Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
maƙoshi, tana nan zaune kafin ta shiga sai ga wata mata nan da ka ganta kasan kuɗi sun zauna mata sosai, domin ko suturar jikinta ma kaɗai abar kallo ce, Ayla bin ta kawai take yi da ido, tana ayyana inama ita ce, musamman yadda ta ga tana zuwa ta shiga wajen likita. "Shegiya naira." cewar Ayla tana hasaso kanta a matsayin matar, har matar ta fito layi yazo kanta tana tufka da warwara. Bayan tambayoyi likuta ya turata wasu gwaje-gwaje ciki kuwa har da na juna biyu, ita dai jinsa kawai take dan tasan babu yadda za ayi ta samu wani ciki, tunda tana tsarin iyali ta hanyar shan ƙwayar maganin tsarin iyalin, kuma bata fashin shan maganin, hasalima ita yaushe rabonta ma da Nazeer tana jin a ƙalla anyi sati biyu zuwa uku. Haka dai taje aka yi mata tasa-tasan ta kawowa likitan sakamako. "Congratulation madam kina ɗauke da juna biyu, sai kuma bp ɗinki da ya yi ƙasa kaɗan amma zan ɗoraki kan magunguna in sha Allah komai zai zama normal." Tunda ya ambaci kalmar juna biyu ta daina fahimtar komai, ta yaya ma haka zai faru, wallahi ba zata saɓuba ai kuwa sai ta zubar da cikin nan don har yanzu ba ta shirya haihuwa ba, yaushe ma akayi daren da har gari zai waye. "Amma na ce da man likita ana iya samun ciki kuma ana yin tsarin iyali" Murmushi kaɗan likitan ya yi, yana dubanta kafin ya ce, "Ƙwarai ma, ai tsari yana wajen Allah, idan baiso mutum ya huta ba to kome zaiyi ba zai huta ɗin ba, sau da dama wasu mata kanyi ƙorafi akan sun saka implan amma sun samu ciki, ko mace tana allura ta samu ciki wannan kuma duk cikin hukuncin Allah ne." Wani numfashi ta sauke ba ta ce da likitan komai ba, haka ya rubuta mata magunguna tare da ba ta wasu shawarwari saboda jininta da ya yi ƙasa, da kuma kare lafiyar abinda take ɗauke da shi, ita dai jinsa kawai ta yi don tayi rantsuwa cikin nan bazai zauna ba balle ma akai ga haifarsa. Haka ta wuto gida ranta a dagule, ta yi niyar biyawa gidansu amma sai taji ta fasa ranta a ɓace ta dawo gidan tana jira Nazeer ya dawo ayi wacce za ayi. BASH Cikin hukuncin Allah sai ga shi ankai kuɗin aurensa har da sanya rana wata biyu masu kamawa, kasancewar kowanne tsagi a shirye suke sai hakan bai ba su matsala ba, ai kuwa Bash da Fatu sun yi murna sosai da man sun tsara haka sai dai ba su zata abin za su same shi ta sauƙi, don sun yi tsammanin za a ƙara akan wata biyun. Duk wani rigima da tashin hankalin Yasira bai sa an fasa ba, ƙarshe ma takanas hajjo ta taka tazo gidan ta dinga lallashinta tare da nuna mata auren da zaiyi ba shi ke nuna ba ta da ƙima da daraja ba, kuma tana da tabbaci yana sonta koda kuwa zai yo mata kishiya. Ba wai don ta gamsu da zancen hajjo ɗin ba, sai dai kawai don taga babu yadda zata iya, amma fa ba wai ta haƙura ba ne, alƙawari ta ɗauka ba za ta zauna da kishiya ba, za ta sauya salo, tana nan tana jiran wacce ta yi gigin cewa za ta shigo ɗin da sannu za ta saita mata hanya ta koma inda ta fito, don ta yi rantsuwa ko kaffara ba za ta yi ba, Bash ba zai zauna da wata ɗiya mace bayan ita ba. Bash ya yi mamaki sosai da yaji ƙurar Yasira ta d'a lafa, ya ga ta saki ranta ta mayar da komai kamar ba komai ba, ita ce har da tambayarsa a ina zai ajjiye matar. "Bana da burin raba kan iyalaina, a nan za ta zauna za a gyara ɗaya sashen ne, ko Kuma a gyaran can dakin ya zamana falonku ɗaya kicin ɗaya" "Uhmm" ta ce masa, shi kuwa ya shiga washe baki, har yana faɗin, "Wallahi Yasira na ji daɗin yadda kika watsar da komai, na gode miki Allah ya saka miki da gidan aljanna. In sha Allahu ba zan bari ki wulaƙanta ba" Amin ta amsa masa a taƙaice tana zamewa ta kwanta, daman a jingine take jikin fuskar gado, shi kuma yana daga bakin gefen gadon. Bin ta ya yi da kallon tausayawa, yasan dole za ta ji babu daɗi, amma zai yi ƙoƙari ya cigaba da kwantar mata da hankali, zai kuma kiyaye mata mutumci da darajarta ba zai bari Fatu ta shigo gidansa ta wulaƙanta ta ba ko babu komai ita ce ta fara sanin sirrinsa, kuma yana jinta a cikin zuciyarsa don a yanzu idan har ya ce baya son Yasira to shima yasan zance ne ya faɗa da babu bakin kamawa. Da wannan tunanin ya miƙe ya faɗa banɗaki, Yasira ta bi shi da harara tana jan siririn tsaki ƙasan zuciyarta kuwa babu abin da take binsa da shi face baƙaƙen maganganu, ita mamakinsa take yi ma yadda yake wani rawar kai kamar bai taɓa aure ba, lallai ɗan adam butulu mai manta halacci, duk haƙurin zama da shi da tayi bai duba wannan ba, ta tuna sanda aka aura mata shi aka rabata da manemanta, suka zauna dukansu basa son junansu yadda da fari ya fara ƙuntata mata ita kuma tana ƙoƙarin ganin farin cikinsa har Allah Ya sa daga ƙarshe ta samo kansa shi ne amma ya manta da wannan, shi ne yanzu Dan zai auri wata matar shi ne yake yi mata rawar ƙafa, lallai ciki mai manta gobe, ƙwafa ta yi tana ayyanawa a ranta ayi bikin yadda yarinyar zata shigo da ƙafafaunta haka zata fita da ƙafafunta dan ba zata taɓa bari wata ɗiya mace ta zauna mata da miji ba, idan rabon haihuwa ya tsaga ma shi kenan ita ta zama hotiho ko, ita kuwa abin da ba zai taɓa faruwa ba ne alwashi ta ɗauka babu wata mace da za ta raɓu Bash ɗinta har abada. AHMAD Kwana biyu da maganarsa da mom nasa amma ya gaza tunkarar gidansu Zahida, sai ya yi nufin haka sai wata zuciyar ta ce ka ƙyaleta da kanta zata dawo, ko kuma mahaifinta ya koro ta kamar yadda ya saba. Sai dai kuma haka nan yake jin wata kewarta da bai san daga ina take fitowa ba, duk da wani sashi na zuciyarsa na ba shi ba ita yake kewa ba kawai abin jikinta yake kewa saboda duk duniya shi shaida ne Zahida ta fita daban, tana gamsar da shi sosai fiye da yadda yake hulɗa da matan waje, hasalima aurenta shi ya fara rage masa bin mata, saboda duk wacce zai kusanta sai ya ji ta salam ba irin Zahidansa ba, ga kuma abincinta da shima tabbas yasan ya yi missing ɗin shi. Mirginawa ya yi kasancewar yana kwance kan lafiyayyen gadon da ke ɗakin, yana sakin hucin iska, dole nema yaje ya dawo da ita, da wannan tunanin ya miƙe ya faɗa banɗaki don yin wanka, yana fitowa ya sauya kaya ya feshe jikinsa da turaruka masu ƙamshi ya ɗau mukullin motarsa ya fice daga gidan, kai tsaye gidansu Zahida ya wuce duk da yadda wani sashi na zuciyarsa na ba shi gurguwar shawarar ya juyo, amma haka ya danne ya nufi gidansu kai tsaye ba tare da wata fargaba ba. To fa,ƙaƙa-ƙara. Mene ne zai faru da Ayla da cikin jikinta? Shin Ahmad zai samu nasar bikon Zahida? Shin Zahidan za ta yarda ta dawo ko kuwa za ta juyawa roƙonsa baya? Ya ya zata kasance da auren da Bash ke son yi? Ya ya zai yi da rigimar YASIRA? Shin da gaske ne ta kwantar da hankalinta ta amince ayi auren? Shin Wahida za ta samu abin da take so na cinma muradinta? Ku dai biyo ni, cikin wannan littafi nawa mai taken ƘARIN KUNAMA domin jin yadda za ta kasance, kar ku manta ba a soma ba,yanzu ne za a fara wasan. Za ku iya tura #700 akan wannan asusun 8160675983 opay, Maryam Abdulaziz. Maiƙosai 08160675983 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6