka raka shi zuwa office nasa mai tsabta da nutsuwa. Ya wanke fuskar sa da ruwa, ya ɗan share gumin sa, amma duk da haka, sai yake jin kamar har yanzu warin Indo yana shawagi a hancinsa.
Sai ya jinjina kai yace a hankali ya sauke ajiyar zuciya “This girl is definitely a walking trouble…”
Ana sa mata hydrogen peroxide, sai taji tamkar an zuba mata wuta
cikin kakkarfar murya ta kurma ihu kamar wacce aka banka wa gobara.
“Wayyo Allah na! sun kashe ni fa! A kashe Indo! Ku kashe ni da kyau idan dai hydrogen ne, ai dai a zuba yaji kawai, ya fi sauƙi!”
Likitan dake dubata, wani small body nurse , ya ɗan ja da baya yana duban ta da mamaki, saboda ihu ya cika ɗakin.
Dr. Sadeeq kuwa yana wajen window, sai ya girgiza kai yana faɗin a ransa:
“What kind of village madness is this?”
Indo ta ɗora da ihu, tana zabga wani zagi da harshen fulatanci wanda ba kowa ke gane shi ba, amma kowa ya san ana nufin Dr. Sadeeq. “Wannan Balaraben mugun nan! Shi ya buge ni! Allah ya tsine masa! Ko dai ba likita bane, ɗan fasinja ne da ya gudu ya koma likita!”
Likitan da ke mata wanke ciwo ya ƙyar maida dariya, amma driver da Atika sun rufe baki suna ta kokarin dariya suna kallon drama.
Da ƙyar aka gama mata dressing, sai Indo ta fashe da kuka tana rawar jiki:
“Wallahi bazan iya tafiya ba! sai an bani kaza da lemo! ko a ƙauyenmu idan aka buge mutum, sai an kawo masa kaza da lemo kafin ya warke. Ku duba ni fa, babu wanda ya kawo komai!”
Dr. Sadeeq, wanda tun ɗazu yake kokarin kauce wa drama, ya zura masa hannuwa cikin aljihu yace da kasala , "Hasbunnallahu wani'emal wakil "
Driver ya kasa danne dariya, yana daidaita murya cikin dariya yace, “Sir, let me just take her home before she requests goat meat.”
Indo ta rufe kai da zanenta tana faɗin,
“Wallahi bazan tafi ba! sai na ga wancan Balarabe mugun da ya buge ni! sai ya bani kaza, ko dai ba’a yi adalci ba a kasar nan.”
Dr. Sadeeq ya gaji da rigimar ya kalli driver ɗin yace da gajiya,“Send me your account ka saya mata kaza ka kaita gida, I’m tired.”
ya juya ya wuce, ko kallon Indo bai sake yi ba.
Driver kuwa ya kalli Indo yace da ita, “To, mu je a saya miki kazar.”
Haka suka nufi kofar gidan su. Sai dai tun daga nesa suka hango damdazon mutane a kofar gida.
Kafin ma su ƙarasa, sai ga Mairo ta fito da gudu tana kurma ihu,
“Gata nan! Gata nan! bata mutu ba! ta dawo!”
suka fada jikin juna suna kuka da dariya lokaci guda.Mama ta fito da gudu tana cewa,
“Allah na gode maka! su mai unguwa kuzo ku gani, dama duka muna shirin zuwa asibitin ne kamar biki!”
Itakan Indo ba ta damu da taron mutane ba, duk da an buga ta mota, burinta ɗaya kawai — ta shiga gida ta ci kazar da aka bata.
Suna shigowa gida sai su Dijee, Haule, Mairo suka biyo ta da gudu kamar masu tseren olympic, ita kuwa Indo ta riga su ta shige ɗaki tana wage baki kamar wacce ta ci kyautar duniya.
“Mamaaa! Ashe yau arziki ya sauko! zanci kaza da lemo wallahi!”
ta faɗa tana girgiza kafa ɗaya wacce taji ciwo
Mama ta dafe ƙirji, ta dubeta da mamaki ta ce:
Na rantse da Allah idan za. samu kaza da lemo ai kowacce mako gwanda mota ta bugi ne “ ta faɗa ta yagar nama "Indo! Akan kaza gwanda mota ta buge ki? wannan fa abin dariya ne ko kuka?”
ndo ta ɗaga hannu tana cewa,
“Mama wallahi ni dai idan duk bugun mota zai kawo kaza da lemo, ni kullum ina yarda a bugeni sau ɗaya a sati!”
Su Dijee da Mairo suka fashe da dariya suka tafa, Haule ta ƙara da cewa,
“Indo wacce ke neman bugun arziki! Sai ki fara zuwa titi da safe ki tsaya kina jiran mota.”
Mama ta dubi su cikin dariya tace:
“To ku tsaya a raba kazar nan, tunda Indo ce ta sha wahala.”
Babu ɓata lokaci ta raba musu kazar da lemonta. Indo ta zauna da farin ciki tana ci tana cewa, “Ni dai na ji dadi, kaza ɗaya ta sa mutane uku suna ta tsalle kamar masu rawa!”
Da suka cinye, sai fa aka fara faɗa — Dijee tace, “Ai mu ma mun fita murna, ya kamata mu samu kazar mu.” Indo ta kalle su cikin zolaya ta ce:“Ku tsaya mota ta buge ku ma! kowa ya sami kaza tasa!” 🤣🤣🤣
Gaba ɗaya gidan ya kaure da dariya, har Mama ta kasa magana tana dariya tana hawaye,
“Indo haukar ke bata gayamiki gaskiya Amman ai kaza bazaifi lafiya daɗi ba "
To be continued......... the drama is beginning 🔥
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
🩺 DR SADEEQ 🩺
by
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739
CHAPTER 0️⃣5️⃣
2/ 11/ 2025
Wanan page in naku ne my fan's ina jin daɗin sharhin ku da addu'ar ku a kaina Allah ya bar ƙauna , much love to you guy's..
“The Day Destiny Screamed”
**“BABBAN DAMUWAR DR. SADEEQ”
Da misalin ƙarfe shida na yamma, Dr. Sadeeq ya kammala aikin sa, jikin sa har ya gaji.
ga ciwon kai sanadin ihu da hayaniyar Indo, sai kuma wahalar aiki da ta tara masa pressure tun daga asibiti.
Yana dawowa gida, ko sallama bai iya yi ba kai tsaye ya cire lab coat ɗinsa kamar wanda yake gudun ɗan iska, ya shiga wanka.
Ruwan sanyi ya sauka a jikinsa yana cewa:
“At least now, peace at last.”
Bayan ya gama, ya yi alwala cikin natsuwa, ya sa dogon riga jallabiya kalar ƙasa yana kamshi ya fita zuwa masallacin kusa.
duk wanda ya gan shi yana cewa da mamaki:
“Wannan fa ba irinmu bane kamar Balarabe ne wallahi.”
Haka suka ci gaba da sallah cikin natsuwa, shi kuma Dr. Sadeeq yana muryar karatun da ta kwanta a kunne bayan ya idar da sallah ya dawo gida da nufin ya samu hutu, ya kwanta a kan gado, yana jin daɗin shiru da sanyin waje.
sai ya lumshe ido yana niyyar yin baccin da zai biya hakkin gajiya amma kafin zuciyarsa ta natsu, sai kawai ya hango Indo a cikin mafarki tana birgima tana ihu kamar ɗazun ya buɗe idanu da sauri, yana haki:
“Oh my goodness! This dirty girl again?! ”
Sai ya dafe kai, ya tashi da fuskar takaici yana cewa: “Ganin ta kawai yasa na ce… I hate this place ta hanani sukuni, ta ƙara min pressure… wallahi ta zama ciwon kai!”
Sai ya kwanta yana juye-juye, bacci ya gudu gaba ɗaya, yana ta tunanin “Na rasa meye kuskure na a wannan garin da na haɗu da wannan ƙazamar yarinyar…”
Da ƙyar bacci mai nauyi ya ɗauke Dr. Sadeeq bayan daren gajiya da damuwar Indo asuba kuwa ya tashi ya yi sallah cikin nutsuwa, sai ya kwanta da niyyar “zan tashi da bakwai, kawai in huta kaɗan.”ai kuwa baccin ya wuce niyya.
Sai kawai aka ji kiran Atika tana ta kwala “Sir! Sir!!” daga ƙasa ya buɗe ido da sauri yana murza su, yana faɗin da tashin hankali:
“What?! I’m late!”
Ya zuba ido a agogo har 9:00 AM!
a cikin gaggawa ya farka kamar wanda aka zuba masa ruwan sanyi, ya shiga wanka da gudu ruwansa kawai ake ji tana faɗuwa a ƙasa, yana cusa brush a baki da hannun dama, da ruwan sabuku a hagu , yana fitowa da tawol a ƙugu a gurguje yasa kayan sa , idanu har yanzu sun cika da barci, sai ya ɗauki bakin medical glass dinsa ya saka yana fitowa Atika ta gaishe shi da fara’a tana cewa,
“Good morning sir!”
Ko amsa bai bata ba daman ta saba, idan yana da stress haka yake kamar mutum biyu ne a jikinsa..
Kai tsaye suka shiga mota.
yana tafiya cikin natsuwa, zuciyarsa cike da “ya Allah yau Wednesday — clinic day… mata masu ciki da yawa za su zo.”
koda suka isa asibiti, ya yi signing, ya saka lab coat dinsa, sai ya fara karɓar marasa lafiya daya bayan ɗaya.
Gidan magani cike yake da mata masu ciki — wasu na daurin zani, wasu suna da jariri, wasu kuwa na ta koka “Likita kai dai Allah ya saka da alheri…”
“Likita yanzu fa baccin baƙin ciki nake yi…”
shi kuma Dr. Sadeeq yana da murmushi kaɗan, yana aiki da natsuwa — amma cikin zuciyarsa, yana addu’ar Indo kada ta bayyana yau…
Indo da team nata suka fito su katsaya a dai dai bakin layin su ,chan saiga mai machine ya tsaya asibiti suka roge shi zasu bashi Naira saba'in da farko yace ɗari haka suka hau gaba ɗaya su bai ajiye su ko'ina ba sai bakin MODIRRE SPECIAL HOSPITAL suna isowa Indo ta gyara tsayawawar ta , " yauwa yanzu kai tsaye mu shiga zan nuna muku Dr Balarabe yau sai kungansa kyakkyawar Irrin Larabawa nan wanan Mutum min fa idan kun ganshi to shi ko tusa bayayi bare yayi fitsari kai mu shiga kugani da idon ku , "
A hankali suka fara shigewa sai ga wani ma'aikacin cikin shigar uniform Kore " yauwa don Allah Mallam ina zamuga Dr Balarabe wani fari kyakkyawar dogo haka " girgiza kai yayi don ya fahimci cewa Dr Sadeeq suke nufi wanda aka masa transfer emergency work for two months.
" What happened"? ya faɗa yana ɗaure fuska Indo ta zato ido kaga Mallam ba wani jin turanci nan muke ba juya ya buge ne da mota shine nazo yabani kuɗin kaza " sai yayi dariya ya ɗaga murya da ɗan ƙarfe kadan yana kiran " Security!!! Ku daina barin yara mabarata na zuwa cikin nan me aikin kune "?
ya faɗa yana juyuwa charraf Indo ta ɗaga murya " ƙarya ne wallahi ba bata muka zo ba ai kaine ƙaton mabarachi kana jiran masarasa lafiya suzo ka roge su kuɗi ai" security ya matso yana ta ce musu " kufita asibiti ba gun wasa yara bane " Indo ta dawo kansa da Dijee Haule da Mairo na ta leqe keke ku zasu ga Balarabe . " bazamu fita ba azo a bani hakkinna "
Security bai yi wata-wata ba, ya kamo Indo da ƙawayenta da bullala, yana tsala musu duka.
“Ku fita! Na ce ku fita daga asibiti nan kafin in muku kyau da bulala!”
Indo ta nufi ƙofar tana tafe tana tsalle, tana ihu kamar wacce aka kama da fashi.
“Kai kai kai! Wallahi idan na dawo sai na ɗauke fansa! Ni Indo bint Modirre, ba a doke ni a banza ba!”
Wani ɗan security ɗin ya yi dariya yana cewa:
“To a dawo mana, sai ki karɓi maganin bullala part two.”
ndo ta juyo tana daure fuska kamar ta fi kowa muhimmanci “Kai ba ka isa ba! Inajin ɗankwalina? Wannan dankwalin nan yafi albarkar uniform ɗinku!”
Ƙawayenta suna dariya suna ce mata “Indo mu tafi tukunna kafin su dawo!”
Ta yi tsaki ta ce “Ku bari in gama rantsewa. Wallahi sai na dawo! Wannan kyakkyawan Balaraben da suka ce ya tambaye mu — in dai har duniya bata ƙare ba, sai na same shi. Sai ya san ya buge ne da mota !”
Suka tafi suna gudu, Indo tana ta magana tana kiran kansa “Kai Indo, jaruma! An doke ki, amma baki faɗi ba. Sai dai fansa!”
############
ABUJA
“Rahama gaskiya baki kyauta min ba!”
Nabila ta faɗa tana kallon screen ɗin wayarta da fuska a daure.
“Yaya zakiyi min haka? Kina tura min littafi ba complete ba! Wallahi littafin BAYAN WATA ina cikin karantawa sai kawai marubuciyar tace ce ‘a haɗu a sabon