An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
FALLASAR
UWAR MIJI
Anty sadiya Garba Yakasai
HAUSAВООK.COM
FALLASAR
UWAR MIJI
Anty Sadiya Garba Yakasai
(Mrs Sani Haruna Fanisau)
1
"yan alkawari cikawa, ga shi na ga Wahiddahi, babu zancen "KYusuf. Na ga da ko ba ya nan, kina kya barin zancensa. Na
san yau dole a gayan labarin wannan irin soyayyar da kuka yi da
Yusuf, alhali da saurayin kawarki ne. yaya aka yi kuka yi aure?
Yaya labarin Hajara da na ji labarin kun yaudara?"
Wahhida ta yi ajiyar zuciya gami da murmushi ta kuma
kalli Rashida, da alamar ta yi mata tambayar da ta fi tada mata
hankali da zarar an ambaci sunan Hajara. Ta runtse idanunta kana
ta bude su ta kalli Rashida, ta ce, "Rashida, kin san an ce komai
mukaddari ne daga Allah? Kuma matar mutum kabarinsa."
"Haka ne." Rashida na kallon amaryar tata 'yar shekara
talatin a duniya. A yanzu har wannan lokacin kyakkyawa ce ajin
farko, idan ka ga Wahiddah ka rantse da Allah ba ta kai wannan
shekarun ba. Har yau Wahiddahh 'yar gaye ce, kyakkyawa kamar
yau, ba ka ce tana da 'ya'ya biyu 'yan tagwaye ba 'yan kimanin
shekaru shida-shida, don steel tana nan kamar da a Wahiddahnta.
"Yaya na ji kin yi shiru ne Wahiddahh?"
"Me kike so na ce maki Hajara."
"Na ce so nake na ji gaskiyar labarinku da yadda aka yi
har Hajara ta hakura bar maki Yusuf ta auri Umar. kuma har gobe
kuke kamar da, har ma kuke business tare, ina mamakin haka.
Wahiddahh ta yi murmushi ta ce, "Ba ki ga komai ba
Rasida. Zumuncinmu da Hajara ba zai taba karewa ba, kuma
kowacce mace kika gani da mijinta, sai dai in ba mutum ba ce, ko
kuma za ta auri mijinta karfi da yaji. To wannan kuwa.
Bara na buga ma Yusuf waya tukunna, na ji sanda zai
dawo gida, kar na saki baki na manta da ango.
"Oh Wahiddah." Rashida ta ce tana rike habarta. "Ya yi
tafiya ne kika gani?"
"Ba inda ya je yana ofis kalau."
"Amma sai an jiwo shi tukunna?"
"Ai ya zama dole muddin zai taso daga Ofis da wuri to,
dole fa ki hakura da inda labarin mu ya tsaya middin lokacin yi ma
Yusıf hidima ya z0.
Okey go ahead, ina jiranki Laila majnun wadda ta wuce
kan wani lafiyayyan tebur na gilas ta dauko 'yar karamar wayar
tafi-da-gidanka ta kara a kunnanta, fuskarta kunshe da murmushi,
ta juyo ta dawo ta zauna tana kallon fuskar Rashida, da ta zura
mata ido, ta ce
"Hello my dear Yaya aiki?.... Sam ba haka bane, ina da
bakuwa ne.... ka santa mana Rashida ce fa.
D.K, ni ma ka san kawai maleji nake muddin ka fita, to fa
bani da sharan sukuni sai dai in su Salwa na guna. Haba Oga karfe
takwas ba ka yi dare ba? You know yadda muke damuwa da su
'yan biyu muddin ba ka nan.
Don Allah kar ka zarce takwas din, kai ma ka san abin da
na tanadar maka. Na yarda Allah ya kai mu.
Yanzu dai nake shirin buga mata na gaya mata kayan da
muka saro sun kare, okey see you Dear." Ta kife wayar tana
dariya. "Yusuf ba shi da dama, har yau bai san ya girma ba," "Ke
din fa kinga yadda kike wani lanlankwayewa, wai ke mai masoyi
ko?"
"Kai Rashida meye laifina ne? Mu fara ko ko kin fasa, na
ji da yin hidimomina?" "A'a ta Yusif, Allah ya huci zuciyarki, ke
nake saurare. By the way ina su 'yan biyun ne? Ni duk na sha'afa
wallahi ban tambaye su ba, suna ina? Don ban jiyo duriyarsu ba?
"Kin san yau Juma'a, suna can gidan su Yasuf, sai jibi za
su dawo.""Oh lallahi kam jininsu 'yan biyun ya hadu da Hajiya."
Wahiddah ta yi dariya ta ce ba dole ba, baki ga fa yadda
ake son Yusuf ba, tun da shi kadai ne gun ta."
"Well fara, lokaci na tafiya," Wahiddah ta gyara gashinta
dake neman rufe mata ido ta ce "Well, da farko ni mutuniyar
Sokoto ce. Mahaifana haifaffun garin Sokoto ne, kuma mu Fulani
muke, don sana'ar mahaifina Mado sayar da shanu da kuma
kiwonsu, duka rigarmu shi ne mai arziki. Sunan mahaifina Mado,
amma asalin sunansa Alhaji Muhammadu, kasancewar matsayin
sunan ake sayewa da Mado. Allah ya hada jinin mahaifina da
mahaifiyata Safiyya, muna kiranta da Innawuro. Mace ce
kyakykyawar łokacinta, duk da mahaifina ma ba baya bane, to
amma a gun mahaifiyata na gado kyau da goshi. Abu daya na
dauko daga mahaifina shi ne tsaho da kalar fatarsa. Fatarmu baka
ce amma ba kirin ba, a'a irin fatar nan mai haske da sulbi, babu
yadda ma za ki iya tantancewa farare ne mu ko bakake ne.
Rashida mu takwas ne gun babarmu, mata hudu maza
hudu, wake da shinkafa muka yi. Babbanmu shi ne. Yaya Najir, sai
Safiyanu da Nasir da kuma Naja'atu da Salma da Hadiya da ni
Wahiddda, sai autanmu Haidar, saboda sunan mahainmu aka sa
masa shi ne muke ce masa Haidar. Allah ya hore ma mahaifanmu
sani saboda haka sun ba mu kyakykyawan Ilmi. Tun muna Sokoto
aka aurar da Yayyena mata, Yaya Naja'atu na garin Bauci tana
auren wani soja, Salima na Bauci tana auren ma'aikacin Lahda, sai
Hadiya dake nan garinmu Sokoto, tana auren dan hakimin
rugarmu.
Yaya Nadir ma ya yi aure yana kaduna kasancewar
aikinsa haka Yaya Nasir shi ma yana nan Sokoto da matarsa. Yaya
Safiyanu ma haka, amma shi ma yana Sokoto. Ni da Haidar aka
taho damu nan garin Katsina, saboda Baba ya gina tankasheshen
gida mun koma, sai dai su Yaya sun ringa zuwa.
Muna zaune a unguwar sarki nan Baba ya gina gida muna
tafiya makaranta ni da Haidar nan muka haďu da Hajara da yake ita
ma kyakykyawa çe kuma kamilalliya. Sai ta shiga raina muka yi
kawance, idan ba'a zo daukarmu da wuri ba, to motar gidansu
muke bi. Ba inda bana shiga a gidansu haka ita ma, har iyayenmu OWSD 2
suka yi kawance.
Kaya iri daya ake dinka mana walau daga gidansu ko
daga gidanmu, komai namu daya ne ga mu da dan jiki, saboda
haka muna shekara goma sha tara - tara muka gama Secondary, sai
jiran sakamako don mun yi alkawarin tafiya Jami'a.
Muna gama makaranta muka tafi Sokoto don ganin gida
nan na shiga kalle kalle kamar bakuwa don rabona da Sokoto tun
ina form one, to yau ga shi na gama, Allah-Allah nake mu je ko na
ga 'yan'uwana. Baba na karatun jarida amma sai da gilas yake
gani, saboda tsufa amma in ka gan shi lafiyayye, saboda kudinsa.
Ya kuma samu kulawa, duk da yana fama da ciwon zuciya muna
kula da shi yadda ya kamata, ba'a bari ransa ya baci gudun kar a yi sm
masa laifi ciwonsa ya tashi.
6
Inna ta kalli Baba ta ce "Dubi ka ga yadda Wahiddah ke
faman zumudl, ni har dariya take ban" Baba ya dan kallan ya ce
"Wa ya ga sabon shiga, ni ma ban san dalilin murnar ba."
"Abba Zango su da Yaya Salima suna farin ciki da kuma
zan je gidan Yaya Naja'atu,""Eh, lallai kam kya yi murna da
haka." Muna hira muka isa Sokoro kofar gidan mu direba ya yi
fakin an gyare shi kamar me. Nan na fito da murna ban saurari
komai ba, gidan Yaya Najir na nufa da murnata ban ma jiwo kiran
da Mani direba yake yi min ba, mutane sai kallona suke suna
mamakin girmana da irin shigar kayan da na yi.
Na fada gidan Yaya nan na ga motarsa a waje, na tabbatar
yana nan, da sauri na shiga ina "Yaya ga mu mun zo", matarsa ce
ta fito da sauri ta tare ni tana "Auta, auta ina ki ka bar min karamin
maigida?"
Na kalli Yaya Umaima na ce "Ina masu kula da Babana
ne? Haidar kawai Yayana nake son gani da 'ya'yana, ina suke?"
Na shiga ina "Hello children." dukkan su suka taso suka
rungume ni da oyo oyo, har kasan kafet suka kai ni muna murna.
Yaya Umaima na kallon mu tana dariya, uwar fitina Murja ta ciren
dan kwali ta shiga ja min ribbon din da na kama kaina da shi, duk
sai da ta yi min kaca-kaca da adon.
Yaya ya fito fuskarsa washe da fara'a ya ce "Wahiddah ke
ce haka kika zankale, kin koma Inna sak," na`mike da fara'a na
gaida Yaya, ya amsa da fara'arsa, ya ce "Wonderful, ina su
Abban?" "Suna gida har Haidar bai san nan zan gudo ba," ta fada
cikin alamun yarinta. Najir ya dubi yadda kanwarsa ta hade duk sai
ya ji kamar ita kadaice mai kyau a garin Sokoto.
"Yaya ina za ka ne?" Na tambaye shi? “Gun su Inna za ni
mana, ko zaki bi ni?" "A'a Yaya sai na huta na taho, don yau ma
daga nan gidan Yaya Halima za ni na gan ta."
"A`a ki bari na dawo na kai ki, ba na son ki fita ke kadai,"
ya zari makullansa. Faisal ya ce "Abbana zan bi ka," dole Yaya ya
tafi da shi. Yaya ya kalli Yaya Umaima ya ce "Na manta, Mustafa
Zai zo ki ce ya jira ni za ni gida su Abba na sun zo.
Ta ce "to zan gaya masa" ni ko ina ta kokarin bude food
flaks din da na gani kan kafet, "Yi a hankali sarauniyar kyau
7
abınem Yayan ki ne a ciki," na yi dariya jin ba'ar da Yaya tai min
"Ni ce ma sarauniyar kyau, Yaya Umaima har da tsokana
tsakaninmu," ta yi dariya "Allah ba tsokana ba ce, don dai ba ki ga
yadda ki ke bane. Wai ina Hajara ne?" "Tana Katsina ita ma
garinsu suka tafi shi ya sa ba ki gan ta ba, amma in kin haihu za
mu zo." "Allah ya nuna mana lokacin, yanzu kuma sai aure ko?"
Na firfito da idona na ce "aure kuma Yaya? Wace ni da aure, ina,
ai sai mun ga karshen biro. Ko zancen samartaka ma ba na yi,
balle in sami mijin auren."
"Wa zai bar ki yi karatun Baby?" "Babana mana," "Shi
Abban ne ya ce?" Na hadiye burabuskon bakina, na ce "kwarai
kuwa, muna komawa za'a sai min form."
"Da kyau" 'Yar sallamar da muka jiyo ce ta katse mana
hirar. Yaya ta ce "Shigo mana Mustafa kamar wani bako." Ya
shigo kaina na duke, saboda haka ban ga fuskarsa ba. Ya ce “A'a
ta Najir bakuwa kuka yi ne?" Ya fada daidai lokacin da yake
kokarin zama.
"Ba ka santa ba ke nan?" Yaya ta tambaye shi, “Ai ko a
jikina ban taso ba bare ya ganni, ko ni na gan shi, "Don Allah
wacece wannan?" "Kai Musty to kanwarka ce Wahiddah," "wacce
Wahiddahr?" ya fada a gaggauce, "Wahiddahh dai ta gidansu
Najir."
"Ita ce haka I can/t believe my ears,""Wallahi ita ce, to
don haka na dago don na ga mai yi min magana. To a nan na ji
yawun bakina ya kafe, don tafiya birnin tunani da na yi waye
wannan? Shi ma kallona yake kamar sabon maye, har na ji kunya
na sunkayar da kaina kasa.
"Musty yaya ne?" Ya dan motsa ya ce"Ba komai
Umaima," ta yi murmushi kawai ta ce "Ina fa ba komai," na dago
kaina na ce "Ina kwana?" ya ce "lafiya kalau Wahiddah, yaushe ku
ka zo garin mu?"
Na yi murmushi na ce dazu muka zo, yaya su Abba? Suna
nan lafiya, ice ko za ki yi mana dan kwana biyu a garin namu, Eh,
sati daya zamu yi mu koma, sati daya Wahiddah ai ya yi kadan.
a'a bai yi ba na ce masa, ya ce to ai shi ke nan.
8
Ke madan ina angonki? Ya tafi can gidan gaida su Abba
ya ce ka yi jiransa, ya kamata ni ma na je na gaida su kar na yi
laifi, Wahiddah zo mu tafi ki raka ni mana? A'a ni ba yanzu zan
tafi ba, haba kanwata kya ki raka yayan naki gida kuwa? Dole na
bi Yaya Mustafa ba don na so ba.
Duk na dabarbarce a motar, ban san dalili ba, sai da na
tsinci kaina ina jin kunyar Mustafa, abin da ban taba ji ba a
rayuwata. Ya kula da hakan sai ya shiga zolaya ta, wani na tanka,
wani kuma na yi masa shiru. Ya dan kalli fuskata cikin sigar so, ya
ce "waye gwanin ki?" Na ce "Ban gane ba," nufina waye surikin
namu a can Katsina? Na ce ba ni da wani gwani, ni sai biro da
takarda," Mustafa ya sheke da dariya, ya ce "Wahiddah baki da
dama, kin taba ganin biro da takarda sun zama saurayin budurwa?"
na ce kwarai ma kuwa", ya ce a'a don Allah abar biron da takardar,
ga wani masoyin kin samu," na kalle shi na ce "Waye? Ya kanne
ido ya ce "Ni Mustafa ina ciki, ko na yi maki tsufa?" Na rasa bakin
magana sai kawai na sunkuyar da kaina. Hakika Mustafa ya hadu
sosai, illah gaskiya ba na son soyayya, muna farawa aure za a yi
min, shi ke nan na rasa karatuna. "Me ki ke tunani ko ban yi maki
ba? Na ce "A'a kawai dai ba na soyayya, ya dan bata rai kamar
yaya ba kya soyayya? Nufinki ba kya so na kе nan na hakura?"
Na kalle shi naga duk ya rude na ce "Ba haka nake nufi
ba, nufina muddin ka nuna ma su Abba da Yaya cire ni za'ayi a yi
min aure, ni kuma karatuna nake so.
Ya dan saki rai, ba komai ba zan shaida masu ba, har sai
kin fara Jami'ar in ya so sai a yi maganar tamu, kin amince?" Na
daga kai na dai-dai lokacin da muka isa kofar gidanmu. Yaya ya
fito ganinmu ya tsaya ya ce "Kai da na ce kai jira na? Ka san dole
na zo gun su Abba?" Ni ko ban saurare su ba, na wuce saboda
kallon da Mstafa ke min kar yaya ya gano.
Inna na damu na taddata na dan jingina kan cinyarta na ce
"Inna kamar kin san ina son shan furar nan," ta yi dan murmusi ta
ce "Abbanki ya sani damu, amma ta ishe ku, har yana fada wai me
ya sa yayanki bai taho da ke ba, ya bar ki a can, shi ba ya so ki
ringa nisa." Nnayi dariya na ce "Ba ga Haidar nan ba," "A to, ai
kin kwace mini mai gidan nawa",", na yi dariya na ce "Ina Abban
9
yake?" "Yana samansa", na mike da guduna na nufi sashin Abba
kai na ba dan kwali, dai-dai lokacin su Yaya suka shigo.
Mustafa ya kuran ido cikin sha'awa ya ce "Yi a hankali
kar ki fadI." na dan waiwayo shi na yi dariya na haye sama. Yaya
Najir ya kalli Mustafa ya ce "In ka biye ta Wahiddah, sai ka sha
kallo. Tun tana karama Allah ya sanya mata fitina kamar biri, ka
ga har yanzu ganin kanta take kamar yarinya."
"Haba Najir shekarunta nawa? She steel a Baby, sha tara
fa. In da an yi mata aure da wuri da yanzu tana da 'ya'ya amma to
kai meye ra'ayinka?"
"Kawai ta samu miji ta yi aure da ya fi mana kyau” Daidai lokacin da suka shiga falon Inna tana kallon talabijin suka yi
sallama Inna ta gyara lullubinta ta ce "Ku shigo mana kai da
wannan yaron ne." kasancewar shi ma ba ta fadar sunansa wai
kara, dalilin babban abokin danta ne na fari.
Inna yaya kuka zo gida lafiya? Lafiya kalau ina manyan
naku ice ko suna lafiya? Lafiya kalau Inna basu san da zuwan ku
ba. da sun zo ai ba komai muma bamu jima da zuwa ba, kai ka kai
su gun Abban naka ne? a'a nan muka fara zuwa, to kuje yana sama
ku gaisa mana, Mustafa cikin jin kunya ya mike ya ce bara muje
mu gaisa wai kuwa anyi bikin naka? Najir ya yi sauri ya café ina
sam ya ki yadda har yau kuma bai yi ba kin gan shi nan.
Mustafa ya shiga hirar Yaya ai gaskiya nee kake harara ta.
Inna ta ce to lallai ba ka kyuta ba, don Allah a yi kokari a yi ka ji
ko, zaman haka ba shi da wani amfani sam. To Umma insha
Allahu za'ayi. Allah ya taimaka ai komai lokaci ne kuma shi aure
ba a yi masa garaje. Mustafa ya hankada Najir suka hau sama
wallahi Najir ba ka da sirri, me ye na gaya ma Inna gaskiya. To
kayi auren ne?
Hayaniya suka jiyo, ni da Haidar muna kallo a falon
Abba. Mustafa ya zuban ido yana wani murmushi, nan kunya ta
dan kama ni na sakı Haidar. Ke uwar kokawa ina Abban? Yaya ne
ya tanbaye ni. yana bandaki yanzu zai fito. Suka samu kujeru suka
zauna. nı ko da na koma kuryar falon na makure saboda
mayataccen kallon da nake samu daga Mustafa.
10
Ke kin fasa zuwa baccin ne? Ban fasa ba Abba P כב PU
bari gobe ka kai ni wai shi ba zan kwana ba, Uhum ba zan maki karya ba unguwa za mu da Mustafa sai dai Manu ya kai kı
Na turfune, gaskiya kai za ka kai ni, na ce maki bani da
lokaci ba ga Manu ba, Abba ya fito kai meye na yi mata ihun
haka? Yaya ya ce wai sai lallai na kai ta gidan Yayarta Salima, na
ce ba ni da lokaci ga Manu nan ya kai ta shi ne take wani bori.
Baba ya ce ba ka ganin yarinya ce ko ba za ka kai ta ba ai sai ka lallaba ta ba ka tsaya kana mata ihu ba.
Abba ka fa sangarta Wahiddah da yawa to in daina ni na kai ta, da dai Yaya ya ga Baba ya yi fushi da shiri ya ce Allah ya huci zuciyarka tashi mu tafi.
Ni kuma na yi hajin nawa na ce na fasa na shiga daka na yi sororo jikin kujerar Babansu. Ban san ka zama babban banza ba
sai yau ashe in har na mutu ba za ka iya kula da ita ba balle Haidar.
Nan jikin Yaya Najir ya kama rawa har na tausaya masa ya ce ka yi hakuri Baba, na yi kuskure ya juyo gareni ki yi hakuri Wahiddah.
Na share hawayena na ce na hakura yaya don Allah ni ma ka yi hakuri ka san ba na so ka tafi ka bar ni ne.
Yaya ya yi murmushi ya ce shi ke nan ya wuce Baba ga Mustafa ya zo gaisheka, wanne Mustafan? Baba Mustafa abokina
na gidan Alhaji Umar, Oh oh ka ce abokinka tun kuna makaranta shi ne yazo gaishe ni.?
Mutafa ya durkusa har kasa ya gaida Baba nan suka fara hirar wancan da wancan, in takaice maki Rashida Allah munji dadin hutun mu kuma baki sani ba soyayya mai karfi ta shiga tsakanin mu da Mustafa, ranar da za mu tafo kamar anyi masa mutuwa
Dukkan 'yan uwana sun zo yi mana sallama nan muka bar Haidar gidan Yaya Najir tun da ya ga su Faisal ya like dole muka taho muka bar Haidar
Bamu iso Katsina ba sai yamma likis tun kan na shiga gida na tsinkayo muryar mutuniyar tawa, da gudu muka rungumi juna muna tsalle. Hajara ta ture ni ta ce ke don Allah tafi can kın
11
barni da kewarki, yi hakuri kawalliya wallahi ban so haka by the
way ina Yusuf dinki?
Ta share hawayenta ta ce mun rabu, kunyi me? Na
tanbaye ta, mun rabu na ce maki, me ya faru fada kukayi? Ta
jijjiga kai zuwa nayi na same su da wata da nayi masa magana sai
ya ce da ma yana son ya gayan shi gaskiya ba ya sona, na tambaye
shi me ya faru tsakanin mu? Sai ya ce min kawai shi ba zai iya ci
gaba da ni ba don Allah nayi hakuri ya canja ra'ayi.
Na ce masa wata ka samu? Ya ce min shi ba wacce ya
sake illah ya gaji da sona na shawo kansa amma ina sai ya ce min
wai is over na yi tsaki gwarma da Allah ya sa ban san shi ba to ke
me ye na kukan ki ki hakura kawai ki yi fatan Allah ya hada ki da
rabonki, ayya Wahiddah ina ga ba ki san yadda na ke son Yusuf
bane ina ga ba zan iya rabuwa da shi ba.
Ba za ki iya me ba? Don Allah kar ki ba da ni, wallahi ba
zan iya ba ina ga fushi yake da ni amma na san zai wuce zamu
shirya ne.
To Allah ya sa, wanda bai ji bari ba ai ya ji hoh na ce da
ita ta yi dariyar karfin hali ta ce yaya labarin Sokoto? Nan na saki
murmushi na mance da wani zancen Yausuf na shiga lassafa mata
duk abin da ya faru a can, ta yi shewa ta ce at last Wahiddah na
zancen soyayya lallai za'ai ruwa da kankara.
Kin san me ya faru Rashida? Rashida ta girgiza kai cikin
alamar Wahiddah ta ci gaba, ta ji yadda aka yi suka hadu da Yusuf.
Wahiddah ta kur61 ruwan lemon da aka kawo musu ta ce
bayan mun yi sallama da Hajara ta tafi ni kuma na fada gyaregyaren daki na bayan na gama na ce me zan yi ba bacci ba, bacci
mai nauyi ya kwashe ni ban farka ba sai da Inna ta shigo da kanta
ta ce to Wahiddah a tashi a yi sallar asuba baccin ya isa haka.
Na dan murje ido na alamar baccin bai ishe niba na ce
Inna ta manta ina fashin salla tun jiya. Inna ta ce oho wallahi
ko na manta, amma dai ya kamata ki tashi ki yi wanka ki je
Abbanki ya ganki a huta. Na ce to Inna gani nan fitowa Allah tilas
Inna ta fita, ina ganin fitarta na koma baccina, ban tashi ba sai
karfe lakwas. Na yi salati na mike duk jikina a mace na zagaya
12
bayi na shiga wanka, don mun yi za mu hadu'da Hajara yau d
gidansu, saboda haka na shiga da sauri na watsa ruwa na fito.
Ina tsane jikina wayar jikin gadona ta dau ruri, na dan ja
tsaki na ce wane gwanin ne da sassafe haka. Kamar kar na dauka,
sai na canja shawara na dauka a wulakance na ce wanene? Haba
gimbiya fada ne da ke haka lallai zan yi aiki Babba, na dan saki
murmushi hadi da ajiyar zuciya na ce Musty kane? Ni ne gimbiya
yaya kuka zo gida?
Well lafiya sai dai ..... nai dariya, ya ce dai dai me? Fadi
mana, shi ke nan abar maganar mu shiga wata, ba zai yuwu ba sai
an gayan kafin na cigaba, O,K dama ca zan yi sai dai ke warka shi
ke nan ko? Ya yi dariya ya ce amma da za'a ce min bakomai bayan
gashi an gayan abu mai dadi da muhimmanci.
Na dan fada gado na ce kai Musty me ye abin dadi anan
ya ce kince kina kewata kin ga ke nan ina da matsayi me ki ke yi
ne honey ya fada a sanyaye?
Na