sai kakkauran haɗin ruwan shayi amma wai kunu da dankalin hausa" Mits ta ja wani ƙaton tsaki tana dungure jug ɗin kunun .
"Ga dai gida iya gida, amma dai talauci ya yi masa sallama ya hana mutum kataɓus aikin banza aikin wofi." ta sake furtawa tana sangamo flask ɗin da dankalin hausan ke ciki tayo waje.
Falo ta dawo ta zauna ta soma ci ke nan ta jiyo ƙarar wayarta da hanzari ta ajjiye dankalin da take ƙoƙarin turawa bakinta ta miƙe da sauri ta isa wajen wayar, lambar da ta gani a jiki ce ya sa ta saurin haɗiye ɗan guntun dankalin dake bakinta ta sanya hannu ta latsa maɓallin amsa kira ta kara wayar a kunnenta.
"Shegiyar kina duniya da man?" ta yi maganar tana washe baki.
"Ke dai bari wallahi, jiyan nan na dawo kin san na ce miki zan je dubai to ban samu dawowa da wuri ba shi yasa ban neme ki ba to how fa yaya garin da kujiba-kujiba?"
Daga can bangaren aka yi maganar ana sakin murmushi.
'Hmm ka ji fa masu ƙumbar susa aje can a dawo a sake lulawa wata duniyar mu kuwa muna nan muna zaune waje ɗaya kamar shirgin kayan wanki' tayi maganar a zuciyarta, a fili kuwa cewa ta yi,
"Wallahi ke dai bari, gamu muna ta jujjayawa dai, sabgogi sun yi mana yawa, ni ma da yake bana gari shi yasa ban jima da dawowa ba."
"Ayya shi yasa, to ya zancen business kinsan na ce miki bana son wasa a lamarin tunda neman kuɗi kake ai da kuɗi ake neman kuɗin."
"Yana nan ke dai bari, da man ina jira na ji ta ɓangarenki ne."
"Ok babu damuwa, zan bayar da share na miliyan d'aya sai ki bada wanda zaki iya sakawa sai a fara saro kayan akwai shagon da baban Saifu ya bani za a zuba a can sai a saka yaron da zai zauna a ciki, idan yaso duk wata shida sai a dinga raba ribar ko yaya kika ce?"
Sai da ta nisa ta sauke numfashi kaɗan gudun kar ta jiyota kana ta ce,
"Eh hakan ma ya yi, tom zan taɓoki bari ogan ya dawo babu matsala."
"To babu damuwa, amma ina ta so zan shigo gidanki fa sai rowa kike yi min kuma ya kamata dai mu san juna"
Wani ƙuuu taji cikinta ya bayar, da ƙyar ta iya furta,
"Ok za muyi magana, ina so ne oga ya dawo sai ayita ta ƙare ko yaya kika ce?"
"Alright hakan ma is ok, sai na jiki bye."
Ba ta jira amsarta ba ta katse kiran, ita kam Ayla wata iska ta furzar tana samun gefen gado ta zauna jagwab wani tunani na ɗarsar mata cikin zuciyarta, wani sashe kuma na tambayarta ta yadda zata ɓullowa al'amarin karfa taje garin neman gira ta rasa ido, sunan da take son yi ba ta yi ba ta ƙare da jin kunya, koda yake shi ramin ƙarya da man ƙurarre ne amma ba ta so takai wannan gaɓar tana fata ta cinma ƙudirinta kafin komai ya faru.
YASIRA
Tun da bash ya fita ta shiga sake kimtsa gidan, bayan ta kammala komai cike da nutsuwa ta dawo falo ta zauna, wayarta ta ɗauka ta kunna data saƙonni suka shiga shigowa, ba ta fara bibiyar saƙonnin ba sai da ta ga kaf sun shigo sai waɗanda ake aikowa yanzu, group ɗinsu na manyan mata ta shiga ganin message ɗari uku da wani abu, a hankali ta soma bibiyar hirarrakin, wasu ta yi dariya wasu ta danna emoji wasu kuma ta wuce.
Kacokam hankalinta yakai kan wani saƙo da ta ga an tura da ta bibiyi maganar ta ga akan maganar ma ake tattaunawa, murmushi ta yi tana sake karanta saƙon kamar haka;
"Ni nan zan faɗa muku don wallahi ɗari bisa ɗari namiji ba ɗan goyo ba ne, namiji ƙarin kunama ne idan ya harbeki sai ya saka miki gubar da sai ta zama ajalinki, ke idan bai kasheki ba to ya saka miki jinya, ni nan ganau ce ba jiyau ba ƙanwata mijinta iskancin da yake zuba mata wallahi kuka gani sai kun koka mata, amma shegiyar yarinyar nan wai anzo ana son raba auren ta botsare wai ita tana son mijinta a barta da kayanta."
Aikuwa caa aka yiwa saƙon, a hankali kuma ta soma bibiyar raddin da ake mayarwa saƙon.
_"Ka ji shegiya ita ana ga gabas tana sai kudu, sai ka ce jaka ai sai taje idan ya kasheta a ɗakko gawarta."_
_"Wallahi kuwa bari ke dai, ai wallahi ni banga namijin da zai min kan kara ban masa na itace ba, yo jakarsa ce ni, iyayena basu min ba sai kai, in ɗau ɗawainiyarka kuma ka dinga zuba min juji akaina ai kayi kaɗan." _
Maganar da wata tayi ke nan ƙasan wancan comment ɗin.
Haka ta dinga bin comment kala-kala wani tayi dariya wani tayi murmushi fita tayi daga group ɗin tana shiga cikin group ɗinsu na family, message ɗin ta dinga bibiya tana amsa wasu kafin daga bisani ta fita a haka ta cinye lokacin wajen bibiyar message wasu tana amsa musu wasu kuma tana danna musu like, har wajen azahar sannan ta kashe datar ta ajjiye wayar tana nufar kicin.
Kaitsaye abincin rana ta shiga kiciniyar ɗorawa, so take yi ta kammala da wuri kafin Bash ya shigo, dan taga uku saura mintuna goma kuma duk inda uku da rabi take yana gida, ganin wankin hula na neman kaita dare ya sa ta yanke shawarar yin sakwara da miyar ganyen ugun, sai busasshen kifi da zata saka a ciki, nan da nan kuwa ta shiga aikinta bata kammala ba har wajen uku da ashirin da biyar, a gurguje ta faɗa toilet tayo wanka tazo tana shiryawa, tana cikin fesa turare taji buɗe gate ɗin da baba mai gadi ya yi wa bash ya shigo, tana jiyo horn ɗin motarsa wanda hakan na nuna mata alamun ne na ya iso ta fito taryarsa.
Cike da kewarsa ta ƙarasa fesa turaren ta fito fuskarta ɗauke da yalwatacciyar fara'a, babu kunya da jin nauyinsa ta rungumo kayanta ta manna masa kiss a kumatu shi ma taryarta ya yi yana mayar mata da martani, jin junansu suke yi kamar sun shekara ba su haɗu da juna ba, cike da nuna kulawa ta janyo shi suka shigo falon, sai dai kaitsaye ɗaki ta yi masa izini domin ya watsa ruwa, bai musa mata ba domin shi ma hakan yake so. Bai samu kansa ba sai bayan ya kimtsa sannan suka zauna zaman cin abinci cike da so, ƙauna, haɗi da kulawar junansu.
ZAHIDA
Zubar hawayen nata baisa ta ji sassaucin raɗaɗin da ke addabar zuciyarta ba, ji take yi tamkar an ɗora mata bulo akan shimfiɗar ƙirjinta, tana nan zaune har lokacin Haulat ta fito wannan karan ta sauya kaya ta saka riga da wando na kanti, sai hula da ke kanta, sai taunar cingum take yi kana jin tashin sautinsa yana ƙaras-ƙaras. Ko kallonta ba ta yi ba ta miƙe tana bin bango, har ta gota ta dawo da baya ta janyo kicin ɗin ta saƙala masa kwaɗo.
"Kicin ɗin na yayana ne ai ina da right nayi duk abin da nake so dan haka ki buɗe min." Haulat ta yi maganar cikin nuna isa da gadara, banza tayi mata ba ta kulata ba,sai ma shigewarta da tayi ɗaki. Ganin haka yasa Haulat take mata baya, tana yi tana mita.
"Wallahi ki buɗe min ko na kira shi in faɗa masa, idan yaso sai ki ga hukuncin da zai ɗauka."
Nan ma dai Zahida ba ta tanka mata ba, ganin tana ta kumfar baki yasa Haulat ɗin sake faɗin,
"Aikin banza ci ba auki, sai dai a cikawa mutane masai, a ɗabi na banza akai gidan tsofaffafi..."
Ai ba ta gama rufe baki ba taji saukar yatsun Zahida akan kuncinta, wanda ya sababa mata ganin gilmawar wasu ƙananun taurari. Hannu takai ta dafe kuncin ta saki baki galala tana bin ta da ido kafin ta iya furta,
"Ni kika mara? Wallahi ki sani baki mari banza ba, wannan marin sai na rama shi."
"Idan kin gama ramewa ke nan, an faɗa miki ja da baya ga rago tsoro ne, kar kiga kina yi ina shareki ba tsoronki nake ji ba wawiya kawai."
Tana gama furta maganar ta wuce ta koma ɗaki abin ta.
_Wannan littafin na kuɗi ne akan #700,idan ya zama complete 1k_
8160675983
Maryam Abdulaziz
Opay
08160675983
[10/2, 5:25 PM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA
©Mai ƙosai
Daga Marubuciyar:
•Hafsatul kiram
•Ƙaddarata ce a haka
•Ƙayar ajali
•Zahra
•Da mun bijire
•Matar Mamman
•Wani yanayi
•A dalilin son zuciya
•Budurwar wawa
_Ban amince a juya min littafi ta kowace siga ba tare da izinina ba, yin haka ya sa'ba doka, a kiyaye._
BABI NA UKU
AYLA
Tagumi ta zuba a duka kumatunta, tunani ne fal cike a kwanyarta ta yaya zata ɓullowa al'amarin? Ta ina za ta fara da kuɗaɗen da take son kafa kanta, ta san ko giyar wake tasha Nazeer ba zai taɓa ba ta su ba, hasalima ina ya gansu alhalin da, da yanzu ba ɗaya ba, da ace a lokutan baya ne tabbas ba ta da haufi ko nawa ta nema zai bata, to amma fa ita kanta ta sani ban da yanzu da al'amuran suka canza, saboda iftila'in da ya saukarwa dukiyar tasa, wacce har yanzu ga shi nan ko kwatanta bai samu ya mayar ba. Tsaki taja tana dafe goshinta, wata zuciyar na raya mata wani abu da take ganin kamar zai fissheta hanya mai kyau, wani sashen na raya mata karta kuskura sam ta ma ce za ta fara. Da wannan tunanin da taga ba zai amfaneta da komai ba ya sa ta miƙe ta fito falo ta soma safa da marwa kamar wata mai ɗawafi, kayan karin kumallonma gabaɗaya ta watsar da su gefe don tana jin yanzu ba ta da lokacinsu, lokaci ne take da shi na neman mafita saboda so take yi koda tsiya-tsiya ta samu jarin nan ta yi kasuwancin nan saboda ta kece reni ta wuce sa'a.
Ba ta iya taɓuka komai ba, sai tunani da hasashen abin da ba zai amfaneta ba, duk da cewa a wajenta mai amfani ne har lokacin dawowar Nazeer daga kasuwa ya yi.
Tun da ya buɗe gate ɗin gidan da yake madaidaici ya tabbatarwa kansa babu abin da Ayla ta taɓuka, domin kallo ɗaya zaka yiwa tsakar gidan ka tabatar babu shara, da yake gidan gida ne flate irin safecounter ɗin nan wanda da ka buɗe ƙofa ana kallo falon gidan. Ko ina biji-biji tarin shara, ga da ma kwandon sharar ya cika fal yana ta alla-alla yau idan ya dawo ya fitar da ita. Wani kallon takaici yake ƙarewa wajen, da ƙafa yasa ya ture kwanukan wanke-wanken da aka barbajesu ya samu hanyar wuce wa, yana shiga ledar biskit da kayan abincin da ta ajjiye a falon suka yi masa maraba, wani irin ƙamshi ya shaƙa da ba zai ce yaji daɗin shaƙarsa ba, tana kwance saman kujera mai cin mutum uku, idanunta a lumshe sai dai ba bacci take yi ba hasalima tana jin duk wani motsinsa.
"Ayla!" ya kira sunanta cikin wata tattausar muryarsa, kallo ɗaya zaka yi masa ka san ya cika namiji cikakke, domin yana da kyau da haiba da wani irin kwarjini, wanda shi yake sawa Ayla ma wani lokacin rashin kirkinta yake yin ƙasa idan taso yi masa tijara.
"Ayla!!" karo na biyu da ya sake kiran sunanta, sai dai tana kwancen ba ta motsa ba har sai da ya sake kiranta a karo na uku sannan ta miƙe zaune tana taɓe baki tare da jan tsaki.
"Wai mene ne kake ta kirana sai ka ce na ci maka bashi?"
Wane yawun takaici ya haɗiye yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasar ɓacin rai, sai dai duk da haka cike da nutsuwa ya yi mata magana,
"Yanzu abin da kike yi Ayla kina ganin shi ne daidai a rayuwarki? Kina ganin wannan ya dace da rayuwar matar aure? Fisabilillahi ba za ki yiwa kanki karatun ta nutsu ba ki fuskanci ibadarki Ayla"
Da wani irin sautin amo mara daɗi a lafuzan nasa ya ƙarashe maganar. Galala Ayla tayi tana binsa da kallo, kallon ka ji mini mutum, kallon ba fa zai takura mata ba haka kawai, dan tayi aure ba shi ke nuna sai yadda aka yi da ita ba, ba shi ke nuna ba ta da 'yanci ba sam.
"Dakata min Nazeer ni fa ba baiwarka ba ce, ba an kawo maka ni don ka dinga bautar da ni ba ehen, wallahi ashana wannan idan ban ji ra'ayin ƙyasta ta ba bazan kunna ba, balle aje ga ɗora tukunya ko wanke-wanke da ma dai sauransu, ni ba wannan ya kawo ni ba."
Zuruu yayi yana ƙare mata kallo, duk da cewa ba wannan ne karon farko da idan irin haka ta kasance yake kallonta ba, kuma kallo na al'ajabi da mamakinta.
sai dai a lokuta irin haka baya bari ya rasa faɗa mata abin faɗa, yanzuma haka ya danne zuciyarsa ya soma furta mata magana.
"Idan har ba su ne suka kawoki ba, mene ne kenan Ayla?"
"Hutu da jin daɗi" ta ba shi amsa a gatsale.
"Haka kika ce?"
"Yah" shi ne amsar da ta ba shi, tana miƙewa tsaye haɗi da tattakawa ta shige ɗaki abin ta hankali kwance.
ZAHIDA
Zaune tayi kan bakin gefen gadonta, tunani kala-kala ne ke zagaye kwanyarta, mafita kawai take nema sai dai ta san wannan ƙaddararren auren babu mai warware shi sai Allah, amma da ace yau tana da iko wallahi sai ta datse igiyar auren ta huta da cin mutuncin da ake yi mata.
Yadda ta tafi tabar Haulat na nan tsaye a wajen ƙiƙam kamar bishiyar da aka dasa, hunnunta na hagu dafe akan kuncinta, tamkar wacce aka tsikara da tsinin mashi haka tayi zaraf ta faɗa ɗakin tana neman layin yayanta, cikin ikon Allah ringin ɗaya ya ɗaga kasancewar daga can bangaren da yake babu wani aiki da yake yi, hasalima tare yake da wata yarinya suna soyewarsu, ganin lambar Haulat yasa shi ɗaga wayar yana karawa a saman fatar kunnensa na dama.
"Hello yaya don Allah ka dawo, Zahida ce ta gaggaura min mari fuskata har ta kumbura." ta yi maganar cikin muryar kuka. A wani irin zafin rai da ƙuna ya soma yi mata magana,
"Me? To akan me ta mareki?"
"Wai dan na iske ta rufe kicin nace ta bani key ɗin zan dafa abu na saka a cikina shi ne kawai babu zato babu tsammani ta wanke fuskata da mari, wallahi yaya har wulgawar taurari na gani ta cikin idanuwana."
"Kan bala...." ya ƙudundumo wata ashariya ya lailayo kana ya ɗora da faɗin,
"Ina zuwa bari zan kirata, kuma ki saka a ranki marinki da tayi bata ci banza ba." bai jira amsarta ba ya kashe wayar ji kake ƙitt. Yana yanke wayar ya shiga neman layin Zahida sai dai kira uku ya yi mata ba ta ɗaga ba, saboda tana zaune kawai taji ɓarin kanta na hagu na ciwo, lokaci guda ta soma ganin wasu irin layuka, ƙarar wayar da yake sake ta'azzara mata ciwon kan ne yasa takai hannu da nufin kashe wayar gaba ɗaya sai taci karo da sunan Ahmad, hakan ya sa ta ɗaga tare da sakata a amsa kuwwa. Ba tare da ya yi mata sallama ba ya soma zazzaga masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.
"Ke har kinyi kaurin wuyan da zaki sanya hannu ki mari 'yaruwata Zahida? Hala kin sha omo ko? To bari ki ji wallahi baki mari banza ba dan sai ta rama marin da kika shimfiɗawa lafiyayyen kuncinta, kuma na baki nan da sakan ɗaya ki ba ta key ɗin, daga yau kar ki sake sanya ƙafarki cikin kicin ɗin idan ba haka ba wallahi sai na sa kin gane banbamcin dake tsakanin shayi da ruwa kuma..."
Ba ta bari ya ƙarasa ba ta katse kiran tare da kashe wayar ma gaba ɗaya tana kifeta, ji take ciwon nata na ƙaruwa da duk daƙiƙa ɗaya, ba ta san me yasa Ahmad sam kwata-kwata baya ganin daraja da ƙimarta ba, ba ma haka ba idan shi baya ganinsu me yasa ba zai sanyasu cikin idanuwan 'yanuwansa ba, idan yaso su ganta da su, wace iriyar rayuwa ce wannan haka? Idan har haka rayuwar auren take wallahi tana alla wadai da ita domin ita ba ta ga ci gaban da ta samu a cikinsa ba tsawon waɗannan shekarun da ta shafe tana tare da shi in ka ɗauke; ƙyama, hantara, tsangwama da zubar mata da aji.
Jin yadda ta yanke masa kirin ya sake hasala zuciyarsa, a ƙufule ya furta,
"Kuut! Ni har za ta yankewa kira, lallai ma ta ga makwancina dole, amma wallahi zan yi maganinki zahida zaki gane Ahmad ba kanwar lasa ba ne."
Lambar wayar Haulat ya laluba ya dannawa kira, kasancewar da man jiransa take ai tana fara ringin ta ɗaga tana karawa a kunne.
"Yaya ya kuka yi da ita?"
"Kina ji na, ki nutsu ki kwantar da hankalinki zaki rama marinki dan wallahi ba ta isa taci banza ba, sannan ki je ki amso key ɗin kitchen ɗin kuma ban yarda ko da wasa ki buɗe mata ba idan tana buƙatar hakan, ke idan bake bama ban lamunce ƙafar wata ta sake taka kicin ɗin ba kinji ko?"
"To yaya" ta ce da hanzari tana shigewa ɗakin, haɗi da sake furta,
"Eh, gani na zo zan amsa ai yaya, to sai ka dawo" tana gama faɗar haka ya katse kiran, ita kuma sai ta doshi cikin ɗakin da zahida ke zaune, tana shiga ta soma cika tana batsewa kana ta soma furta,
"Kin ga ikona yanzu ko ai hakan ya isheki hisabi, nan gaba sai kiyi lissafi da ƙwaƙwalwa ba zuciya ba, kuma kamar yadda na ce miki mari sai na rama ki rubuta ki ajjiye sai na rama tunda har yaya ya furta haka da bakinsa. Abu na ƙarshe ki bada mukullin idan kuma ba haka ba wallahi..."
Ba ta jira gama sokiburutsunta ta jefo mata key ɗin a fuska ba tare da ita ta ankare da haka ba, kwanciya tayi taja bargo ta rufe kanta ruf, ita kuwa Haulat tsugunnawa tayi ta ɗauka tana yada mata magana, kafin ta taka ta fice daga ɗakin.
WAHIDA
Kwance take tayi ɗaiɗai akan kujera mai cin mutum uku, domin kuwa ƙafarta ta hagu ta ɗageta ta aza bisa fuskar kujerar hannunta riƙe da wayar android ƙirar kamfanin Infinix, murmushi ne ya suɓcewa fuskarta da babu yabo babu falsar kyau a tattare da ita.
Shewa tayi ta miƙe zaune kan kujerar tana sake murmusawa. Kafin takai hannu ta taɓa maɓallin da aka dannawa wajen yin voice message ta soma magana,
"Ai wallahi duk macen da take ragawa namiji to mata ta rako duniya, shi namiji idan baki yi masa faka-faka ba ai sunanki sorry nickname naki die, don a sannu zai harɓa miki ƙarinsa wanda ke ɗauke da gubar mutuwa wacce za ta dinga ratsaki a hankali har takai ki kushewa, ke ni fa wallahi namiji ya yi kaɗan ya sakani abin da banyi ra'ayi ba, shi yasa na jima da takawa baban sadik burki da naga take-takensa na son kawo min wargi yo akan me ana zaune ƙalau sai ka ce a garin gaɓa-gaɓa, ki zau zauna garin kallon ruwa kwaɗo yayi miki ƙafa, don namiji ƙarin kuma ne wallahi ya harbeki ya karki har lahira."
Tana turawa ta kece da wata dariya da ba zaka iya gane manufarta ba, kashe datar tayi ta miƙe da hanzari tana ɗora hannu a ƙirjinta tare da zare idanuwa.
"Na shigesu lokaci haka yaja, yanzu yaya zanyi idan baban sadik ya dawo ban masa tuwon nan ba ai na shige su" tayi maganar tana rarraba idanuwa kamar wacce aka kama tayi sata. Da hanzari ta nufi kicin tana harɗe ƙafafu kamar zata kifa ta soma ƙoƙarin ɗora tukunya, addu'a da burin tayi komai akan lokaci take yi, tana kuma fata tayi komai daidai. Ta san ba ta da isasshen lokaci amma yaya zata yi haka zata daure tayi masa tuwon tunda ko da zai fita idan ba ta manta sai da ya sake jajjada mata tuwon alkama miyar ɗanyar kuɓewa yake so, ta saka kifi yaji sosai ga shi ko gyara kifin ba ta yi ba. Haka ta buɗe fridge ta ɗebo kifin yadda zai isheta ta zuba a tunkunya ta saka ruwa daidai wa daidai ta jefa lemon tsami rabi ta ɗora don ya tafaso. Yana tafasowa ta sauke ta tsame ta zuba ruwa ta ɗauraye sosai ta hau gyara shi, nan da nan ta tsayar da sanwar miya tunda gas ɗin nata biyu ne.
Cikin nutsuwa da iya taku ta kammala girkinta tsaf, ta shirya kayan akan dinning table, ta shiga wanka. Tana banɗaki ta ji shigowar motar baban sadik, wata ajjiyar zuciya ta sauke tana hamdala a zuciyarta da Allah Ya sa saida ta kammala ya shigo, shiri wannan ba mai wahala ba ne a wajenta kafin ya shiga ya watsa ruwa ta shirya kanta ta fito fes da ita.
_Wannan littafin na kud'i ne akan #700 idan ya zama complete 1k ne_
8160675983
Maryam Abdulaziz
Opay
[10/2, 5:30 PM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA
©Mai ƙosai
Daga Marubuciyar
•Hafsatul-kiram
•Ƙaddarata ce a haka
•Ƙayar ajali
•Zahra
•Da mun bijire
•Matar Mamman
•Wani yanayi
•A dalilin son zuciya
•Budurwar wawa
_Ban amince a juya min littafi ta kowace siga ba tare da izinina ba, yin haka ya sa'ba doka, a kiyaye._
BABI NA HUƊU
NAZEER
Yana tsaye har tsawon wasu mintuna bai motsa daga yadda ta wuce ta bar shi a falon ba, wani numfashi ya ja kafin ya iya ɗaga ƙafarsa ya soma tattakawa ya shige ɗaki shi ma, sai dai kamar yadda zuciyarsa ke ta hasaso masa ɗakin ilai kuwa haka ya tarar da man ya san ba baƙon abu ne wajensa ba tun da ta saba da haka, ya kuma lura ita sam ko a jikinta. Idan fa har yana son yaga tsaftar waje to sai dai shi ya share da kansa amma ba dai Ayla ba, yanzunma hakance ta kasance, kayan jikinsa ya sauya da wasu ya ɗauki tsintsiya ya soma tattare ɗakin, sai da ya gyara shi tsaf, dan ya yi mopping ya kuma killa ce komai ya ajjiye a bigirensa sannan ya koma falo, shi ma haka ya yi, bayan ya gama ya wuce tsakar gida ya gyara ya soma kiciniyar wanke kwanukan, wanke-wanken ya ɗauke shi tsayin mintuna dan suna da yawa tunda yana da tabbaci har kayan jiya, kai ba ma za a rasa na shekaran jiya a cikinsu ba don ita kwano ya yi sati ba komai ne a wajenta ba. Haka ya kammala tilliƙar aikinsa shi kaɗai Ayla na kwance a ɗaki tana chart, sannan ya shiga ƙoƙarin samawa cikinsa abin da zai ci.
A duk sanda zai zauna ya yi tunani sai yaji yama kasa tunani akan komai, saboda har yau tunani ɗaya ne kawai ke damunsa akan Ayla, shin da man ita haka ta ɗauki rayuwar auren? Shin a gida ba a tarbiyartar da ita yadda auren yake ba? Shin ba a sanar da ita haƙƙoƙin auren ba? Mata da yawa ai ba haka suke yi ba. Kuma yana ganin yadda inna ke yi a cikin gidanta, da yadda take tarairayar mijinta, har yana mamakin yadda soyayyar tasu taƙi tsufa kullum take zama kamar sabuwa.
Da sauri ya miƙe ya ƙarasa kicin saboda ƙaurin da hancinsa ya soma jiyo masa, ya zurfafa cikin tunanin da har ya manta da cewa girki yake yi. Ai kuwa taliyar ta kama sosai dan ruwan dake cikin ta ne ya yi mata kad'an sai ya ƙone ya ba ta damar kamawa, saukewa ya yi ƙasa ya ɗebo ruwan sanyi da ke zube cikin drum ya zuba ya ɗakko matsami wato colender ya tace taliyar, sannan ya ɗakko kasko ya tsiyaya mai ya suya manja, haka ya zuba taliyar a faranti ya zuba manja da yaji sai maggi ya dawo falon, a ƙasa ya zauna saboda shi sam ba mutum ba ne mai iya cin abinci a sama, baya jinsa daidai shi yasa yafi ganewa zama a ƙasan ya ci.
Ya kai loma ta uku ke nan Ayla ta fito tana murmushi ganinsa zaune bai sa ta tsagaita da murmushin ba sai ta nemi hannun kujera mai zaman mutum ɗaya ta zauna tana ƙarewa farantin nasa kallo kafin takai ga furta,
"Nazeer ka rage