Bash ya faɗi yana dafe goshinsa, shi yasa yaso yin shiru da bakinsa sai dai Hajjo ta nusar da shi wannan sam ba mafita ba ce gwara ya faɗa mata ayi komai a wuce wajen, yanzu ga shi ya sanar da ita ga kuma abinda hakan ya haifar, bai san ma ta ina zai soma rarrashinta har ta fahimce shi. Ganin zaman ba zai amfanar da shi komai ba yasa ya yi ƙundunbala ya bita, tana kwance kan gado sai rasgar kuka take yi, a hankali ya ƙarasa inda take ya miƙa hannunsa kan saman gadon bayanta da nufin rarrashi sai dai cikin wani ƙaraji da tsantsar masifa ta ɗago kanta ta soma yi masa magana a tsawa ce.
"Dont touch me Bash, na tsaneka na tsani mai irin sunanka ma ka tashi ka fitar min a nan idan ba haka ba wallahi sai na yi ajalinka."
_Wannan littafin na kuɗi ne akan #700, idan ya zama complete 1k_
8160675983
Maryam Abdulaziz
Opay
Maiƙosai
08160675983
[10/12, 9:27 AM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA
©Maiƙosai
Book 1
BABI NA SHIDA
AHMAD
Tun da zahida ta saka ƙafa ta fice daga gidan yake sababi don koda ya fita ma kasa zaman wajen yayi haka ya dawo gidan yana ta surfa tijara kamar ya ari babu yaci, koda yake hakan baya rasa nasaba da yadda Haulat ke ƙara tunzura shi, kalamanta su suke sake ji mishi cewa lallai Zahida ta raina shi ba kaɗan ba. Zumbur kamar wanda aka tsikara ya miƙe ya zira rigarsa ya ɗau mukullin motarsa ya sake ficewa daga gidan kaitsaye kuma gidansu ya nufa, Haulat da ke kwance tana waya da saurayinta Junaid, sai ta katse wayar ta miƙe tana ɗaukar gyalenta tare da baro cikin gidan, ƙofar ta janyo kasancewar mai jamulak ce idan kaja daga waje ka rufe ta rufu idan za a shiga sai da mukulli, bata tsaya tunanin komai ba ta wuce gidansu dan dai kam ita ba ta jin zata iya zaman gidan, gwara ta tafi nasu gidan, haka ta nufi hanya zuciyarta cike da maɗaukakin farinciki abin da ta jima tana jira ne sai gashi yau ya faru, duk da ba wannan ne karon farko da Zahida ta taɓa zuwa gidansu ba amma tana fata wannan ɗin ya zama na ƙarshe, tana fata ba zata sake raɓar musu ɗan uwa ba.
Tana shiga gidan a farfajiyar gidan ta iske motar yayan nata Ahmad, haka ya nuna mata wajen momy yazo,ai kuwa da sauri ta sake cilla ƙafa tana fata ta iske zancen da suke yi domin tasan babu makawa zancen Zahida zai yiwa mom.
Ai kuwa hasashenta ya zama gaskiya, domin tana shiga falon muryar mom na dira cikin kunnuwanta, sai dai zuciyarta ce ta ji na neman tsinke da jin kalaman mom nasu, ita da take fata zahida ta tafi kenan sai ga shi mom na neman ɓallo mata ruwa.
"Idan har ba so kake ranka ya ɓaci ba Ahmad ka tashi ka nufi gidansu kayi gaggawar dawo da ita na faɗa maka."
"Amma mom kin san kuwa mene ne ta aikata min, mom yarinyar nan ta riga totally ta zama..."
Katse shi tayi ta hanyar furta masa,
"Bana so na san kome ta aikata maka, wallahi ko kaffara ba zan yi ba kai ne mai laifi Ahmad, ka tashi min a gabana tun kan ka kai ne bango."
Da sauri Haulat ta ƙaraso falon tana faɗin,
"Mom daga gidan nake a gabana aka yi komai wallahi baki ga yadda..."
Wani kallo ta watsa mata wanda ya daskarar da sauran kalmomin nata ta kasa ƙarasawa, fuu ta wuce zuwa ɗakinsu tana kunburu baki,tana jiyo maganar mom na faɗawa Ahmad,
"Zaka ɓace min daga gabana ko kuwa?"
Bata iya jiyo me ya cewa mom ba ta ƙarasa shigewa ɗakin. Kaitsaye kan makeken gadon ɗakin da yazama mallakinsu ita da 'yar Yaya Saudat Na'ima ta nufa tana mai rubda ciki akansa. Ko kallon inda take Na'ima da ke zaune kan stool tana duba wani littafi ba ta yi ba, sai ma taɓe bakinta da tayi ta cigaba da aikin gabanta, ita kuwa Haulat ji take komai ya tsaya mata caak, bata da wani buri nata fa ce ta raba Zahida da yayanta, amma har yau ta kasa cinma wannan ƙudurin, sai komai ya kusa kammala sai ya koma baya komai ya tarwatse. Tsaki taja babu adadi tana gyara kwanciyarta da tunanin ta inda zata sake ɓullowa da lamari.
Shi kuwa Ahmda bai musawa zancen mahaifiyartasa ya miƙe ya fi ce daga gidan, da man yazo ne ya sanar da ita Zahidan tana gidansu kuma hakan na nufin ƙarshen zamansa da ita yazo sai dai bai samu goyon bayanta ba, kuma ba zai iya tsallake umarnin da ta basa ba, zai je yayo bikon Zahidan amma wallahi sai ta gane cewa shayi ruwa ne da wannan zantukan ya fi ce daga gidan zuciyarsa a ƙuntace.
AYLA
Tana nan kwance tana aikin taɓe-taɓen wayarta Hasina ta gama komai, ta dawo falon ta shiga gyara shi.
"Sannu fa sis, yo wannan uwar aiki ba dole in sake dagewa a kawo mai aiki ba, don Allah jibi fa yadda kike zufa ba dole ma na san abin yi ba, shi yasa fa kin ganni nan wallahi ko shekara gidan zai yi ba zan kalleshi ba, zan iya saka hannu dai in matsar da abinda ya tokare ni shima idan ba mai takura ba ne sai in barshi inda yake."
Wani kallo Hasina ta bita da shi tana sake mamakin Ayla acikin zuciyarta.
"Wai ke don Allah yanzu baki ji kunya ba, kin gwammace ki kwanta kiyi ta aikin latse-latsen waya da shige da ficen da ba zai amfanar da ke komai ba, wallahi Ayla ki nutsu ki san inda ke yi miki ciwo."
"Sorry madam ustaza ci gaba da aikinki kar ki wani dameni ni wallahi."
Gyaɗa kai kawai tayi ba ta tanka mata ba ta cigaba da tattare kayan falon tana ƙoƙarin kimtsa shi, cikin abinda bai haura wasu mintuna ba ta tsaftace falon tas ita ce har da kunna turaren wuta, turaren da Ayla sam baya gabanta, idan ta ɗau turare da zumma turara gidanta to kayanta ta turara waɗanda zata fita dasu suma idan wajen da zata fita kunya ne wato wajen ƙwayenta 'yan ƙarya. Amma idan har ba haka ba to gidan sai ya shekara bai ga turare ba, gata nan da su kuma kala-kala wasu ma har sun siƙe.
Ɗebo turaren tayi ta zuba a cikin abin turare take kuwa ƙamshi ya gauraye gidan, ita kanta Aylan sai da ta tankawa ƙamshin ta shiga tsokanar Hasina tana dariyar shak'iyanci.
"Wallahi madam ustaza mijinki ya caɓa ya samu ɓagas, masu wahaltawa mazan aurensu."
"Hmm" kawai Hasina ta ce da ita, don fahimci Ayla dai tayi nisan da ba zata ji kira ba. Sai da ta sake tsaftace mata gidan har da girki tayi mata sannan tayi mata sallama zuciyarta cike taf da tausayin Nazeer, gefe guda na sake mamakin Ayla yadda ta ɗau rayuwar aurenta a hagunce yanzuma ƙiri da muzuru taƙi tashi ta yi wanka haka ta barota bayan sun gama shan faɗansu akan wankan, ta ce ita wanka ɗaya take yi idan tayi biyu sai dai idan zafi ne ya isheta taji bata jin daɗin jikin nata, kuma ga shi nan bata wari ko hamami, idan batun ƙamshin jiki ake yi ai tana wanka da turare to me zai dameta. Haka suka rabu baram-baram da ita, a wajen Ayla kuwa tasan fushin Hasinan ba komai ba ne zata sakko, wuyarta bata kirata a waya ta tsarata ba.
BASH
"Haba beb me ya yi zafi haka, don Allah ki tsaya ki fahimce ni wallahi auren nan da zan yi bawai don in tozartaki ba ne, ko dan baki gamsar da ni."
"Babu wani abu da zaka faɗa min su yi tasiri a cikin kunnuwana Bash, me ya rage wane tozarci ne baka yi min ba kuma da zai biyo bayan wannan, na tsaneka bana son ganinka ko kaɗan ka fita ka bani guri."
Duk yadda yaso ta tsaya ta saurare shi abin ya ci tura, ya turza ya murza amma a banza ƙarshe ma kamar wata mai jinnu haka ta koma masa ta dinga fashe-fashen kwalaben dake ajjiye gaban mudubi, sai da ya fito daga ɗakin ya daina jiyo hargaginta. Ita kuwa yana fita ta durƙushe a ƙasa tana sake fashewa da wani irin kuka, jin zuciyarta take kamar zata tarwatse ita Bash zai yiwa kishiya akan me? Wannan wane irin tozarci ne,wallahi ko zata yi yawo tsirara bazata taɓa bari haka ta kasance ba, ita da shi su zuba su gani shege ka fasa zai san wace ce Yasira ra'ayul aini yadda da kansa zai bada labari ba sai an ba shi ba.
Bash kuwa yana fita daga ɗakinta nasa ya wuce kaitsaye, ji yake kansa na wani sarawa bai taɓa tsammanin kishin nata yakai haka ba, ashe duk yadda yake zata ya wuce tunaninsa. Har ga Allah yana matuƙar son ƙara auren nan kuma zuciyarsa na ba shi goyon baya ɗari bisa ɗari, ƙarin daɗawa hajjo ma ta amince masa, maganar da ake yi yanzu jibi kawun nan sa zasu je kai kuɗin aure, idan har ya ce ma ya janye shi kansa ya san bai kyautatawa yarinyar ba saboda yasan shi kaɗai take kulawa samari na zuwa wajenta tana korarsu ba dan komai ba sai dan yadda ya dage mata akan ta riƙe masa alƙawari.
_Don Allah Fatu ki riƙe min amana, ina da kishi bana son ko kaɗan na ga kina tsayawa da wani, alƙawari na ɗaukar miki in sha Allahu ba zan gujeki ba, ba zan ƙi aurenki ba. Ki saka a ranki ni naki ne Bash mijinki ne_
Wannan shi ne roƙonsa wajenta kuma ta riƙe masa amana sai kuma yanzu kawai yaje mata da batun ya janye, ina ba zai ma iya ba, zai cigaba da lallaɓa Yasira har Allah yasa ta kwantar da hankalinta ayi komai lafiya. Da haka ya ƙarasa kan gadonsa bai iya cire kayan jikinsa ba, da su ya kwanta yana sauke numfashi, so yake ya yi tunani ko yaya yadda zai shawo kan wannan al'amarin na Yasira, bai tab'a sanin da gaske akwai mata masu tsananin kishi irin haka ba sai yanzu da Yasira ta nuna masa kalar nata, ashe dai da gaske ana samun ire-irensu.
Ya juya ya waiwaya ya rasa samun matsayar yadda zai ɓullo mata, baya san tashin hankali ko kaɗan Allah ma shaida ne shi yasa bai zamo mafaɗaci ba, ko a makaranta idan an takale shi faɗa baya biyewa, idan kuwa tsokanarsa aka yi baya tankawa masu tsokanar, an sha biyo shi har gida an zane shi a sanya shi kuka sai da ma hajjo ta taɓa taka masa burki ta ce, duk sanda ya kuma tahowa ana biyo shi a baya ana dukansa da tunkuɗa ƙeyarsa kamar wani gaula sai ta ƙara masa da nata dukan, shi ne fa ya soma taɓuka wani abun, idan aka takale shin sai ya tsaya ya rama haka ma idan an tsoka ne shi zai tsaya ya rama da haka yaran sai suka soma janye masa sai ya zamana kamar ma sun fara shakkarsa, shi ma kuma da haka ya samu salama.
To yanzu ga Yasira na neman tayar masa da hankali, tana son sanya shi rigimar da bai shiryawa zuwanta ba, don ko kusa bai kawo kishin nata haka ba, duk da dai yasan ba ta ƙaunarsa da kowace mace amma bai taɓa tunanin abun zai kai ga 'yar haka ba.
Rasa mafitar da ya yi, da kuma yadda yake jin kansa na sara masa ya saka shi miƙewa tare da yanke shawarar ya fita ya bar mata gidan, zuciyarsa na raya masa wata shawarar da yake ganin ko kusa sam bata dace ba, da haka ya yankewa kansa shawarar zuwa gidan Hajjo, zai tare ta ya faɗa mata cewar kawai ya fasa auren.
AHMAD
Duk yadda yaso kaucewa maganar mom nasa ya kasa, a zahirin gaskiya ma ya fita san kasancewar zahida a cikin gidansa sai dai Allah shaida ne akansa mutum ne da ba zai iya ɗaukar raini ba shi yasa ma ko me zahidan take yi masa yake ɗauka kamar wani raini ne, ɗan wasan nan da mata baya son shi yana ganin babu abin da hakan zai haifar sai raini.
_kira gareku mazajen aure masu ɗaukar yin wasa da dariya ga iyalansu kamar raini ne, to ba haka ba ne wannan yana daɗa ƙarawa juna danƙon soyayya, domin da ace raini ne da ma'aikin Allah bai yi wasa, raha da iyalansa ba. Don Allah ku gyara zamantakewarku da matanku, ku jasu a jiki ku zame musu mahaifi, yaya, ƙani, aboki ta hakane kaɗai zasu shaƙu da ku, su sake da ku suji basa shakkar yi muku magana ko tsoronku_
Ahmad mutum ne da baya tsayawa iyalansa wajen basu farinciki, yabo ko kyautawa ba su dame shi ba yana ganin haka ba daidai ba ne, ai biyan sadaki ya yi ya aurota ya zama wajibi tayi masa duk abinda yakeso, ta kuma kyautata masa ta faranta masa ba tare da shi ya duba dacewar itama ya yi mata haka ba.
Tsawon shekrun da suka shafe da zahida idan za ta yi kwalliya sau dubu ba zai tanka mata ba, kuma har lokacin da suke yanzun ba ta fasa ba sai dai wani kaso na ciki ya ragu daga yadda ta taso ada, duk ta sakwarkwace babu wani gyara ta koma kamar ba Zahida ba.
Tun da ya shiga gidansa yake ta zagaye falon, idan ya zauna sai ya miƙe yaja tsaki, so yake yaje yayi bikonta amma zuciyarsa na ce masa ya ƙyaleta za ta dawo kamar yadda ya faru a lokutan baya. Ya saba ya korata gidansu, a ranar ma sai an dawo da ita, idan kuma da dare ne to kuwa safiyar Allah ta dawo masa, wani zubinma mahaifinta baba malam ne zai tasota a gaba ya dawo da ita to yanzunma zai bari ɗin har ta dawo ko a dawo masan da ita, da wannan tunanin ya kwanta yana zaro wayarsa ya shiga dannawa wata lamba kira yana sakin ƙayataccen murmushim da ya ƙawata fuskarsa.
[10/12, 9:48 AM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA
©Mai ƙosai
Book 1
BABI NA BAKWAI
FCW ASS.
Marubuciyar:
•Hafsatul-kiram
•Budurwar wawa
•Zahra
•Ƙaddarata ce a haka
•Ƙayar ajali
•Da mun bijire
•Matar Mamman
•Wani yanayi
•A dalilin son zuciya
ZAHIDA
Da wani irin matsanancin ciwon kai ta tashi, kusan za ta ce ma kwanansa uku tunda tun daga gidan Ahmad ta taho da shi, sai dai na yau yafi na kwanakin da suka shuɗe, tasha faracitamol amma shiru har boska tasha shi ma bai daina ba. Inna ce ta kafe akan sai sun je asibiti gwara su je a auna jininta a gani Allah yasa ba hawan jini ne ya kamata ba saboda wulak'ancin ɗa namiji.
Da ƙyar ta samu ta cusa ƙosai da kunun gyaɗar da Inna ta kawo ta ajjiye mata, shi ma ba wai duka ba dan dudu-dudu ƙosan bai fi guda huɗu taci ba, kunun kuwa ko rabin kofi bai kai ba, tana jin idan ta ce za ta ƙara to wanda ya shiga cikin nata ma zai iya dawowa, haka Inna ta ƙyaleta ta ce taje ta ɗaurayo bakin nata tazo ta saka hijabinta su wuce asibitin. Haka kuwa aka yi, dan goma da 'yan mintuna suka fice daga gidan, kaitsaye asibitin Marmara da ke kusa da su na gwamnati suka shiga, suna zuwa zahida ta tsaya wajen masu karɓar kati ta amsa sannan suka hau kan layi.
Kasancewar ranar ranar juma'a ce sai Allah ya taƙaita musu jama'ar dan babu mutane a gabansu sosai, duka-duka mutanen da ke gaba da su basu fi mutane tara zuwa goma ba, cikin ikon Allah ma kuma sai ya kasance likitan ba mutum ɗaya ba ne, sai kuwa ga shi cikin abin da bai gazasu da yawa ba sun samu damar shiga. Tambayoyi likitan ya yi mata kafin ya rubuta mata wasu gwaje-gwaje ciki kuwa har da na juna biyu ya turata nan cikin lab ɗinsu akan taje tayo ta kawo masa.
Wajen da ake biyan kuɗi suka nufa, inna ce wannan karan ta amshi katin ta biya kuɗin da aka rubuta musu a wajen lab ɗin, bayan ta biya aka miƙo mata rasit ta amso ta taho, tana zuwa suka miƙa rasit ɗin, aikuwa aka ce Zahidan ta zauna za a ɗibi jininta dan yin gwaji.
Duk yadda take tsoron allura tana ji tana gani haka aka ɗaura mata siririyar roba a tsintsiyar hannunta tare da umartarta ta damƙe tafin hannunta aka nemi jijiya aka tsira allura aka zuƙo jinin, sai da ta rumtse ido tare da taune leɓen ƙasan bakinta sanda ake zare allurar, jinin da ya biyo baya aka miƙa mata audiga aka ce ta danne, ba ta musa ba ta amsa ta ɗora audigar a wajen tana jin tsigar jikinta na tashi, kafin ka ce me sai ga amai na ƙoƙarin zuwar mata, miƙewa tayi da nufin ta ɗan fita ta shaƙi iska ko ta daina jin tasowar aman sai dai ina fitowarsa da zuwanta daidai bakin ƙofa sunyi daidai da daidai, dan tana zuwa ya ɓalle mata a nan ta durƙushe ta shiga kwara shi kamar babu gobe, ga shi da man ɗan abin da ta cin bai taka kara ya karya ba, daga baya ma aman ruwa ta koma yi, sannu inna da wasu mutane suka dinga jera mata. Halin da ma'aikatan suka ga tana ciki ne yasa suka ɗau jinin nata suka fara aiki akansa, mintuna kusan arba'in ne ya jasu kafin fitowar sakamakonta, nan suka miƙa musu katin inna ta amsa tana sake bawa zahida ragowar ruwan leda ta sake kuskure bakin nata, kana suka koma wajen likitan.
Tun da suka shiga zahida take jin ƙirjinta na mata nauyi sosai, tana jin likitan na magana amma hankalinta na ga wani wajen can daban har sai da inna ta zungureta da yake wannan karan tare suka shiga saboda jikin nata babu ƙarfi sai da inna ta riƙota.
"Binciken ya nuna tana da shigar ciki, sai kuma zazzaɓin cizon saura. Sannan zamu riƙeta a nan saboda yanayin jikin nata, za ayi mata wasu allurori da kuma ƙarin ruwa, sannan tana buƙatar hutu saboda gaskiya jininta ya hau da kaso arba'in, kuma ba a buƙatar hawan jini ga mace mai juna biyu."
Su ne bayanan da likita ke yi musu, tunda kuma ya ambaci ciki zahida ta daina gane komai, tunani ta tafi yi tana hasashen yadda wasansu zai kaya da ahmad idan yaji samuwar cikin nata. Sai inna ce ta ce da likitan,
"To dakta babu damuwa, mu ai lafiyarya muke so. Sai dai ɗazu muna wajen gwajin tayi amai sosai."
Ya ɗan muskuta kafin ya ce da inna,
"Mama babu matsala zan rubuta mata maganin aman in sha Allahu zata daina, yanzu ga katin aje a fara siyo waɗannan tukunna ita kuma yanzu za azo a kaita ɗakin da za a kwantar da itan."
"To na gode ɗan nan." Inna ta ce, tana amsar katin. A nan tabar zahidan ta fice dan siyo abubuwan kamar yadda likitan ya ce, kasancewar akwai kuɗi a wajenta, dan da zasu fito ta ɗebo kuɗi masu ɗan yawa.
NAZEER
Sanyayyen ƙamshin da ya doki hancinsa ne yasa shi yin mutuwar tsaye, tunda ya shigo gidan yaga komai ya canza masa kamar ba gidansa ba, bai ƙara sumewa da mamaki ba sai da ya shigo falon yaji yadda wani daddaɗan ƙamshi na tashi, ya kuma ƙyallara ido yaga komai fes-fes kamar dai ba gidan da ya sani ba, yana jinsa kamar wani gidan daban ya shigo tamkar dai wanda ya yi ɓatan hanya. Sai dai hango Ayla da ke kwance kan kujera kanta babu hula, jikinta kuwa ɗaurin zani ne da ta kawo shi ƙirjinta ya tabbatar masa da gidansa ne ba wani gidan ba. Zuciyarsa da farinciki ya ƙarasa shigewa falon yana sake sakin wata sallamar.
Ayla da ke kwance tana typing ta amsa a yatsine tana wani yi masa kallon tara saura kwata kamar ba mijinta ba, madadin ta miƙe ta taroshi sai ta sake muskutawa ta ci gaba da abin da take yi.
Bai yi ƙasa a guiwa ba ya ƙarasa kan kujerar da ke kallon ta Ayla ya zauna, yana ajjiye ledoji biyun da ya shigo da su.
"Sannu da gida" ya ce yana duban Ayla da ke sakin murmushin da bai san me take yiwa ba.
"Yauwa" ta ba shi amsa cikin ko in kula.
Sai shima ya tattara ta ya watsar bai sake gangancin yi mata wata maganar ba, ledojin ya ɗauka ya fice da su zuwa kicin. Koda ya shiga ledar farko ya buɗe mai ɗauke da kayan fruit a ciki ya ɗibi waɗanda za su iya ci ya zuba a faranti sauran ya zuba a cikin fridge, sai ya ɗauki waɗancan ɗin ya hau wankesu kafin ya sanya wuƙa ya yanka su yadda yake so. Ɗaya ledar kuma naman kasuwa ne na ƙaramar dabba, shima cikin firinjin ya saka dan ya san ba lallai tabi takansa ba tunda ya ganta da waya a hannu, idan bai yi wasa bama shi ne zai yi aikinsu.
Fulas ɗin abinci da ya gani an jere akan babban faranti ya hau buɗewa nan yayi arba da white rice mai kayan lambu, sai ɗayan miyar albasa ce zalla sai kifin jiya da ya shigo da shi yaga an saka aciki. Gefe guda kuma jug ne aka haɗa lemo na lemontsami da cocumber. Mamaki iya mamaki ya mamaye shi, dan yasan ko giyar wake Ayla tasha ba zata yi masa wannan garar ba, amma bai sani ba ko wataƙila kuma shiriyar da yake ta nema mata ce Allah ya kawo
Abincin ya zubo a faranti, sai lemon da ya tsiyayo a wani ɗan madaidaicin kofi ya fito falon ya koma ya ajjiye su ya sake dawowa kicin ɗin ya ɗauki farantin da ya zuba kayan marmarin nan ya sake komawa falon ya zauna, har lokacin Ayla na nan yadda ya barta.
"Sannu da aiki, na gode." ya ce da ita yana kallon fuskarta.
Ajjiye wayar dake hannunta tayi ta tashi zaune tana yatsina fuska kafin ta ce da shi,
"Kar ka ɓata bakinka domin ni ban girka maka komai ba, kai duk abinda ka gani a gidan nan ba aikina ba ne aikin Hasina ne, dan haka ita zaka yiwa sannu ba ni ba, saboda ni na faɗa maka ba 'yar aikinka ba ce, banzo gidan nan dan na yi bauta ko wata wahala ba shi yasa ma na ce ka ɗakko mai aiki kai kuma da taurin kai kamar mutanen farko kaƙi ai shi ke nan sai ayi ta zama a haka."
Ta ƙarasa maganar tana yarfar da hannu, haɗi da komawa ta kwanta.
Saƙaƙe ya yi yana bin ta da kallo, kaf kalamanta babu wanda ya ƙona masa rai irin abu biyu, na farko cewar ba ta isa ta girka masa abin da zai ci ba, na biyu kiransa da tayi da mai taurin kai kamar mutanen farko.
"Ayla ni ne mai taurin kai kamar mutanen farko?" ya jefa mata tambayar da mamakin da har yanzu bai bar shi ba.
"To ƙarya na yi da zaka wani tsattsare ne da na mujiyarka, ka ga ni daina kallona haka don Allah kar na sake lalacewa."
Ta ƙarasa maganar tana wurga masa harara. Bai san yaushe aka yi daren da gari ya waye har ya yi saken da ta raina shi har haka ba, bai san me yasa ya kasa ɗaukar hukunci mai tsauri akanta ba. Idan aka ce masa Aylansa ce wannan wacce ta so shi a baya yake ganin kamar za ta yi masa sujjada ce a yanzu haka sai ya musa ya ce sam ba haka ba ne, a yanzunma idan mamaki ya cika shi ji yake wani sashi na zuciyaraa na ayyana masa cewa wata ce ba ita ce ba canza masa ita aka yi.
"Ayla kin san kuwa girman miji da haƙƙoƙinsa da ke kanki?" ya watsa mata tambayar yana sake kafeta da idanuwansa.
"To ustaz masanin Allah da manzonsa da anyi magana sai ka wani wage baki kai ga wanda ya san Allah zaka yi wa mutum wa'azi, koda yake ance wai gwano baya jin warin jikinsa shi yasa kai kake kasa fara yiwa kanka wa'azin kafin ka yiwa wasu tunda kana ganin baka da laifin