Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
komai baka kuskure ko?" ta kai ƙarshen maganar da watsa masa tambaya. "Idan har akwai abin da nake yi miki ba daidai ba sai ki sanar dani ai, sau nawa nake zaunar da ke ina tambayarki laifin me ne yi miki kina ƙin faɗa Ayla" Taɓe baki tayi kafin ta ce da shi, "Eh fa nan fa ɗaya, to ai matsalar ko an faɗa maka baka yarda shi yasa nace gwano ne kai da baya jin warin jikinsa. Idan ba haka ba kai har kana da bakin magana, sau nawa ina rattaba maka abin da ya dace ayi a gidan nan na ga ko ɗakko min mai aiki sau nawa muna zancen dakai amma ka toshe kunnuwanka ka mayar da ni wata mahaukaciya wacce ban san mena ke yi ba ." "To kin san me kike yi ɗin ne Ayla?" Ya ɗan tsahirta yana dariyar gefen baki kafin ya ce, "Idan har da kin san me kike yi da baki zauna kina faɗawa mijinki waɗannan kalaman ba, da kin rungumi aurenki kin duƙufa wajen nemo aljannarki Ayla." "Allahu akbar kabiran!" Ta yi maganar haɗi da shewa kafin ta sake furta, "Nazeeru idan kai kake da aljanna da wuta don Allah idan na mutu ka saka ni a can ƙarƙashin wuta ka ji." "Ba ni ke da ita ba, amma ga dukkan alamu idan baki gyara ɗabi'unki ba zaki tafi can ƙasan-ƙasan wutar ai Ayla." "Mits to ai sai ka sakani aikin banza aikin wofi ka ji da yawarka. Wallahi ni Ayla na sha gabanka nafi ƙarfinka ehe dan baka isa ka mayar da ni jaka baiwarka ba, bar ganin ka biya sadaki an baka ni, ba shi ke nuni da cewa na zauna ka takani yadda kakeso ba, nima ina da gata kuma gatan ne zaisa na samarwa da kaina 'yanci, dan ba zan yadda nazo a sahun mata gidahumai ba da suke jin kamar su kai goshinsu ƙasa su yiwa mijinsu sujjada, suke jin kamar su kwanta miji ya taka ruwan cikinsu ya tsallake ya yi gaba." "A ra'ayinki kenan da idan mace ta yiwa mijinta biyayya shi kesa ta zama jaka baiwa, amma ita macen da tasan ciwon kanta tasan darajar Allah da Manzonsa tasan darajar iyayenta da ta mijin nata ita ce kaɗai zata fahimci cewa yiwa miji biyayya ba shi ke sakawa ta koma jaka baiwa ba. Ina miki fatan shiriya Ayla, idan kuma ba zaki shiryu ba ina fata Allah ya yi mini maganinki, ya kawo min sauyi da mafi alkhairi." Yana gama maganar ya miƙe ya wuce ɗakinsa, ji ya yi ma abincin kwata-kwata ya fice masa a rai, ga shi dai yana jin yunwar amma kuma abincin baya da wajen shiga. Har ya zauna sai ya dawo falon ya ɗau farantin kayan marmarin ya koma ɗaki da niyyar ya shasu ko sa toshe masa wata kafar. Wannan littafin na kuɗi ne akan #700 book 1&2 idan ya zama complete 1k. 8160675983 Opay Maryam Abdulaziz Maiƙosai 08160675983 [10/12, 9:50 AM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA ©Mai ƙosai FCW ASS. Book 1 BABI NA TAKWAS Marubuciyar: •Budurwar wawa •Hafsatul-kiram •Ƙaddarata ce a haka •Zahra •Da mun bijire •Wani yanayi •Matar Mamman •Ƙayar ajali •A dalilin son zuciya BASH "Da man hajjo cewa na yi ko za a haƙura da zuwa neman auren nan." Bash da ke zaune gaban mahaifiyarsa hajjo ya yi maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa. Kallon ɗan nata take yi, tana son gano mene ne ya sauya shi, ɗazu-ɗazun nan ya bar nan kuma bai tafi ba sai da suka ajjiye magana akan jibi za a je nema masa auren yarinyar da ya ce mata yana so ɗin, kuma bawai ɗazun ne tasan yarinyar ba hasalima har bincike duk anyi akanta, basu gano wani aibu nata ba. "Ita yarinyarce ta ce ba ta yi da kai?" Sake sunkuyar da kai ƙasa yayi, yana miƙa hannu ya sosa ƙeyarsa kafin ya ce da ita, "A'a hajjo" "To me ya faru?" ta watsa masa tambayar idanuwanta na kansa har lokacin. Gaba ɗaya dirircewa ya yi musamman yadda yake jin idanunta suna yawo a jikinsa, yasan da man tambayar da za ta yi masa kenan idan taji cewa babu laifin Fatu ɗin, sai dai har ga Allah bai shiryawa amsarta ba, bai ma san me zai ce da Hajjo ɗin ba. "Kai nake sauraro Bashir me ya faru da za a fasa zuwa nema maka auren yarinyar?" "Am da man hajjo Yasira ce..." Sai yayi shiru ya kasa ƙarasawa. "Uhmm ina jinka, cewa tayi ba zaka yi auren ba ko me?" "Eh to hajjo kusan haka, ɗazu bayan na bar nan to sai nake faɗa mata cewa zan ƙara aure, wallahi hajjo baki ga yadda hankalinta ya tashi ba gaba ɗaya ta fita hayyacinta." Wani murmushi ta saki tana kana ta ce, "Karka kuskura ka zama lusari acikin gidanka Bashir, ba zan hanaka abinda kake so ba amma ka sani ba zaka mayar da ni ƙaramar mutum ba, kai da bakinka ka shaida min yarinyar nan ta kori samarinta ba ta kula kowa sai kai, kuma kai ka ba ta wannan umarnin ka kuma tabbatar mata da kai zaka aureta shin ita ba mutum ba ce da ba zaka yi mata adalci ba, saboda kawai matarka ta tayar da hankali sai ka ce ka fasa auren? To ka buɗe kunnuwanka da kyau ka jini aure babu fashi wallahi sai anyi da yardar Allah, ka koma ka je ka ci gaba da rarrashin matarka duk wata mace da man ai tana da kishi dole idan taji za ayi mata kishiya hankalinta ya tashi, kaje ka rarrasheta ka kwantar mata da hankali ka nuna mata kai kake da gida, ban ce ka cutar da ita ba amma dai ka nuna mata kai tsayayyen namiji ne ba lusari ba." Ya san za a rina da man wai an saci zanin mahaukaciya, hajjo ba za ta fahimce shi ba duk da yasan gaskiya take faɗa masa, amma irin wutar da yaga tana neman kunno masa acikin gida tafi gaban haka shi yasa da yake so ya yiwa tufkar hanci tunda wuri, amma tunda ya ji zancen hajjo yasan ta gama magana, kamar yadda ta ce ne aure kam yasan babu fashi sai dai idan Allah bai ƙaddara Fatu matarsa ba ce. Jiki babu ƙwari ya miƙe ya yi mata sallama ya fice daga gidan, cike da kallon tausayi tabi ɗan nata. Tasan hakan da man zai faru, dole Yasira zata tayar da hankalinta musamman da ya kasance ba ta taɓa haihuwa ba, tasan zata iya hasashen domin haka zai ƙara auren, kamar yadda wasu matan da dama suke tunanin haka wasu ma suke gani idan aka auro musu kishiyar tazo ta haihu shi kenan miji ya daina sonsu, sun zama ababen wulaƙantawa uwa uba suzo su haɗu da kishiya mara tsoron Allah da imani ta tarwatsa musu kan gida wata ma ta yi musu farraƙu da mijin tana jin ta ci dubu sai ceto. Amma fa hakan ba zaisa ta goya masa baya ya fasa auren ba, tabbas tana son ganin jikokinta daga tsatsonsa sai dai idan Allah ya ƙaddara ba shi da rabon kuma ba ta yi masa fatan haka, ita babban burinta da fatan tama Yasiran ta fara haihuwar kafin wacce ta shigo ɗin tayi, tana kuma yi musu addu'a akan haka. WAHIDA Kujiba-kujiba da zirga-zirga take tayi tsakanin falonta da kicin, abinci take so ta kammala haɗawa kafin shigowar mai gidan nata wato abban sadik Taj ke nan. Wayarta ce da ke kan kujera zube a falo ta hau ƙara daidai lokacin da ta ɗakko ɗan ƙaramin fulas mai ɗauke da miya zata ajjiye akan dining ɗin, wayar ta fara ɗauka ganin sunan maigidan nata akan sikirin ɗin wayar yasa ta ja wajen da ke nuna alamar amsa kira, a handsfree ta sakata ta ƙarasa wajen dining ta ajjiye fulas ɗin taja kujera ta zauna. "Assalamu alaikum my abban sadik" Tayi maganar da sanyayyiyar muryar da take da tabbaci tana ɗaukewa maigidan nata hankali. Tana jiyo sautin murmushinsa kafin ya amsa mata sallamar. "Wa'alaikumussalam da farar aniya mai sanyaya zuciya, hope komai normal?" ya ƙare da yi mata tambaya. Tana ɗan murmushi ta ba shi amsa. "Lafiya lau kai kawai muke jira." "To ma sha Allah. Me kika dafa mini?" "Taliya ce da source sai farfeson kan rago." "Auch!" ta jiyo sautin furucin nasa kafin ya ɗora da faɗin, "Taliya Wahida ita kaɗai, kin san fa ni ba ta wani riƙe mini ciki don Allah idan ba so kike na mutu ba ki sama min wani abu mai nauyi dai, ko kuma kinga kawai dafa min shinkafa idan yaso sai na haɗa da ita." "An gama yallaɓai, isowarka kawai muke jira." "Wait wai sadik ya dawo ne kike ta cewa kuke jira" 'yar dariya tayi kafin ta ce, "A'a kasan sabo da faɗa shi yasa bakin ya saba." "Haƙƙun ban manta ba fa." ya yi maganar cikin sigar tsokana. Dariya tayi wannan karan sosai kafin ta ce, "Kai abban sadik" cikin shagawaɓar da tasan zata narkar da zuciyarsa, ta kuwa yi sa'a dan yadda ta ƙare maganar sai da tsigar jikinsa ta motsa. "Wash me kike tanadar mini sweet." ya ce da ita a kasalance. "Komai ma, kai dai kawai Allah ya dawo mana da kai lafiya." "Ki ce yau ɗan gata nake, amin sai na dawo bye." Ya ƙarasa kalaman nasa da kai mata sumba a wayar kafin ya katse kiran, lumshe idanuwa tayi tana jin ƙaunar mijin nata har cikin ranta. YASIRA Bakinsa ɗauke da sallama cikin nutsuwa ya turo ƙofar ɗakin nata, tana durƙushe yadda ya fita ya barta, bakinta babu abin da yake gauraye shi sai zallar ɗacin kalaman da ya dinga cusa mata cikin kunnuwanta, wai ita Yasira Bash zai kalli ƙwayar idanuwanta ya furta mata kalmar kishiya, da ranta kai ko babu ranta ai tana ganin ba ta canci ya yi mata kishiya ba. Durƙusawa ya yi inda take ya kai hannunsa na dama ya ɗago fuskarta wacce tayi shaɓe-shaɓe da ruwan hawaye wasu sun bushe wasu kuma suna kan gangarowa. saboda ita shigowar da ya yi ma ba ƙaramin fama mata raunin da ya gama ji mata ya yi duk da cewa ba wani kamewa wajen raunin ya soma yi ba, amma ita kam ji take yi kamar tayi rauni ne ya ɗakko hanyar warkewa sai aka yi mata kamunsa. Tar ta ware idanuwanta kan fuskarsa tana kallonsa tana kuma son ta gano sauyin da aka yi mata da Bash ɗinta na baya, kai ita fa so take yi ma taga ta farka dan tuni zuciyarta da ƙwaƙwalwarta sun faɗa mata tana duniyar mafarki ne. "Don Allah ka tashe ni daga baccin nan Bash, ka ce min duk wasa ne abin da ka faɗa mini ba gaskiya ba ne." tayi maganar cikin karyewar murya tana sake cusa idanuwanta cikin nasa. "Ki yi haƙuri beb ba mafarki kike yi ba da gaske ne, Bash ne gabanki tsugunne da ƙoƙon bara don Allah ki kwantar da hankalinki kar ki samu wani ciwon" Wani murmushi tayi da ta gaza tantance muhallin da zata ɗora shi akai, kafin ta iya furta masa, "Ciwo hmmm!" ta yi ƙwafa kana ta ɗora, "Idan har babu ƙarya a cikin kalamanka ka tabbatarwa kanka da ciwo na riga da na jima da samun ciwo, kuma ciwon da zai zama silar ajalina. Bash me yasa za ka yi mini haka? Me na rage ka da shi? Ko dan ba na haihuwa? Ko kuma dan ni matar shige ce a wajenka?" "Haba beb duk me ya kawo wannan zancen wallahi babu ko ɗaya, Yasira ni Bash ina sonki kuma tsananin ƙaunarki ki yarda da ni plz." "Idan har kana so na gasgata ka to ka faɗa min ƙarya ne babu wani aure da zaka ƙara." Wani nishi kamar mai naƙuda ya saki kafin ya iya furta mata, "Don Allah Yasira, don Allah ki yi mini kyakkyawar fahimta ki fahimce ni kiyi mini uzuri, babu yadda zanyi in fasa wannan auren Yasira idan nayi haka ita yarinyar sam ban kyauta mata." "To kuwa wallahi ka sani babu kai babu zaman lafiya a gidan nan na rantse da sarkin da ya busa mini numfashi duk wacce tayi gigin aurenka ta tabbatar ta shigo kabarinta domin gidan nan sai ya zame mata kushewarta wallahi." Tana gama faɗin haka ta miƙe ta shige banɗaki tabar shi a wajen kamar wani mutum mutumi, shi fa gaba ɗaya tsoronta ya mamaye shi, ya san tana da kishi amma ko da wasa bai tsammanin zafin kishin nata zai kai haka ba. Ganin ba shi da wani zaɓi face ya ƙyaleta har zuwa ta sakko, zai ba ta lokaci wataƙila ta daina fushin da shi, sai ya tattara 'yan ƙafafunsa ya fice daga ɗakin, ɗakinsa ya shiga yana mai neman wajen zama gefen gado, agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya kwance ya ajjiye gefe yana saƙa wasu tunanuka ƙasan ransa,kafin ya ƙarfafawa gangar jikinsa ya miƙe ya shige banɗaki, ruwa ya watsa kana ya fito, gaban madubi ya tsaya yana goge sumar kansa da ɗan ƙaramin towel, bai shafa mai ba saboda yanayin garin ana ɗan zafi-zafi, sai kawai ya ɗau turare ya fesa ya shiga neman kaya masu sauƙi ya saka suma ya fesa musu turare duk da ƙamshin da suke yi, aikin Yasira ne da duk kayansu duk sati sai ta turare musu su, kai har turaren cikin sif ta sanya musu shi yasa kayansu basa rabo da ƙamshi, ƙamshin ma ya zauna a jikinsu ko an wanke sai ka ji wannan ƙamshin mai sanyi. Wayarsa ce tayi ƙara ya ɗauka yana kallon sikirin wayar, sunan Fatu ne ya bayyana kasancewar da FATUNA ya yi saving lambar, duk halin da yake ciki bai hana shi ɗan murmusawa ba kafin ya amsa kiran yana kara wayar saman fatan kunnensa na hagu. "Uhm barka da hantsi" yaji saukar muryarta cikin kunnuwansa. Murmushi ya sake fitarwa yana son hirarsa da ita wasu lokuta dan kawai ya yi nishaɗi yake zuwa wajenta taɗi, a ƙauye aka haifeta ta kuma taso, tana shekara sha huɗu ta dawo hannun kawunta ƙanin mahaifinta ne wanda shi ma cirani ne ya kawo shi Kanon, sai ya nemi waje ya zauna har ya yi aure ya tara iyali, yana da mace ɗaya sai yara biyar uku mata biyu maza sai kuma ita Fatun da ya ɗakko sakamakon rashin mahaifinta da tayi, zuwanta kanon kawu ya sanyata makaranta wacce yaransa ke zuwa, kuma Alhamdulillah tana ja don babu laifi kam, bayan ta gama sikandire sai manema suke ta zuwa da fari taso basu dama sai dai kuma ita har ga Allah so take yi tayi karatu mai zurfi idan da san samu ne ta zama 'yar jarida a dinga jinta a gidan radiyo ko a dinga ganinta a gidan TV, Suhaima 'yar kawun nata kuwa da taji kalamanta ita ce ta ba ta shawara akan sai dai ta kori duka samarin ta fuskanci karatun shi ne kaɗai za ta cinma abin da take so, hakan kuwa aka yi dan gaba ɗaya ta daina kula samari, har Allah yasa ta samu gurbi a makarantar BUK, ta dage sosai tana karatunta, tana level 2 suka haɗu ita da Bash a wajen siyan kayan marmari, kawu Manu ya turo ta ta siyo musu ita da Suhaima, shi kuma lokacin yaje siyawa Yasira. Abin da ya soma jan ra'ayinsa da ita tsiwarta, ganin yadda take yiwa mai siyar da kayan marmarin tsiwa akan zai yi musu runto, da yake ma mutumin ba babba ne ba sai tafi zagewa tana yi masa tsiwarta ta, da sannu-sannu ya bibiyeta ya samu kusanci da ita, har ya yi mata alƙawarin aure, san da ya fara magana da ita tashin farko ya fahimci ita wace asali ce saboda har yau HE tana bakinta, wasu abubuwan ma na ƙauye basu barta ba, ita kanta tana mamaki sosai da ya ci ace yanzu ta daina yinsu. "Hello my yallaɓai kana ji na?" Maganarta cikin siriryar muryata ya dawo da shi daga duniyar da ya wulga. "Uhm!" ya ce, ta kuma fahimce me yake nufi da haka, sai kawai ta ɗora da abin da take son faɗa masa. "Da man kawu ne ya ce ina sake tambayarka da gasken iyayen naka za su zo jibin?" "Uhmm za su zo Fatu, amma kin san me?" Sai da gabanta ya bayar da sautin rass kafin ta iya amsa masa da, "A'a" Ya lura da yadda muryarta tayi rauni, ya san baya rasa nasaba da yadda shi ma ya yi mata tambayar, yana jin cewa ta shiga fargaba ne kuma yasan fargabar ba zai wuce tayi tunanin ko dai ya fasa. "Ina jin kamar idan sunzo su saka sati guda bikin nan." "Hmm!" ya jiyo ajjiyar numfashinta, da kuma sautin murmushinta kafin ta ce, "lokaci komai zaizo a muhallinsa fa yaya." Yadda ta ƙare maganar sai da gashin jikinsa suka tashi, yana sonta don ba zaice baya sonta ba wannan ma zance ne maras tushe, ita ce macen da ya fara kalla da sigar so, ba zai ce ba ya son Yasira ba amma a kaso ɗari kaso arba'in yake jinta a ransa sauran kuwa duka sun tafi wajen Fatu. "Shi ke nan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi." "Amin yaya." "Ok zan kiraki anjima, yanzu ina gida kin ji. Kin ga lokacin aunynki ne ko?" "Tom ka gaishe min da ita, na gode sai anjima ka kula min da kanka ka ji." Ba ta jira amsarsa ba ta kashe wayar, wani murmushi ne ya suɓce masa, murmushin da ya yi daidai da shigowar Yasira ɗakin sai shaiɗan ya yi mata huɗubar da ta tafi akan gaɓa, ta ji cewa ai da wacce zai aura yake wayar har yake mata wannan tsadadden murmushin da ita kaɗai ya canci ta ganshi, lallai ma ya rainata ita zai yiwa haka, namiji kenan, namiji ƙayar ajali, namiji ƙarin kunama. Wannan littafin na kuɗi ne akan #700 book 1&2,idan ya zama complete 1k. 8160675983 Opay Maryam Abdulaziz Maiƙosai 08160675983 [10/16, 11:20 AM] Maikosai(Matar Abduul): Follow the MARYAM MAI ƘOSAI NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6lO6KJ93war7Sywv0G ƘARIN KUNAMA ©Mai ƙosai FCW ASS. Book 1 BABI NA TARA ZAHIDA Bayan dawowar inna ne likita ya jona mata ruwa kamar yadda ya ce, sai kuma allurorin da ya dace da ciwon nata ya yi mata. Suna nan zaune har kusan mintuna talati kafin inna ta ɗau wayarta ta kira gida, nan ta shiga sanar da su halin da ake ciki. Nan take mama ta soma haɗa musu abinci domin yaya kamal da kansa ya ce da ita zai kai musu, Huwaila kuwa tana makarantar islamiyya ba ta dawo ba. Ko da ya karɓi abincin sai da ya tsaya wajen mai balangu ya siya musu ya haɗa musu da kayan shayi ya wuce asibitin kaitsaye. "Sannu inna yaya mai jikin?" cewar yaya kamal bayan ya ajjiye kwandon abincin da kuma ledar biba wacce ya yi musu siyayya da ɗan abubuwan buƙatarsu da aka haɗo musu daga gida. "Yauwa Kamalu, jiki da sauƙi gata ta samu bacci ma." Kallo yabi Zahida da ke kwance da shi, ƙasan zuciyarsa na jin tausayin 'yaruwartasa, tun da tayi auren nan babu kwanciyar hankali, ita ce yau kaza gobe kaza,yaso a raba auren nan amma baba malam ya kafe ya tsare akan babu dalilin da zaisa akashe aurenta, dole ya tattara ya watsar da batun sai dai kullum addu'a yake yi mata akan idan da alkhairi a zaman nasu Allah ya daidaita mata lamuran, idan kuma rabuwar tafi alkhairi to Allah ya warware igiyar auren. "Akwai abin da kuke buƙata inna?" ya jefawa inna tambayar. "A'a babu, don na jima likitan ɗazu bayan ya jona mta ruwan yana faɗin wataƙila anjima ya sallamemu idan ya ga yanayin jikin nata, idan kuma kwanan ta kama ma dai gaskiya bana jin akwai abin buƙata." "To shi kenan, Allah dai ya ba ta lafiya." "Amin" cewar Inna tana ɗan gyara zamanta, sai da ya ƙara hutawa sannan ya yiwa inna sallama ya tafi. Huwaila na dawowa daga islamiyya taji batun asibiti ta ajjiye jakarta ta wuto, don ko abinci ba ta tsaya ci ba, san da tazo ta iske har an jona mata ruwan na biyu wancen ya ƙare, kuma Zahidan ma ta farka tana cin abinci. "Sannu yaya" cewar Huwaila ga Zahida. Tana bin ta da kallon tausayawa. Gyaɗa mata kai kawai tayi, don wata yunwa take ji tana sassaƙarta, ga shi zura abincin take yi amma ji take kamar ma ba ci take yi ba. "Ki ci a hankali idan baki ƙoshi sai a ƙaro wani akwai ai." Faɗin inna da ta lura da yadda Zahidan ke kai lomar abincin hannu baka hannu ƙwarya. "To inna" Zahida ta ba ta amsa a taƙaice. "A miƙo miki balangun?" inna ta sake yi mata magana cikin salon tambaya. "A'a sai anjima." zahidan ta ba ta amsa tana kai loma bakinta. Can gida kuwa sanda baba malam ya dawo ya riske labarin, da sannu ya bita da shi, tare da nema mata sauƙi a wajen Allah, mama kuwa itama tana gefe tana bin ɗiyarta ta da addu'ar samun sauƙi da rahamar Allah. Ayla Yau da wata irin kasala ta tashi, tun jiya kanta ke ciwo, wajen bayan magrib, tadai b'alli farasitamol tasha, sai dai sam babu sauƙi abun ma kamar ƙara gaba yake yi, yanzu kuwa da ta tashi har da wata juwa take ji, ga wata yunwa kamar an rarake cikinta. Nazeer na kallonta yadda take yatsina fuska, da yadda ta mik'e a kasalance ta shige banɗaki, yana zaune gefen gado yana ƙoƙarin ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa, san da ya kammala ɗaurawa ita kuma ta fito ya ɗaga kai ya dubeta yana faɗin, "Baki da lafiya ne?" "Kusan haka" ta ba shi amsa a taƙaice, bai sake ce mata komai ba ya miƙe tare da zira hannunsa cikin aljihu ya zaro dubu uku ya ajjiye mata saman durowar gefen gado yana faɗin, "Ga shi nan dubu uku ce babu yawa ki je asibiti, abinda ake ciki idan na dawo sai in gani." Wani sheƙeƙe ta bi shi da kallo don har yakai bakin ƙofa, kamar yasan zata raina kuɗin shi yasa ma ya yi hanzari ficewa, yana jiyo tsakinta da furucin da ta jefe shi da shi. "Tsiyar talauci kenan, kai wallahi talauci baiyi ba a rayuwa.Yazu a rasa abin da za a bani sai wata shegiya dubu uku ita ce zanje asibiti da ita, idan banda ma dai mutum ba mutum ba ne ba kamata ya yi ya ɗauke ni ya kaini da kansa yadda ba sai na sha wahala ba." Haka ta gama mitarta ta fito falo, tana jiyo tashin babur ɗinsa da fitar daga gidan, sai a sannan ma ta wuce kicin tasan ya ajjiye mata abin kari, ai kuwa ta tarar da wainar fulawa da kunu. Tsaki taja tana mai kushe kayan karin, waɗanda wasu na can suna neman kwatankwacinsa ita ta samu amma ta kasa godewa Allah ni'imar da ya yi mata. Falo ta dawo ta zauna ta soma cin wainar, dan bama ta zubo kunun ba sam ba ta jin za ta iya shansa. Nan ta miƙe tabar farantin a wajen ta koma ɗaki tana dafe kanta da yake sara mata, jirin ne dai kam ta rage jinsa wataƙila hakan nada nasaba da yunwar ma da take ji. Wanka ta faɗa banɗaki tayo, ta fito tana tsane jikinta kafin ta murzawa fatarta wani lotion da takanas ta siye shi wajen wata mata da suka haɗu gidan biki, ta ce mata yana saka hasken fata sosai, ga laushi da sulɓi, ita kuwa abinda take buri kenan aga fatarta na walwali ta yadda duk wanda ya kalleta dole ya sake kallonta. Sai da ta gama tsirface-tsirfacenta sanan ta zira kayan ta yafa wani shara-sharan mayafi ta ɗau jaka ta zira takalmi mai tsini sai dai ba can sosai ba ta fice daga gidan ba tare da ta kalli gidan ta gyara shi ba, asibiti ta nufa bayan ta tare mai napep ta shiga, ana sauketa kuwa ta wuce sashen karɓar kati ta amsa ta koma layin ganin likita tana jan tsaki a ranta tana raya yanzu da Nazeer wani hamshaƙin mai kuɗin ne da sai dai su je firabet a mutunce a yi mata komai ba tare da ta wani biyo layi ba, katin ma tasan file ne za a buld' mata da anje kuwa babu wani sanya za a zak'ulo shi, wani ƙululun baƙinciki ne ya taso mata ya tokare mata

Chapter 5 of 6