An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
🩺 DR SADEEQ 🩺
Story and writing
by
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739
CHAPTER 0️⃣1️⃣
بسم الله الرحمن الرحيم , اللهم صل على النبي محمد صلى الله عليه وسلم تسليما كثيرا.
Sometimes, destiny brings you love in the most unexpected way
When a doctor heals with love, even pain becomes laughter.” 🩺
THIS STORY IS LOVINGLY DEDICATED TO MY SWEET, BLOOD, SISTER AISHATU INDO...
AND BELOVED BLOOD BROTHER ABUBAKAR SADEEQ.
THIS ONE IS FOR U BOTH'S
MAY ALLAH CONTINUED BLESSINGS U ALL WITH HIS MERCY GRANT YOU JANNATUL FIRDAUSI
AMEEN
MUCH LOVE
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
Typing...📲
ADAMAWA YOLA SOUTH MODIRRE
Cikin wata ƙaramar farfajiyar makaranta da ya malllake class guda ukku da yara dake wasa suna waƙoƙin suna rawa suna ta ɗibo ƙura tamkar babo malamai ko manya manyan cikin su ,
" Ayyari iye alagiddibo , Ayyari iye alagiddibo, alagiddibo alagiddibo Babo ruttu (alagiddibo".) " Inda nice mai kuturu "!
( To da kice matar kuturu )
idan ina ɗinki to zan fasa ƙwarya da gangan gangan "
( alagiddibo )
" inya ɗinka muyi aure in bai ɗinka ba a bakin auren sa kinan alagiddibo"
" Ga Mallam Ga Mallam " tsitt kake ji tamkar babo masu wakar gaɗa a cikin wannan dandalin makarantar duk sun nitsu yara ne da ba zasu haura shekaru goma sha biyu ba duk sunyi ƙura da dutti kamar ba ruwa da sabulu a duniya lallai da Company masu tsabtace tsabtace jiki da muhalli sun san da zaman wanan ƴan matan dandalin to ba ƙaramin roba zasu samu ba domin duk cikin su Babo wacce zaka gani ka maimaita kallon ta saboda ƙura da ke jikin su tamkar zumar tawadda aka shafa musu
A yanda ya shigo Babo fara'a a fuskar sa nan ya tabbatar musu da cewa sun shiga ukku domin tsaff Mallam Isa ya gansu juyawa yayi ya zaƙulo wata shigiyar bulallar sa mai baki biyu, duk kufotto nan mara kunyar yara nan islamiyya ne ko dandali lallai yau zakuci ubanku " a hankali suka fara marai marai da ido sauran ɗalibai sai dariya sukiye suna toshe bakin su Mairo ce gaba da Haule sai Dijee ta biyo bayansu, chan yayi dogon wuya da aswakin bakin sa ( yana sanye da wata kuɗaɗiyar dogon jallabiya da dogon charbi a hanun sa ya karkatar da hular sa yana muzirai " Ina shugabar mara kunyar taku " kifitoo kunazo nachi ubanki "
Chan Buba yace Mallam gata nan a bayan dutse chan " Zaki fito ne ko sai nazo " bai rufe baki ba sai gata nan ta santalo dogayen ƙaffaunta da suka fusata da rashin ruwa da takalmin duk faso ta yachinye su ga gurza gurza a yatsunta tamkar wacce ta fito daga sansanin manoma ƙaramin bakin ta ta ya mutsa kamar mai raɗa duk ya bushe sai fata da ya mammane akai, tana da sirrin hanci da kyawun gashin gira da ganin goshinta akaiw alamar tambaya domin gashi ne kwance liff luff Irrin na Fulani .
" Wallahi wabillahi lazi Buba zakaci ubanka idan Mallam ya zanane " tana magana wari ne ko karni ke fitowa a bakin ta haƙuran fa duk sun sauya zuwa ruwan ɗuraawa fitowa gaba d'aya taye duk dacewa farace Amman zaka rantae wanan halittar baƙace ga manyan manyan ido da take zarowa Buba, kamar zasu fito fili suye bayanin halin da take ciki .
AISHATU INDO kinan yarinya ce kyakkyawan bugun farko ƙazama number ɗaya babo wanda baisan Indo a duk faɗin ƙauyen Modirre ba salon ta da haukarta suka jawo mata suna fitina da tsokana Babo abinda zai sa kaga nitsuwar Indo sai bulalla a rayuwar ta idan ka cire Kadangare to tabbas sai bulalla take tsoro ƙawayen ta ukku ne , Haule da Mairo sai Dijee.
tana ƙarasowa Mallam Isa ya basu Bulala biyar biyar sai kuka sukiye amman Indo kam na ciza baki don batason raini Babo mai ganin hawayen ta don juriya ana gama musu bulalla Mallam ya ɗauke abin rubutu ya rubuta musu KITTABUN ( LITTAFI ,) QALAMMUN ( AL ƘALAMI ) SAIYYARATUN ( MOTA ) a take ya umurce su da rubutu ya fita ana buga ajin ƙarshe suka tashe kai tsaye Indo tana ƙawayen ta zuwa gida suna tafiya suna jan wa Mallam Isa
, "Allah ya isa mugun malami watarana sai mu saka kuka yanda kake sa mu kuka" cewar Dijee Indo ce ta tsaya chak takama wani hanya kamar lungo bayan panpanpam ruwa ta tsaya tana jiran Buba ya yanki hanyar yana " Kittabun littafi " bai ankara ba yaji wufff Indo ta chukumu wuyar sa nan su Dijje suka taya ta suka hau jibgar sa yana ihu yana kiran taimako mutane "
Mallam Yusuf mahaifinsa yazo da gudu Indo na hango su suka rufta cikin lungu da gudu ba waiwaye yana isowa yana zagi " yau Indo sai kinsan ki lakaɗawa yarona dukka yau sai naga mai rabani da dukkan ke wallahi sanyi maganin ku ƴan iskan yara yana yaron sa suka shiga gida yana ta sababi da ihu
Indo na ganin sun tsira ta shiga gida kai tsaye ganin ba kowa hanyar kitchen ta nufa kwanon ta ta ɗauka dambu shinkafa ne da zogale ko wanke hannun ta bayar ba hannu baka hannu ƙwarya tace don tana sauri kar Mama ta shigo ta gabata fita waje tana gamawa tasha ruwa ta fita a guje ana dafff da kirar sallah mangariba ta tsaya a ittace sai ga
Team nata sun nufa suna dariya tace kun shirya ko baku shirya ba don wallahi billahi lazii tsoron Uban Buba nake wanan jibgiggin ƙaton bashi da tausayi gwanda muyi rigakafi kafin magani a tare suka ce MUN SHIRYA
" LET'S GO "
Tace ta shafa abin da yazo dashi daga gida ta buɗe bayan rigar ta haka suka shafamata suna ta hakkin kai tsaye suka nufi gidan mai unguwa sai murza idon ta takiye wanda ya lafta masa barkono don taye hawaye " Waiyoo Allah na shiga ukku Waiyoo Dijje ku rigi ne Mallam Yusuf ya kashe ne yau da dukka duk aka tsaya cirko cirko Mai unguwa da ya fito daga bayangida jin sautin Indo yasan Yau kuma akwai case a gidan sa yana tattaki ya fito " ke Indo lafiya kike ta zabga uban ihu Kamar ana cire miki ido."?
"Kawai don a Islamiyya munyi faɗa da Buba shine ya zagi ne na rama ya harba min dutse shine munaye dambe Mallam Yusuf ya kamani yamin dukkan kamar zan mutu ga shaida ma , kuma a tambaya su Dijee"
Duk zaro ido sunaye suka amsa da sauri basu taɓa kawo cewa wanan ƙatuwar sharri zataye ba , basu kaɗai ba harda Mallam Yusuf Da yau kam ya gaji ya kawo ƙarar Indo"
"Amman yarinyar nan baki da kunya Yanzu rashin kunyar take hardani Indo " ya faɗa cikin mamaki Da tsoron yaran yanzu , mai unguwa sai ya tsaya jimmmm liman ya fara korar sallah nan mai unguwa yace " ku tafe gida gobe zamuyi maganar dashi kiye ha'kuri kinji " ya faɗa da sigar rarrashi duk girgiza kai sunaye don su san wanan hukunci ya wuce kinan mai unguwa baya taɓa hukunta Indo asali ma yana ɗaure mata a duk lokacin da ta jawo magana ko sharrin ta ...
WACCE CE AISHATU INDO
Wanan shine asalin ta an haifi ta rana mai daraja da girma 27 ga watan Ramadan mahaifin ta Allah ya masa rasuwa tun tana cikin mahaifiyar ta, ta taso cikin maraice da kulawar maman ta wacce ta shagwaɓa ta a rayuwar ta ganin ita kaɗaice ƴar da Allah ya bata Mai unguwa yaya ne a gun mahaifin ta wato Baffan ta tana da ƴan uwa sosai a cikin wannan ƙauyen tana zuwa Arabiyyar Mallama Larai , ga islamiyya boko kuma , tana aji biyu har yanzu , Domin rashin karatun ta kullum tana aji ɗaya ta kasa gaba kullum sai baya Baya
A taƙaice wanan ittace Indo .................
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
🩺 DR SADEEQ 🩺
Story and writing
by
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739
CHAPTER 0️⃣2️⃣
بسم الله الرحمن الرحيم , اللهم صل على النبي محمد صلى الله عليه وسلم تسليما كثيرا.
Sometimes, destiny brings you love in the most unexpected way
When a doctor heals with love, even pain becomes laughter.” 🩺
THIS STORY IS LOVINGLY DEDICATED TO MY SWEET, BLOOD, SISTER AISHATU INDO...
AND BELOVED BLOOD BROTHER ABUBAKAR SADEEQ.
THIS ONE IS FOR U BOTH'S
MAY ALLAH CONTINUED BLESSINGS U ALL WITH HIS MERCY GRANT YOU JANNATUL FIRDAUSI
AMEEN
MUCH LOVE
29 / 10/ 2025
Hasken safiya ya shiga cikin dakin Dr. Sadeeq mai tsabta da kwalliya, yana haskaka farfajiyar tsantsi, bango fari, da wani makeken farar gado an ƙawata shi da hasken fari , shimfidar kawai abar kallo ne Labuloli masu haske sun rataye a tagogi, suna bari rana ta lullube dakin da haske mai nutsuwa. A gefe guda, glass table mai kayan ado na kayan karya ya kasance cikin daidaito — vase mai furanni, statuettes masu ƙyalli, da wasu ƙananan kayan kyautatawa, suna ƙara ƙyalli a cikin dakin.
Dr. Sadeeq ya zantalo da dogayen ƙaffaunsa daga gado, zazzafan saurayi mai ƙirar gym, Gashinsa a ƙirji yana lankwasa cikin haske, fuska mai nutsuwa da murmushi mai sirri. Tsokoki a ƙirji, ciki, da hannaye suna bayyana sosai — six-pack abs, biceps da chest muscles sun nuna ƙarfi da kyau, duk motsinsa yana da nutsuwa amma har yanzu sexy aura yana bayyana a jikin sa.
Ya wuce zuwa toilet ɗin fari, tiles masu haske suna haskaka komai, sink da mirror masu girma suna nuna hoton sa, towels fari a rataye cikin tsari, Ya shiga cikin dumin ruwa mai kyau, bubbles suna rawa a jikinsa, gashinsa a ƙirji yana lankwasa da sajen fuskarsa.
Bayan wanka, ya ɗauki towel fari, ya shafe jikinsa a hankali, har gashinsa a ƙirji yana haskakawa. Sai ya ɗauki shirt da pants duka fari, duka masu tsabta da kyau. Yayin da yake saka shirt ɗin, tsokoki a chest da ciki suna bayyana sosai, biceps da forearms suna motsi da kyau yayin da yake ɗan juyawa. Pants ɗin fari sun dace sosai da thighs da calves, suna haskaka symmetry da kyawun jikin sa.
Bayan ya gama saka kaya, Dr. Sadeeq ya ɗauki fruit platter daga countertop: strawberries, mango, da wasu kayan fruit masu launi. Ya ɗauki strawberry ɗaya, ya ɗan latsa a yatsunsa, ya ɗan kallon mirror, murmushi mai sirri a fuska. Sai ya ɗauki ɗan bites cikin nutsuwa, juice ɗin strawberry ya ɗan ja launi a leɓɓansa.
Yana ci cikin style mai kyau, idanuwansa a mirror suna kallon reflection ɗinsa, yana jin daɗin nutsuwa da sirrin sa. Ko da a cikin wannan ɗan lokaci na breakfast, Dr. Sadeeq ya bayyana jarumi mai kyawun jiki, style na musamman, da aura mai jan hankali,
Bayan ya gama cin strawberries da sauran kayan fruit, Dr. Sadeeq ya ɗan ɗan gyara hair ɗinsa a mirror, murmushi mai sirri a fuska. Ya ɗauki coffee cup daga gefen countertop, ya ɗan shanye kafin ya ajiye a gefen table , kayan sa ya sanya wand ya kasance komai fare ne ya ja drawer ya zaɓi agogo hannu Black wanda ya kasance ya tafe da takalmin sa ,
Nan ya ɗauki bag ɗin doctor daga tebur, ya sanya shi a kafadarsa cikin nutsuwa, yana ɗauke da confidence da aura mai jan hankali. Ya ɗan tsaya a gefen mirror da cewa " Alhamdullah" Kowanne motsi yana nuna ƙarfin sa, natsuwa, da kyawun jiki mai ban sha’awa,
Dr. Sadeeq ya fito daga dakin sa cikin takun isa da ƙasaita, yana tattaki cikin nutsuwa kamar ba ya son takawa cikin kassaita da izza hankali, amma duk wanda ya kalli motsinsa zai gane cewa jarumi ne mai ƙarfin hali da aura mai jan hankali masu aiki biyu da suka gaisa da shi sun yi ƙoƙarin kallon sa, amma Dr. Sadeeq bai ɗauki su da idonsa ba, baice komai ba, ya tattara hankalinsa kawai a tafiyarsa.
Direct ya nufi gidan sama, dakin babban parlour ,haske mai kyau yana shiga daga tagogi masu laushi, tiles masu tsabta da labuloli masu launi mai nutsuwa suna ƙara jin daɗin tafiyarsa. Ya nufi babban parlour, inda ya hango wata kyakkyawar mata zaune cikin ladabi.
Yana zuwa har kusa da ita, ya durgusa a hankali, fuska cike da ladabi da nitsuwa. Ya gaishe ta da murya mai santsi:
"Assalamu alaikum, Momma Sabahur khair ."
Matar ta ɗan murmusa, tana mai kyakkyawar nutsuwa da albarka a fuska, ta amsa cikin ladabi "Wa alaikum assalam, Doctor Alhamdullah kaifa lakka "
Dr. Sadeeq ya ɗan juya, ya hango Daddy na sauko daga ɗaki, fuska mai natsuwa da mutunci. Ya gaisa da shi cikin ladabi:
"Assalamu alaikum, Daddy gd morning ."
Daddy ya amsa da murmushi, kuma dakin ya cika da natsuwa da kwanciyar hankali, yayin da Dr. Sadeeq ya tsaya kadan, yana kallon kyakkyawar matar da nutsuwa duk motsinsa, durgusa da ladabi, suna nuna kyawun halaye da nitsuwar sa.
Bayan gaisuwa da Mommy da Daddy, Dr. Sadeeq ya ɗan tsaya kadan, murmushi mai ladabi a fuska, ya ce: "Zan fita aiki, insha Allah zan dawo ku sami albarka."
" A dawo lafiya doctor Allah ya taimaka " sai ya juya, yana ɗauke da bag ɗin doctor, sannan ya fito daga gidan sama cikin takun isa da ƙasaita, tafiyarsa cike da nutsuwa Duk masu aiki da suka hango shi, sun tsaya da kyau, amma Dr. Sadeeq bai damu da kowa ba — zuciyarsa tana kan tafiyar da zata kai shi wajen aikin sa.
Ya isa white Benz sabuwa, motar tana haskakawa a rana kamar zinariya, duk da tsafta da kyau na motar. Ya buɗe motar, ya zauna cikin nutsuwa, kafin ya fara addu’a cikin zuciya, yana rokon Allah ya sa aikin sa ya kasance mai amfani, lafiya, da albarka .
Maigadi ya rufe gate sa, motar ta tashi cikin sauti mai laushi, hasken rana yana shewa a fatar motar, yayin da Dr. Sadeeq ya shiga hanya. Kowane motsi, yana bin surutul Maryam cikin nitsuwa da ƙwarewar karatu
Bayan wani ɗan lokaci, ya isa babban asibitin Federal Hospital of Abuja. Motar ta tsaya a kofar asibitin, Dr. Sadeeq ya fito ciikin ƙasaitar sa kallo mai natsuwa da mutunci a fuska. Duk wanda ya hango shi zai fahimci cewa wannan saurayi mai ƙarfi, mai kyau, da sirri yana shirin yin aiki mai muhimmanci.
“Ƙawata ga Doctor Sadeeq ya iso wallahi guy nan ya haɗu — anya akwai wanda ya kaishi iya wanka da salo a kaff hospital nan?”
“Hummm, Nabila kinan! da kin san yadda nake jin sa, da kin gane cewa wannan likitan ba kawai doctor ba ne — shine dream na zuciyata. Idan na kalle shi, kamar na ga allurar da zata warkar da soyayya ta…” Atika ta faɗi tana ɗan gyara hular nurse ɗinta, zuciyarta kamar zata bugo ta fito.
Nabila ta ɗan turo baki, “Ke dai Atika, kin fara mafarkin mijin mutane kafin ya aure ki ko?!”
Atika ta kwafa, ta ɗan zuba turaren wuta a gefe, tana cewa, “Na fa rantse, sai na mallake sa, ko da da prescription na soyayya ne zan bashi. Ni da shi sai dai Allah ya raba.”
A wannan lokacin kuwa Dr. Sadeeq yana nesa, yana tafiya cikin nutsuwa, white coat ɗinsa yana tafe da iska kamar wani superhero, idanuwansa na ƙasa amma kallo ɗaya daga gare shi ya isa nurse ɗaya ta kasa magana.
Nabila ta ɗan girgiza kai tana cewa, “Kai Atika idan wannan Dr. Sadeeq ya fara magana da mace, zuciyarta sai ta yi beep beep kamar ECG machine fa.”
“To shi ne fa! Ni ma zuciyata ta dade tana bugawa saboda sa!” Atika ta amsa tana dariya.
“Kinga dai gaskiya, sai ki tashi ki tafi aikin ke ke bisa kafin matan likitochi su fara yi miki surgery da kishi!”
To be continued.......
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
🩺 DR SADEEQ 🩺
by
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739
CHAPTER 0️⃣3️⃣
Typing...📲
30/ 10/ 2025
Wanan page in naku ne mu fan's ina jin daɗin sharhin ku da addu'ar ku a kaina Allah ya bar ƙauna , much love to you guy's..
WAYE DR. SADEEQ?
“Mutumin da yake da nutsuwa fiye da kalmomi.” Dr. Sadeeq — matashi ne mai shekaru Talatin da haihuwa, mutum mai kwarjini, ilimi, da natsuwa yayi karatun sa daga primary har secondary school a private university Abuja anan ya samu ya tafe chan ƙasar India yayi karatun degree da master's yayi internship da dukkan wasu nau'in karatu sai da ya kammala ya dawo gida .
Bashi da wani aboki a rayuwar sa sai Dr Kamal , tun yarinta sun tashe tare har ta kai ga sunyi karatu course ɗaya sun kamala yanzu dukkan su biyu manyan likitoci ne masu faɗa aji , Kamal mutum ne mai haƙuri Amman akwai zolaya da surutu tun Dr Sadeeq bai saba dashi ba , har suka sabà daya baya zama sai da ɗayan , haka suke rayuwar su cikin jin daɗi da kwanciyar hankali...
Asalinsa bakano ne amma ya taso ne a Abuja, inda iyalinsa suka kafa gida mai ɗaukaka da mutunci.
Mahaifiyarsa, Hajiya Zainab, uwa ce mai ƙarfin hali da kulawa, wacce ta tarbiyantar da Sadeeq da ‘yan’uwansa Na’eema da Nazifa cikin ladabi da tsantsar ilmantarwa.
Shi ne ɗa namiji kaɗai a gidan Alhaji Mu’azzam — wanda mahaifiyarsa ta kasance uwargida.
Amaryar mahaifinsa, Hajiya Binta, tana da ‘ya’ya uku mata — Layla, Na 'iba , da Sakina,
amma duk da bambancin uwa, Dr. Sadeeq yana kula da su kamar cikakkun ‘yan’uwansa, yana nuna musu ƙauna da adalci.
Duk su ‘yan Kanawa ne Hausawa, masu kyakkyawar alaka da juna, suna rayuwa cikin walwala da nasara a Abuja.
Gidansu gida ne da tarbiyya, girmamawa, da ilimi suka mamaye — sai dai kamar yadda Hausawa ke cewa “ ɗan aman tara yaki cika goma.”
Matsalar su ita ce — Alhaji Mu’azzam da Hajiya Binta sun daɗe da ɗabi’ar tsananta wa talaka su kan ɗauki girman kai da matsayin su a matsayin iyaka — ba sa so a kusance su da talaucin rayuwa.
Wannan ɗabi’a ta yi ƙarfi har ta zama kamar siffar gidan gaba ɗaya.
Sai dai Dr. Sadeeq ya bambanta da su.
Shi mutum ne mai zuciya mai tausayi, natsuwa, da gaskiya.
Baya son hayaniya, baya son rashin tsabta, kuma baya yanke hukunci cikin zafi yafi so ya gyara da ladabi maimakon fada.
A wurin talaka, shi ne mafaka — ko da iyalinsa basu ganin haka.
Wannan kyawawan halaye sun sanya shi mutum mai jan hankali,
mutum da kowa yake girmamawa, amma ba kowa yake fahimtarsa ba a asibiti, ana kiransa da suna daya “The Calm Doctor.
BACK TO STORY
Bayan ya gama round a asibiti, Dr. Sadeeq ya koma ofishinsa jikinsa ɗan gaji ne, amma